Complete Hausa Novels

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Babban Yaro Part 2.txt

Chapter 49 of 69

Hada ido muka yi dashi yana yana tsaye jikin kofa Yana kallonmu jikin sa sanye da shadda fara tas! K'afafun shi sanye da takalman me gidan ya tsaya baki , yayi kyau sosai da sosai,
Idan ba idona ne yayi kin gizo ba sai naga ya fad'a idanunsa sun zurma ciki, a hankali ya k'araso kusa da Umma hade da Dan risanawa yana gaishe ta.
Granny ma k'araso wa tayi tana tsokan Mimi alhalin itama Cikin zuciyar ta daurewa kawai take, tun kafin Suzo take share hawaye: Cikin k'arfin hali aunt Hauwa take rarrashin Mimi hade da karfafa mata gwiwa, shi kam Amjadu suna gama gaisawa da Umma bar gurin.
Motar sa ya nufa, ya zauna bayan ya kunna karatun alk'urani, me girma yana saurara

Muna zaune aka zo a tafi da Mimi.
Duk muka bita da addu'ar samun nasara.

K'arfe Biyu da kwata Dr ya futo ya same mu inda muke zaune.
Umma ya kalle ta da ta zuba masa ido,Sam ta manta da wata surukutaka dake tsakanin su, tsugunawa yayi suka gaisa a mutum CE.
Tace"Ina fatan anyi Lafiya Dr."?
Cikin kwantar da hankali yace." Alhmdullahi anyi nasara insha Allahu an samu damar Ciro k'wayar hallitar da izinin ubangiji d'ayan zai cigaba da rayuwa cikin hukuncin Allah kuma zata haife shi lafiya."
Ajiyar zuciya Umma ta sauke tana tayi ma Dr godiya duk ta rasa yanda zata yi
Sauri kawai nake na idar da sallah ta tun a sujjadar k'arshe nake godewa Allah.
Granny da aunt Hauwa baki har kunne sai addu'a suke masa.
Ciki ya koma ya futo da wani Abu cikin kwali. Kai tsaye hanyar futa ya nufa.
Motar Amjad ya nufa domin yasan yana nan.

Yana ganin zuwan Jahid din gurin shi ya futo daga motar yana bin hannunshi da kallo cikin fad'uwar gaba.

Bakinsa na rawa yace." Meye wannan."?
Jahid yace." Alhmdullahi wannan hallitar ce da aka ciro dole zaka gani sannan ka binne domin ubangji ya soma fidda masa hallita ."
Zuciyarsa babu dad'i yace." Jahid Dole sai na gani hummm? Kawai a binne ubangji Allah ya bani wani."
Cikin sanyin murya ya fad'i maganar.
Ajiye kwalin Jahid yayi ya dafa ka fad'ar Amjad d'in yana fad'in"Colm down Aboki na, ba dole sai ka gani ba, hakkin kane Dole a nuna maka, amma insha Allah ni anan zan sanya a binne shi, ka kwantar da hankalin ka."
A tausashe ya k'arasa maganar.

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yace." Ya jikin Momyna. " ? Dr jahid yace." Alhmdullahi jikinta da sauki hakama babynta insha Allahu zata samu kulawa ka kwantar fa hankalin ka."

Hamdala yayi a fili yana godewa Allah yace." Muje in ganta OK." Ganin yanda ya daga hankalin sa yasa Jahid din kasa yi masa musu, domin babu halin yace. Masa ba'a futo da ita ba tukkuna, dole ya jagoran CE shi har dakin da Mimi take kwance.

*22/11/2019*
[11/23, 10:28 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*MALLAKAR_ BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*

*60*

Lokacin da zasu shiga dakin da Mimi take ji nayi kamar in biso domin na k'agara na ganta, Ashe bani kad'ai ba har su Umma, nauyi ya hanata magana granny tace"Muma zamu iya shiga gurin ta ne."? Mujahid yace." A'a granny Ku bari a futo da ita shima Dan dai mijinta ne, kuma in na hanashi zai iya shak'eni ga yadda yake muzurai."!
Dariya suka yi ni kam yak'e kurrum nake yi nasan da babu shi tsaf! Mujahid zai shiga dani gurin Mimi.

Kusan Mintuna ashir yayi a ciki sannan ya futo domin shi Mujahid din tunda ya raka shi ya futo ya koma bakin aiki. Kallonsa muka yi dukaninmu,
Tsayuwar sa ya gyara kusa da kakarshi ya futo da wani farin hankici daga aljihun sa, yana goge fuskar sa.
Granny tace"Ya jikin nata ta farko amma."?
Girgiza kansa yayi kamar ba yaso yace." Bata farko ba amma dai Jahid yace." Zuwa magariba zata farko insha Allah."
Hamdala tayi tana kallon mu cike da farin ciki tace"Kunji abunda Mujahid yace ko. ? Muna sauraren ikon Allah."

Umma tace"Shine abun dubawa kuma shine abun godiya." Shiru ne ya ratsa gurin na minti biyu kana yace." Zan wuce ina sa meeting da ma'aikatana bayan sallahr isha'i." Umma tace"Ubangji Allah yayi maja jagora mun gode kwarai."

Da "Ameen yake amsawa ya futa daga reception din cikin tafiyar shi ta zaratan maza. Yanzu ya samu kwamciyar hankali kuma jakinsa na bashi cewar akwai nasara kan aikin da a kaiwa Mimi fatan shi ta farfado lafiya domin yanzu a zuciyarsa yaji yana yi mata wani sahihin so na gaskiya ga wani mugun tausayin ta da yake ji mussaman idan ya tuno rayuwar ta, ubanta ya gudu ta taso bata San mahaifiyar ta ba, shiyasa kullum yake jinjinawa Ummansu Asma'u uwace ita me baiwa D'a mama a yanda ya fuskanta yanda ta rike Mimi tamkar ita ta haifeta tana kula da ita sosai kular da bata yiwa 'yar cikin ta Asma'u.

Aikuwa kamar yanda Dr ya fada bayan sallahr magariba Mimi ta farko kuma sa sunana a bakin ta, take Jahidi ya zo ya kira ni.
Ina shiga dakin muka hada ido da ita. Idanunta duk sun kode sunyi ja sosai.
Kallona take yi har na karasa kusa da ita gefan bed din na zauna hade da kamo hannunta na rike tamau.
Nace"Mimi ya jikin naki."?
A hankali tace"Da sauki Habibty kice wa Jahid ya bani ruwa nasha yak'i ya bani. "
Mujahid na kalla cikin tuhuma yace." Ba yanzu za'a bata ruwa ba."

Hannuna ta rike lebanta duk ya bushe, Mimi tayi mutukar bani tausayi. Nan na zauna ina rarrashin ta, su Umma suka shigo dakin. Tunda ta ganta hankalin ta ya kwanta.
Granny kuwa fad'i take"Sannu kinji ko kishiya ta ko wace haihuwa da irin ta sai dai fatan Allah yasa Ku gama lafiya."

Dr Jahid futa yayi daga dakin ya barmu da Mimi. Hannuna na nata bacci ya kara dauke ta.
Kin tashi nayi daga gurin bare in cire hannuna daga nata har wajan k'arfe goma na dare, Amjadu ya shigo lokacin granny har ta soma gyangyadi.

Sallamar sa naji dakin gabana ya fad'i , ciki-ciki na amsa masa, domin Lokacin Umma na toilet aunt Hauwa kuma ta tafi, muryar baban su Munnu na ji sun shigo tare.

Amsawa nayi da sauri na juya INA masa barka da zuwa.
Kan Mimi ya tsaya cike da tausayi da al'ajabi yake fadin"Ashe Abunda ya faru dake kenan Mimi."
Umma dake futowa daga band'aki tace"Sannu da Zuwa."
Baban su Munnu ya juya suna gaisawa da Umma.
Nan yake jajan ta mata abunda ya faru yana kara addu'a ga Mimi tare da fadin"Sam shi bashi da labarin abunda yake faruwa in banda shi Amjad din ya fada masa a waya.

Umma tace"Alkairi shi ake fada bata tashin hankali ba, duk da dai nasan hakkin Ku ne a fada muku munyi laifi."

Baban su Munnu yace." Ya wuce yanzu babu Lokacin yin k'orafi ta lafiyar ta Muke ubamgji Allah ya bata lafiya ."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.