Trending Hausa Novels

Lu'u Lu'u Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LUU LUU BOOK 1 COMPLETE BY HUGUMA.txt

Chapter 45 of 79

Ci gaba tayi da kallon mammina kawai,abinda ya bawa mammina damar karantar abinda yake kai kawo a zuciyarta.

"Tsoron me kike biftu?,kin manta alqawari na?......kina zaton idan sultane zai iya manta alqawarin dake tsakaninku ni zaituna zan iya mantawa?......duk runtsi duk tsanani ina tare dake akhnan" Sosai maganganun mammina suka karya mata zuciya. Bataso tayi kuka,don batajin ya kamata zuwa yanzu ta fara samun rauni har haka a zuciyarta,amma kuma tana buqatar kafadar da zata jingina da ita don samun sassaucin abinda takeji,don haka ta qara taku biyu,ta aza kanta saman kafadar mammina din.

Hannunta ta dora saman sassalkar sumar akhnan dake da tsaho santsi da kuma sheqin baqi tana shafawa a hankali,kaman yadda uwa keyi ga qaramin yaronta da sigar lallashi.

"Indai ina raye ba wanda zan bari ya aurar dake ga mijin da baki aminta dashi ba......ko baki fada ba yalwa ta gayamin.......sultane mahaifinki ne......indai ba zugashi akayi ba,bazai taba aurar dake ga mijin da baiyi miki ba......" Saita daga kan akhnan daga kafadarta tana riqe hannayenta dukka biyun.

"Ki sa a ranki da mahaifinki kike magana.......ki bude bakinki ki gaya masa bai miki ba!". Ta qarasa maganar da wani sauti dake nuna akwai wani abu daban daya taba zuciyarta.

Shuru akhnan tayi tana duban tsakiyar qwayar idanunta,irin duban da a yawan lokuta da dama yake qarfafa mata gwiwa tun daga yarintarta. Kallon idanun mammina din na bata wani irin qwarin zuciya tare da bata qarfin gwiwar aikata abinda take ganin bame yuwuwa bane ko ba zata iya ba.

"Shirya muje.....ya aiko a kiraki,ni zan tsaya miki koda hakan yana nufin yin baqin jini,baqin jini a idanun sultane.......baqin jini a idanun morsa safiyyah".

Zame hannunta tayi daga na mammina,iya Kiran sunan morsa safiyyah kadai ya sake harzuqa zuciyarta,sai ta juya da baya da sauri,ta kai hannunta kawai kan dogayen rigunan dake zube saman gadonta,wadanda dukkaninsu sabbi ne,birra ta soma gyarasu zata zuba mata a closet dinta tace ta barsu ta fice ta bata guri.

Duk yadda take jin zuciyarta ta tsayu amma sai fargaba ta fara ratsata sanda suke nufar sassan sultane din. Tsinkewa kawai takeji zuciyarta tanayi zuwa pieces a cikin qirjinta.

Ta fahimci hakan mammina.......saita damqe hannunta da suke cikin nata tana magana qasa qasa.

"Karkiji tsoro......ina tare dake" Maganar data sake saukar da wani dan guntun sassauci kenan cikin ranta.

To amma daga sanda mammina tayi sallama cikin parlor din sultane din,ta kuma hangi morsa safiyyah zaune a gefansa tana sake tsiyaya masa ruwan markadaddiyar apple sai taji tana neman rasa duk wani qwarin gwiwar tata saboda abubuwa biyu.

Abu na farko yanayin fuskar sultane din. Wani baqon yanayi ne da sai me zuzzurfan kusanci dashi......me zuzzurfan hangen nesa da tsinkaye kuma shine zai iya karantar kwantaccen bacin ran dake kai kawo saman fuskar tasa. Duk da cewa ga me gajeran nazari wanda ba wata zuzzurfar alaqa Taakaninsa da sultane din zai dauka yanayi ne kawai irin na yau da gobe.

Morsa safiyyah. ....wanzuwarta a gurin gabanin zuwansu ya sake rusa mata duk wani kyakkyawan zaton da ta shigo dashi.

Ko sau daya......koda lokaci qwaya daya bata taba saqa alkhairi akan matar ba. Da yawan dagulewar al'amuranta tana alaqantashi da morsa safiyya din,alkhairi bai taba gifta mata ba muddin tana a gurin.

Idanunta ta dauke a hankali tana lumshesu,tana kuma takawa zuwa ga sultane din bisa qwarin gwiwar mammina da kalaman da take gaya mata qasa qasa. Kalaman da ba lallai kai dake kallonsu kai tsaye ka dauka wani magana takeyi da ita.

Cikin qasa da second uku wata irin shimfidaddiyar fara'a ta wanzu a fuskar mammina,idanunta tsakanin sultane da morsa safiyya.

"Sannu da hidima" Tace da morsa safiyya dake qoqarin rufe tambulan din lemon data gama zubawa sultane.

"Kece da sannu zaituna....." Ta amsa mata da salon daya sanya mammina jin wani iri. Kasancewarta mace me wata irin halitta da tasha banban data mata da yawa,irin matan nan da sukan iya shanye komai su kuma jure jin komai daga bakin wanda sukaso,saita maida mata da martanin murmushin,ta kuma qarasa a nutse daura da sultane tana yiwa akhnan mazauni daura dashi din,daidai sanda take cewa.

"Muna neman sassauci da afuwa ranka ya dade........na shigo ba tare da ka nema haka daga gurina ba......zuciyar d'iyata cike take da fargaba da kuma zullumi,bata da qwarin gwiwar tunkarar mahaifinta sam a wannan ranar" Takai qarshen zancan tana zame yatsunta daga cikin na akhnan,ta kuma ja baya kadan alamun dake nuna tafiya zatayi.

"Ina zuwa?" Sultane din ya tambaya kanshi tsaye yana ajiye tambulan din hannunsa.

Duk da yadda morsa taqi jinin yadda dukkan wata kebantacciyar alaqa ko dangantaka data shafesu mammina ke ciki tsulum tsulum,amma ita kanta a yau din tafi buqatar zaman mammina akan fitarta.

"Komai na d'iyarkin yanzu dake za'aci gaga da yinsa......domin shaida ta zama a wuyanki" Ya qarasa maganar yana gyara zamansa,irin zaman cikakken basarake,yana mata kuma nuni da kujerar dake kusa da morsa safiyya.

A hankali ta dawo a nutse,taqi bari wannan murmushin nata yabar kan fuskarta,ta zauna a nutse tana fadin.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Lamarin d'a da uba koda mu iyaye ba kasafai aka fiya son saka kai a ciki ba......shi yasa ban tsaurara ba wajen son sanin laifin da ayau tayi ba". Ta qarasa maganar tana sadda kanta qasa a girmame.

"Bana tunanin tsakanin wannan awannin abinda tayin zai buya daga idanu da kunnen sauran masarautu........" Yayi maganar cikin bagararwa,yana karbar toothpick daga hannun morsa wadda ta miqa masa,dukka tana yunqurin shanye abinda ke taso masa.......tana ta qoqarin shanye bacin ranta ne kawai da controlling din kanta.

Wacce irin gurbatacciyar soyayya ce wannan?,wacce irin mayaudariyar qauna ce ta banza da wofi?.......wanne irin lullubin biri ne wannan?,wanne irin nau'in kisan mummuqe ne wannan?. Dukka lokaci daya morsa safiyya ta yiwa kanta wadannan tambayoyin daidai sanda take zube kallonta kai tsaye akan mammina din tamkar a fili tayi mata dukka wadannan tambayoyin.

Tambayoyine da zataso ace ba cikin ranta ta furtasu ba,tambayoyine da take buqatar bayyanasu da sautinsa don sultane yaji........to amma kuma fitar tasu tayi imanin ba wani sauyi ko gagarumar rawar da zai taka da zata kawo irin canjin da takeso.

A jikinta mammina din taji?,ko kuma tana shirye da karban kallo makamancin wannan daga gurin morsa din?,sai kawai ta daga nata idanun,suka kuma fada cikin na morsa safiyya.

A cikin su biyun,ba wanda bai tantancewa kansa kalar kallon da dan uwansa yakeyi masa ba.......ba wanda bai qissima abubuwa da dama ba,amma kuma sai mammina din ta maye gurbin kallon da jifan morsa Safiyya da wani irin murmushi da ba komai cikinsa sai zallar nuna sanyi da rashin daukan abubuwa da zafi,sannna ta cire idanuwanta daga cikin nata,tana maida dubanta ga sultane din da ayau yake zaune cikinsu da fuskar da yake zama a fadarsa cikin talakawansa.

"Ya kukayi da abood ramadan?" Ya jefa tambayar ga akhnan,wadda banbamcinta da tambayar awanni nawa ya rage ta mutu kadanne.

Dame zata amsawa sultane?,bayan tayi imanin yasan komai.....ya kuma ji komai.......yanayinsa kadai ya gaya mata hakan. Shuru parlor din ya dauka,tamkar babu wani sauran ne rai daya rage a gurin.

"Ya kukayi da abood nace!" Sultane ya sake tambayarta da wata irin tsawa data kada 'ya'yan hanjin dukka su uku dake gurin,saboda wata dabi'a ce dake baquwa ga dukka halayyar sultane din.

"Bap......bapp.......iii"

"Baiyi miki ba" Ya fadi bawai da sigar tambayarta ba......a'ah da sigar bada amsa ta kai tsaye.

Sake yin qasa tayi da kanta tana jin kamar zata narke,tana jin dama qasa zata tsage mata tabbas da zata shiga ciki ta buya daga tuhume tuhumen sultane din.

"Wannan shine ya baki qwarin gwiwar daga hannu ki mari baligin namiji?!!!!" Ya daka mata wata sabuwar tsawar,abinda ya sanyata curewa guri daya tana kuma cukuikuye mammina duk da dan nisan tazarar dake tsakaninsu.

A lissafin rayuwarta gaba daya,sau daya tak zata iya tuna an taba mata tsawa. Tsawa......fada ballantana uwa uba dukka dukkansu wani abune sabo kuma baqo cikin dictionary din rayuwarta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.