Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: KWAI CIKIN KAYA BOOK 2.txt
Chapter 10 of 25
Page 33
...............A ɓangaren gidan Dad komai ya ƙara caƙuɗewa, yakasa barin ƙasar koda kuwa zuwa Niger ne, komai Shahudah batayi yanzu banda aikin kuka da kiran Jawaad, ta tabbatar musu indai basu rabata da Habib sun maidata gidan Jawaad ba saita kashe kanta, kullum cikin lallaɓata suke da mata alƙawarin samun Jawaad duk rintsi kuma har ƙarshen rayuwa, zakuma su rabashi da bily koda tsiya dan ita kaɗai ta mallakesa, acewarsu tabari ya gama hayaƙin rashin mutuncinsa yanzun sunada hanyar maganinsa ne.
Qaseem kan tun bayan barin Jay asibiti da Bilkisu ya shiga wankama Doctor mari akan ya buɗe masa ƙofa, cikin gigitar azaba Doctor ya buɗemasa ƙofar ya fita, koda ya fito sai bai iske su Jawaad ba, cike da mahaukacin gudu ya ɗauka motarsa ya fice daga asibitin. Marukan da yayma Doctor ne yasaka sauran Doctors ɗin asibitin alwashin ɗaukar mataki, atake suka kira police, ko jinin dake fita ta hancin Doctor basu tsaida masaba saida ƴan-sandan sukazo suka gani.
Qaseem daya fita yana can yana bilayin neman su Jawaad titi-titi bayan yaje gidansu ance Jay baizo nanba, ya nufi gidan Jay na A.Y street ne ƴan-sandan da aka tura kamashi da yawun hukumar lafiya ta ƙasa sukai ram dashi, duk yanda yaso musu taurin kai da nuna musu shiɗin wanene ɗan wanene sunƙi saurarensa. Dan kuwa dai shima Doctor ɗin da ya mara ɗan wani ƙusane a ƙasar, gashi ma'aikaci a asibitin gwamnati, shiyyasa kamun Qaseem ya taho tun daga sama.
Yau tsahon kwanakin Qaseem biyu kenan a police station batare dasu Dad sunma saniba, su duk tunaninsu Qaseem na gidansa ne tunda fushi yake dasu bazasu ganshi a yanzuba.
Salman ma dai daƙyar suka lallashesa ya haƙura da batun barin ƙasar, dan yacefa shi lokacin mutuwarsa baiyiba da zai tsaya ɗan-fir'auna ya sakashi cikin jerin waɗanda zai watandarsu kamar kajin salla, da farko Mom masifa ta fara masa, da dai taga babu ci sai ta koma lallaɓashi har Dad ɗinma, da ƙyar ya haƙura akan shifa da yaga wani motsi zai ware abinsa, da wannan ajandar tasa suka yarda, ba komai yasa basason yay nesa dasuba sai sanin halinsa musamman akan shaye-shaye, shiyyasa basason yay nesa dasu, ALLAH dai yasosu abin bai nisaba suka tsaya kansa ya haƙura.
Momy dake haÉ—ama Dad tea takai dubanta garesa, yay shiru tamkar babushi a d/table É—in, gaba É—aya rikicewar da gidan yayi yasa sun fita hayyacinsu daga ita harshi, wani irin jin Æ™arin tsanar Bilkisu tai a ranta, dan kuwa a ganinta duk itace sanadin komai, shigowarta rayuwarsu ne ya tarwatsa musu gida, da Dad bai jajubo musu itaba da yanzu suna zaune cikin kwanciyar hankalinsu, siririn tsaki taja tana mai dangwarar masa da kofin tea É—in gabansa. Kallonta yay da mamaki, yace, “Lafiya kike tsaki? Bayan kinsan abinda nafi tsana kenan a rayuwata?â€.
Momy ta kuma jan wani tsakin tana cigaba da zuba masa farfesun bindin sa ɗin da takeyi, “Bakai nakema tsakiba nikan Dadynsu, sanadin tarwatsewar gidana na tuna, lokacin da zaka ɗako yarinyarnan dana nuna ɓacin raina fushi kaitayi dani, ka ringa nunamin batada maraba da ƴaƴanmu jininmu a wajenka, gashi kaga sakamakon daya biyo baya ai, ka ɗakkota daga inuwa ita ta turamu rana, ranarma mafi munin zafi da ƙuna, nikam dai wannan zuminci naku ai ALLAH ya tsine mar (Wa'iyazubillah, Mom zuminci ya wuce tsinuwa, dan yana ɗaya daga cikin hanyoyin shiga aljannah🙄).
Dad yace, “Humm, wlhy kuma kingafa Aysha duk da wannan abun daya faru sai ban daina jinta a rainaba, a ganina yarinyarnan bata da laifi akan rikicinan, daga gidanku aka harÉ—a komai, kekuma gashi bakison laifin danginki sai nawane sakarkaru ko?!â€. Yanda yay maganar da zafi-zafi ya saka Momy kallonsa da mamaki fuska a yatsine tace, “Ikon ALLAH, kaifa nagama sammun yarinyarnan yafi cinka fiye da kowa a gidannan kai da wannan shashashan Qaseem, to wlhy inma ban É—auki matakin Æ™arshe akan yarinyarnanba kuce ba sunana Aysha Humaira ba Mtsowww!!†ta Æ™are maganar da buge table É—in ta tashi tabar wajen.
Duk wannan abu dake faruwafa tsakanin Dad da Mom Shahudah da Aamilah na zaune a D/table ɗin suma, Aamilah dai earpiece ne a kunnenta tanajin waƙa, shiyyasa batasan mi tsoffin nata je tattaunawa ba, Shahudah kam cikin damuwa take mai gusar da hankali, zuciyarta gaba ɗaya tana ga Jawaad da tunanin ina Bilkisu?, dan a yanzu dai wannan matsalar tafi cin zuciyarta fiye da komai, ɗan-fir'auna tasan ko kotune Dad sai ya kaisa ya saketa, inmafa bai saketanba ita ahaka zatai aurenta tunda ai bada soyayya tsakaninsu aka ɗauraba, a ganinta tunda babu soyayya ai auren bai ɗauruba kenan (Hudah Kai a tukunya😖😂 lol).
Buga table ɗin da Mom tayine ya maido hankalinsu kansu, duk suka bita da kallo kafin su kalli Dad da shima kallon Momyn nasu yake rai a matuƙar ɓace.
Aamilah dai baki ta taÉ“e ta cigaba da sauraren waÆ™arta dacin abinci, Shahudah ce dai ta kalli Dad É—in bayan É“acewar Mom a idanunsu. “Dad wai faÉ—a kukeyi ne?â€. Huda tai maganar tana mai tsatstsare Dad da manyan idanunta da suka koma Æ™anana a yanzun saboda tsabar yawan kuka. Kansa ya girgiza mata yaja bowl É—in data saka masa farfesun ya fara shan romon kawai dan kauda hankalin Shahudah daga abinda take zargin.
___________________________________
Jawaad kam daga wajen baba ƙaura tashar da Gimba ke shiga mota idan zai tafi gida ya nufa. Wajen bawani babban tsasha baneba, dan motocin garin su Gimban ne kawai sai masu ƙarisawa cikin ƙauyikan dake maƙwaftaka dasu. Kowa na sabgar gabansa daga masu talla har matafiya da masu sauka, sai ƴan mashinan Napep dake ɗaukar masu shiga cikin gari idan an saukesu a tashar. Sai da ya gama ƙarema wajen kallo daga cikin motarsa kafin ya ɗauki glasess ɗinsa baƙi ya toshe idanunsa dashi, baya wani cikin mood ɗin farin ciki, hakan yasa sam fuskar babu alamun sauƙi balle rangwame. Tamkar zakin dake taƙama bayan yaci ya ƙoshi haka ya fito daga motar, dama tun fakawarsa mafi yawan jama'ar dake kai kawo a wajen suka zubama motar ido da tsumayen waye zai fito daga cikinta, dan kuwa dai taci ta ƙoshi ita kanta motar balle kuma mamallakinta a ganinsu dole ya zama abin kallo. Yako zama abin kallon dan shi kansa saida ya takura dajin yanda idanu ke yawo a kansa har jinin jikinsa na tsitstsinkewa. Guntun tsaki yay yana sake ɗaure fuska, ya fara taku a hankali yana tunkarosu kansa tsaye.
Tuni da masu kallon nasa da masu gulma suka nutsu, aka shiga gaishesa da tambayarsa ko akwai abinda yake buÆ™ata?. Ta cikin glasess É—insa yake Æ™are musu kallo É—ai-É—ai, sukam sam basa ganin idanun nasa, sai Æ™yawun da glass É—in yayma fuskarsa ba Æ™aramin É—aukar hankalinsu yayba. Jawaad ya shiga Æ™arema saurayin dake gabansa tamkar zai duÆ™a kallo, nuni yay masa da hannu alamar ya miÆ™e da Æ™yau. Babu musu kuwa ya miÆ™e. “Inason ganin shugaban wajen nan naku neâ€. Jay yay maganar yana maida hannunsa guda cikin aljihun wandonsa. Kafinma saurayin yace wani abu wani dattijo da kallo É—aya zakai masa ka fahimci wahalace ba tsufaba ya Æ™araso wajen yana mai amsa maganar Jay data shiga kunnensa. “Gani nan Alhaji, barka da zuwa, naÉ—an zagayane kama ruwa shiyyasaâ€.
Shi dai jay kallonsa kawai yake harya dasa aya. Dattijon ya kuma faÉ—in, “Muje daga cikin runfa Alhaji nan kaga rana na dukankaâ€. Babu musu Jay ya bisa suka shiga rumfar da Æ™uda keta faman bi saboda sanyinta, ga robobin abinci da sukaci harda na fura duk Æ™udan ya baibaye, gefe kuma masu saida abincinne Æ´ammata da yara Æ™anana abin gwanin ban tausayi. Shi kallonsu yake da tausayawa sukuma suna kallonsa da birgewa da sha'awa. Duk da Jay yaji Æ™yanÆ™yamin tebiran dake wajen matsayin abun zama haka yay shirin zaunawa akai da farin wandonsa tas daketa É—aukar ido. Da sauri dattijon nan ya dakatar dashi, abin sallar dake can kan babbar tabarma shimfiÉ—e ya É—akko bayan ya bugata Æ™ura ta tashi, yazo ya saka masa kan bench É—in. Jay baice komaiba ya zauna duk da itama dai sallayan sai a hankali.
Dattijo yace, “Alhaji bara a kawo maka ruwa ko furaâ€. Da sauri Jay yace, “A'a nagode karka damu, tambaya nazo yiâ€. Dattijo yace, “ALLAH yasa na sani to Alhaji. Jay yaÉ—an gyara zamansa, idanunsa dake cikin glass kafe akan Dattijo, yace, “Akwai wani yaro saurayi da bazai wuce shekaru talatin da É—aya ba mai suna Gimba, duk Æ™arshen mako yake zuwa nan ya shiga mota ko kun sanshi?â€. Cike da jimami Dattijo yace, “Tabbas munsan Gimba, ai a wajenan kaf Alhaji babu wani driver da zai ce maka baisan marigayiba, danshi mutum ne na mutane ga barkwanci ga alkairiâ€. Jay Cikin nuna alamun kamar bai sani gimban ba yace, “Naji kace marigayi; kana nufin ya rasu ne?â€. Zama Dattijo ya gyara yana matsar Æ´an Æ™walla, “Alhaji ashe bakasan ya rasuba? Ai jiya-jiya akai zana'idarsa ma, muma yau labari yake zuwa mana akan duk yanda abun ya faru, ance ogansa da yakema aikine yajasa cikin Æ™ungiyar asiri, dama anata Æ™ananun magana akan yanda Gimban kema mutane É“arin abin arziÆ™i a garin musamman a irin wannan watan na Ramadhan dazai kama, to dai kasan mutanenmu da kwaÉ—ayi, dukda anajin tsoro dai haka ake amsa a lashe, sai ya gusa kaji anayi dashi, saifa yanzunne da suka tsotse jinsa zance keta fitowa abubuwa gasu nandai barkatai babu daÉ—in jiâ€. Tunda Dattijo ya fara magana jikin Jay ke wani yaamm na mamaki, haka kuma aka maida zancen rasuwar gimban ahi baida labari?, kai É—an adam sai dai ka gansa ka barsa da halinsa kawai, baiji komai a ransaba tunda yasan ba hakan bane, abinda kawai ya É—auka jahilci ne ke aiki cikin Æ™waÆ™walen kansu. Ya gyara zamansa cike da Æ™warewa cikin salon aiki yace, “Ai nima akan batun mai gidan nasa nazo daman, yanzu haka mun kamashi a hannu bincike mukeyi, idan ka bamu haÉ—inkai kaima kanada naira dubu hamsin sabbi Æ™ar a takarda. Jimm Dattijo yayi yana ninÆ™aya a nazari, mikuma ya tuna sai ya kalli Jay yace, “Nikuwa mina sani akan wannan zance Alhaji?â€. A karan farkio Jay yay murmushi, “Ba canai ka saniba daman ai, sonake dai naji abinda ka sani É—in, ranar juma'a Gimba yazo tashar nan taku?â€. Dattijo yace, “Eh to kamar dai yazoâ€. Jay daketa dannewa bayason ya tsoratashi yace, “Banason Æ™wana-Æ™wana a magana, ka fitomin a mutum mu wanye lafiyaâ€. Ya Æ™are maganar da zare glass É—in idonsa sukai ido huÉ—u da Dattijo. Sosai kwarjinin Jawaad ya sake cikama Dattijo idanu dama wajen baki É—aya. kasa jurar kallon idon da Jay ke masa yayi ya duÆ™ar da kansa. Jawaad yay wani munafukin murmushi yana É—auke kansa shima, “Yaya zan samu amsar gaskiya?â€. Kai Dattijo ya É—aga batare da ya yarda ya sake kallon Jay É—inba. “Tabbas yazo nan ranar juma'a nayan an sakko masallaciâ€. “A motar wa ya tafi gida?â€. “Bai shiga motar kowaba ranar a tashar nanâ€. Cikin Æ´ar fusata Jay yace, “To motar wa ya shiga?!â€. “Ni...ni bansanshi ba Alhajiâ€. Murmushi Jay ya sakeyi irin na zan lailaya kanka a titi É—inan ya É—aga jacket É—insa Æ™aÉ—an yace, “Kalli nanâ€. Koda Dattijo ya É—ago yauy arba da bindiga sai ya waro idanu waje, kafin kace kwabo zufa ta gama jiÆ™esa. Jawaad yace, “Saika zaÉ“a, amsata ta gaskiya kokuma rasa numfashi?â€. “ALLAH ya baka haÆ™uri oga, wlhy inada iyali da Æ™ananun yara a gida, abinne wuya garesa shiyyasaâ€. “Kai kake ganin wuyarsaâ€. Cewar Jay yana haÉ—e fuska fiye da farko. Cikin kakkausan murya yasake faÉ—in, “A wace mota gimba ya tafi gida ranar juma'a?â€. “Tare da É“aleru†Dattijo ya faÉ—a da sauri kamar zai haÉ—iye harshensa.
Jay ya sake zare glass É—in idonsa a karo na biyu, sun sake kaÉ—awa sunyi ja da É“acin rai, “Wanene Æaleru?â€. Ya faÉ—a yana É—aura Æ™afa É—aya kan É—aya da harÉ—e hannayensa saman Æ™afar yanaÉ—an juya glasess É—in hannunsa idanunsa kafe akan dattijon. Kan Dattijo a Æ™asa yace, “Shima É—an garinmu ne, zanma a iya ce maka kamar abokai suke da marigayi gimban, dan duk sa'anni ne kuma unguwarsu ma kusan É—ayaneâ€. “Ina zan samesa yanzun?â€. “Wlhy oga ban saniba, kawai dai nasan yana anan birni shima yana aikin drivernci a wani gidaâ€. MiÆ™ewa Jay yayi tsaye da cewar, “Koma ina yake ni zan memosa, ba'a cin kuÉ—ina a matsayin cin hanci, amma ina biya idan na saka aiki, zan baka aiki nakuma biyaka yanzunan, ya rage naka kaimin da gaskiya kokaci amanata idan anzo an biyaka abinda yafi nawa, biyoniâ€.
Jiki a saÉ“ule dattijo yabi bayan Jay har zuwa isa inda ya faka motarsa. Jawaad ya buÉ—e motar ya shiga ya zauna batare daya rufeba, Æ™afafunsa duka a waje, takarda ya ciro da pen ya kalli Dattijo dake tsaye, “Ka iya karatu ne?â€. Da sauri Dattijo yace, “Eh nayi sakandire Ogaâ€. Jay baice komaiba ya maida kansa yay rubutu da hausa a takardan sannan ya miÆ™a dattijon tare da kuÉ—i bandir É—in É—ari biyar. “Wannan aikin zakaimin, ga kuÉ—in aikinka nanâ€. Daga haka ya shige motar sosai ya rufe abinsa yaymata key tare dayin reverse yabar wajen.
Ganin lokacin sallar zuhur yayi sai ya tsaya yay sallah kafin ya ƙarisa station, tunkan ya shiga office ɗinsa ya samu kira daga sir Ahmad, fasa shiga nasa office ɗin yay ya nufi na Sir Ahmad ɗin. Ba'a masa iso dan zai shiga office ɗin sir Ahmad, knocking kawai yakeyi a bashi iznin shiga. Yanzunma kansa tsaye ya isa yay knocking ɗin, daga ciki sir Ahmad ya bashi izinin shiga dan yana kallonsa.
Cikin girmama ya gaishesa, Sir Ahmad ya rufe file É—in gabansa yana kallon Jay É—in dake zaune, “Ina ka shige hakane tun É—azun nake aike a kiramin kai?â€. “Am sorry sir na fitaneâ€. “Okey to ya Æ™arin haÆ™uri?â€. “Alhmdllh sirâ€. “To ALLAH ya gafarta masa, ya raya abinda ya bari. Na kiraka ne dama akan Qaseem, wai yau kwana biyu yana hannun policeâ€. Cike da mamaki Jay yace, “Police kuma? Basusan shiÉ—in wanene ba?â€. Murmushi Sir Ahmad yayi yana kwantar da bayansa jikin kujera, “Sun sani sarai, gabace da gabanta, ya mari wani Doctor ne a General hospital shekaranjiya lahadi harya fidda masa jini, to Doctor É—in É—an Alhaji É—an-iya warzu ne, shinefa yakai maganar hukumar lafiya ta Æ™asa baki É—aya, sukuma suka saka aka kama Qaseem É—inâ€. Huci Jawaad ya furzar , shi shaf yama manta yabar Qaseem ranar a asibiti, yaso ya koma amma sai aka samu akasi, ya tabbata dalilin abinda ya faru ranarne Qaseem ya mazge Doctor, shi baisan yaushe Qaseem zai daina halin Æ´an danbe ba ya rage baÆ™ar zuciya. Yace, “Yanzu miya faru to Sir?â€. Sir Ahmad yace, “I.G ne ya kirani da safen nan yake sanar min cewar shi Warzu yace sai anje kotu, shikuma yaga É—aya daga cikin yaranane shiyyasa ya kira ya sanarmin dan anrma lauya, kuma ko babansa ma bai sanibaâ€. Murmushi ne ya kufcema Jay, dan kuwa dai yasan lallai da Dad yaji da ba'a zauna lafiyaba, dan inma É“akin son Æ´aÆ´ane Dad yatake Warzun ya shanye. “Miya baka dariya?†Sir Ahmad ya faÉ—a yana tsatstsare Jay da idanu. Kai Jawaad ya shafa yana Æ™ara sakin wani murmushin, “Sir abinne nasu ne ai, ni nasan Dad da yasan Qaseem na cell da yanzu garinan ya fara yawo a gajimare dan rikicinsa, kafaÉ—amin wane station ne? zanje na fiddosa yanzun insha ALLAHâ€. “To aini banÆ™i in baka damar cirosanba, kaima rikicin naka nake tsoro ai, dan baka da maraba da Dadyn naku, ta wani wajenma ka fisa zama É—an Æ™unar baÆ™in wake, nikuma banason ka haÉ—a harÆ™alla da Warzu dan shaiÉ—anin mutumne da kake ganinsa kullum cikin manyan kayaâ€. “Karka damu Sir salin alin zamu dawoâ€. “To shikenan gashi, saika nema lauyan Qaseem É—in kuje tareâ€.
Sallama Jay yaymasa ya fita.
Bai koma office ba ya sake ficewa, harga ALLAH bazai iya jurar tuÆ™iba, haka yake shi baison tuÆ™i saita kama dole, dolene yasan mafita, to amma shikam ‘Wane driver ne zai iya maye masa gurbin Ginbansa?’ yay maganar cikin rai zuciyarsa na masa zafi. Office É—in Jabeer ya shiga, babu jimawa suka fito tare. Jabeer É—inne ya jasu, sai da suka fara tafiya yaÉ—an dubi Jay É—in daketa faman danne-danne a tab ya É—auke kansa ya maida ga titi “Na zatafa wajen rasuwarnan ka koma?â€. Jay da bai É—agoba bai kuma fasa abinda yakeba yace, “A'a, dama sonake sai gobe idan ALLAH ya kaimu mu koma mu dukaâ€. “Okey ALLAH ya kaimu†cewar Jabeer yana maida hankalinsa ga tuÆ™in.
Asibiti suka fara zuwa wajen Doctor Ballo Warzu, cikin girmama ya tarisu yana tambayar jikin Bilkisu?, mafi yawan amsarsa Jabeer ne ya bashi ita, sai da suka gama gaishe-gaishensu sannan Jay yay masa magana akan abinda ya kawosu, da tambayar miya faru bayan tafiyarsa?. Labarin komai Dr Bello ya basu, Jay ya dafe kai cikin takaici.
Shi dai Dr Bello haka kawai komai Jay yayi Æ™yau yake masa da burgesa, haka ALLAH ke sakama bawa Æ™aunar wani batare da wata manufa ba, yay murmushi yana kallonsa, “Karka damu abokina na haÆ™ura indai nine, bansan É—an uwanka bane dana barsa tun a ranarma baza'a kai hakaba saboda kai, naga rashin hankalin nasa ne yayi yawa shiyyasa naga gara aÉ—au mataki, amma yanzu kam yaci darajar mai darajaâ€.
Fuskar Jay É—auke da guntun murmushi yace, “Nagode Doctor ALLAH yabar zuminciâ€. Shima Doctor godiya yaymusu, ya kuma rakosu har inda motarsu take, sai da yaga fitarsu sannan ya koma office yana kiran babansa a waya.
★★★★★
Tunda suka shigo police station É—in aketa basu girma, kai tsaye office É—in d.p.o suka nufa, inda acan É—inma dai suka tarbi juna da girmamawa kafin a É—aura da gaisuwar mutunci. Jay da kansa yayma d.p.o bayanin abinda ya kawosa, ya kuma nuna masa lawyer'n Qaseem É—in da ya shigo a bayansu dan shi isowarsa kenan. A take anan aka kashe magana babu zancen zuwa kotu sannan aka kawo musu Qaseem. Babu abinda akai masa, dan ko hararsa babu wanda yayi tunda aka kawosa gurin saima girmamawa, ko kayansa ba'a cire masaba, sannan ba'a haÉ—ashi da kowaba a cell.
Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Jay, kowa ya ɗauke nasa fuska a tamke, Jay ya fara miƙewa ya fice abinsa, hakan yasa Qaseem jan tsaki, rai a ɓace ya kalli d.p.o yace su maidashi cikin cell ɗin. Duk kallon mamaki suke masa, Jabeer da yasan wasan ya dafa Qaseem ɗin yana magana a hankali, kamar Qaseem ɗin bazai yardaba sai kuma miya tuna oho masa ya nufi hanyar fita Jabeer da lawyer ɗinsa suka take masa baya.
A jikin mota suka iske Jay tsaye yana magana da Engineer É—in da zai masa gyaran gidansa da Bilkisu zata zauna. Suna isowa yana ajiye wayar dan sungama. Sake ma juna kallon ido cikin ido sukai shi da Qaseem, cikin É—acin rai Qaseem yace, “Miyasa ka cironi? Minene haÉ—ina da kai?â€. Murmushin rainin wayeo Jay yay masa yana lasar lip É—insa na Æ™asa, yaÉ—an É—age gira cike da salo dukda idanunsa na cikin glass ne, hannayensa duka cikin aljihun wandonsa suke, Yace, “Inada business da kaine shiyyasaâ€. Wani kallon banza Qaseem yayma Jay shima, yace, “A kasuwa ka ganni?â€. Jay ya sake murmusawa tare da ciro hannunsa yaÉ—an sosa gefen girarsa da É—an yatsa yana karyar da wuya, “Karkai taurin kai, akwai tagomashi mai yawa da ribaâ€. Qaseem yaja tsaki ya motsa zaibar wajen yana faÉ—in, “Zanyi maganin tsagerancinka ne yaro kwanan nanâ€. Cike da rainin hankali Jay yace, “Ai zuru batacin zuru, sai dai a haÉ—u ai zuru-zuru. Nabaka nanda kwanaki bakwai kacal zaka nemeni da kuÉ—inka maâ€. Qaseem yay wata dariyar kai banzane ya wuce motar lawyer É—insa batare da yabama Jay amsaba....
Jawaad yay wani lalataccen murmushi yana zare gilashin idonsa, sai da Qaseem ya shiga motar sannan ya maida glasess É—insa yay salute É—in motar da faÉ—in, “YANZUN MUKA FARAâ€. (Bari na Æ™arasa maka jikan Yusufa🤣. WASAN😉).
____________________________________
Ƙarfe sha biyu da wasu mintuna na farka, ni kaÉ—aice a É—akin, na sauka daga gadon ina addu'a da miÆ™a, naji daÉ—in jikina sosai gaskiya, rashin barci ai masifane. Wanka na shigayi, amma abin mamaki sai nai karo da Jini, cikin mamaki nace, “Jini kuma? To duka yaushe ma nai wankan tsarki? Kofa sati biyu banyibaâ€. Mamaki tamkar zai kasheni nai wanka na fito. Ina shiri ina juya al'amarin cikin raina. Shigowar Amaturrahman ne ya sakani juyawa na kalleta. Tai murmushi da faÉ—in, “Amarya saifa wani Shining kikeyi miye sirrin ne?â€. Murmushin yaÆ™e na mata kawai bance komaiba, itama tai dariya kaÉ—an, “Kefa tuni na lura irin Marwah ce, muskilanci ya muku yawa, idanma an zauna hira daku daga eh sai uhm sai a'a kuka Æ™ware yi, badai haka za'aje anama Yayan namu dunÉ—un dunkum ba kamar hadarin maraice?â€. Bansan sanda na Æ™yalÆ™yale da dariya ba babu shiri, dan harga ALLAH taban dariya musamman yanda tayi da fuska sanda zatai maganar. Ta É—agamin gira da cewar, “Ko kefa, gashi na sakaki kin dara, ki shirya muje Ummu na jiranki, yau dai tace sai taga Æ´artaâ€. Naji daÉ—i a raina, sai dai ina É—anjin tsoro-tsoro, nice yau zan gamu da Sarauniyar gagara badau gaba É—aya, ni Bilkisu É—iyar baba makaho da Asiya gurguwa, ALLAH sarki duniya, duk abinda kaga ba'a gani saboda Æ™anÆ™antarsa wataran zai fito kowa ya gansa saboda girmansa, wataran kuma sai tsufa ya sakayashi, a Æ™arshe mutuwa ta É“oyesa. Tsaf na shirya da taimakon Amaturrahman cikin siket da riga na atanfa da sukaimin É—as a jiki, dukda dai basu kama jikina ba, duk yanda tasi hanani na saka gyale kasawa nai saida na saka sannan muka fito.................âœ
Barkanmu da dawowa, ina fatan kunyi weekend cikin Æ™oshin lafiya😉😘😘ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜.
Masu kira akan zasu sayi ƘWAI CIKIN ƘAYA!! bafa shi ake tallaba, muna tallar buks É—inmune guda goma na zafafa gasunan, duk wanda bai sayaba ya motso ya saya karya bari romon daÉ—i ya wucesa🤗🤗🚴ðŸ¼
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ÆŠAURIN ÆOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ÆŠAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ÆŠAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuÉ—i ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzoðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜˜.
ALLAH ka gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™ðŸ».
[12/23, 6:43 AM] H Inna: ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙ðŸ»
BOOK TWO
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.