Complete Hausa Novels

Kuruciyar Minal Part One Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: _KURUCIYAR MINAL_PART ONE_BY MISS UNTICHLOBANTY_-1.txt

Chapter 3 of 51

*CHAPTER 12*

minal kuwa shayin dazai taimaka mata da condition din da take aka hada mata

Kamin suka samo bowl da ruwan dumi da tsumma

Sannan suka dauko first aid box domin ciwon dake hannunta har yanxu yana zubda jini
duk ya bata mata hijab dinta

Tabawa dukkan maids da securities din gidan tausayi hatta sojojin domin duk rashin imanin wasu daga cikinsu sunsan Cewa minal ta horu

What so ever her fault is?

They all look at her pitifully, how young she is,yet going through all these sort of troubles

First was her hiding inside the Booth,

Then passing out due to lack of oxygen,

Then woken up by a chilled bottle water !

Then fear of being in an army's house as an offender!

Then the blood cascading from her hand making her clothes look like.........

Then the looks and presence of those horrible and terrifying,wicked dogs

The dogs chasing her is the biggest fear of her life

Her falling into the pool.
That one is called helplessness....................

Wata maid me suna tala (mai shara)ce ta sa'a tsumman a ruwan zafin ta matse sannan ta fara goge ma fiskanta

Wani nifashi taja kan ta sauke hawayen wahala suka fara zarya a idonta yadda kasan ruwan sama

Cikin 2 min harta jika hijabinta ta fara jika pillow da hawaye

Maid uku ne Dama a dakin da take daya da first aid,daya bowl din warm water,daya kuma tea and toasted bread

Dukkansu idonsu ya ciko da kwalla musamman da suka ga yadda minal take kuka

Wani mahaukacin atishawan data watsa ne ya dawo dasu saga duniyar da suka fada na halin da take ciki

Katrina wacce take baturiya itace first aider na gidan

First aid box din ta bude sannan ta ciro su cotton,dettol,spirit,iodine,and Bandage.

Treating ciwon ta fara aiko ana fara goge jinin minal tafara yarfa hannu
(nace tabdi tun ba'a saka alhaji dettol da oga iodine)

Yamutsa fiska take yadda kasan mai nakuda

Dettol aka saka domin ayi disinfecting aiko wani kara ta sake ta mike a take tana Cewa

Dan Allah Kiyi hakuri,wallahi ni Ba mai lafi nace karki min mugunta

Itadai Katrina ganin bats gane Ba sai ta kalli sauran with a questioning look

Fassara mata sukayi kamin tace oh sai tacewa minal din

No no my dear am gonna harm you,impact am being gentle with you

Minal dai anzo gurin domin bata gane ko Abu daya data ce Ba

Hasali ma banda harm babu abinda taji sai ta dauka Cewa tayi me yasa ta Tara gashin hammata yana damunta da wari

Nuna kanta tayi da yatsa cike da takaici tace yanxu bayan cinzarafin da oganku yamin,da iriyar muguntan da kike mini shine harda cin fiska?

Ina ruwanki da gashin hammatana?

Tala ne tace Kamar ya?

Minal tace inba wulakanci Ba shine zatace hammata na yana wari Wai na tara gashi.

Tala ta dan dara kamim tace kai da abin dariya kike wallahi ai Ba haka take nufi Cewa tayi..................

Kara kai minal tayi alamun gamsuwa tace kiyi hakuri.

Katrina ta gane me tace domin zama a cikin su tala.
Dukda Cewa dakinsu daban amma ta Dan Koyi wani Abu a Hausa
suma dai su tala dasu maimuna dasu Rabi a primary suka tsaya zama da irinsu Katrina dasu Susan yasa suka koyi English

Sai tace is okay

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.