Kuruciyar Minal Part One Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: _KURUCIYAR MINAL_PART ONE_BY MISS UNTICHLOBANTY_-1.txt
Chapter 18 of 51
*CHAPTER 27*
Juyi minal tayi tace inna bacci,Wai har asuban yayi ne?
Haushi abin yabawa yazeed hakan yasa ya wantsalar da pillow din da take kai,aiki babu shiri ta mike ganin shine yasa taji wani faduwar gaba yazo mata
Tunda take arayuwarta bata tana jin faduwar gaba irin wannan Ba kuma bata taba jin tsoran wani Kamar yadda tsoron yazeed ya shigeta a yanxu Ba.
Wani irin kwarjini yayi Wanda tayi nadamar kallon idanunsa domin kuwa ko lokacin da suka fara haduwa bata kallesa da kyau Ba
Wani kirma jikinta ya fara ta fara karkarwa Kamar mejin sanyi.
A hankali muryatta Kamar zatayi kuka tace sannu da zuwa.
Wani kallo yazeed ya mata Wanda yasa hanjin cinkinta kadawa kamin yace uban Waye yabaki izinin kwanciya akan gadonnan? Wato anzo ansami banza ko shine kikayi yi relaxing kina bacci ?
Da izinin wa kikayi bacci? Tayi shiru...
Bakida kunnene ko yaya?muryanta na rawa idanunta ya cicciko da hawaye tace kayi hakuri yace will get down zaki sauko ko saina taka ruwan cikinki?
Babu bata lokaci ta diro saga kan gadon yayinda tayi kneel down run kafin a bata umarni yazeed ko Ba tare da ya kalli inda take Ba ya taka ahankali cikin takunsa na kasaita da isa amma cikin kuzari Wanda zai nuna maka Cewa shidin wani jarumi ne kuma namijin duniya
Har izuwa bakin gadon ya isa sannan ya zauna ya cire hularsa me mugun kyau da tsada sannan ya ajiyeta a gefe
Dago kansa yayi yanaso ya karewa minal kallo amma hakan ya gagara sabida kirjinsa dake bugamasa da Sauri da Sauri amma dai baikai na minal Ba sai ya dauki hakan amatsayin baccin rai
Dan haka sai ya jingina Kansas da allon gadon yana mai lumshe idanu Kamar yadda yayi scan baya sanda ya fara haduwa da ita a gidansa.
Minal ko gabadaya jikinta yayi sanyi,ta sadakar Dan ita a ganinta Allah ne yake ramawa mutane irin tsiyar data musu sanda take gida.
Tayi tsuru tsuru da ido Kamar Mara Gaskiya,gabadaya jikinta ya jike da gumi ga wani fitsari ga zazzabi ya sauko mata tsabar rudewa.
Dukkanin shikashikan tashin hankali ta cikashi a halin domin ko hawaye sun Dade da fara safa da marwa a kumatunta bakinta ko yayi mata nawi ko hakurin ma takasa badawa sai tsilla ido take tana kallon kafafunsa Wanda Duke dake da Zara zaran yatsu da kuma gashi kwance luf luf akai.
Sanda suka dauki kusan minti goma a haka kamin yazeed yace sannuki da zuwa cikin masifa da bala'i hade da tashin hankali.
Minal Kam ta kasa dabbaka Komai Dan ita ko a film bata tana ganin irin yanayin da tashiga Ba ganin take ko yaushe ma ziciyarta zai iya bugawa ta mutu zaboda yadda yake bugawa har cikin dodan kunnenta takeji
Abubuwa dayawa ke yawo azuciyar yazeed Wanda yana fahimtar wasu,Wasu kuma baya fahimtar su
Ba tare da buds idanunsa Ba yace kinsan ni soja ne jarumi kuma naga alamun kinason zama dani,kuma kinsan jarumi sai jaruma,Dan haka kamin infara considering dinki a matsayin matata sai kin cika wa dannan sharudan
Shiru ne ya biyo baya kamin yazeed yace ;
Na farko daga yau ke zakinayin dukkanin shara,moping,dusting, wanke-wanke,inkika saba wadannan to zan hada mini da wankin mota da safe sukuma masu aikin zasuyi girki da sauransu da yamma kuma zakiyi sharan bangarena sannan zaki dafa abinci kuma ni Vance ki kawomin jagwalgwalonki Ba.
Na biyu karki sake koda wasa ki na ganki a Inda nake domin ganin fuskarki kadai nakanji Kamar zanyi amai
Na uku abinda nace kiyi agidannan su kadai zakiyi idan kina neman izinin yin wani abu to ki rubuta a paper ki ajiyemin ka kibi duk umarnin da matata zata baki saboda marabarki da yar aiki shine darajar mom
Na hudu karki sake mahaifiyata tasan da wannan maganar idan Ba haka Ba to kin kusa ki bakunci barzahu
Hope kin gane ta gyada masa kai yace bakida bakine
Tace na gane
Yace good idan kinbi wannan dokokinn to zaki zauna lafiya amma idan kika saba to kema kinsan sauran.
Sannan ban yarda ki kwanta akan gadonnan Ba harsai naga how serious are
Itade taji bazata kwanta a gadon Ba sauran kuwa to kunde San sauran .
A hankali ta bude bakinta tace oga sir Dan Allah idan na cika sharudanka zaka sakeni yayi shiru kamin yace hakan ya ta allaka da yanayin biyayyarki may be in sakeki
Yana gama fadan haka ya tashi ya fice wani nauyayyan ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin numfashinta Wanda bata masan ta rikeshi Ba sannan ta goge hawayenta sannan tadau bargo ta Komai kan kujera ta kwanta tare da rufe kafafunta
Yazeed kuwa yana komawa dakinshi yayi wanka tare da brush sannan ya fito dressing room dinshi ya Shiga ya dauko pyjama dinshi blue tare da Rigan ya saka sannan ya haye gadonsa ya kwanta yana mai lissafi yanda rayuwa ta kasance masa
Hakadai bashi yayi bacci Ba sai wuraren asuba koda ya tashin sallahn asuba Kansa yayi masa mugun nauyi hakadai ya daddafa yayi sallh yayi azkar yau ko karatun Qur'ani bai samu yayi Ba ya koma bacci. Dama Ba kullum yakeyi saboda yanayin life.
Minal ko tunda tayi asuba taje kitchen ta nemi kayan aiki aiko batasha wahala Ba ta samu ta kama aikintakarfe 8 cif saiga su atine da su larai sun shigo sukaga babu kayan aikinsu parlour suka leko jin motsin mutum aciki aiko da gudu gudu Sauri Sauri suka karaso
Atine tace Allah sarki yar uwa yaushe Rabin da mu ganki ziyara kika kawo manane ko wajen hajiya kikazo kika bage da aiki saide kash hajiya ma jiya da daddare tabar kasan itada danginta kinsan fa mai gidan ya karo aure
Duka atinen ta fada a numfashi daya zuwa biyu Asabe ta kara da ya karo wulakanci Ba larai tace baza'aji mutuwar sarki abakina Ba
Minal ko murmushi take tana binsu da idanu Dan batada abin Cewa
Aikin sukayi kokarin karba minal tace ah ah sukace to shikenan suyi tare kamin ta yarda amma dukda haka tana tsoran kar yazeed ya ganosu
Su kuwa sai hira suke mata yarda tambayarta ko zata kwana musu Dan sunaso suyi kawance da ita tace musu ai Ba kwana Ba kwanaki ma zanyi ta fadi haka tana bawa kwanakin karfi, aiko sunji dadi Dan su nasu gane me take nufi ba
kafin karfe 10 sun gama Komai saura part din yazeed Wanda dama tunda basu ke gyarawa Ba lukman ne kuma yazeed yayi masa message Cewa Ba sai yazo Ba.
Su atine sai janta suke da hira tun tana nokewa har ta saki jikinta sumo abin ya musu dadi, binta tace ni wallahi na kosa naga amaryar Allah dai yasa Ba irin madam zakiyya bace
Atine tace yo imma batada mutunci ai ita ya shafa minal de tayi tsit tana jinsu
Minal tace to ita bari taje sama tayi wanka larai tace Wai ko kema bikin kikazo ne naji kina Cewa bari kije sama kiyi wanka ? Rasa amsar da zata nasu tayi sai atine tace kinada kayan sawa?
Binta tace ki wani tambaya dole da kayanta zata zo mana
Minal tacewa atine Dan Allah kinga rabu dasu zo Kiyi mini wani taimako
Sukace to sai kun dawo kamin su minal suka wuce dakinta ta cire hijabinta sannan ta kalli atine
Atine ko zare idanu takeyi domin in batayi kuskure Ba nanne dakin da aka kawo Amarya
Minal tace kinga kwantar da hankalinki nice amaryar ni zoki nuna mini Inda zan sami kayan sawa
Atine ta zaro ido tace Kece ME?
Minal tace kinga shiyasa ma ban dadi muku Ba saboda ban Shirya yin bayaniba zoni ki nuna Mani
Nuna mata dakin dressing atine tayi da yadda zata canja combination din saga 00000 sannan mata na toilet ma
Kamin ta fita tana mamaki da kuma al'ajabi minal kam wanka tayi sannan ta koma parlour jin shiru yazeed bai fita Ba yasa tace kika ma ya five run asuba idan Ba haka Ba ya za'ayi ace mutum yana bacci har 12.
Alokacin data koma kitchen domin dauko su tsintsiya su atine na kitchen din Suna cin abinci Suna ganinta sukayi caaa Wai meyasa bata fada musu akwai chemistry a tsakaninsu da oga sir Ba ?Wai kuma me yasa oga sir ya mata abinda ya mata kaman wata 3 zuwa 4 da suka wuce?
Murmushi tayi tare da tabe baki tace sirrin ne
Daukar tsintsiyarta da packer tayi ta wuce side din yazeed
Kirjinta ne ya fara tsinkewa karfa yaje yananan,hakan yasa ta fara sanda Kamar Mara Gaskiya sannan a hankali ta bude kofar da take ganin side dinshi ne tunda de tasan na mom
Leko kanta tayi taga..........
Me tagani?
Uhm kun ganni all of the sudden ko?ai bazan iya babu Ku bane kun zama wani bangare na life dina.
Ina sonku sosai fans dina😘
Don't forget to vote,share and comment
Miss untichlobanty💕
4th October, 2019
[1/11, 1:54 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.