Jiddatulkhair Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: JIDDARTUL KHAIR CMPL.txt
Chapter 85 of 99
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
Abuturrab was Speechless.... ya rungumeta sosai, wani sabon sonta na fixgarsa ya rufe ido cikin sanyayyan muryarsa yace "I have a lot to say to you but not today, i will reserve it for another sweet night, they are so many lovely night to come...." Ita dai bata bude idonta ba tana sauke numfashi a hankali. Washegari da asuba Abuturrab na dawowa masallaci har ya nufi bangarensa sae kuma ya dawo yana kallon kofar dakin Aneesah ya karasa ya bude kofar dakin yana kallon ciki, kwance ya ganta kan manyan duvets dinta guda biyu da ta shimfida a kasan tiles daga gefen gadonta, ya karasa cikin dakin ya kai hannu ya buga duvet din, ta bude ido yace "Sallah" Daga haka ya mike ya fita dakin ya koma bangarensa, xaune ya tadda Jiddah kan darduma tana azkar dinta a xuciya, ya xauna gefen gado ta daga kai a hankali ta kallesa, bayan wani lkci tace "Ina kwana" kallonta kawai yake, ta mike ta dauke darduman da tayi sallah ya tashi shi ma ya nufeta ya jawota jikinsa yace "Good morning Jiddatul Khair" daga kai tayi ta kallesa ya sakar mata murmushi yace "How was ur night?" A hankali tace "Alhmdlh" yace "Let sleep a little more" Kafin ta ce komai ya ja ta saman gadon suka kwanta, sae da yayi cuddling dinta iya son ransa sannan ya kyaleta, har bacci ya fara daukarta ta bude ido da sauri tana kallonsa taga ya koma baccin, kallon dogon hancinsa ta dinga yi da eyebrows dinsa, ta sauke idonta a hankali ta xame jikinta daga nasa ta sauka daga saman gadon ta fita parlonsa agogo ta kalla taga bakwai saura na safe, ta daure gashinta da yayi scatter waje daya sannan ta fita parlon ta sauka downstairs, sae da ta fara share ko ina a parlon tayi mopping, kayan kallon ma duk ta gogesu, parlon ya dawo wani fess da shi, da alamar an dade bai samu irin wannan gyaran ba, ta haura sama ta bude kofar dakinta a hankali tana kallon ciki, takalminta ta tafi ta dauko a downstairs sannan ta dawo dakin ta saka takalmin ta shiga cikin dakin da shi, burner dinta dake ajiye gefen madubi ta dauka sannan ta samu ta harhada turarrukan wuta a wani kwalba da bai karasa fashewa ba ta sauko downstairs ta jona burner din a socket, ta debi turaren ta xuba a ciki ta mike, kitchen ta wuce, sae da tayi minti daya tsaye tana kare ma kitchen din kallo snn ta girgixa kai, ta fara tidying din ko ina har cikin store ta fitar da duk kwalayen da babu komai ciki ta kofar backyard, bayan kitchen din ya dawo a bit tidy ta fara wanke wanken duk plates da cups, sai kusan karfe takwas da rabi ta gama da kitchen din, ta goge ko ina ta wanke abinda xata iya wankewa a jikin gas ta goge na gogewa, tayi dusting ko ina, kan kace me kitchen din ya dawo so sparkling kamar ba shi ba... gas ta kunna ta daura ruwan Lipton, ta duba taga babu kayan kamshi, kawai ta debi irish ta fara ferewa, dicing it almost equally, tana son making Crispy french fries na dankalin ne ba irin wanda aka saba soyawa ba, bayan ta wanke dankalin da ta yayyanka ta bar sa cikin ruwa ya d'an jiku na wasu mintuna sannan ta wuce sama, corridor din rooms da bata share ba ta share tayi mopping, sai kuma ta shiga part din Abuturrab, parlon kadai ta gyara tsaf nan ma ta goge da kayan kallon, ta koma downstairs ta dauko burnern turaren wuta ta jona a parlon nasa sannan ta sauka ta koma kitchen, paper towel ta shimfida saman tray, ta xuba dankalin da ta tsane daga ruwa ta dau wani paper towel din, patting the potatoes very dry, bayan nan ta daura veg oil a saman gas heating it for about just 300° Fahrenheit, wato man bai yi wani xafi ba, bayan nan ta xuba wasu quantity na dice Irish din a cikin man gyadan, ta soya dankalin for just 3mins sannan ta kwashe ta xuba su a kan wani paper towel din, mutum na iya ajiyesa a freezer a hakan har xuwa sanda xai yi amfani da shi even if not that day, amma tunda ita a lkcn xa a ci, barinsa kawai tayi ya huce, ta tafi tana yanke yanken abinda xata soya kwai da shi, bayan ta gama ta juye ruwan Lipton dake tafasa cikin flask, ta duba dankalin da ya d'an huce ta barbada masa a little quantity of salt sannan ta sake daura man gyadan a wuta ta bar shi yayi xafin 400° Fahrenheit sannan ta xuba irish din, ta soya shi dai dai yanda take so, cikin minti sha biyar ta gama soya har da eggs din sannan ta fita da warmer din dankali da kwan ta kai saman dining, ta dawo ta kara gyara kitchen din kamar bata yi girki a ciki ba ta koma sama, dakinta ta shiga da takalmi a kafarta ta tafi bandaki tayi wanka ta fito, bayan ta dau abubuwan da xata dauka ta koma can dakin baki ta shirya, bayan ta gama shafe shafenta ta dau doguwar riga na atamfa ta saka ta daura dankwali, sosai kayan yayi mata kyau ta dawo sak amaryarta, lallen da ya haska hannunta sai sheki yake gwanin sha'awa, babu abinda ta shafa a fuskarta banda kwalli sai man lebbe, amma kyan da tayi ba a cewa komai, ta kalli agogo dake nuna goma da minti biyar ta mike ta fita dakin, dae dae nan Aneesah ta fito daga nata dakin sanye da kayan bacci, Suna hada ido Jiddah ta dauke kanta kamar yanda Aneesan ma tayi da sauri, ko tsayawa bata yi ba ta sauka downstairs abun ta, kamar ance Jiddah ta juya taga Abuturrab shi ma ya shirya cikin kananun kaya lkci daya kamshin turarensa ya xagaye corridor din, ya d'an kalli Aneesah da har ta kai downstairs don bata gansa ba ma, ya karasa gun Jiddah ya rungumota jikinsa yayi mata light french kiss, underneath his breathe yace "U look beautiful" A hankali tace "Thank you" ya xame dankwalinta yayi kissing bak'in gashinta me tsantsi sai kuma ya sauke lips dinsa xuwa wuyanta, jin taku a stairs ya saketa da sauri ya koma baya, Aneesah ta hauro saman tayi masu kallo daya ta yi hanyar dakinta, ya bi ta da kallon gefen ido, kafin ta shiga dakin yace "Good morning" Ta watsa masa wani kallo tace "Same" Daga haka ta shige dakinta, tuni Jiddah ta sauka downstairs, murmushi yayi ya shafa kansa sannan shi ma ya sauka. Ko kadan Abuturrab bai yi mamakin abubuwan da Jiddah tayi ba, da yanda tayi transforming kitchen da parlon gida, he was so happy ya xauna gefenta yace "Allah ya maki albarka Wife, a haka gidan nan yake a ko da yaushe kafin ki bar sa" Ita dai ko kallonsa bata yi ba, ya bude warmer din ya dau irish daya ya kai baki, ya juya ido bayan few seconds yace "U made this or u bought it??" Still ta ki cewa komai, sauka kasa yayi ya xauna saman carpet ya tankwash kafa ya bude kwan ya dau spoon ya deba ya kai baki, lumshe ido yayi yace "umm.... So Yummy" mikewa tayi ta durkusa kusa da abincin ta dau plate ta dibar masa, sannan ta fara hada masa shayi, shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, komai tayi burgesa yake, ba kuma yau ya fara jin hakan ba, for long ya ke ji hakan... bayan ta hada shayin ta dauka ta ajiye masa a gabansa a hankali tana kallonsa, kissing lips dinta yayi ya lumshe ido yace "Thank you MPG💖" ita dai kallonsa kawai take da manyan idanuwanta, under neath his breathe yace "My Precious Gift 💖" Ta sauke idonta amma har ranta taji dadin words din nasa, yace "kiyi serving kanki sannan ki dibar ma Aneesah ma, i will be back soon" Daga haka ya mike ya wuce sama, ta bi sa da kallo. Yana shiga dakin Aneesah ya tar da ita xaune can karshen dakin ko tunanin me take oho, ta d'an kallesa yace "Taso mu yi breakfast" Shiru tayi yace "I am talking to you" a takaice tace "Aa ku dai ku ci, ai kune masu gidan yanxu" Ya karaso cikin dakin yace "U admitted kina son xama da ni as ur husband Aneesah, and for peace to continue reigning in our midst duk abinda na fada just adhere and obey that's all, nace ki taso mu yi breakfast, i wasn't expecting you to decline that" Bayan few seconds ta mike ta dau mayafinta ta yafa sannan ta nufosa ya bi ta da kallo har ta fita, fitowa yayi ya kulle kofar dakin sannan ya bi bayanta downstairs din, Can gefe jikin kujera ta samu ta xauna, ya dau dankali da kwan da Jiddah ta debar mata ya ajiye gabanta, sannan ya hada mata shayi ya ajiye mata, Jiddah dai ko kallonsu bata yi ba, a hankali take shan shayin hannunta, Ya dau fork din dake plate din potatoes da Jiddah ta debar masa yana kallonsu both yace "Kun gaisa yau?" Babu wanda yace komai cikinsu, ya kalli Jiddah sannan ya kalli Aneesar duk babu wanda ya kallesa, yace "I am talking" Jiddah ta ajiye shayin hannunta ta mike, ya daga kai ya kalleta yace "Ina xa ki?" Without looking at him tace "I want to ease ny self" daga haka tayi wucewarta sama, Aneesah ta dau fork ta fara cin abincin gabanta, shi dai Abuturrab bai ce komai ba, bayan mintuna kadan ya kalli Aneesah yace "You met her downstairs, sannan she made this meal and tidied the whole house, why not even tell her weldone" Aneesah ta kallesa tace "Ni ban taso a gidanmu naga Babba na gaida yaro ba, ai darajar girmanta da nayi ya ci ace ta gaisheni kafin ni kuma in ce mata sannu da aiki, but tana jira ni in gaisheta, na san kuma na bata at least 7 good years, autarmu ma ta girmeta" Abuturrab yace "Amma sai ki yi mata sannu da aiki ki ga ko xata gaisheki ko baxata gaisheki ba, balle u met her ba ita ta xo ta sameki ba" Aneesah tayi wani murmushi tace "I am not surprise u are always supporting her, to ta dawo ta xauna sai in gaisheta i know i won't loose" Abuturrab bai ce mata komai ba, bayan some minutes yace "U asked for something few weeks ago, do u still need it?" Ta ajiye fork din hannunta tace "Bana bukatarsa, kawai yanxu cikon kudi xaka bani a kawo min wasu furnitures din, kudin da xa a turo min baxa su isa ba...." Ya girgixa kai yace "Bani da kudin furnitures because i didn't budget for it this month... anjima xan saka maki abinda kika tambaya 2 weeks ago" Bata dai ce masa komai ba, yace "And ki shirya before 12 xa mu shiga gidan neighbors dinmu a gaisa, so we can know each other more" Tace "Aa ni baxan je ba, ku je dai da matarka..." Calmly yace "Ni kuma nace ki shirya mu je" Bata ce masa komai ba, hakan ya sa ya mike ya koma saman kujera ya dau wayarsa dake vibrate, kallonsa take har ya gama wayar sannan ta sunkuyar da kanta tace "Captain i think i have to go to do hospital don jikina baya min dadi, ina yawan jin jiri da kasala sannan i don't have appetite na cin abinci...." yace "Ohk, Allah ya sauwake" tace "Ameen, i need to see a doctor" kwashe duk kwanukan tayi da plate ta wuce kitchen da su ya bi ta da kallo. Mikewa yayi ya wuce sama, bangarensa ya tafi hoping to see Jiddah there, ganin bata nan ya dawo dakin baki, kwance ya ganta saman gado idonta rufe, ya xauna gefenta yayi kasa da murya yace "Jiddah" Kin bude idon tayi ya dagota ta 6ata fuska tace "Ni bacci nake ji" Yace "Me yasa kika ki cin abincin?" Ta bude ido tace "Saboda na koshi" Yace "Amma baki ci komai ba" shiru tayi masa, yace "Or are u angry at anything?" Tace "Not at all" Ya kamo hannunta yayi lowering voice dinsa yace "U know what?" A hankali ta daga ido ta kallesa, yace "For the sake of ta girmeki ku dinga gaisawa da safe pls idan kin ganta..." Ta xame hannunta daga nasa tace "It's not necessary" da mamaki yake kallonta, can dai yace "Why?" Tace "That's just my stand on it" yayi kasa da murya yace "No Jiddah ina son ku xauna lafiya kamar yaya da kanwa pls, nasan in sha Allah Aneesah ta canxa halinta xa ku xauna lafiya without any problem" Murmushi kawai Jiddah tayi tace "Ae da kai ya kamata ta xauna lafiya ba ni ba, ni ina ruwana da ita tunda ba xamana take ba" Mamakin furucin dake fitowa bakinta upon her age ya dinga yi, and he saw nothing other than sheer jealousy a idanuwanta, ta mike tayi shigewarta bandaki ta bar sa a xaune, shafa kansa yayi thinking of where to start from, can ya mike ya sauka downstairs yana ta xaune parlon har kusan 12 jin footstep a sama ya daga kai, Aneesah ce ta sauko cikin English dressing da veil dinta ta karaso parlon ta xauna ba tare da ta kallesa ba tace "Na shirya" kallon agogo yayi sai kuma yace "Ohkk" ya mike ya tafi sama, dakin Jiddah ya shiga, ya sameta xaune da wani littafi a hannunta, yace "Xa mu shiga gidan neighbors dinmu mu gaisa yanxu, are u ready?" Taki cewa komai, ya karasa ya xauna gefenta ya amshi takardan yayi kasa da murya yace "Shkkn babu wanda xai gaida wani cikinku tunda baki so, i am sorry plss ban san ranki xai baci ba" Rungumeta yayi jikinsa yace "I am so sorry for making u sad wife" Kuka ta sakar masa, lkci daya ya rikice mata yace "Na fa ce kiyi hakuri ni ban san ranki xai baci ba wllh, don Allah kiyi hakuri" Cikin rawan murya tace "Bayan ita ce ta sauko ta gan ni ko sannu da aiki bata ce min ba tun asuba na tashi nake gyara gidan da bata gyarawa, sannan...." Bai bari ta ci gaba ba ya fara kissing dinta. Har aka kira azahar Aneesah na xaune parlon bata ga saukowarsu ba, tana ta xura idon ta ga ya fito xai je masallaci nan ma har aka idar da sallah bai fito ba, ganin karfe daya da minti arba'in ta mike ta wuce sama ta shiga dakinta. Karfe biyu da minti biyar Abuturrab ya fito daga dakin Jiddah sai a sannan ya tuna Aneesah da ya bari a parlor, ya d'an buda ido ya sauka kasa da sauri bai ganta ba, dawowa yayi ya bude dakinta ya ganta kwance tana danna wayarta, ya kasa hada ido da ita, ya dai shiga dakin, kallo daya tayi masa taga wani kayan ya canxa ta dai ci gaba da danna wayarta, still not wanting to look at her yace "Sorry i kept u waiting, i was busy with my laptop, taso mu je" Bai jira me xata ce ba ya fita daga dakin, Jiddah ta fito daga dakinta ta ki yarda ta kallesa kana ganinta kasan ta sha kuka, ta nufi stairs tana sauka a hankali, shi dai da ido ya bi ta, sai ga Aneesah ma ta fito daga dakinta ya sauka downstairs tare da ita, Kallo daya Aneesah tayi ma Jiddah dake xaune kan kujera a parlor ta dauke idonta, abaya ne jikinta da veil dinsa, Abuturrab ya kalli Jiddah yace "Ta so mu je" Daga haka ya nufi kofa, Jiddah ta mike ta bi bayansu. Abuturrab ya xauna a wajen shan isa bayan sun shiga compound din gidan, Aneesah ta danna bell din parlon aka bude kofar wata warce da alamar mai aikin gidan ce ta gaishesu, Jiddah dai ko kusa da kofar bata je ba sbda Aneesah dake tsaye, mai aikin tayi masu Bismillah, Aneesah ta fara shiga parlon sannan Jiddah ta shiga, wata matashiya da baxata wuce shekara talatin da biyar ba dake xaune parlon ta shiga welcoming dinsu tana kallon Jiddah, mai aikin gidan ta tafi ta kawo masu ruwa da lemo, Matashiyar matar dai tana jiran su fadi daga inda suke, Aneesah na wasa da xobunan hannunta tace "Nan makota ne, gidan da yake kusa da naku" Matar tace "Ayya sannunku da xuwa, ai kam ba a ta6a gaisawa ba, bari in kira Hajiyar tana sama" Wata yarinya ce da baxata wuce 19 ba ta fito daga kitchen, Matar tace "Yauwa Khaleesat ce ma Mama tayi baki" Khaleesat tace "Toh" Sai da ta fara gaida su sannan ta wuce sama, Jiddah ta bi yarinyar da kallo, haka ma Aneesah... Matar na kallonsu tace "Yaya da kanwa ce amma" Aneesah ta kirkiri murmushi, Ita dai Jiddah ta sunkuyar da kanta, Aneesah tace "Haka ne" Khaleesat ta sauko mahaifiyarsu na biye da ita a baya, da fara'a ta shiga welcoming dinsu, duk suka gaisheta ta amsa tace "Maa sha Allah naji dadin shigowarku wllh, ina me gidan naku?" Aneesah tace "Yana waje" Tace "Au haba, ce masa ya shigo mana" Aneesah ta mike ta nufi kofa ta fita... Hajiya Fatima tace "Khaleesat xo ga me shige da ke" Matar dake xaune parlon tace "Auu, ashe kema kin lura Mama, wllh tun daxu nake ta kallonta dubi har dimple din" Khaleesat tayi dariya tana kallon Jiddah tace "Ya sunanki?" Jiddah tayi murmushi a hankali tace "Jiddah" Hajiya Fatima tace "Maa sha Allah, amma in ji dai babu wata matsala yanxu jiddah?" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Hajiya fatima tace "Duk sanda kika samu lkci ki shigo xan yi magana da ke kin ji?" A hankali Jiddah tace "Toh" Matar dake xaune warce ita ce first daughter din Hajiya Fatima tace "Ashe kin sansu Mama, ni ban ma ta6a lura da su a anguwar ba" Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Nima shekaranjiya na shiga gidansu, warce ta fita yanxu ai kishiyarta ce"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.