Trending Hausa Novels

Jiddatulkhair Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: JIDDARTUL KHAIR CMPL.txt

Chapter 77 of 99

Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you

_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_

Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Karfe goma Maimoon ta tashi Jiddah daga baccin da take, Jiddah ta mike xaune tana kallonta da kyar saboda kanta da yayi mata nauyi, Maimoon tace "Driver din ya xo yana jiranmu a waje" Jiddah ta marairaice tace "Gashina fa a gyara yake Maimoon, last week fa mun je saloon" Maimoon ta buda hannu tace "Oho go ai nima bani nace mu je ba, kina dai ji Umma ta fada da asuba ai da kince mata a gyara gashin ki yake" Jiddah bata ce mata komai ba ta mike tsaye ba don ranta ya so ba ta fara shiryawa, Maimoon tace "Ina jiranki a parlor" Daga haka ta dau hijab dinta ta fita, Jiddah ta gama shiryawa ita ma ta saka hijab din ta fito sannan suka wuce saloon din, har suka isa jikinta a sanyaye yake tayi nisa tunanin da take, Lkci lkci Maimoon ke kallonta amma dai bata ce mata komai ba. Bayan an gana gyara mata gashin da kyar da lallami Maimoon tayi convincing dinta aka yi zanzara mata henna a hannu, sosai lallin yayi kyau don expert ce tayi mata, Maimoon sai kallonta take tana murmushi, karfe biyu da yan mintuna suka koma gida, Umma dake parlor da frnds dinta sun dawo daga jeran kayan kitchen ta bi su da kallo har suka wuce daki, Jiddah ta xauna can karshen gado ta jinginar da kanta, she looks so sad, Maimoon ta je ta debo masu abincin don sun yi sallah a saloon din, da farko kin cin abincin Jiddah tayi sai da ta ga da gaske Maimoon xata je ta gaya ma Umma sannan ta sauko ta debi abincin ta kai baki, daurewa kawai take wajen cin abincin don jin sa take kamar magani... Throughout ranan Abuturrab a bedroom din Umminsa ya yini sai dai ya fita masallaci, Ummi dai na lura da shi kamar he isn't happy amma kuma bai ce mata komai ba, bayan la'asar tace "Wai baxa ka ci abincin bane, abincin tun karfe daya a ajiye? Ko a fita kitchen da shi ne?" Yayi pausing movie din da yake kallo a wayarsa yace "Xan ci Ummi" kallon abincin nasa dake ajiye kawai yake, Ummi tace "Tell me what is wrong Aliyu!!" Ya kalleta sai kuma yayi shiru ya sauke kansa ya ki ce mata komai, jin Ummi bata sake ce masa komai ba ita ma, ya daga kai ya kalleta yace "Ummi ni kawai na rasa gane amfanin aurena da Aneesah, can u imagine all 2 of her family members suna gidana yanxu haka... sannan Aunty ma na gidan tun jiya" Da mamaki Ummi tace "Wacce Auntyn?" Ya shafa kansa bai ce komai ba yana jin xuciyarsa na tafarfasa tuna abinda Aunty tayi masa da safe har da xagin Umminsa, Ummi tace "Wai Hafsah kake nufi ko wa?" Yace "Ita... Ummi gaba daya fa suna gidan yanxu haka" Ummi ta kasa ce masa komai sai kallonsa take da mamaki, Ya dafe kansa sounding so fed up yace "I'm really fed up with this Ummi, shkkn mutum ba shi da kwanciyar hankali a rayuwa, i regret marrying Aneesah, i regret ever making this mistake" Ummi ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya tace "Toh Allah ya kyauta, amma ban san me xance ba gaskiya, i think it's better kaje yanxu ka sanar ma Hajja, ita xata fi daukan Action, ko kace xaka gaya ma Abbanka ba wai sauraranka xai yi ba yanxu" Shi dai bai ce komai ba, Ummi tace "Haka Allah ya kaddaro maka sai kayi hakuri, kowa ma hakurin yake, kuma babu hakurin da yake tashi in vain, there is always a reward for that, Allah yayi mana maganin duk abinda ya dame mu" shirun dai Abuturrab yayi but he looks so worried, Ummi tace "Yanxu jiran tarewan Jiddah suke kenan da suka rigata tarewa a gidan? Toh me yayi xafi sai ka bari next week idan sun gama xaman nasu koh" Ya kalli Ummi da sauri, sai kuma ya sunkuyar da kansa yace "Aa nothing is going to change because of them Ummi" Ummi tace "Amma gaskiya kaje ka sanar ma Hajja, amma kar ka gaya ma Ramlah don bana son tashin hankali" Ya amsa mata da toh kawai. Ana kiran isha Abuturrab ya isa gidan Umma, sai da ya gama waya da Ahmad da ya kirasa for almost 10min sannan ya shiga masallacin dake layin yayi sallah ya fito, ya fi minti daya tsaye bakin kofar parlon Umma don shi ko kadan bai son matsalan Umma, a hankali ya bude kofar daga karshe ya shiga ciki da sallama, su Safiyya ne a parlon ya karasa ya xauna duk suka gaishesa, ya amsa without looking at them yana danna wayarsa, Umma na bedroom dinta tare da Jiddah dake xaune saman darduma a gabanta ta sunkuyar da kanta, lafiyayyen lace me tsada ne jikinta wanda yayi mugun amsan fatar jikinta, ko ba a fada maka ba xaka san kuka take duk da mayafin da ya rufe har fuskarta, nasiha sosai Umma ke mata kamar yanda uwa xata ma 'yar ta, Maimoon ta shigo dakin da sallama ta duka kusa da gadon jin Umma na magana bata ce komai ba, Umma ta kalleta tace "Ya aka yi?" Tace "Yaya ne ya xo yana parlor" Umma ta ci gaba da yi ma Jiddah maganar da take har ta kai aya sannan tace "Toh shkkn abinda xance maki kenan daughter, and i hope u won't disappoint me by taking all my words for granted, Allah ubangiji ya bada xaman lafiya... Sai da safe" Jiddah ta kasa tashi ta fara rera mata kuka, Umma da taji tausayin har ranta ta kalli Maimoon a hankali tace "Kama hannunta ku tafi" Maimoon taji kamar ta fara kukan ita ma, ta mike a sanyaye ta daga Jiddah suka nufi kofa, Umma ta bi Jiddah da kallo cike da tausayinta, babu yanda ta iya da yayarta ne amma banda haka in dai ta Hajja ne ko yakin duniya xa ayi baxata bar Jiddah ta koma gidan Aliyu ynxu ba, kawai duk abinda xai faru ya faru, but babu yanda ta iya da Ummi.... Tun da Maimoon suka fito parlor Abuturrab ke kallon Jiddah babu ko kiftawa, sosai kayan jikinta da mayafin suka mata kyau, ya mike yana kallon Maimoon yace "Umma fa?" Maimoon tace "Tana daki" Bai ce komai ba ya tafi dakin Umma, kasa shiga yayi yana ta tsaye kamar mara gaskiya can dai yayi shahada daga karshe ya tura kofar da sallama kasa kasa ya shiga ciki, Umma dake linkin Hijab dinta tayi kamar bata gansa ba ta hade rai, ya xauna saman carpet murya can kasa yace "Ina yini Umma" Ba tare da ta kallesa ba tace "Lafiya lau" Shiru yayi bayan few minutes ya mike yace "Toh sai da safe Umma nagode, Allah ya kara girma" Umma ta juyo tace "Ba ka gode ba Aliyu, wllh ko k'uda ka bari ya cuci wannan er marainiyar Allahn, Allah ya isa ban yafe ba, ba wai an ce sai ka ajiyesu gida daya ba dole.. Wllh duk abinda ya samu Jiddah ina me tabbatar maka xan mance relationship din meye tsakaninmu in ma rashin mutunci in dau matakin da ya dace, matarka kuwa ka ja mata kunne kar tace xata yi crossing part din 'ya ta, ta tsaya iya lane dinta, she should take her eyes off my daughter don wllh bani da mutunci, a al'adanmu na fulani kusan abun kunya ne ace uwa na sintirin xuwa gidan 'ya babu dalili to kuwa sai dai a kirani da mara kunya in this case" Shi dai Abuturrab bai ce komai ba yana sauraronta kansa a kasa, Umma tayi kwafa ta ci gaba da abinda take tace "Allah dai ya ba kowa sa'a..." Jin bata sake cewa komai ba, a hankali yace "Toh in sha Allah Umma, sai da safe" Fita yayi dakin, Maimoon dake xaune kusa da Jiddah kan kujera ta mike ta kama hannun Jiddah suka fita parlon safiyya da Huraira suka rakasu har bakin motarsa, shi dai yana biye da su a baya, Maimoon ta bude ma Jiddah front seat taki shiga sai kuka take tana rike da hannun Maimoon gam, Abuturrab na kallonsu gaba daya yace "Sai da safe" Babu wanda yace komai duk suka juya, Maimoon ta kwace hannunta cikin na jiddah ta nufi gate tana goge guntun hawayen idonta, yana kallon Jiddah calmly yace "Shiga" taki shiga taji kamar ta bi su Maimoon ciki da gudu, bin kofar gidan yayi da kallo tana ganin xae dagata tayi saurin shiga motar tana kuka sosai, ya kulle motar sannan ya xaga ya bude driver seat ya shiga... Har suka isa gida kuka Jiddah take, shi dai bai ce mata komai ba yayi horn driver ya bude gate ya shiga yyi parking ya kashe motar, sae a sannan ya jinginar da kansa jikin kujeran motar yana jin yanda take shessheka, juyawa yyi ya kalleta, Lowering his voice yace "Jidderh..." Kukanta kawai take, ya kamo hannunta a hankali yace "Gaya min kukan me kike" Ta xame hannunta taki cewa komai wani sabon kukan na taho mata, bude motar yayi ya sauka ya xaga ya bude side dinta ya sauko da ita, ya kulle motar yana rike da hannunta ya nufi cikin gidan da ita, sosai take jin gabanta na faduwa tana fatan ace mafarki take yau, tsaye yayi balcony yana kallonta ganin kamar ana dada tunxurata da kukan, ya dage mayafin kanta yana kallon kyakkyawan face dinta da ya baci da hawaye, side hug yyi mata murya can kasa yace "Ohk then! Next week in sha Allah xan maida ki gidan Umma amma sai kin daina kukan nan, stop the cry now..." cikin kuka sosai tace "Next week is too far, don girman Allah kayi hakuri ka maida ni yau, wllh bana son gidan nan, don Allah nace maka...." rungumeta yayi ta dinga rera masa kuka kamar ranta xai fita tana shessheka, ya lumshe ido yana jin yanda xuciyarta ke bugawa, ga kamshinta da ya cika hancinsa, bayan few seconds ya bude idonsa a hankali yace "Gobe xan maida ki, but sae kin daina kukan..." Cikin rawar murya tace "Kace wllh" yayi kasa da murya ya daura goshinsa a nata yace "Na ce" ta dauke kanta da sauri tace "Aa wllh xaka ce" ya juyo da ita yayi kissing lips dinta lightly, underneath his breathe yace "Ga shi nace" bai jira me xata ce ba ya manna mata wani kiss din a cheeks dinta yana rike da hannunta ya bude kofar parlon suka shiga, ba ita ba har shi sae da gabansa ya fadi ganin Aunty, Safara'u, Falmata da Aneesah duk xaxxaune a parlon, lkci daya ya dauke kansa yana ci gaba da tafiyarsa fuskarsa a daure, Jiddah kuwa tunda ta hada ido da Aunty da Aneesah ta dinga bobboyewa gefensa kamar xata shige jikinsa, hakan da tayi ya sa shi rungumeta ta side dinsa har suka wuce sama su Aunty duk suka bi su da kallo, A hankali Aneesah ta fara kuka tana jin xuciyarta na mata xafi, Safara'u tace "Meye haka? Kun ga wani shashanci ko, ke kam wllh dole ma miji ya rainaki... Haka aka koya maki kiyi? To kukan uban me kike masu yanxu don uwarki??" Falmata dake hararanta ita ma tace "Wlh ke kam baki yo halinmu ba Aneesah, ga dai yanda aka shirya abu da ke, kawai ki kama yi ma mutane kuka kamar wata mara class" Aunty dau takaicin yanda Abuturrab ya wuce bai ce mata kala ba ya cikata, tun dai da wnn yarinya Jiddah ta shigo rayuwarsa ya daina mata biyayya, ya daina ganinta da girma, sai kuma ga raini yanxu, to kuwa ai babu wanda ya kamata yaji haushin Jiddah fiye da ita tunda ita ce silar rabata da Abuturrab, Sosai xuciyarta ke k'una, can ta ja tsaki tana kallon Aneesah tace "Toh kukan uban meye haka? Shi kike ma kukan ko ita?" Aneesah dae bata ce masu komai ba kuka kawai take tana jin dama duk mafarki take yi wnn bakar rana da take witnessing, yanxu kishiyarta a ka kawo mata gida tana ji tana gani, a d'an tsawace Falmata tace "Baxa ki tashi kije ba, ni fa wllh sai in tattara kayana gobe in bar gidan nan idan baxa ki bi abubuwan da aka daura ki a kai ba don xaman lafiyan ki, wannan wacce irin yarinya ce haka don Allah" Aneesah ta goge idonta ta dake ta mike da kyar ta wuce saman duk suka bi ta da wani kallo, Aunty ta ja tsaki tace "Ni abinda ke min takaici da ita trusting dinmu da ta kasa yi har yanxu, shekarana ashirin da shidda tare da mahaifinsa sai yanda nace a gidan wllh, ko uwarsa da ta kusa shekara talatin da takwas bata isa bane, idan nace eh toh eh ne, Aa kuma Aa, to kuma waye Aliyu karamin alhaki?" Wani dariya Aunty tayi tace "Toh ko abinda ya faru kwanan nan da yanda ubansa ya birkice ma ya isa a san ba da wasa nake xama gidan ba, kwanansa biyar a Abuja shi ma sai da na dinga lallabasa ya tafi sabida aiki, to kuma waye Aliyu" Safara'u tace "Dalla rabu da ita har mijina ya mutu wllh ko kallon wata Mace bai yi da sha'awan aure, ita Aneesah ta cika hanzari ne sannan ga uban son da ta dauka ta daura masa duk shi ke cutanta" Aneesah na haurawa sama ta goge idonta sosai, tsaye tayi kofar dakin Jiddah dake ta xuba kamshi don tun daga bakin stairs ake jin kamshin, ta dake, ta danna xuciyarta ta kwankwasa kofar ta koma gefe, bayan wani lkci jin ba a amsa ba ta sake kwankwasawa sai kuma ta murda kofar ta ji a kulle, Abuturrab dake duke gaban Jiddah da ta ki daina kukan da take don ganin mutanen da tayi a parlor ya kara tsoratata, ya daga kai yana kallon kofar, lkci daya tayi tsit ita ma tana kallon kofar, gaba daya a tsorace take, mikewa yayi ya nufi kofar babu yabo babu fallasa yace "Waye?" Aneesah ta dake tace "It's me Captain" bude kofar yayi yana kallonta, tun da Jiddah ta kalleta sau daya ta dauke kai, Abuturrab ya juya ya koma ya xauna gefen gado, ta bi bayansa tana tafiya a hankali tace "Sorry for the interruption..." Ba dai wanda ya tanka ta, tana murmushi tace "Sannu da xuwa amarya" Jiddah ta hade rai ta d'an ja mayafinta ta rufe fuskarta, Aneesah ta xauna saman kujera daya dake cikin dakin, tana kirkiran murmushin karfin hali a hankali tace "Welcome to our home Jiddah, Allah ubangiji ya hade kanmu ya bamu xaman lafiya, ya kauda fitina tsakaninmu..." Ko dagowa Jiddah bata yi ba balle ta amsa mata, Aneesah tayi karfin halin cewa "Kin yi shiru... I only came to welcome u for being part of us, and i thought u will also welcome...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka ba tare da ta shirya hakan ba, shi dai Abuturrab kallonta kawai yake, ta tashi ta nufi kofa da sauri ta fita daga dakin, Abuturrab ya kalli Jiddah kamar baxai tashi ba sai kuma ya mike ya bi bayan Aneesah, sai a sannan Jiddah ta daga kanta ta bi sa da wani kallo, yana fita dakin ta tashi ta karasa tayi locking kofar da makulli. Aneesah ta shige dakinta hakan ya sa ya bi ta cikin dakin, kuka take kamar ranta xai fita, ya tsaya bakin kofa yana kallonta yace "What's the meaning of that?" Girgixa masa kai kawai tayi, ganin yanda take kukan ya karasa cikin dakin, ta hade kanta da gado cikin kuka sosai tace "Captain baka ce min xaka min kishiya ba, baka ce min xa mu xauna tare ba, u once told me baka da burin mata biyu a rayuwanka, kullum cikin nuna min kake babu komai tsakaninka da Jiddah tun aurenku na farko, you deceived me all this while, me yasa baka gaya min gaskiya ba tun a farko in cire ran cewar ni kadai ce, me yasa tun sannan baka gaya min ba in hakura da tunanin ni kadai ce Captain, ka bar ni na sakankance, sannan ka dawo ka min haka? this is too painful to bear..." Yayi shiru yana kallonta, sai kuma ya xauna gefen gadon yana kallonta a hankali yace "We plan... But God plans best Aneesah, we were together before i met Jiddah, and i am sorry i never bargained for this, kaddara ta ce a haka, Allah ya rubuto min dole xan auri Jiddah kuma xan yi rayuwa da ita, and i am sorry to let u know that i can't live without her, babu yanda xanyi ita matata ce kamar yanda kike matata kema..." kuka kawai take kamar ranta xai fita, ya dagota ya jawota jikinsa yace "I am sorry all this happened Aneesah, ke ma kuma ba wai bana sonki bane, da bana sonki baxan aureki har in kai warhaka dake ba, i married u because i love u too" Ita dai kuka kawai take, ya rungumeta yace "Is that okay now?" Girgixa masa kai kawai take hawaye masu xafi na xuba idonta tace "Kasan ina sonka so me tsanani Captain..." yace "Yea na sani, kuma sai ki so abinda nima nake so ku xauna lafiya" Kai kawai ta gyada masa bata iya tace komai ba, yace "Kuma in sha Allah xan kwatanta adalci a tsakaninku" Sai da Abuturrab ya tabbatar ta daina kukan sannan ya mike yace "Yaushe su Aunty xa su bar gidan nan?" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, shiru yayi na wani d'an lokaci sai kuma yace "Sai da safe" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo wasu sabbin hawayen na sauka idonta har ya fita ya kulle kofar, dakin Jiddah ya nufa yana murda kofar ya ji a kulle, ya kwankwasa Jiddah dake kwance taki motsawa balle ta tashi ta bude, kwankwasawa ya sake yi gently amma taki budewa. Juyawa yayi ya tafi bangarensa, wanka yayi ya sauya xuwa Pajamas sannan ya xauna yana danna laptop dinsa, yana son shan shayi but come to think of the set of people sitting down at the parlor ya sa shi kin fita yayi making tea din, kuma bai son ya sa Aneesah tayi masa, ma'anar abinda Jiddah tayi ne ya kasa ganewa har lkcn, ya dai ci gaba da operating laptop dinsa kawai, he doesn't even know if he is angry or not... Sai kusan karfe sha daya da rabi su Aunty suka hauro sama jin Aneesah shiru shiru kamar an aiki bawa garinsu, Aunty ta gama kare ma kofar dakin Jiddah kallo sai kuma tayi wani murmushi ta nufi dakin Aneesah, su Safara'u na biye da ita a baya suka bude kofar, kwance suka sameta tayi bacci da hawaye a fuskarta, Safara'u ta rike ha6a tace "Toh Allah ubangiji ya sa dai ba xubda mutuncinta da kimarta taje tayi a gabansu ba, kai wannan yarinya dai bata yo mu ba wllh yanda kika san ba jinin mu ba, ko kadan bata da xuciya sai hauka da shashanci" Aunty ta tada Aneesah tace "Shine kika shanya mu a parlor kamar yan iska, ya ake ciki?" Ta murxa ido a hankali, agogo ta kalla taga karfe sha biyu saura da sauri ta dira daga kan gadon ta fita dakin hawaye na taruwa idonta, duk suka bi ta da kallo Falmata tace "Toh wajen ubanwa xata, idan kun bibiya wllh bata yi abinda ku ka ce ba, xuwa tayi ta sha kukanta ta koshi ta kwanta, wnn fitina har ina ni falmata, anya xa ayi abun arxiki da er nan kuwa?" Aneesah na fita ta dinga kallon dakin Jiddah wasu hawaye na xuba idonta, she just can't imagine this, yanxu Aliyu na dakin kenan a nan xai kwana, jingina tayi da bango ta dinga rera kuka a hankali tana jin xuciyarta na mata xafi, kamar ance ta kalli part dinsa taga hasken wutan parlor na reflecting don an kashe fitilar corridor din wajen, da sauri ta karasa xuciyarta na bugawa, tura kofar tayi ta gansa xaune parlon ya daga kai yana kallonta, ta karasa ta xauna kasan carpet ta marairaice masa tace "I am not feeling okay captain, wllh ji nake kamar xaxxabi xai rufeni" yace "Toh sai ki sha paracetamol ai" Tayi shiru bata ce komai ba, amma tana son gano ko Jiddah na dakin ko bata nan, bayan few seconds a hankali tace "paracetamol dake gidan nan na bedroom din ka ai" bai ce komai ba ya mike ya nufi dakin ya shiga, da sauri ta tashi ta tafi tana leka cikin dakin taga babu jiddah, alamar dai tana can dakinta, ji tayi hankalinta ya d'an kwanta, to kenan ba a dakinta xai kwana ba? ta koma ta xauna tayi jigum xuciyarta babu dadi, fitowa yayi daga dakin rike da paracetamol din da wani spare key, ta dinga kallonsa ya mika mata paracetamol din ta amsa yace "Idan kin sha sai ki tafi ki kwanta, sai da safe" bata iya ta ce masa komai ba ya kashe laptop dinsa ya ajiye sannan ya nufi kofa, ji tayi kamar xuciyarta xai daina aiki kwata kwata at that moment, har sai da ya fita parlon sannan ta fashe da kuka sai kuma ta mike da gudu ta nufi kofar tana lekansa taga hanyar dakin Jiddah ya nufa, tana ta lekensa har ya bude kofar da makullin hannunsa sannan ya shiga ya kulle.[7/26, 9:00 AM] Ummuanwar🥰: Abuturrab ya bi ta da kallo ganin da speed din da tayi use ta shige bandaki ta kulle kofar, ya karasa cikin dakin ya tsaya kusa da window ya rungume hannunsa, lkci lkci kuma yake kallon kofar bandakin, at first he pretend he isn't angry at all, yayi iya kokarin ganin bai ji haushin hakan da tayi ba, but he realize he was only deceiving himself cause he was jet angry, few days ago tayi masa rashin kunya, daxu kuma ya fita kafin ya shigo ta kulle kofa da makulli another rashin kunya, yanxu kuma ya shigo ta shige bandaki ta kulle... kallon kofar bandakin yayi for almost 3 minutes, kawai ya ji dole ma sae yayi maganinta yau, kofar ya nufa ya murda duk da ya san ta sa makulli, Jiddah dake tsaye jikin washing machine din bandakin ta wani harari kofar ta juya masa baya kamar irin yana ganinta din nan, calmly yace "Xo ki bude kofar nan right away" K'in cewa komai tayi, yace "Ba ki ji na ne?" Tayi masa shiru still, yace "Don't allow me to get that door open my self" Tace "Toh ni me xan maka idan na bude kofar, ka tafi wajen matarka mana, ai na xata a can ya kamata ka kwana tunda ka bi ta..." Shiru yayi na kusan one minute abinda ta fada na rotating a kansa, can yace "Ohk fine" Tana jin ya bude kofar dakin ya kulle, tayi ta tunanin to fita yayi? ita dai tana ta tsaye bandakin ta gaji da tsayuwa daga karshe ta durkusa, tana nan a haka har bacci ya fara damunta, xaro ido tayi ganin duhu ya gauraye bandakin lkci daya, hasken wata kadai ke reflecting ta window, mikewa tayi ta karasa kofar bandakin gabanta na faduwa ta murda makullin a hankali ta bude, without making any sound ta fito cikin dakin, ji tayi an fixgota da karfi, sbda rudewa da yanda ta gigice bata san sanda ta tsala wani ihu da karfi ba jikinta na rawa ta fara basa hakuri, da sauri ya rufe bakinta don bai ta6a xaton xata yi wannan ihun ba yace "Baki da hankali ne, baki san dare ne ba" Kuka ta fara yi tana son kwace kanta amma ya ki saketa, ba Aneesah da Falmata dake daki daya ba, har su Aunty da Safara'u dake room din karshe sae da suka ji wannan ihu na Jiddah duk da sun fara bacci ma, ita dama Aneesah ba baccin take ba falmata ce ke bacci, tun bayan da taga Abuturrab ya shiga dakin Jiddah ya kulle almost an hour ago ta wuce dakinta hawaye na xuba idonta kamar famfo, shine tun sannan take ta juye juye kan gado abin duniya yabi ya dameta, taji kamar da gaske xaxxabin karyan da ta ce masa na neman rufeta, sae kuma ga wannan ihun Jiddah da ya kara gigitata, sauka tayi daga kan gadonta ta xauna kasa tana jin kamar mashi ake soka mata a kirji ta dinga rera kuka tana imagining ihun meye Jiddah tayi, Falmata dae na kwance tana jin ta, ita ma dai takaicin ne ya cikata ta dinga jin kamar ita aka ma wannan kishiya... Ganin yanda Jiddah ta tsorata ya sa Abuturrab ya ji gwara ya kara tsoratata ya fidda rainin tsakaninsu ko xata shiga hankalinta da shi, don ya ga wani tashe raini take ji, ai kam Jiddah ta tsorata iya tsorata don taga sababbin al'amarin da kanta ya kasa iya dauka daga Abuturrab, taga abinda ya fi karfin tunaninta, bata ta6a sanin haka Abuturrab yake ba, gashi ya ki bata daman ko tari, roko ne fal bakinta da take son yi masa ko xai tausaya mata ya kyaleta amma yaki bata chance din hakan, Bai yi tunanin tsoronta ya kai haka ba, duk da babu abinda yayi niyyar mata without her consent amma sai yaga yana neman crossing boundaries dinsa shima, he was finding it hard to control himself anymore, ba karamin namijin kokari yayi ba na ganin ya kyaleta ya koma can end din gadon yayi kwanciyar upside down, ai tana samun wannan opportunity din saketa da yayi ta dira daga saman gadon ta kwala wani ihun ta fashe da kuka tana kiran Umma, ta kira Umma yayi sau biyar, gaba daya tayi mugun tsorata, bata ta6a xaton abinda ya mata ba, shi kam ina ya ga strength din hanata kukan nata da kiraye kirayen sunan Umma, kyaleta kawai yayi tayi me isarta, daga karshe ma tashi yayi ya shige bandaki ya kulle, wannan dare dai daga Aneesah har su Aunty kusan kwanan xaune suka yi, Aneesah ta ji dama ta mutu kafin safiya da wannan mugun abinda taji ma kunnenta, Falmata kuwa sae cewa take da gangan Jiddah ta dinga wannan abun duk karya ce, abu ne da aka kissa mata tun daga gida, Abuturrab ya fi awa daya a bandakin kafin ya fito wajajen karfe uku saura, switch din dakin ya kunna ya ganta kwance kasan tiles ta takure waje daya tana bacci, bai san lkcn da yayi murmushi ba ya kashe wutan ya nufeta ya duka a hankali ya kai hannu xae dauketa, wani ihun ta sakar masa a raxane, ya rufe bakinta da sauri murya can kasa yace "Ba abinda xan maki..." Daukanta yayi ya kwantar da ita saman gadon ya lullubeta da blanket, ita dai jikinta banda bari babu abinda yake, ta gama tsorata da lamarin Abuturrab, don ma ta saki jiki tayi bacci without fear, far end of the bed ya tafi ya kwanta ya juya mata baya, kasa bacci yayi gaba daya daren nan, tunaninsa kawai ya ranan da xae san jiddah xai kasance, gaba daya ya gama gano cewar raguwa ce kuma matsoraciya, ba ma wannan ba he couldn't find any way duk kokarinsa, unlike Aneesah... which the case is different on that very day... Da asuba a kan kunnen Aneesah ya bude kofa ya tafi masallaci, bai kuma tafi masallacin ba sae da ya sa ma kofar dakin Jiddah key, bayan ya gama azkar dinsa a masallaci ya shigo gidan, bude kofar dakin yayi ya ga har sannan Jiddah bata tashi ba duk da ya tasheta tayi sallah kafin ya fita, karasawa yayi ya xauna gefen gadon yana kallonta ya kai hannu fuskarta yana shafawa gently, sae kuma ya ta6a forehead dinta ya ji da dumi, a firgice ta mike xaune ta koma baya yace "Are you okay?" Ta kasa kallonsa xata sauka saman gadon ya jawota, ji yayi jikinta da xafi ta marairaice masa tace "Xan je in yi sallah" yana kallon duk jikinta yace "Are u feeling pain anywhere?" Girgixa masa kai tayi bata yarda sun hada ido ba ta wuce bandaki da sauri, gaba daya she looks afraid, ya bi ta da kallo, toh ae shi kuma ba irin wannan tsoron nasa yake son ta dinga yi ba, yana ta xaune har ta fito bandaki ta tada sallah... Bayan ta idar ta ki daga kai ta kallesa, a hankali yace "Jidderh" Kamar jira take ta fashe masa da kuka taki yarda ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Ki je kiyi wanka ki shirya" ita dai bata ce komai ba, ya mike ya fita dakin sannan ya kulle da makulli ya tafi da makullin bangarensa, wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya ya dau jakar laptop dinsa da makullin mota sannan ya fito, yana xaune dakin nata ya jira har ta gama shiryawa, ko da wasa bata yarda ta shirya a gabansa ba, a bandaki tayi komai, shi dai kawai murmushi yake yana danna wayarsa, bayan ta fito ya sa ta hada kayanta kala uku a karamin jaka ya amshi jakar sannan suka fito dakin, kulle kofa yayi ya sauka downstairs tana biye da shi, babu kowa a parlon infact kamar ba mutane gidan ma gaba daya, Jiddah dai ta xauna kan kujera har sannan taki yarda su hada ido da shi, shi kam sai kallonta yake don hakan da take dariya yake basa, Wayarsa ya ciro ya shiga kiran Aneesah, Aneesah dake xaune dakin da su Aunty suka kwana idonta yayi bulu bulu ta kalli wayarta dake hannunta, sai kuma ta jefar da wayar gefen gado fuskarta daure, Safara'u ta dauka ganin me kiran wayar ita ma ta ajiye a gefe, Aunty ta kallesu tace "Wa ke kiran nata?" Safara'u ta kyabe baki tace "Shi yake kiranta, to uban me xata masa? Ki ita xata gasa masa amaryar" Aneesah ta matse kwallar idonta, Aunty tace "Je ki kiji kiran meye yake maki, tashi ki je" Aneesah dai bata ce komai ba, Safara'u tace "Tabbb!! Lallai ni naga abinda ban ta6a ji ba jiya, a cikin surkanka sbda baka daukesu da mutunci da kima ba? Muna gidan xai yi wannan ta6arar?" Ba dai wanda ya amsa mata, ta kalli Aunty tace "To idan mu ya maida mu banxa ke kuma fa? Yana fa sane kina gidan nan ba tafiya kika yi ba yayi abinda yayi, idan uwarsa ce ke gidan xai yi haka?" Aunty dai takaici, bakin ciki, da bacin rai duk ya baibayeta, yanda take ji iyakar haka Aneesahn ma xata ji, Aneesah ta sakar masu kuka tace "Ce min fa ku ka yi har xamansu ya kare ance baxai kusanceta ba, haka fa ku ka ce min, kuma duk kun ji abinda aka yi a gidan nan jiya, shkkn sai ya ji dadin min kallon gantalalliya kenan? Shkkn sai yaji dadin fara min gori kenan" Kuka sosai take cike da takaici, Aunty tace "Haka aka ce maki ya kusanceta? Ke baki san makircin mace bane, wllh wllh baxan yi kaffara ba babu abinda ya wakana tsakaninsu, an fa gaya min komai, to meye na daga hankali, ashe ma abu me sauki ne kusantar nata, tsabar makirci ne kawai irin na mata fa" Mikewa Aneesah tayi ta dau wayarta ta fita dakin ganin yana sake kiranta, sai da ta shiga dakinta ta dau hijab har kasa ta saka ta jawo hijab din ya kusa rufe rabin fuskarta sannan ta daga kiransa kafin tace komai yace "Ki sauko downstairs yanxu" Bai jira me xata ce ba ya katse wayar, saukowa kasa tayi ta gansu xaune a parlon, bata yarda ta kalli inda Jiddah take ba, kamar yanda Jiddah ma ta ki kallon inda take, ta tsaya bayan kujera babu yabo babu fallasa tace "Good morning" yace "Morning, dama xan ce maki xan koma aiki, hope ba ki bukatar wani abu?" Aneesah ta d'an saci kallon Jiddah dake sanye da Hijab har kasa ta sunkuyar da kai, sai kuma tace "Toh fa!! aiki kuma captain? Har an gama cin amarcin kenan? Ni da na xata hutu xaka dauka" Bai bata amsa ba kuma bai kalleta ba, tayi murmushi tace "Toh shkkn Allah ya tsare hanya, amma baxa kayi breakfast ba?" Yace "Xan yi a jirgi" tana ci gaba da murmushi tace "Toh shkkn, in Allah ya yarda babu wata matsala har kaje ka dawo, hope ka gaya mata ta saki jikinta da ni, ni kam kai ma kasan bani da matsala, xa kuma mu xauna lafiya xan dauketa tamkar kanuwata... Babu wani damuwa" Sai a sannan Abuturrab ya daga kai ya kalli Aneesah, tayi murmushi irin tana assuring dinsa din nan kar ya ji komai, bai ce mata komai ba, sai tace "Amma baxa ka shiga ka gaisa da su Aunty ba kafin ka tafi? sun tashi fa" Yace "Xa mu yi hakan ta waya, Jiddah kuma da ita xan tafi..." Sosai gaban Aneesah ya fadi tana kallonsa don duk a tunaninta barin Jiddah xai yi tunda dai ba xama xai je yayi a waje daya ba, A hankali tace "Da ita kuma? Naga ai ba xama kake a gari daya ba" Yace "Ehh" yana fadin haka ya mike ya dau jakar kusa da shi yace "If there is anything sai ki kirani" yana kallon Jiddah yace "Tashi mu je" a hankali ta mike ta nufi kofa tana tafiya kamar bata son yi, Aneesah ta bi ta da wani irin kallon tsana, ya bi bayanta har suka fita parlon, da gudu ta koma sama taje sanar ma su Aunty ai da Jiddah xai tafi.... Karfe biyar Abuturrab ya shigo gidansa na Abuja bayan sun sauke jirgi a garin Abujan, Jiddah ta xauna parlon da babu abinda ya canxa daga yanda ta san shi months back, har a lkcn taki sakewa da Abuturrab har xuciyarta taji tsoronsa take, bayan wani lkci ta saci kallonsa suka hada ido don kallonta yake, dauke kanta tayi da sauri, yyi lowering voice dinsa yace "Since u are uncomfortable staying with me here, sai ki shiga daki ko?" Ko rufe baki bai yi ba ta mike ta wuce daki tana rike da handbag dinta ta rufe kofar, ya bi ta da kallo yayi murmushi a ransa yace "Xaki ji tsoro me dalili soon yarinya" Da yake sun ci abinci a garin lagos kwanciya kawai yayi kan 3 seater yana kallon movie da ake yi a Tv, shidda da yan mintuna aka danna bell din parlon ya mike ya isa kofar sanin wanene, ya bude kofar, Ahmad na murmushi ya shigo yace "Latest ango in town, irin wannan fresh din haka Captain... Uhnnn" Abuturrab ya shafa kansa yace "Xan dai yi fresh din" Xaunawa suka yi kan kujera Ahmad yace "Toh ina Jiddar? Kace min kuna tare" Abuturrab ya kalli hanyar bedroom kafin yace komai Ahmad yace "Ohh shigewa ciki kace tayi don na xo??" Abuturrab yace "Not at all, i think bacci take yi, she is been inside since" Ahmad yace "Better!! Hope ka dau shawaran da na baka?" Abuturrab yace "Wanne a ciki?" Ahmad ya hararesa, a hankali Abuturrab yace "I want to ask u Ahmad" Ahmad yace "I am all ears" Abuturrab ya d'an yi shiru sai kuma ya shafa beard dinsa alamar dai ya rasa ta inda xai fara tambayar, Ahmad yace "Akan me kake son min tambayar?" Abuturrab yace "Marital Bed" Dariya Ahmad yayi yace "Then we should chat..." a hankali Abuturrab yace "That will be better" Ahmad yace "Hope no intimate relationship took place between u and...." Abuturrab ya kallesa yace "I couldn't find the way" Wani dariya Ahmad ya fasa ya jinginar da kansa jikin kujera, Abuturrab ya hade rai yana kallonsa, Ahmad yace "We really need to chat about that then, so bak'in naka sun bar gidan ko suna nan har yanxu" Abuturrab yace "Suna nan" da mamaki Ahmad ke kallonsa, can yace "Ohk haka xa ka xuba masu ido kenan, na gaya maka they have a mission to accomplish ka ki taking dina serious Captain, tun da can me ya sa basu xauna gidan naka ba gaba dayansu sai yanxu?" Abuturrab dai bai ce komai ba. Ana kiran magrib Abuturrab ya shiga dakin da Jiddah ke ciki ya sameta tana bacci, ya rasa me yasa ta dawo so silent, ya tasheta tayi sallah, sannan suka fita masallaci tare da Ahmad, bayan sun dawo masallacin Ahmad yace "Baxa mu je can gidana ku ci abinci ba" Abuturrab yace "Is ur wife around?" Ahmad yace "Yea tun da Jiddah ta koma gun Umma kawai na dawo da ita Abuja, baka yi mamakin me yasa na rage xuwa weekend kd ba" Abuturrab yace "Ohk ban sani ba" Daki Abuturrab ya shiga ya sa Jiddah ta shirya su tafi gidan Ahmad, hijab dinta kawai ta sa ta fito, ta gaida Ahmad tana sunkuyar da kanta ya amsa da murmushin sa, Ahmad hira kawai yake da Captain, amma da ta daga kai sai sun hada ido da Abuturrab dake kallonta, daga karshe ta koma can end din a hankali ta xauna har suka isa gidan. Sosai Ramlah tayi farin cikin ganin Jiddah a gidanta don Ahmad bai gaya mata suna xuwa ba, Jiddah ma taji dadin ganinta sosai. Abinci ta kawo masu nan parlon, Ahmad ya dibar masa shi da Abuturrab, ita dai Jiddah na xaune kan kujera idonta na kan tv dake aiki, Ramlah ta xuba masu a plate ita da Jiddah tana kallonta da murmushi fuskarta tace "Sauko Aunty Jiddah" Jiddah dai tayi murmushin karfin hali amma bata sauko ba, Ramlah tace "To tashi mu shiga ciki" Ba musu Jiddah ta mike ta bi ta suka wuce bedroom dinta, Ahmad dake kallon Abuturrab da ya bi Jiddah da kallo yace "Uhnn wannan kallo haka Captain?" Abuturrab ya shafa kansa ya ci gaba da cin abincin gabansu... Ba laifi Jiddah ta ci abincin don a lagos ta ki sakewa ta ci sbda Abuturrab da ya sa ta gaba, hira suka dinga yi da Ramlah har aka yi isha, karfe takwas da rabi Ahmad ya shigo dakin da sallama yana kallon Jiddah yace "Captain na jiran ki Jiddah" Marairaice masa tayi tace "Ya Ahmad don Allah kace masa ya bar ni in kwana a nan" Tana fadin haka sai hawaye ya cika idonta, shi dai Ahmad dariya ta basa, Jiddah ta kalli Ramlah tace "Don Allah ki masa magana ya bar ni a gidan nan" Ramlah tayi dariya tace "Aa wnn sai dai Dr yayi masa magana" Ahmad na kallon Jiddah yace "Ki je ki gaya masa xai bar ki ma sani" Gaba daya a tsorace take, Ramlah dai sai kallonta take, Ahmad yace "Yea kije ki gaya masa xai bar ki" A sanyaye ta mike ta fita, Ramlah ta wara ido tace "Toh ko tsoron Yayan take?" Ahmad yayi murmushi ya xauna gefen gado, Jiddah na fitowa parlor suka hada ido da Captain dake xaune, karasawa tayi kanta a kasa ta durkusa d'an nesa da shi a hankali tace "Dama don Allah ka bar ni in kwana a nan plsss" Kallonta ya dinga yi, ta daga kai ta kallesa jin yayi shiru, lkci daya hawaye har ya kawo idonta, yace "Tsorona kike ji Jiddah?" Girgixa masa kai tayi da sauri, yace "Toh shkkn, sai da safe" Mikewa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, sai kuma jikinta yayi sanyi, amma dai wata xuciyar tace mata gwara haka, da dai abinda Allah ya nuna mata jiya gwara kawai ta kwana gidan Ramlah. Washegari Abuturrab yayi piloting xuwa Kano leaving Jiddah behind in Abuja shi kansa ya ga hakan ya fi tunda ya lura bata son hawa jirgi, a kwanaki hudun nan duk abinda Ramlah ke amfani da shi na mata wanda Umma ta hana Jiddah haka ta dinga bata, to tunda ita bata san meye shi ba haka xata amsa ta sha, all this while kuma Aunty da su Safara'u na gidan Aneesah suna jiran dawowar Abuturrab da Jiddah gidan, Ranan Thursday Ramlah na parlor tare da Jiddah aka danna bell, mikewa Ramlah tayi ta nufi kofar ta bude tana tambayar waye, Abuturrab ta gani tsaye bakin kofar, ta washe baki tace "Sannu da xuwa yaya" sai kuma ta basa hanya ya shigo parlon, sai da gaban Jiddah ya fadi da ta hada ido da shi, ya karaso ya xauna parlon yana kallonta yace "Tashi ki dauko kayanki" Ramlah dai na tsaye gefe sai murmushi take, Jiddah taki motsawa a inda take, Ramlah tace "Mu je ai kayan a hade suke" Daga haka ta nufi dakin da jakar kayan Jiddah wanda Ahmad ya taho mata da shi yake, mikewa Jiddah tayi ta bi bayan Ramlah tana tafiya kamar xata yi kuka ya bi ta da kallo, Ramlah ta rufe kofar bayan Jiddah ta shigo tana kallonta tace "Me yasa kike haka Jiddah yana maki magana kin yi shiru" Jiddah ta fashe da kuka ta xauna gefen gado, Ramlah ta xauna kusa da ita da mamaki tace "Gaya min meye damuwarki?" Cikin kuka tace "Wallahi ni tsoronsa nake ji" Sake baki tayi tana kallonta, can tace "Tsoronsa kuma Jiddah? To saboda me" Jiddah tayi shiru tana share idonta xuciyarta na bugawa, Ramlah tayi shiru sai kuma tayi murmushi tace "Kin ta6a jin inda mata ke tsoron mijinta? Look Jiddah ki ajiye duk wani kuruciya aside babu wannan a aure sannan kishiya gareki, kishiyar kuma ba mai tsoron Allah ba, ko so kike ta kwace maki miji?" Kallonta Jiddah ta dinga yi, Ramlah tace "Wllh idan kina masa haka fita harkanki kawai xai yi ya kama kishiyarki tunda ita ai bata tsoronsa, dubi ranan fa kiri kiri kika ki binsa sai shi kadai yayi wucewarsa, so kike ya daina kulaki ya barki da tsoronsa da kike?" A hankali Jiddah ta girgixa mata kai, Ramlah tace "To kar ki sake yarda ki sa ma ranki kina tsoron mijin ki, kuma kar ki xama raguwar mace... It's something that happens just once in lifetime, you get me" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Ramlah ta mike ta dauko jakarta ta mika mata tace "Tashi ki je yana jiranki, sai da safe, xan kira wayarsa gobe sai ya baki mu yi magana" Jiddah ta goge idonta ta amshi jakarta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.