Ind Rai Part 1 Complete Hausa Novel By Aisha Aliyu Garkuwa
Reading file: Inda Rai Book 1 By Aisha Aliyu Garkuwa.txt
Chapter 2 of 2
*Page biyu kacal suka rage mu gama free pages bayan wannan, ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276, kuma mutan Niger 1000fc ne rak zaku biya ta wurin Mommy +22790899076.*
Cikin shesh-sheƙan kuka taci gaba da cewa.
“Yah Afif ne ya mata ciki babu wanda zai mata ciki a duniya bayan shi,shine ya maidata tamkar matarsa”.
Wani irin karkarwa da rawa jikin Yah Abana ya ɗauka maganar tazo masa abaxata baiyi zato ko tsammanin jin irin waɗannan kalaman ba.
Rawa zuciyarsa keyi domin sam bata yarda ba kuma bata amince ba lokaci ɗaya yaji jinsa na ƙoƙarin ɗaukewa..
Yayin da Taj kuwa tunaninsa, nazarinsa da ƙwaƙwalwa suka tsaya daga bugawar da suke haka zalika kunnuwansa sunyi dif daga sauraren abinda suke kana idanunsa sunyi dulum daga kallon abinda suke babu abinda yake gani face duhu haka nan yaji numfashinsa na ƙoƙarin barin gangar jikinsa fahimtar yana gab da sumewa In yayi garajene yasan ya ɗan gyara zamansa cikin ƙarfin hali yayi saurin fisgo salati da tasbihi daga cikin zuciyarsa zuwa harshensa duk da bai fito kan lips ɗin sa mutane sunji ba amma da taimakon kalmar _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun Allahumma Ajirni Fii musibati Wa'alhlifli khairan minhaa_ da yake naimaitawa ya bawa numfashinsa damar dai-dai-tuwa ya koma ya zauna kana ya bawa kunnuwansa damar jin maganar da ake yi sai dai har zuwa lokacin zuciyarsa bata samu salama da sa'idar da zata iya komawa bugawanta na aihini ba, sai wani irin bugawa da yake da azabebben ƙarfi da watsa jini liter ɗaya acikin ko wani second saboda ɗinuwar daya shiga...
Ummey kam baki ɗaya daskarewa tayi ji take kamar tana yawo asararin samaniya takasa fahimtar cewa araye take ko amace.
Mom Amal kuwa wani murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
“Uhum haba shiyasa mana ashe da dalili, shiya ko yaushe in akace aje ayi gwaji yake ta lauye-lauye haba koda naji al'amarin nan da ban mamaki da ɗaure kai”.
Da sauri Yah Hafiz ya shiga girgiza kansa cikin tsananin mamaki yace.
“Noooo!,Noooo dan Allah kuyi shiru bana son jin maganar nan Mom Amal ki daina faɗa”.
Yah Yusuf kuwa hannunsa yasa ya toshe kunnuwansa duka biyu yana mai girgiza kansa yayin da Hajiya Halisa Mahaifiyar Yah Hafiz ta juya ta kalli Meymer tare da cewa.
“Meymer kiji tsoron Allah kiji tsoron irin abinda kike faɗa Meymey kisan akan wakike magana,Afif fa, Taj kike cewa wai shi yayiwa Laylah ciki ƴar daya ɗauka ya riƙe kana ya maye mata gurbin Uwa, Uba,Yayu da ƴan Uwa yanda yake riƙe da ita yake rainonta tamkar ƴar cikinsa”.
Cikin matsanancin kuka Meymey ta rarrafo ta dawo gabanta cikin rawan murya tace.
“Wallahi Hajiya idan nayi mishi ƙazafi Ubangiji yana gani, idan na mishi ƙazafi Allah ya hanani kwanciyar hankali.
Yanda ya maye mata gurbin uwa, uba haka zalika ya zauna a gurbin mijinta.
Kuna gani koda tafiya zaiyi da Laylah yake ya barni baya tafiya dani. ki gafa kwanan nan suka dawo daga Nigeria kwana goma sukayi wallahi ba ƙazafi nake masa ba ai gashi nan suna zaune yayi inkari mana ba gashi nanba, kawai shiru yayi ba tunda yasan baida gsky”.
Ta ƙare maganar cikin matsanancin kuka da gigita har kamar numfashinta zai yanke...
Ummey kuwa cikin tsananin kaɗuwa jikinta ya ɗibi wani irin karkarwa tamkar wacce aka tsoma cikin ruwan ƙanƙara baki daya ilahirin jikinta ɓari yake numfashinta na kokowa da juna da ƙyar ta samu ta fara fisgo kalmar _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun Allahumma Ajirni Fii musibati Wa'alhlifli khairan Minha_ sune abinda take iya maimaitawa wannan kalmar da take maimaitawa shine yasa Taj ya fara ji da ganin ninsa ya dawowa ahankali ya fara kallon mutanen cikin falon duk da cewa dishi-dishi yake ganinsu.
Ganin tana ƙoƙarin shiɗewane yasa cikin sauri Ummu Aryaan ta miƙe kana ta ɗauki roban Swan dake gaban Malam ta balle murfin kana ta tallafe Ummey tasa mata goran abakinta cikin sanyi tace.
“Kisha”.
Kai Ummey ke girgizawa tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun”.
Ji take sam ba zata iya ba...
Yah Yusuf kuwa tun lokacin daya toshe kunnensa yake jujjuya kansa har zuwa yanzu bai bari ba.
Yayin da Kabeer da Aryaan kuwa ido suka zubawa malam suna son karantar wani irin yanayi yake ciki da kuma hukuncin da zai iya ɗauka.
Malam kuwa baki ɗaya ilahirin jikinsa tsuma yake yayin da idanunsa suka kaɗa sukayi jawur tamkar garwashi kana jijiyoyin kansa sun tashi musamman babban jijiyan dake kan hancinsa ta taso har tana harbawa tsaban tsananin tashin hankali da kiɗima kana da yanda kalmar ta dake shi ji yake cikin gigicewa mai haɗe da ɗimuwa, fahimtar kamar yana gab da ɗimaucewa ne yasa shi maimaita _Allahuma Ajirni Fii musibati Wa'alhlifli khairan Minha Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun Lahaula walaƙuwwata illah billah_.
Jin yanda sautin addu'oin ke fitowa daga bakinsa ne yasa kowa dake cikin falon ɗaukar addu'oi banda Kabeer, Aryaan da Mom Amal ko wannensu da tunanin da yake aransa.
Ita kanta Meymer batasan lokacin data fara maimaita _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun ba_.
Laylah kuwa cikin rauni ta saki wani marayan shesh-sheƙan kuka mai haɗe, da ɗimuwa, tashin hankali, gami da rauni ganin yanda baki ɗaya falon ya gigice wasu na kuka wasu sun ɗaura hannuwansu akai zuwa yanzu ta fahimci duk akanta ne sosai kukan da take ya tsananta wanda har ta kai matakin da numfashinta ke shirin barin gangar jikinta.
Ganin halin da take cikin yasa Meymer yin saurin rarrafawa ta jawo ta jikinta ta rungumeta tana shafa kanta kana itama tana cigaba da kuka.
Cikin shesh-sheƙan kuka tace.
“Kiyi haƙuri Laylah ba laifin ki bane ya cuceki ya cuci rayuwarki.
Nima ya cuceni ya wulaƙantani iyayena sun aura masani amma bai ɗaukeni matsayin mace ba bai kalleni matsayin mace ba”.
Laylah kam kuka take tamkar ranta zai fita Meymer kuwa cikin tashin hankali ta cigaba da cewa.
“Baki da laifi dan shine ya cucemu ya wulaƙantar dani ya ajiyeni tamkar gunki bai taɓa kallona Amatsayin matarsa ba ya ɗauke ki ya maye gurbina dake azuciyarsa da kuma jikinsa ya maidake abar biyar buƙatarsa”.
Ta kai karshen maganar tana sake fashewa da kuka.
Cikin wani irin fusgar magana Malam ya kalli Taj akaro na farko a rayuwarsa yace.
“Tajuddeen”.
Cikin ruwan murya kana lips ɗin sa na karkarwa ya kira sunansa...
Taj kuwa cikin ruɗu ya rarrafo akan gwiwarsa yazo gaban mahaifinsa ya tsugunna.
Malam kuwa cikin tsira masa Idanu yace.
“Taj me nake ji?,Me ake cewa?,Me zaka iya cewa akai?”.
Ina ya kasa mgn sai kansa kawai yake jujjuyawa.
Cikin tsananin tsoro da kiɗima Ummey ta dafe hannunta aƙirji tsoronta ya hau-hauwane saboda sanin shi mutum ne da baya taɓa iya kare kansa arayuwarsa, baya taɓa iya in kari kuma, baya musu tafi kowa sanin yanda Taj yake tasan yanda ya tashi ko bashi yayi laifi ba muddin akace shi yayi baya taɓa iya In-kari wannan tunanin da tayi yasa ta saki wani maraitaccen kuka mai cike da ƙuna a zuciya.
Taj kuwa kansa kawai yake juyawa.
Malam kuwa cikin ɗimuwa da kaɗuwa ya cigaba da cewa.
“Taj ka buɗe baki kayi min magana me nake ji?.
Me nake ji Tajuddeen?”.
A kuma dai-dai lokacin Uncle Jibril tare da Momyn Meymer sukayi sallama jin kamar falon Aruɗe ne yasa cikin sauri suka ƙara sa shiga Falon.
Momyn Meymer na shiga cikin sauri ta nufi kan Ummey kana ta tallafo ta jikinta tare da faɗin.
“Subhanallah Hajiya Fati meke faruwa?”.
Sai kuma tayi saurin juyawa jin Mom Amal na cewa.
“Menene ma bai faru ba Hajiya Ruƙayya babu abinda bai faru ba. Tajudden ya zubar mana da mutuncin gida ya tozarmu ya wulaƙantamu ya tozarta tarbiyyar da ake gina wa tun daga kan yayun sa har ƙannensa”.
Cikin tsananin mamaki Momyn Meymey ke kallonta tana jin tashin hankali Mom Amal kuwa cikin tarin tsanarsa ta cigaba da cewa. “Tajuddeen ya tozartamu ya bamu kunya yaci amanar hadddar Alkur'ani izu sittin dake kansa Tajuddeen yayi kwance kwance ya ɗibgawa Laylah ciki ya rasa wacce zai yiwa ciki sai marainiya dan jarabar tsiya matarsa bata ishesaba sai ya ƙara da yarinyar amana”.
Cikin sauri Ummey ta sake toshe kunnuwanta tare da cewa.
“Laaaa, la, laaaa, la No Noooo bana son ji bana son ji.
Da sauri Uncle Jabril ya ƙarasa gaban abokinsa ya zauna tare da cewa.
“Ya Salam Malam Muhammad kai ya kamata kayi control ɗin su amma sai kuma ka ɗimaucewa ka ɗimautar dasu”.
Sai kuma ya juya ya kalli Yah Hafiz yace.
“Hafiz ka kwantar da hankalinka”.
Sai kuma ya sake maida kallonsa kan Yah Yusuf yace.
“Me haka kuke ɗinaucewa!?”.
Kallonsa ya kuma mayarwa kan Yah Abdurrahman wanda tunda Meymer tace Afif ne yayiwa Laylah ciki ya buɗe bakinsa bai rufe ba sai hawaye dake ta kwaranyo nasa Aransa yace.
kenan mafarkin da nayi yana ƙoƙarin tabbata akwai, ƙalubale da masifa da zata saƙƙo acikin family na, ta watsa mana farin ciki ashe kalubalen dana gaani akan Tajuddeen zai sauƙa!.
Yah Abana kuwa hannu ya ɗaga tare da dakatar da Uncle Jibril kana ya kalli Taj da cewa.
“Taj me nake ji?,Me Meymey take faɗa?, Tajuddeen me nake ji?,”.
Shi kuwa Taj har zuwa lokacin ya kasa magana sai jujjuya kansa yake yayin da lips ɗin sa ke rawa kana Idanunsa sun kada sunyi jawur Araunane ya juya ya kalli Ummey jin tana cewa.
“Kayi magana Afif shirunka awannan lokacin zai iya yi mana cutar da har abada baza ku warke ba. Tajuddeen ka buɗe bakinka kayi In-kari akan abinda nake da yaƙinin baza ka aikata shiba”.
Araunane ya runtse idanunsa ya kasa magana kwata-kwata bazai iya magana ba dan da zaran ya buɗe baki da niyar zaiyi magana sai yaji tamkar zare ake sawa ana tsuke bakinsa saboda nauyi da zuciyarsa tayi masa.
Cikin tsananin fushi Yah Abana ya ɗaga hannu tare da tsinka masa mari akan kumatunsa kana yace.
“Ba magana nake maka ba? kayi shiru kana kallona?”.
Sake risinar da kansa ƙasa yayi sam ba zai iya magana ba sai dai atake fuskarsa ta rine tayi ja jijiyoyin jikinsa suka tashi lokaci ɗaya jikinsa ya sake rikicewa da karkarwa wani irin kiɗima da ɗimuwa yake ciki wanda tunda yake a iya tsawon rayuwarsa bai taɓa riskar kansa aciki ba, kana nadama mai tarin yawa ta rufe mishi dukkan jiki da zuciya.
Hajiya Babba ce ta miƙe kana ta ƙarasa gaban Yah Abana tare da risinawa tace.
“Dan Allah na roƙeka dan darajar Annabi kada ka yanke hukunci cikin fushi. ka fini sanin waye Tajuddeen wani ma zai bada shaida akansa, bare kuma kai kada kayi gaggawan yanke hukunci akansa kai masa uzuri sannan ka bashi dama”.
Cikin sauri Ummu Aryaan ta taso, ganin abinda take sonyi yasa Aryaan sa hannu da niyyar riketa ahanzarce ta buge hannunsa kana ta tsugunna gefen Yah Abana tare da cewa.
“Kada ka manta cewa Tajuddeen bai taɓa kare kansa ba tun yana Karami Tajuddeen bai iya musu ba koba shi ya aikata abuba, kamar yadda ko baya son abu baya musu in ka sashi haka yake aikata shi. Baya iya musu bare ya kare kansa sam bai iya In-kari ba dan Allah dan darajar Annabi ka riƙa maimaita Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun za'a samu bakin zaren”.
Ummey kam wani irin sassayan kuka take cikin rauni da miƙa lamuranta zuwa ga Ubangiji mabuwayi gagara misali tace.
‘“Taj kayi magana kayi magana”.
Baki ɗaya haka falon ya ruɗe ko wannensu na cikin tashin hankali da Alihini saɓanin Aryaan Kabeer Mom Amal...
Uncle Jibril kuwa gyaran murya yayi cikin nutsuwa yace.
“Kuyi haƙuri kuyi shiru duk abinda yayi tsanani yana tare da sauƙi ”.
Jin haka yasa suka shiga maimaita Kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun yayin da muryoyin su keyin ƙasa...
Meymer kam rarrafowa gaban Mahaifinta tayi cikin matsanancin kuka tace.
“Abba Yah Afif yaci amanata Abba ka aura min Yah Afif na zauna aƙarƙashinsa duk da ba sona yakeyi ba, na bishi nayi mishi biyayya dan nagartasa da ban zaci zai iya aikata wannan ƙazantan ba.
Yah Afif ya rasa yarinyar da zai nema yana lalatawa sai yarinyar da ya ajiye agabana na riƙe?, Yarinyar marainiya du-du-du ƴar shekara sha uku”.
Cikin wani irin azabebben bugun zuciya Taj ya runtse idanunsa kalaman Meymer na barazanar toshe masa ji cikin matsanancin kuka da sarƙewar murya ta cigaba da cewa.
“Yah Afif bai taɓa kallona matsayin matar Aurensa ba, duk tsawon zaman da mukayi dashi watanni kusan takwas kenan yanzu in ƙarya nake mishi gashi nan ya faɗa, wlh ko yatsata bai taɓa riƙewa da sunan muyi zaman aureba ashe duk yana shareni ne dan ya samu Laylah a kusa”.
Cikin Mamaki Uncle Jibril ya zuba mata ido ganin tayi shiru ta kife kanta ajikin kujera tana cigaba da kuka.
A hankali ya gyara zamansa cikin sanyin murya mai haɗe da tausayin ƴar tasa yace.
“Kiyi shiru Mamana kukan nan ya isa haka”.
Momy Meymer kuwa cikin wani irin yanayi take kallon Meymer kallo irin na tuhuma da son fahimtar wani abu cikin takaici ta buga mata tsawa tare da cewa.
“Dan Allah rufe min baki,
kike ta maimaita magana ɗaya kamar kin samu karatun Alkur'ani ko karatun Alqur'ani ba kya maimaita shi haka kamar yanda kike ta maimaita Yah Afif yamin kaza Yah yamin kaza ki rufe min baki ki kuma bace min da gani”.
Kallonta Uncle Jibril yau kana yace.
“Ya za'a yi ki tayiwa Mamana tsawa? Ki barta bana so kada ki sake yi mata tsawa ki bari taji da abu ɗaya”.
Jin abinda ya faɗa yasa tayi Ƙwaffa...
Yah Abana kuwa idanunsa sun sake jajur tamkar zasuyi aman wuta kallon Taj yayi kana yace.
“Tajudden ka tashi agana kada ka sake zuwa gabana har sai ka tabbatar kana da abinda zaka faɗa min bana son ganinka bana son zargin da ake ya tabbata akan ka.
Ka sani in dai zargin da ake ya tabbata akan ka Tajuddeen baka da amfani arayuwata”.
Runtse Idanu Ummey tayi kana muryanta na rawa tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun”.
Ta ƙare maganar tare da fita ta nufi ɗakinta.
Taj kam jikinsa rawa yake so yake ya miƙe yabi bayan Ummey ganin yanda ta fita amma ya kasa.
Mikewa Yah Yusuf yayi kana ta tallafe sa ya ɗaga sa kallon yanda jikinsa yake rawa yayi kana ya riƙe sa suka nufi sashen Ummey...
A nan cikin falon kuwa Yah Hafiz ne ya juya ya kalli Meymey Muryarsa dashe yace.
“Meymey dan Allah dan darajar Annabi kada ki sake faɗan irin wannan kalaman akan Tajuddeen”.
Sabon kuka ta fashe dashi kana cikin gaskiyar abinda take gani shine dai-dai tace.
“Yah Hafiz abinda ya aikata nake faɗa idan bai aikata ba bazan faɗa ba”.
Laylah kam kuka take...
Taj da Yah Yusuf kuwa suna shiga Falon Ummey suka sameta zaune gaban 3sitter ta jingina kanta da jiki tana shesh-sheƙan kuka yayin da Zakiyya ke gefenta itama kuka take cikin damuwar ganin halin da Mahaifiyarta ke ciki tace.
“Ummey menene ki faɗa min Meyafaru?”.
murya can ƙasan maƙoshi sukayi sallama jin sallamarsu yasa ta ɗago kai ganin Taj da Yah Yusuf yasa tayi saurin miƙewa kana ta matsa gabansa muryanta na rawa kana hawaye na zuba daga Idanunta tace.
“Ko wani lokaci a kowani yanayi baka iya In-kari kan abinda ya shafe ka baka iya musu adai wannan lokacin muddin baka buɗe baki kayi In-kari ba sannan kayi abinda zai tsarkake kanka daga idon Mahaifinka ba, zaka ja mana baƙin cikin da zamu dawwama aciki Afif ka buɗi baki kayi magana”.
Kansa kawai ya girgiza saboda bazai iya ba ya sani haka Allah ya haliccesa Allah yasani bazai iya ba.
Kuka Ummey ta fashe dashi mai tsuma zuciya tafi kowa sanin wanene Taj ciki da waje haka zalika tafi kowa sanin Wanene Malam wannan dalili yasa ta sake fashe da kuka.
Ganin yanda take kuka yasa Taj zubewa akan gwiwoyinsa ya rasa ya zaiyi kana ya rasa mai zai ce.
Cikin sanyi da disashewar murya tace.
“In dai baza kayi magana ba, ka cutar dani Tajuddeen adai wannan karon idan har ba kayi magana ba ka gama cutar dani ka cutar da kanka”.
Ta ƙare maganar tana zama kan kujera.
Yusuf kuwa ganin bazai yi magana ba yasa ya Daga shi suka fita direct mota suka shiga ahankali Yah Yusuf ya kallesa kana yace.
“Ina muka nufa?”.
Shiru Taj yayi saboda bazai iya magana sai wani irin karkarwa da lips ɗinsa keyi duk da yana taune su maganganun Meymey basu zauna a ransaba ko kaɗan ganin alamun fushi da fusatar Yah Abana ne ya hautsina mishi lissafi.
Bayan sun danyi nisa da tafiyar Yah Yusuf ya sake kallo sai tare da cewa.
“Afif ina zamuje?,Ko dai in kai ka gidan Addawa ne?”.
Kai ya gyada masa kana kai tsaye ya juya akalar Motar zuwa gidan Addawa...
A can falon Yah Abana kuwa kallonsu yayi cikin Muryarsa dake ƙunshe da tarin damuwa ya kallesu kana yace.
“Ku tashi ku tafi”.
Cikin mutuwar jiki kowa ya watse da zullumin dake ransa Momyn Meymer kuwa side ɗin Ummey ta nufa.
Meymey kuma hannun Laylah ta riƙe suka fita suna fita tashiga motarta suka wuce gida.
Acan gidan Addawa kuma cikin tsananin tashin hankali take sauraren bayanan da Yah Yusuf ke mata baki ɗaya ilahirin jikinta rawa yake kana hawaye na zuba mata tamkar an buɗe famfo tsoronta kuwa sake hau-hawa yake nan take firgici ya bayyana ƙarara asaman fuskarta Babu kalmar da take maimaitawa face Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un tana mai cigaba da cewa.
“Ya Allah ka tsare wannan bawan naka da abinda ake zargin sa da aikatawa”.
Sosai suka riƙa tausan Taj kan yace wani abu amma ina kasa magana...
Jin kiran sallar maghariba ne yasa suka tashi suka tafi masallaci sukayi sallah masallacin unguwar su Addawa ranan agidan Addawa ya kwana anan falonta ita kanta har zuwa lokacin bai buɗi baki ya mata magana ba.
Washe gari da Asbah bayan an idar da Sallah yana shiga Falon ya sameta tana waya wanda bisa duk kan alamu da Ummey ce jin tana cewa.
“A gidana ya kwana gashi nan kuma tunda yazo bai ce min komai ba haka zalika baiyi magana ba”.
Ganin shigowar yasa tayi saurin cewa.
“Yawwa gashinan ya dawo yanzu”.
Sai kuma ta matsa kusa dashi kana tace.
“Tajuddeen ga Ummey ka nan,tana son magana da kai”.
Ahankali ya gyaɗa mata kai kana ya zauna tare da karɓan wayar ya manna akunnensa cikin wata iriyar murya mai cike da tsananin sanyi da rauni wanda har ta bawa Ummey tsoro yayi sallama da damuwa atare da ita tace.
“Lafiyarka kuwa Tajuddeen?".
Cikin sanyayyar murya ya gyada mata kai kamar yana gabanta kana yace.
“Lafiya lau Ummey ”.
Cikin jin ƙai irin na uwa da ɗanta ɗan ma mafi soyuwa azuciyar ta girgiza kai tare da faɗin.
“Tajuddeen Me zaka iya cewa?, Tajuddeen ka buɗe baki kayi magana ”.
Idanunsa ya lumshe kana ya taune lips ɗin sa na ƙasa tare da cewa.
“Kiyi haƙuri Ummey bazan iya ba”.
Wani irin kuka ne yazo mata cikin zubda hawaye tace.
“Tajuddeen ba zaka iya bafa kake ce min?.
Kasan abinda ake tuhumar ka dashi kuwa?,kasan me ake tuhumar ka dashi Tajuddeen? Kasan cewa duk mutumin daya taɓa Aure mace ko Namiji hukuncin haddi kisa ake yanke masa Tajuddeen shine kake cemin baza ka iya magana ba?”.
Kansa ya jinjina yana mai jin tausayinta akasan ransa yace.
“Kiyi haƙuri Ummey bazan iya ba kiyi haƙuri, gwara ma a kashenin kawai kowa ma ya huta”.
Ya ƙare maganar zucin yana miƙawa Addawa wayar suka ci-gaba da magana.
Ganin ya miƙe yasa tayi saurin cewa.
“Ina zaka je?”.
Ahankali ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.
“Gida”.
Yana fita sai ga Abu Hashim yazo bayan motar ya shiga yana zama wayarsa na ringing yana dubawa yaga Sunan Ishmah na yawo wayar iska mai zafi ya furzar yasan ta kira ne su gaisa kamar yanda suka saba ko wacce safiya kuma yanaji bazai taɓa iya bari bai amsa kiranta ba picking call ɗin yayi ya manna akunnensa ya shiru.
Daga ɗaya bangaren cikin sanyayyar murya mai cike da nutsuwa tace.
“Barka da Safiya Taj".
Ahankali yace.
“Hmmm”.
Cikin bugawar zuciya mai gauraye da jin alamun yana cikin damuwa tace.
“Ya Salam Taj me yake damunka?”.
Ahankali ya sake cewa.
“Hmmmm”.
Still da damuwa afuskarta tace.
“Dan Allah Taj na roƙeka kayi min magana in samu salama”.
Sai alokacin ya ɗan cije lips ɗin sa murya can ƙasan maƙoshi yace.
“Me kika ji”.
Tana jujjuya kai tayi saurin cewa.
“Taj muryanka ta faɗa min baka cikin nutsuwa da kwanciyar hankali muryanka na tattare da damuwa meke faruwa? Jikina ya jiyo min alamun kana cikin damuwa. Me yasamu Laylah”.
Sai alokacin yaji wani irin zafi da zugi azuciyarsa tunaninsa ya tafi kan Laylah dagaske ne kenan?,ciki ne da ita, to idan ya bari aka kashe shi waye zai kula da rayuwar Laylah, Ya Ummeeyshi zataji, waye zai meyewa Ishmah gurbinsa?”.
Asanyaye ya furzar da iska mai zafi jin Ishmah na kiransa a hankali yace.
“Ba abinda ya samu Laylah Ma'eesha”.
Itama cikin sanyi tace.
“Toh yanzu meye ne matsalar”.
Ahankali ya sake runtse idanunsa tare da faɗin.
“Kiyi min Addu'a Ma'eshaa”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“In sha Allah zanyi, to amman addu'ar me zan maka?”.
Tsintar kansa yayi da cewa.
“Kiyi min Addu'a Allah ya bani ikon cinye Jarrabawar dake kutso kai cikin rayuwata”.
Cikin gamsuwa tace.
“In sha Allahu zan yi maka addu'a yanzu ma ina kan sallaya bari nayi maka addu'a”.
Kai ya gyada tare da katse kiran.
Da kallo tabi wayar jin ya katse yasa ta sake tabbarwa yana cikin matsala.
Bisa kan sallaya tayi sujjada tare da cewa.
“Ya Allah ka kare wannan bawan naka, ka tsare wannan bawan naka daga sharrin masu sharri, ka ɗaukaka darajarsa ka kare mutuncinsa ka hanasa ta ɓewa ka yalwata duniyarsa da lahirar da farin ciki ka bashi ikon cinye Jarrabawarsa”.
Haka dai tayi ta mishi addu'oi...
Taj kuwa dai-dai lokacin ya shiga ya samu Meymey na zaune kan 3sitter Laylah na gefenta tana bata tea wani irin kallo ta bishi dashi.
Ahankali ya girgiza kansa kana ya saki Murmushi wanda yafi kuka ciwo Murmushin da yake nuna zallan Jarumtakarsa wanda yake nuna rashin nasarar maƙiyansa a kansa Murmushin dake nuni da alamar Fahimtar abinda ke ranta.
A hankali ya wuceta ya nufi bedroom ɗinsa yana shiga ya kwanta saboda yanda yake jin tsananin ciwon kai da yanda yake sarawa kwanciya yayi ya rasa mai zai tuna a duniya arayuwar ya rasa abinda zai tuna ranan haka ya yini aɗaki, ko jami'in Sallah agida yake yi tunda ya shiga ɗakin bai fito ba sai washe gari da safe ya fito.
Yana fitowa ya tsaya atsakiyar falon kana ya ɗan ɗaga sautin muryan sa da bai fita yace.
“Laylah!, Laylah!!, Laylah!!!”.
Cikin yanayin tsoro da firgita ta fito da sauri ta tsaya gefensa baki ɗaya ilahirin jikinta na karkarwa matsawa kusa da ita yayi tayi saurin ja da baya Muryarsa asanyaye yace.
“Laylah ki tsaya ba abinda zan miki”.
Kai ta shiga jujjuya masa amma ba tace komai ba.
Yana sauƙe ajiyar zuciya yace.
“Yau ba kije school bane?”.
Kai ta gyaɗa cikin tarin tsoro tace.
“Malam yace in daina zuwa school”.
Cikin matsanancin tsoro da firgita ta kai karshen maganar.
Da mamaki yace.
“Yah Abana da kansa ya faɗi haka?”.
Kai ta gyada masa.
“To saboda me?”.
Ya tambaya yana kallonta murya na rawa tace.
“Yace wai kar inje a gane ina da ciki in zubar mishi da darajar sunansa da gidansa”.
lip ɗin sa na ƙasa ya cija da ƙarfi tare da juyawa ya fita.
Yana fita yayi kiciɓis da motar Amal tana shiga...
Yana fita ya wuce asibiti da nufin ko zai iya aiki koda yaje yaji bazai iya aikiba ji yake to mai zai yi daga can ya wuce gidansu Ummey kai tsaye falonta ya wuce yana shiga ya samu falon shiru sai Aunty Maryam da
Rashida,Rashida na ganinsa tayi saurin cewa.
“Taj".
Cikin sanyi ya amsa mata kana ya zauna gefenta itama Aunty Maryam zama tayi gefensa ta zamana sun saka shi a tsakiya.
Ummey kuwa jin an kira sunansa ne yasa ta fito daga bedroom bisa duk kan alamu walaha tayi hannunta riƙe da Carbi zama tayi aƙasa agabansa tace.
“Afif”.
Idanunsa da suka jikkata da dimuwa da tsantsar tashin hankali ya ɗago ya kalleta kana har zuwa lokacin suna nan Ja-ja-jur ahankali tace
“Afif na roƙeka ka yakice wannan ɗabi'a taka ka raba bakinka da wannan nauyin, ka cire wannan zurfin cikin, ka kare kanka Tajudden al'amarin nan fa Babba ne kada ka ɗauke shi da wasa lamarine da zai ruguza duk kan wani farin cikinmu”.
Ahankali ya juya ya kalli Rashida da tun kiran sunansa bata sake cewa komai ba sai kuka.
Aunty Maryam kam zamewa tayi ta kifa kanta jikin kushin ta zubda hawaye.
Ahankali ya zame ya zauna gefen Ummey har gwiwoyinsu na gugan juna ahankali ya ɗaga tafukan hannayensa ya daura kan haɓarta ya shiga share mata hawaye.
Cikin sanyi tace.
“Ba abinda zaka min ka share min hawayena wadda ya wuce ka buɗi baki kayi magana ka fadi abinda yake zahiri ka fadi abinda yake gaskiya, sannan ka fadi abinda yake tsakaninka da Ubangiji ka kuma fadi abinda ka sani akan cikin Laylah”.
Runtse idanunsa yayi yana jin tausayinta aƙasan ransa Ummey kam cikin tarin tausayin sa da kuma jin kai ta cigaba da cewa.
“Ni ban sani ba Yah Abananka bai sani ba daga kai sai Allah ne kuka sani, dole sai ka buɗi baki kayi mgna ne zamu sani ka samu ka kuɓuta da kan ka Tajuddeen”...
Sake runtse idanunsa yayi jin yanda ƙahon zuciyarsa ke harbawa cikin sanyayyan murya yace.
“Kiyi haƙuri Ummey bazan iya ba ban san me zanceba”.
Cikin sauri da matsanancin tausayinsa Rashida ta ɗago kai tare da cewa.
“Afif zurfin cikin ka zai ja mana bala'i kayi magana dole ka fito kayi magana kayi In-kari”.
Ahankali ya subkuyar da kansa ƙasa Ummey kam tafin hannunta tasa ta tallafo fuskarsa kana ta riƙe haɓarsa dai-dai gemunsa tace.
“Ka kalli Idona ka faɗa min me gaskiyar abinda Meymey ta faɗa”.
Cikin yanayin dashi kansa bai sani baya kalleta araunane yace.
“Ummey nima ban sani ba”.
Idanunta na tsatstsafo da ruwan hawaye tace.
“Kamarya baka sani ba?,ka faɗa min gaskiyar abinda Meymey ta faɗa kai kayiwa Laylah ciki?”.
Kansa ya sunkuyar tare da cewa.
“Ummey i don't know bansan abinda zan ceba”.
Yanda yayi maganar ne zai nuna daga ainihin ƙoƙon zuciyarsa yake fita”....
Daga Page 15 zan gama free pages in dai Kinga littafin INDA RAI a wani group ɗin ba group ɗina na littafin ba to na satane kika karanta.
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/16, 7:57 AM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 14*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Littafin INDA RAI na kud’ine wannan free pages ne mukeyi kuma suna gab da k’arewa, littafin INDA RAI 1k ne kacal biya ki karanta cikin aminci, zaki iya tura kud’inki ta wannan account d’in 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, zaki tura shaidar biyanki ta wannan numbern- 09097853276. Mutane k’asar Niger kuma 1000fc ne jaka d’aya kenan rak zaku tura kudin karanta littafin +22790899076 ita zaku yiwa magana.*
A dai-dai lokacin kuma Addawa tashigo, zama tayi a bayansa kana ta janyo kansa ta manna da guiwowinta, ahankali cikin sanyi da tarin tausayinsa tace.
“Kayi gadon zurfin cikin nan, amma kuma a dai wannan karon idan kayi zurfin cikin zai matuk’ar cutar da kai sannan zai cutar damu Afif, ka fito kayi magana ka faɗi abinda ka sani kuma yake shine gaskiya.”
Idanunsa da suka sauya launi yayinda jijiyoyin dake cikinsu suka yi jajaye ya ɗago ya kalleta, lips d’insa ya d’an cije kana ahankali yace.
“Ba abinda na sani da zan iya cewa”.
Da yanayin damuwa Aunty Maryam ta kallesa kana cikin sark’ak’iya tace.
“Kamar ya ba abinda ka sani Tajj? wani irin maganane wannan? wacce iriyar magana kake zaka ce mana ba abinda ka sani?”
Ta ƙare maganar cike da jin tsoron anya kuwa Taj bai shiga tarkon shaiɗan ba.
Dai-dai lokacin Zakiyya ta fito hannunta riƙe da waya tana hawaye wanda bisa alamu da Aunty Halima take waya.
Ita kuwa Aunty Halima shesh-sheƙan kuka take Ummey ta mika wa wayar.
Ummey na amsa tace.
“Toh Halima ya zamuyi addu'a kawai zamuyi masa amma lallai muna cikin ƙalubale, muna gab da fuskantar wani kalubale mafi muni a rayuwarmu, muyi ta addu'a Allah ya kawo mana da sauƙi, ni da Abbanku jiya kwana mukayi ba muyi bacci ba, sannan yau da safe naje na samu Dr. Abbas na duba shi BP d’insa ya hau.”
Jin hakan yasa Taj sunkuyar da kansa ƙasa tare da d’an yunƙurawa ya miƙe ahankali.
Kallonsa Ummey tayi tare da faɗin.
“Ina zakaje?”.
Ƙwayar idanunsa ya risinar ƙasa kana atausashe cikin had’iye tarin damuwarsa yace.
“Zanje duba Yah Abana”.
Ya ida maganar yana mai jin ƙaunar iyayen nasa acikin ransa.
Yana shiga ɗakin kuwa ya samu kusan baki daya yayunsa Mazan suna nan sai kuma ya ɗan tsaya jin Yah Hafiz na magana cikin sanyi da taushin lafizi da biyayya yana cewa Mahaifin su.
“Abbah kafin ayi komai a nutsu abi abin ban Ahankali, Abba kaine mafi sanin halayen mu gaba ɗayanmu mu ƴaƴanka. Allah ne ya tarbiyyantar damu amma kaine ka daura mu kan hanya Abba ka sani cewa Taj baya ɗaya daga cikin irin mutanen daya kamata ace wannan zargin ya hau kansu, kuma ka tuna cewa Taj mutum ne ajizi dan girman Allah da Manzonsa koda an sameshi da ajizanci a cikin maganar nan ayi mishi uzuri a sassauta mishi”.
Cikin sauri Yah Yusuf ya karbi maganar da cewa.
“Sosai ma Abba dan Allah asan abinda za'a yi akan maganar nan, ni inaga Maganar nan anyi masa bahagon fahimta ne yarinyar nan Meymey ita kanta batasan mai take faɗa ba”.
Ahankali Yah Abana ya ɗago gajiyayyun idanunsa dake nuni da damuwa ya kalli Tajj sai kuma ya sunkuyar da kansa.
Tajj kuwa lokaci ɗaya yaji hankalinsa yayi masifar tashi fiye da wanda yake ciki zuwa yanzu ya fahimci mahaifinsa kamar baison ganinsa ne jiki amace ya isa tsakiyarsu kana ya zauna a gaban Yah Abana tare da faɗin.
“Yah Abana Barka da safiya”.
Batare daya amsa gaisuwar nasa ba yace.
“Menene gaskiyar abinda Meymey ta faɗa?”
Ahankali ya motsa Lips ɗin sa zuciyarsa na wani irin mummunan bugawa yace.
“Ban saniba Yah Abana”.
Kai Yah Abana ya kawar batare daya sake bi ta kansa ba.
Murya na rawa ya ɗan zuba masa Idanu ganin yanda lokaci ɗaya ya ya faɗa, asanyaye kuma yace.
“Yah Abana ya jiki?”.
Ƙin amsawa yayi sai ma rufe idanunsa da yayi.
Ganin haka yasa ahankali Taj ya zauna kana ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da sa hannunsa da nufin kamo ƙafar mahaifin nasa dan yi masa tausa.
Saidai hakan baikai ga samuwa ba yayi sauri janye hannunsa sakamakon Yah Abana da ya dakatar dashi ta hanyar janye ƙafarsa.
Kafaɗarsa Yah Abdurrahman ya dafa tare da faɗin.
“Afif kai namiji ne fa ya kamata ace kana da ƙarfin zuciyar da zaka iya yaƙi da komai.
Ya kamata ace zurfin cikin ka ya tsaya iya kan hakuri bakan abinda zai cutar da kai ba kana ya cutar damu”.
Sai kuma duk sukayi shiru suna kallon Aryaan dake cewa.
“Akan komai dai ɗan Adam zai iya zurfin ciki mun shaida Afif nada zurfin ciki amma dai akan wannan maganar in dai yana da gaskiya yasan ƙazafi akayi masa dole ya fito ya wanke kansa”.
Ya ƙare maganar da iya yaƙinin gaskiya yasan dole in dai Afif yana da gaskiya acikin maganar dole ya fito ya wanke kansa.
Taj kam shiru yayi batare daya tanka kowa ba...
Dai-dai lokacin kuma Meymey ta shigo hannunta riƙe da Laylah da kuma sauran Matan Yah Abana duka su huɗun suna shigowa Hajiya Babba tace.
“Ni yanzu ma an tabbatar da cewa shin akwai cikin?,ko yaya?”.
Cikin sauƙe nannauyan ajiyar zuciya Yah Hafiz yace.
“Batun ciki kam tabbas akwai shi domin likitoci sun gwada an gani cewa akwai ciki harna wata 2”.
Cikin sauri Ummu Aryaan tace.
“Aje dai asake gwada wa shine kawai abinda yafi dacewa”.
Cikin sanyi Meymey dake zaune a gefen Mom Amal tace.
“Wani gwaji kuma ya rage Umma? ai ba gwajin daya rage, likitoci nefa sukayi gamayya a kan gwajinta kuma suka tabbatar da cewa tana da ciki.”
Kai Ummu Aryaan d’in ta girgiza tare da cewa.
“Ai shima Taj ɗin likita ne yaje ya gwada da kansa a tabbatar mana”.
Cikin sauri Meymey tace.
“Toh Umma in dai da kansa zai gwada ai bazai taɓa fadar gaskiya ba, tunda yasan abinda yake tafiya, nifa nasan cewa shi ya aikata duk wannan abun kuma shima ya sani.”
Cikin taɓe baki Aryaan ya karbi maganar ta hanyar cewa.
“Toh dama ya za'a yi wanda ake tuhuma ya zama shine mai yin gwaji? kamar fa Shari'a ce ace an bawa mai laifi alƙalanci, kawai Idan ba'a yarda bane sai asake tafiya wani waje aje a gwada”.
Cikin sauri Yah Yusuf yace.
“Toh shikenan asake ayi wani gwaji a tabbatar”.
Asanyaye Yah Abdurrahman yace.
“Toh shikenan bari na haɗa ku da abokina Dr Sonail Khan ɗan Indi'a ne amma anan yake aiki ”.
Amsawa sukayi saɓanin Tajj da har zuwa lokacin kansa ke k’asa, bayan ciwon da yake ji acikin zuciyarsa ya gaza iya cewa komai, dan har yanzu ganin abun yake kamar acikin mafarki.
Meymey, Laylah, Yah Abdurrahman, da kuma Khabeer tare suka tafi asibitin.
Bayan awa uku da tafiyarsu suka sake dawowa dai-dai lokacin kuma anyi sallar la'asar bayan sun dawo sun zauna Kabeer da takardun gwajin ke hannunsa ya miƙawa Yah Abana tare da cewa.
“Gashi fa tabbas akwai ciki har na tsawon watanni biyu”.
Azuciye cikin b’acin rai me tsanani Yah Abana ya wurgawa Tajj takardun, cikin k’unan zuciya ya kuma cewa.
“Menene gaskiyar waɗan'nan takardun?Tajuddeen me gaskiyar wannan abin? Me dalilin faruwan haka? Waye Uban cikin nan?”.
Ya jero masa duka tsauraran tambayoyin ajere Akuma lokaci ɗaya.
Shiru ya kumayi kamar yanda ya saba saboda bazai iya cewa komai ba.
Saidai jin ya sake jero mai tambayoyin a hargitse ne ya sashi buɗe baki hankali yace.
“Kayi haƙuri ya Abana”.
Kusan duk a tare suke kallonsa cike da fara karaya.
Ita kuwa Meymey kai ta girgiza alamun.
“Toh kun ji dai”.
Zazzafan Iska Yah Abana ya furzar daga bakinsa kana akausashe yace.
“Tunda baza ka iya magana ba ka fita bana son ganinka!”
Ahankali ya yunƙura kana lips ɗinsa na rawa cikin wani irin yanayi me wahalar fassaruwa yace.
“Yah Abana kayi haƙuri ka gafarceni”.
Idanu Yah Abana ya rumtse tare da nuna masa k’ofa rai b’ace yace.
“Ka fita sai lokacin da kasamu hujjoji abakin ka kazo ka faɗa min”.
Jikinsa ne gaba d’aya ya d’auki rawa cike da tsananin ruɗani ya miƙe ya nufi hanyar fita.
Yana fita kuwa Ummey tabi bayansa da sauri, tare da riƙo hannunsa murya araunace tace.
“Ina zaka je Afif?”
Kansa dake masifar ciwo ya d’an girgiza kana cikin mawuyacin halin da yake ciki murya can ƙasan maƙoshi yace.
“Zan tafi gidan Addawa”.
Numfashi ta fesar cikin tsananin tausayin d’an nata tace.
“Toh ai itama Addawan tana nan bari in mata magana sai ku tafi tare, kaci abinci ma kuwa?”.
Kansa ya girgiza cikin lumshe idanunsa ahankali yace.
“Bana jin yunwa".
Addawa kuwa jiyo maganar su ne yasa ta fito, tare da bin bayanshi suka shiga mota suka tafi...
Ummey kuwa direct parlorn ta ta koma sai kuma ta kalli Rashida dake cewa.
“Ummey yayi magana”.
Kai ta girgiza tana kokarin maida hawayen dake kokarin zubo mata tace.
“Um-um baiyi magana ba Rashida, sai haƙurin da yake badawa dake tayarmin da hankali, Abban ku kuma naga bai fuskanci lamarin nan da fuskar daya kamata a ɗauke shiba yanzu cewa ma yayi baya son ganinsa”.
Da sauri Aunty Maryam ta girgiza kanta tana maimaita kalmar “Allahumma Ajirni Fii musibati wa akhlifliy khairan Minha!”
Ummey kuwa araunace ta cigaba da cewa.
“Yace ya fita ya bashi waje In har ba zai yi magana ba, yayi maganar nan kamar ya manta waye ne Taj kamar ya manta menene halinsa mutumin da tun yana karami baya iya In-kari”.
Atsorace Aunty Maryam ke kallonta cikin tarin damuwa kuma tace.
“Toh yanzu Ummey ya zamuyi?”.
Cikin sanyi Ummey tace.
“Yanzu sai dai ku tashi kuje gidan Alaramma Sulaiman tunda ni kona tambayi Abbanku bazai barni in fita ba, kuje kuyi masa bayanin ga abinda yake faruwa inada yakinin shi kaɗai ne zai iya fahimtar da Abbanku wani abu, dan na fahimci Uncle Jibril bazai taba bincike akan duk maganar da Meymey take faɗa ba”.
Kai Aunty Maryam suka gyaɗa daga nan suka fita suka tafi kai tsaye gidan Alaramma Sulaiman suka tafi wanda shine Aramman Mahaifinsu mai ja musa baƙi suna tafsir bayan sunje gidan suka masa bayanin iya abinda suka sani.
Da kansa ya rakosu har bakin mota yana mai jaddada musu cewa in sha Allahu da daddare zai zo su gana da Yah Abana.
Da daddare Alaramma Sulaiman yazo bayan sun zauna da Yah Abana bayanin da Yah Abana ya masa da yanda Taj yaƙi yin magana sai jikinsa yayi sanyi hankalinsa ya tashi Yah Abana kuwa ya ɗaura da cewa.
“Kwanan nan fa da Afif yai tafiya Nigeria yarinyar ya ɗauka kwana goma fa sukayi da ita kafin suka dawo, na gaya maka cewa acikin lamuran Taj akwai alamun ayar tambaya?”.
Idanunsa ya runtse yana jin wani irin ɗaci acikin azuciyarsa kana ya cigaba da cewa.
“Sannan koda nasan tabbas Taj yana da zurfin ciki acikin al'amarin nan kamata yayi ya fito ya wanke kansa asalima Taj sai shiru yake duk abinda na tambayesa sai yace bai sani ba ko yace wai inyi hakuri me haka yake nufi kenan? Taj ya gama ɓata min sunan zuri'a ya gama tozartani ya gama cimin zarafi kana ya ƙasƙantar min da zuri'a”.
Cikin sauri sheik Sulaiman yace.
“Kada kace haka ka bari sai an tabbatar da komai kayi magana akai ”.
Kansa ya girgiza yana mai jin daci azuciyarsa yace.
“Wani tabbaci ne ya rage?na rasa ta ina zanbi in samu tabbacin da zan iya gamsuwa dashi”.
Haka dai sukayi tattaunawar suka gama bayan Alaramma Sulaiman ya sake tunarsa dashi amma duk da haka basu gano bakin zaren ba...
Wasa gaske haka aka ɗauki tsawon kwanaki biyar ana ta gumurzu Taj ya kasa wanke kansa kana Meymey babu abinda take sai ƙara jaddada cewa shi yayiwa Laylah ciki.
Ahankali ya shiga cikin gidan yana mai sauke zazzafan Ajiyar zuciya yau kwanansa biyu bai zo gidan ba saboda koda yazo mahaifinsa daga gaisuwarsa da yake amsawa babu wata magana da take sake haɗa su.
Ahankali ya ƙarasa shiga Falon Yah Abana zaune ya samu Hajiya Babba agefensa kasancewar yau girkinta ne bayan sun gaisa ne ya ɗan kallesa kana yayi kasa da kansa tare da cewa.
“Yah Abana zan ɗan yi tafiya akwai Passenger da zan ɗauka daga nan Ethiopia zuwa Malaysia kwana biyu zanyi.”
Ɗagowa yayi ya kallesa cikin tsuke fuska ya kawar da kansa gefe tare da nuna mishi hanyar fita.
Jiki amace ya miƙe ya nufi hanyar fita sai kuma ya juya jin Hajiya Babba na cewa.
“Allah ya kiyaye hanya Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya”.
“Ameen”
Ya amsa kana ya fice, kai tsaye Airport ya nufa ɗakin da za'a masa gwaje-gwaje ya nufa gwajin farko da akayi masa kuwa aka samu jininsa ya hau 180 kana ga tsananin masifar ciwon kai ga kuma zuciyarsa dake harbawa da k’arfi, atak’aice dai matsaloli kusan guda biyar aka samu a tare dashi wanda hakan yasa dole aka soke tashinsa da jirgi wanda dole baza a iya barinsa ya tafi da Passenger ba nan dai aka bashi magunguna kana Driver’n sa ya maida shi gida.
Har sun kusa gida ya kalli Abu Hashim tare da cewa.
“Ka kaini gidan Addawa”.
Kai Abu Hashim ya gyaɗa tare da nufar gidan Addawa.
Taj na shiga kiran Ishmah na shigowa wayarsa yana ɗaukar kiran kuwa tace.
“Taj”.
Murya sanyaye yace.
“Na'am”.
Cikin tarin damuwa tace.
“Kayi min bayani, gaba d’aya ka sauya cikin kwanakin nan guda biyar zuwa bakwai na kasa fahimtar ka, sannan ka kasa yimin bayani, Tajj ya kake son inyi da rayuwata hankalina ya tashi zuciyata ya kasa kwanciya kayi min bayani”.
Cikin sanyi ya girgiza kai tare da taune lips ɗin sa cike da b’oye ciwon da yake ji aransa yace.
“Ma'eesha ba komai ki cigaba da yimin addu'a kinji ko?”.
Kai ta gyaɗa kamar yana agabanta kana murya na rawa tace.
“Toh In sha Allah, amma ya jikin Laylah kwana nawa baka haɗani da ita ba”.
Iska mai zafi ya furzar daga bakinsa gami da cewa.
“In sha Allahu zan haɗaki da ita”.
Asanyaye tace.
“Toh shikenan”.
Washe gari ya kasance ranar Laraba,kamar yanda akasani gidan a cike yake saboda kiran Family meeting da Malam yayi na gaggawa. kamar yanda aka saba gaba ɗaya family’n sa dake state ɗin in dai jumma'a ko ya kira taron gaggawan nan gidan suke zuwa maza da mata.
Daidai lokacin da za'a gabatar da Sallah azahar Taj ya tashi daga sahun farko da yake ya kara matsawa gaba sanin cewa muddin yana ƙasar shi yake jansu sallar Juma'a madadin mahaifinsa da kuma kamsutSalawat a masallacin su na gida.
Sai kuma ya danyi sauri yaja da baya ganin Yah Abana ya ɗaga masa hannu alamar ya tsaya ahankali ya koma ya tsaya a sahun farko.
Yah Abana kuwa da kansa ya tada iƙama akayi sallar azahar, bayan an idar da sallar duk gida suka koma Taj kuwa gidan Addawa ya wuce.
Acan gefen gidan Yah Abana kuwa gaba ɗaya yasa Iyalansa suka taru kasancewar Meymey bata zoba yasa Yah Abana ya kalli Kabeer kasancewar shine karami atausace yace.
“Kabeer je ka ɗauko min Laylah da Meymey.”
Kai Kabeer ya gyaɗa cikin sauri tare da ficewa ya nufi Parking space...
Motar Kabeer na ƙoƙarin fita na Taj na shigowa cikin gidan ahankali ya fito daga motar bayan Abu Hashim yayi Parking hannunsa na riƙe da wata sanda me kyau wanda Sheikh Taju Usman Bauchi ya bashi zuwansa Nigeria yana shiga cikin gida direct Falon Ummey sa ya wuce zaune ya sameta tare da Yayunsa har Aunty Halima wacce itama ayau ta taso tazo saboda sun fahimci kiran taron baya rasa nasaba da ɗan uwansu.
Ganinta yasa ya fesar da numfashi kana cikin yanayin sanyinsa yace.
“Aunty Halima me ya kawo ki Lafiya kuwa?”.
Cikin shesh-sheƙan kuka mai cike da tarin tausayinsa tace.
“Taju ka manta kenan?
Tambayata ma kake lafiya?,ka mance halin da muke ciki?”
Adai-dai lokacin kuwa Falon Yah Abana cike yake da ƴaƴansa jikokinsa da kuma Uncle Jibril da Momyn Meymey saura Meymey sannan Laylah, da kuma Khabeer had’i da ahalin Ummey.
Cikin hakane Aryaan ya shigo falon Ummey tare da cewa.
“Ummey Abba yana neman ku”.
Kai ta gyaɗa kana suka miƙe suka bi bayan Aryaan suka shiga dai-dai lokacin kuma motar Kabeer dake dauke da Laylah da Meymey yayi Parking.
Yah Abana kuwa hannu ya d’aga tare da nunawa Taj gabansa alamar yaxo ya zauna yayin da baki d’aya sauran ƴaƴansa kowa yana inda yake.
Dai-dai lokacin kuma Meymey, Laylah da kuma Kabeer suka shigo falon.
Da hannu Yah Abana ya nunawa Meymey da Laylah tsakiyarsu kan su zo su zauna.
Suna zama Yah Abana ya ɗago kansa ya kalli Taj tare da cewa.
“A yau ɗin nan awannan lokaci nake baka dama ta ƙarshe Akuma yanzu ka buɗe baki kayi min maganar da zan fahimta zan gane.
Wannan itace dama ta ƙarshe da zan iya baka a rayuwata ka faɗa min me gaskiyar abinda ke faruwa ya akayi Laylah take da ciki”.
Idanunsa da suka kuma yin jawur ya rumtse tare da d’an jijjiga kansa, cikin sanyi had’i da bugawar zuciya ya jujjuya kansa tare da faɗin.
“Yah Abana kayi haƙuri ban sani ba….”
Jin abunda yace ne kuma yasa baki ɗaya hankalin Ummey, Aunty Rashida, Aunty Maryam, Aunty Halima, da kuma Zakiyya ya tashi sosai, cikin kid’ima had’i da gigituwa suke kallonsa hawaye na zuba a idanunsu.
Yah Abana kuwa kallonsa ya mayar kan Meymey dake zaune cikin tsukakkiyar fuska yace.
“Meymey me kika ce ranan?”
Baki ta bud’e cikin zubda hawayen munafurci tace.
“Abbah wallahi Yah Afif shi yayiwa Laylah ciki”.
Cikin sauri Hajiya Babba tace.
“Toh me hujjarki Sannan menene Shaidar ki?”
Cikin shesh-sheƙa ta yi wa Taj da kansa ke ƙasa wani irin kallo kana tace.
“Ina da hujjoji da yawa da kuma shaidu”.
Lokaci d’aya Yah Abana cikin rashin walwala had’i da tsuke fuska yace.
“Menene shaidun ki?”
Tana goge hawayen dake zubo mata tace.
“A tambayi ita Laylah ɗin”.
Da sauri Yah Abana ya juya ya kalli Laylah sai kuma ya maida kallonsa ga Taj.
Taj kuwa juyawa yayi yana kallon Laylah haka zalika duk wanda ke cikin Falon Laylah yake kallo.
Sabanin Momyn Meymey data zubawa ƴar Tata Idanu tana mai Binta da wani irin kallon tuhuma.
Laylah kuwa kanta ta sunkuyar ƙasa.
Cikin murya mai cike da damuwa da tsantsar tashin hankali daya bayyana asaman fuska Yah Abana ya kalli Laylah tare da cewa.
“Laylah”.
Kanta a ƙasa tace.
“Na'am”.
Sake kiranta yayi amsawa tayi batare data ɗago kanta ba.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya ya sake kiranta akaro na uku tare da cewa.
“Ɗago kanki ki kalleni”.
Ahankali ta ɗago kanta ta kallesa.
Yana mai jin bugun zuciya yace.
“Kinsan akan me ake magana?”.
Kai ta gyaɗa.
Ɗan muskutawa yayi tare da faɗin.
“Magana zakiyi”.
Cikin shesh-sheƙan kuka tace.
“Eh”.
Yana mai runtse idanunsa yace.
“Kinsan cewa ance kina da ciki a asibiti?”
Jikinta na tawa tana me kokarin danne kukan dake taso mata tace.
“Eh”.
Cikin sanyi gami da tsoro had’i da fargaba Yah Abana yace.
“Laylah waya Miki ciki?”.
Kusan baki ɗaya zukatan mutanen dake Falon bugawa yake musamman ma masoyan Taj.
More especially Ummey zuciyarta yafi na kowa bugawa.
Laylah kuwa cikin sanyi da rawar murya tace.
“UNCLE TAJJ NE!!”
Lokacin ɗaya Taj yaji baki ɗaya ilahirin jikinsa yana narkewa kamar an shanye jinin jikinsa ji yake tamkar yana zama yashi yana narkewa jin yanda kalmar ya daki ƙoƙon zuciyarsa cikin sauri ya juya ya kalli Laylah sai kuma ya juya ya kalli Meymey da ta saki wani Murmushi wanda daga shi sai Ubangijin daya haliccesa suka san manufarsa.
Da sauri Aunty Halima da jikinta ke rawa ta matsa kusa da Laylah’n cikin tarin damuwa da kuma tashin hankali tace.
“Laylah kiji tsoron Allah ki faɗi gaskiya Uncle Taj ɗinki nefa”.
Kai Laylah ta jinjina cikin zub da hawaye tana me ci gaba da sakin shesh-sheƙan kuka tace.
“Wallahi shine kullum in ya dawo gari aɗakina yake kwana kuma yace idan na faɗa zai yankani…”
A yanzu kam baki ɗaya ilahirin jikin Taj karkarwa yake da tsuma idanunsa sunyi jajur sun kada tamkar wuta, yayinda yake jin kamar ana kwara masa narkakkiyar dalma tun daga tsakar kansa har zuwa k’asan k’afafunsa, tabbas aduk rayuwarsa bai tab’a ganin tashin hankali da masifa irin wannan ba.
Yah Abana kuwa baki daya idanunsa ne suka rikice tare da sauya launi suba farare ba haka kuma su ba jajaye ba, kar-kar-kar haka jikinsa ke rawa.
Laylah’n kuwa kuka ta ci gaba da rerawa batare data kuma yin magana ba.
Yah Hafiz kuwa cikin wani irin yanayi na tsoro da kiɗima jikinsa na rawa yace.
“Meymey kiji tsoron Allah kisan abinda kike faɗa”.
Sai alokacin Uncle Jibril ya dago Kai ya kalli Yah Hafiz tare da cewa.
“Hafiz Mamana bata ƙarya tun tana ƙarama ban shedeta da ƙarya ba”.
Cikin takaici da wani irin yanayi Momyn Meymey ta katsesa da cewa.
“Ɗan Adam yana iya sauya hali akowani lokaci Alh ka daina shaidar Meymey”.
Cikin sauri Yah Abana ya karɓi maganar da cewa.
“Kamar yanda kuma shima Afif dan Adam ne da zai iya sauya halinsa akoda yaushe ba.”
Ummey kuwa cikin tashin hankali marar misaltuwa take kallonsa kana murya na rawa cike da tarin d’imuwa had’i da karyewar zuciya tace.
“Babana kayi magana! kayi magana Afif ka wanke kanka kace wani abu!!”
Me zaice? Bazai iya cewa komai ba, bazai iya ba, kansa juyawa yake yana jin kamar mafarki ne, zuciyarsa tayi masa mugun nauyi, yana jin kamar ana caka masa mashi akan k’ahon zuciyar nasa, komai ya riga da ya k’wace masa, baida wani abunyi sai kansa kawai da yake girgizawa, again ya kasa magana jikinsa ne kawai keta karkarwa.
Mom Amal kuwa cikin wata murya me ɗauke da wasu irin manufofi da ita kaɗai tasan ma'anar su tace.
“Wannan ma bai isa hujja ba Meymey idan kina da wasu hujjojin sai ki fito dasu mugani ”
Cikin sauri Meymey ta ciro wayarta ta bud’e tare da shiga Gallery bayan ta shiga kan abunda take son shiga ta juyo da screen d’in wayar zuwa fuskar Yah Abana.
Da sauri Yah Abana ya rumtse idanunsa sai kuma ya miƙe tsaye yayin da numfashinsa ke fusga yana ƙoƙarin ɗauke wa.
Sakamakon ganin hoton Taj da yayi tsaye tsirara Laylah na durƙushe ta riƙe gabansa.
Da wani irin firgita had’i da gigita mai tsanani ya fara cewa.
_“Auzubillahi minarshaiɗanir rajim Auzubillahi da kai Tajudden Subhanallahi da kai Tajuddeen ka ƙazanta ka barranta daga zuri'ata ka barranta daga ahalina.“_
Taj kuwa kansa ya soma girgizawa cikin son yaga abinda Mahaifinsa ya gani da ya kiɗimashi haka.
Uncle Jibril kuwa cikin sauri ya miƙe ya karbi wayar daga hannun Meymey yana kallo cikin tashin hankali yace.
“Innalillahi wa inna ilaihirraju’un! Afif ka zama guba ka zama ƙazanta acikin al'umma wannan wani irin nasiface Tajudden wace rayuwa ka zaɓawa kan ka”.
Ya ƙare maganar tare da sake wayar ta faɗi ƙasa, haka yasa ta ɗan sule zuwa gaban Taj ɗin.
Shi kam Taj ya kasa tantance yanayin da yake shin araye yake ne ko ko kuma amace? Saboda ganin tabbas shine a hoton kuma tabbas tsirara yake, kuma tabbas Laylah ce gabansa durƙushe tana riƙe da al'aurarsa, so yake ya rufe ƙwayar idanunsa ya buɗe ko zai daina ganin ɗigon tawadan Allah da yake a saman mararsa wanda yasan duk duniya banda iyayensa da suka raineshi a ƙuruciya babu wanda yasan dashi.
Cikin kuka Meymey tace wlh gashi in ba shi bane ya faɗa.
Cikin wata iriyar muryar dake cike da hargitsi Yah Abana yace.
“Tajjuddeen wai kaine a hoton nan!?”.
Cikin jin ƙahon zuciyarsa na gaba da faso ƙirjinsa murya na rawa yace.
“Eh Yah Abana ”.
Yayi mgnar da iya kar gskyar sanin cewa yess tabbas shi ɗin ne.
Ummey kam kuka mai tsanani ta fashe dashi ta kasa magana haka zalika sauran ƴaƴanta da mafi akasarin Mutanen falon...
Meymey ko gyara zama tayi tana matsar ƙwalla tace.
“Kuma har Video ma akwai”.
Cikin sauri Taj ya ɗago kansa jin yanda Yah Abana ya kira sunansa atsawace.
Ahankali ya ɗago raunatattun idanunsa da suka ciko da k’walla suna sheƙi ya kallesa jin yana cewa.
“Afif ka tashi ka fitar min agidana kabar min gidana bari na har abada bana son ganinka.
Bana son sake kallon wannan ƙazantacciyar fuskartaka arayuwata Afif bana son ka sake shigowa cikin gidana.
Wallahi Allah kenan idanka sake yarda mu kayi ido huɗu Allah ya isa tsakanina da kai!!!”
Cikin tsananin ruɗu mutanen dake falon ke kallonsa.
Passs sautin fashewar glass cup dake hannun Yah Abduraham dake bayan Taj ya ratsa kunnuwansu.
Shi kuwa Malam cikin tsanar halayyar Taj ya cigaba da cewa.
“Kaje na sallamawa duniya kai Afif.
Na barrantarwa duniya kai na cireka daga cikin ƴaƴana daga yau ka fita acikin ƴaƴana.
Tajudden daga yau Allah ya isa idan har ka sake ambaton sunana a bakin ka matsayin mahaifinka”.
Cikin tsananin kaɗuwa mai gauraye da ruɗani Yah Hafiz da Yah Yusuf suka runtse idanunsu suna masu girgiza kansu Yah Abdurrahman kuwa wani sanyayyan kuka ya saki mai cike da ɗimuwa ganin halin tashin hankali da ahalinsa ke ciki.
Su Aunty Maryam kuwa, tamkar an daskarar dasu da dusar ƙanƙara haka suka zama.
Ummu Aryan ko da Hajia babba riƙe kai sukayi.
Mommyn Meymey kuwa da ƙarfi tace.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”.
Yah Abana kam cikin ƙunan zuciya da tsananin fushi ya cigaba da cewa.
“Daga yau ka yanke sunana daga cikin bakinka bana buƙatar ka acikin rayuwata na barrantar da kai daga cikin zuri'ata ku kuma kuji ku shaida dalilin da yasa na taraku”.
Sai kuma ya dire maganar yana kallon ƴaƴan nasa.
Rai cike da ƙunci ya sauke ajiyar zuciya tare da juyawa falon yana kallon ƴaƴansa yayin da numfashinsa ke sama da ƙasa alamar yana son barin gangar jikinsa yace.
“Ku kuma kuji ku shaida duk wanda ya sake mu'amala da Tajudden Allah ya isa ban yafe masa ba, na kuma tsine masa duk wanda ya sake mu'amala dashi bani bashi, ku kuma Matana duk wacce ta kiramin sunan Tajuddeen zata ga fushina, kai kuma Tajuddeen ka tafi kai bazan tsine maka ba, kuma bazan maka baki ba, dan laifin da kayi ya isheka tsinuwa, kawai ni sharaɗin tsinuwana idan ka sake yarda mukayi ido biyu da kai to akan igiyar auren mahaifiyarku kuma bazan yafe maka ba muddin kayi sanadin rabani da Fatima”.
Wani irin kuka mai gunji Aunty Halima, Aunty Maryam, Aunty Rashida suka sake suna masu shiga ɗimuwar jin abinda mahaifin nasu ya faɗa.
Haka ma sauran Matan Mom Amal kuwa fuskarta ba yabo ba fallasa baza ka gane shin farin ciki take ko akasin saba.
Tajudden kuwa kansa na ƙasa ji yake tamkar almara ne ji yake shin mafarki yake ko ko afarke baki daya ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa sun gaza auna kalaman Yah abanansa...
Yah Abana kuwa cikin wani irin kunci zuciya mai tafe da nadamar kasancewar Tajudden jininsa ya cigaba da cewa.
“Idan ka sake yarda kayi ka nunani a matsayin mahaifinka Allah ya isa ban yafe maka ba idan ka yarda ka sake shigowa gidan nan ko kuma ka sake magana da ɗaya daga cikin Ahalina ban yafe maka ba kuma akan igiyar Auren Mahaifiyar ka...
A dai-dai lokacin da yake fadar haka kuma Ummey taja wani dogon numfashi mai nauyi take ta fadi asume.
Lokaci ɗaya kukan Aunty Maryam Aunty Halima Aunty Rashida ya sake tsananta
Yah Yusuf da Yah Hafiz kuwa da rarrafe suka isa gaban Mahaifinsu kana suka riƙe ƙafafunsa tare da cewa.
“Yah Abana kayi haƙuri Tajuddeen bai cancanci wannan abin ba,Wannan hukunci ya masa tsauri kuma muma ya mana tsauri Yah Abana kayi hakuri kada ka yanke wa Tajuddeen hukunci cikin fushi”.
Yah Abdurrahman kuwa da ƙarfi ya matso yana buga kafaɗar Tajuddeen tare da cewa.
“Afif kayi magana Tajudden ka wanke kanka Tajuddeen ka wanke zargin da Mahaifin mu yake akanka Nasan cewa baka aikata ba”.
Taj kam ya kasa motsa laɓɓansa bare ya iya sarrafa harshensa wajen magana.
Aryaan da Kabeer kuwa duk da irin tsanarsa da kuma haushinsa da suke ji sai da hukuncin da Yah Abana ya ɗauka ya girgizasu...
Cikin sauri Taj ya miƙe jin Yah Abana na cewa.
“Ba naso ka ƙara koda 5 minute ne acikin gidana idan ka ƙara ban yafe ba Tajuddeen in ka sake kusanto inda mahaifiyarka take ban yafe ba kuma wallahi akan igiyar Aurenta su Maryam kuma na rabaka dasu”.
Ya kai ƙarshen maganar tare da faɗawa kan kushin .
Cikin kifewar tunani da cushewar zuciya gami da rashin sanin abinyi Taj ya juya tare da ɗaga ƙafarsa dan fita.
Kan glass cup ɗin da ya fashe a hannun Yah Abduraham ya dire ƙafarsa ta hagu.
Cikin sauri Ummu Aryan tace.
“Ya Salam Taj glass ka taka fa”.
Ina baya jinta bare ya iya tsayawa, hasali ma zogin zuciyarsa ya hanasa jin zogin sukan glass ɗin.
A haka yaci gaba da takawa yayinda tuni jini yake meye gurbin shatin sawun nashi.
Da gudu Aryaan ya shiga ɗakin Yah Abana ya ɗauko maganinsa kana ya basa.
Aunty Maryam da Aunty Rashida kuwa Ummey suke jijjigawa.
Ganin haka yasa Yah Yusuf cicciɓan Ummey ya nufi asibiti Aunty Maryam da Aunty Rashida na biye dasu.
Taj kuwa Ahankali ya ɗan kuma juyowa tare da zaro sandar da Sheikh Tajuh Usman Bauchi ya bashi ya ajiye agaban Mahaifinsa tare da faɗin.
“Yah Abana gashi wannan saƙone daga wurin Sheikh Tajuh Usman Bauchi Nigeria daya bani in baka ban samu na baka ba sai yau”.
Cikin tsawa Yah Abana yace.
“Ka fita daga nan bana son ganinka ka ɓace min da gani idan ka sake minti biyar acikin gidan nan Allah ya isa ban yafe maka ba kuma zan tsine maka!!!”
Da sauri ya miƙe tsaye sai kuma ya tsaya jin Yah Abana na cewa.
“wannan ɗin kuma da kayiwa ciki kai zaka ɗauketa kasan yanda zakayi da ita,' saboda cikinka ne bana uban kowa ba.
Kuma dama kai ka kawota cikin ahlina so yadda ka kwasota ka kawo haka zaka kwahseta ku tafi tare da abin kunyarku.
Sannan ka saki Meymey ƴar Aminina ba zata zauna da ƙazamin mazinaci ba ka tabbatar a yau ɗin nan ka saketa”.
Idanunsa dake gane masa duhu ya rumtse tare da mik’a hannunsa ya kamo hannun Laylah suka fita.
Tafiya kawai yake amma baisan inda yake sa ƙafarsa ba, hasalima baya cikin hayyacin sa, meye zaiyi ko ina zai dosa duk baisani ba, ahaka ya ci gaba da tafiya k’afarsa na zubar da jini sannan yana rik’e da hannun Laylah dake ta kuka haka suka dinga tafiya da sawayen su har suka k’araso gidan Addawa...
Cikin murya mafi rauni da sanyi yace.
“Addawa ga Laylah nan ance cikine da ita kuma ance wai ni nayi mata cikin kuma itama ta tabbatar da hakan”.
Hankali atashe Addawa ta kalli Laylah murya na rawa tace.
“Laylah waya miki ciki?”.
Da sauri da kuma alamun tsoro Laylah ta matsa gefen Addawa, again murya na rawa tace.
“Uncle Taj ne”.
Cikin tashin hankali marar misaltuwa Addawa tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Afif meye gaskiyar maganar? menene gaskiyar lamarin”.
Kai ya girgiza kana cikin rauni, had’i da k’unan zuciya me tsanani yace.
“Nima ban sani ba Addawa, na dai san Ummey na bata da lafiya sun tafi da ita asibiti Yah Abana yace idan na sake kusantar ta”.
Sai kuma yayi shiru yana jin wani abu mai ɗaci na toshe masa maƙoshi.
Dai-dai lokacin kuma Aunty Halima tashigo falon da kuka kana ta bawa Addawa labarin abinda ya faru.
Hawayen dake zuba a idanunta Addawa ta share mata kana ta kalli Taj tace.
“Allah yana tare da mai gaskiya kada ka damu Tajuddeen komai yai farko zaiyi ƙarshe komai yayi tsanani maganinsa Allah”.
Idanunsa ya lumshe batare da yace komai ba.
Bayan wasu mintunan kuma ya buɗe idanunsa ya kalli Laylah yace.
“Laylah ki daina tsorona”.
Dan ya lura da yanda yarinyar take tsoronsa abin har mamaki yake bashi.
Aranan anan gidan ya yini sai bayan maghariba ya kira Abu Hashim ya kaisa gidansa yana shiga side ɗin sa ya shiga ya tattara duk wasu abubuwa nasa masu muhimmanci da na amfanin yau da kullum ya haɗa.
Yana mai jin zamansa a Ethiopia yazo karshe Rayuwa''.
a Ethiopia tazo ƙarshe ahankali ya ciri paper guda biyu daga cikin jotter dake cikin Weldrop ɗinsa ya dauki biro ya rubutawa Meymey ta kardan saki sai kuma a ɗayan yayi rubu mai ɗan tsawo kana ya ninke yasa a aljuhu, kana ya cigaba da tattare duk wani abun bukatarsa sannan ya fita.
Abu Hashim kuwa ya lura ubangidansa na cikin tashin hankali kai tsaye gidan Addawa suka nufa.
Yana shiga gidan Addawa ya samu Aunty Halima da Addawa na zaune sunyi zugum-zugum.
Asanyaye yace.
“Addawa Ni zan tafi”.
Aunty Halima kuwa ganin yana juyawa tace.
“Taj ina zaka je?”.
Batare da yace mata komai ba ya kalli Addawa tare da cewa.
“Ki faɗa mata cewa Yah Abana yace idan wani ahalinsa ya sake yimin magana Allah ya isa bai yafe ba ta kiyaye kada Allah ya isan Mahaifin su ya hau kanta”.
Araunane Aunty Halima ta fashe da kuka murya na rawa tace.
“Yanzu Taj ina zaka je”.
Baice mata komai ba ya juya ya fita ya shiga bayan mota Abu Hashim yaja tare da cewa.
“Sir ina zamuje?”.
Cikin sanyi murya yace.
“Gidan tsohon nan da yasa aka auri ƴarsa……”
*Wasa farin girki saidai ba a ma fara wasan ba, kar dai ku manta wannan book d’in na kudine sannan daga page 15 free pages sun k’are saboda haka kar ku bari ayi babu ku, biya 1000 kacal domin samun daman karatu 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa.*
*BY*
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/16, 8:56 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 15*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Last free page*
_LITTAFIN INDA RAI DAI NA KUƊINE 1K NE KACAL, 0661110170 GTBANK Aisha Aliyu Garkuwa. MUTANEN KASAR NIGER KUMA 1000FC JAKA ƊAYA KENAN RAK ZAKU BIYA TA WURIN MOMMY +22790899076_
*Last free page! Last free page!! Last free page!!! Daga wannan Page 15 ɗin na kaɗe na gama free pages koda Kinga littafin INDA RAI a wani group ɗin ki wata ta tura miki to ba satane kuma haƙƙin mallakarsa nawa ne, in kuma baki/baka biyaba kika/ka karantaba mgnar gaskiya haƙƙina dai bazan yafe ba. Littafin INDA RAI na kiɗine ki biya ka biya ku karanta cikin aminci ba haƙƙin kowa bisa kanku a rayuwar nan ta duniya kada ka raina haƙƙin wani dan haka gwara ku biya, 1k ne rak fa 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Ku kuma mutanen Niger ga number wacce zakuyiwa magana ku biya ta wurinta +22790899076. Dan Allah in dai kin san zaki sayane ki kin sayane dan ki fidda min littafina ki barmin abina ko ki gaya min in maida Miki 1k dinki.*
Cikin mamaki Abu Hashim ya ɗan juyo ya kalli ubangida nasa, tare da ɗan rage gudun motar jin yana faɗin.
“Gidan su yarinyar nan da mahaifinta keta kuka a aureta zamu je”.
Ya ƙare maganar murya can ƙasan maƙoshinsa, tare da rumtse idanunsa saboda suya da ƙunci da zuciyarsa keyi, wanda ya hanashi jin azabar yankar da glass cup ɗin daya fashe a hannun Yah Abduraham.
Wani irin sassayan numfashi Abu Hashim ɗin ya fesar zuciyarsa cike da rauni da tsananin tausayin ubangidan nashi, domin yaga tsananin damuwa tare dashi duk da bai fahimci me nene ainihin matsalarsa ba.
cikin girmamawa yace.
“Sir gidansu Adaya kenan”.
Ya dire ayar tambayar yana nazarin halayen Adaya da binciken da yayi a kanta ya nuna mishi.
A hankali ya ɗan gyara zamansa tare da kallon Tajj ɗin ta mirror.
So yake yayi mishi cikekken bayanin akan tarbiyya da halayyar Adaya to Amman ta ina zai fara? More especially yanzu da yaga ubangidan nashi yana cikin yanayi mai wuyar fahimta, saboda zurfin cikin sa da haƙurinsa da jumriyarsa, yasa bazaka iya tantance halin da yake cikiba.
Shi kuwa Taj.
Numfashi mai zafi ya fesar dai-dai lokacin da yaga sun ɓullo kan titin nan da bazai taɓa mancewa a rayuwarsa ba.
A hankali ya dire ganinsa kan masallacin da ƙaddarar auren Adaya ya riskeshi a ciki.
A hankali ya ɗagawa Abu Hashim hannu jin yana faɗin.
“Sir lamarin yarinyar fa, ba daɗi a bisa binciken da...”.
Sai kuma yayi shiru ganin Taj ɗin ya ɗaga masa hannu tare da jujjuya mishi kai.
Shi kuwa Abu Hashim a hankali ya sauƙe numfashi tare da fuskantar gate ɗin gidansu Adaya, kana ya matsa hon.
Da sauri maigadin gidan ya leƙo, ganin dantsatsetsiyar motar dake tsaye tana zuba ƙyalli ne yasashi saurin buɗe musu gate ɗin.
A hankali ya yayi parking, tare da buɗe marfin motar ya fito yana mgnar zuci.
Nazari yau kusan kwana ashirin da biyar kenan da yin wannan binciken Amman ya rasa ta ina zai fara faɗawa ogan nashi sabida ganin tun ranar da aka ɗaura auren bai sakeyi mishi mgnarba, gashi ya roƙeshi mgnar ta kasance sirri a tsakaninsu.
Da sauri ya ɗan miƙawa Maigadin hannu tare dayin mishi sallama yana mai mmkin wani irin kallon da maigadin ke binshi dashi.
Shi kuwa Maigadin cikin nazari da tuno fuskar Abu Hashim ɗin da dan farin sani gani da yayi mishi a ranar da yace ya aura wa ɗansa Tajuddeen Adaya, cikin tsananin jin daɗi yace.
“Mahaifin Tajuddeen mijin da ka aurawa Adaya ko!”.
Da sauri Abu Hashim ya gyaɗa mushi kai yana mai mamakin yadda akayi bai mance fuskarsa da sunansa ba harma da sunan Tajuddeen ɗin.
“Kai Masha Allah, yau mai gidan zaiji kekkyawan labari da yake fata”.
Ya ƙare maganar yana murmushi.
Shi kuwa Abu Hashim cikin sanyi yace.
“Masha Allah, to kayi mana sallama dashi, kace dashi yau ga mijin Adaya na kawoshi”.
Gyara tsayuwarsa yayi tare da ɗan jim kaɗan cikin sanyi jiki yace.
“Baya gida, yau kwanansa biyu a asibiti, ciwonsa ya tashi”.
Cikin sanyi da alamun damuwa ya ƙare maganar, shi kuwa Abu Hashim cike da tausayawa yace.
“Ayyah Allah ya bashi lfy, to Ma'aruf fa?”.
Yana ɗan sauƙe numfashi yace.
“Duk basa gidan sai Adaya itama yanzu ta dawo, daga asibitin da ƙaninta to shi yanzu ya fita”.
Shi kuwa Tajj shiru yayi cikin motar tamkar ba kowa, haka nan yakeji duniyar na juya mishi.
Ji yake yi tamkar ba'a raye yake ba, haka nan yakejin ƙasar Ethiopia tamishi zafi da ƙunci, to me zai yi a cikin ƙasar tunda Yah Abana ya barrantar dashi da kowa nashi.
Sai kuma ya rumtse idanunsa da ƙarfi saboda wani irin ƙunci da zuciyarsa keyi masa, so yake yayi tunanin ta ina zai fara bawa wannan kamilin dottijon haƙuri akan abinda yasan in yayinshi dottijon zaiji ƙuncin zuciya da rayuwa.
Shi kuwa Abu Hashim a hankali yace to.
“To ayi mana iso da ita ɗiyar tawa ace mata ga mijin ya iso”.
To yace jiki a mace ya nufi cikin gidan domin ya san wacece Adaya da kuma yadda take ƙin batun aure, dama yadda take wargaza duk aurenta da mahaifinta ke shiryawa, da wannan nazarin ya nufi size ɗin Ummin Adayan inda yake jiyo kiɗa na tashi.
Bakin motar Abu Hashim ya dawo, tare da ɗan leƙawa ta ciki kaɗan.
Ganin haka ne yasa Taj ɗin ɗan sauƙe glass ɗin kaɗan tare da zuba mishi ido.
Cikin girmamawa ya gaya mishi yadda sukayi da Mai gadin.
Kai kawai ya jinjina mishi.
Ita kuwa Adaya da ɗan sauri ta miƙe tsaye daga zaman da take a gaban dressing mirror bisa dukkan alamu yanzu ta fito wanka.
Dan Towel ne a daure a ƙirjinta.
Jin yadda ake ta buga ƙofar ne, yasa tayi saurin jawo hijabin dake gifenta ta zura shi kana ta nufi ƙofar.
Ido ta zuba wa Maigadin nasu lokacin data buɗe ƙofar.
Shi kuwa ɗan rusunar da kanshi yayi yana maijin kiɗin data sake yana buwayarsa.
“Lfy meke faruwa?”.
Tayi tambayar tana girgiza ƙugunta, saboda haka take bata taɓa iya nitsuwa.
Ita a zatonta su Ummi ne suka dawo.
“Kinyi baƙi ne!”.
Ya faɗa yana ɗan jan baya.
“Toh kace su iso mana, ya za'ayi ka barsu a waje, su Asina ne da Izzin suka zama baƙi kuma”.
Tayi tambayar da alamun tana tsumayin jiransu ne, zasu fita su tafi wurin ibadar rawar da suka ɗaurawa kansu.
Cikin sauri yace.
“A'a basu bane!”.
Tana mai ɗan juya ido tace.
“Toh su waye ne?”.
Cike da tsoro yace.
“Bawan Allah nanne daya aurawa ɗansa ke, to shine yazo da mijin naki”.
Wani irin murmushin mai sauti ta saki tare da juyi a tsakiyar Parlour kana tace.
“Da gaske?”.
Da sauri yace.
“Wallahi kuwa gasu can a harabar gidan”.
Ya ƙare maganar yana mai kafeta da ido da mamakin yadda fuskantar ta cika da farin ciki.
Ita kuwa Adaya cikin Tsananin jin daɗi samun damar yadda zata watsa auren ba tare da wani mushkila ba, kasancewar ba kowa a gidan babu mai taka mata birki da fesa mishi salon tijarar da zatasa dole a yau ɗin a yanzu ya saketa ta samu damar cimma burinta cike da jin daɗi tace.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma tayi maza ta wuce ta gefenshi tare da cewa.
“Bari in kawo maka key ɗin BQ kaje ka buɗe mishi kace ya isa”.
To yace kana ya bita da ido.
Da sauri ta dawo tare da miƙa mushi key ɗin.
“Yauwa Baba ya yanayinshi yake?”.
Yana ɗan lallonta yace.
“Toh gsky dai ban ganshi ba, Amman zan iya nazartan yanayin mahaifin nasa mutumin kirkine, kuma shima ɗan hakanne domin naji Muryar karatun Sheykh Afif Muhammad Taj ne ke tashi a cikin motar tasa bisa alamu mutanene managarta ne masu kamala”.
Da sauri tace.
“To je kayi mishi iso”.
Ta ƙare maganar tana komawa ciki.
Wayarta ta ɗauka tare da dannawa Asina kira bugu ɗaya ana biyu ta ɗauka.
“Ke wai dan Allah kuna inane har yanzu baku iso ba?”.
Cikin juya ido Asina tace.
“Gani nan ban fito Bama Izzin nake jira yazo ta ɗaukeni”.
Wani dogon tsaki taja tare da cewa.
“Kai Izzin na mana wulakanci wlh rashin mota na damunmu, Amman ba komai nasan in sha Allah muna dawowa gasar rawar nan, motoci sai wanda mukeso zamu hau, ke dai muyi fatan Allah ya bamu sa'a”.
Cikin ƙwaffa Asina tace.
“Wlh kuwa Kinga nayi ta kiranshi ma baya ɗauka.”
Tana gyara wuyan hijab dinta tace.
“Dan Allah ki fito ki hau taxi ki taho, Kinga wai yanzu wannan wai Tajuddeen da Abpu keta cewa mijina, ne yazo so kuyi sauri kuzo mu tace mishi mutunci dan naji alamun ustadz ne so da makircin karuwaci zamu sa ya sakeni yanzu”.
Cikin sauri Asina tace.
“Kan bala'i gani nan fitowa yanzu kice zamu goge haddar kan ustadz”.
Cikin jin daɗi tace.
“Fes ma kuwa.
Yauwa maza kiyi sauri bari in kira banzannan kuma, dan kin san dashi abin zaifi tafiya zaifi zargin Izzin ɗin Guy ɗin dake ɗebe min kewa ne Kinga saki dolen doliya kafinma su Ummi su dawo munkorasu”.
Da sauri Asina ta miƙe tsaye, tare da katse kiran kana ta fitowa Parlour inda ta samu tsohuwar kakarta wacce tsufa ya cimmata.
“Yanzu Asina bazakiyi kanki faɗa ki raba kanki da wannan shegen yaronya ku kama kanku ke da Adaya kusan cewa akwai mutuwa da kwanciyar ƙabari da hisabiba.
Tana yamutsa fuska tace.
“Ni Kinga tafiyata ki rufe ƙofarki, dan acan zamu kwana, saboda rihazal ya fara zafi”.
Taƙare mgnar tana fita, da ido tsohuwar nan ta rakata ido na cikowa da hawaye.
Tace.
“Yah Allah kaine mai shiryawa ya Rabbi ka shiryi yaran nan shirin musulunci.”
Ita kuwa Adaya Parlour ta fito waya na maƙale a kunnenta.
Cikin wata iriyar muryar dake nuna Izzin ɗin yana tare da macene yake mata mgn.
Tsaki yaja tare da cewa.
“Please kayi sauri kazo gidanmu, zamu kora mijin da Abpu ya aura min. Wai yau yazo, karka biya Asina ita ta fito”.
Da sauri yace.
“Ok gani nan zuwa”.
Ya ƙare maganar da raba jikinsa dana arniyar ƙaruwar tasa.
A hankali ya iso gefen Abu Hashim tare da cewa.
“Bismillah ku isa BQ na buɗe, Adaya nan fitowa”.
“To mun gode”.
Ya ƙare maganar da bashi hannu.
Kai ya gyaɗa kana juya ya koma bakin gate wurin aikinsa wanda yake da ɗan rata daga inda motarsu yake.
Da sauri ya buɗewa Taj marfin motar tare da cewa.
“Bismillah ka isa”.
Cikin sanyi ya ziro ƙafarsa waje tare da fitowa yana mai rumtse idanunsa.
A lokacin ɗaya a rana ɗaya ƙaddara ta sauya mishi komai, ta kuma sashi zai akata abubuwan da yafi tsana a rayuwarsa a tun lokacin daya kasance aboki ga Ishmah da ya san sanadin abinda zai aikata yaune ƙaddararta.
A hankali yake taka ƙafarsa ya nufi BQ ɗin yana mai jin tausayin Dottijon shin ya zaiyi ya zaiji in yaji abinda zai akaita akan ɗiyarsa to Amman ya zaiyi dole ne ta bar Ethiopia ya kuma nesanta da ita da duk abin cikinta dan gudun tsinuwar mahaifinsa da kuma tsoron kada ya zama silar mutuwar auren iyayensa da gudun faɗawa Allah ya isan mahaifinsa akan ƴan uwansa domin yasan muddin dai in yana cikin Ethiopia to su Aunty Maryam da Rashida dasu Yah Abduraham dasu Hafiz Yusuf bazasu iya hana kansu alaƙa ko magana da shiba.
Cikin wannan nazarin ya isa BQ ɗin a hankali ya shiga cikin Parlour mai wadace da tsabta.
Sai dai Parlour yana da duhu sosai, kasancewar windows ɗin Parlour a lungu suke kuma a rufe suke ga kuma labuyen dake sassake.
Shi yasa haske bai wadaci Parlour ba dan iya ɗan hasken bok ɗin dake wajene ya ɗan bawa Parlour'n haske kaɗan.
A hankali ya zauna bisa 1 setter dake fuskantar 3 sitter.
Ita kuwa Adaya wani irin makirin murmushi tayi tare da sauƙe Towel ɗin dake ƙirjinta ƙasa ta ɗaurashi bisa ƙugunta, kana ta gyara wuyan hijabinta wanda hakan ya bawa turmusa-turmusan breast ɗin ta dama sakewa da rausaya wa, a haka ta nufi BQ ɗin.
A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗesu a hankali,.
Cikin sanyi ya gyara zamansa saboda ganin duhun ya ɗan raguwa idanunsa kasancewar ya ɗan jima kaɗan a Parlour.
Ƙasa yayi da idanunsa lokacin da yaji sallamarta da shigowar ta duk a tare ta haɗasu,
Murya cike da kamala yace.
“Wa alaikissalam”.
Wani irin numfashin da yafi kama da na jarababbun mata ta fesar.
Wanda haka yasashi ɗago kansa.
Da sauri ya kwaɓe fuska ganin yadda take wani irin girgiza mishi Ballong ɗinta gami da yin wani fitinenne murmushin mai cike da makirci da fidda ainihin rashin jinta da fitsararta.
Tare da ware idanunta dan ita har yanzu duhun ya hanata ganin fuskarsa.
Shi kuwa Taj.
“Wa iyazubullah”. Shine abinda ya furta a kan lips inshi tare da yin ƙasa da kanshi.
Jin haka ne yasata saki wani sabon sautin karuwanci fahimtar eh lallai plan dinta zaiyi aiki.
A hankali ta matso garesa, tana mai lumshe idanunta tare da shaƙan sassayan ƙamshin jikinsa da yasata saurin rusunawa.
Allah ya sani bata taɓa jin ƙamshin wani ɗa namiji da yayi matuƙar sauya mata nutsuwarta ba kamar wannan.
Da sauri ya ɗan ƙara matsawa gefen kujerar.
Ita kuwa Adaya cikin jin feelings ɗin gsky yana diro mata a jiki da zuciyarta ne, ta dire guiwowinta a ƙasa tare da kife kanta bisa guiwowinshi.
“Innalillahi”. Shine abinda kunnenta ya jiyo mata yana faɗi.
Shi kuwa Taj wani irin tafasa da ƙuna yaji zuciyarsa tana ruɓanya yi saboda ganin lalacewar da ko a mafarki baya fatan gani.
Wani irin zare idanunsa yayi a lokacin da yaji ta sa hannunta duka biyu ta zagayo ƙugunsa murya cike da shu'umci ta fara mgna.
“Hi my life, Barka da zuwa”.
Hannunshi yasa da sauri ya fara tureta daga jikinsa.
Da sauri tasa hannunta ta zare hijabinta tare da cilla shi can gefe.
Cikin wani irin tsoron ganin tsananin lalacewar tarbiyyar ta, ya rumtse idanunsa da masifan ƙarfi.
Sai kuma yaji jikinsa ya saki wani irin fitinenne rawa da tsuma, lokacin da yaji ta kamo hannunsa ta diresu bisa tamfatsa-tamfatsan breast ɗin ta.
Da ƙarfi ya yunƙura da nufin yin mgn sai kuma ya rumtse idanunsa jin ta zira mishi harceta cikin bakinsa.
Dai-dai lokacin kuma Ummeey dake kwance bisa gadon asibitin ne takeyin wani irin maraitaccen kuka mai raunata zuciyar mai sauraro.
Hannun Malam ɗin dake tsaye a gefentan ta ruƙo cikin tsananin rauni tace.
“Dan Allah Malam kada ka nesan tani da Afi...”.
Da sauri yasa hannunsa ya rufe mata bakinta fuska cike da fusata gami da tsana da hargitsewar tunani yace.
“Kada ki kira min sunansa, wlh muddin kika sake kira min sunansa a bakin aurenki, kuma in har ya zama sanadin rabuwata dake bazan taɓa yafe masa ba, domin ya rabani da mace mafi soyuwa da jinƙai a gareni, duk kuma ɗan dake jinina in ya kira min sunansa ko yayi alaƙa dashi Allah ya isa ban yafe ba, kuma tsinuwata zatabi bayan Allah ya isan”.
Da ƙarfu Yah Hafiz, Yusuf, Abduraham, Maryam, Rashida, Zakiya, Halima dama duk sauran suka rumtse idanunsa.
Addawa kuwa cikin sanyi ta kalli ɗiyartata cikin bada umarni tace.
“Fatima in dai ni na haifeki, kuma zakiyi min biyayya to ban yarda ba ban yafe ba ki sake kira mishi sunan da yace in kin kira akan aurenki ba”.
Cikin tsoro da tashin hankali Ummeyn Taj ɗin ta kalli mahaifiyar tata tana mai zubda hawaye masu ƙuna tace.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun, Allahumma ajjirni fi musibati wa...”.
Sai kuma ta kasa ƙarasa saboda numfashi daya toshe mata daga ƙasan zuciyarta domin zafin abubuwan sunyi mata yawa.
Ita kuwa Addawa da sauri ta juya ta fice.
Cikin sassarfa Rashida tabi bayanta.
Shi kuwa Malam cikin zafin zuciya yake mgnar zuci da take iyakar gskyar sace
“Wallahi Allah kenan kab cikin Matana babu macen da ɗanta zaiyi abinda Taj ya aikata, ban haɗa da ita na sakaba.
Allah kaine mafi sanin irin yadda ka jarabci zuciyata da son Fatima shiyasa ban haɗa da ita na korata da ɗanta ba”.
Sai kuma ya juya ya fita.
Su Hafiz kuwa zagaye Ummeey sukayi suna bata baki..
Nigeria acan Adamawa kuwa, sosai jihar ke cika tib da baƙin manya malamai da ƙananan saboda ƙaratowar taron ƙarawa juna sani, da haɗa kan izala da ɗarika da za'ayi a jihar.
Anyi yarjejeniyar yin taron a Adamawa ne, saboda kab Nijeriya Adamawa ne dai muka rage da tutar Shehu Usmanu danfodiyo, hatta Sokoto da yake tushen Shehu tuni tutarsa daya kafa musu ta ƙare.
Sai na Yola Adamawan Modibbo Adama Yola dogge doggitore.
To Shi yasa taron ya kasance anan.
Tuni Mai girma shugaban izala ta ƙasa yake amsar tawagar bakwancin malaman suna na kasar.
Yayinda Masarautar Lamiɗo kuma yake mai masauƙin malam ɗarika da sarakunan gargajiya da suka samu daman halartar.
Kasan cewar yau Laraba gobe al'hamis jibi jumma'a da dare ne za'ayi zaman.
Ishmah ce kwance bisa gadonta, yayinda ƙanwarta autarsu da Hamisu da Adam ke zaune a tsakiya ɗakin suna hira.
Tun bayan rasuwar Dadeey itace ta meye musu gurbinta, kamar dai yadda Daddy ta bar mata watsiyar kula da ƙannenan nata.
A hankali Rahma ta ɗan miƙo mata plate ɗin data sa mata kankana tana faɗin.
“Adda lfy kuwa”.
Tana amsar plate ɗin tace.
“Yau fa tun safe neke kiran Taj Amman baya ɗagawa”.
Gyara zama Adam yayi tare da cewa.
“Wata ƙil yana sararin samaniya ne Adda kin sanshi ba mazauni bane”.
Da sauri tace.
“Kuma baifa cemin zaiyi tafiya ba”.
Sai kuma ta amshi wayar ta da Hamisu ke miƙa mata yana faɗin.
“Ga Bappa Kawu na kira”.
Amsa tayi tare da yin piking call ɗin.
Su kuma hirarsu sukaci gaba da yi.
A hankali ta sauke numfashi bayan sun gaisa sai kuma ta ɗan zare ido jin yana cewa.
“In sha Allah ranar Friday zan shigo Yola zanzo cikin tawagar Sarki Abubakar.
Zanzo da cikar shirina in kin amince dani ko a ranar ma a ɗaura mana aure”.
A hankali tace.
“Uhmmm”.
Sai kuma tayi shiru shi kuwa Bappa Kawu cikin sanyi yaci gaba da kafa gwamnatinsa.
A can Parlour Abba kuwa kishingiɗe yake yayinda Yah Abubakar ke gefensa waya yakeyi da Uncle Bello.
“Toh ai dama rayuwa ta gaji haka, kuma dole Aysha dai aure zamuyi mata.
Domin ko ɗazu da Yamma yaron nan Mukhtar saida yazo min da yayansa da bappansa wan mahaifinsa. Kuma yace ranar jumma'a zasu zo Yola.
Kaga dole haka zaka daure kayi aure, in dai anyi sadakan arba'in ɗin marigayi ya.”
Cikin sanyi da tarin rauni mai raunata zuciya yace.
“Kayya ni kuma wani aure ya rage min Yah Bello, ai aure kam sai yara ita dai Mamana in samu tayi sauren shine burina, sai kuma batun auren Adam, kasan jibin za'a kai kefensa”.
Cikin sanyi Uncle Bello yace.
“To Abdullahi zaka zauna hakane, ai zama haka bazai yuwuba. Dole kayi aure ko dan Rahma da Hamisu”.
Cikin sanyi yace.
“Hummm”.
Littafin INDA RAI na kiɗine karki karanta in baki biyaba dan Allah 1k ne ga account no in da zaki turo min kuɗinku 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, ku kuma mutane Niger ga number Mommy ita zakuyiwa magana ta gaya muku yadda ta inda zaku tura mata kuɗin 1000fc ne haka ɗaya kenan +22790899076
Ethiopia.
Motarsu na fita daga gate ɗin Asina na shiga ta ƙaramar ƙofar, da kallo tabi motar tamkar zata liƙe idanunta akai.
Yayinda shi kuma Baba mai gadi bin motar yajeyi da idanun tamkar zai liƙasu a jikin motar, har leƙawa yakeyi gami da karkata kanshi, saboda wai ko zai samu yaga angon Adaya.
Amman ina hakan bata samuba saboda Glass ɗin motar tintek ce mai ɗan karen duhu gashi kuma dare ne, duk dama dai akwai wadatar haske Amman daga shi har Asina babu wanda ya iya ganinsa.
Ita kuwa Asina cikin mamaki take kallon motar har saida ta ɓacewa ganinsu, kafin shima Maigadin ya iya rufe gate ɗin.
Da sauri ta nufi cikin gida, da sallama ta shiga Amman shiru ba motsin kowa, da sauri ta juya ta nufi BQ ɗin tunowa cewa Adaya tace can zata sauƙi baƙon nasu.
Abu Hashim kuwa driving yakeyi cike da tsananin mamaki mai haɗe da ɗumuwar ganin yadda ogan nashi ya fito daga BQ ɗin.
Ta jikin mirror ya ɗan saci kallonsa.
Wani irin rawa da tsuma illahirin jikinsa keyi, yayinda gaba ɗaya jijiyoyin saman goshinsa har na kan idanunsa suka tattaso.
Yayinda tsikar jikinsa ke tsaye har yanzu.
Kana yasa hannunsa duka biyu ya kama kanshi ya matse da masifan ƙarfi.
Dai-dai lokacin kuma ya karya kwanar da zai bar layin.
A kuma dai-dai lokacin motar Yah Ma'aruf ta danno kai dan shiga layin
Yayinda Ummin Adayan ke baya, saboda yau Mommynshi ce zata kwana da Abpu a hospital.
Cike da mamaki Ma'aruf ya zaro idanunsa, ganin Fuskar Abu Hashim ta Glass ɗin fuskar gaban motar.
Cikin mamaki yace.
“Wannan bawan Allah nanne fa daya aurawa ɗansa Adaya”.
Cikin sauri Ummi tace.
“Kai haba dai ina yake”.
Ta ƙare maganar tana leƙa inda ya nuna mata.
Shi kuwa Abu Hashim tuni ya hau kan babban titin ya cilla hancin motarsa ya kama hanyar da zata sadashi da Airport.
Cikin sauri Ma'aruf yayi sauri dawo da kanshi kan tuƙin da yake yi tare da cewa.
“Inaga fa gida yaje”.
Da sauri Ummi tace.
“Sosai ma, tunda kaga a layin namu ya fito ai, mu ƙarasa gidan.
Nasan ai ya samu Aminu a gida.”
Ta ƙare maganar tana gyara zamanta cike da jin daɗi tace.
“Alhamdulillah Malam zaiji labari mai daɗi”.
Cikin jin daɗi Ma'aruf yace.
“Sosai ma kuwa, dan wlh nasan da matsalar Adaya ce ƙarin cutarsa”.
A can gida kuwa cikin tsananin tsoro da kaɗuwa Asina ke kallon Adaya dake zaune a ƙasa ta haɗe guiwowinta tare da cusa kanta a ciki tana rusa wani irin maraitaccen kuka dake nuna tana cike da jin raɗaɗi.
Da sauri ta durƙusa gabanta sai kuma tayi saurin jawo hijabinta ta rufe mata jinkinta tare da cewa.
“Innalillahi Adaya me ya faru”.
Cikin kuka murya a raunace tace.
“Asina ni nayi da yaudara na jawa kaina ya tureni ya targaɗa min ƙugu ya kum.”
Sai kuma ta kasa ƙarisawa saboda yadda takeji wani irin fitinenne zogi da raɗaɗin a muhallinta daya ratsa cikin fitar hayyaci.
Dai-dai lokacin kuma Ma'aruf yayi parking da sauri ya fito yana tambayar Baba maigadin.
“Baba munyi baƙi ne?”.
Da sauri ya matso kusa dashi tare da cewa.
“Eh yanzu nan suka fita kun haɗu ko, Wannan mutumin ne daya aurawa ɗansa Adaya yazo ya kawo ango”.
Cikin sauri Ummi da yanzu ta fito tare da cewa.
“Allah dai yasa ya samu Adaya a gida?”.
Yana gyaɗa kai yace.
“Eh sun ɗan jima ma, bata fito bama tana BQ ɗin”.
Ummi najin haka ta juya ta nufi BQ ɗin.
Tana shiga ta zare ido cike da mamaki yadda Adaya ke kuka, bayanta ta zauna bisa kujera.
Sai kuma tayi saurin ɗan matsawa tare da ƙara buɗe idanunta ganin rafan sabbin kuɗi kusan ɗauri biyar sai kuma wata takarda daga gefensu...
Shi kam Taj gaba ɗaya jikinsa rawa yake da tsuma.
Haka nan yake ji tamkar ya tsinewa kanshi da kanshi ji yake dama mutuwa kawai yayi ya huta da wadannan jarrabobin da sukayi mishi rubdugu suka sauya rayuwarsa, kenan shi dai Allah bai sashi cikin masu sa'ar aureba.
Ya tabbata kenan rayuwarsa ta shiga garari ko dai Yah Abana ya tsine mishi ne, ya tambayi kanshi cike da zulumi.
A haka suka isa Airport.
Isarsu da 40 minute jirginsu ya tashi daga Ethiopia zuwa Dubai.
A hankali Abu Hashim ya daga kansa yana kallon jirgin tare da sauƙe numfashi mai tafe da hawaye.
Maganganun Ubangidan nashi na mishi amsa kuwa a kunnuwansa.
“Abu Hashim zan bar ƙasar nan, bari kuma na har abadan. Shi yasa na biya na saki Adaya domin bazan tafi inbarta da igiyar aurena a kantaba.
Ga kuma wannan takardar itama ta sakice
Ka kaiwa Meymey shi ka damƙashi a hannunta.”
Wasu hawaye ne masu masifar zafi suka fara kwaranyo mishi wasu na korar wasu lokacin da yaga jirgin ya ɓacewa ganinsa a.
“Sir wacce ƙasar zaka koma, kuma ya batun aikinka?”.
Ya tuno tambayoyin da yayiwa Ogan nashi da amsa da ya bashi.
“Ban saniba Abu Hashim bansan ina zan samu karɓuwa ba, domin gaba ɗaya duniya ta ƙini”.
A hankali ya juya akalar motarsa ya nufi gidan Uncle Jibirin.
Kamar yadda ya duba tun kafin ya biyo jirgin Dubai cewa washe gari da yamma akwai jirgin Nigeria zai tashi.
Hakanne ma ya sashi biyowa Dubai, kasancewar su Ethiopia saura kusan kwana biyu ne kafin jirgin Nigeria ya tashi.
Hakance da yammacin al'hamis jirgin Nigeria ya tashi daga Dubai.
Yau jumma'a haji babbar rana, sanin Bappa Kawu da iyayensa suna kan hanyarsu ta zuwa ne, yasa Ishmah shirya musu abinci tare da kimtsa BQ da tunda Taj ya koma tsawon kwana talatin kenan ba'a buɗeshi ba sai yau.
Ƙarfe goma dai-dai ta gama komai,
Kana ta shiga tayi wanka a hankali ta fito tare da zama bakin gado cikin sanyi ta kalli Rahman dake yiwa Khairat kitso.
Cikin sanyi dake nuni da tsananin damuwa ta jawo wayarta tare da kiran Taj ɗin a karo na barkatai.
Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe jin ya amsa kiran, kawai sai ta saki siririn kuka mai sanyin sauti.
A hankali ya lunshe idanunsa dai-dai lokacin da yake zaune a gaban Sheykh Tajuh Usman Bauchi da ya kasance ɗaya daga cikin baƙin da aka karrama aka kuma tarba a cikin masarautar Joɗa.
A hankali ya kuma buɗesu murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Wayyo Ma'eesha zuciyata zata fashe”.
Ya ƙare maganar a saman lips inshi yadda ko Sheykh dake gefensa bai jishi ba.
Da sauri tace.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun, Taj kana ina? Meke damunka? Meyasa wayarka bata shiga? Addawa tace min ba'asan ina kake ba, Please Taj tell me now ina kake?”.
Ta ƙare maganar cikin sassayan shesh-sheƙan siririn kuka.
Cikin sanyi murya da ƙara jin ƙarfin guiwa da karsashin ƙudurinsa yace.
“Maeeshah yi haƙuri kiyi shiru, ina tahowa gareki yanzu”.
Daga nan ya katse kiran.
Da sauri tace.
“Please Taj tsaya”.
Sai kuma tayi saurin kiransa ganin ya katse kiran.
Sai dai jin wayar bata shigane yasa ta tallabe habarta cike da damuwa.
Shi kuwa Taj ido ya zuba Sheykh Tajuh Usman Bauchi dake jinjina mishi kai alamun ƙarfafa guiwa kana ya miƙa mishi hannu tare dayi musu alamun su tafi.
Ƙarfe sha daya dai-dai.
Adam ya shigo Parlour tare da kiranta a jere a jere.
Da sauri ta fito sanye cikin Nevy blue ɗin Turkey Abaya mai masifar sheƙi da sulɓi tayi rolling kanta da ɗan gyalan.
Cikin sauri yace.
“Abba yayi baki yace, maza-maza ki bani ruwa in kai musu”.
Ya ƙare maganar da nufa dinning area Yana buɗe fridge, ita kuma tray dake kan Dinnin table ɗin ta miƙa mushi.
Tare da tayashi kwasar Juice tana faɗin.
“Ko dai su Bappa Kawu ne suka iso”.
Da sauri yace.
“A'a”.
Tana ajiye gorunan Faro water data ciro a fridge din tace.
“To ko dai Uncle Bello ne ya iso”.
Ɗaukan trayn yayi tare ficewa bai bata amsaba a bakin Parlour Abban ya haɗu da Yah Muhammad da Uncle Bello da yanzu ne isowarsa.
Amsar tryn Yah Muhammad yayi tare da cewa.
“Kaje ka ɗauko Cups kuma idan da Nono ma ka kawo in babu a wurinku kaje wurin Asma'u tana dashi ka amso”.
Ya ƙare maganar yana komawa ciki.
Shi kuwa Adam yana koma Parlour yace.
“Adda wai ki bani Nono in akwai”.
Cikin sanyi tace.
“Baka gaya min su waye bane”.
Cikin sauri yace.
“Nifa ban gansu ba Amman dai manyan baƙine dan yadda naji Abba da Yah Abubakar suna musu sannu da zuwa da kuma irin motocin da suka zo”.
Ya ƙare maganar yana zaro trayn data cikashi da fruits.
Sai kuma ta iso tare da ɗago kwarya nono ta miƙa mishi tray ta daura kan kwaryar kana ya fita.
A bakin ƙofar Parlour ya haɗu da Yah Abubakar na cewa.
“Maza kawosu koma ka ɗauko Cups da mugs da spoon”.
Da sauri yace to.
Kana ya koma tare da fara haɗa cups da mugs ɗin da spoon kana ya fita.
Ita kam Ishmah jiki a sanyaye ta zauna bisa kujerar Dinnin table ɗin, sai kuma ta fara ɗan lallatsa wayarta tare da kiran Bappa Kawu a zatonsa shine ya iso da Sarkin Gombe shiyasa ake musu wannan hidimar.
“Hello Bappa Kawu kun iso ko?”.
Sai kuma ta ɗanyi shiru tana jin me yake faɗi.
“No bamu isoba, muna sabana, kafin mu iso kuma lokacin salla zai ƙarato so zamu wuce masallacin Lamiɗo Berkinɗo Aliyu Mustapha, sai an sauƙo sallan jumma'a zamu zo”.
Jin haka ne yasa ta faɗa tunanin to su waye ne sukazo.
Shi yatsaya yana ta mata mgn bata jin shi bare ta bashi amsa.
Jin shirunne yasa ya katse kiran.
A can Parlour Abba kuwa shiru Parlour yayi baka jin mgnar kowa sai sassayan sautin muryar Tajj.
Dake ratsa kunnuwansu da zuƙatansu da sasu daskarewa a zaune a hankali yake motsa lips inshi tare da fito da kalaman dake fitowa daga can ƙasan zuciyarsa.
A hankali ya ƙara rarrafawa ya matso gaban Abba tare da zubewa kan guiwowinsa duka biyu.
Ido suka zuba mishi baki ɗaya.
Murya cike da rauni da gskyar zuciyarsa murya cike da rauni yace.
“Abba ina son Ishmah, ina kuma roƙonka da girman Allah da Manzonsa ka bani aurenta Abba na fara son Ishmah tun aranan farko dana fara ɗaura idanuna akanta.
Abba ina yiwa Ishmah wata irin sihirtacciyar ƙauna wanda zuciyata bazata iya samun nutsuwa ba tare da ita ba”.
Sai kuma ya lumshe idanunsa dake cike tab da da ruwan hawaye wanda yake ji tamkar ana sauƙe masa wani abu mai masifar nauyine azuciyarsa bai damu da duk wanda ke falon ba burinsa ya faɗi abinda ke zuciyarsa cikin wanda yake tsagalgalar rayuwarsa cikin gaskiyar abinda ke zuciyarsa na tsawon shekaru yace.
“Abbah na ɗauki tsawon shekaru ina dakon soyayyar Ishmah araina itace mace ta farko dana fara so atarihin rayuwata ban taɓa son wata ɗiya mace irin yanda nake sonta ba itace kaɗai nake kallo a duniya a matsayin matar aurena”.
Abba, Yah Muhammad Yah Abubakar kam cikin mamaki suke kallonsa, murmushi dake cike da kunya Yah Abubakar yayi tare da zaro wayarsa.
Taj kuwa cikin sanyi da taushin lafizi ya cigaba da cewa.
“Abbah nayi alƙawari zan riƙe maka Ishmah da amana. Abba Ishmah itace duniyata, itace farin cikia, itace muradin raina, Abba dan girman Allah ka Aura min Ishmah koda zan samu nutsuwa da salama acikin rayuwata. Dan Allah Abba ka kusanta min Ishmah cikin rayuwata ko zan samu sauƙin raraɗi da azaban zafin da ƙaddara ta haddasa min”.
ya ƙare maganar cikin wata raunatacciyar murya...
Idanu Yah Rabi'u ɗan Uncle Bello ya zuba masa yana hango tsananin soyayyar Ishmah acikin ƙwayar idanunsa tabbas yayi soyayya yasan kuma menene so duk wani abu da Taj ke faɗa yana fitowa ne daga can ainihin ƙoƙon zuciyarsa zuwa kan harshensa babu wani daɗin baki ko yaudara acikin kalamansa.
Tunaninsa ne ya katse jin Taj na cigaba da cewa.
“Abbah My life is nothing without Ishmah she's one in Trillion in my Heart Abba ina ƙaunar Ishmah da duka zuciyata wanda ban taɓa yiwa wata ɗiya mace ba kuma babu wacce zan yiwa irinsa har gaban Abadan”.
Abba kam lumshe idanunsa yayi yana mai jin wani irin nutsuwa na ratsa magudanan jinin jikinsa tamkar ana sauƙe masa ni'imah lokaci ɗaya kwakwalwar sa ta shiga tariyo masa mafarkan da Daddy tace masa tayi akan Taj da Ishmah tabbas Taj shine zaɓin addu'ar da suka daɗewa suna yiwa Ishmah...
Uncle Bello kuwa tsuke fuskarsa yayi tare da yin kici-kici da ita tare da tsare Taj ɗin da wani irin kallon tuhuma.
Yah Abubakar kuwa cikin matsanancin farin ciki ya gyara zamansa yana mai cigaba da kallon Taj tamkar ya samu TV tare da ci gaba dayi recording duk kalamansa.
Aransa yake jin cewa tabbas karshen matsalar Ishmah akan Aure yazo yanaji Aransa cewa lokacin da ƙanwarsa zata kasance da irin abokin zaman da suke mata fata yazo...
Cikin rauni gami da neman alfarma Taj ya kalli Sheikh Taju Bauchi tare da cewa.
“Yah Sheikh dan Allah kace wani abu da gaske ina matuƙar kaunar Ishmah fiye da tunanin mai tunani nayi dakon soyayyar Ishmah tsawon shekaru wanda a yau bazan iya ɓoyewa ba itace duniyata i love her more than More”.
Sheiky Taju Usman Bauchi kuwa wani irin sanyayyan Murmushi yake yi yana mai tuno wasu shekarun baya da yayi wata ƙuriciya akan uwar gidansa na farko daya mata wani irin soyayya da yake ji zai iya sadaukar mata da komai sai yanzu ya fahimci ashe nashi wasa ne ga wanda yake kallon yanzu da za'a ce ya ɗauki rayuwarsa ya bawa Ishmah TOH tabbas shi mai iya aikata hakan ne...
Taj kuwa ganin duk sunyi shiri basu ce komai bane yasa ya maida kallonsa kan Abba da har zuwa lokacin fuskarsa na ɗauke da Amintaccen Murmushi cikin karfafawa kansa gwiwa yace.
“Abbah nayi al'ƙawari zan zamewa Ishmah bango majinginar tsayuwarta, nayi al'ƙawari zan hana hawayen baƙin ciki kwaranya daga idanun Ishmah.
Abba nayi maka al'ƙawarin zan zamewa Ishmah hasken fitilar da zai haskaka zuciyarta da duniyar ta da farin ciki. Abbah nayi al'ƙawari zan kare Ishmah ga duk wani abin cutarwa.
Abbah nayi al'ƙawarin zan bawa Ishmah duk kan farin cikin da duk wata maɗaukakiyar ɗiya mace ke samu agidan mijinta. Abba nayi al'ƙawarin baza ku taba danasanin Aurena da Ishmah ba.
Abba nayi al'ƙawarin zansa Ishmah ta soni kafin in tabbatar da ita a matsayin matata”.
Ya ƙare mgnar cikin bayyanar matsananciyar soyayyar dake ɗawainiya da zuciyarsa da ruhinsa.
Kusan duk a tare suka juyi suka zuwaba Uncle
Bello idanu jin yana cewa.
“B......!
*Last free page daga yau na gama free pages na kab daga wannan Page ɗin ki biya ki karanta 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276, mutanen Niger kuma 1000fc ne kacal zaku turawa Mommy +22790899076 Jaka ɗaya kenan.*
Littafin INDA RAI na kiɗine karki karanta in baki biyaba dan Allah 1k ne ga account no in da zaki turo min kuɗinku 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, ku kuma mutane Niger ga number Mommy ita zakuyiwa magana ta gaya muku yadda ta inda zaku tura mata kuɗin 1000fc ne haka ɗaya kenan +22790899076
By
*GARKUWAR MARUBUTA*********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************