Complete Hausa Novels

Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 9 of 12

Page 9

MD da ya fara rud'ewa da yadda ya ga Fadila ya ce , "Ku kamata mu tafi Asibiti mana? " D'aya daga cikin likitocin ta ce " Nak'udarta ta riga ta kankama zata iya haihuwa a mota muna tafiya sai dai mu bari ta haihu a nan " Tana fadin haka ta kalli MD ta ce " Ku d'an bamu waje "

MD da Muhammad da Jamilu duk a tare suka fita.

Duk wani taimako da ya kamata sun ba Fadila anma bata haihu ba, hakan ya sa d'aya daga ciki ta fito ta zo ta samu MD ta ce" Ina jin fa sai dai mu tafi da ita Asibiti, saboda kan yaron bai gama yowa k'asa ba "

Muhammad da takaici ya cikasa ga haihuwa nan kusa amma tsabar rashin sanin aiki wai sai sun je da ita Asibiti. Muhammad kallan MD ya yi ya ce " Ku sanar da mijinta idan ya amince ni zan amshi haihuwarta " MD shiru ya yi yana kallan Jamilu , kamar mai son tuna wani abu sannan ya ce " babu damuwa ai taimako zakai zaka iya dubata "

Muhammad kallan likitocin ya yi ya ce " Ku muje in gwada muku wani abu "

Tare da Muhammad suka koma wajan Fadilar.

Muhammad koda ya duba ya ga halin da Fadila ke ciki bai tab'a taba fita ya yi ya ce ma MD " Bata da k'arfin da zata iya haihuwa da kanta sai dai ayi mata aiki ( theater) yanzu bari mu k'arasa Asibitin sai ka sanar da mai gidanta kafin nan "

Da taimakon Muhammad da na likitocin mata su ka sa Fadila a motar MD suka tafi.

Suna isa Asibitin aka shigar da Fadila theater room.

Muhammad suna kaita ya juya zai tafi MD ya kamo hannunshi da sauri ya ce " Kasan cewar muna saurine ya sa na kawota Asibitin nan , gaskiya daga gani kamar ma basu da kwararrun likitoci da kayan aiki , idan babu damuwa ka dubata mana, zan yi magana da d'aya daga cikin likitocin Asibitin"

Muhammad da gaba d'aya shima ya raina Asibitin dan daga gani ma kamar basu da wasu kayan aiki , hakan ya sa ya amince saboda hakan nan sai ya ji tausayin mai haihuwar ya ke.

Muhammad da kanshi ya shiga theater room nasu . Cikin kwarewarshi ya yi ma Fadila aiki ya zaro mata baby boy d'inta.

Sannan ita kuma ya yi mata al'lurai masu k'ara kuzarin jiki , sannan aka maidata d'akin hutu.

Lokacin da Muhammad ya fito da yaron da sunan ya ba MD shi sai ya ga baya nan sai Jamilu kad'ai . Muhammad da alamun mamaki ya kalli Jamilu ya ce " Har yanzu wani nata bai zo ba ? "

Jamilu ganin kokarin da Muhammad d'in ya yi akan Fadila , hakan ya sa ya ce " Ranka shi dad'e, bata da aure shi ne dalilin da kaga har yanzu babu wanda ya zo wajanta " Muhammad da mamaki ya kalli Jamilu jin furicinsa amma sai ya share ya ce, " Shi kenan, ni zan tafi " Jamilu da sauri ya ce " Ranka shi dad'e , tabbas Fadila zata so yi maka godiya, idan babu damuwa ka tsaya ta farka ko ka ban numberka in bata dan ta isar da sakon godiyarta gareka " Muhammad kai ya girgiza ya ce " Karka damu na yi mata dan Allah bana buk'atar godiyarta " Muhammad na fad'in haka ya juya zai tafi .

Jamilu da sauri ya kuma cewa " Ranka shi dade, nasan Fadila tana daga cikin halittun Allah musu godiya da son saka ma duk wanda ya taimaketa koda ko kad'anne tom bare kuma kai , tabbas nasan zata shi ga damuwa idan har akace ta rasa hanyar da zata isar da sak'on godiyarta a wajanka " Muhammad kai ya jinjina sannan ya ce " MD na da number ta" Ya na sanar da shi haka ya tafi.

Jamilu ko ganin Fadila zata farka ba kowa kusa da ita hakan ya sa ya yi tunanin zuwa ya sanar a gidansu.

Mahaifiyar Fadila suna zaune da Aisha suna fira da Jamilu ya yi sallama ya shigo. Bayan sun gaisa ne Jamilu ya ce " Mama , Fadila ce ta haihu bayan an yi mata theater an ciro yaron , yanzu haka tana nan Asibitin sawa , shi ne na zo in sanar ko Aisha ta je gudin karta farka ba kowa kusa da ita " Mahaifiyar Fadila wadda tun da Jamilu ya fara bayani kirjinta ke dukan uku-uku . Hannuta ta d'aga sama tana godiya ga Allah tana cewa a cikin rawar murya mai son fidda kuka " Alhamdulillah ! Allah na gode maka da ka amsa rok'ona kasa Fadila bata zubar min da wannan bak'in jinin anan ba " Mahaifiyar Fadila mai da kallanta ga Jamilu ta yi ta ce " Allah ya raya abun da ta haifa ya kuma bata lafiya , amma babu wanda zai je acikinmu " Mahaifiyar Fadila ta fad'i maganar tana goge hawayan da ke zubar mata.

Jamilu shiru ya yi dan ya rasa abun cewa ,sai zuwa can ya ce " Mama , dan Allah ki y....." ? Mahaifiyar Fadila d'aga ma Jamilu hannu ta yi ta ce " Jamilu , sai an jima ka sanar da ni haihu tom na yi mata addu'a da ita da abun da ta haifa , tom sai me ye kuma ya rage ? " Ta fad'i maganar da alamun ranta a b'ace yake.

Jamilu tashi ya yi bai kuma cewa komai ba.

Har ya tafi mahaifiyar Fadila ta ce " Ka sanar da ita katta dawo min nan bana buk'atar kara zama da ita "

Jamilu ganin idon mahaifiyar Fadila ya rufe ya sa bai k'ara cewa komai ba ya tashi ya tafi.

Aisha k'anwar Fadila goge hawayanta ta yi ta ce " Mama , ki yi hak'uri ki bar Aunty Fadila ta dawo nan ta zauna , idan kin koreta ina zata ? "

Mahaifiyar Fadila cikin kuka ta ce " Aisha , zuciyata ba zata iya jurewa ba inga Fadila da yaron shege tana raino , ina ba zan iya daure haka ba , ku yi hak'uri karku sake rok'ona wata alfarma akan Fadila ta zauna , idan kuma kun matsa sai dai ni in bar muku gidan "

Aisha shiru ta yi bata k'ara cewa komai ba.

B'angaran Fadila ko lokacin da ta farka ba kowa kusa da ita . D'akin ta bi da kallo, daga gani dai Asibiti ne hakan ya sa ta shafa cikinta da sauri sai jin shi ta yi wayan ba komai. Fadila cikin jin dad'i ta ce " Alhamdulillah . Allah kai ne abun godiya Allah na gode maka " Fadila ta fad'i maganar tana goge hawayan da ke zubar mata dan ita ta yi tunanin cikin da ke jikinta ya zube ne .
Fadila na a wannan halin ne d'aya daga cikin likitocin da suka dubata ta shigo ringume da jaririn yana kuka.

Fadila d'aga kai ta yi tana kallan Jaririn da ke a cikin tsunma a hannun likitar. Fadila cikin rud'ewa da ganin jaririn ta ce " Jaririn waye ? " Murmushi likitar ta yi ta ce " Jaririn da kika haifa kenan, amsarshi ki shayar da shi" Ta fad'i maganar tana d'ora ma Fadila jaririn akan k'afarta.

Fadila duk'ar da kai ta yi tana kuka sosai ta kasa magana. Likitar ko dama ta riga ta gama fahimtar Fadila babu aure ta haihu , hakan ya sa ta ce " Kukan me kuma kike yi bacin mai faruwa ta faru? Yanzu saidai ki rungumi yaronki gaba kuma kin kiyaye, dama abun da ake hangar muku kenan ake muku fad'a kuke ganin kamar takura muku ake yi "

Suna cikin haka ne Jamilu ya shigo . Jamilu zama ya yana yi ma Fadila ya jiki .

Fadila bata samu damar amsa mai ba saboda kukan da ta ke yi.

Haka Fadila ta yi ta kuka Wanda Jamiku ya kasa ce mata komai yana zaune yana sauraranta .

Jamilu d'akko jaririn ya yi jin yana kuka . Babu kalar jijjigar da bai yi ma jaririn ba amma ya dage sai kuka ya ke gaba d'aya ya cika Asibitin . Inda kukan jaririn ke k'ara tun jira Fadila tana k'ara nata kukan itama .

Jamilu gyaran murya ya yi sannan ya ce " Fadila , yanzu fa maganar kuka ta riga ta k'are , kukan nan babu wani magani da zai miki , ni shawarar da zan baki ki yi hak'uri ki bar sa ma kanki damuwa saboda tsoran wani ciwo.." Jamilu shiru ya yi saboda sugowar likita, likitar kallan Fadila ta yi ta ce " Bi ki ji baby na kuka ba ? Ki d'auke shi ki shayar da shi mana " Fadila ci gaba da kukanta ta yi ta kasa d'aukar jaririn.

Ana cikin haka ne MD ya shigo da flask babba a hannun shi da kuma ledar kayan tea.

MD da kan shi ya had'a ma Fadila tea ya mik'a mata. Kacan cewar Fadila na jin yunwa bata musa ba ta amsa ta sha.

MD d'aukar jaririn ya yi ya yi masa hud'u ba sannan ya kalli Jamilu ya ce " Nasa ma baby boy d'inmu Ahmad " Allah ya raya shi" Jamilu ya ce.

Fadila na gama shan tea d'in MD ya kalleta ya ce " Mu je in kaiki gida " Jamilu Kallan MD ya yi ya ce " MD , idan babu damuwa akwai maganar da nake son mu yi " MD tashi ya yi suka fita.

Bacin sun fita ne Jamilu ya kalli MD ya ce " MD , Fadila fa ba zaiyuwu ta koma gida da zama ba , saboda a halin yanzu mahaifiyarta tana cike da jin zugun zafin haihuwarta , gani nake idan zaiyuwu ka sama mata wani wajan ta zauna kafin nan da ta sakko "

Shiru MD ya yi baitanka ba sannan ya koma d'akin da Fadila ta ke ya ce ta shirya yanzu zai zo "

Shiru-shiru MD bai dawo ba , Jamilu kasa jurewa ya yi ya tafi gida ya ce mata yana zuwa.

D'aya daga cikin likitocin ko jin kukan jaririn ya yi yawa ya sa suka tursasa Fadila ta shayar da yaron.

MD ba shi ya dawo ba sai 10:40 PM dan Fadila ma har ta cire ran dawowar shi.

D'aya daga cikin likitocin ce ta rungume jaririn ta rakasu har motar MD sanna ta juy.

Fadila da mamaki ta bi MD da kallo ganin ya d'auke wata hanya daban maimakon hanyar gidansu. Hakan ya sa ta ce " MD ina zaka kai ni kuma? " MD bai tankama Fadila ba.

Daidai wani babban gida MD ya yi parking , Fadila dai kallan shi kawai take batace komai ba . MD kuma fita ya yi daga cikin motar ya bud'e get d'in gidan sannan ya dawo ya shiga da motar.

MD kallan Fadila ya yi ya ce " A nan gidan za ki ci gaba da zama har zuwa lokacin da Mama zata yi miki afuwa ki koma ku ci gaba da zama tare "

Fadila kallan MD ta yi wanda ke rungume da jaririn ta ce " Mama, ta hana in ci gaba da zama da ita ko ? " Ki yi hak'uri komai zai wuce watarana m...." Barka da zuwa ranka shi dad'e, har kun iso ? " Cewar wata karfaffar dattijuwar mata da ta fito daga cikin gidan ta katse maganar da MD ke yi.

MD jaririn hannun shi ya mik'a mata sannan ya ce " Ga mejegon nan ki bata duk watakulawa da ta kamata " In sha Allah , ranka shi dad'e "

MD mik'a matar nan jaririn ya yi ya kalli Fadila ya ce " Ni zan tafi Allah ya sawake " Fadila kai kawai ta iya d'ama mai ya juya ya tafi , ita kuma ta bi bayan matar nan suka shiga cikin gidan.

Three bedroom plate , ma sha Allah gidan ya yi kyau. Fadila zama za ta yi dattijuwar matar nan ta ce " A'a jikata, kar ki zauna mu je ki gasa jikinki " Matar nan goya jaririn ta yi sannan suka shiga bayin ta gaggasa Fadila suna fitowa ta kai Fadila har d'akin da yake mazaunin nata .

Fadila da mamaki ta bi dak'in da kallo dan komai sabo ne na d'akin , bud'e manyan jakunkunan da ta gani ta yi , d'aya cike take da kayan sawa kamar nata , d'aya kuma da kuma kayan jariri ne cike . Fadila na nan tsaye tana mamakin kayan, matar nan ta shigo da jug cike da kukun gyad'a ta kawo ma Fadila ta ce " Ga kunun gyad'a nan na yi miki ance sai zuwa gobe za'a fara baki abinci shima ba mai k'arfi ba in da an yi miki theater ne"

Fadila cikin sanyi ta ce " Tom, na gode "

Matar nan fita ta yi shima jaririn ta wankoshi tas kamar dai yadda ake ma jarirai sannan ta yi mai gashin cibi ta kawo ma Fadila shi ta fita.

Fadila tagumi ta yi ta tasa yaron gaba tana kallo tana kuka . Sai da ta yi kukanta ta gaji sannan ta kwantar da shi ta zuba kunun gyadan tasha ita ma ta kwanta , take barci b'arawo ya saceta.

Cikin dare jaririn ya tashi yana ta kuka amma kasancewar barci mai nauyi ya d'auki Fadila bata ji ba, sai Baba Lami ce ta ji ta shigo d'akin Fadilar .
Bubbugata ta yi ta tashi ta mik'a mata yaron sannan ta fita.

Fadila aduk lokacin da zata kallin yaron sai ta ji hawaye na zubar mata . Goge hawayan ta yi tana kallan yaron ta ce " Ina tausayinka sosai araina, ina tausaya maka yadda zaka tashi ka rayu babu uba , ina ji maka gorin da zaka rik'a fuskanta wajan jama'a , saidai ba zan gajiya ba wajan rok'a maka Allah ya nisantamu ni da kai ya kaimu duniyar da za mu rayu babu gorin zama'a acikinta " Fadila ta idasa maganar tana kuka sannan ta kwantar da yaron ta kwanta gefan shi , har aka kira Sallah barci ya gagari idon Fadila.

Washegari Baba Lami da wuri ta tashi ta yi ma su abin Kari , ta taimaka ma Fadila ta yi wanka ta wanke jaririn .

Fadila na zaune tana shan kunun gyadan da Baba Lami ta dama mata Kiran Jamilu ya shigo wayarta , bayan sun gaisa ne Fadila ta ce " Jamilu, MD ya taimakeni alokacin da nake tsananin naiman taimako Allah ya saka masa da alkairi " Jamilu "Ameen "ya ce ya k'ara da cewa " Ba MD kad'ai za ki gode mawa ba har da wanda ya yi miki theater , Fadila, Muhammad Sagir mai shadda kamar sunansa kenan ? Wanda ya halarci taron anniversary namu shi ya amshi haihuwarki , bawan Allah nan ya yi k'okari sosai haka muka tafi muka barshi , gaskiya ya yi miki k'ok'ari sosai " Fadila sai yanzu ta tuna da shi ta ce " Allah sarki har ya tafi ko ? " Eh , ya wuce " Jamilu ya bata amsa. Fadila cikin sanyi ta ce " Amma naso in yi masa godiya Allah ya saka masa da alkairi " Nima na rokeshi akan ko numbersa ya baki ki yi masa godiya amma ya k'i, da na dameshi ya ce ki amsa wajan MD "
Fadila ta ce " Aiko zan amsa gaskiya in yi masa godiya "

Bayan Fadila sun gama waya da Jamilu MD ta Kira ta rok'eshi ya bata number Wanda ya yi mata theater zata yi mai godiya .

Take MD ya tura mata number Muhammad.

Number na shigowa Fadila ta Kira shi har kira uku bai dauka ba, hakan ya sa ta tura mai text message kamar hak....✍🏻

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo musu na gyaran jiki a cikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.