Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 5 of 12
Page 5
Muhammad cikin tsananin furgici da tashin hankali ya ke kallan Maryam wadda ke kwance cikin jini an mata yankar rago.
Tsananin tashin hankali da furgici ya sa Muhammad ko kukan ma ya kasa yi.Zuwa ya yi yana ta girgiza gawar Maryam da ke kwance cikin jini.
Zuwa can kuma ya fad'i gefanta a sume.
Washegari alhaji Sagir ya yi ta sauraran zuwan Muhammad ya kai shi airport kamar yadda su ka yi zai zo ya kai shi amma shiru .Hakan ya sa ya kira Muhammad d'in a waya.
Alhaji Sagir sai da ya yi ma Muhammad kira hud'u amma bai d'auka ba, take hankalin Alhaji Sagir ya tashi.Kallan Hajiya Baturiya ya yi ya ce" Anya ko Muhammad lafiya na kira shi bai d'auka ba?" Tom, ka kira matarshi Mana" Cewar Hajiya Baturiya .
Alhaji Sagir Maryam ya Kira, itama dai ta b'angaranta haka ya yi ta Kira ba ta d'auka ba.Take jikin alhaji Sagir ya fara rawa ya ce "Ina ji ajikina babu lafiya na kira Muhammad bai d'aga ba haka Maryam ma "
Alhaji Sagir ya na maganar ya na tafiya da sunan za shi gidan Muhammad d'in.Hajiya Baturiya da sauri ta taro shi tana cewa "Alhaji, ka kwantar da hankakinka babu abin da zai samu Muhammad in sha Allah, bari in zo in yi driving d'inmu yadda ka rud'e haka ai ba zaka iya tuk'i ba"
Hajiya Baturiya ita ta tuk'asu duk da itama hankakin nata a tashe yake dan ta kusa yaddasu .
Suna tafiya a mota Alhaji Sagir ya na kuma Kiran numbobinsu amma shiru.
Suna zuwa Alhaji Sagir ya tambayi masu gadin cewar jiya ko sun ga dawowar Muhammad.Suka amsa mai da "Eh"
Ya ci gaba da cewa "Lafiya dai ko babu wani abu da ya faru?" Nan ma suka amsa mai da"Eh,ranka shi dade babu abin da ya faru wani ne ya ce maka wani abu ya faru ne ?"
Alhaji Sagir bai amsa musu ba ya nufi in da zai sadashi da k'ofar falon Muhammad d'in.
Saidai babu kalar bugun da ba su yi ba amma shiru.
Hajiya Baturiya na ganin haka tasa kuka cikin kuka take cewa "Na shiga uku sun kashe mana Muhammad" kukan Hajiya Baturiya ne ya sa d'aya daga cikin masu gadin ya k'araso yana tambayar " lafiya? "
Alhaji Sagir goge zufar da ke feso mai ya yi ya na nuna mai k'ofar falon alamun ya bud'e mai ita.
Babu kalar jijjigawar da bai yi ma kofar ba amma tak'i bud'uwa, saida ya Kira wani daga cikin su suka taru suka bud'e k'ofar da kyar.
Alhaji Sagir da Hajiya Baturiya atare suka shiga cikin hanzari.
Koda suka shiga bedroom d'in Muhammad lokaci d'aya tsoro,ranaza,tashin hankali ya mamaye zukatansu...
Hajiya Baturiya da gudu ta yi kan Muhammad da ke kwance babu alamun rai a jikin shi tana jijjigashi .
Alhaji Sagir gun Muhammad ya yi da niyyar amsarshi daga hannun Hajiya Baturiya jiri ya dibai ya yanke jiki ya fad'i, dan a tunanin shi Muhammad d'in ya mutu ne.
Mutum biyu daga cikin masu gadin gidan jin alamun kuka suka biyo bayan su Hajiya Baturiya suka shigo .Sosai suka rud'e ganin gawar Maryam kwance ak'asa an mata yankar rago.
D'aya daga cikin su ne ya yi ta maza ya kira office d'in su ya sanar da su.
Cikin lokaci motar folisawa ta iso gidan.
Atak'aice dai nan 'yan sanda su ka yi bincike- binciken su sannan suka d'auki gawar su ka yi asibiti da ita.
Duk wani bincike an gudanar akan gawar Maryam sannan aka yo gida da ita.
Haka aka yi zana'idar Maryama aka kaita gidanta na gaskiya. Har aka yi aka gama daga Alhaji Sagir har Muhammad basu san abin da ake ba saboda allurar barcin da likita ya yi musu.
Iyayan Maryam lokacin da idonsu ya yi tozali da gawar Maryam sun yi kuka sosai da danasanin had'a auran Maryam da Muhammad da su ka yi.
Muhammad ba shi ya farkaba sai gaf magriba, inda Alhaji Sagir har lokacin baisan wanda ke kanshi ba sai can cikin dare ya farka.
A wannan lokacin abin ya fi tab'a Alhaji Sagir dan har ya farka baya magana, saidai ya kalli mutane.
Muhammad na kwance kan shi a sama, yana tunanin me ke faruwa da rayuwar shi haka ne. Yana a wannan yanayin ne Hajiya Baturiya ta shigo. Kallan Muhammad ta yi tana shafa kan shi ta ce "Muhammad, kar ka sa kanka cikin tunani wani mugun ciwan ya zo ya kamaka, sannan ni kaina idan ina ganinka haka hankalina ba zai kwanta ba"
Muhammad tashi ya yi ya zauna yana kallan
Hajiya Baturiya ya ce "Mommyna, soda dama ba zafin ciwo ake ma kuka ba, tunanin halin da ake ciki ne .Sannan, mommy duk jarumtar Jarumu ba kowana rad'adi yake iya juremawa ba" Hajiya Baturiya kai ta d'aga ma Muhammad alamun haka ne, ya ci gaba da cewa "Mommyna, na rasa yadda zan lallashi kaina in yi hak'uri da rashin Hafsat a rayuwata. Amma da na yi wani nazari sai naga ko ba wannan lokacin ba Hafsat zata mutu watarana,sai na yi tunanin fara ba kaina hak'uri in amshi Maryam a matsayin mata, saidai ina cikin tunanin hakan ne zuciyata na gaf da amince min da ita suka kasheta suka rabani da ita itama" Muhammad shiru ya yi kamar mai tunani ko mai son tuna wani abu, sannan ya ce"Mommy! Su waye ne? Waye ya kashe su? Me su kai musu ? Shi nake son san..." Hajiya Baturiya rufe bakin Muhammad ta yi tana kuka, ta ce "Ka yi shiru Muhammad, karka sa kanka cikin wata damuwar, koda ace abin da mahaifinka ya mallaka zai kare ne sai an binciko wa inda suka aika haka, ni na san haka. Ka tashi mu je ka ga mahaifinka abun nashi ya fara bani tsoro, baya magana tun da ya farka na yi na yi ya k'i yin magana"
Muhammad cikin daure yadda yake ji da tsoran karya rasa mahaifin shi ya nufi bayan Hajiya Baturiya suka yi falon Daddynshi.
Kwance ya samu mahaifin nasa kansa a sama kamar mai k'okarin tuno wani abun da ya shege mai .
Muhammad cikin k'arfin hali ya kalli mahaifinshi ya ce"Daddy, ka tashi ka ci abinci plz"Alhaji Sagir da sauri ya mai da kallan shi kan Muhammad .
Ya dad'e yana kallan Muhammad d'in sannan ya ce "Muhammad, ka ci abinci kai ?" Kai Muhammad ya d'aga mai.
Muhammed Hajiya Baturiya ya sa ta kawo mai tea ya ba Alhaji Sagir. Kad'an dai su ka samu ya sha.
BAYAN SATI D'AYA DA RASUWAR MARYAM .
Ma sha Allah. Yanzu Alhaji Sagir da Muhammad sun fara kwantar da hankalinsu.
Bincike ko har masu gadin gidan an kama amma babu wata hujja ko d'aya da aka samu daga kan rasuwar Hafsat har ta Maryam.
KADUNA GARIN GWAMNA.
Yau Sati d'aya da kenan da komawar Fadila aiki.Saidai kullum cikin takurar Oganta ta ke.Dan tunda Jamilu ya sanar da shi ta amince da soyayyarshi tun daga nan ya fara ta kurata. Haka dai Fadila ke daurewa ta na biye mai suna fira badan tana jin dad'in firar da shi ba.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya Fadila kullum sai ta je aiki.Mahaifinta kuma babu tasa dole ya kauda kai da surutan mutane.
Babu laifi yanzu suna rayuwarsu da sauk'i .Dan kullum Fadila ta tashi aiki sai gogannata ya bata kud'in mashin din zuwa gida, tom da sune take kaiwa su yi cefane.
WATA UKU KENAN DA KOMAWAR FADILA AIKI.
Yanzu Fadila ta saki jikinta sosai da Ogan nata duk da bata wani son shi ta fara tunanin auranshi, dan wa'adin da mahaifinta ya bata yana gaf da cika.Kuma har yanzu mahaifinta kullum cikin k'ara tunatar da ita yake akan yana nan fa akan bakarshi daga wa'adin da ya sa mata ya cika ko ta yi aure ko kuma ta bar mai gida.Wannan ya sa ta fara sakar ma ogan nata fuska, idan ta ga ba hali ta yi hak'uri ta aure shi.
Yanzu har gidan su Fadila sun san soyayyarta da ogan nata.
Yau Fadila bayan ta dawo aiki, mahaifinta ya kirata .Ya dad'e ya na kallan Fadila kamar mai neman wani abu a jikinta, sai zuwa can ya ce"Fadila, yau saura wata biyu wa'adin da na baki ya cika, amma har yanzu bikice min komai ba?"
Fadila shiru ta yi gabanta na fad'uwa.Haka dai ta daure ta ce"Eh, Baba ban manta ba"Ya yi kyau"Mahaifin Fadila ya ce.
Fadila ranar haka ta kusan kwana tana tunanin mafita, abu d'aya da ta sani shi ne bata son Ogan nata, saidai za ta yi hak'uri haka nan ta aure shi in da bata da wata mafita.Haka Fadila ta yanke ma kanta auran ogan nata ba wai dan tana son shi ba sai dan mahaifinta da ya hura mata wuta.
Washegari Fadila ko da taje aiki zama ta yi shiru, kallo d'aya za ka yi mata ka gane tana cikin damuwa.
Jamilu abokin aikin Fadila, da zuwan shi kenan cikin tsokanar Fadila ganin ta yi nisa a tunani ya ce"Alamar tambaya ta na ga mai yawaita tunani, musaman in ya shiga halin soyayyar zamani , ya...." Kallan da Fadila ta yi ma Jamilu ne ya sa ya yi shiru yana dariya ya ce"Ko za ki cemin wannan shurun naki ba soyayya ba ce sila?" Ba ita bace hasali ma k'i ne sila"
Jamilu zama ya yi ya ce"To fa, ba ni in Sha?"Fadila cikin sanyi kamar za ta yi kuka ta ce"Jamilu zan auri MD ba dan ina son sa ba saidan banda wata madafa"Jamilu ko da har kullum bai ga wani aibun MD d'in ba ya ce"Fadila, ki kwantar da hankalinki MD ba shi da wata matsala, sannan shi d'in masoyi ne gareki na hak'ik'a"
Haka dai Jamilu ya yi taba Fadila kwarin gwiwar auran MD d'in.
Fadila bacin ta tashi aiki kamar kullum sai sun tab'a hira da Ogan nata sannan take tafita gida.Tom yau acikin firar ne take sanar da shi ta bashi dama koda yaushe zai iya aikowa gidansu.
Murnar da MD ya yi kad'ai ta k'ara tabbatar ma Fadila da son da yake mata.
Cikin tsantsar farincikin da ya kasa b'oyewa ya kalli Fadila ya ce"Zan iya aikowa gobe kenan?" Kai Fadila girgiza mai ta ce "Gobe Baba zai yi tafiya saidai in ya dawo "
Haka Fadila suka rabo da MD d'in akan daga mahaifinta ya dawo daga tafiyar da zai yi za su aiko.
Washegari mahaifin Fadila da wuri ya shirya tafiyar da zai yi zuwa Gombe.
Fadila da mahaifiyarta su ka yi mai rakiya har tasha. Sai da motarsu ta tashi sannan suka dawo, in da Fadila ta nufi wajan aiki mahaifiyarta kuma ta yo gida.
Satin mahaifin Fadila d'aya ya dawo.
Yau Fadila bayan ta tashi daga aiki ne MD ya rakota kamar yadda ya saba ya kalleta ya ce"My Fadila, har yanzu Baba bai dawo ba?" Fadila ji tai bata buk'atar sanar da shi yanzu in da tasan maganar aikawa zai mata, hakan ya sa ta ce " Bai dawo ba "
Kallanta ya yi ya ce "Sai yaushe kenan?" Duk lokacin da ya dawo zan sanar da kai" Fadila ta ce atak'aice.
Sai da Fadila ta samu keke-napep ta hau sannan MD ya juya ya tafi.
ADAMAWA STATE
BAYAN WATA UKU DA RASUWAR MARYAM.
Ki manin wata uku kenan da rasuwar Maryam. Yanzu Muhammad ya dangana har ya koma bakin aikin shi.
Alhaji Sagir zaune yana danna waya Hajiya Baturiya ta kallai ta ce "Alhaji, ban ji dadi ba da ka hana Jibirin dawowa, yanzu ace Muhammad ya yi aure har biyu duk ba matan amma ace be zo ba" Alhaji Sagir murmushi ya yi ya ce"Tom ba gashi ba yanzu ya gama karatunshi lafiya lau, ko da ya zo me zai mai? "Alhaji Sagir suna cikin haka ne Muhammad da ya je airport d'akko Jibirin suka shigo tare bakunansu d'auke da sallama.
Alhaji Sagir cikin washe baki ya ke cewa"Ka ga mutanan Turai, jibirin ka ganka ko har ka fara komawa kalarsu"Gaba d'ayansu dariya su ka yi sanna Jibirin ya zauna suka gaggaisa da iyayan nasa.
Alhaji Sagir kallan Jibirin ya yi ya ce"Jibirin ku je ka ci abinci ka ga isowarka kenan.
Jibirin tare da Muhammad suka ci abincin, dama kuma komai nasu tare su ke yi.
Dawowar Jibirin tasa Muhammad ya kuma sakin ranshi sosai ya fara mantawa da duk wata damuwarshi.
Alhaji Sagir zaune da su Muhammad suna fira, kamar yadda suka saba kusan duk dare in Alhaji Sagir na gari.Alhaji Sagir ya kalli Muhammad ya ce"Muhammad ina so in baku shawara kai da Jibirin, duk kanku ya kamata ace duk kun yi aure, duk da dai kai Muhammad ka yi amma Allah da ikon shi ga abun da ya faru, amma duk da haka hakan ba zai zama hujjar da zaka rik'e kace wai ba za kai aure ba, gara ma Jibirin k'aninka ne "
Muhammad kamar zai yi kuka ya d'ago yana kallan mahaifin nashi ya ce"Daddy, dama za ka kuma iya yi min maganar aure? ,Daddy, na za ci kai kanka ka hak'ura da wannan batun, wa kake gani yanzu zai iya ban auran 'yarsa ma? " Muhammad ya idasa maganar kamar zai fasa ihu.
Jibirin cikin tausaya ma Muhammad ya dafa kafad'ar shi ya ce"Ni na yi imanin babu wadda za ka je naiman auranta ta k'i Muhammad, kuma ta bakin Daddy haka ba hujja ba ce ka jaraba naima ka gani mana"
Muhammad shiru ya yi baitanka musu ba.
Alhaji Sagir ya ce "Muhammad, ka yi shiru?" Muhammad cikin gatse dan ya san babu ma wanda za su k'ara ba shi aure ya ce"Daddy, idan an samu wadda zata iya aure na shi kenan babu damuwa na amince"
Jibirin kallan Muhammad ya yi ya ce"Amma kasan Laila na sonka? "
Muhammad da ya tabbatar ma kanshi babu wata wadda zata aure shi ya ce"Idan ta amince babu damuwa Jibirin"
Alhaji Sagir kallan Jibirin ya yi ya ce"Wacece ita yarinyar? " Yarinyar Mansur Inuwa ce" Shiru mahaifin Muhammad ya yi sannan ya ce"Shi kenan ka yi min magana da yarinyar tukun idan ta amince"
Da daddre Jibirin ya je wajan Laila ya sanar da ita abin da ke tafe da shi.Bud'ar bakinta sai cewa ta yi "Allah ya tsareni, wato in je nima a tsotse jinina kamar yadda aka yi ma wa in can" Haka dai ta yayyab'a ma Jibirin magana ta tafi ta bar shi anan.
Jibirin cikin damuwa ya sanar da Alhaji Sagir yadda su ka yi da Lailar.
Muhammad ko ko da ya ji basu k'ara tada mai maganar ba ya san sun je ba a dace ba.
Tun daga ranar mahaifin Muhammad bai kuma yi ma Muhammad zancan aure ba.
KADUNA GARIN GWAMNA
Fadila kullum tana so ta sanar da MD akan ya aiko gidansu kafin mahaifinta ya kuma yi mata maganar, amma zuciyarta ta k'i aminta da shi a matsayin miji a gareta.
Yau dai Fadila ta yi alk'awarin sanar da MD d'in ganin saura sati biyu wa'adin da mahaifinta ya bata ya cika, duk da yanzu taga gaba d'aya MD d'in ya fara jan baya da ita ba kamar da ba.
Yau ne ranar da Fadila ta yi k'udirin sanar da MD ya aiko gidansu.Saidai ko da taje aiki yau da ta gaida shi sama-sama ya amsa gaisuwarta daga nan bai kuma saurarta ba ya ci gaba da abin da yake.Hakan sosai ya ba Fadila mamaki, amma saita bar hakan akan k'ila jamai ran da take yi ne kullum tace mai yau tace gobe.
Fadila cikin sanyi da yanayin yarda ya yi mata ta ce"Na san ni mai laifice a wajanka, amma ya wuce, ina mai yi maka albishir d'in duk lokacin da ka shirya koda ko yaune ka aiko wajan mahaifina"
MD ya dad'e yana kallan Fadila bayan ta kai bayananta, sannan ya kauda kan shi ya ce"Fadila, ina miki fatan Alkairi Allah ya baki miji na gari, babu maganar aure yanzu tsakanina da ke sai zumuminci"
Fadila cikin tsananin mamakin take kallan shi, so take ta yi magana ma amma ta kasa. Sai da ya furta mata haka fargaba ta ci kata idan mahaifinta ya b'ullo mata wuta ya za ta yi.
Fadila cikin murmushin yak'e ta ce"Sir, ko na yi maka wani laifin ne?" Kallanta ta ya yi ya ce"A'a, biki min komai ba, son ne kawai ya fita araina, amma zumincinmu na..."
Fadila bata saurareshi ba ta yi tafiyarta.
Fadila cikin sanyi ta shiga Office dinsu. Jamilu da kallo d'aya ya yi ma Fadila ya fahimci tana cikin damuwa, dan ita Allah ya halicce ta cikin wa inda ba sa iya b'oye damuwarsu.
Jamilu cikin tsokanar Fadila, ya ce"Kowattab'aki zo ki gaya min, in dai a kanki ne ba a iya min, nasha aradu kanki nasha Yasin, akanki zana aika mutum yanzu ko da ko MD ne" Fadila murmushi ta yi ta ce"MD ne ya tab'a ni Jamilu, bana son MD amma abun mamaki wai dan MD yace ya fasa aurena ka ji yarda na ji kuwa?" Jamilu cike da mamaki da al'ajabi ya ke bin Fadila da kallo ya ce"Fadila, ban fahimta ba? Na ji kin zo min da wata sabuwar tatsuniya ne"
Shiru Fadila ta yi tana kallan Jamilu ,sannan ta ce"Na yi mamaki sosai da jin furicin MD dama kuma kwana biyu ya fara sauya min" Jamilu shiru ya yi sannan ya ce " Tabbas wannan abun mamaki ne, da ace bansan halinki ba da sai in ce k'ila ya samu abin da yake so ne, to amma ni d'in nasan wacece Fadila" Cewar Jamilu da al'ajabi ya isai.
Atak'aice dai Fadila haka ta koma gida tana jinta duk babu dad'i. Abu d'aya yake damunta shi ne mahaifinta yana gaf da ya yi mata magana ga shi ta gama sakin jiki da MD d'in akan shi zata aura duk da ba wai dan tana son shi ba.
BAYAN SATI D'AYA
Fadila ta tashi yau bata jin dad'in jikinta haka nan dai taje aiki.Koda ta je bayan sun gama gabatar da Shirin da take ne ta kalli Jamilu ta ce"Jamilu, bari in yi ma MD magana gida zani bani da lafiya" Fadila tana fad'in maganar ta tashi da sunan tafiya, saidai sakamakon jirrin da take gani tana tashi ta yanke jiki ta fad'iâœÂðŸÂ»
📚 FADEELAH 📚
ðŸâ€â€Ã°Å¸â€œÅ¡
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
💪ðŸÂ»J.A.W 💪ðŸÂ»
Naga
Fadila Sani Bakori.
SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH .
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.