Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 8 of 8
Page1ï¸âƒ£5ï¸âƒ£âž¡ï¸1ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
*BEELAL*
Duk yadda yake zaga wurin ko sau ɗaya bai buɗe baki da sunan yin bara ba. Kawai zagaya wuraren yake amma ko kaɗan ya kasa buɗe baki ya yi bara, ga yunwa bashi da karazana ko kaɗan, dan gani yake ma tuƙin keken ma kamar ba zai iya ba.
Wanda Allah ya sa yana miƙa masa kuɗi ko a bashi abinci.
Tun da suka ƙaraso wajen da yake suka tsaya daga can gefe, Idrisu sai harara yake aika masa amma Beelal bai ma san suna yi ba, hankalinsa ba a kan su ba yake, ya tafi tunanin Mamarsa. Idrisun ne ya cigaba da tsayuwa a wajen shi kuma Imran ya gewaya a hankali yadda mutane ba za su lura ba ya je wajen Beelal ɗin cikin ɗaure fuska ya kalli Beelal ɗin ya ce
"Dalla ka wani zo ka tsaya a wuri É—aya kai baka yi barar ba ka tsaya sai kallon mutane kake kamar ka ga hoto"
"Ina yi mana" Cewar Beelal da sai lokacin ya lura da Imran.
"A gidan uban wa kake yi, ka ɗauka duk ba ma ganinka to duk abin da kake muna hangoka, bani abin da aka samu" Ya faɗa yana miƙa wa Beelal ɗin hannu. Ledar ya miƙa masa tare da sanya hannu a aljihunsa ya ɗakko kuɗin ya miƙa masa,lissafawa ya yi, ya ga ɗari uku da arba'in ne sai da ya duba ya ga babu wanda ya lura da su ya ce
"Wallahi ka kutsa cikin mutane ka ware murya ka yi bara ta kirki ka samo mana abubuwa, dan wannan in'innar ma sai kana danneta saboda ake fahimtar bara kake, dan na ga alama in'innar za ta sa ake kasa gane bara kake ko roƙo, ko kuma waƙa, murya ce gabaɗaya a dagule" Imran ya faɗa yana yiwa Beelal wani kallo tare da miƙa masa wata ledar da zai cigaba da zuba abincin in ya samu, juyawa ya yi, ya bar wajen, da kallo kawai Beelal ya bishi yana jinjina rashin tausayi da imani irin na Babansa da abokinsa su basa ma ta shi kawai ta kansu suke ya samo abincin amma sai hannu ya suɗe sun karɓe za su je su cinye dan zalunci.
Imran na ƙarasawa inda Idrisu yake suka bar wajen suka koma ƙasan wata bishiya kusa sa wata mota suka zauna suka cinye abincin suka sayi pure water suka sha abinsu.
"Gaskiya abokina ba ƙaramar dibara ka mana ba da ka taho mana wannan annakasun" Cewar Imran yana cilla ledar pure watern da ya gama sha, sama ya bugata da ƙafarsa ta yi gefe guda.
"Ai nake faÉ—a maka sai da na yi dogon tunani kafin na yanke hukuncin" Idrisu ya faÉ—a yana wani washe baki jin abokinsa ya yabe shi da abin da ya yi.
"Aikuwa dai ka ceto mu daga yunwa da rashin kuÉ—i, ji fa yanzu ba ko asinmu amma mun ci mun sha har da kuÉ—in kashewa gashi za mu raba, dan ma dai na ga kamar har yanzu bai saki jikinsa ba yana É—ari-É—ari da abin da za mu samu ma ya fi haka"
"Rabu da shi zai ware ne, yanzu dan farko ne amma idan ya ga dole uwar naƙi dole ya rage dantse ya samo mana ko dan ya ci shi ma, dan idan bai samo da yawa ba yana ji yana gani za mu cinye ɗan wanda ya samo ɗin" Idrisu ya faɗa yana dariyar ƙeta.
"Kana lokacinka nawan" Cewar Imran yana miƙawa Idrisu hannu suka tafa.
Beelal kuwa ganin sun karɓe abincin da kuɗin sai ya rasa ma ya zai yi dan yunwa yake ji kamar me gashi kuma la'asar ta yi sosai, haka ya shiga can ciki yana bin wurin sana'ar mutane yana tsayawa wani wajen a koreshi, wani wajen a tambayeshi mai zai siya, idan ya ce sadaka yake nema sai a hantareshi a ce barar ce kuma ba za kake yi da bakinka ba sai ka tsayawa mutane zoƙoƙo. Hakan ne ya sanya Beelal ɗin ya cigaba da tafiya sai dai yana bara saboda ya ga ba a bashi sadaka saboda ba ya bara dan haka babu yadda ya iya ba dan ransa ya so ba haka ya shiga faɗin.
"A taimakawa almajiri da sadaka, almajiri yana bara" Amma duk lokacin da zai ambaci sadaka sai ya ji wata ƙwalla ta kawo idanunsa saboda ya san dai ragas yake Allah bai masa nakasar da zai ke yin bara ba.
Cikin iko da hikima ta ubangiji sai kawai yake ta samun sadaka, dan sai ya ga jama'a ma kamar shi kaÉ—ai suke baiwa sadakar saboda idan ya ce
"A taimakawa almajiri da sadaka, almajiri yana bara"
Sai kuma ya ƙara da cewa.
"Duk wanda ya bayar domin Allah, Allah zai mayar masa fiye da abin da ya bada" Wannan hikimar d ya sanya a cikin barar tasa ita ce ta sanya mutane ko basu da niyyar bashi sadakar sai su bashi, shi kuma wannan hikimar maganar ya koya ne a wajen Mamarsa, saboda idan suna da ishashshen abin da za su ci, kuma sai almajiri ya yi bara to tana kiran almajirin ne ta bashi ko da a cikin wanda za ta ci ne, idan Beelal É—in ya ce
"Mama ya kika bayar da abincin da za ki ci kika bar É—an kaÉ—an?" Sai ta ce masa
"Beela ai duk wanda ya bayar domin Allah to Allah zai mayar masa fiye da abin da ya bada, ka ga kenan idan na bai wa almajiri sai Allah mu ma ya ƙara kawo mana ta wata hanyar da bamu yi zato ba" Wannan abin da take faɗa masa ne yasa yake saka hikimar maganar tata cikin barar tashi sai gashi kuma hakan ya sanya yana samun sadaka, lallai abin da uwa za ta koya wa ƴaƴanta ba iya lokacin zai musu amfani ba har da bayan wasu lokutan ma dan yanzu gashi Beelal ya yi amfani da abin da ya koya daga mahaifiyarsa ya samu hanyar samun bara cikin sauƙi.Tabbas tarbiya ba ƙaramin makami bane mai kyau da uwa take bai wa ƴaƴanta wanda wannan makamin zai amfane su duniya da lahira, mahaifya ta gari idan ta bai wa ƴaƴanta tarbiya mai kyau haƙiƙa tana jifan tsuntsu ne da dutse biyu, tarbiyar za ta amfane su duniya ne da kuma lahira.
Sai da ya ji an fara kiran sallar magriba ya fara tuƙo keken yana fitowa daga cikin jama'a, yana ta kallon yadda mata inyamurai ke ɗakko ƙaton baho ko daro a kansu cike da kaya, tabbas ya jinjina musu dan ya san hausawan mu ba za su yi haka ba. Yana fitowa ya hangi wurin da ya ga su Imran suna tsaye amma basa wurin hakan ya sanya ya rinƙa kutsa mutane ya samu ya fito ya samu gefe guda, cikin abincin da ya samu, ya sanya hannu ya fara ci, sai da ya ɗan ci amma ba sosai ba dan yana tsoron kar ya ci ya ƙoshi su gane ya ci su masa wani abun.
Ledar ya ƙulle ya rataye ta a jikin hannun keken nasa, masallacin da ke kusa wanda ya ji ana kiran sallah ya nufa yana zuwa ya ajiye keken a gefe guda, aikuwa sai da ya faki idanun mutane ya tashi tsaye daga kan keken gudun kar a ganshi da ƙafarsa a ce ya hau keken guragu mutane ba a iya musu duk da ma dai akwai nakasa a jikinsa amma ba wacce zai hau keken guragu ba. Wajen famfuna ya nufa ya yi alwala ya shiga masallacin sai da ya yi sallar la'asar dan bai yi sallah ba amma Idrisu bai damu da ya ce ya yi sallah ba ko abincin da zai sanya a cikinsa, ko dan shi ma Idrisun sallar ba damunsu ta yi ba. Ya idar da sallar kenan sai aka tada sallar magriba dan dama wa'azi aka gama a masallacin shi ne kuma za a yi sallah.
Bayan an idar da sallar ya yi addu'arsa sai ya fito ya ƙarasa wajen keken, idanun mutanen dai ya faka ya hau keken ya baro cikin masallacin, yana fitowa kwa ya hango Idrisu da Imran sai sintiri suke a wajen suna nemansa, hangoshi da suka yi, ya fito daga masallacin cikin hanzari suka nufo shi suna wani zare
"Kai gurgun mage ina ka tafi ka sa sai duba ka muke a wajen nan?" Idrisu ya jefa masa tambayar yana kallon ledar da Beelal É—in ya rataye a jikin keken wacce abinci ne da yawa a ciki.
"Masallaci na shiga na yi sallah, ko la'asar ban yi ba"
"To sallau, wato kai ga mai sallah to mu nan ko azahar bamu yi ba" Imran ya faÉ—a yana kallonsa.
Shiru ya yi shi dai Beelal bai ce komai ba dan shi in banda larura ma babu yadda za a yi ya haÉ—a salloli amma su gasu manya da su wai ko azahar basu yi ba kuma gashi yanzu har an yi magariba, kuma ko alamar yin niyya babu a tare da su.
"Kawo kuÉ—in" Cewar Idrisu.
Hannu ya sanya a aljihun nasa ya fito da duka kuÉ—in dan a farar leda ma ya sanya sannan ya sa a a ljihun. Su duka baki suka washe ganin har da Æ´an É—ari biyu guda biyu a ciki sauran kuma canjuna ne, lissafawa É—ari takwas ne da naira ashirin. Hannu Imran ya sanya a cire ledar abincin ya ce.
"Miƙo hannunka mu san maka abincin"
Hannu Beelal ya haɗe duka biyun Imran ya zuba masa abincin, Idrisu naira ashirin ɗin ta saman kuɗin ya miƙa wa Beelal ya ce.
"Karɓi wannan in ka tafi hanya ko za ka siyi wani abu ka ƙara" Abincin hannun nasa ya cinye ya karɓi ashirin ɗin.
"Ai dai ka ga inda muka biyo a tahowa, waccen hanyar inda da wancan motar yashin take tsaye, ka bi nan ka koma shagon namu, mu akwai inda za mu je" Cewar Imran yana kallon Beelal.
"To" Kawai Beelal ya ce ya juya kan keken nasa ya tafi, su ma suka kama gabansu. Wata mai soya dankalin hausa ya bai wa ashirin É—in ita ma da ta tausaya masa ganinshi a kan keken gurragu kuma ga in'inna kawai sai ta cika masa farar leda.
"Duk na ashirin É—in ne wannan" Ya faÉ—a da mamaki.
"A'a sadaka na baka sauran" Mai dankalin ta faɗa tana murmushi dan sai ta ji ya birgeta ganinshi mai nakasa kuma mabuƙaci amma kuma har yana buƙatar halal ɗinsa kawai.
"Allah karɓa, ai na ɗauka ko baki lissafa dai dai bane"
"Ina sane" Ta faɗa tana zubawa wani fa ya sayi dankalin a baƙar leda.
Haka ya kama hanyar da suka biyo da su Imran yake tafiya da yake ma unguwar duk jama'a ne sai ya zama ko ina ma akwai mutane ga haske tarr kamar safiya, cikin ikon Allah sai gashi ya gane shagon, a buɗe ya ga ƙofar lokacin da ya zo, keken ya ajiye yana jin bayasa duk ya ƙage ga mazaunansa duk ciwo suke saboda zaman kan ƙarfen keken. Daga bakin ƙofa ya tsaya yana yin sallama hannunsa riƙe da ledar dankalinsa. Amimulla da ke ciki jin muryar Beelal sai ya tashi da sauri ya fito aikuwa yana fitowa ya ga Beelal ɗin ne wani tausayin yaron ne ya ji ya kama shi hakan ya sanya ya amsa masa sallamar tare da miƙa hannu ya kamo Beelal ɗin ganin shi kaɗai ne babu iyeyen gidan nasa wato su Imran
09030283375
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
*BEELAL*
💦💦💦💦💦💦💦
*BOOK 2*
FCW
Book 1 free
Book 2 paid 300
Mai buƙata zai biya ta asusun Fa'iza abubakar unity bank
0020281885
Shaidar biya ta 09030283375
Last free page 1ï¸âƒ£7ï¸âƒ£âž¡ï¸1ï¸âƒ£8ï¸âƒ£
*HAMEEDA*
Gabaɗaya ta yi narai-narai da ido za ta yi kuka, sai dai tuna furucin Musty a kan yankan da yace zai mata sai ta fasa sakin kukan, hannu biyu ta sanya ta dafe pant ɗinta, shi kuma ya shiga kiciniyar rabata dashi, amma duk yadda ya so ya cire pant ɗin abin ya faskara dan dama da ya haɗe hannayen nata ya riƙe ƙafafunta da take haurawa tana bangajarsa da su hakan ya sanya shi sakin hannayen nata ya maida hankali wajen cire mata wandon.
Hakan ne ya bata damar riƙe pant ɗin nata gamgam taƙi sakawa, dan duk da ƙarancin shekarunta amma bata manta yadda Ummarta ke nuna mata kar ta yadda wani ya cire mata wando bare har ya taɓa mata wajen fitsarinta, da yake komai yana zama ne a ƙwalƙwalwar yaro shi yasa bata manta da hakan ba duk da cewar mahaifiyar tata bata duniya amma tarbiyar da ta bata tana nan zaune daram a ƙwalƙwalwarta, shi yasa ake son kar ka raina ƙanƙantar yaro ka ce wai sai ya ƙara girma zan koya masa abu kaza da kaza shi yaro abu yana zama a kwanyarsa fiye da yadda zai zauna a kwanyar babba. Dan abu a kwanyar yaro tamkar rubutu ne a kan dutse baya goguwa saɓanin abu a kwanyar babba da yake kamar rubutu ne a kan ruwa gogewa yake.
Ganin ƙaramar yarinya na son wasa fa damarsa da kuma lokacinsa sai ya sanya mugun ƙarfi ya fisgi wandon nata daga gefe guda cikin nasara kuwa sai pant ɗin ya yage daga kan ɗinki, amma dan ƙarfin hali irin na Hameeda sai ta ƙara riƙe saitin da ya yaga mata, cikin fusata ya sanya hannu ya hankaɗata ta faɗi reran a kan gadon, haka ya haye kan gadon jikinsa babu kaya sai ƙaramin wando dan ya sanya a ransa a yau sai ya biya buƙatarsa da yarinyar dan shi babu abin da ya fi masa sama da ya kusanci ƙananan yara ya lalata musu rayuwa babu ruwansa su yi rai ko su mutu.
"Mustapha, Mustapha,Mustapha" Musty ya jiyo muryar Mom tana ƙwala masa kira daga falo kamar ta ari baki, wani irin miƙewa ya yi tare da sakkowa daga kan gadon cikin ɗaga murya ya shiga amsawa a lokaci guda kuma yana ƙoƙarin maida kayansa. Hameeda zaune ta tashi a kan gadon tare da kama wurin da ya yaga mata wandon ta shiga ƙullewa ta ja rigar tana rarraba ido, yana gama maida kayansa hakan ya yi dai dai da kama handle ɗin ƙofar da Mom ta yi domin buɗewa jin ƙofar a rufe sai ta shiga nocking tana kiran sunan Musty.
Musty kuwa gabaɗaya hankalinsa a tashe yake bashi da wata nutsuwa ko ƙwayar zarra a yanzu gabaɗaya hankalinsa ya ɗugunzuma zuwa maɓoyar da zai sanya Hameeda a ciki, waige-waige ya shiga yi har dai ya samu wurin da ya ɓoyewa ta tare da zare mata ido ya mata gargaɗi a kan kar ta kuskura ko tari ta yi bare magana ko kuma ta yi yunƙurin fitowa. Sai da ya murje idanunsa suka yi ɗan ja sannan ya buɗe ƙofar yana wani yamutsa fuska irin ta mai bacci, Mom kuwa gadan -gadan ta nufi shigowa ɗakin sai matsawa ya yi ya bata hanya ta wuce ciki shi ma ya mara mata baya.
A jikin mudubi ta ɗan jingina da katakon ta zubawa Musty ido da ya ƙaraso yana sakin wata uwar hamma ta mai bacci amma baccin ƙarya, ya samu bakin gadon ya zauna yana fuskantar Mom ɗin.
"Wai yaushe ma ka dawo? Ina aiken da na maka? Kawai sai motarka na hango kuma ashe har kana nan kana bacci"
"Kaina ke mini ciwo Mom ina dawo wa ban samu ƙarasawa ɓangarenki ba na zo na kwanta dan in ɗan ji sauƙi shi ne bacci ya samu nasarar ɗibana" Cewar Musty cikin muryarsa ta baccin ƙaryar da ya ƙirƙira.
"Ayya sannu ni fa in ce ashe dai akwai abin da ke damunka shi yasa baka je ka faÉ—a min aiken ba"
"Eh, eh, eh" Cewar Musty da ke ƙoƙarin bai wa Mom amsar sai dai haɗa ido da hijabin Hameeda da ya yi wanda ke yashe a ƙasan ɗakin ya sanya gabansa mugun faɗuwa har hakan ya sa maganar da yake son yi ta zama inda-inda
shi bai san dalilin da yasa yarinyar bata ɗauke wannan ƙazamin hijabin nata ba, kuma shi ma da yake ba a nutse yake ba burinsa kawai ya ɓoyeta sai bai lura da hijabin ba, gashi tana neman ta jaza masa jaraba a kansa, dan idan Mom ta ga hijabin ai asirinsa ya gama tonuwa . Cikin sauri ya faki idon Mom ya sanya ƙafarsa ya tura hijabin ƙasan gadon ba tare da Mom ta lura da abin da ya yi ba.
"Eh me?" Ta tambaya tana kallonsa dan ta ga ya É—an ruÉ—e sai dai bata san dalilin hakan ba.
"A'a cewa na yi eh akwai abin da ke damuna, amma ai na karɓo miki saƙon naki"
"Ohk yana ina?"
"Yana falo a kan kujera, dama nufina idan na ji ɗan dama-dama sai na miƙa miki"
"Ayya sannu bari in ajiye maka wannan sai in ɗan barka ka huta in na fita na ɗauki saƙon nawa" Ta faɗa tana barin jikin mudubin tare da yin hanyar bayi da wasu robobi guda biyu a hannunta da sai yanzu Musty ya lura da su amma ya ta,allaƙa hakan da rashin nutsuwar da yake ciki da kuma ruɗu shi ya sa bai ga robobin ba.
A sukwane ya tashi daga bakin gadon da yake zaune, wanda shi ma bai san hakan ba sai dai ganinsa da ya yi tsaye cankarkar a kan ƙafafunsa yana zare ido kamar wanda ya yiwa sarƙi ƙarya dama ƴan magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Aikuwa cikin sauri ya sha gaban Mom yana ƙirƙirar dariyar yaƙe ya ce
"Mom mai za ki yi a bayina kuma?"
"Haba Mustapha kai da baka da lafiya ya za ka taso, kuma ma mai zan yi a bayi wurin da ba kicin ba shi ba ɗaki ba, wannan robobin da kake gani shampoo ne da conditioner wanda na maka odar ɗinsu kwanaki sai jiya suka ƙaraso to shi ne zan ajiye maka" Ta faɗa tana ɗaga masa robobin hannun nata.Kafin ya haɗa kalmomin da zai rinjayeta ta fasa shiga bayin ta kewaye shi ta nufi bayin gadan -gadan.
_FATIMA_
"Tambaya nake dama?"
"Tambaya kuma" Matar ta tambayi Fatima cikin mamaki.
"Eh tambaya nake, wani nake nema sunansa Idrisu" Ta faÉ—a tana kallon matar.
"Ikon Allah wato dai matar nan ke ba ma ki san wanda kike tambaya ba ko wani ne ya ce miki a nan wurin yake zama?"
"A'a ni ban sani ba, hasali ma daga arewa na taho nemansa mijina ne" Cewar Fatima cikin sanyin murya.
Tabbas ta ƴan magana ne da suka ce in da ranka kasha kallo, in ba ƙarfin hali ɓarawo da sallama ba ma za yi ki taho tun daga arewa ki zo neman mijinki, bayan in ban da rashin godiya irin na wasu matan mijinki ya barki ya taho nemo muku abinci, amma ki biyo shi, saboda son zuciya da kishi gani kike nan ɗin wani saɓon Allah yake aikatawa ko wani abun da ban wanda bashi ya zo yi ba, to yanzu ko zaki yi shekara kina zaga garin Lagos ai ba za ki ganshi ba" Cewar ɗaya daga cikin masu cin abinci a wurin.
"Ikon Allah wai mai yasa mutane suke da saurin yanke hukunci ba tare da sanin ainihin gundarin magana ba? Daga tambaya kai baka san mai ya baro da ni gida ba har na biyo shi amma ka saki baki kana ta faɗar maganganu mararsa kai da ƙafa, Allah na tuba idan ba dalilin Beelal ba ni mai ma zai sa na ɗakko hanya na biyo bayan Idrisu tun daga arewa zuwa kudu, to ma kishin mai zan yi? Mutumin da bai sauke nauyin haƙƙinmu a kansa bane har zan ɓata lokacina wajen yin wannan doguwar tafiya da bibiyar rayuwarsa, ai komai ya yi kansa kuma kowa ya aikata da kyau zai ga da kyau"
"Malama ki bar nan ki ƙara gaba ko kya samu wanda za su ɓata nasu lokacin a kanki, amma ba dai a nan ba" Matar nan ta faɗa wanda hakan ne ya katsewa Fatima zancen zucin da take. Cikin sanyin jiki ta juya ta bar wajen, tana jiyo muryarsu suna ta faɗar son ransu a kanta.
Haka ta dinga tafiya tana ta kalle-kalle tana fatan Allah sa ta yi gam da katar na haɗuwa da tilon ɗanta a hanya, amma haka ta karaɗe wajen gabaɗaya amma ko mai kama da Beelal bata gani ba sai dai ta sha ganin masu nakasa a hanya wanda hakan ke sanya ta ji raunin zuciyarta ya ƙaru sannan damuwar son ganin Beelal ɗin ta ninku a ranta.
Har ƙarfinta ya ƙare amma bata samu cimma burinta ba na ganin Beelal ko kuma Idrisu wanda zai sada ta da Beelal ɗin. Duk lokacin sallah ta kan siya pure water ta yi alwala ta gabatar da sallah, a haka har ta ƙaraso wata unguwa mai shiru kamar ba mutane kowa yana cikin gida sai mutane jifa-jifa da ke ɗan wucewa, lokacin ana kiran sallar magriba ƙarewa unguwar kallo ta tsaya yi kamar mai son gano wani abu, daga ƙarshe dai ta samu ƙofar wani gida wanda ke da benci a wurin ta yada zango a kan bencin.Shiru ta ɗan yi a ranta tana ƙiyasta ina ma za ta hango Beelal yanzu da bata san irin farincikin da za ta tsinci kanta a ciki ba, amma ina... Hakan bai samu ba a haka ta yi alwala da sauran pute water guda ɗaya da yake wurinta ta shimfiɗa ɗankwalinta ta gabatar da sallar ta yi addu'o inta a kan samun nasarar abin da ta zo nema wato ɗanta.
Tana nan zaune a wajen har aka kira sallar ishsha'i, ta yi sallar ishsha'in bayan ta kammala ta koma kan bencin ta zauna ta lula duniyar tunani.
"Allah sarki rayuwa kenan wato shi bawa babu abin da ya sani wanda zai faru a yau ko gabe Allah shi ne masanin haka, da a ce na san Idrisu zai ɗauke Beelal da a ranar ko runtsawa ba zan yi ba bare har ya samu damar hakan. Amma kaddara ta riga fata, bawa bai san mai zai faru ba hakan ya sanya ma ubangiji ya ɓoye wa bawa ranar da ajalinsa zai sauka, dan da a ce mutum ya san ranar mutuwarsa da zai rayu ne cikin tashin hankali amma cikin hikima ta ubangiji sai ya ɓoye hakan, ko da a ce saura minti ɗaya ne tak a ɗauki ran mutum amma sai ka ga bai sani ba. Wannan kaɗai ya isa ya sanya bawa yin abubuwan masu kyau domin samun yardar ubangiji"
Ƙaran buɗe get ɗin gidan da Fatimar ke zaune a ƙofar shi ya dawo da ita daga tunanin da zancen zucin da take, mota ce ta fito daga ciki, sannan wani mutumi ya ja get ɗin ya rufe da alama dai mai gadin gidan ne. Da ido Fatima ta bi motar da ta zo ta wuce ta gabanta wacce ke ɗauke da gilashi baƙi wanda hakan ba ya barin na waje ya hangi wanda ke cikin motar.
Har motar ta ɓacewa ganin Fatima sannan ta koma ta ɗan kishingiɗa a kan bencin. Jin ta take garau babu alamar bacci a tare da ita bare kuma yunwa, tabbas ashe dai lafiya da kuma kwanciyar hankali ke sanya mutum jin yunwa har ya ci abinci sau uku a rana ko ma fiye da hakan, amma ita yau da take cikin wani hali sai ta ji yunwar ma bata ji
Kimanin awa guda kenan sai ga motar ta dawo, har motar ta gifta Fatima sai kuma cikin sauri motar ta dawo da baya, sai da ta zo dai dai inda Fatimar ke zaune ta tsaya cak, hakan ya sanya Fatima saurin tashi zaune daga kishingiɗen da take ta shiga wurwurga ido gabanta na faɗuwa, dan bata san su waye a cikin motar ba sannan mai ya tsayar da su a wajenta, alkairi ko akasin haka? Shin korarta za su yi daga ƙofar gidansu ko kuwa taimakonta za su yi, ko kuma wani abu ne yake tafe sa su saɓanin abubuwan da zuciyarta ta ƙiyasta mata...
Shin ya rayuwar Beelal za ta cigaba da kasancewa a garin Lagos? Rayuwarsa a hannun mahaifinsa da abokin mahaifinsa da basu da tausayi bare imani sai tarin son zuciya.
Menene dalilin tsayuwar motar wannan a gaban Fatima shin su waye a ciki? Ya Fatima za ta kasance a cikin Lagos yaushe ne za ta haÉ—u da Beelal a kwana kusa ne ko sai an É—auki dogon lokaci.
Ina labarin Hajiya Laɗifa wane hali za ta tsinci kanta idan ta samu labarin barin Fatima da Beelal arewa? Shin wace waina za a cigaba da toyawa a wannan gidan da basu da alƙibla masu bahagon aƙida wanda basu san komai ba sai ƙyamar nakasassu, shin waye ɗan da Hajiya Nuratu ta haifa mai zai zame musu a cikin gidan?
Akwai tarin tambayoyi wanda ake buƙatar amsar su, da kuma wasu abubuwan da sai dai wanda ya karanta labarin Beelal har ƙarshe zai sani, dk amsoshin suna tattare da 300 da zaki biya kuɗin karatu ki karanta har ƙarshe ba tare da kn jira wani ya samo miki ba wataran ma ki rasa wani page ɗin.
Ko daga yau zaki iya biyan kuÉ—in karatunki, alÆ™alamin maman afrah ba ya rubuta shirmeðŸ˜
Mai buƙatar buk 1 ya min magana kyauta ne, mai son buk 2 ya biya 300 idan complt ne 500
09030283375