Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 2 of 8
Page3ï¸âƒ£âž¡ï¸4ï¸âƒ£
"Yanzu ka san me za a yi abokina?" Imran ya faÉ—a yana kallon Idrisu.
"Sai ka faÉ—a"
"Ka san akwai keken guragu a cikin wancan rufeffen shagon na wannan gurgun da suke zaune a cikin shagon da ya mutu, sauran ma suka fasa hayar shagon to tun da ba wai so ake ba shi za mu É—akko shi wannan sai yake hawa"
"Kamar ya yake hawa, bayan yana tafiya gani nake duk inda zai je kafin ya je a keken ya je a ƙafa, kuma ma so kake ka sauƙaƙa masa tafiyar ya zama yana yin barar yana samowa a ɓagas ba zai san zafin nema ba kenan? Ai gwara dai yake yawo da ƙafafunsa duk da dai ba wata tafiyar kirki yake ba sai ka je wuri sau goma ka dawo ka tarar da shi yana hanya bai je ba"
"Haba ka gane mana ba wai dan ya samu hutu za a bashi keken ba ka san yanzu idan aka ganshi zaune a keken kuma hannu da ƙafa a lanƙwashe za a ɗauka gurgu ne a haka sai ya fi samun sadaka, a kan a ce da ƙafarsa aka ganshi"
"Shege Baaba wallahi kwanyarka na ja amma a wajen son samu fa" Idrisu ya faÉ—a yana baiwa Imran hannu suka kashe.
"Wallahi nake faɗa maka ko kaɗan ni ma kawai jin maganar na yi ta sauka a kwanya ta ba tare da dogon nazari ko tunani ba na ce bari dai na faɗa maka tun da dai na san ai ni da kai bata ɓaci"
"Ai tuni ma an gama yanzu je ka fito masa da keken ya hau ya fara fita tun yanzu ka san da zafi-zafi a kan daki ƙarfe"
"Kai Idrisu wutar cikin naka ta yi yawa yanzu daga zuwanku kake cewa ya tafi bara ko hutawa baku yi ba kuma bai samu komai ya ci ba, kuma ma na ɗauka sai an ɗan nuna masa wajejen zuwa tun da ba inda ya sani kar ya je ya ɓata a shiga tara" Imran ya faɗa yana kallon Idrisu.
"Kai ka jika da wani zance, to me ma za a bashi ya ci ai sai ya nemo mu ma za mu ci, kuma da kake cewa daga zuwanmu, zai fara fita to ma wai shin mai za a fasa mutuwa ko hisabi? Kuma zancen ɓata a shiga tara ai ko uku ba za mu shiga ba dan ya ɓata Allah raka taki gona gaba ta kaini gobarar titi na huta da yiwa gyatumarsa bayanin dalilin da ya sa na tafi da duk da dama ba wai tsoronta nake ba, shi idan ya ɓata sai na nuna ba ni ne na tafi da shi ba"
"Ni fa ba wai rasa shi ne tarar da za mu shiga ba, to in dai zai ke samo mana kuma a rasa shi dole mu shiga tara tun da haryar samu ta toshe mana"
" Kuma fa haka ne, amma yanzu idan ya hau keken mu za muke tafiya yana bin mu a baya sai mu kai shi inda za a fi samun sadaka muna daga gefe a tsaye kamar ba tare muje d shi ba idan muka ga ya tara mana abin da muke so sai mu dawo" Idris ya faɗa yana dariya. Shi dai Beelal yana nan durƙushe bai ce komai ba kansa sunkuye a ƙasa yana sauraren duk abin da suke cewa.
"Bari na ɗakko masa keken" Imran ya faɗa yana miƙewa tsaye.
"Zan yi a hakan ba sai da keken ba" Beelal ya faÉ—a cikin in'innarsa.
"Kai dalla rufewa mutane baki, kai har wani zaɓi ne da kai, wato kai ma duk a yadda kaken nan a nakashe ta ko ina har kana ƙyamatar hawa keken guragu dan kar a kiraka gurgu ko?" Idrisu ya faɗa yana hararar Beelal da kansa ke sunkuye.
"Ba haka bane Alhaji, ni da a ce ma bani da nakasa ba na jin zan ƙyamaci kowane irin halittar Allah kawai dai tun da Allah ya mini ni'imar samun ƙafa ina tafiya bai kamata in hau keken guragu ba, in ɓata ni'imar da Allah ya mini ta ƙafafu bayan ni ba gurgu bane saboda kawai in samu abin duniya sai na butulcewa baiwa da ni'imar da Allah ya mini" Ya faɗa cikin in'innarsa yana ɗago kansa a karo na farko ya sanya idanunsa cikin idanun Imran.
Wani uban haushi ne ya turnuƙe Imran cikin zafin nama ya ɗaga hannu ya kaiwa fuskar Beelal wani gigitaccen mari, Beelal ma cikin sauri ya duƙar da kansa ƙasa, Imran ya mari iska, ganin iska ya mara bai samu fuskar Beelal ba daga Imran har Idrisu suka tsaya kallon -kallo da mamaki.
"Kai har ni ka ɗaukewa kai na mari iska" Cewar Imran cikin ɓacin rai.
"Ni ma mamakin da ya kasa barin raina kenan" Idrisu ya faÉ—a cikin mamaki.
"Ai ban yi laifin da za a mare ni ba" Beelal ya faÉ—a cikin in'innarsa.
"Lallai ma yaron nan, kai da kake a ƙarƙashinmu sai yadda muka yi da kai kana garin da baka da kowa baka da uwa ba uba babu dangin iya bare na Baba amma har kana da ƙarfin gwiwar butulcewa umarni ko tsallake abin da muka yi niyyar yi?" Imran ya faɗa yana wani zare idanu.
"Bani da kowa amma ina da Allah, shi ke tare da bayinsa daɗi ko wuya, shi ne wanda baya gajiya da buƙatun bayinsa, shi ne yake bayarwa ya ƙara kuma yana tare da duk wanda bai manta da shi ba" Beelal ya faɗa hawaye na kwaranyo masa saboda gabaɗaya abin da yake faɗa daga ƙwalƙwalwarsa yake tahowa domin gabaɗaya kalaman Mamarsa ne wanda take faɗa mas suke zama daram a ƙwalƙwakwarsa.
"Lallai gurgun mage ka ga makwancinmu wato har kai ma kana iya musayar yawu damu, a haka bakinka babu daÉ—i kana magana da in'inna har kana rufe idanu saboda in'innar amma a hakan kake faÉ—ar ra'ayinka"
Cewar Idrisu da mamaki fal a fuskarsa. Shi dai Beelal bai ƙara cewa komai ba.
"Rabu da shi abokina da mu yake zancen, keke ne dai ko ba ya so sai ya hau dan shi da gurgun ni ban ga maraba ba" Imran ya faÉ—a yana fitowa daga shagon domin É—akko keken a É—aya rufaffen shagon.
"Dan Allah Alhaji ka yi haƙuri ka ce kar ya ɗakko keken nan, ya kamata ɗan adam ya zama mai godiya ga ubangajinsa a duk yadda Allah ya haliccesa, Allah ya bani ƙafafu bai kamata nake yawo a keken da duk wanda ya ganni zai yi zaton bani da ƙafa ni gurgu ne, kuma in har a ƙafartawa ma nake iya rabona kawai zan samu a barar babu wanda zai haɗa min da rabon wani...
"Kai dalla ka rufewa mutane baki waye sa'anka a cikinmu? Ko dan ka ga ana ɗaga maka ƙafa, to bari ka ji na faɗa maka kai baka isa ka sa mu yi abin da bamu yi niyya ba, sai shegen surutun tsiya, ga wa'azi kamar wani limami, kai ga wanda mahaifiyarka ke koya maka sanin Allah da sanin ya kamata" Idrisu ya katse shi cikin ɗaga murya.
Shiru Beelal ya yi dan yadda Idrisu ya masa magana ya tsorata saboda da ƙarfi ya zafice shi dan haka sai ya ja bakinsa ya yi shiru.
"Baaba na ɗakko keken nan fito ka gani, ko a san a bin yi ka san maganin abu a yi shi" Imran da ke can waje ya faɗa da ɗan ƙarfi.
Haka Idrisu ya fito daga cikin shagon yana washe baki, ya baro Beelal a can ciki.
"Kai gaskiya abokina ka iya bada shawara to ka ga wannan da babu shi ma sai mun nemo amma tun da gurgu ya bar wa É—an uwansa gurgun mage gado ka ga mun huta da nema" Idrisu ya faÉ—a yana kallon tsohoh keken guragun da ya ya tsufa jikinsa duk tsatsa.
"Eh mana, ai mu gaba ta kaimu gobarar titi, kai kana ina fito dalla ka zauna a ciki kamar wanda kake ganin dodanni" Imran ya faÉ—a yana kiran Beelal da bai fito daga shagon ba.
"Ka fito da rarrafe saboda tsaro ba dan tsoro ba, dan yanzu idan ka fito da ƙafarka wani ɗan sa ido ya gani sai a gama gane lagonmu" Idrisu ya faɗa yana kallon shagon nasu yana jiran fitowar Beelal.
A hankali Beelal ya sanya hannu ya share hawayensa, ya yi dibara ya miƙe ya tahowarsa a ƙafarsa ba tare da ya rarrafo ba kamar yadda aka buƙata.
Ganinsa ya fito a tsaye sai Imran ya tafi da sauri ya je bayan Beelal ya sanya hannu ya hankaÉ—o Beelal, aikuwa Beelal ya tafi tagal -tagal sai kuwa ya faÉ—a a kan gwiwoyinsa aikuwa ya ji faÉ—uwar sosai wani zafi ya ziyarci gwiwoyinsa.
"Ka min dai dai ai maganin marar kunya da rashin jin magama kenan" Idrisu ya faÉ—a yana kallon Imran.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ya haka" Cewar Aminullah da ya ƙaraso wajen cikin sauri dan tun lokacin da ya shawo kwana ya hango Imran ya hankaɗa wani yaro da ya fito daga cikin shagonsu hakan ya sanya ya ƙaraso da sauri.
"Kai ba fa da kai ake yi ba mu ba ma son shishigi da shiga shiri ba shanu" Idrisu ya faɗa yana hararar Aminullah. Aminulla kuwa ganin abin da suka yi da gangan ne sai kawai ya nufi wurin Beelal cikin tausayawa musamman ma da ya lura da larurar da ke tattare da yaron sai ya ji wani mugun tausayinsa ya mamaye masa zuciya. Cikin sauri da azama ya sanya hannu ya ɗaga yaron tsaye yana masa sannu tare da dudduba jikin Beelal ɗin dan ganin ko ya ji ciwo. Dan shi Aminullah duk tunaninsa ma yaron bara yake suka masa wannan wulaƙancin.
"Kai fa wannan zaƙiyar da kake yiwa mutane, da shiga shirgin da ba naka ba, ba ka ji ba an ce mutum ya bar abin da babu ruwansa ba, amma kai kullum cikin kutsa kai cikin abin da bai shafe ka ba kake" Imran ya faɗa yana hararar Aminullah da ke riƙe da Beelal.
"Ko ma dai me zaku faÉ—a ku faÉ—a amma dai abin da kuka yi baku kyauta ba in sadakar ce ba za ku bashi ba sai ku ce ya tafi amma ba wai ku masa wannan kora da halin ba" Aminullah ya faÉ—a shi ma yana kafe su da ido.
"To kai an faÉ—a maka kowa ma irinka ne, ko kuma an ce maka bara yake, to wannan da kake gani tun daga arewa na taho da shi kudu saboda yake bara yana samo mini kuÉ—i, dan haka babu ruwanka ka sake shi ya zo ya hau kekensa" Idrisu ya faÉ—a yana kallon Aminullah.
Baki sake Aminulla yake kallonsu yana rayawa a ransa wace uwa ce wanann marar dogon tunani za ta baiwa mutum kamar Idrisu yaro kamar wannan da sunan a zo da shi ya yi bara, Idrisu da ko ciwon kansa bai sani ba ta yaya har haka za ta faru.
"Sake shi to tunda ka ji kanun labaran sai ka kiyaye shiga abin da baka ciki wanda babu ruwanka" Imran ya ce yana wani É—aga kai sama.
"Amma duk da kun ce ba ruwana ya za a yi ku ɗakko wannan tsohon keken ku ce ya hau bayan kuma keken ya riga da tsufa duk ya yi tsatsa, bayan ma yana da ƙafarsa ya za a yi ya hau keken guragu" Aminullah ya faɗa yana kallon fuskar Beelal cike da tausayawa dan ya san ba da son ran yaron ba.
Da sauri Imran ya sanya hannu ya fisgi Beelal daga hannun Aminullah yana aikawa Aminullah É—in wata harara tare da Beelal É—in.
"Ka rainawa mutane hankali har ka tsaya ja in ja damu, shin ma ina ruwanka da mu ne? Menene alaƙarmu da kai, ko muna da wani haɗi ne da kai bayan na addinin muslunci, da kuma haɗin kama hayar shago ɗaya? Dan haka ka fita idanunmu mu rufe in har kana son zama lafiya"
MMN AFRAH 09030283375
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
*BEELAL*
💦💦💦💦💦💦
NA
MAMAN AFRAH
Book 2
*FCW*💛