Complete Hausa Novels

Bayan Wuya Complete Hausa Novel

Reading file: Bayan Wuya Complete Hausa Novel.txt

Chapter 3 of 4

*Page* 5&6

___________✍️A hanzarce ta ɗago dara_daran idanunta ta saukesu akan Nazeer wanda ya kafeta da idanu yana sakar mata lallausan Murmushi,itama murmushin ta sakar masa tana gaida shi, sannan ta turo ɗan ƙaramin bakinta tana faɗin "jiya fa da naita kiran wayarka ban samu ba,gashi kamin alƙawarin zaka zo," ta faɗa tana sake turo ɗan mitsilin bakinta wanda turosa ya zame mata al'ada,

Murmushi yayi yana faÉ—in "kinga yanzun jeki islamiyya idan kin dawo mayi magana."

Sallama sukayi cikin shauƙi da ƙaunar junansu,tunda taje islamiyya taketa walwala,don yau batama wani nuna damuwar kyaran da ƴan ajin nasu ke mata ba, Hafsat dake zaune kusada ita ce ta kalleta tana faɗin "waini yau Muneebba wane albishir aka miki ne? kike ta faman farinciki haka."

juya fararen idanunta tayi tana faɗin "wannan ai yama fi albishir ɗin Hafsat saboda na haɗu da farincikina Nazeer," ta faɗa tana mai ƙara sakin wani murmushin

kallonta Hafsat tayi tana mai girgiza kai saboda tana tausayin ƙawarta akan mugun son da take yiwa Nazeer ɗin, saboda tasan halin mahaifiyar Nazeer ɗin yadda ta tsani talaka, "Allah dai ya barki da Nazeer ɗin nan Muneebba,amma fa wannan son da kike masa yayi yawa Allah."

ɓata fuska Muneebba tayi tana faɗin "kinga Hafsat idan ba zaki ƙara ƙarfafa man gwiwa akan naso Nazeer to ƙara kawai kiyi shiru."

"Allah ya baki haƙuri keda kan Nazeer sai ki ƙulla gaba da mutum." banza Muneebba tayi mata har aka tashi babu wanda ya kula wani,saida kowa zata shiga lungun gidansu sannan Hafsat tayiwa Muneebba Sallama shima Muneebba nata fushi ta amsa, sannan shiga wani ɗan ƙuƙut ɗin lungu wanda duka gidajensu na marassa ƙarfi ne,wani ɗan ƙaramin gida da yafi na lungun nasu lalacewa naga ta duƙa ta ɗage zanen da suka lulluɓe ƙofar ta shiga da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin gidan,

Sallama tayi taji tsit hakan ya tabbatar mata da Mamma ta shiga lazimi,wucewa tayi ta cire uniform ɗin, wayarta ta ɗauko INFINIX HOT 10 wacce Nazeer ɗin ya siya mata, Number Nazeer ta dannawa kira,saida tayi 3 miss call sanna ya ƙara kira,sosai tai mashi ƙorafi ya lallasheta sannan suka ci gaba da hira da junansu cikin so da ƙaunar junansu, a ranar ne kuma Nazeer ɗin zai ako gidan su Muneebba, sosai ranar Muneebba ta yini cikin farinciki da murna

*Bayan kwana biyu*

sosai Muneebba ke murnar saka musu baiko da akayi da Nazeer, saidai matsalarta guda ita ce Mahaifiyarsa,don tayi mata warning yafi a ƙilga akan ta rabu da Nazeer amma taƙi, don saida Baban Nazeer ɗin yai mata jan ido sannan ta bari akayi baiko amma ta ci alwashin bazata taɓa bari Nazeer ya auri Muneebba ba,

Kwance take bisa cinyar Mamma, Mamma na mata fira tana dariya, shigowar Mutum suka ji babu ko Sallama,

ɗaga kanta Muneebba tayi taga Maman Nazeer ce,miƙewa tayi tana ce "Hajiya ina yini"

"dalla rufe man baki da ban yini ba kin ganni, Warning nazo buge miki, akan ki ni sanci kanki da yarona,don bani son haɗa jini da marar asali da galihu,ku ɗin nan da ba'a san asalinku ba anfi danganta ku da ƴaƴan shegu, to wallahi na faɗa akan ki auri Nazeer ƙara na saka a nakasa ki,na faɗa miki karma ki ce ban faɗa miki ba" sosai maman Nazeer ta ciwa Muneebba da Mamma mutunci tana gamawa ta kaɗa bujenta ta ƙara gaba

faɗawa jikin Mamma Muneebba tayi tana fashewa da wani Matsanancin kuka ta ce "Mamma shin laifi ne danna auri Nazeer saboda ina Talaka, me yasa ake ƙyamar Talaka? talaka yafi kowa ƙasƙanci a gurin wasu masu kuɗi ne???, ni ɗinnan Mamma saboda na kasance talaka kuma marar Mahaifi shiyasa nake shiga cikin tozarcin Al'umma" ta faɗa tana sake fashewa da matsanancin kuka

a faƙaice Mamma ta share hawaye tana murmushin takaici ta ce " ko kaɗan Muneebba ke ɗinnan baki rasa uba ba kina da cikakken uba nagartaccen Mahaifi,da Mutane sunsan wanda ya haifeku da ba zasu kuskura ko kallon banza suyi maku ba, sai dai ko wane bawan da tashi ƙaddara mu tamu jarabtar kenan,kiyi haƙuri komai lokaci ne"

"Mamma kullum ce mana kike inada uba kuma yana raye, me yasa ya zaɓa mana wannan tozarcin me yasa bai nemu ba duk tsawon shekaru, shin anya uba ne??? bana tunanin cikakken Mahaifi zai iya ƙyale yaransa suyi rayuwan tozarci a cikin Al'umma,Mama naji na tsani Mahai......."

wata uwar tsawa Mamma ta daka wa Muneebba daya saka ta yin shiru, cikin matsanancin ɓacin rai Mamma ta ce "kina da hankali ? zaki ce kin tsani Mahaifinki wanda ya kawoki duniya,to karna sake ji idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci" Mamma ta faɗa cikin ɓacin rai

Kallonta Muneebba tayi ta ce "Mamma hakan bazai ƙara fitowa daga bakina ba kiyi haƙuri,amma har yanzun kina son wanda ya banzatar dake a rayuwa yaja miki tozarci a cikin Al'umma ya ci amanarki........"

"Muneebba!!!! bana son wannan zancen ya ƙara fitowa daga bakinki ki" sosai Mamma take yiwa Muneebba faɗa

hawaye kawai ta share tana tashi ta shige ɗaki,ji tayi duniyar yai mata zafi da ɗaci ta ƙara jin tsanar Mahaifinta fiye da kowa na duniyar dukda bata sanshi ba sai dai a labari, sosai take kuka,kukan da ya zame mata jiki a duk lokacin da irin wannan abun ya faru, sosai take baƙin ciki yadda Mamma ke son Mahaifinta

har yanzun sosai take ganin tsantsar ƙaunar mahaifinta a idon mahaifiyarta, ita dai har abada ba zata taɓa son mahaifinta ba.........✍️

*Wai minene asalin su Muneebba,me yasa ta tsani mahaifinta insha Allah a next Page zamu ji mafarin lamarin*

Wannan kenan Comment Share fisabilillah

*WaÉ—annan sune karsashin Dukkan Marubuci*

*By Riamcool, Star of the Squad*

Only Call

*08109554986*
[5/21, 8:07 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

Book 1

By Riamcool

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*بسم الله الر حمن الر حيم*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.