Complete Hausa Novels

Bayan Wuya Complete Hausa Novel

Reading file: Bayan Wuya Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 4

Page 3&4

_________✍️girgiza kansa kawai yayi ya haura sama Zuciyarshi na mashi zafi bisa ga halayyar Matarsa,ya san da cewa Uba shi ke zaɓar ma ƴaƴanshi Uwa ta gari amma shi sam baiyi da cen Mata ba dukkan yaranta babu wanda ta Koyar da shi tarbiyya,kowa dukkan abinda yaga dama shi ya keyi,shiya sa ga Matannan duk wacce aka aura sai ta dawo.

Tunda Dad ya shiga Mom tana nan tana danna Wayarta bata tashi ko sannu batayi mashi ba ballantana ta tashi tabi bayanshi.

Kwance yake bisa tamfatsetsan gadonshi, ya lumshe idanuwanshi, Kyakkyawan Saurayi ne ajin farko,wanda kallo ɗaya zakayi mashi kasan cewar ya kai duk inda ake son ɗa Namiji ya kai,yana da kyakkyawar ƙira irin ta ƙarfafan Maza, dogo ne, fari tas da shi, yana da kwarjini duba da yadda ya haɗe rai kamar bai san miye dariya ba, ƙarar wayarshi ne ya saka shi buɗe lumsassun idanunsa masu kama da na Mage,a hankali yasa hannu ya ɗauki wayar yana yatsina Fuska,ko duba sunan waye ke kira bai tsaya yi ba, yana ɗagawa yaji anyi shiru,shima shiru ɗin yayi na tsawon wasu mintuna,har zai kashe Wayan yaji Muryan Dad yana faɗin "Son duk inda kake kazo ina nemanka,"

"Ok Dad," shi kaɗai ne abinda ya furta kamar wanda akayiwa dole,ajiye wayan yayi yana ƙara ɓata fuska yana motsa ɗan ƙaramin bakinshi me ɗauke da pink lips,tashi yayi ya shiga Toilet yayi wanka sannan ya fito ɗauki Lotion ɗinsa masu daddaɗan ƙamshi ya shafa,kai tsaye wajen Wardrope ya wuce, kaya ne jere kala_kala, ko wanne da ɓangarensa,ƙananun kaya ya zaɓo wanda zasu amshi jikinsa, a gurguje ya shirya ya fito Securities ɗinsa na take masa baya,da sauri wani security ya buɗe masa Mota ya shiga Driver na jar Motar, cikin shakku Driver ya ce "Sir ina muka nufa?," Da hannu yai mashi alamar inda zasu nufa, kaɗa kanshi Driver yayi ya maida hankalinsa kan aikinsa

Haka har suka isa Tamfatsetsan gidan nasu, danna Horn Driver yayi,da gudu masu gadi suka wangale masu makeken get ɗin,suna shiga Driver yai parking da gudu Security yazo ya buɗe masa Motar, a hankali ya zuro ƙafarshi guda, sannan ya ziro ɗayar ya fito cikin Izza da ƙasaita,da kuma taƙama,tafiya yake irin ta ƙarfafan Maza masu ji da kansu, a haka har ya iso Side ɗin Mom, Yana shiga ya harɗe hannuwanshi a ƙirji yana kallonsu da ɗai_ɗai,gyaran murya yayi wacce ta maido da hankalinsu daga kan Abinda suke yi,har Mom da sauri Mom ta taso tana isowa wajenshi tana faɗin "Son miye haka kayi? Kai daga yi maka Maganar aure shine zaka ɗauki fushi dani har kai ƙaura daga gidannan,kasan kuwa irin tashin hankalin da na shiga?," Ta faɗa tana kafeshi da idanunta,

A hankali ya buɗe Bakinsa yana faɗin "afuwan Mom," yana gama faɗa ya haura Sama,da Sallama ɗauke a bakinsa ya shiga,ɗagowa Dad yayi Fuskarshi ɗauke da yalwataccen Murmushi ya amsa,zama ƙasa yayi yana tanƙwashe kyawawan ƙafafunsa, Sannan ya gaishe da Dad,amsa masa yayi cikin kulawa yana maido da hankalinshi kanshi," bayan wasu ƴan Second Dad yai gyaran murya yana faɗin "Son miye hakan da kayi? Tsawon 2 weeks baka ɗaukar Wayar Mom ɗinka sannan kabar gidan, dama kaga za'a isheka shine ka kashe Wayoyinka gaba ɗaya ba'a samu,saida na dawo jiya Mom ɗinka ke faɗa man daga tayi maka Maganar aure shine kayi fushi da ita, kana tunanin abinda ka aikata kayi dai_dai kuwa? Ka sani ita Mahaifiya sam ba'a musu da maganarta ballantana har kayi fushi da ita,kasan kuwa iya baƙincikin da ka ƙunsa mata? To maza _maza ka nemi yafiyarta idan ba haka ba kana cikin fushin Ubangiji,"

É—ago kanshi yayi a hankali ya ce "ayi man Afuwa Dad insha Allah zan nemi yafiyarta,kuma insha Allah hakan bazai sake faruwa ba,"

"Yawwa ko kaifa Son Allah yai maka Albarka," Dad ya faÉ—a yana sakin Murmushi

Tashi yayi ya fito ya samu Mom zaune ta zuba uban tagumi,a hankali ya tako yazo ya sauke mata hannun daga tagumin da tayi, kallonta yayi yana sakar mata Murmushi sannan ya samu waje kusa da ita ya zauna, sadda kanshi ƙasa yayi yana faɗin "Mom ina mai neman gafararki da ki yafe man akan abinda na aikata maki,"

Murmushi ta saki tana faɗin " na yafe maka *ASAD* dama ni ban riƙeka da komai ba,Matsalata guda shine rashin amincewarka ga wannan auren," ta faɗa fuskarta ɗauke damuwa Sosai

"Indai aure ne damuwarki Mom na amince zan auri Maheer," ya faÉ—a yana mai tashi daga Falon ya haura zuwa É—akinsa

Kowa na Falon da Mamaki ya bishi,ganin yadda ya amince cikin sauƙi haka don ko ita Mom batayi tunanin zai amince ba,ɗaya daga cikin Matan dake zaune su Ukku, wato Suhaima ta ce "anya Mom bada wata a ƙasa ba? ace Yaya Asad shine ya amince da wuri haka," ta faɗa fuskarta na nuna Alamar tantama.

*MUNEEBBA*
Tunda sanyi safiya da ta tashi ta kammala ayyukanta da wuri komai ta riga da ta kammalashi, a gurguje ta shirya ta nufi islamiyya,tafiya takeyi sam hankalinta baya tare da ita ta lula wata duniyar ta tunanin Rayuwa,batai aune ba taji ta ci karo da Mutum,ƙamshin Turarensa ya tabbatar mata da ko wanene, a hanzarce ta ɗago dara_daran idanunta tana kallonshi......✍️.

Wannan kenan

*Comment

*Comment Shine karsashin Dukkan Marubuci, So Comment, Share fisabilillah*

Waɗannan sune ƙwarin guiwata

*Daga Alƙalamin Mariam sani✍️*

*08109554986*
[5/21, 8:07 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*BY RIAMCOOL*

*MIKIYA WRITER'S Ass*

*بسم الله الر حمن الر حيم*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.