Complete Hausa Novels

Bahiyya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bahiyya Part 1.docx

Chapter 4 of 6

*BABI NA SHIDA*

Jingina bayan sa yayi a jikin cushion É—in tare da lumshe idanunsa relaxing himself yana digesting shawarar da Mahi ya basa.

Shi kuwa Mahi ganin ya ƙi ce masa komai yasa ya miƙe tsaye yace.

“Ni zan tafi I'm leaving to Ghana in sha Allah, kai kuma sai ka shirya kayi scheduling time ɗinda zaka gana da mutanen nan da na faɗa maka sun iso tun shekaranjiya, sunce ba za su gana da kowa ba sai kai”

Daga haka ya juya ya fice daga gidan.

Farooq kuwa yafi hour a haka duk wanda ya gansa zaiyi tunanin cewa bacci yake nan ko ba baccin da yake kawai matsalolin gidan sa yake ta lissafi yana neman hanyar warware su.

Miƙewa yayi ya shiga ɗakin da Madinah ta ke, gefen window ya sameta tana tsaye tana kallon waje amma ganin quick action ɗinta tana goge Hawaye ya tabbatar masa da cewa kuka take, cikin mamaki yace.

“Wai Madinah minene? Why have you been crying since yesterday ? da na san cewa tilas taki ki amsamin tamboyoyin zai sa ki yi ta kuka da na haƙura kawai,ko dai akwai wani abin ne bayan wannan ? Please idan har kina da wata damuwa just tell me”

Matsawa yayi in da ta ke tsaye ya rungumeta cikin nuna kulawa yace.

“Madinah Farukun ki ne idan akwai wani abu dan Allah ki faɗamin, idan ina ganin ki kina kuka zuciya ta ba zata iya daurewa ba”

Murmushi tayi tace.

“Haba ba fa komai, kawai dai tunawa da nayi da Azizat da Modu ne yasa zuciya ta ta kasa daurewa”

Cikin tausayawa yace.

“Nasan ba zan taɓa fahimtar yadda kike ji ba domin ke kika rayu tare da su ke kika san zafin su da muhimmancin su a rayuwar ki, to amma ni kuma da na san ke kaɗai ce rayuwa ta dole zan damu idan kina cikin wata damuwa, kiyi haƙuri”

“Na gode Umar”

Sake tambayar ta yayi yace.

“But Grand Ma, is that only my Mom you gave birth to?”

GyaÉ—a kai tayi alamar eh sannan tace.

“Bayan haihuwar Azizat nan ma wata Azal ɗin ce ta sake faɗamana ni da Modu, bayan wata shida da haihuwar ta na je wajen wani spiritualist shima daga garin mu Enugu ya fito na san shi tun daga gida, buƙata ta na faɗa shi akan ina son maganin tsayar da haihuwa kafin yarinya ta ta girma saboda bana so inyi ciki da goyo, ya tambayeni sunan Mijina da kuma sunan da na canja nima na faɗa mishi, daga nan ya tashi ya shiga wani bukka sai da ya ɗauki lokaci ya fito ya ce min an gama aiki,aikin na binnewa a cikin ƙasa saboda haka duk lokacin da na ke buƙatar haihuwa in zo daga zaran an to ne shikenan. Hmmm! Faruku ban sake komawa wurin mutumin nan ba sai da Azizat ta cika shekara biyar cif a duniya, ko da naje na riski labarin da har in koma ga Mahalicci na ba zan manta da shi ba, domin kuwa ko da naje mutumin ya mutu shekara biyu da suka wuce, wurin nashi ma gaba ɗaya an rushe shi anyi gini kamar bai zauna a wurin ba. Kuma asirin an riga an binne sai idan an tone zan iya sake haihuwa, to kaji yadda mahaifiyarka ta kasance a gare ni ita kaɗai, nayi kuka nayi kuka har na gode Allah na riga na aikata kuskuren da ba zai gyaru ba, a duk lokacin da naga abokanan hulɗa ta da yara fiye da uku huɗu sai na ji zuciya ta ta tsinke in yi ta kuka ina istigfari. Hakan yasa ni da kakan ka muka ɗauki son duniya muka ɗorawa Azizat bayan ta mutu kusan zaucewa na kusa yi, hakan yasa da soyayyar kaka da jika da kuma soyayyar mahaifiyarka duk muka haɗa muka baka har Modu ya mutu ya bar mu daga ni sai kai”

A labarin jiya da ta bashi bai ji abinda ya girgiza shi irin na yau ba, haƙiƙa ya tausayawa wannan tsohuwar matuƙa.

Shiru ne ya ratsa tsakanin su bayan some minutes ya ce.

"I'm so sorry Grand Ma”

Murmushi tayi tace.

“thank you. Ka je ka shirya ka zo ka kai ni gidan Victoria nayi mata alƙawarin watan watarana zan zo tare da kai idan damar hakan ta samu”

“Wace Victoria?”

“She's my old friend since from child hood we were from the same state”

"OK.”

Bayan ya gama duk abinda yake suka shirya around 12:00pm suka bar gidan.

Sun samu tarba mai kyau gidan da suka je, sai 4pm suka dawo.

Madinah tayi hakan ne domin ta rage masa damuwar da take damun sa, Mahi yayi mata duk bayanin da yake ciki to amma ba zata shiga al'amarin gidan sa ba, zata dai taya shi da addu'ar da ta saba yi masa kullum, kuma shi ma bai damu da ya sanar mata ba saboda duk lokacin da ya mata lodging wani complain tsakanin shi da Hanifah sai dai ta ba shi haƙuri tace yayi haƙuri Hanifah yarinya ce watarana zata daina.

A haka tayi ta É—au ke masa hankali suna yawon kai ziyara na tsawon kwanaki daga baya kuma ya warware ya koma Office, amma Kullum kwanan duniya da matarsa yake kwana a rai da ita yake tashi.

***********

BAHIYYA

A 'ƴan watannin nan na samu kuɗi ba laifi domin Malama Rabi ta sama min customers da nike wa aikin lalle da kitso sun fi a ƙirga kuma kowa da kalar irin biyan da yake min na karamci. Hakan yasa muka haɗa kuɗi kusan dubu saba' in Mama ta baiwa Malama akan mu tafi tare a samu makaranta private dai dai da matsayin mu a sanya Nuhaira kafin zuwa wata shekara ni kuma a biya min kuɗin WAEC.

A ta dalilin rashin samun Baba Maharazu a waya shine sanadiyyar da Malama ta shiga gaba gaba aka yiwa Nuhaira komai har uniform har komai ya kama kuÉ—i dubu saba'in da huÉ—u termly kuma Dubu ashirin da biyu. Ss1 to Ss3.

Malama ta kasance maƙociyar mu ce tunda muka dawo nan garin Kaduna Road suka haɗu da Mama, da ita da mijinta duk malaman makaranta ne suna da yara huɗu, bariki ba kamar gida ba ne namiji zai bar matarsa ita ma ta fita ta nema domin su taru su rufawa juna asiri matuƙar zata iya, hakan yasa Malama bayan aikin koyarwa ta shiga hulɗa da mutane daban daban tana kai kayan mata cikin gari da kuma sauran State tana kuma da shago ƙofar gidanta. Ta iya kanta sosai shiyasa duk yadda kake tana iya zama da kai tana kuma da kirki irin nata.

Sanadiyyar komawar Nuhaira school yasa aiki ya taru ya min yawa ni da Mama in kuma na fita cikin gari ita kaÉ—ai tayi ta wahala shiyasa na nema mata almajiri mai taimaka mata.

Yauma haka nayi ta bada kayan miya idan an kawo niƙa kuma in tashi in yi domin Mama ta ɗan fita unguwa, ƙarfe uku nayi na yamma na shirya na fita islamiyya nabarwa Sharifu almajiri sauran aikin kafin Nuhaira ta dawo daga school domin sai uku da rabi suke tasowa kafin ta iso gida kuma huɗu tayi shiyasa take zuwa islamiyya yanzu a makare.

Ko da muka shigo gida ana kiran sallar magrib ganin banga mama a waje ba na shiga ɗaki na tadda ta kwance a duƙunƙune da sauri muka isa gareta ni da Nuhaira muna rige rigen tambayarta mike damun ta,ko iya ɗaga kanta ba tayi hakan yasa hankalinmu ya tashi sosai na cakumota da ƙarfi nace.

“Mama mi ne ne? Mi ya same ki?”

Sai tin zuciyar ta ta shiga nuna min da hannu alamar nan ne yake mata zafi. Cikin ruÉ—ewar kuka nace.

“InnaLillahi! Wannan ciwon zuciyar ya matsa miki Mama. Tashi ki daure mu tafi chemist, yau da ke zan tafi domin ya duba ki.... Nuhaira ɗauko mata hijabi da mukulli mu tafi”

Da sauri Nuhaira tayi yanda nace muka rufe gidan a hankali muka lallaɓa da ita wanda ko a chemist ɗin kasa zaunawa tayi sai da na zauna ta kwanta a jiki na. Tambaya ta mutumin yayi mike damunta.

Kai tsaye na share hawayena na ce.

“Ta daɗe tana complain cewa ƙirjinta yana ciwo, to duk lokacin da abin ya tasar mata sai inzo in sayi mata magani ko nan ko kuma wani wuri in bata tasha, to yau dai bama nan ko da muka dawo kuma mun cimmata a haka”

Nidai ganin nayi ya ɗauko wani abu ya ɗaura mata a hannun ta sannan ya saka wani a kunne bayan ya gama. Ya kalle ni yace min hawan jini ne da ita kuma ya hau sosai fiye da ƙima.

Cikin tsantsar mamaki ni da Nuhaira muka haÉ—a baki wurin kiran.

“Hawan Jini likita?”

Cikin kuka na sake cewa.

“Hawan jini ta yaya? Wane irin hawa jini dan Allah, muna zaune lafiya”

Mutumin yace.

“While, ba abin mamaki ba ne ai, musamman idan akwai wata damuwa tare da ita tana yawan tunani da rashin samun ishashshen bacci, amma...”

Sai ya juya ya hahhaÉ—o magunguna ya bani na kusan dubu goma sha É—aya.

A nan ya buÉ—e ya bata maganin, sannan yace

“idan akwai abinda yake saka ta damuwa kuyi ƙoƙari ku ɗauke mata hankali a kai, ta riƙa samun bacci yadda ya kamata tana cin abinci mai kyau, in sha Allah zata ji sauƙi”

Daga haka na cewa Nuhaira taje gida ta ɗauko masa kuɗin shi, bayan ta dawo muka koma gida, kafin shiga bacci har mun samu taji sauƙi domin har ta tashi tayi Sallah taci abinci.

Washe gari bayan mun gama sallar Asuba muka je muka gaishe ta nayi sauri na haÉ—a mana break fast Nuhaira ta shirya ta fita makaranta ni kuma na kai mata abin karin nata É—aki bayan ta É—anci ba yawa na bata magani kamar yadda likita yace.

Bayan na kwashe kayan na dawo na zauna cikin tausasa murya na kalle ta nace.

“Mama miye yake damunki haka? Mi kike tunani da har ya sa miki hawan jini nan take? Dan Allah Mama ki gayamin”

Girgiza kanta tayi tace.

“Ni dai ban san ina da wata damuwa ba Bahiyya, gaskiya ban sani ba.....”

Cikin rashin gamsuwa da maganar ta nace.

“A'a Mama, dan Allah ki gayamin minene damuwar ki,irin wannan ciwon ba zai kama mutum ba muddin ba damuwa ce a ransa ba.”

“Ni kam bani da wata damuwa Bahiyya”

Juyin duniyar nan nayi amma Mama ta kafe tace min babu abinda yake damunta dole na hak'ura na ƙyale ta ina faɗin.

“To tunda kince ba abinda yake damunki, dan Allah ki kwantar da hankalinki idan ma akwai wani abinda ba zaki iya gayamin ba kiyi haƙuri ki cire sa a ranki, bana so mu koma wurin likitin bayan kwana biyu ya aunaki yace min ga wata damuwa, idan wani abu ya sameki Mama ban san ya zamuyi ba. Kece ƙwarin guiwar mu, kece kaɗai muke da, ke kika zama bangon jinginar mu idan wani abu ya sameki ban san in da zamu shiga ba. Mama ke ce fa kullum kike min faɗa akan in dai na damuwa, in zama mai tawakkali, yau kuma ace kece wai hawan jini ya kama, mi kika nema kika rasa? Idan ma mutuwar Baba ce ya kamata ace kin saba kamar yadda kike faɗamin Mama...”

Hawayen da suka gangaro min na share tare da Miƙewa tsaye na fita waje jin sallamar yaro ya shigo gidan namu.

Mama kuwa mirginawa tayi ta kwanta akan pillow wasu hawaye masu zafi na bin gefen kuncin ta. Haƙiƙa mutuwar Jafaru ta nakasa mata zuciya ta yadda ma bata yi tsammani ba. Idan tace tana samun wadataccen bacci tsawon shekarar nan tayi ƙarya, babu abinda take tunani sai mijinta da kuma rayuwar marayun 'ƴa' ƴan ta mata guda biyu, waɗannan mutanen da suka kashe mijinta sunyi mata illar da har ta kwanta damanta ba zata warke ba. Domin shine jigonta shiya kawo ta wannan ƙasar ta Nigeria ba tare da tasan wani mutum na daban ba bayan shi. Gashi har ya koma ga Allah ƙasar ta sa ta gagare shi komawa akan wani dalilin banza na son zuciya irin na mutanen yau. Har baro garin Gusau tayi ko zata samu sauƙi ta manta da rayuwar su ta baya amma abin ya ci tura. To kuma yanzu ga ƙarin wata matsalar ta kunno kai tunda likitan ya faɗa mata tana da hawan jini damuwar ta da fargabar ta suka ƙaru, damuwa ta ƙara baibaye ta fiye da ta baya.

Ita tsoron ta kullum idan ta mutu a wane halin rayuwar 'ya' Æ´an ta za su kasance? Sannan idan suka isa aure wa zai aure su idan akaji cewar ba su da dangin uwa babu na uba suka É—ai ne su uku suke rayuwar su.

Bayan kwana biyu kamar yadda likitan yace, na shirya na cewa mama ta shirya mu koma wurin mai chemist kamar yadda yace, ƙin amincewa tayi ta kafe kai da fata tace min taji sauƙi ba sai mun koma ba. Ƙarshe ma faɗa ta rufe ni da shi wai duk laifi na ne, daman su mutanen nan matuƙar kana ziyartar su to kullum cikin kira maka matsala suke, da ace na siyo mata maganin ta tun ranar tasha da yanzu kowa na nan hankalin sa kwance, to ita babu in da za ta je ta warke.

Dole na na kama kaina na ja baki na nayi shiru na ƙyale ta, amma Ina kula da ita sosai duk wani motsin ta yana kan idona, sai dai daga baya na gano tabbas Mama bata samun bacci kamar yadda likita yace, akai akai idan na farka naje ɗakin ta zaune nike samun ta kan sallayah.

Tun daga wannan lokacin na bata shawara ta riƙa sai ta lokaci idan ma tashin zatayi na dare to ta ta shi amma ta rage ɗaukar dogon lokaci.

Haka mukaci gaba da rayuwa, Mama ta samu sauƙi sosai a gaban idanunmu kamar yadda take nuna mana idan abin ya tasar mata sai ta tafi can wani chemist ta sayi magani ta dawo gida ta ɓoye tana sha don kar mu gani hankalin mu ya tashi. Nuhaira taci gaba da karatun ta, nima ina yawon lalle na da yanzu na ƙara yawan customers.

*************

Hanifah

Ko bayan rabuwar su da Farooq sai da ta sake share wata biyu da sati biyu a Dubai sannan ta wuce Egypt ta sake yin sati biyun ta masu kyau sannan ta dawo.

Duk iya yanda Farooq ya ɗauki fushi da ita kasa daurewa yayi dole ya dawo kiranta a waya yana jin muryarta amma bai taɓa tambayar ta cewa ina take ba, mi take yi ko yaushe zata dawo. Iyaka suyi wayar su idan sun ƙare su kashe. Sau biyu tafiya tana kama shi zuwa Dubai bai taɓa attempting na cewa ya je wurinta ba. Ya ƙyale ta har lokacin da ta ga dama ta dawo don kan ta.

Ko da ta iso ma baya ƙasar yana Saudiyya tare da Madinat sun je aikin Umrah sai da tayi kwana huɗu da dawowa sannan ya dawo.

Tare da Madinah suka shigo gidan, tunda yayi rashin lafiyar nan ta zo bata koma Kaduna ba. Cikin murna tazo ta tare shi tana faÉ—in.

“Welcome”

Kamar wanda yake mafarki haka yayi hugging É—in ta back yace.

“Am i dreaming?”

Dariya tayi tace.

“No! Not at all. Is your Hanifah”

Ƙara riƙe ta yayi gam a jikin shi yana faɗin.

“Welcome back home my love”

“Thank you”

Ganin Madinah yasa tayi saurin janye jikin ta taje gareta with soft smile on her face ta bata side hug tace.

“Welcome Grand Ma”

Cikin Kalaman hikima Madinah tace.

“Thank you Hanifah. Da fatan an dawo lafiya”

Hanifah tace

“Lafiya lau Grand Ma”

Madinah tace

“Ya kasuwa? Ya familyn ki? Da fatan komai lafiya?”

Hanifah tace

“Everything is fine, my family are doing good”

“That's nice to hear.”

Madinah tace tare da kama hanyar zuwa masaukinta,luggage É—in ta da suke hannun shi da kanshi ya wuce har É—akin ya kai mata, daman tun a mota da suka sauka ya hana kowa É—aukar kayan yace aikin shi ne saboda haka shi zai kwashe kayan.

Yana fitowa ya zarce ɗakin shi ya je yayi wanka ya shirya itama Hanifah da sauri taje ta sake yin wanka ta shirya cikin riga da wando da suka amshi fatar ta sukayi raɗau, sai wata hular net da ta saka ta naɗe kanta da ita tayi matuƙar kyau. Daman kuma kafin ta shiga ciki sai da ta saka Nafisat cook ɗinta cewa ta shiryawa Farooq table kafin su fito.

Ta riga shi fitowa hakan yasa ta wuce É—akin shi direct ta sa meshi ya gama shiryawa yana tsaye jikin window yana kallon waje, hannayensa soke a cikin trouser pocket É—in shi.

A hankali taje ta rungume shi ta baya tare da É—ora kanta a bayan shi tayi lamo, dukkan su babu wanda yacewa kowa komai tsawon lokaci suna a haka. Sai daga baya ta ja numfashi a hankali sannan cikin pleading tone tace.

“I'm sorry. I'm very sorry for what I did. I know that I hurt you, but what ever it is you are....”

Da sauri ya birkito ta ya rufe bakin ta da nasa yayi kissing ɗinta passionately sannan ya janye ya kalle ta cikin shauƙi yace.

“karki damu ni komai ya riga da ya wuce a wurina Hanifah”

Murmushi tayi tace.

“Thank you. Muje kaci abinci Nafisat ta gama shirya table”

Ba musu ya bi ta suka je suka zauna zaman cin abinci, yana cikin ci ya ji an kira sallahr magrib a masallacin gidan sa, da sauri ya miƙe yace.

“Hanifah an kira sallah, ya kamata ace na bar cin abincin nan har in dawo daga isha”

Kallon shi tayi tace.

“To kabari ka ƙarasa mana tunda ka fara”

Hanyar waje ya nufa yana faÉ—in.

“No, Idan na dawo after isha prayer sai ki sa a sama min wani abin”

Daga haka ya wuce ya barta. Zaman sa tare da Madinat wannan karon ya sa shi ya É—an canza sosai, domin a lokutan baya Sallah a jam'i bata wani dame shi ba musamman idan yana gida. Amma yanzu ya dage sosai har asubahi yana fita.

Sai bayan ya dawo ya wuce ɗakin Madinah direct ya cimma bata nan, ba kayan ta, Wayar ta ya kira kai tsaye tace mishi gata a Kaduna. Abin yayi matuƙar bashi mamaki kamar wadda ake kora, ya rasa ya ta ɗauki Hanifah a rayuwar ta ko dai surukar ta ce iyaka kenan.

Ko da ya shigo bata nan, dining ɗin ya wuce ya ci abinci sannan ya shige ciki. Kwantawa yayi yay lamo yana tunani. Shi yanzu ya gama yankewa ba zai sake matsawa Hanifah ba akan buƙatarsa ba domin ɓacin rai ne kawai zai yi ta addabar sa, shiyasa yanzu ya yankewa kansa yin azumi domin ya riƙa samun sauƙi.

Yana nan yaji an murɗa handle ɗin ƙofar a hankali, ko bai duba ba yasan wacece ta shigo.

Kwantawa tayi akan ƙirjinshi ta saƙala hannayenta cikin wuyan shi. A hankali taji sautin Muryar sa yana faɗin

“Hanifah time yayi da ya kamata ace munyi settling mun samu yara, duk wannan maganar taki a baya ba tunani ba ne”

Cikin fargaba da tashin hankali tace.

“What! Haba Farooq yanzu duk tsawon lokacin nan da muka ɗauka ba ma tare da abinda zaka tare ni kenan? Bayan kasan cewa abinda ba zai yi yu ba ne....”

“Zai yi yu mana Hanifah,I'm fertile you are fertile too, to minene ba zai yi yu ba a nan?”

“Farooq No!”

“Hanifah abinda nike so kenan”

Miƙewa tayi without thinking twice kawai ta bar mishi ɗakin, abinda ba zai taɓa ma yiyu wa ba kenan. To Farooq Wai ko dai ya fara shaye shaye ne? Kawai kuma sai tayi tsaki domin babu abinda ya faɗo mata a rai sai Grand Ma Madinah da Mahid, ta sani sarai duk sune manyan munafukai da suke so su sanya mata ido a rayuwar gidanta. Ba ta taɓa jin ta tsani Madinah ba a rayuwar ta ba sai yau.

Ƙarshe kwanciyar ta tayi abinta tayi baccin ta ta ƙyale shi bata sake komawa kan shi ba, domin ta gama yankewa a ranta komai zai faru ba zata amince da wannan shirmen nasa ba, iyakaci dai ya gama fushi da ya huce zai dawo, ballantana ma tasan Farooq ba ya iya fushi da ita.

Washe gari ko da ta fito har ya fice daga gidan ko break fast Bai yi ba, nan ya bar mata kayanta yayi tafiyar sa.

Wanda hakan ba ƙaramin shayar da ita mamaki yayi ba.

Waya ta ɗauka tayi ta kashin wayar sa amma yaƙi ɗagawa, Ƙarshe sai ga text ya turo mata kamar haka.

“Ki amsamin buƙata ta kawai Hanifah”

Ajiye wayar tayi tare da zaunawa tayi break fast É—in ta sannan ta shirya ta fita.

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMEER)*

*BAHIYYA NOVEL ÆŠIN KUÆŠI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

          *BABI NA BAKWAI*

  BAHIYYA

   Yau ma da wani irin matsanancin faɗuwar gaba na farka sakamakon mummunan mafarkin da nayi a daren jiya,wanda har yafi wanda na saba yi a kullum muni. A sukuku na fito ɗaki bayan na gama sallah tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, ɗakin mama na shiga na gaidata sannan na fito waje na zauna na buga tagumi ina karanta wasiƙar jaki. Ganin wankin hula na nema ya kai ni dare ga tarin ayyukana a gaba na yasa ni yunƙurawa da nufin miƙewa sai kwatsam Malama tayo Sallama ta shigo.

Cike da mamaki na amsa mata sallamar ta domin duk da cewa ban duba agogo ba nasan cewa iyaka ƙarfe shida ne yanzu na safe.

Da sauri tace min.

“Bahiyya ina mamanku? Yi maza ki shirya mu tafi Maman Khadijat ta kira ni yanzu tace dan Allah ki zo tafiya biki ta kama ta garin su ki zo kiyi mata lalle zuwa ƙarfe biyu zata wuce.”

Nima miƙewa nayi cikin sauri nace.

“Mama tana ciki bari naje to na shirya”

Bayan sun gaisa da Mama tayi mata bayani na shiga É—aki na É—anawa Nuhaira duka a cinya saboda takaicin baccin da take kwantawa bayan asuba, duk da cewa tasan tana zuwa school amma akan mugun bacci kullum sai ta sake kwanciya bayan sallar Asuba.

Firgigit ta miƙe cike da mita tace.

“Haba Aunty Bahiyya!”

Cikin jin haushi nace.

"Dan Allah ta shi kije ki nema abinda zaku karya ni fita zanyi, kada kiyi latti”

Miƙewa tayi tare da yin gunguni ta zo ta wuce nima naje na yiwa Mama Sallama muka tafi.

Ina jin daɗin zuwa gidan Maman Khadijat masu kuɗi ne na gaske amma babu ruwanta, ta iya sakin jiki da kowa, bata da wulaƙanci, hakama 'yar ta Khadijat da ta ke ji da ita, Allah ya haɗa jinin mu da ita sosai, bata ma wani jin Hausa sosai ni kuma ba wani dogon turanci nike ji ba, haka zamu zauna in tsantsara mata kalar kitson da suka nuna min in yi mata lalle tayi ta santi, tana ce min Aunty Bahiyya Thank you.

Hakama yayanta Ahmad da zaran ya ganni muna haÉ—a ido zai sakar min murmushi yace. Aunty Bahiyya hi! Mamar take gayamin cewa kullum idan suna fira ta sai yayi ta ce mata ina da kyau sosai ina burgeshi. Shiyasa ni ke jin daÉ—in zuwa gidan domin ba su da matsala.

*************

HANIFAH

Duk iya ƙoƙarin ta tayi akan cewa taga ta shawo kan Farooq amma abu ya faskara, zata iya cewa tunda take da shi wani abu makamancin haka bai taɓa shiga tsakanin su ba, duk yadda zasu samu ƙololuwar misunderstanding bai taɓa ɗagawa daga wurin ba sai ya tabbata ya shawo kanta komai ya wuce. Baya fushi da ita kai zata iya cewa ma basu taɓa samun makamancinyar wannan matsalar ba, domin zata iya bugun gaba ta tsaya ko a gaban waye tayi alfahari da mijinta tace yafi na kowa kaf a faɗin duniya.

Amma yau Farooq ne yake gudun ta, ko da zata farka ta wayi gari ya wuce abinshi ko da zata dawo daga office kuma bai dawo wa gidan ba sai cikin dare ya ke shigowa koda zai shigo tayi bacci.

Ranar da ta ritsa shi kuma sai ya wayance mata yace aiki ne yayi masa yawa a Office shiyasa.

Har office ta je ta sameshi yace mata taje gida idan ya gama zai dawo haka ta koma amma ƙarshe ma da ta bincika wai yayi tafiya zuwa Kenya.

Ganin ta kasa gane masa yasa ta shirya da wuri ta wuce gidan Rasi'at her best friend.

Tana shiga gidan ta cimma Rasi'at rungume da Khadijat Bahiyya na yi mata kitso.

Murmushi Rasi'at tayi tana mai kallon ƙawarta ta tace.

“Welcome Hanifah”

Ƙugu Hanifah ta riƙe cikin mamaki tace.

“Wai Rasi har yanzu ba zaki sararawa kanki ba ki daina ɗora Khadijat a jikin ki, yarinya shekara bakwai amma kullum kin maidata kamar 'ƴar shekara ɗaya.”

Khadijat waving É—in hannunta tayi da lalle tana murmushi domin bata ma fahimci wane zancen Hanifah ke yi ba tace.

“Hi' Aunty Hanifah! See my beautiful Henna Aunty Bahiyya done it for me”

Duba lallen tayi tana murmushi tace.

“Wow! You look beautiful Baby, how are you?”

Khadijat tace.

“I'm fine, welcome...... ”

Sai kuma ta kalli Bahiyya tace.

“Aunty Bahiyya can't you greet Aunty Hanifah? But you are the one that told me to be greeting our visitors”

Sai yanzu Bahiyya ta É—ago cike da kunya ta kalli Hanifah tace.

“Ina wuni”

Kallon ta Hanifah tayi up and down sannan tace lafiya ta sakai ta wuce Babban farlourn Rasi'at.

Cikin hanzari Rasi'at ta sauke Khadijat daga jikin ta tacewa Bahiyya su ci gaba tana zuwa.

Tana shiga ta iske Hanifah ta dafe goshinta alamar damuwa ta bayyana akan fuskar ta tace.

“Friend is there any problem?”

Hanifah mace ce mai zurfin ciki da wuya abu ya dameta ta nemi wani ta faÉ—a mishi ko mahaifiyarta bata iya faÉ—awa abinda yake damunta in dai ba ta kama dole É—in sai ta sanar mata ba.

Gyara zama tayi cikin damuwa ta fallasawa Rasi'at sirrin ta gaba ɗaya komai bata ɓoye mata ba har abinda ya faru a Dubai tsakanin ta da Farooq sai da faɗa mata.

Shiru ne ya ratsa tsakanin su na É—an lokaci sannan Rasi'at ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Hanifah tace.

“You are at fault for everything Hanifah,kuma kin bani mamaki matuƙa. Miye a cikin haihuwa da zaki ce ba zaki iya ba? 'ƴa' ƴa sune farin ciki Hanifah, knock senses in to your brain, ba'a haihuwa aka haifeki?.....”

“Look Rasi, please I just need a way out, ni ba wani dogon zance nike so ba”

Cike da ɓacin rai Rasi'at tace.

“You are not serious Hanifah! Wallahi you better shine eyes, tunda har mijinki ba haka yake ba ta ƙarfin tsiya kika canja shi to ina tabbatar miki kwaɓarki tana gab da yin ruwa. Ni ban ma taɓa jin miji irin Farooq ba, abu sai kace a film ko a novel, duk abinda kika ga dama shi kike yi kuma wai ranshi bai taɓa ɓaci ba, ji abinda kika ce kin Mishi a Dubai kuma ya dawo kiran ki sannan kika dawo gida yace miki ba komai komai ya wuce, wallahi in baban Amed ne a ranar sai na gane nayi kuskure. Miye a cikin haihuwa? na haifi Amed gashi shekara Goma na haifi Khadijat she's seven years now, kinga wani abu ya fita a jiki na?....”

With full confidence Hanifah tace.

“Wallahi kin ragu Rasi, ke kanki kin san ba zaki taɓa haɗa kanki da wacce ba ta taɓa haihuwa ba irina”

Rasi tace.

“Eh bazan haɗa ba domin nasan cewa Allah ya bani girman da yafi naki, ke bari in faɗa miki wani ɗan ƙaramin sirrin samun yara da baki sani ba; a duk lokacin da kuka samu wani saɓani da namiji ya ƙona miki rai, da zaran kin zo ga yaran ki kin kalle su kunyi fira sai kiji duk wata damuwar ki ta wanke to idan baki da su fa? Sai dai damuwar nan ya kashe ki a banza kuma wata matar zai sake aura. Hanifah ki zama mai tunani da hangen nesa kar ki zama mai son kai, ki duba duk irin ƙaunar da mijinki ya nuna miki amma ke ace Common ƙaramin abu ba zaki iya yimai ba ya neme ki alfarma, Haba ki yi tunani in dai ke mai hankali ce...”

Hura hanci Hanifah tayi tare da runtse ido ta buÉ—e ta kalli Rasi'at tace.

“Is that all you have for me? A matsayin ki na aminiyata na kawo miki damuwata ina neman mafita abinda zaki faɗa min kenan?”

Matsowa Rasi'at tayi tare da janyo hannun Hanifah ta riƙe ta saukar da murya ƙasa tace.

“Hanifah, in dai ni kin yarda cewa best friend ɗin ki ce, to ina roƙon ki da ki amsa buƙatar mijin ki, ki haihu tare da shi matuƙar kina son sa, dan Allah Hanifah, wallahi babu abinda zai rage ki da shi face ma ƙara kusanta ki da mijinki ƙaunar da yake miki ta ƙara ninkuwa ninkin ba ninkin. Maza da dama basu yarda cewa matayensu na son su sai idan sun haihu da su to a lokacin zasu yarda cewa mace ta na son su and she is ready to die together with him. Let me give you an example with my self Hanifah ;ko da mukayi aure da Abdul-fatah bai yarda cewa ina son shi na shirya zama da shi ba sai da na haifi Amed, a lokacin na fara ma sanin miye soyayyar namiji kuma har yau muna respecting juna, I'm a business woman like you, but nothing can deprived me daga kula da mijina. Hanifah ki riƙa kulawa da mijinki, Farooq ba ƙaramin yaro bane kuma ba ƙaramin mutum bane, karki yarda ki bar wata ƙofar da zai fara yarda da cewa bai samu matar da ta dace da shi ba. Ki duba irin kyau da zubin da Allah yayi miki ki kuma duba siffar mijin ki shima, zaku samu 'ya' ƴa masu kyau da nagarta. Hanifah from the bottom of my heart that's the only advice I have for you Ko Nasibat ce sister na iya abinda zan faɗa mata kenan, idan kin ɗauka yayi miki amfani idan baki ɗauka ba watarana zaki ce na faɗa miki haka”

Ajiyar zuciya Hanifah ta sauke tare da gyaÉ—a kai tace.

“Thank you Rasi. I will think about it”

Miƙewa Rasi'at tayi tace.

“Thank you for understanding. Let me bring you something, kinzo na cika ki da surutu ba tare da na kawo miki abun taɓawa ba”

Dawowa tayi hannun ta É—auke da tray with handmade juice da Kuma tsire tana dariya tace.

“Kin zo a daidai friend saboda na yi tsiren tukunyar da kike so”

“Wow! Thank you”

Bayan ta ajiye mata tace.

"Let me check on Bahiyya, Kar taga kamar na ƙyale ta....”

Ajiye Juice É—in hannunta Hanifah tayi tace.

“Wait Rasi! Ina Wai kika samo wannan ita kuma? I wanted to ask you na manta ne, duk shagun nan da ke akwai na masu saloon komai kuma ana yi na masu kuɗi shine zaki ƙare da wannan tana taɓa miki jikin ki har kuna dariya da ita”

Zaunawa Rasi'at tayi tana murmushi tace.

“Eyyah! She's Bahiyya by name, wallahi Malama Rabi ce ta kawo min ita, yarinyar tana da kirki bata cika hayaniya ba, kuma ta iya sosai, Abdulfatah bai cika son zuwa saloon ba shi yasa na raba kaina. Hanifah yarinyar abin a tausaya ce, Mahaifin ta ya rasu daga ita sai Mahaifiyarta da ƙanwar ta ne a nan Nigeria duk sauran dangin su suna Nijar, kuma ba zasu iya Komawa ba...”

Cikin mamaki Hanifah tace.

“And who told you all this, is she the one? Kin san buzayen nan sun iya ƙarya, so karki wani saki jiki da ita wallahi zata iya aure miki miji, daga wannan kirkin nata zaki ji zance ya canza”

Dariya sosai Rasi'at tayi sannan tace.

“No! Ba ita ce ta faɗa min ba malama ce kuma ko shi ni na tambayeta bayan Bahiyyar bata nan nace miyasa bata yin school. Allah na tuba mi Abdulfatah zai yi da Bahiyya”

Daga haka Hanifah ta miƙe ta ɗauki jakar ta tace.

“Ni dai kar ki ce ban gaya miki ba watarana, kice mi Abdulfatah zai yi da ita, ko ni da na san na fiki kyau Rasi wannan yarinyar ta Cuna min balle ke. Ni Kinga tafiyata”

Dariya sosai Rasi tayi sannan tace.

"To ba matsala ni yoruba ita Buzaye sai mu shiga asirtar juna in ga ni da ita waye zai yi nasara”

Hanifah tace.

" Maganin dai kar ayi kar a fara, ki kore ta kawai”

Ko a parlorn sai da Hanifah ta sake ca ke ta da kallon ƙurullah, ganin yadda suke ta karatu ita da Khadijat da Ahmed suna dariya yasa ta taɓe baki ta wuce abin ta.

Rasi kuwa tsiren ta kawo wa Bahiyya tace.

“Bahiyya na gaya miki daman tafiya zan yi kuma sai gashi nayi baƙuwa, lokaci kuma yanzu ya ƙure ba zaki iya yi min ba. Sai dai idan na dawo kamar zan iya kai 1week saboda auren ƙanwata ne zanje idan nadawo zan aika Malama ta kiramin ke”

Cikin girmamawa Bahiyya tace.

“Allah ya kai lafiya, ya sanya alheri ya bada zaman lafiya”

Ƙarfe biyu na rana ta saka driver ya kai Bahiyya gida bayan ta cika ta da sha tara na arziki.

***************

BAHIYYA

Duk irin É—aukin da na shigo da shi gida akan irin abin arzikin da maman Khadijat tayi mini lokaci guda ya suranye samakon wani irin mummunan yanayin da na riski Mama a ciki. A bakin bishiyar tsakar gidan mu na iske ta kwance shame shame a jikin Nuhaira Ko motsi bata yi. Wani irin jifa nayi da duk wani abinda yake hannuna nayo kanta tare da zunduma ihu nace.

“InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Nuhaira miye ya samu Mama? Miye ya same ta dan Allah??”

Itama cikin Kuka tace.

“Nima Aunty Bahiyya ban sani ba, Ina makaranta Sharifu yazo ya kirani wai Mama tana cikin yin Niƙa a injin shi kuma yana wanke wanke kawai suka ga ta yanke jiki ta faɗi, ko da nazo har Maman Walida ta shigo tana tare da ita, ni kuma na ruga wurin mai chemist na ce ya zo dan Allah ga halin da Mama take ciki shine bayan ya zo yace kawai muyi gaggawar kai ta asibiti, to naje Malama da mijinta duk basa nan, shi ne na zauna jiranki....”

Cikin masifa na ce.

“Amma sai yau Nuhaira na yarda cewa baki da hankali, shine zaki zauna ki barta ta mutu? bayan kinji abinda likitan yace cewa ayi gaggawar kai ta asibiti, uban mi kika tsaya jira baki san in da kuɗi yake ba, wawiyar banza”

Da gudu na faÉ—a É—aki na É—auko kuÉ—in da ban san ma adadin nawa ba ne na fito.

Da gudu na fita waje na hau mashin naje na É—auko mota nadawo.

In banda kuka itama Nuhairar ba abinda take sai famar bani haƙuri take tana cewa ta ruɗe ne shi yasa.

Wata private hospital muka kaita in da aka taɓa admitting ɗin ɗiyar Malama wato Umaimah. Da sauri suka karɓe mu aka shiga da ita emergency. Tare da tsare mu da tambayoyin mi ye yake damunta.

Kusan kwanan mu biyu muna reto tare da Malama har da mijinta ƙarshe suka tura mu federal medical center bayan sun caje mu kuɗi sunfi dubu hamsin.

Ni dai biye kawai nike daga Malama sai mijinta Uncle Idris suka É—ai ke kai da kawo.

Ƙarin ruwa ne ake ta yi mata da allurai, tun muna waccan asibitin ta farfaɗo amma dai tana nan zurum kawai tana bin mu da ido malama kuma ta kasa yi min bayanin komai.

Ranar da muka cika kwana huɗu a ranar akace muna result ya fito na gwaje gwajen da duk aka yi mata wanda ko a nan an caje mu kusan dubu saba'in, har kuɗin da muke da yayi ƙasa nan ta ke.

Malama ta jima a ɗakin ganin likitan sannan daga bisa ni ta zo ta kirani muka shiga tare. Shekara ta sha takwas yanzu, duk da irin ƙananun shekaru na, Ina iya fahimtar abu akan fuskonki mutane na daɗi ko aka sin haka. Kafin ma likitan ya fara mini magana naji gaba ɗaya zuciya ta ta gama tsinkewa domin ji nike a jiki na wani mummunan abu ya faru da Mama.

“Bahiyya ko?”

Likitan ne ya faɗi hakan lokacin da ya dallomin Fitilun ganin sa babu ko ƙyaftawa.

GyaÉ—a kaina kawai na iya yi ina wani muzurai tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi.

“Da ace akwai wani na gaba da ke da dashi zamu tattauna wannan zancen, but unfortunately you are the only person na kusanta da zan iya yiwa bayani, Allah yasa zaki fahimce ni”

Lumshe jiƙaƙkun idanuwa na nayi waɗan da suka shabke da ruwan hawaye na sake buɗe su akan shi nace.

“Ina jinka likita. Miye matsalar, na roƙe ku da girman Allah ku faɗa min gaskiya kada ku ɓoyemin komai, nayi muku alƙawari zamowa jajirtacciya”

“To Alhamdulillah! Bahiyya haƙiƙa kowa ne irin mutum a duniya yana da irin tashi ƙaddarar ke musulma ce saboda haka nasan addinin ku ya koyar da ku yarda da ƙaddara...”

Ta wutsiyar ido na sake ƙare mishi kallo a karo na biyu, a raina nace yanzu kai duk haibar nan taka da iya bada magana kahiri ne kenan? To kuma ji yadda yaji Hausa kamar jakin Kano.....

“Bahiyya are you listening?”

Da sauri na gyaÉ—a kai na alamar eh sannan yaci gaba da cewa.

“Mahaifiyar ki tana ɗauke da ciwon hawan jini wanda ya fara cin jikin ta ne a hankali har ya girmama yayi tsanani ba tare da kunyi wani huɓɓasa wurin kawo ta asibiti da wuri ba sai da komai ya lalace”

Cikin matsanancin kuka nace.

“Likita muna yawan zuwa da ita chemist, da farko ni nike zuwa ina siyo mata magani a duk lokacin da tace tana jin ciwon ƙirji, daga baya da abin ya matsa mata sai muka kaita chemist likita ya duba ta ya bata magani, tun daga lokacin gaskiya ta warke”

Murmushi yayi cikin nutsuwa ya kalleni yace.

“Bahiyya baku san bambancin asibiti da chemist ba ne shiyasa, baku kaɗai ba mutane da yawa basu san bambancin tsakanin asibiti da chemist ba. A Nan asibiti muna da kalolin likitota sun fi a ƙirga, misali ;ni yanzu likita ne na zuciya, duk wani abinda ya shafi heart is my field, akwai likitan yara wanda shi harakar ciwon yara ne kawai ya sani, akwai likitan kunne, akwai likitan ƙashi, akwai likitan ido, akwai likitan tiyata shi aikin tiyata kawai ya sani, akwai likitan matsalolin mata duk abunda ya shafi ciki da haihuwa da reproductive system complication Shi ya sani, kowa da irin aikin sa da irin abinda ya karanta ya ƙware a kai, idan kika zo asibiti akace miki dukkan waɗannan conditions ɗin da na ambata da ma wanda ban ambata ba akace miki mutum ɗaya duk yake managing ɗin su renin hankali ya shigo ciki ko bai shigo ba?”

Cikin gamsuwa da bayanin sa na gyaÉ—a kaina alamar Eh haka ne.

Yace.

“To mai chemist Kamar haka ya ke Bahiyya duk kalar ciwon da za'a je mai da shi kai tsaye zai karɓa ya bada magani ko maganin yayi daidai da ciwon ko bai yi daidai ba shi dai kawai ya bayar, in ya bayar da abinda ba'a nan ya kamata a bada shi ba kinga shi kenan ya sanya rayuwar mutum a matsala, ba zai taɓa kallon condition yace ayi asibiti ba sai ya gwada yin karambani to sai kiga idan ba'a dace ba kuma an ƙara shiga wata wahala. Saboda haka ku riƙa kiyaye wa ku riƙa zuwa asibiti duk lokacin da kuka ji matsala, bance kada kuje gun mai chemist ba, amma sai idan an rubuta muku magani daga asibiti kuka ga can yafi sauƙi sai ku je ku siya idan yana da shi shine zaman lafiyar ku....”

Hannu ya miƙa ya janyo folder ɗinta ya buɗe ya bani duk gwaje gwaje da hotunan da aka yi mata yace.

“Wannan shine sakamakon gwajin da aka yiwa mahaifiyarki, sakamakon hawan jinin da take da shi yayi yawa har ya kai ga taɓa jijiyoyinda ke harɓa jini zuwa ga zuciyarta sunyi blocking wanda ake kira (Coronary artery diseases) wannan ya samu asaline sakamakon rashin samun cikakkiyar kulawar likita da kuma rashin bin ƙa'ido jin shan magani. Idan mutum yana da High BP abinda ke kawo irin wannan ciwon nan take ya haɗa da; yawan damuwa ta ƙololuwa, rashin samun wadataccen bacci, rashin motsa jiki da sauran su...”

“InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Allahumma ajirni fi musibatina wa akhlufni khairan minha”

Abinda na ke ta nanatawa kenan yayin da idanuwa suka ci gaba da tsiyayar da Hawaye marar misaltuwa.

“Bahiyya! ba kuka zaki yi ba a yanzu mafita zaku nema, a gwaje gwajenda muka gabatar ya nuna sai anyi mata wani aiki da ake kira Coronary artery bypass grafting (CABG). Wanda idan anyi shi shine zai taimaka jijiyon su buɗe jini yaci gaba da gudana yanda ake buƙata”

Cikin damuwa Malama Rabi tace.

"Yanzu likita aikin zai iya kaiwa naira nawa??

" While CABG procedure ta kasu kusan gida huɗu, sannan ko wane da kalar irin kuɗin da ake yin sa wanda ni dai a sanin da nayi mishi gaskiya a nan gida Nigeria ana yin sa, 4-8 million, akwai na 5-10 million, akwai na 6-12 million a sanin da nayi mishi amma ban sani ba ko yafi haka a yanzu, sai mun bincika munji....”

Kafin ma ya iyar da rufe bakin sa ban san lokacin da na yanke jiki na faÉ—i somammiya ba.

*************

Hanifah

Tunda taji shawarar Rasi sai ta ɗan ji maganar ta shige ta kaɗan, shiyasa tunda ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye tana neman mafita. Kwana tayi zaune cikin internet tana ta searching tana samun bayanai da wankin ƙwakwalwa akan tana so ta haihu da mijinta ba tare da wahala ba amma bata san ya zatayi ba nan tayi ta samun bayanai kala kala har ta zo kan Surrogacy, sai da ta karanta bayanai da kyau wanda ya sanyata taji har cikin ranta cewa ta gamsu da wannan hanyar. Gari na wayewa ta wuce wurin Family doctor ɗin su wato doctor Nicholas.........

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

               *BY*

*AMINA IBRAHIM*

  *(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ÆŠIN KUÆŠI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

          *BABI NA TAKWAS*

Nicholas Clinic and

            Maternity Hospital.

                  Kubwa, Abuja

 

  Zaune ta ke office ɗin Dr. Nicholas, Bayan sun gama gaisawa ta yaɗa masa manufarta ba tare da wani tunani ba.

Tunda ta fara magana Nicholas ke murmushi yana ta hasaso abubuwa na wauta irin na Mrs mai gishiri.

Bayan ta gama ya kallleta yace.

“While! you made a very sound decision, but Mrs. Mai gishiri i want to explain what surrogacy actually means. So that you may be able to decide what will be best for you and your family. Surrogacy mostly is for the couples who are infertile dealing with inferlity complications waɗanda suka kasa achieving pregnancy due to may be ga macen ne take yawan samun recurrent miscarriage, cancer or pelvic surgery, premature ovarian failure da sauransu, ko kuma may be ga mijin ne ya ke da problem na low sperm count or poor sperm quality, Ko kuma erectile dysfunction. Waɗannan suna daga cikin dalilai da suke sa ayi Surrogacy. But you Mrs. Mai gishiri and your husband doesn't have any problems,so to me, my suggestion for you shine kiyi haƙuri ki haihu da kanki, since you are not facing any challenges, you can do it......”

Da sauri ta girgiza kanta tace.

“Doctor Nicho, I have already made my mind, so I just need your help and please don't let my husband know about this until I decide to tell him my self. Yanzu ya ka ke ganin za'a yi, miye way out, zai yiyu ko ba zai yiyu ba ?”

With full confidence yace.

“Zai yi yu mana, sai dai akwai kuɗi sosai...”

Hanifah tace.

“No don't worry money is not a problem”

Yace mata ba damuwa, nan ya shiga yi mata bayani tiryan tiryan yadda procedure É—in ta ke da duk process É—in da za'a bi wurin ganin anyi achieving abunda ake so, but akwai high risk complications especially abortion, multiple gestation more than one, two, or even triplets.

Cikin gamsuwa da bayanin sa tace.

“I understand, to yanzu idan har buƙatar hakan ta kasance, a ina zan iya samun wadda zatamin in biya ta? You know it cewa kunfi hulɗa da mutane daban daban, I think you can get someone to do that for me right?”

GyaÉ—a kan shi yayi yace.

“Since cewar akwai kuɗi, I will find some one for you”

“And which country do you think is the best to perform the procedure successfully, or can we go to UK?”

Yace.

“Yes, UK suma sun ƙware sosai wurin wannan aikin, may God help you”

Miƙewa tayi cikin farin ciki tace.

“Thank you so much doctor Nicholas for the help, Idan har buƙatar hakan ta taso zan nemo ka, sai muji ya za'a yi”

“You are must welcome Mrs. Mai Gishiri, till I hear from you”

Daga haka ta fito hospital ɗin driver ya tuƙa ta zuwa gida.

****************

BAHIYYA

Tunda likitan ya shaidamin zunzurutun uban kuɗin da ake da buƙata domin ayi wa mama aiki ban sake sanin ina kaina yake ba, sai da na farka na ganni kan gadon asibiti.

Da ƙarfin tsiya na juya na hantsilo ina mai ƙara rushewa da kuka nace.

“Miye na wani ɗora ni akan gado, ni ba wannan gadon ne buƙata ta ba, Mama ta ni ke buƙata malama, dan Allah ki gayamin ina zan samo wannan kuɗin kaf a faɗin duniya? Ko kurkukun gidan mu aka siyar ba zai biya ko kwatar kuɗin da aka nema ba. InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Yah Allah kai ne Mahaliccin mu, kai ne kafi mu sanin daidai a cikin rayuwar nan tamu, yah Allah ka kawo mana mafitar wannan masifar da ta kunno mana kai”

Rungume ni Maman Walida tayi cikin tausayawa tace.

“Bahiyya kin riga kin gama magana tunda ki ka ce Allah, in sha Allah shine manyasha'u shi zai yi muku mafita”

Murya malama na tsinkaya tana faÉ—in.

“Bahiyya kiyi haƙuri in sha Allahu zata samu lafiya”

Juyowa nayi da rinannun idanuwa da suka gama canza launi tsabar azabar kuka nace.

"Malama ta yaya? Gaban ki fa likita ya ambata mana zunzurutun kuɗi da bansan adadin su ba, bamu da kowa sai Allah, nasan haka zata mutu ta barmu mu biyu, kaico..”

“Tashi kije kiyi Sallah zuhr ki zo mu tattauna mafita, wannan kukan bashi da wani amfani a yanzu”

Ina dirowa daga kan gadon na wuce ɗakin da Mama ta ke kwance na tsaya bakin ƙofa ina ƙare musu kallo daga ita har Nuhaira wanda su basu san cewa ina wurin ba. Wani abu mai ɗaci naji ya zo ya tare mini maƙogwaro na, girgiza kai kawai nike ina ƙara jin wani sabon tausayi da ƙaunar mutum biyu ɗin nan suna ƙara yiwa zuciya ta ƙawanya. Idan muka rasa Mama ina zamu shiga kuma a duniyar nan?

Jin wani sabon kuka na neman ƙara ƙwacemin yasa nayi saurin janye jikina na wuce wurin ɗoro alwala.

************

Farooq

Duk gudun Hanifah da ya ke ba wai yana yinsa ne cikin daɗin rai ba, sai dai kawai yana so ta amince da buƙatarsa su samu ɗa tare kamar yadda Mahi ya bashi shawara, shi a plan ɗin sa Idan har ta amince ta haihu wata ƙila zasu iya samun fahimtar juna yadda yake so, idan ta haihu it may be ta fara sanin muhimmancinsa da kuma bashi damar da zai ji cewa yes shi ɗin mijinta ne. Domin abinda tayi masa ranar da ta dawo Nigeria tayi matuƙar bashi Mamaki, taya za'a ce duk tsawon lokacinda suka ɗauka basa tare saboda kawai ya yi mata zancen haihuwa zata hau dokin zuciya har ta iya barinsa tayi tafiyar ta ɗakin ta, to shi dutse ne da baya da zuciya a cikin ƙirjinsa ko ya ya?

Shiyasa kawai ya bata iska wata ƙila nisantar ta zaisa taji ko kaɗan ne a cikin ranta cewa tayi masa ba dai dai ba. Allah ne shaidar sa da irin tsananin son da yake yiwa HANIFAH, ya na so su rayu cikin soyayya da kulawar juna, yayi mata duk abinda take so haka shima tayi masa duk abinda yake so

amma ita sam bata gane hakan a wurinta ba abu mai yiyuwa ba ne, saboda haka he must take action Ko da zai sa ta shiga hankalin ta.

Idan yana tuna irin stories É—inda Madinat ke basa dangane da rayuwar ta da mijinta Modu sai yaji ina ma ace Hanifah zata amince suyi irin wannan rayuwar tare da juna.

Ya jima tsaye a balcony É—in gidan nasa kafin daga bisa ni yaja É—an guntun tsaki ya shige cikin gidan, turus sukayi suna masu kallon juna tamkar yau ne ranar haÉ—uwar su ta farko.

Murmushin yaƙe yayi mata wanda iya ka cinsa kan leɓensa sannan yace.

“Hi..”

Da gudu taje ta rungume sa tare da sakin wani rikitaccen kuka tana faÉ—in.

“Why? Why are you doing all this to me? Farooq Ko ka daina so na ne ka faɗa min inji?”

Jin yanda take kuka yasa zuciyar sa jin wani irin ba daÉ—i.

Hannayensa ya sanya ya zagaye bayan ta a hankali yace.

“Idan na daina sonki wa zan so a duniyar nan? You are my heart beat Hanifah, da sonki kaɗai zuciya ta take bugawa. So ni ke mu haihu Hanifah, idan har kina so na kasance cikin farin ciki to tabbas ki amince ki haihu dani”

Janyewa tayi ta koma jikin faÉ—eÉ—iyar windown palourn tana mai zurawa waje ido tace.

“Sai naji kamar zan iya Farooq sai kuma zuciya ta tayi ta nuna min ba haka ba, ɗan Allah Farooq kayi haƙuri.....”

“No Hanifah, ni a yanzu shine kaɗai ni ke so daga gare ki”

Cikin ƙara ji tace.

“Toh let's adopt a child mana, zamu iya, yes we can get as many children as we want Saboda muna da dukiyar da zata iya bamu ko adadin 'ya' ƴa nawa muke so...”

Runtse idanunsa yayi tare da girgiza kansa sannan ya buÉ—e yace.

"No Hanifah! That's not part of my plan, ba zan iya adopting child ba as far as ubangiji na ya bani lafiyar samun yara bani da wata naƙasa....”

Rintse idanunta tayi tare da yarfar da hannuwanta alamar zancen ya fara harzuƙa ta tace

“OK... OK! We can get a child through Surrogacy, Hakan yayi maka?”

A matuƙar mamakance ya kalleta yace.

“What!..”

Da sauri ta zo ta zauna in da yake zaune tare da cukuikuye hannunsa ta karyar da wuya in a pleading tone tace.

"Dan Allah mana Farooq ka amince. Ƙwanmu dai ka ke so ka gani a duniya ko? To we can achieve it through Surrogacy, Sperm ɗinka za'a haɗa da Egg ɗina a dasa cikin mahaifar wata macen in 9 months data haife mana shi kenan sai ta kama gabanta...”

“No Hanifah...”

Wani Sabon kukan ta sake fashe masa da shi, tana faÉ—in.

“Dan Allah mana Farooq! Dan Allah ka amince, matuƙar kana sona kana kuma son farin ciki na to ka amince.”

A duniya cikin abubuwan da Farooq ya tsana a rayuwar sa akwai kukan Hanifah ciki, baya son kukanta ko kaÉ—an baya so.

Ba tare da wani tunani ba yace.

“Shi kenan na amince. But yanzu a ina kike ganin zamu samun macen da zata amince tayi mana wannan sacrifice ɗin.”

Cikin murmushin nasara tace.

“No kar ka damu, just leave everything in my hand, Ni zan samo macen da kaina, babu zancen sacrifice a nan tunda biya zamuyi, kawai dai everything have to be in secret between us daga zaran 9 months yayi ta haife sai ta kama gabanta”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.

“OK. Allah yasa a dace”

“Amin sweet heart, let me ask Nafisat to prepared table for us, today is a special day to us. Thank you”

Murmushi yayi mata yace.

“Thank you too Hanifah, I love you”

Matsowa tayi gab da shi ta yi brushing lips É—inta da na shi sannan ta kalle shi tace.

“Na miss I dey miss you Love”

Miƙewa yayi cikin jindaɗi ya miƙa mata hannu yace.

“Shall we?”

Itama hannun ta miƙa masa suka nufi sashen sa, da taimakon ta yayi wanka yau tana tare da shi har ya gama shiryawa suka zo dining yaci abinci, sannan suka wuce nata ɗakin itama ta shirya. Soyayya suka sha abinsu tamkar wani abu na ɓacin rai bai shiga tsakanin su ba, Farooq ya zage ya nuna mata irin yadda yayi mugun missing ɗinta,That's her sweet test wanda yake mugun driving ɗinsa crazy, ga taushin fatarta da take shan gyara kullum da kuma haɗaɗɗen ƙamshinta mai canza duniyar sa zuwa wata duniya mai wuyar fassarawa.

A daren ranar through out tare suke maƙale da juna ta zamto masa wata kalar Hanifah ta daban tamkar yau ya fara sanin ta.

Da gari ya waye tana gama shiryawa suka yi break fast shaf-shaf ta É—auko Jakarta ta na dariya ta kalle shi tace.

“Mission started, so I need your absolute support”

Murmushi yayi yace.

“My support is always there with you Hanifah, bye bye”

Daga haka ta fice.

Tun a hanya ta kira Doctor Nicho tace mishi she's on her way coming ya samu matar, yace mata ya samu, cikin farin ciki tayi mishi godiya kafin ta ƙara sa.

Tana zuwa kuwa ya tarbeta, bayan sun gaisa yace.

“She's Agnes by name, er asalin jihar Oyo ce, ta amince ne bayan na gabatar mata da manufarki.....”

“OK.. Bani Account na ta in fara bata kafin alƙalami”

Ba musu ya janyo wayar sa ya buÉ—e details É—inda already ta riga turo mai ya bata account number É—in take yanke ta tura mata 5million.

Ba'a fi minti biyar ba sai ga kiranta ya shigo wayar Doctor Nicho, Hanifah tayi zaton godiya zatayi kawai ta ji ta fara bragging cewa mi ta ɗauke ta ne talaka ko me, kamar ita da girman ta tana neman irin wannan sacrifice ɗin amma ta tura 5million wannan ai abin kunya ne, ya faɗa mata kuɗin aikin ta tunda har lafiyar ta ƙalau haihuwa ce bata so to zata bayar da 100 million idan yayi mata to idan kuma bai yi ba shikenan.

Da sauri Hanifah tace.

“Tell her that I will pay the money, kawai ta zo a fara shirye shirye.”

Bayan ya gaya mata abinda Hanifah tace, sai tace. Ita yanzu haka ma bata ƙasar, su jira idan ta dawo zata neme su but ta tura kuɗi kawai idan zata tura. Kai tsaye ta sake ca ke mata 45 plus wancan ya zama 50,tayi mata godiya tace sai taji daga gare ta.

Godiya ta sake yiwa doctor Nicho tace yanxu shi take jira taji daga gare sa su a shirye suke.

*************

BAHIYYA

A Yanzu kallo ɗaya zaka yimin ka fahimci cewa bana cikin hayyacina sakamakon gigicewa da ɗimautar da na shiga wurin neman kuɗin da za'a yiwa Mama aiki. Yanzu haka a kan magani take wanda a ƙalla anci kuɗi sunfi dubu dari uku. Malama Allah ne zai saka mata da mafifin alheri ita da mijinta domin kuwa sun dage wurin neman mana taimako wanda sun haɗa kuɗi yakai dubu ɗari bakwai, shima likitan namu doctor Samuel wanda ake kira doctor Sam ya taka rawar gani sosai wurin ganin cewa ya haɗa mu da ƙungiyoyi masu taimakawa marasa lafiya marasa ƙarfi, wanda a yanzu an haɗa mana kuɗi sunkai million ɗaya da rabi.

Nayi yawon nayi yawon har takalmin ƙafata sai da ya tsinke, yawo nake lungu lungu kwararo kwararo ina neman taimako amma ban iya haɗa ko dubu ɗari ba duk tsawon kwanakin nan, nayi ta gwada numbern Baba Maharazu amma shiru bata shiga tamkar malam yaci shirwa.

Har Gusau na shirya na tafi in da muka baro ko Allah zai sa a dace in samu Baba Maharazu da kuma mutanen unguwar mu ko zan samu wani taimako amma abin ba sauƙi saboda mutane rayuwar kowa ta kansa yake, haka dai suka yita yi muna addu'ar samun mafita ƙarshe sai maƙoncin mu ɗaya ne ya bani dubu ashirin yace dubu goma in yi na mota dubu goma kuma muƙara mu sayi magani.

Duniyar tayi min zafi, gabas da yamma kudu da arewa na duba na waiga na hanga amma babu wani sauƙi sai a wurin Rabbis-samawati.

Yau ma haka ne na gamo bilin bito na ban samu uwar komai ba sai tsabagen yunwar da ta addabi ciki na sai ƙugi yake, duk kuɗin mu sun ƙare komai yanzu sai a hankali ga asibitin kullum cikin bani bani.

Ɗakin na turo na shigo, a rakuɓe na hango Nuhaira gefe da alama bacci ɓarawo ne ya biyo ya saceta, domin ita na faɗa mata kada ta ɗaga ko ina, ko wane lokaci dole ta kasance tana kusa da Mama.

“BAHIYYA!”

Da gudu naje gare ta jin ta kira sunana, na fashe da kuka nace.

“Sannu Mama, in sha Allah zaki samu Lafiya ba jimawa..”

Girgiza kai tayi tare da sakin wani murmushin da yafi kuka ciwo tace.

“Bahiyya, abinda nike so in faɗa miki, ko da ta Allah ta kasance a gare ni, ki kula da ƙanwarki ku kuma tsare mutuncin ku duk wuya duk tsanani, sannan ku gwada tafiya tushen ku....”

Gefen yagalallen hijabi na na saka na share sabbin hawayen da suka gangaro min nace.

“Dan Allah Mama ki daina zancen mutuwar nan, wallahi a duk lokacin da kika ambaci mutuwa ki na mugun ɗaga min hankali. Shekara ɗayar nan da mukayi babu Baba ki duba yadda Rayuwa tayi mana juyin masa, Ina ga ace kema babu ke, duk kika tafi ki ka barmu Mama baki yi mana adalci ba, wallahi baki yi muna adalci ba, Ina kike so muje....”

A hankali Mama tace.

“Kayya Bahiyya! Ta Allah ai itace haƙƙun...”

Hannun ta na riƙe na kalleta nace.

“Na sani Mama, amma in sha Allah ba zaki mutu ba, sai mun samu kuɗin aikin nan an yi miki kin tashi da yardar Allah”

"Allah yasa haka Bahiyya, na gode, Allah yayi muku albarka”

“Amin Mama, dan Allah ki daina godiyar nan Mama”

Wani irin ƙarfi ne naji ya shige ni, duk wata yunwar da nikeji naji ta bar ciki na, miƙewa nayi ba tare da na san ina na nufa ba na fito daga cikin asibitin nayo kan titi. Lokaci guda tunani ya harɓa a ƙwakwalwa ta na cewa in tafi gidan Maman Khadijat mana, ai sati ɗaya ne tace zata yi nasan yanzu ta isa dawowa ko ban samu duka ba na ɗan rage wani abu ai zai fi.

Kai tsaye na yiwa gidan Maman Khadijat tsinke, a bakin gate ɗin unguwar su aka tare ni domin ban taɓa zuwa nikaɗai ba sai tare da malama da roƙo da magiya da komai na samu aka yi nasarar yin waya gidanta jin an ambaci sunana suka barni na tafi.

Ina shiga maman Khadijat ta tsuramin na mujiyarta ko ƙyaftawa babu. Bayan ta gama kallona murya a karye tace.

“Bahiyya what happened to you? Kin ganki kuwa?”

Ban tsaya nauyin baki ba na feɗe mata tun daga biri har wutsiya ban rage mata komai ba, a ƙarshe na fashe mata da kuka ina magiya nace.

“Ki yiwa Allah maman Khadijat ki taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeki ki taimaka mana da ko nawa ne Allah ya hore miki.”

Guntun hawayen da ya sauko mata ta share tare da tasowa daga inda take zaune ta É—ago ni tsaye tace.

“share Hawayen ki Bahiyya, in sha Allah daga yau matsalar ku ta ƙare har abada, ni zan biya miki duka kuɗin in sha Allah, fatar mu ubangiji Allah ya bata lafiya yasa ayi aikin cikin nasara”

Bansan lokacin da na kai mata wata iriyar cakuma ba, na riƙe ta gam ina ta sabbatu wanda ni kaina ban san mi nike cewa ba.

Daga ƙarshe ta janye jikinta tace.

“Zauna ina zuwa yanxu”

Mai aikinta ta saka ta kawo min lafiyayyen abinci tace in cinye tana zuwa in bari ta shiga ta shirya ta fito mu tafi. Ni kam jin matsala ta tazo ƙarshe na zage na cinye abincin ras na kora da ruwan lemu.........

*OUM AMEER*

💝 *BAHIYYA*💝

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*BY*

*AMINA IBRAHIM*

*(OUM-AMIR)*

*BAHIYYA NOVEL ÆŠIN KUÆŠI NE KIBIYA 500 TA WANNAN ASUSUN 3132703269 FIRST BANK AMINA IBRAHIM SAI KI TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08068974831*

*FREE PAGE*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.