Alkawarin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Alkawarin Zuciya by M Shakur Cmplt.txt
Chapter 58 of 75
“Mara mutunci wai bazaki zo wajena ba” parking tayi awajen parking sanan takashe motan tabude tafito ahankali waya na kunenta still tana sauraron labarin da Batool kebata awaya, sanan tasa hannu tadauko jakanta da ledan goron Gwaggo kafin tadauki gyalenta dake kan sit tarike a hannu shima sanan tamaida kofan tarufe tafara tafiya tana murmushi tace “are you serious Batool, yanzu yaushe zasuzo asa ranan I am so happy for you Batool” tai maganan tana kokarin saka hannunta tabude kofan dakin Gwaggo daidai anrigata bude dakin, Amal da Khadija suka fito dagudu dan Gwaggo ce tabiyosu sata sukai mata ko kadan basusan da ita ba suna bude kofan suna fitowa aguje suna bugeta wani irin ihu tayi daga jakanta wayanta dake kunnenta da car keys din hannunta zubewa sukai akasa itama tai wani irin baya zata fadi dan gabaki dayama tasadakar faduwa zatayi chak taji an tarota bayanta yafada kirjin mutum hannunshi gabaki daya kan flat cikinta ta kankame idanunta gam sabida yanda ta bala’in tsorata ahankali ta furta “Ya Aliyu” danshi kawai yafado mata arai yanda he always hold her idan zata fadi, tsayawa chak Amal da Khadijan sukayi jikinsu narawa suna kallon Gwaggo datafito arude tace “Innalillahi badai ihun Khairy naji ba zubarmin da diya kukayi” murya dakuma kamshin turaren da bazata taba manta kalanshi ba da jikin datasaba jinshi ba yasa ahankali tashiga bude idanunta tadaurasu kan Gwaggo dake gabanta tana kallonta, dasauri Gwaggo tace “sannu Khairiya da Aliyu bai tareki ba dakinyi mummunan faduwa barayin banza kawai ku kwashemata kayayyakinta” ahankali tagyara tsayuwanta jikinta narawa gabanta nafaduwa sotake tajuya takalli Aliyun amman takasa tsoron yin hakan ma take tanajin beating heart dinshi abayanta, gently taji yana zare hannunshi dagakan cikinta kafin yacire gabaki daya, gently taji yaraba jikinshi da nata yajuya dasauri, dasauri Gwaggo tace “bazuwa kayi kasha furan ba dakace nadama maka” kaman daga sama Ummulkhairy taji maganan Aliyu.
“Nafasa sha adakin ki, kiba yaran nan sukawomin” Dawani irin sauri Ummulkhairy tajuya tadan saci kallonshi bayanshi kadai ta iya tagani dudda bataga fuskanshi ba gani tayi yakara wani irin haske gashin kanshi yakara yawa kaman tunda yaje baiyi aski ba gashin yay baki sun nannade looking so coily, hannunta dataji an kama yasa dasauri tajuyo Gwaggo ce tana rikeda kayayyakin ta dasuka fadi akasa tace “wuce muje kukuma barayi duk wacce tashigomin daki wlh saina chanza mata kamanni” dariya su Amal sukayi suka wuce flat din Mami abinsu.
Suna shiga daki Gwaggo tace “dazu kina tafiya Saloon mijinki na dawowa nai nai da shegun yaran nan sukiramin wayanki nace ki dawo sukaki, zoki kaimai furanshi flat dinshi kidawo” kallon Gwaggo tayi dasauri hakanan taji gabanta nafaduwa kwaryan furan Gwaggo tabata data rufe ahankali takarba tana kallon Gwaggo, Gwaggo tace “wuce ki kaimai tunda yadawo baici komi ba yanzu ma da kyar nasamu yace zai sha furan, tafi kafin yay fushi” Gyadamata kai tasake yi sanan ahankali tajuya jikinta rawa yake sosai tafice daga dakin tai flat din Ya Aliyun kirjinta na bugawa more the more she’s getting closer to flat din, tsayawa tayi agaban kofan takasa motsi ahankali tadaga hannunta knocking kofar tayi shiru babu wanda ya amsa babu wanda yabude mata takai kusan 3min ahaka sanan kaman wacce tazo sata tasa hannunta tabude kofan ahankali tana kallon falon ganin bataga kowa ciki ba yasa ahankali tashiga cikin falon dakenan sanyin Ac mix da kamshin turarenshi, ahankali takai kwaryan furan kan centre table na dakin tsugunnawa tayi ta ijiye sanan tamike tsaye dasauri tajuya zatai kofa tafice kaman daga sama taji muryan Ya Aliyu yakirata. “You!” Chak ta tsaya batare daya juyoba gabanta nafaduwa sosai, cikin wata kalan murya da she will define it more of hatred voice yace “zokidau abinda kika ijiye and take it out” gyadamai kai tayi ahankali sanan tajuyo batare datama iya dagakai takalleshi balle tamasan daga ina yakamata maganan ba sanan tazo ahankali ta taugunna tadauki furan sanan tamike tsaye. “Next time idan tanason naci kome tamin tabama wani yakawomin not you” wani irin sanyi jikinta yayi dasauri tadaga idanunta dasuka wani cikeda hawaye ganinshi tayi yana tafiya akan stairs zai koma sama bakinta harwani rawa rawa yake tace “Ya…..Ali….yu” chak ya tsaya batare daya juyo yakalleta ba, ahankali takai dayan hannunta dat is very tashare hawayen dasuka zubomata sanan gently tace “Ya Aliyu I am sorry, dan Allah kayafemin”
6️⃣3️⃣
Wucewa sama taga yayi abinshi batare daya juyo yakalleta ba, tadade tsaye awajen sanan ahankali tajuya tafice daga dakin rikeda kwaryan furan jitayi babu abinda kemata dadi, dakin Gwaggo tashiga ganinta da kwaryan furan yasa Gwaggo tace “ya shanye”? Girgixama Gwaggo kai tayi tace “yace bazai sha ba” cikeda masifa Gwaggo tace “shiya sani ijiye kije kihuta abinki kinji” ijiyewa tayi sanan tawuce dakinta tana shiga tafada kan gado kwanciya tayi dasauri tafashe da kuka sosai murya chan kasa tace “he hates me, he hates me” tama rasa mezatayi wayanta da Gwaggo ta ijiye mata akan gado ta dauka sanan tai dialing number Batool tana kira tadauka tace “maiya sameki dazu naji kinyi ihu haka faduwa kikayi” kasa magana tayi kawai tafashe da kuka cikin kuka sosai tace “Batool Ya Aliyu yadawo ya tsaneni sosai, Batool I don’t even know what to do dan Allah help me, kinji” yanda taji tana kuka yasa Batool tace “batun yauba bayan kin bani labari what u told him nagayamiki kinyi kuskure Khairy that’s not how to make him rabu dake, but that one now is bygone, yariga yafaru Khairy rana daya so baya komawa yazama ki, bansan Aliyun kiba kene kika sanshi, kinsha bani labarin fushin shi da Kishin shi, Aliyu na sonki har gobe har jibi so ma mai karfi kuwa, you should just be diplomatic about it, kinunamai kin waye u are a graduate, cikin sauki kija ra’ayinshi make him come for you batare dayasan he’s even coming for you ba, you know his weak point, karki bada mata please, zan turamiki number M shakur kibiya kudi ki shiga group din matan aurenta kiga yanda ake karkato da hankalin muji mai taurin kai stop crying kinji kiyi wanka pray kije ki nemi abinda zakici” gyadama Batool kai tayi ahankali murya chan kasa tace “thank you” katse wayan Batool tayi hakan yasa ta ijiye wayan share hawayenta tayi tass sanan tasauka daga kan gadon, ahankali tawuce bayi bayan tacire kaya tana kallon kalaban da akamata dasukai bala’in kyau kaman anmata kafin attachment nan ko gashinta ne, hannunta tanunama madubi ta kalla shima yayi kyau sosai sanan tawuce tai wanka tadauro alwala tafito daure da towel akirji tabude wardrobe wani rigan bacci pink tasaka daya saukan mata zuwa guiwanta, rigan bacci yazo dawani open cap dinshi hakan yasa ta ijiye cap don kan gado tahau kan dadduma tai sallan magrib, tana idarwa wayanta tadauka takira Ya Maheer sunata hira sai wajen isha’i sanan sukai sallama ta tashi tai sallan isha’i, jin cikinta na kuka dan saida yanzu ta tuna tun wainan safe bata sakecin wani abu ba yasa ta tashi hulan kayan baccin tadauka tasaka ipen cap ne hakan yasa duka gashinta yazubo gadon bayanta, tai kaman wata Cinderella, silipas dinta na gida tazura akafa sanan tabude kofa tafito ko kadan batasan Aliyu na falon ba saida tafito falon, da kallonshi kadan tayi tadauke kanta dasauri sai yanzu nema taga fuskanshi woww! Wlh kaga Ya Aliyu zaka dauka balarabe ne gashin gemunshi da sajenshi sundan kara yawa kadan daya haskaka fuskanshi, yana kwance kan dogon kujera waya a kunnenshi yana magana ahankali, kallo daya tamai tadauke kai dasauri Gwaggo dake binta da kallo tace “indomie ko Khairiya”? dan murmushi tayi akunyace dayar karaman muryanta tace “Gwaggo Kwai zan soya” tai maganan zata shiga ciki dan kunya takeji Ya Aliyu yaganta ahaka daga ita sai Yar rigan baccin da pant da tasaka aciki ko bra bata sakaba, ganin zata komaciki yasa Gwaggo tace “ina kuma zaki yoo ba kitchen zakiba tundake bakicin abincin da normal mutane keci” ahankali tace “Gwaggo hijabi zan dauko” baki Gwaggo tasaki tace “yau kuma nikike sama hijabin koko mijin naki Hydar, wuce kitchen kije kinemi abinci kisama cikin ki kafin ciwon yunwa yakamaki” gyadama Gwaggo kai tayi sanan ahankali tafito tawuce feeling so uncomfortable tana tafiya kafafunta na harhardewa, daga inda yake kwance dudda waya yake but all abubuwan da Gwaggo kefadi yanaji, kasa hana kanshi yayi yakalleta dan satan kallonta yayi sanan yamaida kanshi kan wayan dan bayason yana kallonta motsamai da soyayyanta yake aranshi, juyowa Gwaggo tayi tana kallonshi cikeda korafi tace “ni babanka yamazo yay maganan bikinku akaita chan gidanka, yarinya batacin abinci salon wani abu yasameta ace nine bana bata abinci Iyye ni wlh banajin dadin wanan lamarin ko kadan, tun safe fa waina biyu kawai taci bata karacin wani abu ba” kofan da aka bude yasa tajuyo ganin Meena ne yasa ta watsa mata harara tace “munafuka dayake yayanki yadawo dole na ganki a bangarena to fita” dariya Meena tayi tashigo wata kyakkyawan budurwa dake kama da Mami biyeda ita tace “Hajo tazo hutu gidanmu shine fa nakawota ta gaidaki, Mami tahanamu dafa indomie a kitchen dinta shine mukazo mudafa anan” tai maganan Meena na zama kusada Ya Aliyu da gama wayanshi kenan yana kallon Meena, Hajo datadan saci kallon Aliyu tashigo tana gaida Gwaggo da Ya Aliyu dabai amsata bama sai tambayan Meena su Amal dayake tacemai sunyi bacci sanan ta tashi takalli Meena tace “zomuje mudafa” wucewa kitchen din sukayi Gwaggo na ihu karsu bata mata kitchen ganin Khairy a kitchen tana soya kokarin soya egg guda daya tahada tea a mug tana juyawa da cokali yasa Meena tajuya cikedajin haushi tace “zomuje” dasauri Hajo takalli Khairy da itama kallonsu taje batare data kulasu ba tace “akan mene muda kitchen din gidanmu zamu tafi” dan tana ganin Khairy tagane matan Ya Aliyu ce dantaga video bikin da akayi a gidan nan, wucewa Meena tayi tafice tace “to nidai ina falo kika dafa saiki kawo mana muci” tai tafiyanta itakuma Hajo tashigo kitchen din tana daukan tukunya daya dan tara ruwa tana habaici, “adai gama yawo da kaya babu breziya bazamu so mutum ba, dazu inaji rokonshi ake yama zauna da ita yanaki aikin banza” tafashe dawani makirin dariya, dudda maganan ya sosama Ummulkhairy rai batace komiba besides bamatasan waye yarinyar ba, juya kwanta tayi sanan tawuce tadauko plate tazo ta kwashe itakuma Hajo tadaura ruwa agas din tanabin Ummulkhairy kallo da gefen ido ganin yanda yarinyar keda shape dakuma diri ga kirji kaman zasu fasa riga atsaye fam dasu hada komi Ummulkhairy tayi a tray tazo zata wuce da gangan Hajo tazo dabaya dabaya kaman mai neman abu ta bangaje Ummulkhairy da saura kadan tafadi tai maza ta dafa fridge dinsu amman gabaki dayan tray da kwan ta dakuma shayinta saida yazube akasa da tray abin suka hadu sukai wani bala’in kara dayasa Gwaggo tai ihu daga falo tace “meya faru wayamin bari a kitchen!” Takalli Aliyu tace “dubomin kitchen dina dan Allah”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.