Alkawarin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Alkawarin Zuciya by M Shakur Cmplt.txt
Chapter 4 of 75
PROMISE OF THE HEART đ
âđ»M SHAKUR
4ïžâŁ
Kafin ma Baba yabude kofa tasa hannu tabudemai kofan jikinta har rawa yake tanajin dadi. âBaba oyoyo, Baba sannu da zuwaâ wani magidancin mutum ne babba sosai yana sanye da babban riga yanada gemu dayacika da furfura, ga kuma katon ciki irin na manya wayanda suka manyanta dinan, exactly idanunsu iri daya da ita manya saidai nashi daya soma kankancewa sabida tsufa, wani kalan kyayataccen murmushi yasakin mata, cikin kamilallen muryanshi irin na magidantan nan yace âyarinyar Babantaâ yay maganan yanajan dan hancinta, murmushi tayi sosai tace âsannu da zuwa Babaâ fitowa daga motan yayi yace âto akwasomin kaya akai cikiâ gyadamai kai tayi tace âto Babaâ yawuce yana kallon yaranshi maza su uku da duk suke tsaye suna jiran fitowanshi, Manaf wanda yake Babba yanada 27yrs, sai Muâaz shima 27yrs twins ne shida Manaf saidai ba identical twins ba ko kadan ma basuyi kamaba idan baa gayamaka yan biyu bane bazama ka yardaba, Manaf na kama da Mama, Muâaz na kama da Baba, sai Maheer dakenan 24yrs, dukansu sun gama makaranta duk a company Baba suke aiki yanzu.
Gaida Mahaifin nasu sukayi cikeda girmamawa kana ganinsu kaga yaran dakeda tarbiya dakuma natsuwa. Cikin so da kauna ya amsasu yana tambayan kowa ya aiki sanan suka wuce masallaci, itakuma kayan Baba su files da wasu yan tarkace tafito dasu daga motan sanan tai cikin gida.
Sama tayi direct zuwa lafiyayyen hadadden falon Baba, ijiye kayan tayi sanan tajuyo tabude kofa ahankali, ganin Mama tsaye abakin kofan kaman ita take jira daman yasa takarasa fitowa tareda maida kofan tana rufewa tana kallon fuskan Mama dake kallonta tana murmushi, harara Mama ta watsa mata tace âba murmushi nace kimin ba, quietly go to that kitchen kidafa sabon abinci wanda zaâaci agidan nan this night tunda wanda aka dafa dake da kawayenki kun cinyeshi tatasâ dan turobaki tayi dan wlh tagaji ahankali kaman zata rushe da kuka tace âMama maisa Ladidi bata dafa wani ba wlh nagaji school fa najeâ cikin fushi sosai Mama tace âare you stupid Umma? Inba so kike na makeki ba kiwuce yanzun nan kafin raina yabaci kije ki daura abincin dazaâaci this night, I am talking to you kina gayamin Ladidi tadafa, kin zaci sabida ke nadauki Ladidi aiki kokin dauka jakace ita batasan ciwon kanta ba dazata zake tai girkin gida keda kawayenki kuzo kutasa abincin agaba ku cinye tas, yanzu ina gayamiki kije ki daura wani kina neman kawomin gabli da baâadi, to the kitchen my friend!â Mama tadaka mata tsawa kaman zata kurma ihu tawuce hawaye sun cika idanunta tass tai kasa, harara Mama tabita dashi sanan takada kai kawai tawuce tashiga dakinta.
Kitchen din tashiga tamaida kofan da mugun karfi tarufe kaman zata Balla kofan sanan ta jingina da kofan tana maida numfashi takai kusan 5min sanan tawuce ta kwaso kayayyaki tashiga shirin hada girki.
Saida akai Ishaâi sanan Baba da su Manaf suka shigo gida, afalo suka tarda Mama zaune gaidata duk sukayi, Mama ta gaida mijin nata zama duk sukayi, Maheer yace âMama me aka dafa yunwa nakejiâ ahankali Mama tace âKhairy na kitchen tana girki, itada kawayenta suka cinye duka abincin da aka dafa tass shine yanzu dannace taje tadafa wani abincin take kumbure kumbureâ dan murmushi Baba yayi yana duba wayanshi ganin yanada miss call, cikeda kufulewa Maheer yace âwlh Mama Allah zan zane yarinyar nan, duk randa takawo kuchakun kawayenta tashiga kitchen tamusu girki da kanta ba abincin mubaâ cikin fushi shima Muâaz yace âni I donât even know wani kalan brain Khairy keda shi, ni tunda nake bantaba ganin wacce takai Khairy yawan kawaye ba, kawayenta sunfi dari biyu, tamaida mana da gida nanne majallisar kawayenta ai gobe Saturday Allah sa takawo mana wata gidan nan wlh daga ita har kawar saina kakkaryasuâ Baba daduk ke jinsu yana taba wayanshi wayan ya ijiye yakalli Mama yana murmushi sanan yakalli su Maheer yace âku kyale yarinyar nan sheâs just a small girl, idan making friends makes her happy so be it, abincin gidan banike siyaba taita kawo kawayenta sunaci is no big deal, and you wifeâ yajuyo yakalli Mama yace âidan abincin gida da kawayenta keciki ki kara yawan abinci since kinsan yarki mai mutane ce, ta yanda zasuzo suci su koshi sanan muma muzo muci okayâ tabe baki Mama tayi tace âdaman babu wanda ke bata yarinyar nan saikai kacigabaâ Mama tai maganan da fushi dan murmushi Manaf da tuntuni baice komiba yayi ganin yanda ran Mama yabaci yace âMama kudena making issue out of this small thing please bagashi yanzu tana kitchen tana dafa mana wani ba, is just friends ta tara bawai wani bad hali ko dabiâa takeyi wanda yaran yanzu sukeyi ba Mama, please ku kyaleta, sheâs still a small girl, inda ace bata gama secondary school dawuri ba da har yanzu bamata shiga university ba ballema tazo hartana final year, ku barta please Mama ahankali zata gyaraâ murmushi sosai Baba yayi yanajin maganan da Manaf keyi, Manaf nada dabiâunshi sak, ga hakuri ga iya tafiyar da gida gashi da halin manyanta halin Baba, amman Muâaz da Maheer jin kansu suke kaman saâonnin Ummul Khairy. Baki Mama tabude zatai magana aka bude kofan kitchen din aka fito Khairy ce tadauko wani hadaden warmer, ko kallonsu batayi ba sai uban turo baki take tawuce zatakai warmer dinning Baba yace âzo kawo kulan nan Umma anan falo zamuciâ ahankali tajuyo tazo Muâaz da Maheer sai uban ballamata harara suke tana karasowa ta ijiye kulan Baba na kallonta yace âyauwa sannu da aiki Yanmata naâ Maheer dake kallonta yace âyi sauri kije ki kawomin plate dina da forkâ dasauri ta kalleshi da manya manyan idanunta harara ta watsamai wani irin mikewa tsaye yayi kaman zaiyo kanta dasauri tai baya tareda dan sakin ihu. âWayyo Ya Manaf kaganshi koâ hararanshi Manaf yayi batare dayay magana ba hakan yasa Maheer yakoma yazauna yana kwafa, Manaf yakalleta yace âgo and bring the plate and serve usâ gyadamai kai tayi tajuya tana turo baki daga Baba har Mama suka bitada kallo, bata wani dade ba tafito dauke dawani babban tray da plates spoons, bottle water da drinks ke kai sanan takawo tsakiyan falon, sanan tabude kulan wani kamshi ne yadaki hancinsu tadafa wani lafiyayyen taliya da nama, zuzzubama kowa tayi sanan ta tashi, Baba yace âina zaki zauna kici nakiâ ahankali tace ânakoshi naci shinkafa dazu, wanka zanje nayi Baba nagajiâ âjikiyi yarinyar kirkiâ wucewa tayi sama sukuma sukahau ci, saida Maheer yajuya ganin hartama shiga dakinta yasa yajuyo yace âat least sheâs good in one good aspect, wato girkiâ murmushi Baba yayi yakalli Mama yace âakwai wacce zata zauna da Wife bata iya girki ba ballema yartaâ murmushi kawai Mama tayi batacemai komiba, saida suka gamacin abincin tsaf sanan Maheer ya kwashe komi yakai kitchen kafin su tashi suma iyayensu sallama suka wuce side dinsu.
Tashi Baba yayi yana kallon Mama datai shiru yace âplease kidena sa zancen shirmen Khairy aranki, is just like what Manaf said at least friends kawai ta tara bawani mugun hali baâ dan ijiyan zuciya ta sauke sanan ahankali tace âAlhaji still yawan kawaye basu da amfani wlhâ ahankali Baba yace âI promise duk randa nai sensing wani bad behavior kokuma wani abu nida kaina zan rabata dasu, please this matter of her friends shouldnât be an issue again okâ Ahankali Mama tace âai shikenan dama kaine ke bata Umma aiâ Mama tai maganan tai gaba abinta binta yay abaya yace âwifeyyy commonâ bata biyemishi ba tabude kofar dakinta ta shige, murmushi yayi kawai aranshi yace âI will handle u laterâ sanan yay hanyar dakin Khairy, knocking yayi ahankali tareda kiran sunanta. âUmmaâ jin shiru yasa ahankali yabude kofan dakin, dakine nai kyau dakana gani kasan dakin Yar gata ne anyimai Fenti pink dakuma design na flowers everywhere, tana kwance kan lafiyayyen gadonta mai kyau tana sanye da dogon gown na bacci tana bacci hankali kwance ga dakin uban sanyin AC tachure alamun sanyi takeji, karasowa gaban gadon yayi yace âUmma Umma, mamar ki dake fada ita batasan rashin jin maganan ta kika daukobaâ yay maganan yanajan bargon gadon yarufa mata sanan yadau remote don AC yarage AC sosai kafin ahankali yajuya ya kashe wuta sanan yarufe mata kofan yawuce dakin matarshi!!!!
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.