A Deen House Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: A DEEN HOUSE BY OUM HAIRAN-1.txt
Chapter 26 of 32
Da wannan ya tashi daƙyar ya nufi gidansa part ɗin Zainab ya shiga ya fara birkitashi kamar zautacce kome yake nema oho haka ya gama hargitsa komai dake gidan kafin ya nemi guri ya zauna ya dafe kai yana huci yana furta “hasbunallahu wa ni'imal wakil" yanayi yana dukan kansa so yake ya tuna sanda ya shigo part ɗin da dare har yayi wannan aika²r ya kasa dole ya miƙe yana layi kamar wanda yasha giya ya isa part ɗin Nafisa da tun shigowarsa tagansa tana jiran taji wanne labari zaizo mata dashi duk da tasan komai amma tanajin tsoron kada aiki ta ya lalace kamar yanda ya saba lalacewa indai akan Zainab ne.
Yana shigowa ta tare shi tana cewa “Wani abu ya faru ne Shamsu naga alamun tashin hankali a tattare dakai?" Kallonta yayi idanunsa ya kaɗa yayi jawur zuciyarsa na neman faso ƙirjinsa yace “Na haukace ne Nafisa wai don Allah da gaske Ni mahaukacine haukacewa nayi?"
Da rashin fahimta take dubanshi tace “Ni don Allah kayimin bayani sai ninkeni kakeyi baibai" kama hannunta yayi yace “jiya da dare a ina na kwana ne?" Da zaƙuwa tace “a nan part ɗin mana wani abu ya faru ne?" Da daren Kinga na fita ne?" Ya sake jefa mata tambayar. Kasa bashi amsa tayi sai hilatarsa data fara ya dubeta yace.
Dana fita sallar asuba naga gidannan a bude nayi mamaki so bayan na dawo hankalina yaƙi kwanciya shine na shiga part ɗin Zainab shima na gansa a buɗe har ɗakinta batanan wannan tasani fita na nufi gidanmu batacan dukkanmu hankalinmu ya tashi muna tsaye zaman jiran tsammani Daddy mahaifin Zainab ya kira Abba yake sanar dashi jiya da dare wajen ɗaya yazo nan gidan ya tafi da Zainab sakamakon sakin da nayi mata Nafisa da yaushe naje ɓangaren Zainab har na saketa kuma yanzu na kasa tunawa?"
Da alamun mamaki tace “Amma dai Shamsu wannan lamari naka da mamaki to ai koni jiya bayan ka dawo dana tambaye ka ina kaje cemin kayi kaje ka saki Zainab ne har nake cewa dakai akan me zaka saki mace da tsohon ciki kaikuma kacemin ba damuwata bace na ƙyaleka don bansan abinda kakeji bane...."
Katseta yayi da cewa “Ƙarya kukeyi wlh bani bane Nafisa karkimin haka kinsani jiya tunda na kwanta sau ɗaya na farka don Allah kibada shaidar ban saki Zainab ba kar...." Dakatar dashi tayi da cewa “Aa fa Mal karka wani dameni da maganar wata sakakkiyar matarka kaine da kanka kace bai shafeni ba don haka na barshi a be shafeni ɗin ba" tafiya tayi ta barshi da sakakken baki ya zube a kujera yana cewa “Allah don Allah Allah ka tabbatar min da ban saki matata ba wlh bansan sanda na saki Zainab ba Nikam ko da gaske na haukace ne?" Daidai lokacin wayarsa ta shiga bugawa ya zarota da sauri ganin number Abba ya ɗaga yace “Abba kun bincika kun gano gsky ko? Zainab nasan tanasona bazata yarda na Cutu ba Abba bazamu jure...." Dakatar dashi Abba yayi da cewa “Muna Lugard Hospital Yanzu haka Zainab ta haife maka ɗanka namiji....
_Kuyi hkr da yanayin typing É—in an very busy wlh_
Please karki karanta in baki biya ba Nrml group 300 VIP 600 PC 1k acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 Æ´an Niger zaku turo kati Airtel
[10/22, 8:48 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*
*Paid page*
Miƙewa Deen yayi tare da sakin wayar cikin wani yanayi me kama da gushewar hankali yace “Hai...ta haihu kuna nufin ta haihu?" Nafisa dake fitowa dauke da cup na madara ta tsaya turus tace “Wace ta haihu?" Da sauri kamar wanda yake tunanin mafita a gareta yace “Zainab..."
Dafe ƙirji tayi tace “Na shiga uku ya akayi ta haihu...." Da sauri ta gimtse bakinta duk da kallon da taga Deen yana binta dashi sai kuma tayi saurin waskewa tace “Banso ta haihu yanzu ba naso ace sai komai ya daidaita Shamsu yanzu fa Shikenan ta haramta gareka tunda dama iddar me ciki haihuwa ce kuma ta haih...."
“Ya isa don Allah..." Ya faɗa tare da miƙewa yace “Duk da ina tuhumar kaina da hauka nasan cewa in har da gaske haukacewa nayi na samu gushewar hayyaci to babu alƙalami akaina saboda haka har yanzu inada igiyoyi uku na aure akan Zainab...." “Ta yaya meye yasa kakeson wahalar da kanka da iyayenku ne nifa inada tabbacin kaine da kanka ka saki matarka babu wani ja ko jayayya saboda haka abinda yafi sauƙi kazo muje muga Bby"
Wata uwar harara ya watsa mata ya juya ya fice yana duba agogon hannunsa ɗaya da rabi na rana asibitin da Abba ya sanar dashi can ya nufa bai sha wahala wajen gano ɗakin ba da Umma sukayi karo ta kwaso kayan da aka ɓata zataje ta wanke ta watsa masa harara tare da jan tsaki ta wucceshi duk sai jikinsa yayi sanyi yaja ƙafafunsa daƙyar ya nufi ɗakin Hajiya Sadiya dake fitowa tace “Aa Shamsu ashe sun sanar dakai yanzu nake shirin kiranka" shafa kansa yayi yace “Abba ya sanar dani"
Sake gaisawa sukayi sukayiwa juna Barka ya shiga É—akin ita kuma ta nufi pharmacy domin siyo magani Allah ya taimake shi É—akin sai Zainab ita kaÉ—ai tana zaune ta haÉ—e kai da gwiwa sai sauke ajiyar zuciya takeyi, ya jima tsaye kanta bata sani ba har Saida yakai hannu zai É—auki yaron sannan ta É—ago Idanunta ya shiga cikin nasa gabansu ya faÉ—i tare ta janye idanunta daga kansa ya sanya hannu ya É—auki yaron da keta baccinsa hankali kwance buÉ—e masa fuska yayi yana kallonsa yaron masha Allah kyakkyawa dashi bai É—auko komai na kamannin Zainab ba hatta haskensa na ubansa ne.
Sake sauke idanunsa yayi kan Zainab yace “Na gde ƙanwata" daga haka bai iya sake ce mata komai ba tsayin lkc har Umma ta shigo ɗakin ta tsaya turus tace “Aa ikon Allah Shamsu baka gama ganin ɗan naka bane?" Yasan Umma sarai bata ɗaukar abubuwa da wasa hakan yasashi yin ƙasa da kansa yace “Ku fahimceni Umma...." Dakatar dashi tayi da cewa “Dakata don Allah ba sai kace komai ba in ka gama kallonsa ka ajeshi ko kaje dashi ina buƙatar kaɗaici da Zainab"
Kora da hali Umma takeyi masa ya sani don haka ya aje bbyn ya fita Matsawa tayi ga Zainab tace “Meye yace Miki?" Girgiza kai tayi alamun baice mata komai ba ta sauke numfashi tace “Ki nutsu kisan inda ke Miki ciwo Zainab Ni na haifi Deeni amma bazan iya cewa komai game da halinsa ba, Zainab duk abinda kake tunanin bazai iyaba iyawa yakeyi kija darajarki ki zama me zuciya duk mutumin daya nuna baya son kasancewa tare dakai kaima ka janye jikinka daga gareshi Zainab rabuwarki da Deen bazai zama ƙarewar nasarar ki ba indai akan wannan ne kike zubar da hawayenki to ki daina"
Kalami ta rinƙa bata masu sanyaya zuciya har Saida taga ta saki ranta sukaci gaba da karɓar Barka wajajen yamma suka koma gida basu jima da komawa ba Deen ya shigo da kayansa niƙi² duk yanda yaso ganin Zainab bai samu ba kasancewar Umma ta kasa ta tsare Deen ya shiga damuwar da bai taɓa shiga ba a haka akaci gaba da tafiya har zuwa ranar suna akayi sunan babu wani armashi duk da ba ƙaramar bajinta Deen yayi ba a haihuwar amma rashin walwalarsu yasa kowa ma walwalarsa tayi ƙaranci.
Sai ranar suna sannan ya yarda ya kawo Nafisa tun daga get É—in gidan ta raina kanta ta dubeshi tace “Shamsu inane nan É—in?" â€Gidansu Zainab ne" ya faÉ—a batare da ya ko kalli inda take ba bare ya fuskanci mamakinta ya fice daga motar itama ta fito tana kallon gidan tana jinjina mamakinta wai ashe mahaifin Zainab attajiri ne lallai dole ta sake É—aura É—ammara ashe ita da Æ´ar attajirai take kishi bata sani ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.