Ni Da Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: NIDA YAYA HABEEB.txt
Chapter 40 of 82
```WASHE GARI ```
_10:00am_
Haleesa na zaune a gaban dressing mirror tana Shafa lotion, ta d'a Shafa powder had'e da kwalli ta mik'e tanufi tarin trolley's d'in da ke jere tasauke guda d'aya tasoma kallon kayan da ke ciki duk tari kayan da ke ciki rasa na sakawa ta yi domin ganin take yi, matsayinta bai kai na saka wad'annan tsadadu kaya tsohuwar trolley d'inta tadauko ta zuge zip karaf idanuta suka sauko bisa wata fitted gown na shacking material a sanyaya tadauki rigar nan take kwakwalwa ta tasoma tuno mata da abunda yawuce ba za ta6a manta ranarda marigayi yaya Habeeb ya kawo mata d'inki rigar nan daga d'akinta tafito sanye da rigar zip yak'i rufewa sai fama gunguni take yayin da yaya Habeeb ke tsaye a k'ofar kitchen suna fira shi da Ammi tun kafin tafito daga d'aki take kwada masa kira yaya Habeeb! Wannan wane irin d'iki ne ka yi min zip yak'i rufewa"?
"Yaya Habeeb yadafe bakinshi yana dariya tak'araso daf da shi yaya Habeeb ina magana ka kyalle ni tafad'a cikin shagwa6a ya sauke hannunshi daga dafe bakinshi da ya yi ya k'ura mata ido ba ko kiftawa a shagwa6e tace me ye haka yaya Habeeb ya ina maka k'orafi akan zip d'in riga na yak'i rufewa kai kuma kana aikin kallona"?
Ya yi murmushi had'e da cewa babylove rigar nan ta yi masifar yi miki kyau, muddin nayi sake kika fita da ita ba k'aramin "accident za ki had'a dad'i ya lullu6e Haleesa ta kada kwayar ido ta kyalkyale da dariya Ammi da ke kitchen tace Allah yaraba mu da masifa duk abunda kyau shi ya zama masifa abun gudu ne yaya Habeeb ya dube Haleesa suka kyalkyale da dariya Ammi tace au ni ku ke yiwa dariya to maza ko bace min da gani gaba d'aya kun toshe k'ofar kitchen kun hanawa iska shigowa sai fama shak'ar hayaki nake Yaya Habeeb yarik'o hannunta zo mu je d'aki mu yi sirri banaso Ammi ta ji abunda za mu fad'a a bakin k'ofar d'akin Haleesa ya ja birki ya yi k'asa da murya kada Ammi ta ji abunda yakeso fad'a babylove ina matuk'ar sonki shiyasa nake kishinki wallahi banaso kowane d'a namiji ya kalli kyakyawa surarki na rok'e kada ki saka rigar nan ki barta sai mu yi aure ki yi min kwalliya na dinga gani ni kadai kinji babylove"?
Murmushi Haleesa ta yi tace yaya Habeeb rigima ina lissafi kusan kala 4 ka yi min d'iki kana hanani sakawa kace na ajiye sai mu yi aure ni fa hijab nake sakawa ba haka zan fita ba tak'arasa magana had'e da turo baki yaya Habeeb yak'ara narkewa sai kace manshanu na amince ki sakawa wad'anchan amma wannan ki ajiye ki yi min kwalliya amarci dariya sosai Haleesa ta yi daga bisani tace shikenan amma bana iya rufe zip din rigar da kaina cikin sigar jin dad'i yace wannan ba matsala bane ranarda da duk kika saka rigar ni da kaina zan k'arasa rufe miki zip da sauri Haleesa tarufe fuskarta da tafin hannunta yaya Habeeb yayi dariya yace bara na koma shago salman yana jira na in nadawo da dare zan ji dalilin wannan rufe fuska yajuya yafice Haleesa tadawo daga dogon tunani da ta afka tafashe da matsananci kuka "Allah sarki yaya Habeeb Allah ya yi nufi bara maka kwalliya da wannan rigar wance na d'auki tsawon lokacin ina adana ta kuka sosai Haleesa ta yi mutuwar yaya Habeeb tadawo mata sabuwa dal tsawon lokacin tadauka tana kuka duk ta6ata kwalliya da ta yi saida tagaji don kanta ta yi shiru, cikin sanyi jiki tanufi bathroom ta wanke fuskarta tasake Shafa powder da kwalli duk da haka kallo d'aya za ka yi mata kagano ta yi kuka har ta linke rigar ta mayar a trolley sai kuma tafasa domin bata ga amfani ajiyar ta da take yi tasaka inner wears ta zura rigar ta yi tsaye gaban dressing mirror tana kallo yadda rigar ta yi matuk'ar yi mata kyau hawaye suka ciko mata ido da sauri ta mayarda su ta rufe zip amma yak'i rufewa duka kamar yadda ya yi a wance lokacin kasancewa Haleesa bataso d'a kwalli shiyasa ta yane kanta da d'a k'aramin mayafi zuciyata a chukushe tafice tunawa ta yi da dokokin da Habeeb Lamido ya gindaya mata gabanta na fad'uwa tasoma haura upstairs karon na farkoda k'afarta ta ta6a takawa bedroom d'in shi......
Jeeddah Aliyu🌹
. [09/11 12:02 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```
_❣the sweetest love_❣
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
```®NWA```
°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*
```65```
~~Hannunta na rawa ta rik'e handle sai ta yi niyar ta bud'e k'ofar sai kuma tafasa yayin da gabanta yacigaba da fad'uwa, tak'ark'arewa ta yi ta danne numfashinta ta yi ta maza ta murd'a handle d'in kutt...sautin da k'ofar ta bayar kenan ta wangale saura kiris numfashinta ya fita daga gangar jikinta sakamako hango Habeeb Lamido ta yi yafito daga bathroom yana sanye da bathrobe yana goge sumar kanshi da d'an 'karamin towel Haleesa ta yi mugun tsorata da ganinshi domin bata yi zato yana cikin d'akin ta juya da sauri da nufi ta koma inda tafito har ta riko handle ta bud'e k'ofa, yadaka mata tsawa ke! Ta tsaya chak saboda tsabar tsoro numfashinta yafara Kara kaini, ke! Ba magana nake da ke ba ne"?
Yafad'a azafafe a hankali Haleesa tajuyo ta dube shi, ta yi narai-narai da idanu kamar za ta fashe da kuka ta d'an rusuna cikin rawar murya tace _ina...kwana...yaya Habeeb"?_
Tagwaye harara ya watsa mata had'e da 'yar k'aramar tsoki, a dak'ile yace da ban kwana ba kya ganni meye dalilinki na dako samako ki shigo min bedroom batare da izzini na ba"?
"Ka yi hankuri Dan Allah da ma na zo ne nayi maka gyaran d'akin kamar yadda ka umurce ni, duk magana da ke yi kanta na sunkuye a k'asa bata yarda sun had'a ido ba tabe baki ya yi amma shine don wulak'anci kina ganina za ki koma kina nufi tun da ina ciki bara ki gyara ba koh"?
Ba haka bane yaya Habeeb na ga kafito daga wanka kana buk'atar "privacy shiyasa zan koma in kama abunda ka ke yi sai na shigo kallon k'asan ido yake mata ya ja iska kamar yaci yaji gaban Haleesa yafad'i a zuciyata tace kai Habeeb Lamido mugun shu'umi ne dube yadda yake ja iska sai kace d'an air ya lashe lips d'inshi batare da yatanka mata ba yanufi "dressing mirror d'auki robar mai yasoma shafawa yayin da Haleesa tacigaba da tsayuwa Imaan da ke kwance akan bed tana sharar bacci ta falka "Daddy na tashi
'Yar k'aramar muryarta ce tadawo da tunani Haleesa ta juya tana kallonta, Habeeb ya dire robar mai yanufi wurinta yad'aga ta sama "Morning my angel kintashi lafiya"?
Imaan ta wangale d'an k'aramin bakinta tana dariya Haleesa ta tsura musu ido sunyi matuk'ar bata sha'awa ya bata peck a kumatu mu je ki yi brush na yi miki wanka da sauri Haleesa ta tari numfashinsa ta hanyar cewa yaya Habeeb kawota na yi mata yatsine fuska ya yi bar shi kawai yafad'a adak'ile ta girgiza kai wannan aikina ne zai fi kyau ka barni nayi mata ya tabe baki yadire Imaan k'asa yajuya yacigaba da abunda yakeyi Haleesa ta sunkuya tadauki imaan tanufi bathroom da ita tana jefa k'afarta a bathroom d'in ta yi turus mamaki ya baiyana akan fuskarta tasaki baki da hanci tana kallon tsarin bathroom d'in babban abunda ya yi mugun bata mamaki bai wuce gani katuwar plasma manne a jikin bango takara yadda ganinta akan stool na farin glass madauke da tarin news paper da magazines ikon Allah lallai in baka mutu ba kasha kallo wannan, ae dabi'ar nasara ce ko miye abun sha'awa da burgewa da har Habeeb zai dinga koyi da su d'ayan 6angare zuciyata yace Haleesa kenan kinmanta da Habeeb half caste ne {ruwa biyu}, ta tabe baki tanufi bathtub ta tara ruwa ta darje imaan tass wurin wanke fuska ne suka fara artabo Imaan ta yi tsaye kai da fata bataso a wanke mata fuska cikin sigar rarrashi Haleesa tace haba! Imaan ki bari na wanke miki fuskarki kinga da hannu zan wanke miki ba da soso ba"
Imaan ta mak'e kafada banaso ni ki kyalle ni Haleesa ta zare mata ido tace Allah ba ki isa ba sai na wanke miki fuska, ta goga sabulu a hannunta tana murzawa akan fuskar Imaan ta kwala d'an uban ihu za ka yi tsanmani idanuta ne Haleesa ta kwakwale "Wayyo Daddy ido na wayyo za ta cire min ido"!
Habeeb da ke tsaye yana rufe bottoms d'in rigarshi jin ihun Imaan yakarade gida yasa cikin hamzari yanufi bathroom, d'in _ke! Menene"?_
_Me ki ka yi mata ne"?_
A tsorace Haleesa tad'ago ta dube k'ofa inda Habeeb yake tsaye cikin sark'ewa halshe tace wai bataso na wanke Mata fuska "Habeeb ya ja tsoki yace Imaan ki bari aunty ta wanke miki fuska miye amfani wanka ba'a wanke fuska ba Imaan ta turo baki yayin da Habeeb yajuya yafita Haleesa tadauko towel karamin ta rufa mata koda Haleesa tafito Habeeb yafice daga d'akin bayan ta Shafa mata mai tace imaan je ki tambayo Daddy ina ya ajiye kayanki, Imaan tace aunty nasan Inda ya ajiye ta bud'e wardrobe tasoma kacaniya janyo wata k'atuwa Leda Haleesa ta dakatarda ita ta hanyar cewa bara na dauko miki ta bud'e Leda kayan sawa ne birjik Imaan ta yi karaf tace aunty jiya "Daddy yasiyo min su yace nadawo gidanan da zama zai dinga siya mini chocolate da ice cream kuma ya......dariya da Haleesa ta yi ne ya katsiwa imaan surutu ta Haleesa ta tsagaita da dariya da ta ke yi tariko hannun Imaan uhm....Imaan sarki surutu irin wannan zuba ba "comma balle full stop Imaan ta washe hak'ora aunty miye comma da full stop"?
Dariya Haleesa ta yi tace zan fad'a miki amma ba yanzu ki zo nasaka miki kaya ki je ki yi "breakfast ta Ciro wando Jean's blue had'e da White top mai Zane teddy bear kayan sunyi matuk'ar kar6a Imaan Haleesa tace oya ki je parlour ganinan zuwa kinji"?
Imaan tad'aga kai tafice da d'an gudunta "A hankali Haleesa ta bi room d'in da kallo idanuta suka sauka bisa bedside a hankali ta taka zuwa wurin ta mik'a hannun tad'auki d'an k'aramin frame mai d'auke da photo Habeeb da salma suna manne da juna ga annuri shinfid'e akan fuskoki su Haleesa batasan lokacin da ta tsintsire da dariya a zuciyata tace kalli wannan luk'ek'iya mata ace ita ce matar Habeeb da ganinta za ta girme mishi, wannan shi ake kira to match takara kyalkyalewa da dariya da sauri ta rufe bakinta ta dube bakin k'ofa daga bisani tafara wurwurga idanuta kamar tana neman wani abu a sannu ta ajiye frame d'in tafara karkade bed ta tattara kayan da yacire ta zuba a laundering basket nan take ta gyara d'akin ya yi fass ta fesa air freshener masu k'amshi gaske tanufi bathroom ta wanke shi tass duk ta bi ta jek'a k'asan, rigarta a hakan tafito kaitsaye ta doshe downstairs parlour Habeeb da Imaan na zaune a 2 sitter Imaan na ta fama zuba masa, surutu yayin da shi kuma yake zabga murmushi, a zuciya Haleesa tace uba kurma 'ya parrot ta tabe baki da sallama takarasa shiga parlour ta zauna a 1 sitter da ke facing d'in Habeeb ta talabe kumatu ta da hannunta na dama ta sukunyarda kai kallon k'asan ido Habeeb ya watsa mata ya yatsine fuska peter yashigo parlour ya dan rankwafa cikin girmamawa yace "Boss breakfast is ready"
Chan k'asan mak'oshi ya amsa masa "okay yarik'o hannun Imaan suka nufi dining area peter ya yi musu serving dai-dai lokacin da Bala P.A yashigo fuskarshi d'auke da murmushi yace _ina kwana amaryar boss"?_
Haleesa ta yi dumm" takasa amsawa gani haka yasa Bala ya yi murmushi yanufi dining area _Good morning Boss_
Bala yafad'a had'e da Jan kujera ya zauna kallon banza Habeeb ya yi masa yacigaba da cin abinci shi Bala yace Imaan ba gaisuwa"?
Imaan ta turo baki had'e da cewa nayi fad'a da kai tun da ka k'i siya mini goriba, Bala ya kyalkyale da dariya kai Imaan har yanzu baki manta da zance goriba nan ba"?
Imaan tad'aga kai
"To shikenan zan nemo duk inda goriba yake na siyo miki Habeeb ya mik'e yanufi parlour har yanzu Haleesa na zaune idan yabarta, ya zauna had'e da murtuk'e fuska a wulaqance yace ke! A nutse tad'ago ta amsa da na'am"
Saida yadauki tsawon dak'ik'a uku yana mata kallon da ta tsana, ki je bedroom d'ina a cikin bedside drawer akwai file's ki dauko min kiyi sauri Karki bata min lokacin.
"Haleesa ta mik'e tanufi stairs Habeeb ya rakata da ido sai lokacin idanunshi suka hasko masa rabin zip d'in rigarta a bud'e har yana iya hango brown colour bra d'inta ga wani dingo bak'i a bayanta{Mole} cike da takaici ya girgiza kai tuni Haleesa ta yi nisa domin har takai last stairs ya ja tsoki yadauke kanshi kamar Wanda aka mitsina ya mik'e da k'arfi ya haura stairs Haleesa na shiga d'akin tafara bubbud'e bedside drawers gaba d'aya ta duba a tafarko ba komai a ciki ta nufi gudan d'ayan wance ke d'auke da frame akai tana bud'ewa taci karo da tarin file's tana daukowa Habeeb na murd'a handle yashigo ya jigina jikinsa a jikin k'ofa ya hard'e hannaye shi a k'irji a firgice Haleesa ta dube shi ta ware idanu ta tsanani tsoro ya lullu6e ta, zuciyata tasoma yi mata wasi-wasi me yashigo da Habeeb"?
Ko dai wani tuggu ne ya had'a mata"?
Kafin ta lalla6o amsa tambayoyinta Habeeb ya yi mata alama da yatsanshi ta zo tak'ara rud'ewa 'yan hanjinta suka hautsine takasa bin umurninshi ganin haka yasa yafara dunfaro ta a tsorace tafara ja da baya yayin da Habeeb bai fasa tunk'ara ta jin ta yi karo da bango yasa tagano ba bu saura wurin gudu, kawai ta sadakat hannunshi yasa a bayanta yadafa bango ya rankwafa dai-dai bakinta da sauri Haleesa ta runtsi idanuta a tunani ta Habeeb sumbata ta zai yi hakan yasa jikinta yadauki rawa, ke! Banaso iskanci bud'e idanuki yak'arasa magana cikin d'aga murya ba bu shiri Haleesa ta bud'e idanuta ya dank'ara mata uwar harara nasan kwakwalwa ki yabaki cewa zan sumbace ki, in har tunaninki yabaki hakan kin yi kuskure, domin da na sumbace wannan bakin naki gwara na sumbace bakin akuya yak'arasa magana yana Shafa lips d'inta da yatsanshi ya ja iska a bakinshi jikin Haleesa yacigaba da rawa kidaina wannan karkarwa da ki ke yi ni tambaya ki zan yi
Haleesa tad'ago idanu ta fuskarta shinfide da mamaki, wance irin tambaya ce Habeeb Lamido zai yi mata da har sai ya matsita a jikin bango
_Miye dalilinki na barin zip d'in rigarki a bud'e"?_
_ko kinaso ki nuna min wannan abun ya Shafa mole in bayanta"?_
_Ko kuma colour din brazier da kika saka ki keso nagani"?_
Haleesa tarasa bakin magana sai fama girgiza kai take
Abunda yak'ara harzuk'a Habeeb yadaka mata tsawa ke! Bara ki bud'e baki ki bani amsa ko sai na yi miki wulaqanci"?
Cikin rawar murya Haleesa tace duk abubuwa da ka lissafi banida manufa da su kawai zip d'in ne yak'i rufewa tak'arasa magana had'e da sunkuyar da kai
"Habeeb ya yi shu'umi murmushi yad'ago fuskarta yace karki yi min k'arya Co's nasan duk wannan abu da ke yi kina yi ne saboda ni kuma kin yi a banza domin ni ba burgeni za ki yi, yafisgo ta da k'arfi ya murd'e hannayeta da hannunshi d'aya yasaka d'aya hannunshi ya rufe mata zip yadaura bakinshi dai-dai kunnenta ya rad'a Mata wannan ya kasance na farko na karshe da zan K'ara ganin zip d'in rigarki a bud'e ya wulgar da hannunta da k'arfi ya duk'a ya kwashe file's d'in da ta zubar yafice Haleesa ta zauna k'asa dabass tadafe saitin zuciyata da ke barazana fita daga k'irjinta saida ta share tsawon _10 minutes_ ta na jiyar zuciya da gangar jikinta daga bisani ta mik'e jiki a sa6ule tafita tun kafin ta k'arasa saukowa ta idanuta suka hasko mata Habeeb tsaye yabawa k'ofa baya hannunshi guda cikin aljihu wandonshi d'aya hannu yana rike da waya ya kara a kunnenshi, a nutse tashiga parlour Bala da Imaan na zaune Imaan nata zuba masa surutu yana dariya Bala yace amarya kina fama da surutu Imaan koh"?
Haleesa ta yi murmushi Habeeb ya kamalla wayar da yakeyi fuskar nan a had'e yace Bala tashi mu tafi in ka biyewa Imaan za Ku kai gobe tana zuba batare da tagaji bakinta Sam baya ciwo Bala ya yi dariya yasauke Imaan yayin da Imaan tasaka rigima "Daddy zan bi ka
"Habeeb yarik'o hannunta my angel office zan tafi ki zauna ki taya aunty hira zan siyo miki ice cream kinji"?
Imaan ta washe hak'ora "Daddy hadda chocolate da teddy da Ku....da sauri Habeeb ya katsita my Angel irin wannan lissafi ba ko numfasawa to naji duk abunda kike so zan siyo miki
"Uncle Bala karka manta da goriba na
Bala ya yi dariya yace to babyn Daddy insha Allah ba zan manta ba tak'ara juyawa wurin Habeeb Daddy yaushe za ka fiddo min Rahul da Rita mu yi wasa Habeeb yatafe goshi surutu Imaan yafara kai shi bango ya sumbace kumatu ta yace Bala mu tafi yajuya da kyar Haleesa ta iya sarafa halshenta ta furta _adawo lafiya Allah ya tsare_
Ya juya ya galla mata harara da sauri tadauke fuskarta.
Kamar jira take su fita ta mik'e tanufi dining table tacika tumbinta Imaan tadame ta da surutu _aunty Dan Allah ki kunna min cartoon_
Haleesa ta chanza mata channel zuwa Nickelodeon Imaan tadinga ihu Haleesa na dariya shirme ta daga bisani Haleesa ta kwanta a 3 sitter kwakwalwarta tasoma yi mata backward d'in abunda yafaru tsakaninta da Habeeb a haka baccin ya sace ta, Imaan ta d'auki katuwar tissue tadinga yagewa tana zubarwa ta wargaza wata kyakyawa flowers da ke sama stool ta yi daidai da remote cikin d'an k'ankani lokacin ta sauyawa parlour kamanu yayin da Haleesa batasan abunda take aikatawa sharar baccinta kawai take.
Habeeb na fita direct gidan madam Hindu yawuce yana shiga parlour gidan house maids {'yan aikin} suka dinga kwasan gaisuwa, ya amsa adak'ile ya dube yarinye a yatsine yace mom fa"?
Tana sama tafad'a cikin rawar murya a natse ya haura stairs cikin sand'a yashiga d'akin madam Hindu na tsaye gaban dressing mirror tana fesa turare taciki mirror ta hango shi yana zuwa ya yi hugging nata yadaura kanshi a kafadarta _Good morning sweetheart_
Madam Hindu ta yi murmushi _morning son me yafito da kai da sanyi safiya nan"?_
Habeeb yak'ara narkewa kamar Imaan cikin shagwa6a yace _just to see you sweetheart are you not happy"?_
Madam Hindu ta girgiza kai son baka girma abunda ka ke yi ko Hannah da take Auta bata yi shi yasake ta ya zauna a gefen bed nafi Hannah matsayin a wurinki domin ita gidan wani za tafi ni kuma _Ina tare da ke_
Murmushi madam tayi ta ajiye kwalba turare ta zauna kusa da shi _ina Haleesa da fatar ba wata matsala a tsakaninku"?_
Ras-ras gaban Habeeb yafadi nan take yafara tunani k'arya da zai sharawa madam ya
Wani karkace kai yace.......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.