Min Qalb Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Min-qalb Part One.txt
Chapter 51 of 94
A aikata hakan Amma kafin Nan ayau nakeson Modibbo dukkanin Abinda Khalil ya mallaka na zabeera a karbe.
Kallonsa Modibbo yayi da sauri saikuma ya sauke Kai Yana jinjina hukuncin sbd kaf 'yayansa bama shikadaiba kusan duk yayan zabeera da arzikin Zabeera suke tinqaho MAHMOUD ZABEERA ne kawai Babu qwandalar zabeera acikin dukiyarsa da guminsa da wahalarsa yatara arzikinsa,
Idan akace akwace komai na Khalil to motarsa ta hawa da kudaden account dinsane kawai zai tsira dasu Dan kuwa ko asibitinsa dayake tinqaho da ita MAHMOUD ne ya Gina Masa ita amatsayin tayasa murnar zama cikakken likita.
Koda commissioner yabasu izinin shiga bai nuna musu komaiba suka gaisa kafin Khalil yafara Masa bayanin Abinda yakawosu Babu dogo musu yacewa Khalil din an janye qara belinta kawai zasuyi akan kudi naira miliyan daya sai kudin tarar bacin suna miliyan daya da rabi duba da yanayin gidan da akayiwa bacin sunan.
What?????"""Khalil yafada cikin tsananin mamaki da yiwa commissioner din kallon rashin hankali yace"
Beli ne wannan kokuwa hukuncin Rai da Raine wannan???
Murmushi commissioner yayi Yana gyara zama yace"
Dr khalil zabeera zaka iya Kiran lawyer dinka zamu basa komai a rubuce sbd samun qarin fahimta.
Kallon bakinsa kawu keyi cikin yanayin tsoron dayafi mamakinsa miliyan biyu kudin beli?gwarama su fito su fada musu bada itane bazasuyiba.
Koda lawyer din Dr khalil ya iso aka miqa Masa takardun belin da aka bugo cikin qanqanin lokaci ya karanta yasake karantawa zuciyarsa na tafasa ko ba'a fada yasan shirine akayi Dan quntata Masa shida su Amatun,
Koma menene akayi Dan a cimma bazai taba rabuwa da Amatu ba,
Idan anyi ne Dan aga gazawarsa tabbas bazai taba gazawaba zaiyi komai iya iyawarsa zaikuma qwatar Mata mutuncinta da yancinta.
Dagowa yayi ya kalli kawu da idanuwansa sukai jajir sbd tashin hankali saiyaji zuciyarsa ta sake karyewa ya waiwayo ya kalli commissioner cikin yanayin na nuna rashin gazawa yace"
Ahada takardun belin su zama ready zuwa gobe zankawo kudin.
Kallonsa sukayi da sauri duk su duka commissioner na boye mamakinsa akan Khalil din yace"
Shikenan Dr khalil zabeera muna jiranka goben.
Miqewa yayi ya fice kawu da Barr Bashir na bayansa kowannensu cikin damuwa Yana Isa bakin mota ya tsaya ya juyo ya kalli Barr Bashir da idanuwansa dasukai jajir yabude busashen bakinsa yace"
Barr zankiraka gobe muhadu anan abasu kudin inshallah.
Kallonsa Barr yayi cikin kulawa da jimami Yana cewa''
Dr khalil kana ganin zamu karbi belin Nan ahaka?
Inaga muje can zabeera aroqi maganar tarar ajanye Mana ita zaifi....
Girgiza Kai yayi Yana qoqarin boye rauninsa yace"
Ba buqatar hakan zanhada kudin zuwa goben Inshallah.
Shikenan tunda zaka iya biya ba damuwa Allah yakaimu goben.
Suna Shiga mota yayi shiru cikin tsananin damuwa da tashin hankalin ta inda zai Fara hada kudin sbd dukkanin kudin account dinsa ya rabesu gurin case dinnan cikin kwanaki kadan
Duka duka abindake account dinsa baifi dubu dari bakwaiba Kuma gidan haya yayi niyar kamawa dasu ya ajiye Amatun.
Bayan kudin account dinsa da motarsa baida wata babbar kadara sai tsadaddun agogunansa da wayoyinsa,
Asibitin dayake tinqaho da ita bata cikin lissafi sbd tamkar alamar qaunarssuce me qarfi dake tsakaninsa da 'dan uwansa.
Kallonsa kawu yayi cikin tsananin damuwa da sarewa yace"
Khalilu kada ka takura kanka da hada wainnan kudaden daba haduwa zasuyiba,
Qaddarace wannan me girma ta samemu wadda Allah zai fitar damu inshallah.,
Zamuje muyita addua Allah yabamu ikon cinye jarabawa sbd koba komai munqara bambamce halaye irin na wasu masu arzikin Wanda bayan suna Babu Abinda suka damu dashi,
Farin cikin yayansu da walwalarsu bai damesuba kamar yanda sunansu da girman kansu ya damesu.
Ahankali yaja motar suka bar gurin suka kamo hanyar gida har lokacin bai iya cewa ko qala ba sbd nisa da yayi a tunani.
Koda suka Isa ajiye kawu yayi ya wuce zuwa zabeera.
Parking yayi daidai sashen Modibbo yafito ya nufi ciki jikinsa da zuciyarsa amatuqar sanyaye.
Sallama yayi palon yashiga cikin sa'a Modibbon na zaune shikadai Yana kallon labarai Koda yaga khalil din Saida yaji tausayinsa Amma bai nunaba sbd ya dauke Kai Yana cigaba da kallon labaransa.
Gabansa ya zube tareda sunkuyar dakai wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanuwansa akaro na farko daya nuna gazawa cikin wani irin sauti Mai tsananin sanyi yace"
Modibbo Ina roqon yafiyarku akan dukkanin Abinda yafaru Dan Allah ku sassautawa Amatu wlh batada laifi akan hakan kuskure ne da rashin sanin ciwon Kai wlh batayi Dan wata manufar Bata suna ko wani Abu ba dabam tayine kawai sbd kudi Wanda tsananin rayuwa yakaita ga hakan.,
Modibbo Dan Allah Ina roqon gafara da yafiyarku Dan Allah ku duba maraicinta kada ku tsaurara Mata.
Juyowa Modibbo yayi ya kallesa sosai ganin yanda babban namiji jajirtacce kamarsa ke kuka ya sauke ajiyar zuciya Yana cewa"
Khalilu zancenka ba'a hannuna yakeba Amma amtsayina na mahaifinka zanfada maka Abu daya,
Kada kayi Abinda zai kawo maka matsalarda bazaka iya tsayawa kaga wucewartaba,
Idan kanason yarinyar Nan tsakani da Allah Dan tallafawa maraicinta to tabbas na amince maka ka aureta sbd aurenta ne kawai zaisa Andi ya iya sassautowa tunda tariga tazama Zabeera Amma idan kasan tsakani da Allah yarinyar Nan batada nasaba to Ina baka shawara kayi gaggawar cireta daga rayuwarka shine kawai sauqi da mafita agareka..
Da jajayen idanuwansa ya dago ya kalli Modibbon Yana nazartar zancensa wani irin sanyin sassauci na shiga zuciyarsa sbd ya fahimci zancen mahaifin nasa take sabon qwarin gwiwa yasake shigarsa ya sunkuyar dakai cikin sanyi yace"
Nagode Modibbo Allah yaqara tsawon Rai.
Yana fitowa sashen ummensa ya nufa inda ya tararda ita zaune tayi tagumi kamar koyaushe cikin kwanakin tana ganinsa tayi saurin miqewa ya hanata ta hanyar mayarda ita zaune yana girgiza Mata Kai murya a mace yace"
Umme zanbar zabeera......
A firgice ta kallesa idonta na cikowa da hawaye zata fashe da kuka yace"
No umme karki manta kinmin alqawarin bazakiyi kukaba Kuma kinyi alqawarin bani support adukkanin Abinda Zan yanke.,
Umme albarkanki nake nema a rayuwar dazanyi wajen zabeera dan Allah umme kimin alqawarin bazaki saka kanki cikin damuwar dazata cutatar dakeba.
Kasa riqe kukanta tayi ta fashe dashi tana cewa''
Khalil Dan Allah kada kabar zabeera kabarni katafi Dani Nima
Wlh bazan iya zama baka nanba,
Katafi Dani duk inda zakaje zanzauna acikinku,
Zan zauna taredaku zanyi renon 'yayan dazaku haifa........
Kasa hkr yayi ya rungumeta Yana girgiza Mata Kai Yana cewa''
Umme Zaki zauna anan gidan aurenki sai mutuwace kawai zata fiddaki zabeera.
Aa khalil zanbika Dan Allah kada ka tafi kabarni.
Ganin yanda ta daga hankalinta yasashi zamewa da sauri ya fice Yana danne zuciyarsa dake neman fashewa yayi hanyar sashensa.
Kayansa ya diba a akwati tareda kwashe agogunansa da takalmansa masu tsada sosai da duk abubuwan dazai buqata ya saka cikin mota tareda dukkanin takardunsa yafito yaja motarsa yabar zabeera.
Daga zabeera gidan Ibrahim yaje yafara ajiye kayansa acikin dakin farkon Shiga ya rufe dakin da mukulli ya fito yarufe gidan ya wuce.
Tareda Ibrahim din sukaje gurin masu Saida agogo akayiwa agogunansa kudi kaf aka shiye suka hada kusan dubu dari uku daganan gurin Wanda zai siye motarsa suka nufa aka Fara cinikin saidai abin son Rai yayiwa mutane yawa Dan siyan wulaqanci sukaiwa motar har kusan mutum shida sukaiwa motar siyan wulaqanci qarshe Dole ya saidata miliyan daya da dubu dari suka karba ya hada hadda kudin account dinsa suka tashi 2.6.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.