Best Hausa Novels

Ibtisam Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ibtisam 1.txt

Chapter 11 of 11

Page 10😘

  Iman ta kama hannun Ibtisam wacce ta mike tana kuka, sama suka wuce nan Iman ta shiga hada mata kayanta, meyasa kowa ke neman daurawa Ibtisam laifi? Bayan kana gani kasan sanda Umar ke mata bana hankali bane? Da alama itama neman kwatar kanta takeyi. Tana hada mata kaya itama hawaye na zubo mata dan yanda Ibtisam ke kuka duk mai tausayi sai ya tausaya mata.
Abba ne ya turo akan Ibtisam tai sauri ta fito, haka suka fito da ita tana tafe tana kuka, dakin Bilkisu ta shiga, Umma ta gani rungume da Bilkisu tana kuka, karasawa tai ta zube a kasa jikin gadan da suke tana kuka tana kiran sunan Umma.
Fuskar Umma a daure sosai ta kalleta tace "Ke kuma kukan me kike? Naji ita tanada hujjar kuka ke fa?"
Kai Ibtisam ta girgiza tace "Umma wlh ba'a san raina bane naki fada muku, har daki na biyoki ina san na sanar dake, sannan lokacin da kuka fara maganar hadin nan kai tsaye na tambayeku dan ni nasan akwai wani abin, amma alokacin kukace inata tambaya ai shi ya fara amincewa, shiyasa na dauka ya hakura dani ne, ita kanta Yaya har daki na biyota na tambayeta ta nunamin ita ke san Ya Umar? Umma ya kukeso nayi? Menene laifina????" Abinda ta fada kenan ta sa wani irin kuka, duk da jikin Umma yayi sanyi ta kuma tuno tabbas duk abinnan data fada ya faru amma haryanzu bata sauko daga bacin kan laifin Ibtisam bane.
Kanta ta kauda wanda hakan ya kara daga hankalin Ibtisam, kanwar Abba ce ta shigo ta fito da ita tana kuka tana ba Umma hakuri tasata a motar Abba.

******
Umar kam a daki ya gama hada kayansa tsaf, cikin bacin rai ya kalli hoton frame din Abba dake makale a dakin wanda suka dauka tare, a kufule ya dau hoton ya makashi da kasa iya karfinsa sannan ya dauko jakarsa yana neman fitowa.
Da sauri Naziru ya maida kofar ya danne iya karfinsa daga waje.
A fusace Umar yace "Naziru kasan Allah in har baka bude kofar nan a duk abinda ya biyo baya karkaga laifina? Wlh zan iya tada gidannan da abinda ke cikinsa."
Naziru ya kara danne kofar iya karfinsa yace "Da alama ka fara haukacewa, ka kuma nunawa duniya kamar yanda aka daukemu 'yan kauye duk zaman birnin da zamuyi bazamu kile ba, banda rashin d'a da tunani mutumin daya rikeka kake neman ruguza rayuwar 'ya'yansa?"
Cikin tsawa yace "In ya rikeni shine ya halliceni? Ko kuwa ni daya nunamin rashin d'a'a anga laifinsa? Ko kuwa ni ba mutum bane?"
Nan fa kokawa ta shiga dan Umar iya karfinsa yake sakawa, daga waje shima Naziru iya nasa karfin yake sakawa, cikin tashin sa'a Naziru yai baya hakan yasa Umar fitowa cikin tsananin karfi.
Wani mugun kallao ya zabgamai sannan ya nunashi da yatsa yace "Inhar kai dan uwanane na jini to ka tabbatar ka kyaleni dan wlh duk mai kokarin rabani da Ibtisam to yana daga cikin makiyana." Yai magana yana rataya jakarsa, mamaki ne ya kamashi dan yana fitowa harabar yaga motar Abba na fita, ai kuwa idanunsa suka leko mai Ibtisam a zaune a bayan mota, sakar jakar yai ya biyo motar da gudu iya karfinsa, Kawunsa da ke kokarin maida gate ne ya bugamai wani kallo yace "Wallahi in har ka kuskura ka fita daga kofar gidan nan to ka shirya fuskantar bacin raina, akan wannan haukar taka zan iya sallamaka."
Turus yaja ya tsaya idanunsa suka canza launi, ya kalli Kawu yace "Kawu inhar su sun manta da farinciki na kai a matsayinka na mahaifi bai kamata ka bi bayana ba?"
Banzan kallo Kawu yamai yace "Inbi bayanka akan hauka? So hauka ne akace maka? Ko kuwa akanka aka fara so? Ko kuma akanka aka fara rasa abinda mutum ke so? Banda hauka da rashin hankali ka kalli mahaifin daya rikeka kace wai zaka saki 'yarsa yasa shima a saki daya 'yar kuma wai ya baka? Tunda nake a rayuwata ban taba ji bayani wanda yake tattare da rashin tunani da hauka ba irin wannan, ko mu dake kauye bamu shigo birni ba munsan wannan hauka da rashin tunani ne."
Huci kawai Umar yakeyi ya dunkule hannunsa yanaji kamar ya naushi gate din gidan, tabbas wlh sai dai suyi abinda zasuyi amma Ibtisam bazai taba barinta ya kwana da wani kato ba inba shiba.
Kokarin fita ya farayi, Kawu ya matso ya wanka mai mari iya karfinsa sannan yace "Wallahi in baka wuce daga nan ba sai jikinka ya fadama."
Babu alamar wucewa a tattare dashi sai dai ya daina kokarin fita, ko gizau baiyi ba da marin dan yana ganin halin da zuciyarsa ke ciki ya ninka wannan marin, a ransa yace "Ai ko tsakar dare ne zan je na dauko matata dan wlh in har wannan sokon namijin yasa hannu ya taba Ibty to lalai za'ai kisan kai a daren yau." A fusace ya juya bangarensa.

*******
Abba kam yana fita cikin karfi yaja motar dan ya hango sanda Umar ya fara tahowa, tafiya sosai yai sannan yaja gefen titi ya tsaya, hannunsa biyu yasa ya shafi fuskarsa wannan wani irin bala'i ne?
Kukan Ibtisam ne yasa ya dan sauke ajiyar zuciya yace "Ibtisam meyasa baki sanar dani halin da ake ciki ba? Da alama wannan halin na Umar ba yau ya fara shi ba."
Dagowa tai tana kuka tace "Abba bansan ya zanyi nasanar dakai ba, yaran nan dan yayanka ne wanda duk duniya ku biyu kuka rage, ka yadda da Ya Umar sama damu, Abba ban isa ko shiga cikin kawaye nai ba, sallama wannan ban isa na amsawa namiji ba, Abba tunda na fara makaranta shi ke kaini shike zuwa daukana wai duk dan karna kula kowa." Ta share hawayenta tace "ko adaidaita na shiga ban isa nai ko murmushi ba sai yace mai adaidaitan nake wa murmushi, haka rayuwata take cikin ukuba saboda shi, jin ya amince zai auri Yaya wlh na dauka hakura yai dani yana ganin ai Yaya batada lafiya tana zaman gida, duk da haka naje na sanar da Umma ta katseni, Abba bansan ya zanyi da rayuwata ba." Kuka ne yaci karfinta, gaba daya tausayinta ya kamashi. Fita yai daga cikin motar, ya kira Baffa.
Suna zaune suna cin abinci shida Aminu a gidan Ummy, dan yau ranar farinciki ce a garesu matuka, Kanin Aminu ma daga Singapo yace gobe zai taho.
Wayar Baffa ce tai kara, ya ajiye cokalin hannunsa sannan yazarota daga cikin aljihunsa. Ganin Abba ne yasa ya kara yana cewa "Sirikina baka gaji da ganina bane?"
Abba yai dan yake yace "Sulaiman ina cikin wani hali ne, wanda nake neman alfarma a gunka."
Jin haka yasa Baffa yadan mike ya maida hankali sosai kan wayar yace "Meke faruwa?"
Abba yai dan murmushin takaici yace "Ya Aminu? Ya akaji da asarar da aka mai dazu?"
Baffa yace "Haba bakomai, tsautsayi ne ai da alama yara ne basu kula ba suka buga mai." A ran Abba yace "Yanzu kam inada yakinin Umar ne."
A fili ya daure yace "So nake Ibtisam ta tare gidan mijinta, yau ta kwana a haka gobe insha Allahu za'a zo ai jere duk inda jibi take an kammala, wani uzuri ne babba ya taso wanda dole ta kwana gidan mijinta ayau din nan."
Sosai wannan kalamai na Abba sunbashi mamaki sai dai tunda yaji bai fadamai dalili kai tsaye ba ya tabbatar akwai wani babban dalilin daya hanashi.
Kallan Amini yai wanda yake cin abincinsa hankali a kwance, gashi basu gama katange Hajiyarcan ba, menene mafita?
Daurewa yai yace "Shikenan yanzu ka kawota gida na, in ma tafiyar ne sai su wuce ita da mijinta, ai dama a musulunce ba ace sai anyi gayya gun kai amarya ba."
Ajiyar zuciya Abba yai yace "Nagode sosai! Insha Allahu zan iso yanzun nan."
Wayar ya kashe Baffa ya fito daga falo ya nufi dakinsa sannan ya kira Ummy a waya. Bata jima ba ta shigo cikin fara'a tace "Alhaji! Ina cikin bakin ma baza'a barni ba?"
Zama yai a bakin gado sannan ya mata nuni data zauna kusa dashi. Kallansa take harta zauna kafin ya kwashe abinda ke faruwa ya sanar da ita.
Tayi mamaki kwarai kafin tace "in har hakane ina ganin Aminu ya dau matarsa su kwana a hotel, suje can suyi kwana uku har a kammala yi mata jeren, kafin nan an gama raba gidan."
"Hotel kuma? Da haka a kawota nan gidan mana."
Ummy ta girgiza kai tace "Dama inata tunanin yanda za'ai a basu dama su fahimci junansu, komai anyishi cikin sauri, Aminu nada yara, duk da agun Hajiya suke kwana amma agunshi suke, daga auranta za'a sata kula da yara? Ya za'ai su samu damar zama su biyu? In kawosu guna suyi sati ne? Duk wadannan tunanin sun cabemin wanda jin hakan yamin daidai, nan gidan ma in an kawota taya zasu zauna su biyu?" Tadan sauke ajiyar zuciya tace "Ga mutane a gidan nan me kake tunanin za'ace in aka ganta?"
Baffa yai shiru alamar tunani, tabbas yanzu ya gane me take nufi.
Sansanyan murmushi yai yace "Asma'u shiyasa a koda yaushe nake alfahari dake, na kuma tabbatar barin Hajiya ba laifinki bane, kinyi iya yinki fin karfinmu tai, wanda na tabbatar Allah yana tare damu."
Falo Baffa ya dawo ya sanar da Aminu wannan hukuncin, mamaki ne matuka ya bayyana a fuskarshi yace "Dama can abinda Ummy ta tsara kenan ko?"
Ummy ta hade fuska tace "Dama can haka nai niyya na tabbatar in na sanar dakai ne bazaka yarda ba, shiyasa nace a bari sai bayan an daura muku aure."
Shiru yai shifa bawai auran ba wannan takurar da za'a dinga bulomai dasu ya tsana, yanzu fisabillilahi nan akacemai ba yanzu zata tare ba, yanzu kuma anzomai da maganar wani hotel? Kamar wanda bashida gida?
Ummy ce ta katseshi tace "Ka tashi ka dau motar Baffanka yanzu za'a kawota ka amsheta ku wuce abinku, in kaje gida dauko kayanka basai ta shiga ciki ba kaje kai kadai ka kwaso ku wuce."
Mamakin yanda Ummy ta daure fuska sosai tana jawabi yake, lalai wannan shine a dakeka a hanaka kuka.
Haka ya fito duk ransa a bace, motar Baffa ya dauka, daga ciki Baffa yamai waya yace "yaje waje sun iso."
Haka ya wuce ya gaida Abba sannan ta fito ta shiga mota, kayanta tasa a baya ta zauna a gaba. Itakam ko a novel bata taba karanta amarya mara gata irinta ba, ace an kawota babu wani farinciki, uwarta ko kallan arziki bata mata ba.
Kanta kawai tasa akan cinyoyinta tana kuka, tana a haka Aminu ya shigo.
Idanunsa yadan runtse dan ya tsani kuka sam, dakewa yai yaja mota suka nufi gidansa, a waje yai parking ya shiga ya dauko jaka ya zuba kaya duk ransa a bace, wannan wani irin lamari ne? Ko auren soyayya sukai ai gida ya kamata a kawota amma wai wani hotel kamar a film sun tafi honeymoon?
Cikin bacin rai ya gama hada kaya ya fito yaja mota.
A Bristol Palace yai parking sannan ya kalleta, haryanzu kuka take, ya daure yace "Zanshiga nai check in."
Bata amsa ba shima bai jira amsarta ba, sai daya gama komai sannan ya dawo ya kalleta yace "Muje."
Dagowa tai duk fuskarta hawaye, gabanta ne ya fadi ganinsu a hotel, me zasuyi anan? Kallansa tai tana neman magana sai dai jitai batada bakin magana.
Aminu ya dau tissue ya mika mata yace "Goge fuskarki kafin mutane su dauka satoki nai."
Ansa tai ta goge fuskarta sannan ta fito sam ta manta da jakarta.
Aminu ya kalli jakar lalai wannan yarinyar, badai da saninta tabarmai jakar ya daukar mata ba?
Kallanta yai kamar zai mata magana sai kuma ya fasa, dauka yai sannan yai gaba, wuceta yai ta bi bayansa.
Babban daki ya kama musu, ta zauna akan kujera, ko sallah batai ba, mikewa tai ta kalli falan ba kowa sai ita, nufar daki tai da niyar tai alwala shi kuma daidainan ya cire manyan kayansa yana sanye da vest da wandan shaddar, kokarin yin wanka da alwala yakeyi.
Idanu ta zaro da sauri ta koma falo, bakijta nadan rawa tace "Yahkuri."
Aminu kam da sauri ya maida kayansa sannan ya zauna akan gado cikin dakewa yace "Shigo ko ba toilet zaki ba?"
Shiga tai kanta a kasa wai dan karta kalleshi, tana kokarin kuma kanta da bango taji yace "Me kikeyi hakan?"
Tsayawa tai sannan ta kalleshi da sauri, ganin saura kiris ta make kanta yasa ta sake kallansa tace "Yahkuri na dauka baka gama shiryawa bane."
Tai maganar tare da wucewa toilet da sauri, alwala tai sannan ta fito ta koma falo tai sallah, ya dade akan sallaya tana kuka tana kaiwa Allah kukanta, shikam Aminu duk kunnensa ya gaji dajin wannan kukan, wai haka amaren yanzu suke? Shi ko dan suna kaunar junansu da Na'ima ne? Dan kuka kadan tai, wannan anya ko abinci ma taci?
Yadan kauda kai ai wannan ra’ayinta ne. Harya gama abinda yake ya kwanta bata shigo ba, yanzu ya daina jin sheshekar kukanta.
Ibty kam tun tana kuka har bacci ya dauketa, dan ta rasa yanda zatai gashi Abba ya kwace wayarta yace “Ko an sai mata waya karta kira kowa saishi, itakam tanasan tasan halinda su Umma kw ciki. A haka bacci ya dauketa a durkushe.
Tun Aminu na lissafi hardai ya kasa kwantar da hankali ya mike, falon ya fito a zaune take inda tai salla ta hada kai da gwiwa, kallanta yai sannan a fili yace “Ba dole bacci ya daukeki ba, kinata kuka kamar ba gobe, kinfi awa hudu kina abu daya.
Kamar zai juya sai kuma tausayin kwanciyar datai yadan kamashi, ko ya sata a daki shi ya kwanta anan?
Hannu yasa yadan tabata yace “Tashi ki koma daki.�?
Sam bataji ba saboda nannauyan baccin daya tafi da ita, dan tabata ya sake yi da dan karfi, ita kuma daidainan tayi mafarkin Umar na janta a daji tana turjewa.
Cikin firgici ta rike hannun Aminu iya karfinta tana wani irin kuka, tana cewa “Kayi hakuri dan Allah! Na tuba!�?
Yanda ta matsemai hannu da kalamanta ne yasa yadan sunkuyo hannu yasa yadan daga kanta yace “Tashi!�?
Bude ido tai gabanta na faduwa, ta zubasu akanshi, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, mamaki ya kamashi yace “Sakemin hannu ko?�?
Kallan hannun tai sannan ta sakeshi da sauri, ya dan gyara zamanta, mikewa yai cikin dakewa yace “Ki wuce ciki ki kwanta, in kuma kinajin yunwa a kawo miki abinci.�?
Kai kawai ta girgiza sannan ta mike a hankali tace “Nagode Ya Aminu, banajin yunwa.�?
Abinda tace kenan ta wuce ciki, kafada yadan daga kadan sannan ya zauna ya jawo wayars ayana dube dube, kallan dakin yai yace “Tunda batajin yunwa ai tasan cikinta.�?

**********

Umar kam ya gama saitawa ta yanda zai je gida ya sato Ibtisam, ya kuma samu abokansa biyu wadanda zasu taimaka mai, sai dai abin tambayar “Inane gidan?�? Taya zaisan gidan? Wannan abu yasa sun rasa yanda zasuyi shi kuma yasha alwashin bazai kwana ba sai da Ibty…�?.

*******
Wayyo🤭 Kinaso kisan yanda rayuwar Aminu da Ibty zasu kasance? Ga kuma Hajiya a gefen hagu? Sannan ga Umar a gefen dama?
Yi maza ki mallaki naki domin free pages sun kare😔

Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:11 - Ummi Tandama😇: 💫 IB💫
      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Dan Allah in baki siya ba karki karanta, kudi kalilan zaki biya ki samu wannan garabasar*

*11*

  Duk yanda Aminu yaso yai bacci ya kasa, sai juye yake akan kujera, ajiyar zuciyar da take tayi irin na wacce taci kuka ta gaji shine duk ya hanashi bacci. Kamar ya jawo dakin ya rufe sai dai yana ganin hakan bai kamata ba in wani abin ya sameta cikin dare fa? Ganin dare natayi gashi yanasan zuwa aiki gobe yasa ya mike ya nufi dakin. Tana kwance ta dukunkune ko bargo bata rufa ba, ta dukunkune jikin hijab dinta, shiru yai yana kallanta yanda take bacci tanata sauke ajiyar zuciya.
A fili yace "In kinsan bakyasan auren meyasa baki bi shawarata ba? Bayan na sanar dake kice bakyaso?" Ganin dai shikadai ke maganarsa ba amsa yasa yai kamar zai juya, haryayi taku biyo sai kuma naga yadawo yaja bargon dake kan gadan ya luluba mata, cikin baccinta taji alamun hannu ana sa mata abu. A hankali ta bude idanunta ta saukesu akanshi.
Da sauri ya saki bargon tare da mikewa sosai yai gyaran murya, kafin yace "Meye amfanin bargon in kinajin sanyi?"
Bakinta tadan motsa a hankali kafin tace "Ya Aminu karfe nawa?"
Agoggon hannunsa ya kalla kafin yace "karfe biyu na dare."
Wani abu tadan hadiya a bakinta kafin tace "Nasan sun kwanta yanzo, amma Yaya dan Allah bani aran wayarka ko text nayiwa Abba."
"Yanzun?" Abinda ya tambayeta kenan tadan mike zaune fuskarta da idanunta duk sun kumbura, shi dama haka amaren suke?
Wayarsa ya dauko ya bude sannan ya mika mata, kafin ya juya ya fita. Zama yai a falo yana mamakin yanda yanayinta duk ya canza, ji yai tausayinta ya kamashi, shifa abinda bayaso kenan azo ana auren dana sani bayan shi ba shine ya tilastata ba.
Ibtisam kam daga daki sako ta turawa Abba tana tambayar ko gida kowa lafiya, ganin anfi miti biyar ba reply yasa tasan bacci yake.
Saukowa tai daga kan gadan a hankali, jitai jiri jiri na yunwa na neman yarda ita, rabanta fa da abinci ashe tun safe ko? Tazo zataci akace tai wanka ta shirya tukunna, bayan ta shirya kuma tayi sallah akace ta fito daukan hoto, daga nan kuma shikenan komai ya rikice, gashi da safen kosai taci kawai tasha dan tea.
Bango ta dan dafa tare da takawa a hankali zuwa falan, kusa dashi taje yana zaune akan kujera ta mikamai wayar da hannu biyu, kallanta yai bai amsa ba yace "Kingama?" Kai ta daga a hankalin sannan tace "Nagode!"
"Wayarki a gida kika barta? Ko kwacewa akai?" Kai tadan girgiza a hankali kafin tace "Mantawa nai da akace na fito bansamu damar daukowa ba."
Kai ya daga sannan yasa hannu ya amshi wayar, juyawa tai, tai dan gefe kadan tana neman faduwa, da sauri ta rike kujerar dake gefe, mamaki ne ya kamashi ya mike ya tako zuwa inda take, hannu yasa akan saman goshinta, wanda hakan yasa ta dawo ta kalleshi, samun kanta tai da saukar da idanta da sauri saboda wani kwarjini daya mata.
Hannunsa ya dauke daga saman goshinta sannan yasa a kan wuyanta, jitai numfashinta na neman daukewa na wucin gadi, ta kasa ko kwakwaran motsi, muryarsa taji yace "Baki da lafiya?"
Bakinta nadan rawa tace "A'a kawai kaina ke ciwo sai dan jiri da nakeji."
"Abinci fa? Yaushe rabanki dashi? Tunda naji ba zazzabi bane.�?
Yanzun ma kanta na kasa a hankali tace "Da safe nasha tea da kosai."
Wani kallo ya mata na bacin rai da alama yarinta na damun yarinyar nan, tun abincin safe bataci komai ba ta zauna kuma tanata uban kuka? Kamar wacce akayiwa rasuwa?
Cikin dan zafi yace "Shiga daki ki zauna."
Bata ko musa ba ta wuce tana tafiya a hankali tana dan bin bango, da kallo ya bita sannan yadan girgiza kai, saman fridge ya kalla kayan tea ne kawai a gun, ya kuna kettle ya dafa ruwan zafi sannan ya hada mata tea, bacci yakeji dan har wata doguwar hamma yai, daukan cup din yai ya nufi daki, harta dan fara gyangyadi, gyaran murya yai yana daga tsaye. Bude idanunta tai tare da gyara zama, mika mata cup din yai yace "Sha kafin ki kwanta"
Hannu tasa ta amsa, idanunta suka dan ciciko a hankali tace "Nagode." Bai amsa ta ba ya koma falo, kwanciya yai kankace me yanzu kam bacci yayi gaba dashi.
Ibty kam tana gama sha tai alwala tai saloli wanda haryanzu babu karfi sam a jikinta, da kyar ta koma kan gado ta kwanta kafin bacci yai gaba da ita, yanzu kam bacci ne mai nauyi ya dauketa.

********
A can bangaren Umar kuwa yayi sintiri harya gaji, ganin bashida wata hanyar dazai sa yasan inda aka kai Ibtisam yasa ya dawo gida.
Yan Uwa yanzu kam ana zaune a falo duk kowa yayi jugum 'yar hirar ma duk kowa ya daina, wasu ma sun tafi sun kwanta bacci.
Shiga yai da sallama kansa a kasa kai bakace shine na dazu ba.
Ganin haka yasa kowa hankalinsa yadan kwanta, tsugunawa yai sannan ya bada hakuri kafin ya nemi shiga dakin Bilkisu wai dan ya bata hakuri.
Wannan abu ya kwantar da hankalin kowa nan fa ya wuce dakinta su kuma kowa ya saki hamdalla.
Bilkisu tana zaune akan gado tana cin abincin da aka kawo mata, da taki ci sai dai Umma da kanta ta zauna ta tilastata sannan ta mata fada, jin sallar Umar yasa Umma ta kalli kofa cikin mamaki sannan ta amsa.
Umar ya shiga ya tsuguna a kasa sannan yaba Umma hakuri, wani dadi ne ya ziyarci zuciyarta, ta fito daga dakin cikin jin dadi tana godiya ga Allah.
Zama yai a kan gadan kafin ya watsa mata wani kallo, Bilkisu gabanta ne ya fadi ganin yanda ya canza, cokalin hannunta ta ajiye cikin tsoro tace "Ya Umar?"
Wayarsa ya mika mata yace "Saka sabuwar number Ibtisam."
Da sauri ta kalleshi kafin ta girgiza kai tace "Ibtisam ai bata canza number ba." Cikin zafi ya nunata da yatsa yace "Kinsan Allah? In har bakyasan na baki saki uku a daren nan ki fadamin gaskiya."
Hawaye ne suka zubo mata tace "Wallahi bansan wata number ba bayan wacce take da ita."
Fuskarsa a daure ya maida wayarsa yace "Wace unguwa aka kaita?"
Nan ma kai ta girgiza tana haways tace "Wallahi shima bansani ba, kaga ko jere ba'a mata ba balle asan wace unguwar ce."
Fuskarsa takai matuka gun baci, hannu ya sa ya fizgo wuyan rigarta, samun kanta tai da numfashi dakyar ya saketa yana hucin bacin rai, yace "ki tabbatar kin binciko inda aka kai ta kafin gobe da safe, kuma karki kuskura ki fadawa kowa ni na sakaki, in kuma takardarki kike nema ni a yanzu ma sai na mika miki."
Yana kaiwa nan ya mike ya fito, da kallo ta bishi tana wasu zafafan hawaye masu zafi.
Umar kam sai shimai albarka su Goggo suke dan tabbas yanzu kam hankalinsu ya kwanta, shikam waje ya fita zuciyarsa na wani irin tafasa, ranar haka ya kwana ko gyangyadi baiyi ba, ko idanunsa ya rufe hango Ibty yake a kusa da wannan sokon mutumin suna mai dariya.

*********
  Har akai kiran assalatu dukansu ba wanda ya farka, sai karfe bakwai na safe Aminu ya bude idanunshi, yana ganin agoggo a zabure ya mike tsaye gashi 8 ya kamata ya shiga office, wayarsa ya dauka yana kokarin sanar dasu zaiyi late kadan, sakon Baffa ne ya shigo "Na sanar yau bazaka samu zuwa aiki ba, ina kuma sa ran ka kula da matarka"
"Baffa!" Abinda ya fada kenan tare da ajiyar zuciya, sakon Abba ya gani hakan yasa ya ajiye wayar tunda sakon ba shi akayiwa ba.
A hankali ya shigo dakin ya bude jakanya kwashi kayan dazai saka, shikam ai a toilet ma zai shirya dan bayasan raini, ina girma ace kanasa kaya yarinya sa'ar kanwar kanwarka ta ganka?
  A hankali ya kwashi duk abinda zai saka sannan ya nufi toilet yana tafiya a hankali, kamar daga sama yaji ance "Ya Aminu ka yadda abu."
Runtse ido yai sannan ya mike sosai ya kalleta fuskarsa a daure sannan ya kalli kasa, jiyai kamar zai nutse ganin boxers dinsa, wannan wani irin abin kunya ne? Cikin takaici ya dauka bai ko kalleta ba ya wuce toilet.
Ibtisam kam batama kula da menene ba, ta danji motsi ne ta bude idanunta ganin abu ya fado yasa tamai magana.
Aminu kam haka yai wanka ya shirya a bandaki duk ji yake raini ya gama shiga tunda har taga boxers dinshi. Fitowa yai fuskarsa a hade yana kokarin komawa falo.
Ita kuma ta yashi ta gama gyara gado kenan tana jiran ya fito ta shiga tai alwala.
Ganin ya fito yasa tace “Ina kwana?�?
Dan kallanta yai na dan second sannan ya maida kansa gefe yace “Ya jikin naki?�?
A hankali tace “Na warki.�?
Harya fara tafiya tace “Ya Aminu? Abba yayi reply?�?
Tsayawa yai sannan ya dauko wayarsa ya bude, mika mata yai bai bari ta kalli cikin idansa ba. Itakam a hankali ta karaso ta amsa ta duba sakon daya bude mata “Ibtisam ki kwantar da hankalinki nan komai ya daidaita, ki kula da mijinki.�?
Idanu ta runtse sannan ta sauke wata ajiyar zuciya wacce yasashi kallanta, daidainan idanunsu suka hadu da juna.
Dauke idanu yai itama ta sauke nata kasa, mika mai wayar tai ya amsa yasa a aljihu, kafin yace “Me zakici? Zan je nai order a restaurant dinsu.�?
Tace “Koma menene ba matsala.�?
Okay kawai yace sannan ya fita daga dakin, falo ya nufa ya tada sallar asuba.
Ibtisam wani ajiyar zuciyar ta sake saukewa yanzu kam najin dadi ne dan da alama komai ya daidaita a gida.
Toilet ta shiga tai wanka tai alwala sannan ta fito tai sallah, jakartata ta bude ta dauko wata doguwar eigar lace wanda bayan an gama dinkin, akazo akai kwalliya da stones wanda ya fito da kyan dinkin sosai, ganin yanda kayan yadan kamata yasa ta dauko mayafin lace din ta ajiye akan gado sannan ta dau hijab ta tada sallah, ta dade tana kai kukanta gun Allah tana addu’ar Allah yasa kar sanadiyarta rayuwar Yayarta ta kara shiga cikin bala’i.
Kallan dakin hotel din tai dan sai yanzu ta kurewa dakin kallo, hijab din jikinta ta ninke ta maida akwatin sannan ta fito falo tana dan tasan bayanan saboda taji alamun fitarsa tana sallah, a ranta tace “Da alama ansha kudi dan tasan babban daki irin wannan mai kyau dole a kashe kudi, jikinta ne yai sanyi cikin takaici tace “Duk laifinane da badan anyi haka ba ai ba yanda za’ai Abba ya sa a kaita cikin gaggawa haka.�?
Zama tai a kan kujera tana mamakin wai ashe Umar shi ya dauka ita zai aura? Itakam ta kasa gane meke faruwa ta kuma kasa fahimtar kwantar da hankalinta ya kamata tai ko kuma kuka? Batasan auran Umar sai dai bazataso dalilinta yayarta ta shiga cikin bala’i da masifa ba.
Ta tafi tunani sam bataji alamun bude kofarsa ba, doguwar rigarnan ce kawai a jikinta ko dankwali bata daura ba saboda ta leko taga falan ne ta koma ta daura dankwali ta sa babban mayafin data fito dashi.
Aminu kam kallanta yai cikin mamaki, a ransa yace “Har ta gama kukan amarcin?�?
Kamar yanda ya saba gyaran murya yai hakan yasa ta kalli gun, idanu ta zaro a tsorace sannan ta mike cikin sauri, samun kanta tai da sa hannu a saman kirjinta, duk kunya ta rufeta tai daki cikin sauri har tana neman faduwa.
Baki yadan bude cikin mamaki, me take rufewa? Lalai yaran zamani dauka tai kallan kirjinta yai ko me?
Itakam daki ta shiga da sauri ta dauko mayafi ta yafa sannan ta zauna akan bakin gado tace “Wannan ai sai ya dauka banida kunya, jiya na kwan ina kuka yau nazo nunamai kaina.�? Fuskarta ta rufe da hannayenta tace “Dama yana min kallan sai a hankali yanzu na nunamai banda kunya.�? Tadan bubuga kafa a kasa tare da sake rufe fuskarta cikin jin haushin kanta.
Aminu dake tsaye inda ta barshi duk yana kallan abinda take a daki, saboda a bude tabar kofar, kuma yana tsaye daga falan ta inda zai iya hango cikin dakin.
“Me kuma takeyi hakan?�? Tambayar datazo mai kenan, Ibty ta bude ido cikin kunyar kanta kawai suka sake hada ido, sam ta manta bata kule dakin ba, shikenan itakam yau ta mutu, wannan abin kunyar har ina?
Sandarewa tai a zaune ta kasa ko motsi shikam komawa yai ya zauna akan kujera tare da girgiza kai, wato yarinyarnan dasu Islam da alama banbancinsu kadan ne, waya ya dauko yana danawa yana jiran su kawo musu abinci.

*********

An fito da kadan daga cikin kayan da aka riga aka siya na kayan dakin Ibtisam, nan wasu daga ciki suka taho dan fara shirin gida, su Umma kuma suka tafi kasuwa dan siyo ragowar, haryanzu Umma bata sauko akan abinda Ibty tai ba sai dai tasan wannan aikinta ne.
Umar kam dama tunda yaji ana fitar da kaya ya shirya tsaf ya tari mai adaidaita ya tsaya daga lungun gidan, suna fitowa yasa abi bayan motar.
Har kofar gidan akaje sai daya karewa gidan kallo sannan yaja wani tsakin takaici ya naushi iska yace “Wato kinga gidan kudi shiyasa kika wulakantani ko? Wallahi kinyi a banza shi kanshi wanda yai gangancin auran naki ya shirya fuskantar bala’i da masifa.
******
Hajiya kam tana waje tana kallan yanda aka katange mata bangarenta, kwafa ta saki ta kalli gefe inda ake cigaba da ginin, lalai sai ta nunawa Asma’u ita ba kanwar lasa bace, ta dauka wannan abinda tai zaisa ta bar gidan ko me? Zama a gidan nan bataga uban daya isa hanata ba, sannan malaminta ya aanar mata inhar Aminu hankalinsa bai karkata kan mace ba to fa bazai taba korarta ba. Ita kuwa tanada yakinin babu macen da zata rudi Aminu, ya tabbatar ‘yarta kadai yakeso kuma har abada bazai so wata sama da ita ba.
Su Ilham suna makaranta, juyawa tai zata koma ciki taji alamun bude gate daga bangaren Aminu, kallan gefe da ba’a karasa ba tai sannan ta nufi gun tana dan leke me Aminu yake a gida bai tafi aiki ba?
Mamaki ne ya rufeta ganin motar kaya ta shigo, nan ta fara jiyo maganar mata daya nacewa “Kai kai kai! Nan ne gidan? Lalai Ibtisam tayi goshi, wannan hadaden gida in na shiga ai nikam banaji zan iya fitowa.�?

Gaban Hajiya ne yai wani irin faduwa, me suke nufi da kalamansu, bata gama tunani ba taji wata ta saki guda tace “Kai masha Allah! Wannan tafkeken gida mai kyau haka? Ah Amarya taji dadi Allah yabarsu tarr ya kawo kazantar daki.�?
Kanta ne taji yayi wani irin sarawa, me take juyowa haka? Jiya taje gun Malam akan a sake rufe bakin su Ummy sam bai mata wannan zancen ba, meke faruwa? Jitai kafafunta na neman kasa daukanta da sauri ta koma ciki, kasa zama tai ta fara yawo a cikin falan gaba daya kwakwalwarta ta kasa daukan abinda ke faruwa.
Dole ta fita taji meke faruwa, dole kuma ta tafi gun Malam yanzun nan taji meke faruwa.

{Nace in kinji ki fadamin nima😏 ni Ayusher naga bala’i da masifa, wannan wani irin naci ne?}

Ayusher Ce😘
2/4/22, 11:12 - Ummi Tandama😇: 💫 IB💫
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Dan Allah in baki siya ba karki karanta, kudi kalilan zaki biya ki samu wannan garabasar*

12
Tayi ta kiran malaminta bai dauka ba gashi gaba sai daya ta kasa sukuni, yanzu tana zaune za'a kawo ma Aminu amarya? Bayan tasa a ranta ko auren ne ma sai wacce ta zaba mai? Lalai akwai bala'i dan in batai wasa ba karshen zamanta anan ya kusa, tunowa tai da yanda 'yan uwanta suke difara mata tuwo bako miya haka za'a sa mata sandararen tuwon dawa, yunwa haka take sa wannan tuwon a gaba ta hau ci kamar mayya tanajin dadinsa, kwana kuwa a kusa da turken dabobi suka bata wata 'yar bukar ajiye kayan abincin gona anan take dan raba ta kwanta, a cewarsu mayya ce tunda maza uku tana aura suna mutuwa, gashi mahaifin Na'ima ne kadai Allah ya basu ziri'a dashi, kowani aure ta sake bata ko shekara mijin ke mutuwa.
Yanda gaba daya zufa ta fara keto mata ne zaisa ka dauka zafi akeyi, hijab dinta ta jawo ta dau jaka ta bude kasan gado ta debo kudi ta zuba a ciki, duk ta rikice da sauri ta zura takalmi sam bata kula wari da wari ta saka ba ta fita ta hau tafiya cikin sauri, sai datai nisa sannan ta tari adaidaita, sai datai canji na adaidaita hudu kafin ta isa canciki wani lungu, sauka tai sannan ta fito ta nufi gidan.
Ta isa sai data jira a waje saboda akwai wasu mata a ciki, ji take kamar zuciyarta zata fita dan ta tuna sanda Malam yace in har ta bari suka canza mata muhali ko ya sake aure har hankalinsa ya karkata kan mace tofa ta shirya komawa kauyensu.
Matan na fitowa ta afka ciki, nan ta kwashe komai ta sanar dashi, yan dube dubensa yai sannan ya sheke da dariya, kai ya shiga girgizawa kamar mai sauraran magana kafin ya kalleta yace "Aure an riga an daura."
Tashin hankali! Cikin faduwar gaba tace "Malam bansan anyi ba wlh munafirtata akai."
Shiru yai yana dube dube kafin yace "Karki damu zamu san yanda zamuyi, mafita daya garemu karki kuskura ki bari hankalinsa ya karkata kanta, bale har wani abu na rayuwar aure ya shiga tsakaninsu."
Hankali a tashe tace "Ba tare bake kwana da ita ba taya zan tabbatar?"
Ya miko mata wasu magunguna yace "Ki tabbatar kinsa a inda suke kwana, sannan wannan kisa a cikin abincin da Aminu zai ci shine zai dauke hankalinshi daga kanta. Banda wannan hanyar banida wata hanya kuma."
Amsa tai sannan ta bashi ladab aiki ta fito, itakam ko cewa akai ta yanko naman jikinta ta bada indai har za'a biya mata bukata a barta taji dadin rayuwa to fa zatayi.

{Nace Allah ya tsaremu da wannan bala'in}

**********
Aminu yana zaune yana waya aka kwankwasa kofar dakin, saurayi ne wanda hannunsa ke dauke da babban tire na abinci, ya gaidashi sannan yace "Sir an gama."
Yana kokarin shiga Aminu ya sa hannu ya amshi tiren yace "Zan shiga dashi."
Amsa yai sannan ya daurashi akan centre table, bakin dakin yazo tana kwance rufda ciki a kan gado, kallanta yai sannan yace "Ki fito kici abinci."
Cikin kunya tace "To."
Uban yunwan da takeji bazai barta tace ta koshi ba, haka ta gyara zaman babban mayafin sannan ta fito daga dakin, a zaune ta ganshi ta kalli tiren abincin sannan ta fara tunani, to yanzu zuwa zatai ta fara zubawabta mikamai sannan tasa nata? Ko kuma nata zata fara zubawa ta faraci shi inya shirya ci yaci nashi? Kai ta girgiza da sauri ganin hakan ba tunani, to meya kamata tai? Shiya zauna yana dane dane a waya.
Dakewa tai ta karasa tare da daukan plate, gani tai ya mike tsaye tai saurin cewa "A daki zakaci abincin?"
"Zan dan fita gun aiki ne na dawo."
Ta kalli abincin sannan tace "Kaci abincin mana tukun sai ka wuce."
Jakarsa ya dauka yace "Ke kici banacin abincin waje."
Baki ta bude sannan ta kalli yanda akansoya dankali da kwai, dayan plate din indomie da soyayyen kwai. Me bawan Allah din nan yake nufi? Ina zata kai wannan abincin?
Kallansa tai tana san magana taga haryasa takalmi, idanunta na kansa taga ya juyo dawowa yai cikin falan sanye da takalmi ya matso kusa da ita kawai ya zare sim dinsa ya ciro wallet dinsa ya dauko wani sim ya saka a cikin wayar, mika mata yai sannan yace "Kiyi amfani da wayata incase in wani abin ya tashi, ba dadewa zanyi ba amma tsautsayi bashida lokaci."
A hankali tasa hannu ta amsa, baiko jira me zatace ba ya juya, sai daya kai kofa ta iya furta "Nagode!"
Bai amsa ba ya maida kofar ya fita, kallan wayar tai wace alan wayar ke dauke da hotonshi da na Na'ima, itakam mutumin nan ta kula sam baya jira yaji ra'ayinta, abinda yamai kawai yake aikatawa, ta kalli abincin rufe dankalin tai kawai tadau indomie ta koma kan kujera ta kuna tv tana kallo tanaci, lalai yunwa takeji dan gani tai ta cinye indomie din nan tas, hamdala tai sannan ta mike ta hada tea ta zauna tana sha, wayar ta dauka ya cire security dan tana tabawa ta bude, hannu tasa kamar zata shiga gallery dinsa sai kuma ta girgiza kai, hakan bai kamata ba daga taimako?
Haka ta zauna ta rasa abinyi, ta kira Abba harsai uku bai dauka ba, tana nan a zaune a falo har bacci ya sake daukanta da alama bashin jiya ne bai barta ba. Tv tanata kara dan bata samu ta kashe ko tv din ba.

******
Aminu kam hankalinsa bai kwanta ba sai daya tabbatar ya saita komai a office dinsu sannan ya fito, gun saida waya ya tsaya yasai waya kirar iphone X Max karamar tashi ya sa sim sannan ya kira Ummy dan ya tabbatar ta nemeshi.
Yana dauka kuwa tace “Aminu inata nemanka wayarka a kashe�?
Yai dan gyaran murya kadan yace “Nadan fita ne Ummy……�?
Ai bai karasa ba tace “Ka fita kaje ina? Allah yasa ba barinta kai ba.�?
Mamaki Ummy ke bashi to yarinyar sa’arsu Islam ce da zai daukota ya dinga yawo da ita?
Ummy ce ta katsemai tunani, “Aminu?�?
Yace “Yanzu na fito ba dadewa nai ba, sannan ba waya a hannunta gashi tanasan kiran ‘yan gidansu.�?
Ajiyar zuciya tai alamar kwanciyar hankali sannan tace “Jiya na manta ban tuna ma kasai kaji ba, sai da asuba na tuna, a raina nace ai nasan Aminu nada zurfin tunani bazai bar ‘yar mutane ta kwana da yunwa ba.�?
Gefen wuyansa yadan shafa yace “Ai Ummy ni namanta da wata kaza, sannan yarinya tanata kuka ina ma take da lokacin cin wata kaza?�?
Takaici ya rufe Ummy sai dai ta dake tace “Amma kai kaci abinci ka koshi kafin ka tafi ko?�?
“Itama ai laifinta ne da bataci abinci a gidansu ba, Ummy wannan kuma ba laifina bane.�?
Ran Ummy ya kara baci tace “Yanzu ta ina zan samu na kirata?�?
Shikam kai tsaye yace “Ki kirata da daya layi na nabar mata wayata.�?
Jin haka yasa tadanji dadi kafin ta kashe wayar.
******

Ibty kam can taji wayar dake kusa da ita tana kara, cikin abin bacci ta dagota sam bata kula da me aka rubuta a jikin alan wayar ba kawai ta kara a kunnenta cikin abin bacci tai sallama.
Ummy daga can bangaren tace "Amarya ko bacci kike? Maman Aminu ce."
Da sauri mike ta zauna sosai kafin tace "Ina kwana? Au Ina wuni?"
Murmushi Ummy tai tace "Na kira naji konkin tashi lafiya ashe wai ya dan fita ko?"
Cikin girmamawa tace "Eh Ummy ya fita yaje ya dawo."
Cikin dan bugar ciki tace "Dafatan ya kula dake yanda ya kamata?"
Kunya ce ta kamata kamar tana ganinta tai kasa da kanta, ko ba'a fada ba Ummy tagane kunyar tambayar taji, cikin zolaya tace "Abinci fa?"
Tace "Naci sosai Ummy."
Ajiyar zuciya tai da alama ya kula da ita tunda gashi ya bata abinci, ya kuma bar mata wayarsa, dan shine yace ta kirata da daya layinsa, da alama hakan na nuna sun fara fahimtar juna.
Cikin jin dadi tace "Ki samu ki huta sosai abinki dan naji kawarki tace wani satin zaku koma makaranta ko?"
Ta daga kai kamar tana ganinta tace "Eh Ummy."
"Gidanki ma an fara gyarawa ina ganin gobe ko jibi zaku samu ku kuma.�?
Shiru tai dan batasan me zatace ba, Ummy tace “Aminu bayacin abincin waje, anjima zan ba direba ya kawo muku abinci, ki saki jikinki mijinki ne kinji?�? Yanzun ma kunya ce ta kara kamata tai kasa dakai.
Sallama sukai sannan ta kashe wayar, Ummy ta girgiza kai tace “Banda shirman Aminu jiya sai yabar amarya ba abinci?�?
*****
Mikewa tai tare da dauro alwala ganin azahar tayi, sannan tazo tai sallah a falo, tagumi ta zuba tana tunanin haka zata cigaba da zama kamar mayya?
Wayarsa ta dauko kawai ta duba game ta fara bugawa, alamun sa key taji da sauri ta mike ta fara tunani ko ta shige daki tai kamar tana bacci? Ko ta kame a kujera tai kamar tana kallo? Ganin an turo kofa yasa ta nufi kujera da sauri ji kake gum ta make kafa a jikin centre table din, wani irin kara ta saki da karfi dan taji wani azababben zafi har tsakiyar kanta.
Da sauri ya maida kofar ya rufe ya shigo cikin hanzari tare da ajiye ledar hannunsa ya kalleta sannan ya kalli kafar.
Dan karamin yatsar ta harya fara fitarda jini, kallanta yai cikin bacin rai kamar zaiyi fada ganin yanda take shishitun zafi tana runtse ido iya karfinta yasa ya fasa, hannunta ya rike wanda hakan yasa ta bude idanunta da sauri, kunya da haushin kanta duk sun rufeta, itakam meke damunta?
Kan kujera ya zaunar da ita tai sauri sa kanta cikin cinyoyinta kunya duk ta isheta.
Tissue ya dauko ya zauna kusa da ita sannan ya riko kafarta, da sauri ta bude idanta ta zubasu a kanshi, kallansa take yanda yake goge jinin dake kafarta, dan runtse ido tai jin zafi na ratsata.
Dagowa yai hakan yasa suka hada ido, cikin bacin rai yace “Shekararki nawa?�?
Rau rau tai da ido tace “Tsautsayine.�?
Ya kalli kafar yace “Daga jiya zuwa yau abubuwan tsautsayi nawa kikai? Sannan in ance muku yara kuce zakuji haushi.�?
Dan kafarta ta zare daga gun ta dan turo baki kadan tace “Ya Aminu wai komai nai sai ace yarinta nafafi shekara ashirin naji daga jiya zuwa yau ina…�?..�?
Kallanta dayai suka hada ido ne yasa ta kasa karasawa sai ta dan motsa baki tace “Allah ni ba yarinya bace.�?
Kafar ya jawo da karfi sannan ya dan nado tissue ya sa a gun ya mata alama data rike da hannunta, rikewa tai ya mike ya kwashi tissues din daya bata sannan ya sa a bin din falan kafin yace “Then act like an adult.�? Ya wuce toilet
Da kallo ta bishi cikin dan shagwaba tace “Nidai Allah a gida ba wanda yake cemin ina abin yarinta.�? A hankali tai maganar dan haka bai masan tanayi ba.
Dan shishitun zafin ta sakeyi.

*******
Masu jere kam sunsha kalli, gashi Ummy ta sa an kawo musu lafiyayyen abinci, an sau an kafa gado da wardrobe sannan sukaci suka sha kafin su koma gida.
Shikam Umar yana nan a tsaye a lungun gidan, sai dayaji yunwa na damunsa sannan ya fito ya nufi hanya yana neman mai awara.
Sai dayai tafiya sosai dan unguwar masu kudice babu masu awara a titi, yana tafe yana masifa “Banda ma muguwar Unguwa ace ko awara ba’a saidawa? Ba wata ‘yar wainar filawa ko kosai?�?
Yai tsaki sannan ya tsaya a jikin wani shago ya siyo bread da coca cola ya zauna yana ci yana kurba, sai dayaji ya koshi sosai sannan ya mike ya kalli agoggo ashefa baiyi azahar ba gashi la’asar ta kawo kai.
Nan ya nufi masallaci bayan yayi sallah ya zauna yanata addu’a akan Allah ya bashi ikon dauke Ibtisam dan ya gama shirinsa tsaf inhar ya dauketa to fa can Sokoto ko Zamfara zai lula da ita tunda yanzu suna cikin kasashen da mutane basa san zuwa hakan zaisa baza’ai tunanin can ya kaita ba.
Can yace “ya kamata na kwashi atamfofi da laces na sarar yanda zan ajiye kudi sosai�?
Yai dan murmushi ai ba matsala tunda ya riga ya sanar da abokinsa wanda yake da dan daki akan zai kawota nan a ajiyeta kafin mutane su daina zarginshi shi kuma ya tattara kudi sai su daga.
Kwafa yai yace “Har na hango idan dan banza a cell an kaishi da sunan yayi garkuwa da amaryarsa.�?
Dariyar keta yai a ransa, ai dama yayi kalar masu shan jini dan ya tabbatar wannan kudin ba na Allah da Annabi bane.

{Nikam Ayusher nace to waya sani ko kai ka taramai kudin?🤔}

🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:13 - Ummi Tandama😇: 💫 IB💫
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Dan Allah in baki siya ba karki karanta, kudi kalilan zaki biya ki samu wannan garabasar*

12
Tayi ta kiran malaminta bai dauka ba gashi gaba sai daya ta kasa sukuni, yanzu tana zaune za'a kawo ma Aminu amarya? Bayan tasa a ranta ko auren ne ma sai wacce ta zaba mai? Lalai akwai bala'i dan in batai wasa ba karshen zamanta anan ya kusa, tunowa tai da yanda 'yan uwanta suke difara mata tuwo bako miya haka za'a sa mata sandararen tuwon dawa, yunwa haka take sa wannan tuwon a gaba ta hau ci kamar mayya tanajin dadinsa, kwana kuwa a kusa da turken dabobi suka bata wata 'yar bukar ajiye kayan abincin gona anan take dan raba ta kwanta, a cewarsu mayya ce tunda maza uku tana aura suna mutuwa, gashi mahaifin Na'ima ne kadai Allah ya basu ziri'a dashi, kowani aure ta sake bata ko shekara mijin ke mutuwa.
Yanda gaba daya zufa ta fara keto mata ne zaisa ka dauka zafi akeyi, hijab dinta ta jawo ta dau jaka ta bude kasan gado ta debo kudi ta zuba a ciki, duk ta rikice da sauri ta zura takalmi sam bata kula wari da wari ta saka ba ta fita ta hau tafiya cikin sauri, sai datai nisa sannan ta tari adaidaita, sai datai canji na adaidaita hudu kafin ta isa canciki wani lungu, sauka tai sannan ta fito ta nufi gidan.
Ta isa sai data jira a waje saboda akwai wasu mata a ciki, ji take kamar zuciyarta zata fita dan ta tuna sanda Malam yace in har ta bari suka canza mata muhali ko ya sake aure har hankalinsa ya karkata kan mace tofa ta shirya komawa kauyensu.
Matan na fitowa ta afka ciki, nan ta kwashe komai ta sanar dashi, yan dube dubensa yai sannan ya sheke da dariya, kai ya shiga girgizawa kamar mai sauraran magana kafin ya kalleta yace "Aure an riga an daura."
Tashin hankali! Cikin faduwar gaba tace "Malam bansan anyi ba wlh munafirtata akai."
Shiru yai yana dube dube kafin yace "Karki damu zamu san yanda zamuyi, mafita daya garemu karki kuskura ki bari hankalinsa ya karkata kanta, bale har wani abu na rayuwar aure ya shiga tsakaninsu."
Hankali a tashe tace "Ba tare bake kwana da ita ba taya zan tabbatar?"
Ya miko mata wasu magunguna yace "Ki tabbatar kinsa a inda suke kwana, sannan wannan kisa a cikin abincin da Aminu zai ci shine zai dauke hankalinshi daga kanta. Banda wannan hanyar banida wata hanya kuma."
Amsa tai sannan ta bashi ladab aiki ta fito, itakam ko cewa akai ta yanko naman jikinta ta bada indai har za'a biya mata bukata a barta taji dadin rayuwa to fa zatayi.

{Nace Allah ya tsaremu da wannan bala'in}

**********
Aminu yana zaune yana waya aka kwankwasa kofar dakin, saurayi ne wanda hannunsa ke dauke da babban tire na abinci, ya gaidashi sannan yace "Sir an gama."
Yana kokarin shiga Aminu ya sa hannu ya amshi tiren yace "Zan shiga dashi."
Amsa yai sannan ya daurashi akan centre table, bakin dakin yazo tana kwance rufda ciki a kan gado, kallanta yai sannan yace "Ki fito kici abinci."
Cikin kunya tace "To."
Uban yunwan da takeji bazai barta tace ta koshi ba, haka ta gyara zaman babban mayafin sannan ta fito daga dakin, a zaune ta ganshi ta kalli tiren abincin sannan ta fara tunani, to yanzu zuwa zatai ta fara zubawabta mikamai sannan tasa nata? Ko kuma nata zata fara zubawa ta faraci shi inya shirya ci yaci nashi? Kai ta girgiza da sauri ganin hakan ba tunani, to meya kamata tai? Shiya zauna yana dane dane a waya.
Dakewa tai ta karasa tare da daukan plate, gani tai ya mike tsaye tai saurin cewa "A daki zakaci abincin?"
"Zan dan fita gun aiki ne na dawo."
Ta kalli abincin sannan tace "Kaci abincin mana tukun sai ka wuce."
Jakarsa ya dauka yace "Ke kici banacin abincin waje."
Baki ta bude sannan ta kalli yanda akansoya dankali da kwai, dayan plate din indomie da soyayyen kwai. Me bawan Allah din nan yake nufi? Ina zata kai wannan abincin?
Kallansa tai tana san magana taga haryasa takalmi, idanunta na kansa taga ya juyo dawowa yai cikin falan sanye da takalmi ya matso kusa da ita kawai ya zare sim dinsa ya ciro wallet dinsa ya dauko wani sim ya saka a cikin wayar, mika mata yai sannan yace "Kiyi amfani da wayata incase in wani abin ya tashi, ba dadewa zanyi ba amma tsautsayi bashida lokaci."
A hankali tasa hannu ta amsa, baiko jira me zatace ba ya juya, sai daya kai kofa ta iya furta "Nagode!"
Bai amsa ba ya maida kofar ya fita, kallan wayar tai wace alan wayar ke dauke da hotonshi da na Na'ima, itakam mutumin nan ta kula sam baya jira yaji ra'ayinta, abinda yamai kawai yake aikatawa, ta kalli abincin rufe dankalin tai kawai tadau indomie ta koma kan kujera ta kuna tv tana kallo tanaci, lalai yunwa takeji dan gani tai ta cinye indomie din nan tas, hamdala tai sannan ta mike ta hada tea ta zauna tana sha, wayar ta dauka ya cire security dan tana tabawa ta bude, hannu tasa kamar zata shiga gallery dinsa sai kuma ta girgiza kai, hakan bai kamata ba daga taimako?
Haka ta zauna ta rasa abinyi, ta kira Abba harsai uku bai dauka ba, tana nan a zaune a falo har bacci ya sake daukanta da alama bashin jiya ne bai barta ba. Tv tanata kara dan bata samu ta kashe ko tv din ba.

******
Aminu kam hankalinsa bai kwanta ba sai daya tabbatar ya saita komai a office dinsu sannan ya fito, gun saida waya ya tsaya yasai waya kirar iphone X Max karamar tashi ya sa sim sannan ya kira Ummy dan ya tabbatar ta nemeshi.
Yana dauka kuwa tace “Aminu inata nemanka wayarka a kashe�?
Yai dan gyaran murya kadan yace “Nadan fita ne Ummy……�?
Ai bai karasa ba tace “Ka fita kaje ina? Allah yasa ba barinta kai ba.�?
Mamaki Ummy ke bashi to yarinyar sa’arsu Islam ce da zai daukota ya dinga yawo da ita?
Ummy ce ta katsemai tunani, “Aminu?�?
Yace “Yanzu na fito ba dadewa nai ba, sannan ba waya a hannunta gashi tanasan kiran ‘yan gidansu.�?
Ajiyar zuciya tai alamar kwanciyar hankali sannan tace “Jiya na manta ban tuna ma kasai kaji ba, sai da asuba na tuna, a raina nace ai nasan Aminu nada zurfin tunani bazai bar ‘yar mutane ta kwana da yunwa ba.�?
Gefen wuyansa yadan shafa yace “Ai Ummy ni namanta da wata kaza, sannan yarinya tanata kuka ina ma take da lokacin cin wata kaza?�?
Takaici ya rufe Ummy sai dai ta dake tace “Amma kai kaci abinci ka koshi kafin ka tafi ko?�?
“Itama ai laifinta ne da bataci abinci a gidansu ba, Ummy wannan kuma ba laifina bane.�?
Ran Ummy ya kara baci tace “Yanzu ta ina zan samu na kirata?�?
Shikam kai tsaye yace “Ki kirata da daya layi na nabar mata wayata.�?
Jin haka yasa tadanji dadi kafin ta kashe wayar.
******

Ibty kam can taji wayar dake kusa da ita tana kara, cikin abin bacci ta dagota sam bata kula da me aka rubuta a jikin alan wayar ba kawai ta kara a kunnenta cikin abin bacci tai sallama.
Ummy daga can bangaren tace "Amarya ko bacci kike? Maman Aminu ce."
Da sauri mike ta zauna sosai kafin tace "Ina kwana? Au Ina wuni?"
Murmushi Ummy tai tace "Na kira naji konkin tashi lafiya ashe wai ya dan fita ko?"
Cikin girmamawa tace "Eh Ummy ya fita yaje ya dawo."
Cikin dan bugar ciki tace "Dafatan ya kula dake yanda ya kamata?"
Kunya ce ta kamata kamar tana ganinta tai kasa da kanta, ko ba'a fada ba Ummy tagane kunyar tambayar taji, cikin zolaya tace "Abinci fa?"
Tace "Naci sosai Ummy."
Ajiyar zuciya tai da alama ya kula da ita tunda gashi ya bata abinci, ya kuma bar mata wayarsa, dan shine yace ta kirata da daya layinsa, da alama hakan na nuna sun fara fahimtar juna.
Cikin jin dadi tace "Ki samu ki huta sosai abinki dan naji kawarki tace wani satin zaku koma makaranta ko?"
Ta daga kai kamar tana ganinta tace "Eh Ummy."
"Gidanki ma an fara gyarawa ina ganin gobe ko jibi zaku samu ku kuma.�?
Shiru tai dan batasan me zatace ba, Ummy tace “Aminu bayacin abincin waje, anjima zan ba direba ya kawo muku abinci, ki saki jikinki mijinki ne kinji?�? Yanzun ma kunya ce ta kara kamata tai kasa dakai.
Sallama sukai sannan ta kashe wayar, Ummy ta girgiza kai tace “Banda shirman Aminu jiya sai yabar amarya ba abinci?�?
*****
Mikewa tai tare da dauro alwala ganin azahar tayi, sannan tazo tai sallah a falo, tagumi ta zuba tana tunanin haka zata cigaba da zama kamar mayya?
Wayarsa ta dauko kawai ta duba game ta fara bugawa, alamun sa key taji da sauri ta mike ta fara tunani ko ta shige daki tai kamar tana bacci? Ko ta kame a kujera tai kamar tana kallo? Ganin an turo kofa yasa ta nufi kujera da sauri ji kake gum ta make kafa a jikin centre table din, wani irin kara ta saki da karfi dan taji wani azababben zafi har tsakiyar kanta.
Da sauri ya maida kofar ya rufe ya shigo cikin hanzari tare da ajiye ledar hannunsa ya kalleta sannan ya kalli kafar.
Dan karamin yatsar ta harya fara fitarda jini, kallanta yai cikin bacin rai kamar zaiyi fada ganin yanda take shishitun zafi tana runtse ido iya karfinta yasa ya fasa, hannunta ya rike wanda hakan yasa ta bude idanunta da sauri, kunya da haushin kanta duk sun rufeta, itakam meke damunta?
Kan kujera ya zaunar da ita tai sauri sa kanta cikin cinyoyinta kunya duk ta isheta.
Tissue ya dauko ya zauna kusa da ita sannan ya riko kafarta, da sauri ta bude idanta ta zubasu a kanshi, kallansa take yanda yake goge jinin dake kafarta, dan runtse ido tai jin zafi na ratsata.
Dagowa yai hakan yasa suka hada ido, cikin bacin rai yace “Shekararki nawa?�?
Rau rau tai da ido tace “Tsautsayine.�?
Ya kalli kafar yace “Daga jiya zuwa yau abubuwan tsautsayi nawa kikai? Sannan in ance muku yara kuce zakuji haushi.�?
Dan kafarta ta zare daga gun ta dan turo baki kadan tace “Ya Aminu wai komai nai sai ace yarinta nafafi shekara ashirin naji daga jiya zuwa yau ina…�?..�?
Kallanta dayai suka hada ido ne yasa ta kasa karasawa sai ta dan motsa baki tace “Allah ni ba yarinya bace.�?
Kafar ya jawo da karfi sannan ya dan nado tissue ya sa a gun ya mata alama data rike da hannunta, rikewa tai ya mike ya kwashi tissues din daya bata sannan ya sa a bin din falan kafin yace “Then act like an adult.�? Ya wuce toilet
Da kallo ta bishi cikin dan shagwaba tace “Nidai Allah a gida ba wanda yake cemin ina abin yarinta.�? A hankali tai maganar dan haka bai masan tanayi ba.
Dan shishitun zafin ta sakeyi.

*******
Masu jere kam sunsha kalli, gashi Ummy ta sa an kawo musu lafiyayyen abinci, an sau an kafa gado da wardrobe sannan sukaci suka sha kafin su koma gida.
Shikam Umar yana nan a tsaye a lungun gidan, sai dayaji yunwa na damunsa sannan ya fito ya nufi hanya yana neman mai awara.
Sai dayai tafiya sosai dan unguwar masu kudice babu masu awara a titi, yana tafe yana masifa “Banda ma muguwar Unguwa ace ko awara ba’a saidawa? Ba wata ‘yar wainar filawa ko kosai?�?
Yai tsaki sannan ya tsaya a jikin wani shago ya siyo bread da coca cola ya zauna yana ci yana kurba, sai dayaji ya koshi sosai sannan ya mike ya kalli agoggo ashefa baiyi azahar ba gashi la’asar ta kawo kai.
Nan ya nufi masallaci bayan yayi sallah ya zauna yanata addu’a akan Allah ya bashi ikon dauke Ibtisam dan ya gama shirinsa tsaf inhar ya dauketa to fa can Sokoto ko Zamfara zai lula da ita tunda yanzu suna cikin kasashen da mutane basa san zuwa hakan zaisa baza’ai tunanin can ya kaita ba.
Can yace “ya kamata na kwashi atamfofi da laces na sarar yanda zan ajiye kudi sosai�?
Yai dan murmushi ai ba matsala tunda ya riga ya sanar da abokinsa wanda yake da dan daki akan zai kawota nan a ajiyeta kafin mutane su daina zarginshi shi kuma ya tattara kudi sai su daga.
Kwafa yai yace “Har na hango idan dan banza a cell an kaishi da sunan yayi garkuwa da amaryarsa.�?
Dariyar keta yai a ransa, ai dama yayi kalar masu shan jini dan ya tabbatar wannan kudin ba na Allah da Annabi bane.

{Nikam Ayusher nace to waya sani ko kai ka taramai kudin?🤔}

🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:13 - Ummi Tandama😇: 💫 IB💫
      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Littafin kudi ne, kudi kalilan zaki biya ki samu wannan garabasar*
13
Da yamma Mamman ya kawo abinci, tunda Aminu ya shiga daki bata ga fuskarsa ba sai yanzu dataga ya fito sanye da jallabiya fara, bai kalleta ba ya nufi kofa, itakam tana zaune tana binshi da ido, wannan shine zaman kuramen, da tana ita kadai yanzu ya dawo ma ba wata maraba.
Kofa ya bude, tare da amsar banbar ledar dake hannun Mamman, tanaji suna gaisawa kafin ya shigo.
Ajiyewa yai akan centre table sannan ya kalleta, idanunta na kansa dama tana ganin ya kalleta tadanyi kasa da ido.
“Abinci ne Ummy ta aiko dashi, ni yanzu zanci kema in zakici yanzu to.�?
Mamaki ne ya kamata nufinshi su ci tare? Kartace a’a yaji ba dadi ko kuma ya dauka gudunsa take, ga kuma dankalin dazu ma bataci ba, sai dai tabawa masu aikin hotel din.
Dakinya koma ta mike ta bude babbar ledar ta dauko manyan kuloli guda biyu masu kyau da tsada, sai kuma karamin bowl mai murfi.
Shinkafa ce da miyan vegetables sunsha kaji, sai bowl din da aka zuba salad a ciki, ta dauko plate ta zuba musu dadan dama sannan tasa miyan a gefe, ganin zata cika plate din yasa ta bar salad din tace “sai kowa yasa a gabansa.�?
Ajiyewa tai a kasa tasa spoon guda biyu, tana kokarin fito da sanyayen kunun ayan dake cikin jug ya fito hannunsa dauke da kwalin waya, bai kula da abinda takeyi ba ya mika mata wayar hannunsa.
Kallan wayar tai cikin mamaki kafin tace “Ta mecece?�?
Gefe ya kalla yace “Bani wayata.�?
Mikewa tai ta bashi da sauri, yasa hannu ya amsa kafin yace “Akwai sim a ciki kiyi amfani da ita, in aka kawo miki taki sai ki zabi wacce kikeso in kuma zakiyi amfani da duka biyun to.�?
Wani irin dadi ne ya kamata, ta dade tanasan iphone amma sanin Abba bayasan kashe kudi ba gaira ba dalili yasa take lalaba ‘yar vivo dinta.
Cikin jin dadi tace “Ya Aminu! Da gaske tawa ce?�?
“To ko tawa ce karya nai?�?
Haushi yadan kamata shiwai maganar mutunci ne bai iya ba?
Takaici yasa ta kasa mai magana, bai damu sai a lokacin idanunsa suka kai kan abincin dake plate, ganin spoon biyu yasa ya fahimci me take nufi.
Cikin mamaki ya kalleta yace “Badai nufinki tare zamuci abincin ba?�?
Sosai wannan kalmar ta tsaya mata ta kalli abincin sannan ta kalleshi tace �? Tace kaine fa kace inyanzu zanci to.�?
Sosai ya kalleta yace “Inyanzu zakici to kema sai kici, a wani bayanin nace zan iyacin abinci dake? Shekararki nawa?�?
Yanzu kam taje makura duk da shakkarsa da take ta kalleshi tace “Wai Ya Aminu dan Allah shekara nawa ka bani? Jaririya ce ni ko me? Sannan maganar abinci ni bangane nufinka ba, tunda ka nuna bakaso ba shikenan ba? Amma meya kawo zancen sheka……�?
Kallanta dayai ne yasa tadan tsaya, kai ta kauda gefe tace “Nagode da kyautar waya sannan bangode ba da bakar magana.�?
Tana kainan ta shiga daki zuciyarta na tafasa, kofa ta bugo dadan karfi sannan ta zauna a bakin gado, takaici duk ya isheta, ko Iman ba’ace mata yarinya ba amma ita komai sai ya wani ce yarinya?
Aminu kam mamaki ne ya rufeshi yama kasa ko magana, sai can yace “Ni ta fadawa magana haka?�?
Yadan furzar da wata iska yace “Ni?�?
Kallan abincin yai sannan ya dau wani plate ya diba ya rufe ragowar ya zauna yanaci, yanaci yana sake maimaita kalamanta aransa, sai daya kusa cinyewa sannan yace “Ba yarinyar bace? Meye na jin haushi dan an kirata da hakan? Sannan ita banda madai ta rainashi taya zata kalleshi babba dashi tace zai sa cokali yaci abinci da ita?

****
Ibty kam a daki sai data gama huce haushinta ta dauko wayarta tana kallo, gani tai yasa mata data ta wata daya sannan akwai katin 2k a ciki, dadi ne ya kamata harta saka number Umma zata kira ta tuna kalaman Abba, jiki a sanyaye ta goge, shige shige kawai ta farayi tanata san gano kan wayar.
Camera ta shiga tanasan ganin kyan hoton canera din, tanata kyas kyas taji an bude kofa, daidai lokacin ta dan gyara zaman mayafinta tana yin selfie, ido tadan zaro ta kasa sauke wayar sai kallansa datai, a ransa yace “In ance mata yarinya taji haushi.�?
Fuska a dan daure yace “Abincinki da kika zuba zai huce.�?
Sauke wayar tai ta mike tace “camerar wayar nake gwadawa ba wani abin nake ba.�?
Kai ya jinjina yace “In ma wani abin kike ai babba ce kinsan me kikeyi no need to explain.�?
Ya maida kofar ya rufe, kai yadan girgiza yace “Ni har ina tunanin tana zaune ranta a bace saboda abinda na mata.�?
Ibth kam yana fita ta rufe fuskarta da hannayenta sannan tadan rankwashi kanta tace “Ba dole yace miki yarinya ba sai shirme kikeyi.�?
Mikewa tai ta ajiye wayar sannan ta danci mazu, ta daure fuska sosai, yanzu kam tasa a ranta komai cikin girma zata yishi.
Falo ta nufa, yana zaune yadan kalleta ta gefen ido. Abincin ta dauka sannan ta koma ciki bata kalli inda yake ba.
Bayan ta shiga daki ta maida kofar ta rufe tadan yi murmushi tace “Ko banza na rama tunda naje daukan abinci ban kalleshi ba.�?

{Nikam Ayusher dariya nasa nace haka ake ramawa?🤣}

*********

Duk yanda Hajiya taso ta kwantar da hankalinta ta kasa, harsu Ilham suka dawo daga islamiya, takaicinta ya kara karuwa dataga ko waya Aminu baiyi ba, bayan a iya saninta ko tafiya yai yana kira yaji yasu Islam suke.
Kallansu tai suna zaune a falo suna cin abinci, islam sai zuba takeyi, wani abu ne yazo mata ta sa hannu ta baza ta gumi, ganin basu kula da ita ba yasa tadan fara abin sheshekar kuka, tana dan goge fuskarta da gefen dankwalinta. Ilham cikin damuwa tace “Hajiya jikin ne?�?
Hajiya ta dan ja majina tace “Kun taba kallan film din Murjanatu ‘yar Baba?�?
Kai suka girgiza alamar a’a tace “Dasu na kalla a wata tasha gashi bakwanan balle mu kalla tare.�?
Islam tace “Hajiya mutuwa akai a film din yasaki kuka?�?
Ta danyi ajiyar zuciya tace “Yarinyar mahaifiyarta ta rasu tunda ta haifeta to sai babanta ya sake aure to matar ta dinga uzura mata tana wahalar da ita, yarinyar duk ta rame kullum kuka.�? Tadan yi jugum kafin tace “Haryanzu in na tuna ji nake zuciyata kamar zata fito, tsorona kar abinda ya sameta ya sameku.�?
Ai nan danan Islam ta rikice tace “Hajiya ai mu munada Dady.�?
Tace “Itama tana da mahaifi amma matsalar shi da yake aiki ina zai san abinda ake ciki a gida?�?
Ilham cikin rawar murya tace “yarinyar bata fadawa Babanta bane?�?
Hajiya ta jinjina kai tace “Ta fada amma bai yadda ba saboda matar tanada kirki a fuska, sannan har tsakar dare take dukan yarinyar.�?
Tsoro ne kiri kiri ya bayyana a fuskokinsu, Islam tace “Amma mu Dady ai bazaiyi aure ba ko?�?
Tace “Islam ai Dadynku ya riga yayi aure, shiyasa jiya da yau baku ganshi ba. Yana can wani guri da matarsa ya fara manta daku.�?
Ido suka zaro suka ajiye cokalin da suke cin abinci suka rarafo inda take, cikin matukar tsoro Ilham tace “Kenan muma haka za’a maidamu?�?
Ta daga kai sannan ta shafi kansu tace “Sai dai inhar ina raye bazan bari a cuceku ba, shiyasa nake zaune anan duk wulakancin da za’amin saboda ku bazan yi fishi ba.�?
Ai kamar ta tabosu nan suka sa kuka suka rungumeta, ta shafi kansu tace “Abu daya zaku taimaka dashi ku kwaci kanku, kunga dai yanzu dole zaku koma gun matar Dadynku sai dai kada ku yarda ta cuceku ta dinga muku wasa da dariya ko tana muku wasa kuna biye mata, tana ganin kun yarda da ita zata fara cutar daku.�?
Ai da sauri suka girgiza kai sukace bazamuyi ba Hajiya.
Dadi ne yadan shigeta dole fa ta shirya kwatan kanta, bayan magani sai ta hada da amfani da jikokinta.

{Nace andaiji asara wallahi an kuma fado ba nauyi🤔}

*******
Yanda yaketa zagaye a layin ne yasa wani mai gadi dake kusa da gidan Aminu ya fara tsarguwa dashi, gidan Aminu yazo ya kwankwasa kofa nan mai gadinshi ya fito.
Kallansa yai sannan ya nuna masa Umar yace “Mutumin can tun yama yake safa da marwa anan layin, bansan meyasa ba hankalina yaki kwanciya.�?
Kallansa yai sannan yace “Muje muji me yake anan in bashi da huja mu rikeshi mu kira ‘yan sanda, kasarmu yanzu ta zama abinda ta zama, yanzu sam ba yadda a kasar mu, kana dai ji tsabar san zuciya abinda malamin makaranta guda ya aikata.�?
Kai tsaye suka nufi inda Umar yake, lokacin yana duba agogo yana jiran abokansa da sukai zasu zo dan tayashi sace Ibty.
Jiyai an tabashi ta baya, ya juyo cikin fada yaga mutane guda biyu, kallansa sukai daya yace “Malam me kake anan layin tun yamma? Gashi har isha’i ta gabato?�?
Umar ya hararesu yace “Kan hanya nake fa ba gidan wani ba.�?
“Bari mu kira ‘yan sanda sai ka musu bayani.�?
Ganin suna neman ja mai masifa yasa yai saurin cewa “Ni yayan Ibtisam ne, matar da Aminu ya aura, ga gidan can.�?
Kallansa sukai, ganin basu yadda dashi ba yasa yace �? Munzo jere dazu to sun manta ba’a kawo wani abinda za’a daure kasan gado ba shine nake jira, yanzun dakukaga ina duba agoggo ganin dare yayi ne nakesan wucewa gida.�?
Kallanshi sosai mai gadin Aminu yai yace “Amma banganka ba sanda suka shigo jere.�?
Yace �? Tare mukazo baka kula bane, mata su hudu ne mu kuma maza biyu.�?
Ganin da gaske yaga mata hudu sannan yaga namiji daya yasa yace “To yanzu ka wuce daga nan, koma menene kwayi da safe. Tunda Amarya bata tare ba ai akwai lokaci.�?
Umar cikin damuwa ya kalleshi a ransa yace “Bata tare ba?�?
Ganin karsu gane yasa ya juya ransa duk a bace, iska ya nausa yana huci shikenan mai afkuwa ta afku wani katan banza ya kwacemai budurcin da yake tattali shekara da shekaru…�?

{🤭 Ansha tattali}

******
Sai datai magrib sannan ta fito ta dan tattare kwanukan, kallanshi tai duk da batasan mai magana amma ya zatai?
Ta daure tace “Ya Aminu wannan kafin ya lalace ko zakaba masu aikin hotel din?�?
Kallan abincin yai yace “Na safen ne baki cinye ba?�?
Ta daga kai tace “Dana gani dayawa na dauka dama hardakai.�?
Ya mike ya zo inda take, hannu yasa ya na kokarin amsar tiren, hannunsu ne suka hadu da juna, a hankali ya zare hannunsa ya amshi tiren, tadan daure tace “Nagode sosai da waya. Allah yabkara budi.�?
Kai kawai ya daga mata ya fita, kalan hanyar dayabi tai tace “Ikon Allah sai kallo, labarin da Ainah take bata akanshi ashe itace zatai rayuwa dashi, dan dama Ainah tace tun bayan rasuwar matarsa ko hira bayayi, Ummy ma intana hira yana gun sai dai yace to ko kuma amsar yar kadan.�?
Ajiyar zuciya tai tace “In na koma makaranta ai shikenan, a kala ina hidimar karatu na rashin kulani da zaiyi bazai damen ba, sannan gasu Islam sa debemin kewa.

🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:13 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

14🤸🏻‍♀�?
Haka ya dawo ya zauna yana tunanin wai haka zai ta zama a falo ba abinyi? Sannan jiya bacci sam baimai dadi ba dan bai saba kwanan falo ba, an hanashi zuwa aiki sannan gadan ma an hanashi kwana? Shi raini ne bayaso amma da tsaf zai wuce ya kwanta akan gadan inyaso ita ta kwanta a falo tunda dai ita yarinyace basu da matsala da inda zasu kwana.
Haka yai ta zaune, ya kishingida ya mike duk dai takaici ya isheshi, ganin magrib tayi yasa ya nufi daki dan yin alwala, Ibty kam tana mimike akan gado tanata latse laten waya, inama zataga Iman ta nuna mata wayarta? Itama ganin magrib tayi yasa ta mike tana dan danna wayarta tana nufar hanyar toilet.
Yatsa taji a goshinta, an dan turata baya kadan, da sauri ta dago ta kalleshi, yatsarsa na saman goshinta yace “Babbar mace me kikeyi hakan?�?
Kallan kanta tai da alama bigeshi ta kusa yi bata kula ba, itakam meke damunta dan Allah? Ji take kamar ta saki ihu saboda kunya da haushin kanta, daurewa tai saboda tasan daga ta nuna zai sake ce mata yarinya tace “Ya Aminu nice fa a dakin kaga kaine baka kula ba ka kusa bigeni.�?
Haryanzu yatsarsa na goshin ya kalli yatsar sannan ya kalleta yace “Then me hannuna yake anan?�?
Tadan daga ido sama ta kalli yatsarsa, idanu tadan rufe sannan ta bude guda daya tana kallansa.
Yace “Ehen?�?
Murmushi tai tasa hannu tadan sauke hannunsa daga saman goshinta tace “Yanzu dai Ya Aminu na bar ma ka farayin alwalar.�? Ta fada tana komawa kan gado.
Kallanta ya kuma yi ta zauna ta ajiye wayar tana murmushin da kana gani kasan na ya ke ne, kai ya girgiza sannan ya wuce toilet, shidai kam zaman nan ya isheshi, bari ai gobe tai ya kira Ummy gaskiya gobe yakesan komawa gidansa.
Harya fito tana nan zaune inda ya barta ta wani kame kamar gaske, shi abin ma so yai ya bashi dariya yanda taci serious haryanzu wayarta tana gefe bata dauka ba.
Kai ya kauda sannan ya bude jakarsa dake dakin da alama abu yake san dauka.
Ibty ta daure ta mike tare da daidaita tafiyarta cikin nutsuwa tanayi fuskarta haryanzu a hade, toilet ta shiga sannan ta rufo kofa.
Da kallo yabi kofar toilet din lalai yarinyarnan, zai gani in zata iya canzawar, ai dai yarintar a jikinta take.
Ibty kam tana shiga toilet tadan danne bakinta tana dariya, ta kalli kanta a madubi tace “Kai da kanka zakacemin babba, dan daga yanzu na bar yin shirme a gabanka.�?

{Nace ni ai ‘yar kallo ce😂}

********

Da safe Aminu yana cikin bacci akan kujera wayar Ummy ta shigo, mikewa yai sannan yai gyaran murya yana kallan agoggo, lalai rashin abinyi ya kamashi, bayan yayi asuba yau shine da komawa bacci? Sannan gashi bai tashi ba wai har tara da rabi na safe?
Daga wayar yai suka gaisa da Ummy, daga can tace “Aminu Allah yasa ba ni na tasheku ba.�?
Yadan yi gyaran murya kadan yace “Ummy dan Allah so nake yau ko zuwa yamma na koma gida, zaman kurkukun nan ya isheni.�?
Tadanji ba dadin kalamansa sai dai ta fahimci dama dole fa sai anyi hakuri, tace “Ba wani abin dan dama yau sukace zasuyi jeren kujerun da kayan kitchen, labulaye ne dai sai a hankali dan san an dinka sannan za’a kawo.�?
Kai ya jinjina yace “Yau din da yamma in dauketa mu wuce kenan?�?
Tace “Eh itama ya kamata ta samu tagama gane gidanta kafin ta koma makaranta�?
Bai tanka ba dan a ganinshi wannan abinda ya shafeta ne bashi ba, Ummy ce ta katseshi “Me kukeso a abin kari? Kai dai na sa an soyama doya da farfesun kayan ciki, ko zaka tambayi Ibtisam me take so?�?
Mamaki ne ya kamashi yace “Ummy ni zan tambayeta me takeso?�?
“To ni da nake nan ko ni zan taso nazo?�?
“Ummy ba kinada numberta ba? Ki kirata kiji mana.�?
Tadan yi shiru kadan kafin tace “Yanzu dan neman magana kuna guri daya sai na kiraka na kashe sannan itama na kirata? Ni tambayomin ita dan Allah.�?
Mikewa yai ransa duk a bace yace “Ummy Allah da saninki kike wannan abubuwan ga kawarta nan a gida ai na tabbatar tasan me take so.�?
“Kawarka takai mijinta ne? A kalla dai kai kuna tare itafa?�?
Dan kai ya kauda a ransa yace “Duk wani salan a rainashi Ummy ta sani, yanzu kawai sai ta sashi yaje yana cewa Ibtisam me zakici da safe?�?
Yana wannan tunani ya isa kofar dakin, daga waje yai dan knocking.
Ibtisam ta fito daga wanka kenan sanye da towel tana duba kayan da zata sa a jakarta, kallan kofar tai da sauri, sannan ta kalli kanta, gashi towel din hotel din ba babba bane dan ko gwiwarta bai sauko ba, jin an sake kwankwasawa yasa ta shiga dibi dibi, me zatai? Ganin mayafin data cire na jiya tai a kan hado da sauri ta nufi gadan daidai nan shikuma ya turo kofar dan yayi zatan ko tana bacci ko kuma tana toilet.
Taje daf da gado shi kuma ya bude kofar, kallansa tai da sauri duk ta rasa ma me ya kamata tai, mamaki ne ya rufeta ganin ko a jikinsa, kallanta yai yace “Ummy ke tambayar me kikesan ci da safe?�?
Kamar wacce aka kamar da ita haka ta tsaya, hannu tasa a saman kirjinta, dakyar tace “Koma menene zanci.�?
Bai jira wani abu ba ya juya yabar dakin, ya maidawa Ummy abinda tace sannan ya kashe wayar.
Zama yai a falo yana tuno abinda ya faru yanzun nan a daki, meyasa ta rufe kirjinta? Badai ta dauka kallan jikinta yake ba? Kai ya girgiza yace “Lalai yarinta da ciwo.�?
Ibty kam kaya ta saka tana sawa tana mamakin yanda ya nuna ko a jikinshi daya ganta a haka, a kalla ta dauka zai koma ya barta ta shirya, to ko dan yana waya da Ummy ne? A ranta tace haka ne ma.

******

Wajen karfe sha daya aka kawo musu abinci, yanzu kam batai gigin cewa zasuci tare ba, ta hada kwanukan jiya Mamman ya koma dasu, kasancewar Aminu na wanka yasa ta zauna a falo ta zuba doya da farfesun kayan cikin, sannan ta hada tea, ta kuna tv ta zauna tana ci tana kallo.
Ko bayan ya fito daga wanka kin zuba abincin yai, mamaki ya kamata ta daure tace “Ya Aminu ko na zuba maka?�?
Kai ya daga mata alamar eh yana duba abu a laptop dinsa, a ranta tace “Maza sai a barsh da tsinanen san girma abinci a gabansu amma sainsu baje suna jiran a zuba musu.�? Samai tai sannan ta ajiye kan centre table din, ta kalleshi tace “In hado ma tea?�?
Yanzun ma bai kalleta ba sai kai kawai daya daga mata alamar eh, tana kokarin mikewa yace “Karkisa sugar.�?
To kawai tace sannan ta wuce gun fridge ta kuna kettle, tana yi tana kallansa, haryanzu bai dauki abincin ya fara ci ba, so yake sai ya huce ko me? Can tace Hmm ko meya dameni oho? Mutum da cikinsa?
Kawomai tea din tai ta ajiye a kusa da abincin, kallanta yai sannan ya ajiye laptop din a gefe itama kallanshi tai ganin sun hada ido yasa ta sauke nata idon kasa, dagowa tai tana neman juyawa. “Thanks.�? Abinda yace kenan, juyowa tai suka sake hada ido m, samun kanta tai da mai murmushi mai sanyi, dan harga Allah taji dadi daya gode mata.
Kansa ya dauke ya dau abincin ya faraci, ita kuma ta wuce daki tana ganin bai kamata ta zauna ba yana cin abinci.

********
Su Kawu sun shirya tsaf bayan la’asar zasu koma kauyensu, duk da komai ya lafa haryanzu Kawu bai saki jiki da abinda Umar yai ba, daren jiya suka kai Bilkisu bangarenta ganin Umar ya sauko, sai dai abinda basu sani ba yanda suka kaita haka ta kwana ita kadai, dan Umar baima shigo gidan ba sai da akai sallar asuba, yana can yana lissafin abubuwan da ya kamaceshi.
Balle dayaga wayar Naziru yana sanar dashi ankai Bilkisu bangarenta ransa ya sake mugun baci, haka yai zamansa a masallaci sai bayan asuba ya shiga cikin ‘yan gida suka koma.
Abba kam duk sun dauka a bangarensa ya kwana dan sun ji alamun shigowarshi da suka leka sukaga yayi bangaren da aka kai Bilkisu, sai dai abinda basu sani ba yana shiga ya fita ta kofar gidan, haka Bilkisu ta kwana, taci kukanta har ta gaji, da asuba kawai taji sallamarsa.
Dadi ne ya kamata ta kalleshi tana zubar da kwalla, da yake an juna musu solar a gidan hakan yasa gidan yake da wuta kamar ta nepa.
Dauke kai yai daga kallanta ya fara kallan gidan yana daddaga pillow din da akai jere dasu akan kujera. Kai ya jinjina yace “Ba laifi kujerun suna da kyau, kuma giredi ne amma menene amfaninsu bayan wacce aka siya dominsu bazata iya morarsu ba? Dan soyayyarnan aja mace in tana tsaye su fada kan kujera baza’a iya yi da ita ba?�?
Wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mata tasa hannu ta share, labulayen dakin ya daga yadan tabe baki yace “Nan irin soyayyar nan da ake na mace ta boyewa miji zaki iya?�?
Kasa tai dakai hawaye suna gudu akan fuskarta, ya zauna akan kujera ya daura kafa daya kan daya yana dan girgizawa yace “Da alama jikina ya bani kece silar rugujewar farincikin rayuwata kila shi yasa ko sau daya ban taba tsausayin ibtila’in da Allah ya dora miki ba dan ni Ibty nake so tunda ita lafiyarta kalau hankalina bai taba karkata akan wahalar da kikesha ba, ashe ashe kece bala’i da masifar rayuwata, wacce zata rabani da masoyiyar da duk duniya ba wacce nakeso sama da ita.�?
Umar ya buga mata wani kallan tsana da kiyayga yace “Bandamu da auren da aka mata ba dan wlh ba wanda ya isa rabani da ita, matatace ni kadai shi kanshi wanda yai gigin auran nata tausayinsa nake dan ina tausayawa halin da zan jefashi.�?
Ya zo kusa da ita yadan buge keken da take kai sannan ya wuce daki yana wani kallo yana tabe baki, kwanciya yai akan gadon ya mike kafa yana girgizasu, inhar wannan tsinanen mutumin ya kuskura ya kusanci Ibty to lalai ko sun bar Kano sai ya sa an mai tsinanen dukan da bazai sake kusantar wata mace ba a duniya.
Haka su Kawu bayan la’asar lokacin su Goggo sun dawo daga jere suka dau hanyar garinsu, bayan Kawu yayi tayiwa Umar fada wanda a zahiri fadan ko a kwalar rigarsa bai dauka ba. Amma a fili ya dinga daga kai yana cewa “Insha Allah.�?

*******

Da yamma yana sallar la’asar ya kwankwasa mata kofa, tana zaune akan sallaya bayan tayi sallah tanata lazimi, mikewa tai ta bude ta kalleshi.
Kallanta yai sannan yace “Ki hada kaya zanje nai check out sai mu wuce.�?
Bata san sanda tace “Ina?�?
Dan sam ta sha’afa wani gidan za’ankaita ta dauka gidansu za’a maidata dan har gabanta ya fadi tana tunanin karfa in Umar ya ganta komai ya dawo sabo.
Jitai yace “Gida mana, ko ke zaman nan din dadi yake miki?�?
Sai a lokacin ta tuna ashe fa tayi aure yanzu gidanta daban, kasa tai dakai tace “Bari na hada kayan.�?
Juyawa yai ya fita ita kuma ta fara tattare musu kaya, tanayi tana tunanin ko ya su Islam zasuji in suka ganta? Murmushi tai dan tanasan kyawawan yaran nan.
Aminu bai dade ba ya dawo, hannu yasa ya amshi jakukunan datake kokarin fitowa dasu falo daga daki, kallansa tai bayan ta sakar mai tace “Nagode.�?
“Ki dauko basket din da aka kawo abincin, sannan ki sake dubawa in akwai abinda kika manta, banasan sai munyi nisa kice kin bar wani abin anan�?
Aranta tace “Magana ce dai baza’amin cikin dadin rai ba.�?
Kamar yasan me take cewa sai jitai yace “Tuna miki dai nake.�? Ya wuce hannunsa dauke da jakukunan, dan baki ta turo tace “Kowa ma ai yana mantuwa, kaima kila ka manta da wani abin.�?
Mamaki ne ya kamata ganin duk abinda aka manta nata ne babu abinshi ko daya.
Haka ta fito ta shiga mota…�?

******
Hajiya sai zagaye takeyi tana leken katanga sam bata damu da masu aikin ginin ba har masu jere suka fita sannan tai wuf ta shiga bangaren, mamaki ne ya kamata ganin gidan a garkame, ta gwada key dinta na gidan yaki shiga, kallan gun sa key din tai wato canjashi ma akai? Lalai Ummy wato ita take nema taciwa zarafi?
Haka ta dawo bangarenta zuciyarta duk a dagule, dole in yaran nan suka dawo ta sake hure musu kunne in har ba so take a maidata kauye ba dan wlh akan a maidata kauye lalai zata iya yin abinda har su mutu bazasu manta da ita ba.

🏌🏻‍♀�?
2/8/22, 08:16 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

15🤸🏻‍♀�?

Cikin katafaren gidan yai parking, kallan harabar gidan tai duk da tasan kudinsu Ainah bata kawo gidan Ya Aminu yakai haka girma ba, ganin ya fito daga mota yasa itama ta fito tabi bayansa. Mai gadi ne ya taho da gudu bayan ya rufe gate yazo yana gaishesu, cikin girmamawa ta amsa, sannan ta kada bin bayan Aminu.
Key ya dauko ya bude gidan sannan suka shiga, cikin katafaren falanshi suka tsaya tana kallan yanda falan ya tsaru, kallanta yai yace “Tacan kofar ne bangarenki�? kallan inda ya kalla tai batace komai ba, harzai shiga ciki sai kuma taga ya dawo, gaba yai ta sake bin bayansa zuwa nata bangaren, da alama akwai kofar da in aka tashi shigowa ba sai an shigo ta falansa ba, itama falanta ba karami bane sai dai baikai girman nashi ba, gashi ansa mata kujeru masu kyau, labulaye ne dai sai mai shara shara na ciki aka saka, kallan dakunan dake jikin falan yai guda uku, yana daga tsaye a bakin kofar dake tsakanin falan biyu yace “wancan ne dakinki, na kusa dashi nasu Islam ne sai dayan na baki in kinyi.�?
Kallanshi ta juyo tai tace “Ina su Islam din? Naga basa nan?�?
“Suna gun kakarsu.�?
Kai ta jinjina tace “Da mun sani mun biya gidan Ummy mun taho dasu ai.�?
“Bagun Ummy suke ba.�?
Mamaki ne ya bayyana a fuskarta tace “Gun wa? Naji kace kakarsu?�?
Yadan daure fuska kadan yace “Gun dayar kakarsu, sannan suna nan daya bangaren insuka san na dawo zasu shigo.�?
Gaba daya ta kasa gane me yake nufi cikin dauriya tace “Kakar tasu anan daya bangaren take ko me?�?
Juyawa yai yace “Eh! Agurina take a zaune.�?
Zaro ido tai cikin tsananin mamaki tace “Kakarsu ba mahaifiyar Aunty Na’imah kenan ba? Me take a gidanka?�?
Wani kallo ya watsa mata fuskarsa ya sake murtukewa yace “A karshe cewa kikai gidana ko? Kenan inada ikon ajiye wanda naso.�?
Tsananin mamaki yasa ta zubamai ido, bata gama tattaro tunaninta ba taga yabar gun, kasa daurewa tai a fili tace “Ina aka taba wannan abu?�? Yana jiyota bai tankata ba.
Tana tsaye tana dogon nazarin wannan lamari itakam tunda take bata taba jin inda uwar matarka data rasu take zaune da namiji ba, mutum ba muharaminta ba bakomai ba?
Sam kwakwalwarta ta kasa nutsuwa dajin wannan saban lamari mai abin mamaki.

******
Aminu kam rai a bace ya wuce dakinsa wato daga zuwanta hartana neman nunamai abinda yai baiyi daidai ba? Ita a wa? Haryaushe ma tazo gidan da zatamai gadarar banza?
Toilet ya shiga ya watsa ruwa sannan ya fito, waya ya dauka yaga missed call din Hajiya, da sauri ya kirata.
Ringing biyu ta dauka, dan tunda taji bude gate ta kasa zaune ta kasa tsaye, daki ta shige tabarsu Ilham a falo suna wasa.
Sallama tai cikin muryarta, ya amsa cikin girmamawa sannan ya gaisheta, ta amsa kafin tace “Tunda su Islam sukaji karar gate dinka suke ta ihu wai su sai sunje sun gaisheka.�?
Murmushi yai yace “Su shigo mana Hajiya, sannan inda hali ma su kwana anan tunda gobe asabar.�?
Tace “Ayi haka kuwa? Daga zuwan Amarya sai a daura mata wahala?�?
Jikinsa ne yai sanyi yace “Kiyi hakuri Hajiya nayi aure bansanar miki ba.�?
Shiru tai kafin tace “Aminu magana ta gaskiya naji ba dadi, dan bansan da auranka ba sai ranar da akazo jere, nayi mamaki kwarai da gaske, a tunanina nima mahaifiyarkace, saidai yanzu ka nunamin iyakata, ka tabbatar da banida daraja a gunka.�?
Kai ya girgiza da sauri yace “Wlh Hajiya ba haka bane, komai na auran nan ya faru ne cikin gaggawa, nikaina bansan ya akai abubuwan nan suka kasance ba.�?
Murmushi tai na rashin jin dadi kafin tace “Yanzu dai bari na rako su Islam, sai dai daga jiya zuwa yau na yanke shawarar barin gidan nan, dama nacigaba da zama ne saboda yaran nan, tunda yanzu sunada mai kula dasu inaga gwarw……�?.�?
“Hajiya ki bar maganar nan dan Allah! Ke amanace a garrni.�?
‘Yar karamar ajiyar zuciya tai da alama haryanzu aiki na jikinshi.
Nan sukai sallama akan zata rako su Islam.
Falo ta fito ta kallesu tace “Ku dauko dankwalinku muje ku gaida Dady ya dawo.
Tsale suka fara cikin tsananin murna, Hajiya tace “Kardai ku manta Dady ya kawo matarsa.�?
Yanayinsu ne ya canza lokaci daya, Ilham tace “Muguwar matar?�?
Kai Hajiya ta daga alamar rashin jin dadi tace “Kardai ku manta inhar kunaso karta wahalar daku ta dinga dukanku, kada ku kuskura kuyi hira ko wasa da ita, ko abinci tai kuce baiyi dadi ba kunfi san nawa.�?
Da sauri suka daga kai alamar to, tace “Sannan kada ku kuskura kuce ni na fadamuku inba haka ba in taji nasan sirrinta zatasa Dady ya koreni.�?
Hankalinsu ne ya kara tashi da sauri sukace bazamu fada ba Hajiya sannan bazamu taba yadda a koreki ba.
Ya shafa kansu sannan suka fito tare.
Ibtisam tana tsaye inda Aminu ya barta haryanzu ta kasa tattaro tunaninta, amma ai su Ummy basu sanar a gidansu ba, itakam wani abu ne wannan? Banbarakwai wai namiji da suna Hajara? Ji tai ana kwankwasa kofar dake jikin falanta.
Kallan kofar tai haka kawai taji gabanta ya fadi, daurewa tai ta tako a hankali tana tunanin wanene wannan daga isowarsu?
Jikin kofar taje tace “Wanene?�?
Daga waje Islam cikin tsiwa tace “Su Islam ne.�?
Murmushi ne ya bayyana a fuskar Ibty da sauri ta bude kofar.
Kallanta sukai a tare sukace “Kawar Aunty?�?
Ta rusuno ta lakuci kuncin Islam tace “Mai dimple?�?
Ilham tace “Kema kinzo ganin amaryar Dady ne?�?
Murmushi tai tana kallansu, dan dagowa tai idanunta suka hadu da babbar mace dake tsaye a waje tana kallanta.
Yanzu ma gabanta ne ya sake faduwa, ta daure tace “Ina wuni?�?
Hajiya ta kalleta fuska dauke da Murmushi tace “Kece Amaryar tamu?�?
Tadanyi kasa dakai cikin kunya, kallansu Islam tai tace “Ashe ma kunsan Amaryar Dady din?�?
Kwace jikinsu sukai daga gun Ibty suka nufi gun Hajiya da sauri suka rike hannunta.
Shigowa sukai tace “Kuyi maza ku gaida Mumy dinku.�?
Kallanta sukai fuskarsu duk ta canza, ciki ciki sukace “ina wuni?�?
Kafin Ibty ta amsa sunyi bangaren Dady dinsu da gudu.
Cikin mamaki Ibty tabi bayansu da kallo, Hajiya tace “Yara ne basu san da auran ba shiyasa.�?
Kai ta daga sannan ta tsuguna ta gaisheta, amsawa tai tana kare mata kallo, da alama yarinyar zatai saukin juyawa dan kana ganinta kasan ba irin yaran zamani bane masu wayau ba.
Ibty tai kasa dakai gashi ko kitchen bata sani ba balle ta duba ko akwai ruwa ta kawo mata.
Mikewa tai tana tunanin inane kitchen din? Muryar Hajiya taji a bayanta tace “ga kitchen din can.�?
Yanzun ma gabanta ne ya fadi dan sam batai zata. Jin muryarta a bayanta ba, cikin sanyin jiki ta nufi kitchen din, itama Hajiya tabi bayanta.
Suna shiga ta kalli kitchen din tace “Ansha jere, kamar Na’ima bata zauna a gidan ba, angyarashi tsaf.
Dakyar Ibty ta dan daga kai, Hajiya ta dan matso ta dafata tace “Nasan zakiga zamana a nan bai dace ba, sai dai inasan sanar dake karki damu, dama rashin auransa ne yasa na hakura na zauna, sai dai yanzu tunda kinzo nakuma yaba da hankalinki zan tattara na koma garinmu.�?
Itakam Ibty kai kawai tai kasa dashi dan batasan me zatace ba, bari muga dakin amarya.
Kafin Ibty tai magana sai gani tai ta fito daga kitchen, da sauri ta biyo bayanta dan ko ita kanta bata shiga dakin nata ba.
Kai tsaye taga ta shiga dakin daya nuna nata ne, bin ta tai a tsaye ta ganta tana murmushi tana sanya albarka, Ibty ta kalla tace “Sai naji kamar karar ruwa na zuba daga bandaki ko?�?
Kunne tadan kasa kafin tace “Banji ba, sannan banma shigo dakin ba balle na kuma.�?
Hajiya tadan dafata tace “Kin manta ‘yan jere sunzo? Kije ki duba nidai naji karar ruwa.�?
Kallan wata kofa tai wacce da alama itace ta toilet din, tana shiga Hajiya tai saurin daga gado tasa wannan layar da aka bata a kasan katifa, tana maidawa Ibty na fitowa da sauri ta zauna akan gadan tana cewa “Daki yayi kyau masha Allah! Allah ya kawo kazantar daki.�?
Itadai Ibty ko Amin din ta kasa cewa saboda jin abin take wani banbarakwai.
Hajiya ta sake takowa inda take ta dafata tace “Allah ya baku zaman lafiya, Aminu a haka zakiga kamar mutum ne mai wuyar fahimta sai dai ina tabbatar miki zakiji dadin zama dashi, dan haryau ina tuno irin kulawa da farincikin da Na’imah ta samu a gunsa.
Kanta na kasa kawai tana wasa da yatsun hannunta, Hajiya tadan shafa kanta tace “Bari na wuce, su Islam yace zasu kwana anan saboda gobe asabar.�?
Kai kawai ta daga dan haka kawai ta samu kanta dasan matarnan ta tafi.
Tana fita ta sauke ajiyar zuciya, tare dayin hamdala, tace “Mata ba kishiya ba bakuma uwar miji ba, dame zan kirata?�?

****
Bangaren Aminu ta nufa, tana juyo ihunsu Islam da alama labari take bashi, murmushi tai sannan ta shiga cikin falan, daga daki take juyo maganarsu, kunya takeji ta shiga dakin daga zuwanta, komawa tai bangarenta tana sake kallo, ba shakka Abba yayi kokari a yanda tasan bayasan sakin kudi lalai yayi kokari.
Kayanta ta dauko ta fara jerawa a cikin wardrobe tana yi tana tunanin yaushe Ainah zatazo?
Kamar daga sama taji ana kiranta, da sauri ta fito yana dan jingine da bangon falanta.
Kallansa tai tace “Ya Aminu gani.�?
“Kun gaisa dasu Islam?�?
Ya daga kai alamar eh sannan tace “Gaisuwa kawai mukai da alama zumudin san ganinka suke basu tsaya ko hira munyi ba.�?
“In ke baki jasu da hira ba su ta ina zasu saki jiki?�?
Kalamansa sun bata mamaki, yau fa aka kawota? Ai dai a mata kara a bari susan juna sosai ko?
Jitai yace “Sorry bawai takuraki nai ba daga zuwanki jinai Islam tace kin daure fuska bakyasan su miki magana.�?
Yanayin fuskarta ne ya bayyanar da tsananin mamakinta tace “Tare suke da Kakarsu, Ya Aminu so kake nai abin da za’acemin yarinya a gabanta?�?
Shiru yadanyi da alama ya fahimci laifinsa, amaryace fa ya kamata a barta a hankali tukun.
Gyaran murya yadanyi yadan shigo cikin falan yace “Kin shiga kinga gidan?�?
Fuskarta a hade tace �? A’a.�?
Yanda tai maganar ya tabbatar ranta ne ya baci, ganin basu da abin cewa yasa ya koma bangarensa.
Kallansu Islam yai dake kan gadansa suka hira, yace “Islam kun manta Mumy dinku Amaryace? Sai a hankali zata saki jiki, sannan laifinku ne da baku dade a gunta ba.�?
Kallan juna sukai Islam da Ilham, a ransu sukace wato har anfara hadasu fada da Dady kamar yanda Hajiya tace ko?
Dama Aminu bamai zama yai wasa bane, sai dai in suna hirarsu zai jisu, gaba daya yanayinsu ne ya canza, suka zauna sukai shiru duk suruntu Islam bata sake cewa komai ba, a haka har sukai bacci.
Ilham ya fara daukanya nufi bangaren Ibty da ita, yana shiga ita kuma tana fitowa daga daki zataje kitchen dan kishirwa takeji, kallansa tai da sauri ta bude kofar dakin daya nuna nasu ne, jitai yace “Thanks.�?
Nan ya wuce ya kwantar da Ilham a gadan sama, sannan ya fito ya koma ya dauko Islam ya kwantar a gadan kasa, karasowa tai ta gyarawa Islam kwanciya sannan ta luluba musu bargo, addu’ar bacci ta musu ta shafa sannan ta dago.
Yana tsaye yana kallanta harta iso bakin kofa.
Hanya ya bata ta fara fita sannan shima ya fito, hannu yasa a aljihun jalabiyarsa yace “Akwai ruwan tea kuwa?�?
“Bansan kan kitchen din amma nasan dai ruwan zafi bazai gagara ba.�?
Kitchen din ta nufa yabi bayanta, ruwa tasa a kettle yana tsaye yana kallanta, wato haryanzu bata ware ba? Badai so take ya bata hakuri ba ko?
Neman cup ta shiga ta dauko spoon ta zuba, ina sugar? Da lipton?
Muryarsa ce ta katseta “ki zuba ruwan a flask dashi zan wuce, sannan inada lipton a dakina, cup da spoon kawai nake so.�?
Bata kalleshi ba sainto kawai datace, hadawa tai tasa akan tire, sannan ta nufo kofa, hannu yasa ya amsa.
Kallan juna sukai, a hankali ta dauke idanta jitai yace “Barshi zan wuce dashi.�?
Kai ta daga alamar to, amsa yai sannan ya sake kallanta, “Akwai abinda zakici da daddaren nan ko nasa a kawo miki?�?
Kai ta girgiza alamar a’a tace “Akwai ragowar doyar safe zanci, amma kai daga tea shikenan?�?
“Zan hada da bread naba mai gadi ya siyo kayan tea da bread.�?
Shiru suka danyi kafin yace “Wajen nawa zaki kwanta?�?
“In na gama gyara kayana abinci kawai zanci na kwanta.�? Abinda tace kenan, dan ta tabbatar babu wata sha’awar janta a jiki da Aminu yake dashi balle tasa ran zai nemi su kwana tare, idanunsa kadai inta kalla tasan bashida wannan ra’ayin, to ita ta zauna tayi me?
Kai ya jinjina yace “in akwai abinda kikeso kimin magana, sannan kafin ki kwanta please kikai Islam toilet tai fitsari, Ilham tana tashi da kanta.�?
“To�?
Yadan sake kallanta yace “Gobe sai kimin list din abinda kikeso na kayan abinci, dan duk kayan abinci a gun Hajiya suke, daga bangarenta take dafa mana.�?
Sakato tai tana jin wannan lamari, ikon Allah sai kallo, Aminu ya juya ya tafi bangarensa, daki ta koma ta zauna a bakin gado tana kallan kayanta.
Wannan aure anya zataji dadinsa kuwa? Ai ko a garin gala galu mutum yaji ance zai zauna guri daya da mahaifiyar matar miji wace ta rasu to fa ansan akwai matsala, ta dauka yara ne kawai zataja a jiki yanzu wani irin zama akeso tayi? Itakam anya tanada raban samun farincikin aure a rayuwarta? Ta rabu da Umar yanzu kuma wace rayuwa ta fada?

😢Nikaina Ayusher tambayar datazomin kenan.

🏌🏻‍♀�?
2/14/22, 10:20 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

16🤸🏻‍♀�?

Kallan dakin tai, tausayin kanta ya kamata, ada in tana karanta novel ji take inama abinda ke faruwa a ciki ya faru da ita? Yanda namiji ke dokin daren farko? Asha love, a kaika toilet a gasa ka? Sai dai duk wannan bori nata ya tsaya ne daga sanda ta fahimci lalai Umar bazai barta taji dadin rayuwa ba, ko a skul in kawayenta na hirar kwanciyar aure sai dai tai shiru tana kallansu, to ita gashi ta auri wani ba Umar ba amma ko kadan bataga alamar sha’awarta a tattare dashi ba.
Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki bayan ta kara kallan dakin, namijin da kuka kwana a hotel ku biyu tare bai nemeka ba ina zakasa ran zai nemeka a gatan gida haka? Inda bangarensa daban? Ga yara? Ga kuma wata mata a can bangaren da batasan me zata kirata ba.
Kayan bacci ta saka sannan ta saka hijab ta fito daga cikin dakin, haka kawai ta samu kanta da rashin san kwanciya a dakin.
Bude dakinsu Islam tai kawai ta dauko pillow da bargo ta kwanta a kasa, akalla dai ta dingajin numfashin mutane.
Ta dade tana juyi a kasa bayan takai Islam fitsari kafin bacci ya dauketa, bacci tai sosai dan ta dade tana juyi a kasa.
Aminu kam bayan ya dawo daga masallaci harzai wuce daki sai kuma ya dawo, tunani yake da alama batasaba da gidan ba kila ta makara sallah.
Dakinta yadan murda kadan tare da haska fitilar wayarsa, da karfi naga ya tura kofar ganin ba kowa a ciki.
Ga kuma bandaki a bude, babu alamar mutum a ciki, samun kansa yai da rikicewa, ina ta shiga? Fitowa yai daga dakin ya wuce kitchen, nan ma ba kowa, tashin hankali ne kiri-kiri ya bayyana a fuskarsa, dakin baki ya bude nan ma babu alamarta, saman goshinsa ya shafa sannan ya bude dakinsu Islam dan ya tabbatar ko su lafiyarsu kalau.
Tsayawa yai kawai daga bakin kofa yana kallanta tana bacci a kasa, kai ya girgiza sannan ya shiga cikin dakin, sake haskata yai yana tunanin me takeyi a kasa? Bayan ga dakinta can? A kalla dai ba tsoro take ba tunda yaga ta kwana a daki a hotel ita kadai, sannan bawai kwanciyar kasan takeso ba tunda tai bake bake ta tare gado da suna hotel, to me take anan?�?
Tsugunawa yai yasa yadan tabata gadan, hannun tadan ja tana neman ta dan rike hannun dan ta mike zaune, dayake a tsugune yake tana ja ta sa ya runkufo kanta, wayarsa ce ta haska saman dakin, numfashinta ne ya tsaya cak nadan wucin gadi, ta kura mai ido. Tsayawa yai yana kallanta kafin yace “Yaushe zaki sakeni na tashi?�?
“Kaine fa ka dane ni.�?
Hannunta ya kalla data rikeshi yace �? Ko?�?
Ido ta zaro sannan ta sakeshi da sauri, bata jira ya tashi ba kawai ta miko taba san tashi saboda kunya, ji kake gum ta nake goshinsa, zafi ne ya ziyarci goshinsu a lokaci daya, tasa hannu da sauri tana sosa gun, tana neman yin ‘yar karamar kara yasa hannu da sauri ya toshe bakinta tare da nuna mata su Islam.
Itakam meke damunta?
Mikewa yai ya kalleta sannan ya zare hannunsa daga kan bakinta ya dan girgiza kai sannan ya fita daga dakin.
Kafafunta ta bubuga a kasa tare da sa kanta cikin cinyoyinta saboda jin haushin kanta datai.

Aminu kam yana fita yasa hannu a saman goshinsa tare dayin dan runtse ido dan gaskiya yaji zafi sosai, bayasan ta rainashi ne shiyasa ya nuna kamar ma baiji zafin abin ba. Haka ya wuce bangarensa yana mulmula gun a ransa yace “Anya bama da saninta ta makeni ba? Kila tana san rama abinda na mata jiya akan su Islam?�?

*****
Ibty kam ta dade tana murza gun dan ta bugu sosai, kafin ta mike ta fito daga dakin, alwala tai bayan tayi sallah ta dade tana addu’a wacce rabinta akan Yayarta Bilkisu takeyi, kafin ta mike ta koma dakin su Islam.
Tana kwance tana dadana wayarta bacci yadan sake daukanta, kamar a mafarki cikin bacci taji muryar Islam tace “Ilham me takeyi anan?�?
“Nima bansani ba, badai ta fara abin bako?�?
Islam cikin rashin jin dadi tace “Ina santa lokacin tana kawar Aunty amma yanzu bana santa tana matar Dady.�?
“Nima haka.�? Abinda taji Ilham tace kenan, bata bude idanunta ba tace �? Islam? Ilham? Da kawar da kake tare da ita shekara sama da biyar da wanda kansani a kwana uku wane yafi matsayi?�?
Kallan juna sukai Islam tace “shekara biyar?�?
Ibty ta bude ido ta zauna tana kallansu tace, “kwana dari uku da sittinda biyar ne a shekara kunsan yawansu?�?
Ilham tace “Dayawa kenan�?
Ibty tace, “To haka sau biyar kunga yafi kwana dubu ko?�?
Suka daga kai a tare, tace “Dady dinku dana ke tare dashi na…”tadan bude yatsun hannunta alamar uku “Na kwana uku, wane yafi yawa?�?
Cikin sauri sukace “Na Kawar Aunty.�?
Ta jinjina kai tana musu tafi tace “to kungani? Ni yanzu kawar Aunty ce ko matar Dady?�?
Shiru sukai suna tunani, Ilham tace “Amma duk da haka ke matar Dady ce ko?�?
Ta daga kai alamar eh kafin tace “Amma nafi dadewa a kawar Aunty Ainah, sannan a kawar Aunty na sanku ba a gidan Dady ba ko?�?
Yanzun ma alamar tunani sukai kafin su daga kai alamar eh, ta dan daga hannu tace “Yanzu muyi musabaha a matsayinmu na kawayen Aunty Ainah ko?�?
Nan Islam ta sauko da sauri itama Ilham ta sauko sukai musabaha, dadi ne ya kamata nan suka mike ta musu wanka anayi Islam nata bata labarin islamiyarsu, kaya iri daya suka dauko ta saka musu sannan suka fito falo wani irin dadi takeji dan jiya sam bataji dadin yanda suka juya mata baya ba.
Falo suka zauna tace “Kuje ku gaida Dady bari na hado muku tea kusha.�?
Nan sukai bangaren Dady da sauri suna wasan guje guje. Wanka tai itama tasaka atamfa riga da skirt, ita dama ba wani jiki ba ga kayan sun zauna mata, mayafi ta yafa babba sannan ta fito ta shiga Kitchen “Dandai tarewarta anyita ne ba shiri amma ai da ya kamata ta taho da gara, sai yanzu ta fahimci hakan nada amfani, ruwan zafi ta dora kamar daga sama taji ana kwankwasa kofa.
Zuciyarta daya tai tunanin ko mai gadi ne? Kila Ya Aminu ne ya aikeshi.
Sai datazo daf da kofar sannan tace “Wanene?�?
Sam bata zata ba sai jitai ance “Nice.�?
Gabanta ne yai wani irin faduwa, a hankali ta bude kofar, tare da kallanta.
Hajiya ta saki murmushi tare da mika mata tire din hannunta dake dauke da kuloli biyu da flask, dakyar tasa hannu ta amsa sannan ta gaisheta.
Hajiya tai murmushi tace “Amarya kin tashi lafiya?�?
“Lafiya kalau.�?
Murmushi ta sake tace “Nasan ana shan amarci ba damar tashi ayi abinci, sannan na saba yin girki dasu shiyasa. Ke dai ki huta abinki zan dinga yi muku girki ina aikowa dashi.�?
Tsananin mamakin kalamanta ne yasa Ibty ta kasa ko furta kalma daya dan bata taba tunanin jin wannan maganar ba.
Hajiya ta dan kalli ciki tace “Su Islam nagun Aminu ne?�?
Bakinta nadan rawa tace “Eh.�? Bata sake zata ba taji hannunta a saman kanta, “Allah ya miki albarka ya baku zaman lafiya.�?
Sam ta kasa cewa Ameen saboda yanda taji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, juyawa Hajiya tai ta bi bayanta da kallo.
Dakyar ta iya shiga ta ajiye abincin a kitchen kawai ta zubawa kwanukan kallo ko budesu ta kasa yi, kalamanta ne suke sake dawo mata, itakam gaba daya ta rasa dalili tsoron matar ma takeyi, haka ta kwashi tiren ta kai bangaren Aminu.
Yana zaune yana aiki a laptop dinsa su kuma su Islam suna kallan cartoon a tv. Ajiyewa tai akan dinning dinsa dake gefen falan sannan ta bude flask din.
Soyayyen dankali ne da kwai sai dayan kular farfesun kaza, flask din kuma kunu ne a ciki.
Idanunta ne suka danyi raurau, kafin ta shigo cikin falan.
Gaisheda Aminu tai ya dago ya kalleta, goshinta ya kallan wanda haryanzu da alamar buguwar dazu, itama nashi goshin ta kalla wanda haryanzu shima bai baje ba.
Amsawa yai sannan ya maida kansa yana cigaba da abinda yake, kallansu Islam tai tace “Ilham a kashe kallan azo aci abinci.�?
Ganin yanda suka taho da murna yasa ya dago ya kallesu, kamar jiya ba sune suka nuna basasan zuwa gunta ba. Tadan bi bayansu tana cewa “Wanda ke san yasha tea ya fadamin.�?
Hannu Islam ta daga tace “Kawar Aunty ni, Ilham da Dady kullum sai shan kunu.�?
Murmushi tai sannan suka karasa, sai da suka zauna ta sa musu a plate sannan ta fara hadawa Islam tea, yunwar dayaji tadan motsoshi ne yasa yadan yi gyaran murya tare da ajiye computer dinsa, “Anya tace yazo ma yaci abinci kuwa? Kamar gaisuwa kawai sukai.�? Tunanin me yace me kuma tace bayan sun gaisa yadanyi sai dai gani yai ya kasa tunawa gashi yunwa yakeji.
Mikewa yai yasa hannu a aljihu ya nufi dinning din, zama yai sannan yadanyi gyaran murya yace “Kunu zansha amma karkisamin sugar.�?
Kallansa tai kafin tace “to�? haushin abinda Hajiya ta mata ne yasa kawai taji batasan yimai magana, yanzu dayaga abinci bai kamata ya mata bayani ba? To yace me? Ibty karfa idanki ya rufe saboda jin haushin wata.
Abinda zuciyarta ta raya mata kenan, nan sukaci abinci itakam tea kawai ta hada ta dau bread ta tafi falanta taci dan bataji zata iya cin abincin.
Bayan ta gama ta dawo falo ta kwashe kwanuka, kallansa tai tace “Ya Aminu ko zamuje mu siyo abubuwan gida? Na abinci?�?
Ya mike yace “Eh gwara muje mu dawo ma da wuri dan inasan fita.�?
Hamdala tai a ranta tunda dai ya amince, haka kawai ba haukar da zata sakata ta amince da uwar matarsa ta dinga kawo musu abinci, duk rashin wayanta bai kai nan ba.
Su Islam suka hau tsale suka dauko hijab dinsu suka saka, a tare suka fito hannunta rike da hannunsu.
Gaban Hajiya ne ya fadi dan dama tun bayan ta dawo take leke ta katangar da sauran kadan a karasata, ganin ta gaji yasa ta koma falo, yanzu kam muryarsu Islam kadai dataji yasa ta fito da sauri.
Ranta yakai kololuwa gun tashi ganin hannunta a cikin nasu Islam suna tafe suna dariya, huci ta fara tana kallan muzurai, ko ba komai ai ta fara aikin ta a cikin abinci, sannan jiya tasa mata laya a kasan katifa, kwafa tai ta koma ciki ranta a matukar bace, ta zauna a falo ta daura kafa daya kan daya tana girgizawa. Bata taba tunanin Aminu zai fara daukarta da yaransa su fita ba daga aure.

********

Baya suka shiga ta shiga gaba, Aminu na kokarin shiga sai ga mai gadi ya taho da sauri, “Alhaji! Hajiya tayi bako.�?
Bako? Yai tambayar cikin mamaki, ya dan sake sukunyo na girmamawa yace “Yayanta ne jiya da shekaran jiya dashi aka wuni ana aiki kayan daki, yanzu yazo wai yazo kawo mata abu.�?
Ba tare da ya kawo komai ba yace “Ya shigo mana.�?
Nan ya juya ya tafi kiransa, Umar kam wanda ya samu leda ya cikota da littatafan dayasa Bilkisu ta sa Iman ta dauko na Ibty, sannan ya rubuta mata waskila akan lalai lalai yau karfw goma na dare ta san yanda tai ta fito waje zaiso su wuce Sokoto, karta damu ya tattaro kudin da zasuyi tafiya.
Shigowa yai, kallan gate tai ganin Aminu shima yana jiran ganin shigowarsa.
Wata muguwar faduwar gaba ce ta fadi mata, da sauri ta fara addu’a duk jitai ta rikice.
Idanunta ta kauda daga kallansa ta juya tana kallansu Islam.
Batai zata ba sai ji tai an kwankwasa glass din window dinta.
Inda Aminu yake ta kalla cikin firgice da tsoro, hannunta na rawa ta zuge glass din.
Umar ya zuba mata ido cikin tsananin kishi, ya dauka yanda ya birkice saboda rashinta itama tana nan tana rashinsa? Lalai yau ya tabbatar yarinyarnan munafuka ce, ba sanshi take ba. Sai dai wlh ko tana sansa ko bata sansa sai ta zauna zaman aure na har karshen rayuwa dashi.
Cikin rawar murya yaji tace “Ya Umar?�?
Idanunsa yai jaa sosai ta danyi yake, tana kallan Aminu daya zagayo ya mikawa Umar hannu, kallan hannunsa Umar yai sannan ya kalli Ibty, bai mika mai hannu sunyi musabaha ba kawai yadan ce “Ina kwanan mu?�?
Aminu ya maida hannunsa aljihu yace �? Ashe kaine, ko ba mijin yayarta bane?�?
Wani abu ne ya tokare mai makoshi ya zabgawa Ibty wani kallo sannan ya kalli Aminu da jajayen idanunsa.
Aminu ya kalli Ibty yace “ki fito ku gaisa.�?
Daga zaune tace “Ina kwana?�?
Umar mamaki ya kara kamashi wato fitowarce bazatai ba?�?
Aminu ganin yanda Umar ke kallansa yasa ya shiga mota ya zauna, Umar idanunsa nakan Ibty ya a zuba mata wani mugun kallo, itakam ta kasa sake kallansa sai rawa da jikinta keyi daga ciki.
Aminu na shigowa ta samu kanta da rike hannunsa da sauri.
Mamaki ne ya kamashi ya kalleta, kallansa tai tare da yin yake. Yanda jikinta ke dan rawa ya kalla, tabbas akwai abinda ke faruwa.
Umar kam ji yake kamar wanda ake hurashi a cikin wuta, zuro ledar yai baice komai ba ya zabgawa yaran Aminu harara sannan ya juya ya fita.
Islam ta kalli Ilham tace “Wannan sai yai kama da irin mugayen nan ko?�?
Ilham tace “Nima tsoro ya bani.�?
Haryanzu Ibty bata sake hannun Aminu ba, kallanta kawai yake yanda haryanzu jikinta bai dawo daidai ba.
“Mu wuce?�? Abinda ya tambayeta kenan, ta daga kai alamar eh.
Ya kalleta sannan ya kalli hannunsa, da sauri ta sakeshi sannan ta zauna, nan ya tada mota suka fito.
Daga waje sukaga Umar, Aminu yadan tsaya ganin yana tafiya da kafa yace “Ko zamu rage ma hanya?�?
Ai Ibty gaba daya ta sake rikicewa, Umar ya mai wani kallan tsana yace “Da sayyadata.�?
Aminu yasa hannu a aljihu ya dauko kudi yana neman mikamai, da sauri Ibty ta rike hannunsa dan tafi kowa sanin Umar ya tsani a rainashi, balle akanta. Yanzu saboda kudin nan batasan me zai aikata ba.
Maidawa Aminu yai sannan yace “To ka gaida su Umma.�?
Umar kam hannun Aminu data sake rikewa kawai yake kallo lalai zai iya yin kisa da akwai wuka a jikinsa, tab.
Gaba sukai tadan juyo ta kalleshi ta madubin mota, Aminu kam mamakin yanda haryanzu tai shiru ta takure a gefe yake, ance gida daya suka taso, meyasa take shakkarsa haka?
Umar kasa motsi yai ya tsaya kawai yana kallan motarsu harta kule, lalai duk wanda yake da hannu a cikin abin nan ya shirya fuskantar bala’i da masifa, ai ko bayan ya dauke Ibty wallahi sai ya dau fansar rike hannun Aminu datai.

{Nikam Ayusher kasa ko magana nai, anya mutumin nan nasa man kai?}

🏌🏻‍♀�?
2/14/22, 10:20 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

17🤸🏻‍♀�?
Har suka isa Jifatu muryar Islam da Ilham ce kawai ke tashi, sam ko magana ta kasayi, duk wannan abinda take yana lure da ita, tabbas akwai abinda ke faruwa a gidansu. Baisan ko menene ba amma da alama shine dalilin dayasa mahaifinta ya kawota ba ranar da suka tsara ba.
Parking yai sannan taji muryar Islam tana cewa “Kawar Aunty mun iso.�?
Firgigit tai tare da kallan gun, sannan ta kalli Aminu wanda shima yake kallanta yana ganin zata juyo ya dauke kai tare da kallan gefe.
Fitowa tai sannan ta budewa su Ilham, nan suka fito ta rike hannunsu.
Kallan cikin motar tai bataga alamar yanada shirin fitowa ba. Dan sako kanta tai saitin glass din motar tace “Ya Aminu muje?�?
Ya kalleta sannan ya kalli shagon yace “Kece me siyayya ki shiga kafin ki gama daukan abinda kikeso zan shigo.�?
Mamaki ne ya kamata tace “Yanzu ni kadai zan shiga ga yara ga siyayya?�?
Kallansu Islam yai kamar zaiyi magana sai kuma taga ya sake daurewa, ya gyara zaman farin glasses din dake fuskarsa sannan ya fito.
Da gusu Ilham ta kamo hannunsa sannan ta jashi kusa da inda su Islam suke. A tare suka shiga cikin shagon, kallansa tai tace “Ya Aminu cart din da zamu zuba kaya.�?
Wani kallo ya mata yace “Hannunki fa?�?
Ta kalleshi ta nuna jakarta da hannun Islam datake rike dashi, aransa yace “Lalai yarinyarnan, wannan fa in na kyaleta da alama aiki ma sani zatai.�?
Ya dago yace “Bazai iya ba intaga dama ta turo�? kawai yaga bata gun. Can yadan hangota harta fara daukan abu tana nunawa Islam suna dariya.
Wata kwafa yai sannan yaja cart din kai kace shine ya batamai rai. Takaici duk ya ishehi, banda ta rainashi ina zai dingabin mace zagagai zagagai tana siyan kaya shi kuma yana tura mata kayan? Dazun nan ya gama tausayinta ashe zata wulakantashi. Yanzu in wani ya ganshi ai ta gama zubarmai da girma.
Ibty kam batasan ma yanayi ba, Ilham ta dawo kusa da ita suna tafe suna daukan kaya intaga abin zagin yayi yawa tace a’a.
Haka suka gama siyayyarsu ya biya sannan suka koma mota, a zuciye ya fizgi mota suka hau kan titi.
Wayartace ta fara kara, ta dauko tare da yin sallama cikin girmamawa tace “Ummy ina wuni?�? Jin ta ambaci Ummy yasa yadan rage gudun tare dadan kasa kune yaji me zatace.
Ummy bayan sun gaisa tace “Ibtisam ina Aminu? Na kira wayarsa bansamu ba.�?
Tadan kalleshi kadan tace “Gamu tare mun fita siyayya.�? Kunya ce ta kama Aminu ji yake kamar ya fizge wayar, shikam yarinyarnan yau ta shirya kaskantar dashi.
Ji yai ta karamai wayarta a kunne, dan gyaran murya yai sannan ya gaida Ummy.
Cikin jin dadin da kanajin maganarta zaka gane tace “Aminu ko zaku biyo ta gida tunda kun fito?�?
“Ummy inada aiki wlh�?
Tace “In ka koma kayi, sannan ai ba dadewa zakuyi ba, dama naso zuwa ganin gida ne amma tunda kun fito ku karaso dan Allah.�?
To kawai yace ta kashe wayar cikin jin dadi, dan dama hankalinta ne sam yaki kwanciya tun jiya shiyasa ta yanke shawarar zuwa dan dole ta yiwa Ibtisam gargadi dan sakacinsu ne yaja musu gashinan mata tafi karfinsu.

******
Murna da tsale su Islam suka fara sai da ya kallesu sannan suka zauna, Ibty tai shiru tana kallan wayarta, so take taji muryar mahaifiyarta, da ‘yan uwanta amma ba dama, itakam wannan bala’i dame yai kama?
Gun parking na cikin gidan ya tsaya, tunda suka shigo ta hango Ainah a tsaye a harabar gun tana rike da kugu tana girgiza ta turo dankwali gaba irin ture kaga tsiya din nan, dariya ce ta kusa kwacewa Ibty.
Aminu na fitowa ya kalli Ainah, ai tana ganinshi ta ruga ciki a guje, dakinta ta shige tace “Sam na manta dashi ina jiran masifa.�?
Ibty tana kallan sanda ta ruga ciki, dariya ce tadan sake zuwa, ido suka hada da Aminu tadan maze, kai ya girgiza sannan ya wuce ciki.
Islam ma a guje suka shiga ciki, itakam sai data kara gyara zaman mayafinta ya rufe kanta sosai sannan ta fito.
Ainah tana leke ta kofa tana ganin Aminu ya wuce bangaren Ummy ta fito da sauri, Ibty na shigowa ta fizgo hannunta sukai dakinta.
Rufewa tai ta kara rike kugu tace “Sannu Aminiya wacce bata boyemin sirri.�?
Ibty ta dafata tace “Wannan daurin fa? Bansan kin iya irinshi ba ai da tuni nazo kin koyamun.�?
Ainah ta maze tace “Wai dagaske ke kika auri Ya Aminu? Ni wlh koda Ummy ta fadamin shekaranjiya na dauka karya ne.�?
Ibty ta dan ture dankwalin kanta tace �? To yanzu me kikeso ayi? Ko muje gun Ummy ta shiryamu?�?
Aina tadan shako wuyanta kadan tace “Allah kinci amanata.�?
Dariya sukai sosai, kafin su zauna a bakin gado.
Ibty ta kalli dankwalinta daya fadi sannan tace “Banje na gaida Ummy ba kin turen dankwali.�? Gaban madubi ta koma ta fara gyara dankwalinta, Ainah ta matso tace “Wai ya akai wannan abu ya faru? Sannan ina Ya Umar? Allah dai yasa karya kashe min yayana.�?
Ibty tadan waigo tace “Hmm Ainah nikaina abubuwan dasuka faru jinake kamar a mafarki, ki barni naje na gaida Ummy koma menene zan fada miki ai kinsan bana iya boye miki abu.�?
Tare suka fito suka nufi falan Ummy, su Islam ana zaune kan cinyarta anata zuba.
Ummy kam kallan Ibty kawai take tana hamdallah a ranta, sauke Islam tai sannan tace “Ibtisam muje ciki mu gaisa.�?
Tai maganar tare da nufar dakinta, Aminu na zaune a kasa yana daddana wayarsa, Ainah ta karaso ta tsuguna tana gaisheshi.
Fuska a hade yace “Dazu gidan dambe kike shirin zuwa?�?
Tace “A’a Yaya haushi naji Ibtisam bata fadamin komai ba gameda aurenta.�?
“Sannu Yaya babba, dolene dan kuna kawaye sai kinsan komai?�?
Cikin dan shagwaba tace “Nifa ya kamata na mata babbar kawa.�?
Kai yadan girgiza ya maida hankalinsa kan wayarsa yace “Yanzun ma ai sai kiyi bata baci ba.�?
Tasan magana ya fada mata, ta dan waske ta fara yiwa su Islam magana.
*****
A daki kuwa Ummy bayan Ibtisam ta shigo taga ta mike tasa ma dakin makuli, mamaki ne ya kamata sai dai bata nunaba, zama tai a kasa cikin girmamawa tare da sauke kanta kasa.
Ummy tagani ta zauna kusa da ita, sannan suka sake gaisawa, hannunta da take wasa dasu taji Ummy ta riko, kallanta tai sannan ta maida kanta kasa.
Ummy tace “Ibtisam mun miki laifi ko?�?
Dagowa tai idanunta suka danyi raurau kafin ta girgiza kai tace “A’a!�?
Itama kai ta girgiza tai tace “Bamu sanar dake babbar matsalar dake tattare da auranki ba, Mun rufe miki abu mafi mahimmanci wanda ya kamata ki sani.�?
Shiru tai a hankali hawaye suka taru a cikin idanunta, Ummy ta dan dago da kanta tace “Bansan meke faruwa ba Ibty, munyi iyayinmu munyi addu’a munyi sadaka sai dai matarnan taki fita daga gidan nan, abin tashin hankalin shine yanzu hartakai ta kawo bama iya mata magana a gabanta, wanda na tabbatar abu ta mana, ga magana a bakina amma ina ganinta bana iya zafafawa.�?
Mamaki sosai kalaman Ummy suka bata, habawa shiyasa dan dama itakam ta tabbatar ba kalau ba, ina aka taba wannan kwanacalar?
Ummy ta kara rike hannunta tace “Da Allah muka dogara sai fatan Allah ya baki ikon cetomu daga cikin wannan bala’in.�?
Bakinta na rawa tace “Ni?�?
Kai ta daga tace “Aminu mijinki ne, kinfi kowa hakki akansa, bayan ‘ya’yansa, Ibtisam ki taimakemu ki kwato mana yaran nan daga bala’in dayake ciki.�?
Kallan Ummy take a tsorace, ita me zata iya? Inhar su manya sun kasa?
Hannun Ummy taji a kafadarta tace “Kada ki kuskura kisha ko ruwa daga gun matarnan.�?
Ibty a tsorace take kallan Ummy, “Kada ki bari ta shigar miki dakinki, kitchen ko toilet, duk inda zata zauna to karya wuce falo. Ki taimakemu karki sake bari Aminu yaci abincin matarnan.�?
Ibty gaba daya jitai kanta ya fara nauyi, “Sannan kija mijinki a jiki, Aminu nada saukin kai inhar kika fahimceshi, na sani sarai yanzu bakya gabansa sai dai a matsayinki na mace dole ki mike tsaye ki shawo kan mijinki, kada ki bari kunya ko kuma shakkarsa dan ya girmeki sosai yasa ki kasa kwato mijinki.�?
Ta kasa ko firta kalma daya sai shiru kawai datai tana kallan Ummy.
“Tare kuke kwana?�?
Kunya ce ta rufeta da sauri tai kasa dakai, Ummy ta jinjina kai tace “Nayi tunanin haka, sai dai Ibtisam inaso kimin alkawari daga daren jiya bazaki sake bari ku kwana daki daban daban ba, inhar ba uzuri bane ya kama.�?
Kanta na kasa ta daga kai alamar to.
Ummy ta cigaba da yi mata bayani akan Hajiya wanda gaba daya kanta ya gama kullewa lalai itakam tayi aure a wahale, wannan yaki akeso tayi a gidan miji ko me? Haka suka fito tare itadai gaba daya jikinta ba laka, anan sukaci abincin rana sannan aka hada musu abinci a kula wanda zasu tafi dashi na dare.
Ainah kam tayi mamaki sosai jin yanda auransu ya kasance, tausayin Ibty ya kara kamata dan ta tabbatar Ya Aminu haryanzu matarsa ce a ransa.

*********

Da karfi ya hankada keken saura kiris ta fadi kasa, tai saurin rike bango.
Kallansa tai idanunta na zubar da kwalla, ya matso yasa hannu ya shako wuyan rigarta. Tun jiya ciwonta ya tashi, amma ta rasa wa zata fadawa, sai daurewa kawai takeyi.
Idanun Umar yayi jaa kamar gauta yace “Munafukar banza da wofi daga ke har iyayenki munafukai ne kuma azzalumai ne.�?
Bilkisu ta share kwallarta tace “Ya Umar kayi hakuri dan Allah.�?
Ya kara rikota sosai yace “Wallahi sai na wahalar dake wahalar da saikinyi dana sani, ‘yancinki daya shine abinda nake shiri yau ya tabbata amma wlh in wani abu ya kawo cikas to wallahi ki shirya haduwa da bala’i da masifa.�?
Ya hankadata yai ciki, hawaye ta shiga gogewa, tana tsananin san Ya Umar gani take kome zai mata indai har suna tare to fa zata jure.
Anayin Isha’i ya fito dana ya hada kayansa yakai gidan wani abokinsa.
Kai tsaye yawuce unguwar su Ibty.
*****
Hajiya yau dakyar ta iya cin abinci, ta hanke shawarar kwanciya kawai tace batada lafiya dan ta tabbatar Aminu zai dawo hayyacinsa inyaji ciwonta ya tashi.
Sai dai tunani ya hanata iya kwanciyar, sako ta turamai akan ya taho mata da magani.
Ai yana gani ya tattaro su Ibty suka fito duk ya rikice, mamaki sosai ya kama Ibty yanzu kam ta tabbatar da kalaman Ummy wannan ba’a hayyacinsa yake ba, yana zuwa ko kofar motarsa bai rufe ba ya nufi bangarenta.
Ibtisam ta wuce ciki bayan ta debi wasu kaya, dan Ummy tace abarsu Islam sai gobe lahadi sai su dawo.
Sam ta manta da litattafan da Umar ya kawo mata, da a kusa da ita ta ajiye batasan ya akai ba taga an maidasu bayan mota, ta tabbatar Aminu ne tunda shikadai ne ya shiga motar.
Shiru tai bayan ta shiga daki, kalaman Ummy ne keta mata yawo akai, gaskiya bazata zauna kamar mace mara ilimi ba, ko yaran kauye yanzu sunzan yanda ake tafiya da namiji, balle ita.
Mikewa tai ta farayin wanka sannan ta dauko kayan bacci daya daga cikin na lefen ta dan an kawo mata kayan lefenta, maidashi tai da sauri tana dan dadiya kadan tace “Wannan in na saka ai daukata zaiyi ‘yar iska.�?
Haka tai ya dubawa sai can ta samo wata doguwar riga ta zura sannan ta saka hijab dinta, falo ta fito tana dan sake gyarawa, tana yi tana kallan window sai yaushe zai dawo? Itakam da gun kishiya yaje ma a kalla tasan inda yaje amma wannan dame zata kirata?
Haka ta shiga kitchen ta karasa wanke kufunan safe sannan ta jera abincin da suka taho dashi daga gidan Ummy.

Aminu kam sai dayaga tasha magani sannan ya mike yana shirin fitowa.
Kuka tasa wanda ya daga mai hankali, tace “Aminu nikam komawa kauye zanyi kwanan nan tunanin Na’ima ya hanani sukuni, tunda kai aure nake ganin shikenan rayuwar Na’ima ta kare.�?
Dawowa yai ya tsuguna yace “Hajiya meyasa kike fadan haka? Ko da wasa bazan iya mantawa da Na’imah ba sannan ga ‘ya’yanta nan wanda a koda yaushe inka kallesu zaga tuna da ita.�?
Ta sake sa kuka tace “Na tabbatar matarka ma bazataso zamana a gidan nan ba, dama mahaifiyarka baso take ba, Aminu ka maidani kauye dan Allah.�?
Tausayinta ya kara kamashi yace “Hajiya ki kwanta ki huta, da safe mayi magana.�?
Haka ya fito duk zuciyarshi ba dadi, da alama auren nan ne yasa duk abin duniya ya dameta, tana ganin wata ta maye gurbin Na’imah.

Mota ya karasa ya shiga da ragowar manyan kayan abincin, tana kitchen tana wanke sink ya shigo, kallansa tai tace “Hajiyar batada lafiya ne?�?
Ya kalleta sosai yace “Me Ummy tace miki da kuka shiga daki?�?
Kallan mamaki tamai tace “Hirar duniya mukai tamin nasiha.�?
Kamar zaiyi magana sai taga yana neman fita da sauri tace “Wani abin akace?�?
Ya juyo sosai yana kallanta yace “Hajiya tace kema basan zamanta kike ba, so na dauka Ummy ta miki zancenta ne.�? Abinda yace kenan ya fita, da kallo ta bishi baki a bude.
Ibty kinga ta kanki, yaki yana gabanki, dole na maido da hankalin Aminu kaina kafin na san yanda zanyi na sallami matarnan.
To amma ta ina? Abinda iyayensa suka kasa na isa nayi?

*******

Yayi sintiri harya gaji ga uban sanyi da akeyi, ji yake kamar gabobin jikinsa sun daina aiki.
Karfe sha biyu da rabi? Lalai Ibtisam ta nunamai inda ta ajiyeshi shima kuma yanzu ya dau alkawarin nuna mata wulakantashi datai ba abinda zai jawo mata sai dana sani.
Haka ya koma gida, ya shiga bargo kankace me zazzabin soyayya da rashin Ibty ya rufeshi, wasu zafaffan kwala ne suka zubomai, lalai anci amanarsa kuma wlh bazai yafe ba. Tun yarinyarnan tana yarinya yake santa yake tanadinta yake ajiyarta, sannan wani katan banza yazo ya dauketa? Inya tuna haka jiyake zuciyarsa na wani irin tafasa.
******
🏌🏻‍♀�?
2/14/22, 10:20 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

18🤸🏻‍♀�?
Tsaye tai a cikin dakinta tana tunanin yanda zata tunkari dakin Aminu, ta zauna a gaban madubi tana kallan kanta. Ajiyar zuciya tadanyi mai sauti sannan ta dan gyara fuskarta ta dau turare tadan fesa, shiru ta sakeyi tana tuno yanda Amare ke dan naku-nuku in tana karanta novel, to ita gashi sai dai takai kanta? Hijab dinta ta dauka ta zura sannan ta nufi bangarensa.
Agoggon falansa ta kalla wanda ya nuna karfe goma na dare, kwan wutar dakinsa tana kune da alama bayan yaci abinci ciki ya shiga. Gabanta ne ke faduwa akai-akai harta isa kofar dakin, hannu tasa tana neman bude dakin da sauri ta sauke hannunta. In ya korota fa? Gashi tawa Ummy alkawari? Hannu ta kara sawa cikin shakka ta runtse idanta da karfi sannan ta bude kofar, bakinta dauke da sallama.
Bata kalli inda yake ba dan ta tabbatar suna hada ido zata rasa abinyi, tana jinsa sanda ya amsa sallamar amma kanta na kasa ta nufi gado tana kallan kasan dakin.
Aminu dake zaune akan gado ya mike kafa yana dane-dane a computer ne ya tsaya cak yana kallanta. Me takeyi? Tambayar datazo mai kenan. Bai gama tunanin me take shirin aikatawa ba kawai yaga ta nufi kan gado inda yake.
Dan idanta ta dago kadan ta hango kafar Aminu a saitin da take kokarin kwanciya, da sauri ta koma baya ta zagaya ta daya bangaren, shikam idanunsa na kanta yana kallan ikon Allah.
Kamar zata zauna a gadan sai kuma ta wuce toilet dinshi, brush dinta data dauko ta ajiye a ciki, sannan ta furzar da wata iska, shafar kirjinta tai sannan ta kara fitowa, kan gadan ta karasa, kawai yaga ta kwanta ta juya baya, tsananin mamakin wannan lamari ya hanashi magana.
Jin baice komai ba yasa tadan saki ranta, hannu tasa saboda ta ji sanyi na ratsa kafarta, tana dan laluban bargo, idanunta a rufe sannan ta juya. Kallan hannun yai sannan ya janye bargon daga inda hannunta zai kamo, ganin ta kasa kamo bargon yasa ta dan takure cikin hijab dinta.
“Me kike anan?�?
Abinda taji yace kenan, bakinta nadan rawa tace “Anan zan kwana.�?
“Anan zakiyi me?�? Yai tambayar yana kara kallan bayanta cikin mamaki, Ibty tai shiru tare da maida idanunta ta rufe ta fara dan sauke numfashi kadan kadan alamar bacci.
Abin ma dariya yaso bashi, yace “Anan zakiyi me kikace?�?
Shiru nan ma ba amsa, ajiye laptop dinsa yai a side bed sannan yasa hannu ya juyo da ita saitinsa, haryanzu idanunta a rufe wai a dole bacci take, saketa yai sannan ya zuba mata ido yana ganin sanda zata bude ido. Ibty kam idanunta kam, jin shirun yayi yawa yasa tadan kasa kunne, motsi taji kamar an sauka daga kan gadon, sai kuma taji alamar rufe kofa, idanta daya tadan kyalla kadan tanasan ganin ko yana nan, ganin bakowa agun yasa ta danyi fifita da hannunta sannan ta dan mike ta zauna tana sake fitar da wata ‘yar iska.
Gyaran murya taji daga gefen toilet, idanu ta zaro ai bata kalli gun ba tai saurin kwanciya ta runtse idanunta kyam.
Aminu baisan sanda wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba lalai yarinyarnan.
Karasowa yai ya zauna yace “Tashi ki fadamin me kike a dakin nan? Ko kuma na kinkimeki na maidake dakinki.�?
Kin bude ido tai, yace “in irga uku?�?
Nan taji yace “Daya, biyu, uku!�?
Hannunsa taji ya sakalo ta wuyanta da sauri ta bude ido tare da cewa “Ya Aminu dan Allah ka bari, tsoro nakeji, bazan iya kwana ni kadai ba.�?
Kallanta yai sosai sannan ya saketa, yace “Kina nufin ni kike cewa tsoro kike?�?
Ta jinjina kai da sauri alamar eh tace “tsoro ne dani sosai, bakaga jiya a gunsu Islam na kwana ba?�?
“Ahhhhhh tsoro ko?�? Ta daga kai da sauri. “Oh! Shiyasa naga sanda kike kwana a daki ke kadai a hotel cikin dare ihu kikeyi kina dawowa inda nake.�?
Ganin ya kamota yasa tadan hada labanta biyu ta rufe tace “Na kwana ni kadai ko?�?
Bai amsa mata ba sai kallanta dayai, tadanyi murmushin yake tace “To koma dai na kwana da yanzu tsoro nake.�?
“Tsoro?�?
Ta daga kai yace “Tsoro shine bazaki kwana a kasa yanda kika kwana a dakinsu Islam ba sai akan gadona?�?
Saman goshinta tadan sosa kadan tace “Jiya dana kwana a kasa ne bayana yake ciwo.�? Tai maganar tana dan taba bayanta dayin alamar zafi.
Dan kallansa tai kadan taga yanda ya kafeta da ido, da alama yanzun ma bai kama karyar ba.
“In nace miki yarinya kiji haushi, yanzu wasu tatsuniyoyin kike jeromin?�?
Tadan turo baki cikin jin haushin kalamansa, kallan yanda ta wani turomai baki yai yace “Badai zagina kike a ranki ba ko?�?
Kallansa tai cikin wani yanayi na shagwaba da sakalci da batasan tayi ba tace “Nawa Ummy alkawarin kwana a dakin nan daga yau ne shiyasa. Sannan Allah ni ba yarinya bace.�? Tana fadar haka yaga ta ja bargo ta sake kwanciya, a zaune ta barshi da baki bude eh lalai yarinyarnan taga gadan baccinsa, shi takewa magana haka?
Shi dama yasan akwai abinda suka tattauna da Ummy wato akan kwana tare ne?
Kallanta yai yace “Kina nufin daga yau anan zaki dinga kwana?�?
Gani yai ta daga kai alamar eh, yace “In kuma naki yadda fa? Ko kin manta daki nane?�?
“Sai na fadawa Ummy tasan abinda kace�? Baiyi tunanin jin wannan amsar ba sam. Kasa magana yai sai kallanta dayai, eh lalai Ummy ta kara bari yarinyar nan ta rainashi.
Ko ya sauka ya bar mata dakin? Tunowa yai da kwanciyar kujera dayai a hotel yanda ya dinga tashi da ciwon baya, abinka da shekaru sun dan fara kamawa.
Yanzu haka zai dinga kwana da yarinya a gado daya? Bai kwanta da ita bama ta rainashi balle sun kwana gado daya?
Aikin sam kasa karasawa yai haka yanayi yana kallanta cikin takaici ya kashe wuta ya kwanta, ya dade yana juye-juye kafin bacci ya daukeshi.
***
Wajen karfe biyu da rabi na dare mumunan mafarki ta farayi, wai gatanan Umar ya rufeta a wani daki a daji, abinci ma ta window yake cila mata. Sam saboda tsoro batasan ta shigo jikin Aminu ba, cikin bacci yaji an rikeshi sosai, idanu ya bude sannan yasa hannu ya kuna fitilar wayarsa, mamaki ne ya kamashi ganinta a jikinsa sosai ta rikeshi. Hannu yasa yana kokarin janyeta daga jikinsa, hawayen dayake gangarowa a idanunta ne yasashi tsayawa yana kallanta, wannan yarinyar tabbas akwai abinda ke cinta, to shi bata fadamai ba taya zai tambayeta? Ko saboda batasanshi ne kullum take mafarki da koke koke cikin bacci? Saman goshinsa ya shafa yana sake kallanta, harya sake kai hannu zai tureta sai kuma ya fasa.
Hannunsa ya daura a saman goshinsa kawai ya rufe idansa, da alama yanzu da take jikinsa bacci take shikam sam ya kasa komawa bacci, a haka zai cigaba da kwana da ita? Kwanansa nawa kenan raban dayai bacci mai dadi?
Sai wajen asuba sannan bacci ya daukeshi, cikin bacci taji alamun kiran sallah, idanunta ta bude a hankali, tana neman yin mika.
Ganinta yai a makale a jikin Aminu, ta sakalo hannunta a tsakanin cikinsa da kirjinsa. Idanu ta zaro ta dan janye hannunta a hankali ta shige toilet.
Brush tai sannan tai alwala tana yi tana tuno yanayin data ganta, oh itakam shikenan zai ce batada kamun kai. Wannan abin kunya dame yai kama?
Fitowa tai daga toilet tana gyara zaman hijab dinta, fitilar wayarsa ya hasketa dashi.
Da sauri ta dan juya baya, yace “Kin gama daddaneni kin tashi?�?
Juyowa tai tana dan murmushin yake tace “Ya Aminu kasan in mutum yana bacci baya sanin abinda yakeyi.�?
Kai kawai ya girgiza sannan ya mike yai toilet, wato yarinyarnan da inta kalleshi bata iya magana yanda ya kamata amma yau data kwana dashi harta fara? Lalai wannan yana nuna kwana dashi ne yake kara jawo raini.
Alwala yai ya fito, ganinta yai tana lafila, nan yadau wayarsa da carbi ya fito daga dakin.
Harya isa masallaci yana tunanin meke damun yarinya karama haka? Da ko bacci batayi mai dadi? Ko ya tambayi Ainah? Kai ya girgiza da sauri dan ya tabbatar inya tambayi Ainah zata fada mata ko kuma ta fadawa Ummy.
Harya dawo daga masallaci abin bai bar ransa ba, tunda ya shigo bangarensa yaki jiyo zazzakar muryarta tana karatun qur’ani, har ya nufi dakin sai naga ya dawo ya zauna akan kujera ya dan mike kafafunsa ya kwantar da kansa a saman kujera tare da lumshe ido yana juyo karatunta, baisan tanada murya mai dadin sauraro ba haka, sam baisan sanda bacci yai gaba dashi ba.
Ibty kam sai data kai karshen Suratul Ma’idah sannan ta kalli yanda gari yai haske, lalai karatu rahama ne, kwanan nan bata samu damar yin karatu ba tana tunanin karta takuramai a hotel, jiya kuma batasan ta tashi su Islam, agoggo ta kalla karfe shida da rabi.
Fitowa tai tana mamakin yanda akai bai dawo ba, akan kujera ga ganshi, jikinta ne yai sanyi da alama saboda baisan shiga daki tana nan ne yasa ya kwanta anan.
Sam jitai zuciyarta ba dadi, a rayuwarta batasan taga ta shiga hakkin wani, dan karamin murmushi tai sannan ta koma daki ta kalli bargon dake kan gado tace “Wato a film in naga namiji ko mace suna luluba bargo in ana bacci abin naban dariya yau nima da alama zan kwaikwayesu.�?
Daukan bargon tai ta nufi falo, a hankali ta shiga ya ware bargon sannan ta lulubamai, juyawa tai zata koma sai jitai yace “Dadin ki sake taremin gado ko?�?
Kallansa tai, mikewa yai tare da daukan bargon yace “Yanzu ai safiyace bakya bukatar kwana dani ko?�?
Wannan wani irin mutum ne? Ita a film in aka shimfida bargo gani take ana godiya, ko a rungume ka, ko kuma adan kalleka ai murmushin jin dadi, in kuma mutum bai farka ba inya tashi zaiji dadi. To ita gashi tayi abin arziki an bige da fada mata magana.
Dakinsa ya wuce, gani yai ta gyara gadan, kwanciya yai ya maida idansa ya rufe.
Ibty kam bangarenta ta koma, dakinta ta shiga ta zauna a kan gado tana kallan dakin, kalaman Ummy ke sake dawo mata, itakam gaba daya yanzu komai shakkarsa take a gidan, batasan taganta ita kadai sai taga kamar wani abin zai sameta.
Wayarta ya dauko kawai ta koma falo ta zauna tana dane dane a haka har bakwai da kwata tai sannan ta wuce kitchen, me zata dafa? Nan fa ta fara hidimar harhada ingredients tana tunanin yau ce rana ta farko da zaici abincin ta dole ta zake karya sake ce mata yarinya.

*********

Potato omelette tai sannan tai sauce na hanta, ta dan soya dankali kadan tasa daga gefe, ta dafa tea ta zuba a flask sannan ta shiga tai wanka, lace ta dauko na daya daga cikin lefenta ta saka, tayi kyau sosai, ta gyara gashinta duk dabai bamai tsayi bane sosai amma ba gudil bane. Dan kwalinta ta dan daura ta dan yafa mayafi sannan ta dau turare, tana fesawa taji ana knocking din kofar, gabanta ne ya fadi ta fito daga dakin tare da nufa kofar.
Tace “Waye?�?
Hajiya tace “Amarya kin tashi?�?
Budewa tai cikin dauriya ta kalleta, hannunta dauke da tire na abinci.
Ibty ta gaisheta sannan tace “Ya jiki? Naji ance baki da lafiya?�?
Tana murmushi tace “Na samu sauki, ga abincin safenku.�?
Kallanta tai, cikin dauriya tadan hade hannayenta, tsoro takeji sosai, sai dai inta tuna tsoronta abinda yaja mata a rayuwa sai taji haushin kanta, dan badan tana tsoron Umar ba da tuni ta takamai birki, da ta sanar da iyayenta an dau mataki tun farko.
Bakinta nadan rawa tace “Hajiya mun gode amma na riga nayi abinci.�?
Hajiya taji abin sama taka, balle a yanda take kallan yarinyar kamar wawiya, cikin dauriya tace “Ke da nace ki barshi shine kima wahalar da kanki?�?
Tadan dake tace “In na zauna ba abinyi nima zaman isata zaiyi, ke da ba lafiya ne dake ba gwara ki huta.�?
Lalai kallan kitse nakewa rogo, amma ba tasaka mata laya ba? Badai tare take kwana da Aminu ba?
Kallan zargi tawa Ibtisam wacce ke wasa da yatsun hannunta tana addu’ar tsari a ranta.
Hajiya ta juya hannunta dauke da tire, cikin tsananin kunar rai ta isa bangarenta, abincin ta juye a cikin bola sannan ta zauna ta daura kafa daya kan daya tana girgizawa lalai da alama yarinyarnan ba wacce ya kamata ta raga mata bace.

{Nikam Ayusher sim sim sim na fito tun kafin abu ya ritsa dani🏃🏻‍♀️}

🏌🏻‍♀�?
2/14/22, 10:20 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

19🤸🏻‍♀�?
Tana rufe kofa ta jingina da jikin kofar ta ciki tana addu’a tare da rike kafarta datake rawa. Batasan meyasa take tsananin tsoron matarnan ba, tafi minti biyar agun kafin ta daure ta koma ciki.
Bangaren Aminu tayi, tana shiga yana fitowa daga dakinsa, kamshin turaren daya saka ne ya cika falan, jitai kamar ita batasa turare ba bayan sai da ta saka sannan ta fito. Kallansa tai yayi kyau sosai cikin shadda light blue, Aminu nada kyau ita kanta tasan kudi da kyansa sunfi karfin ta, samun kanta tai kawai da zubamai ido ta kasa daukewa.
Aminu daya fito yana gyara zaman hularsa, ya kalleta tana tsaye tana kallansa.
Gyaran murya yai hakan yasa tai saurin cewa “Yaya ka fito?�?
“A’a ina ciki.�? Ya fada yana shigowa cikin falan.
Aranta tace “oh daga tambaya?�?
Komawa tai ta dauko kayan abinci ta jera akan dinning yana zaune yana duba wasu takardu dake gefen kujera. Kallanta yai yana mamakin yaushe harta gyara falan haka?
Sake gyaran murya yai yace “Ko zaki nemo mai aiki? Dan ni dama mai gadi ke shigowa yadan shashare gidan bayan kwana biyu, to yanzu tunda kina gidan inaga ki nemo mai tayaki.�?
Ajiye plate din hannunta tai tace “Bari mugani in na koma makaranta naga abubuwan sunmin yawa sai muyi shawara, amma yanzu ba wani aiki tunda ba ko ina bane yake datti.�?
Kafada yadan daga alamar yanda ta gani, Ibty ta dan kalleshi tace “Yaya abinci.�?
Ajiyewa yai ya dawo ya zauna akan kujera, ganin abin yake wani banbarakwai dan raban da ya zauna shikadai da mace haka an dade. Plate tasa a gabansa sannan ta bude flask din, kamshin abincin kadai sai sayasa ya kalli flask din, dake wa yai tare da cigaba da dan dana wayarsa. Ganin yanda take ta zubawa yasa yai saurin rike hannunta. A hankali ta dago ta kalleshi, bai kula da hannunta daya rike ba yace “Abincin mutane nawa kike zubawa?�?
Kallan abincin tai tace “Yanzu hakan dayawa na zuba?�?
“A’a dan kadan kika sa kamar cikin Islam.�?
Dan baki ta turo itafa batasan wasan fadar bakar magana.
“Mikomin cup na hada tea�?
Hannunta daya rike ta kalla tace “Ta yaya?�?
Saketa yai yadan sake gyaran murya yace “keda hannunki bazaki kwace ba?�?
Kamar zatai magana kawai ta fasa, cup ta mika mai sannan ta zauna a daya kujerar, tare da mikamai kayan tea.
Hadawa yai sannan yai Bismillah ya fara ci, magana ta gaskiya yaji dadin abincin nan dan ba shakka da badan karta rainashi ba daya yabi girkin, yaci sosai dan sai daya cinye wanda ta zubamai, tea ya kurba sannan yace “Gashinan kin cikamin abinci kinsa ina nishi dakyar.�?
Aranta tace “Sai kaci ka rage.�?
Ya dan sake shan tea yace “Amma Hajiya tasan kinyi abinci? Dan na tabbatar inba jikinta ne ya matsa ba zatai abinci damu tunda ta saba.�?
Jin yace Hajiya yasa hankalinta yadan tashi kadan, murmushi tai tace “Na fada mata zan dinga girki sa kaina, sannan ta girma bai kamata mu daura mata wahala ba.�?
Yayi mamakin jin kalaman nan daga bakinta, samun kansa yai dayin murmushi wanda hakan ba karamin mamaki ya bata ba. Kallansa tai cikin jin dadin da batasani babtace “Ya Aminu? Murmushi kai?�?
Fuskarsa a daure yace “Murmushi kuma?�? Ya karasa maganar yana ajiye cup din hannunsa, kallanta yai sosai yace “In murmushin ma nai menene naki na murna?�?
Dariya tadanyi tace “Bantaba ganin Kayi Murmushi bane�?
Gyaran murya yai yadan mike yace “A kalla naji bakiyi maganar yarinta ba.�?
Haushi ya dan turnuke ta, cikin dan takaici da magana kasa kasa tace “Duk wacce takai lokacin aure ai ba’a kirata yarinya ba.�?
Waigowa yai da sauri anan suka hada ido, zaro ido tai dan ta tabbatar yaji me tace, wata guntuwar shakuwa ce ta taso mata, da sauri ta mike tana neman barin gun, harta fara tafiya taji an riko rigarta ta baya, mayafin dake jikinta ne ya sauko.
Sake shakuwa tai sannan tadan bibigi kirjinta, Aminu ya jawota tana tirjewa, dawo da ita gabansa yai yace “Me kikace?�?
Sake shakuwa tai da sauri ta rufe bakinta da hannayenta biyu ta girgiza kai alamar bakomai.
Hannunsa daya yasa ba wanda ya riketa dashi ba ya dauko ruwa faro dake kan dinning din ya mika mata tare da mata alama datasha, amsa tai ta bude sannan tasha sosai.
Kallanta yai haryanzu hannunsa na rike da rigarta yace “Ehen me kikace?�?
Fuskarta ce tadan shagwabe kamar mai shirin kuka tace “Namanta.�?
“Kin manta?�?
Kai ta daga da sauri alamar eh “to tuno ko na tuno miki?�?
Kai ta girgiza alamar a’a da sauri tace “Allah kaine komai sai kamin zancen girma ni haryanzu banga wasu shekaru dayawa da aka bani ba.�?
Mamakin kalamanta ne ya rufeshi ya kalleta sosai sannan ya nuna kanshi da yatsa yace “Me? Ni kike cewa ban baki wasu shekaru ba?�?
Kasa tai da kanta tare da dan yin raurau da fuska, Aminu yadan furzar da iskar bakinsa yace �? Lalai kinga gadan bacci na.�? Yai maganar tare da saketa yana neman juyawa. Da sauri tasa hannu tadan riko rigarsa ta baya, cikin sanyin murya tace “Yahkuri bawai da raini na fada ba Allah ni banasan kaitacemin yarinya bayan ni ba yarinya bace.�?
Wucewa yai ya zauna akan kujera itakuma tabi bayansa da kallo, komawa tai ta gama cin abincinta tanaci tana kallansa bayan ta gama ta kwashe takai kitchen. Wanke kwanukan tai sannan ta hada turaren wuta ta fito dashi.
Kamshi sosai ne ya baibaye gidan, Aminu nasan kamshin turaren wuta da alama yarinyar ta iya abubuwan gidan, yayi mamaki dan ya tabbatar Ainah akwai abinci sosai bata iya ba. Yana zaune yana kallanta ta gefen ido harta gama turare falan da dakin bayan ta sake gyara kan gadan sannan ta fito ta maida shi bangarenta.
Zama tai akan kujera tana dadana wayarta, tai shiru tana tunanin yanda zata bashi hakuri, ita dai Allah tasan ba laifi tai ba amma da alama yaji haushin kalamanta.
Ibty a haka inka ganta zaka dauka batada magana sai dai a zahiri in ta samu waje to fa sai a hankali, a gidansu sam bata zama sosai ai hira da ita saboda ta tabbatar daga ta zauna Umar zaizo ya kafeta da ido, shiyasa har tafisan ta ganta a daki ita kadai.
Mikewa tai ta nufi falan inda yake ta zauna daga dan gefe tare da daukan wayarta taba dadanawa. Aminu bai kula ta ba ganin haka yasa tace “Ya Aminu wani satin za’a fara registration na second semester.�?
“Okay.�? Abinda yace kenan ya cigaba da duba takardunsa, ajiyar zuciya tai ta zauna kawai dan bayasan me zatace ba gashi kamar aiki yake batasan ya dameshi.
Sunfi minti ashirin a haka, so yake ya tambayeta abinda ke damunta har cikin bacci amma ya rasa ta yanda zaiyi.
Jitai yace �? Ya Ummanku? Kunyi waya?�?
Kallansa tai idanunta ne suka dan canza, cikin dauriya tace “Suna nan lfy na kira Abba dazu da safe.�?
Zancen Umma yai amma amsar Abba take bashi, tun suna hotel ya kula da Abba kawai take waya, a iya saninsa mace tafi shakuwa da uwa.
Kansa nakan takardun hannunsa yace “Yayarki fa da akai aure? Tana nan lfy?�?
Tadanyi yake tace “Lafiya kalau, ai a kusa da gida take.�?
Kai yadan daga alamar gamsuwa sannan yace “Meya sameta naga kamar bata tafiya.�?
Jiki a sanyaye tace “Sickle cell gareta, SS ce to ciwon yaci karfinta ya taba mata kafa, da tana tafiya daga baya ne tafiyar ke bata wahala.�?
Kallanta yai yace “Kinsan tana da SS shine baki nemi sanin genotype dina ba kika amince ki auren?�?
Dagowa tai taga yanda yake kallanta sosai, shiru tadanyi tare da maida kai kasa dan harya dauka batada amsar da zatace sai yaji tace “Na tabbatar Abba ya bincika dan yafi kowa damuwa da ciwon.�?
Sake kallanta yai baiyi magana ba sai dai ya sake girmama zurfin tunaninta a karo na uku.
Ganin yanda yake kallanta yasa tadanyi murmushin yake tace “Kayi hakuri dazu ba rashin kunya nasoyi ba, banaso ne kai ta cemin yarinya.�?
“So kike a cemiki babba?�?
Tadanyi murmushi wanda yasa dimple dinta ya motsa tace “Ba wai acemin babba ba amma bansan aita cemin yarinya ko komai nai ai tamin kallan abin yarinta.�?
Yanzun ma baisan sanda yai murmushi ba tare da girgiza kai yace “Meyasa mu manya in ance mana manya bamajin haushi?�?
Ganin yanda yai murmushi yasa tadan fadada fara’arta tace “Yaya tsakani da Allah kai babba ne? Irin babban babba?�?
Fuska ya daure sosai tare da yi mata wani kallo, ta dan girgiza hanayenta da sauri tace “Karka fassara maganata wlh ni dariya abin yake ban in naga kanata zancen girma, na dauka mutanen dasuka kai 50 zuwa sama sune suke zancen girma.�?
Sosai ya daure fuska yace “Wato dai so kike kice nima ba babba bane?�?
Tana dan guntse dariyarta tace “Kai ma ba babba bane nima ba yarinya bace.�?
Wani kallo ya mata sannan ya cigaba da aikinsa, ya kula in aka tabata to fa akwai magana, shi kuma bai fiya san magana tai tsayi ba.
Ibty kam samun kanta tai cikin farinciki, a kalla yau sunyi magana mai tsayi, murmushi tai tayi.

********

Naman cikin farfesun duk ya juye a cikin plate dinsa, kana gani kasan saboda mugunta yai, Bilkisu kam koko tasha ta gutsiri bread tana hadawa dashi, batama taba farfesun da aka aiko musu dashi ba, jiyai ya koshi duk yanda yake turawa, kallanta yai cikin tsana yace “karki taba roman nan ki juyemin a kwano zan kaiwa abokina.�?
A hankali tace to.
Wani haushi ya kara kamashi danshi ladabin nan konamai rai yakeyi, mikewa yai ya shiga daki ya cire kaya ya watsar a kasa sannan yai wanka, kaya yasa ya fito yana kallanta tanata kokarin gyara falan. Kafa yasa yadan tura keken sannan yace “Dalla ki dinga yi kina kallan hanya, kinso da keke kin cika wannan dan karamin falan, ta ina kikesan mutum ya wuce banda kina kokarin sani na fadi?�? Yaja wani tsaki tare da daukan ledar datasa kwanan a ciki ya fita yana masifa.
Kwallarta kawai ta share ta cigaba da aikinta.

*****
Abangaren Hajiya kuwa tun bayan dawowarta ta kasa zaune ta kasa tsaye, ganin zaman ba inda zai kaita kawai ta fito, abin takaici an gama ginin katangar balle ta leka ta gani ko Aminu nanan.
Waje ta fito kawai ta hau adaidaita ta wuce gun malaminta.
Sai daya dade yana dube dubensa sannan yace “Yanzu me kikeso ayi mata? A haukatata ko kuma a mata ture ta shiga duniya.�?
Hajiya tace “in akai haka kowa zargina zaiyi nidai kawai ka ban abinda zan dinga juyata sai abinda nace sai kuma abinda na tsara, bazata taba kallona tamin musu ba. Sannan ka sake tabbatarwa kar wani abu ya shiga tsakaninsu na auratayya. Sannan ka tura mata aljani wanda zai rikitata yasa Aminu ya fara daukarta mahaukaciya ko mara lafiya.�?
Dariya ya bushe dashi yace “Wannan layar da kikasa inhar ta kwanta akai to fa ita dashi har abada dan bazai taba sha’awarta ba, sannan zancen yi miki biyayya wannan abune mai sauki�?
Ya miko mata magani yace ki tabbatar kinsa mata a abinci taci, inhar taci sau uku ke da kanki zaki ban labari. Maganar aljani kuma karki damu zan shirya komai, sai dai yau kudin aikin sai kin hada da irinta kwanaki, dan dole na mika sakon aljani zuwa cikin jikinki.�?
Tafahimci me yake nufi sosai dan sanda zata rufe bakin kowa akanta sai data bashi kanta ya isar da sakon aljani jikinta. Bata damu ba haka ta wuce cikin daki shima yabi bayanta…�?.

{Allah ka mana tsari da wannan bala’i da masifar, ace saboda buri duniya mutane basu dauki zina wani laifi ba.}

🏌🏻‍♀�?
2/14/22, 21:23 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

20🤾🏻‍♂�?
Boka ko nace malam sai daya gama biyawa kansa bukata dan dana umarnin aljanun dayake amfani dasu ne akan inhar yanaso su cigaba da aiki dashi to fa sai dai ya dinga kusantar manyan mata, tsohon jini.
Itakam Hajiya mikewa tai dan dama bawai abinda ke gabanta ba kenan, burinta ta samu biyan bukatarta, kuma akan wannan zata iya aikata komai, in tace komai tofa lalai tana nufin komai.
Fitowa tai tana tafe tana tunanin yanda zata sa wannan 'yar iskar yarinyar taci abincinta, dan ta kula kallan kitso ashe takeyiwa rogo.

********
Abangaren Ibty kuwa ganin sha biyu tayi yasa ta nufi kitchen dan daura abincin rana, gaba daya hankalinta nakan mahaifiyarta, ta rasa yanda zatai ta kirata a waya.
Dabara ce ta fado mata da sauri ta dau wayarta ta fara duba yanda ake boye number in za'a kira waya. Ai nan danan google ya nuno mata, cikin tsananin jin dadi ta saka sannan ta kira Umma, tana ringing tana addu'ar Allah yasa ta dauka. Harta katse ba'a dauka ba, jiki a sanyaye ta sake kiranta, yanzun ma harta cire rai akan baza'a daukaba dan harta sauke wayar daga kunnenta sai taji ance "Assalamu Alaikum!"
Cikin tsananin jin dadi da zumudi ta dauka tace "Ummana?"
Aminu daya taso dan ya sanar da ita zai fita daga nan zai taho dasu Islam yaji muryarta da yanda take magana cikin farinciki.
Umma tace "Ibtisam? Naga number wayar a boye?"
Tana murmushi tace "Kullewa nai, Abba ne yace karna kira ni kuma hankalina ya kasa kwanciya."
Kalamanta sunyi tsananin ba Aminu mamaki, taya mahaifi zaice karta kira mahaifiyarta?
Bai gama dogon nazari ba yai kamar zai juya sai yaji tace "Umma komai na gida ya dawo daidai? Hankalina yaki kwanciya wlh."
Dan juyowa yai ya kalli kofar kitchen din yana mamakin abinda yake ji. Umma tace "Ibtisam haryanzu ban huce na abinda kika aikata ba, ko tunowa nai zafinki nakeji, taya zaki bari abu ya rincabe haka? Kina sane da irin farin cikin da mukeyi na ganin munyi hadin auran nan?"
Idanunta ne suka ciciko da kwalla sai jiyai tace "Wallahi Umma bansan abin zai kai haka ba, ban kuma san a dalilina abubuwa zasu rikice haka ba, dan Allah Umma ki yafemin ke da Yaya wallahi na kasa samun nutsuwa ina ganin laifin duk nawa ne."
Jiki a sanyaye Aminu ya bar falan yana sake maimaita kalamanta, wayarsa kawai ya dauka ya tura mata sako akan yazo ya sanar da ita zai fita amma yaga tana waya.
Mota ya shiga yai shiru yana nazarin abinda ke faruwa, tabbas wannan ya nuna a dalilinsa ne take cikin wannan halin, sannan saboda haka ne bata samun nutsuwa ko cikin barcinta.
Bayan mota ya kalla inda littafanta suke ya dauko dan ya dawo dasu gaba tunda su Islam zasu zauna a bayan, gefen kujera ne yadan bigi hannunsa hakan yasa ya saki lidar, wasu daga cikin litattafan suka fito.
Hannu yasa ya daukosu yana kokarin maidasu ciki nan wata takarda ta fado daga ciki, kamar karya bude sai kuma ya samu kansa dadan budewa. Kai ya girgiza da sauri ganin bai kamata ba yana kokarin maidawa ya rufe idanunsa suka kai mai rubutun dake jiki. "Ibtisam ki fito waje karfe 10 na dare, zan daukeki mu tafi sokoto.............."
Mamaki ne ya rufeshi matuka tare da wani zargi daya darsu a cikin ransa, wanene yakesan daukarta su tafi? Saurayinta kenan? Lalai wannan ya tabbatar mai akwai wanda take so akai karfin hali aka bashi saboda Baffansa yasan Abbanta.
Ganin tunani suna neman yi mai yawa kawai yaja mota ya fita daga gidan, yayi mamaki sosai dan yana kokarin shan kwana ya hango Hajiya ta sauka daga kan adaidaita sahu, ina taje? Itada ba lafiya ba? Wucewa yai gida kai tsaye, yaje gidan ya tadda su Ummy sun fita dasu Islam da Baffa, Ainah ce kadai a gida.
Juice ta kawomai bayan sun gaisa tace "Yaya ina Ibtis....." sai kuma tadan rufe baki tana dariya tace "Aunty Ibtisam."
Kallanta yai yace "Tana nan lfy." Mikewa tai tana neman tashi taji yace "Kawarki kamar kawarki ce sosai ko?" Tambayar taso bata dariya yanda yai tambayat ta koma ta zauna tace "Yaya wace tambaya ce wannan?"
Fuska a daure yace "Indai kin gane ba shikenan ba?"
Tace "Kawatace sosai yaya tun secondary school muke tare."
Shiru yai yana tunanin ta yanda zaiyi tambayar ba tare da raini ba, yadanyi gyaran murya kafan yace "Ita batada wani saurayi ne ta amince ta auran?"
Gaban Ainah ne yadan fadi kadan badai Umar ya tari yayanta ba?"
Aminu yadan kalleta kadan ganin kamar tana neman tuno amsar da zata bashi ne yasa yai saurin cewa "Meyasa bata aureshi ba? Bayan tana sanshi?"
Ainah tadanyi ajiyar zuciya tace "Data auri wannan ai wlh gwara ta zauna babu aure."
Zarginsa daya ya tabbata kenan, akan tanada saurayin da take so, yadau juice yadan kurba yace "Dan mutum na talaka shikenan sai aki auransa?" Yai maganar cikin alamar bugar ciki, tai saurin girgiza hannu tace "Wallahi Yaya ba haka bane, sanda yake mata ne ya fara zama hauka, ya hanata sukuni, ya hanata rayuwa, makaranta wannan biyota yake fa? Saboda kishinsa na hauka."
Dan idanunsa ya runtse kadan lalai ba shakka silarsa ce ta rabasu, da alama kuma saurayin na matukar santa.
Kallan Ainah yai yace "In tasan yana santa haka meyasa bata sanar dani ba? Ko ta sanar da iyayenta?"
"Tab! Yaya wlh ita Ibty ba sanshi take ba, a gidan su ya taso ya bi ya takurawa rayuwata kallo kadai in namiji ya mata wlh sai an kwaceshi a hannunsa, wannan Yaya ai ba so bane hauka ne, bakasan takura da masifar da ta shiga a dalilinsa bane, gashi ta kasa sanarda iyayenta saboda dan yayan babanta ne kuma a gidansu yake."
Shiru yai kenan yaran daya auri Yayarta ne? Meke faruwa kenan?
Kamar bazaiyi magana ba sai yace "Meyasa ya auri yayarya to?"
Nan Ainah ta sanar dashi abinda Ibty ta fada mata, sannan tace "Ni na bata shawara akan kartai magana kila ya hakura da ita ne, bansan me kuma ya faru ba harta aureka ba."
  Kallan da Umar ya makamai ya tuno da yanda yanayinsa yake, ya kuma tuno da fasamai glass din mota da akai, da kawota da akai ba tare da shiri ba, lalai Umar baisan ba Ibty aka bashi ba kenan sai bayan an daura auran, to amma a ina aka samu matsala? Haka ya zauna sam tunani ya hanashi sukuni, ya daura ya kwance, tabbas tunkararta da maganar shine saukinsa amma matsalar shi baisan ta ina zai fara tambayarta ba, haka ya zauna harsh Ummy suka dawo sannan ya kwaso su Islam suka taho.
Da gudu sukai cikin gida, ya bude musu kofa ta bangarensa, suka shiga ciki suna kiran "Kawar Aunty!"
Da sauri ta fito daga daki sanye da hijab da alama sallar la'asar tai, suna karasowa ta rungumesu, tace "Kawayena kun dawo?"
Islam cikin murna da tsale tace "Kawar Aunty zo kiga abinda Baffa ya sai mana" tai maganar tana jan hannunta.
Ibty ta biyota tana dariya, Ilham tace "Kawar Aunty na dauka kin koma gida har inajin haushi bazamu nuna miki ba."
Murmushin yake tai tace "Kwantar da hankalinki Ilham zan kwana biyu anan kafin na koma."
Falan Aminu suka nufa inda suka ga katan kwali guda biyu dauke da hoton keke, murmushi tai tace “Inyee lalai yau dole asha murna.�?
Kallan Aminu tai cikin girmamawa tace “Sannu da dawowa.�?
Shiru yai yana kallanta, fuskarsa sauke da alamomin tambaya masu yawa.
Nan fa aka fara murna suka zauna ana bubude kwalin, yana zaune yana kallansu.
Kallanshi tai tace “Ya Aminu taimaka mana mu hada dan nikam na kasa.�?
Kamar yace bazaiyi ba dan shi ya tsani a dinga kokarin saka shi abu, sai dai baisan dalili ba ya dan sa hannu ya jawo abin gabanshi yana hadawa.
Mikewa tai ta fara kawo abinci shi kuma yana hadawa, sukam su Islam sun kafa sun tare suna jira a gama.
Ibty tana murmushi tace “Kofa an gama hadawa sai anci abinci sannan za’a fara hawa.�?
Islam ta shagwabe fuska tace “Dady ni yanzu nakesan hawa.�?
Bai kalli inda take ba sai Islam daya kalla yace “In kunci abincin sai kuyi.�?
Taji dadi sosai na yadda yabi bayanta dan kallansa tai tare da sakin murmushi. Sai daya gama hadawa sannan suka zauna sukaci abinci tare, Islam sai da Aminu ya kalleta sannan ta daina zuba surutu.
Ai tana gamawa ta ja kekenta ta fito harabar gida, nan suka fara kokarin yi ita kuma tana nuna musu yanda ake, ba abinda kake juyowa sai dariyar nishadi nasu Ilham da Islam.
Hajiya dake zaune a bangarenta tana yin farfesun kaza wanda takeso ta gama ta zubawa Ibty magani a ciki, ta kai mata da sunan maganin mata. Yanda take juyo muryar yaran ne yasa ta fito waje, takaicinta daya babu hanyar dazata ga abinda ake ciki, itakam wannan katangar an cuceta da akayi ta, kunne ta kasa sosai tana juyo me suke cewa. Wasa suke sosai sosai tana juyo muryar Ibtisam, kwafa tai lalai yaran nan, duk abinda ta fada musu? Kitchen ta koma ta kafa gumbuda maganin a cikin kwanan farfesun data zuba mata, itadai tana fatan an tura mata aljanun da zasu rikitata dan tsanar yarinyar ta kara shiga ranta matuka.

*******
Bayan sallar magrib tana daki tana karatun qur’ani su kuma suna falo suna kallo, kwankwasa kofa taji ta mike ta fito gabanta na faduwa dan ta tabbatar Hajiya ce.
Budewa tai bakinta dauke da addu’a, Hajiya tana tsaye sanye da dogon hijab dinta, su Islam suna jin muryarta suka taho da gudu suka rungumeta. Ibty ta daure tace “Hajiya ki shigo mana.�?
Kai ta girgiza tana murmushi tace “Islam ku shiga ciki zanyi magana da Aunty au da Mumynku.�?
Yanayinsu ne ya canza, Ibty tai saurin cewa “Aunty.�? Dariya sukai sannan suka koma ciki, kallanta Hajiya tai a ranta tace “Wato ke ‘yar duniya ko?�?
Sai kuma tai murmushi ta ciro dan karamin flask din dake cikin hijab dinta tace “Ina zaune nace bari dai na miki kazar amare, na tabbatar ku amaren yanzu baku damu da kanku ba, ga mijinki ba saurayi ba yana bukatar yajiki yanda ya kamata.�?
Tsananin mamakin da Ibty ta shiga ya wuce duk tunanin mai sauraro, me matarnan take cewa?
Hajiya ta dan riko hannunta ta mika mata tace “Daso samuna nane ma a gabana zaki cinye na kwashe kasusuwan na binne, a matsayin ‘yata na daukeki shiyasa nake san na miki duk abinda uwa ya kamata tai, ko dan taimakon da Aminu yamin dole ne kuma hakkinane na kula dake. Naga haryanzu bakizo kinga inda nake ba balle na baki acan shiyasa na taso.�?
Kallan flask din tai tama rasa abin cewa, Hajiya tai murmushi tace “Kimin alkawari zaki cinye tas.�?
Ta kalli kwanan sannan ta daga kai batare da tace komai ba, Hajiya tai murmushi sannan ta koma.
Haka Ibty ta shigo da flask mamaki duk ya hanata sukuni, kitchen takai kawai ta ajiye sannan ta fito, dakinta ta koma ta zauna fuskarta ciki da mamakin wannan al’amari.
*****
Karfe takwas su Islam sukai baccic ta gyara falonta sannan ta wanke ragowar kwanuka, bude flask din tai sannan ta rufe, ita ko da ace ma akwai abinda ya shiga tsakaninsu da Aminu ai batasha maganin nan ba balle ta tabbatar Aminu babu so balle sha’awarta a tattare da shi.
Fitowa tai ta shiga wanka sannan ta saka riga da wando irin masu fadi din nan na bacci, ta zura hijab dinta sannan ta nufi bangaren Aminu, hannunta dauke da flask din ruwan tea da cup.
Yana daki yana waya sanda ta shiga, a hankali ta ajiye sannan ta koma kan gado inda ta kwana jiya ta dau wayarta tana daddanawa.
Bayan ya gama ya kalleta yana tunanin ta yanda zaiyi ya tambayeta, haka yasha tea yanayi yana kallanta, Ibty kam ganin shirin yayi yawa batasan ma sanda bacci ya fara daukanta ba, wayarta na hannunta ko addu’ar bacci batai ba.
Karfe sha biyu Aminu na kokarin kwanciya yaga tana girgiza kai da karfi, da sauri ya karasa inda take yadan dagota kadan, yace “Me nene?�?
Gaba daya tana abu kamar mai firgici, hankalinsa ya fara matukar tashi da sauri ya fara kwaroro addu’oi yana mata, dan abun ya bashi tsoro, ya dade yana mata addu’a kafin ta bude idanunta.
A jikinsa ta ganta a kwance ya ririketa sosai, hawaye ne suka gangaro daga idanunta, idanta yayi jaa sosai tace “Ya Aminu wasu mutane ne ina gudu suna bina, bama mutane bane dan ban taba ganin irin hallitarsu ba.�?
Tausayinta ne ya kamashi yace “Hala bakiyi addu’a ba kika kwanta?�?
Tace “bansan bacci ya daukeni ba, inasan ka gama shan tea ne ko sai da safe na maka.�?
Haryanzu tana kwance a jikinsa yana kallanta, can ya daure yace “Kin tabbatar ba mafarkin tsohon saurayin ki bane yake kokarin jefaki cikin wani hali?�?
Shi kenan ta faru ta kare, Ya Aminu ma yasan abinda ake ciki.
Mikar da ita zaune yai sannan yace “Meyasa zaki jefa kanki cikin wannan halin in har kinsan kina sanshi?�?
Hawaye ne suka zubo saman kuncinta, bakinta na rawa tace “Gujewa masifar da zan fada nakeyi, Yaya in da akwai yanda zanyi da na yakici tarihin rayuwata dashi.�?
Kwayar idanunta ya kalla, wanda ke zubar da kwalla, kamar zai sake magana sai yaga kamar shi bai dace ya dameta da maganar ba, da alama ita kadai tasan halin da take ciki.
Kwanciya yai tabi bayansa da kallo tana share kwallarta, kwanciya tai suka dan juyama junansu baya.
Kamar wanda sukai bacci, itakam addu’a kawai takeyi, sai data gama ta shafe jikinta sannan tace “Kayi hakuri Yaya na boyema abu kafin ka aureni.�?
Bai juyo ba sai dai kalamanta sun bashi mamaki, ya dauka shine ya kamata ya bata hakuri?
“Kayi hakuri a dalilina na ina neman hanaka kwanciyar hankali.�?
Yanzu kam juyowa yai ya kalli bayanta da take kwance da alama hawaye take dan yana jin muryarta tana dan rawa.
“Kayi hakuri in har nice…�?..�?
Hannu taji ansa an dagota ta zauna akan gado tana kallansa, shima kallanta yake, sai dai yanzu ta tabbatar kallan tausayawa ne a idanunsa, wanda bata taba gani ba.

Ayusher🏌🏻‍♀�?
2/17/22, 19:26 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

21
Kasa tai da idanunta cikin jin nauyin sa, a hankali shima ya zare hannunsa daya riketa dashi sannan yai dan gyaran murya yace “In ance miki yarinya kiji haushi.�?
Dagowa tai cikin dan bacin rai tana sanyin korafi, ganin idanunsa akanta yasa tadan kauda kai cikin kunkuni, komawa yai ya zauna yace “Inba yarinta ba, duk darajarsa a gidanku ya kaiki ne? Ko iyayenki zasu bi bayanshi ne suki bin bayanki?�?
Ta sab gaskiya ya fara sai dai�?. Jin kalamansa ne ya katseta “Tsoronshi kike hala?�?
Ta kalleshi tare da dan shagwabe fuska tace “Allah dan bakasan halinshi bane, baiki yamin duka ba da sunan so.�?
Kai Aminu ya girgiza sannan ya kwanta ya danja bargo yace “Ke kuma uwar tsoro ba? Gashinan kullum kikai bacci kina mafarkin yana dukanki hala?�?
Bayanshi ta kalla tace “Allah dan bakasan haukar Ya Umar bane.�?
Bai tanka mata ba, tace “Kuma tsoro a musulunci mafa halak ne, ina zanso a jibgeni?�?
Yanzun ma bataga ya kulata ba haushi ya kamata ta mike ta fito daga dakin, zuwa tai takai Islam fitsari sannan ta dawo ta sake shafe jikinta da addu’oi sannan ta kwanta, aranta tana cewa sai ya dauko magana ya kuma ki karasa magana dakai.
Tana sallar asuba tai karatunta harya dawo daga masallaci sannan ta fito daga dakin ta nufi dakinsu Islam ta tashesu ta musu wanka sannan ta dauko musu kayan makaranta ita kuma ta wuce kitchen tana harhada breakfast.
Tanayi tana shiryasu sai data gama tsaf sannan suka nufi bangaren Aminu, shima ya fito cikin farin yadi, ya sa hula da farin glass dinsa. Ganin su Ilham sun shirya ga abinsu a lunch box ga kuma ta gama jera abinci a dining yasa wani sanyayan murmushi ya bayyana a fuskarsa.
Zama sukai sunaci ita kuma ta wuce toilet tai wanka, doguwr rigar atamfa ta saka bata tsaya kwalliya ba tasa turare sannan ta fito falo. Ta tarar sun gama, haka ta kwashe kwanukan takai kitchen, ta rakosu har waje hannunta rike da Islam da Ilham.
Aminu ya kalleta bayan sun isa motar sannan ya miko mata ledar littatafanta yace “Ainah tace kuma jibi zaku fara registration ko?�?
Ta daga kai sannan ta dora da �? Eh jibi ne.�?
“Allah ya kaimu.�?
A hankali tana murmushi tace “Ameen.�?
Nan suka ja mota suka fita, da kallo ta bisu kunyar kanta ce ta kamata lalai fa yanzu ta zama matar gida, sai take ganin abin kamar wasa.
Aminu ta glass din mota ya kalleta ba shakka tanada hankali da tunani, ya tabbatar zamansu zaiyi dadi duk da ba santa yake ba, a kalla ya kula tasan yanda ake kula da gida tana kuma da dogon tunani.
Ibty kam Ciki ta koma ta gyara gidan sannan ta mike akan kujera tana kallo.
****
A bangaren Hajiya kuwa jiya sam bata samu baccn kirki ba, haka kawai jikinta ya bata Ibty batasha farfesun nan ba, karin bakin cikinta kudin hannunta sun fara kasa, gashi jiya kwata kwata Aminu bai shigo ya dubata ba, a kalla yaci ace yazo yaga ko ta warke ai.
Kwafa tai tace “Wato har karuwar nan ta fara dauke mai hankali?�?
Mikewa tai bayan taji fitar mota tahau yin faten dankali da wannan ragowar maganin, tana gamawa ta zuba a flask ta fito waje, gun mai gadi ta nufa suka gaisa ta mikamai ledar flask din tace “Gashi ka mikawa Amarya kace inji Ummy, kasan Mamman ya saba da bangarena can yakai.�?
Ya amsa ba tare da wani zargi ba ya wuce ciki, ciki ya shiga ya kwankwasa kofar gidan.
Ibty tana kwance har bacci yadan fara daukarta taji ana kwankwasa kofa, gabanta ne ya fadi badai matarnan bace? Mekewa tai jikinta nadan rawa ta nufi kofa, a hankali tace “Wanene?�?
Daga waje yace “Bala ne.�?
Wata nanauyiyar ajiyar zuciya tai sannan ta bude kofar, gaisheta yai sannan yace “Sakone Ummy ta aiko dashi da alama Mamman bangaren Hajiya yakai.�?
Kallan mamaki tadan mai sannan ta amsa tai godiya, ciki ta shiga ta wuce kitchen. Budewa tai taga fatan dankali, murmushi tai sannan ta kalli kular Hajiya ta jiya, batasan asarar abinci sai dai ko almajiri taba gani take batai imani ba, tunda har jikinta yabata akwai wani abin a ciki yanzu inta ba wani shi kuma wani abin ya sameshi fa?
Kamar zataci dankalin sai kuma ta rufe tace “Naci anjima yanzu bari nadanyi bacci.�?
Komawa falo tai sannan ta kwanta, kankace me wani bacci yayi gaba da ita.
******
Karfe sha biyu ta tashi nan ta wuce kitchen ta fara girkin rana, karfe biyu Mamman ya dawo dasu.
Ta fito suka rungumeta cikin murna, har Mamman zai shiga mota tace “Mamman nagode da sako.�?
Kallan mamaki ya mata yace “Sakon me Hajiya?�?
Tadan kalleshi tace “Sakon da Ummy ta baka ka kawo da safe.�?
Kai ya girgiza da sauri yace “Ni kuwa? Ni ai banzo ba sai yanzu.�?
Gabanta ne ya dan fadi, tadan daure tace “Ayya! Kila mistake Bala yai.�?
Ciki ta koma sunacin abinci tana mamakin wannan abin, batasan dogon zargi sai dai babu tantama Hajiya ce kenan ta aiko mata da abincin, wato bayan na jiya ba shine ta aiko mata?
Haka harsu Islam suka tafi makarantar Islamiya, hankalinta ya kasa kwanciya da wannan abin mamakin daya faru.
Hajiya kam ta rasa abinyi, gashi ta kira Malaminta ya duba yace haryanzu bataci ba.
Waya ta dauka ta kira Aminu, yana dauka kawai ta sa kuka.
Hankalinsa a tashe ya fara tambayarta abinda ke faruwa, kin magana tai sai kuka kawai da takeyi.
Bai tsaya wani abu ba ya nemi uzuri tare da fitowa daga gun aiki.
Kai tsaye ya shiga bangarenta hankalinsa a tashe kai kace Ummy ce ke mai kiran gaggawa.
Sallama yai daga ciki ta amsa cikin kuka, ya shiga ciki hankalinsa a taananin tashe. A zaune ya ganta ta gama cika akwati da kaya, ga kuma wani akwatin nan tana hadawa tana hawaye.
Taahin hankaline karara ya bayyana a idansa, yace “Hajiya meke faruwa?�?
Ta girgiza kai kawai tana hada kayanta, cikin kulawa da damuwa yace “Hajiya! Wani abin akace miki?�?
Kallansa tai tare da zama a bakin gadan tana share kwalla tace “Aminu wannan abin nake gudu tunda kai aure shiyasa na nemi barin gidan nan, yanzu kam dan Allah ka barni ko banda inda zanje zan fita daga nan gidan, Na’imah ta tafi ta barni banda kowa a duniya, yanda ta tafi nima fatana Allah ya dau raina.�?
Tsananin tashin hankali ne ya bayyana a idansa, tuno sanda Na’imah zata rasu yai kalma daya take roko daga gareshi akan ya kula da mahaifiyarta.
“Meya faru?�? Yai tambayar cikin kakkausar murya.
Ta girgiza kai cikin damuwa tace “Aminu tunda kai aure matarka ta kwashe su Islam, na fahimci wannan dole ne inhar muna bukatar ta shaku dasu, banyi magana ba. Na kai muku abinci ta dawo dani tace bataso na dinga shiga abinda bai shafeni ba, girki da kula daku aikinta ne, nan ma ta dawo dani dauke da tulin abinci haka na dawo na sa abinci a gaba wanda rashin jin dadin yanda ta zubamin munanen kalamai ya sa ciwo na ya tashi, shima ban sanar dakai ba saboda banaso ku samu matsala, da daddare nai farfesu naga abin kwalama ne bansan na cinye ni kadai nakai muku shima ina kallo ta shiga dashi kitchen babu alamar taba su Islam, yanzu nayi faten dankali ganin su Islam naso na zuba musu a flask nan ma ta hanasu akan bata yarda da abinci na ba. Su Islam zasu Islamiya sun biyo na tambayesu sukace bata basu ba.�?
Kuka tasa sosai, tace “Zan yarda na shanye komai amma banda kokarin rabani da jikokin da su kadai suka ragemin a duniya, Aminu kafin zaman nan ya koma na rashin dadi ka………�?
Yanda ya mike a fusace ne yasa ta fito itama tare da kallan turaren wutan data hada domin shi wanda yasha magani, tana kallo ya fita.
Kwafa tai tace “Kedin banza ke din wofi? Ni da kika gani bala’in dana shiga da yasa yanzu bana shakkar ko wani tsinane, ke din banza?�?

*******
Tana sallar la’asar taji alamun mutum a cikin dakinta, addu’arta ta shafa sannan ta juyo, cikin mamaki ta kalli Aminu dan bataji alamun dawowarsa ba.
Mikewa tai fuskarta a sake tace “Yaya Sannu da dawowa.�?
Yanayin fuskarsa kadai zaka kalla kasan yana cikin bacin rai.
Sallaya ta ninke fuskarta dauke da damuwa tace “Yaya?�?
Fitowa yai daga dakin ba tare dayace mata komai ba, kitchen ya nufa kai tsaye ya fara bubude flask, can gefe ya hango flask din Hajiya, nan ya nufi gun ya bude, daya farfesu ne daya fatan dankali, babu alamar an taba dan farfesun ma harya fara tsami.
Ibty kam kallansa take dan bata fahimci me yakeyi ba. Waigowa yai yace “Me yasa ba’aci wannan abincin ba har daya ya fara tsami?�?
Ta rasa mema zatace, cikin dauriya da dan tsoron abinda zai je ya dawo tace “Yaya jiya da daddare aka kawoshi lokacin su Islam sunyi bacci ni kuma na koshi.�?
“Shine ba’asashi a fridge ba aka barshi a waje?�?
Shiru tai tana tunanin abinda zatace, itakam ta inda ake cutarta kenan, in rai mutum ya baci bata iya yin bayani ba, sai taji duk ta rikici.
Takowa yai yazo inda take daf har tana iya juyo numfashinsa, wani irin faduwar gaba ya sameta akai akai.
“Na dauka na sanar dake matsayin Hajiya a gareni ko? Ko kina tunanin harkin kai matsayin da zaki shiga rayuwar gidana? Kina abu a hankali ina tunanin eh a kalla ko banasanki, zan iya zaman aure dake saboda bayan yarintarki kina da hankali da sanin abinda ya kamata.�?
Ya mata wani kallo yace “Sai dai me? Ashe kema daya kike da munafukan mata wadanda ke nuna Allah a waje shaidan a zuci, ke bakya ko tausayin baiwar Allar nan? In kin rabata da jikokinta me kika mora? Wannan wani irin bakin hali ne? Ko sati bakiyi a gida ba kina neman hanata ganin jikokinta?�?

Dagowa tai cikin matukar mamaki da jin zafin kalamansa, a hankali wasu zafafan hawaye suka zubo idanunta, ta kasa ko magana sai hawaye kawai da takeyi.
“Ki tsaya a matsayinki inhar kinasan zama a gidan nan, sai yanzu na fara fahimtar dalilin dayasa saurayin can ya takura miki da alama yasan wasu daga cikin halayenki ne yake tsoro.�?
Juyawa yai cikin matukar bacin rai, Ibty kam zubewa tai a kasa kawai tasa kuka.
Haryakai karshen falan ya juyo ya kalleta, yanda take kuka yasa kasan ransa ya soso, meya sameshi? Duk da tayi laifi ya kamata ya zaunar da ita ya mata fada cikin sanyi, meyasa ya rufeta da fada haka?
Yafi minti uku yana kallanta sannan ya wuce daki, kansa yadan dafa dake ciwo sannan ya wuce toilet ya shiga wanka. A wanka kam ruwa yai ta zubawa kansa yana jin haushin abinda yai, yanada zafi sai dai bai iya rufe mutum da fada haka ba, sannan wasu kalamai daya mata sun sa yaji haushin kansa.
Ibty kam ta dade tana kuka kafin ta mike, abincinsa ta dauka takai mai, tana kokarin fitowa ya fito daga daki sanye da doguwar riga, idanunsu ne suka hadu da juna, idanunta duk sun kumbura.
Kai yadan kawar da kansa sannan ya karaso, zama yai ta zubamai abinci sannan ta fito daga falan gaba daya jikinta ba karfi.
Haka yaci abincin gaba daya shima zuciyarsa ba dadi, komawa yai ya zauna yadan kunna tv.
Ibty ta dawo ta fara daukan kwanuka, sai datazo na karshe sannan ta kalleshi, haka kawai taji wasu hawayen sun zubo mata.
*****
Gaba daya ba abinda ya sake hadasu harsu Islam sukai bacci, ji take kamar karta kwana a dakinsa sai dai alkawari ta dauka ba yanda zatai.
Dakinsa ta nufa bayan tayi wanka tasa kayan bacci, idanunta haryanzu a kumbure suke, sallama kawai tai sannan ta wuce ta kwanta.
Dakin yayi shiru sai kara keyboard na laptop dinsa dake tashi, duk yanda taso tai bacci ta kasa saboda kalaman Aminu dake dawo mata.
Juyowa tai saitinsa tana hawaye tace “Yaya a matsayinka na babba bai kamata ka fara bincika taba kafin ka dau hukunci akaina?�?
Jikinsa ne yai sanyi, sai dai baisan me zai ce ba. Ta dan share kwallarta tace “Bansan tsakaninku da Hajiya ba bankuma san shakuwarku ba sai dai a kalla nima a bani hakkina aji ta bakina, bansan laifin danai ba ka rufeni da fada.�?
Kallanta yai yanzun ma baisan me zaice ba, juyawa tai kawai ta cigaba da share kwallarta.
Hannu yasa ya dauko tissue din dake gefensa ya dan taba bayanta, juyowa tai ta kalleshi. Nan ya mika mata tissue din yace “Kukan ya isa haka nan.�?
Amsa tai ta dau biyu ta ajiye ragowar sannan ta share fuskarta.
Shiru tai can taji yace “Rainane ya baci bansan ya akai ba na rufeki da fada ba tare da jin ta bakinki ba, sai dai inaso ki sani banasan zuwanki ya zama silar rugujewar farincikin gidan nan, bance sai kinyi komai daidai ba but banasan ki takurawa tsohuwar da batada kowa sai ni, wacce batada lafiya take neman mai kula da ita.�?
Shiru Ibty tai lalai itakam taga ta kanta, har tana murna zamansu ya fara dadi sun fara fahimtar juna yanzu shine matar nan zata fara yi mata sharri.
Sunyi shiru jiki a sanyaye tace “Kayi hakuri�?
Harta dauka bazaiyi magana ba sai taji yace “Kema.�?
Haka ta kwana da bacin ran abinda matarnan ta aikata mata, gashi batasan yanda zatai ta huce takaicinta ba.

Ayusher🏌🏻‍♀�?
2/19/22, 20:55 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*22*
Aminu sam baccin ranar baimai dadi ba, ya rasa yanda zaiyi ya amshi laifinsa, da asuba kam mikewa tai kawai ta fito daga dakin dan ko sallah ba’a dakin tai ba. Yana dawowa daga masallaci ya dauka zai juyo karatunta yanda ya saba yaji shiru, dakin ya nufa bata ciki, hakan ya tabbatar mai bama anan tai sallah ba, nan ya zauna bakin gado tare da dan murza saman goshinsa, baisan meke damunsa ba, tabbas yasan bai kyauta mata ba sai dai baisan ta yanda zai bata hakuri ba.
Bayan ta shirya yara ta kawo abinci, kallanta yai sanye take da riga da skirt na lace, ya mata kyau sosai “Ina kwana?�? Abinda kawai tace kenan ta zauna suna magana dasu Islam, yanayinta ya kalla, haka yaci abincin duk jikinsa a sanyaye, nan suka fito ta rakosu har mota sannan ta koma ciki. Da kallo yabita harta shiga ciki sannan yaja mota suka bar gidan.
Ibty kam gyaran gida ta gama ta zauna tai shiru a falo tana tunanin kalaman Aminu, tabbas an dade ba’a fada mata munanen kalamai irin haka ba, hawayenta ta share, sannan kalaman Ummy suka fara dawo mata, lalai inhar ta bar abin nan batasan nan gaba me matarnan zatace ma Aminu akanta ba, “matsoraciya!�? Kalaman Aminu ne suka daki dodan kunnuwanta, kwanciya tai tana tunanin mafita, ganin damuwa da takaicin abin sunki barinta kawai ta mike ta nufi kitchen, kwanukan Hajiya ta kwaso ta zubar da abincin sannan ta wanke, awarar indomie datai da safe wanda yai ragowa ta zuba a daya daga cikin kular sannan ta dau leda ta zuba kulolin a ciki ta dau wayarta ta kira Aminu.
Yana zaune yana duba wasu takardu yaga kiranta, cikin dan hanzari ya daga tare da yin gyaran murya, sallama tai yana amsawa tace “Zan shiga naba Hajiya hakuri akan abinda ya faru.�?
Cikin sanyin jiki yace “Karki damu komai ya wuce ai.�?
Kai tadan girgiza kamar yana ganinta tace “Yanda rankanya baci jiya ina ganin gwara na bata hakuri da kaina.�?
To kawai yace dan baisan abinda zaice ba, tunanin abinda zaice ya fara kawai yaji an kashe wayar, lalai yarinyarnan dan taga baiji dadin abinda yai ba shine take mai abinda taga dama?
Ibty kam hijab dinta ta zura kawai ta fito, duk da tsoro da fargaba dake damunta sai dai wannan karan bazata bari a maidata wawiya ba, Umar ya koya mata hankali, ita kadai tasan wahalar datasha agunsa.
Dayake gate dinta ba rufewa take ba, turawa kawai tai ya bude, bakin kofar shiga ta tsaya ta dade tana addu’oi kafin ta kwankwasa kofa.
Hajiya tana zaune ta baje akan kujera tana kallan tashar arewa, gefe kuma ga cincin nan da fanta ta kwalba, tana jin wani nishadi, yanzu ma tunanin abinda ya kamata tayiwa Amarya takeyi, murmushi tai ganin ta gama hada abinda zata mata wanda ta tabbatar Aminu sai ya kusa marinta.
Kwankwasa kofa taji, mikewa tai ta bude dan tayi tunanin almajirin datake aika ne, yanda ta zabura kadai ya tabbatarwa Ibty tayi mamakin ganinta.
Cikin dauriya tace “Amarya?�?
Ibty ta gaisheta, nan fa suka fara kallan juna, Hajiya ta daure tace “Shigo mana.�?
Sallama tai ta shiga ciki ta zauna a kasa, sannan ta sake gaisheta.
Hajiya ta amsa tana dan yake ta amsa, Ibty ta miko mata ledar kwanuka tace “Dama kwanukanki na kawo miki, sai abin kwalama danai da safe.�?
Wani kallo ta mata, aranta tace “Badai nima maganin ta samin ba?�?
Ganin yanda take kallan Ibty yasa tai dan kasa dakai tace “Kiyi hakuri bansan ranki ya baci ba, sannan jiya nidai Bala cemin yai dankalin daga gidan Ummy yake.�?
Sam ta manta da wannan karyar datai, dariya tai tana washe baki tare da kokarin boye karyar datai tace “Kinsan Bala wani sa’in akwai shiririta, cemai nai ya kaiwa su Islam kila can ya tafi yana tunanin shirme.�?
Ibty tai murmushi tace “nima nayi tunanin haka, sannan farfesun mata da kika kawo abinda yasa bansha ba, banasan abubuwan mata daga aurena, a gida ma da aka bani bansha ba, amma tunda bakiji dadi ba kiyi hakuri.�?
Hajiya tadan canza murya tace “Aminu dai sai a barshi, nifa sam bancemai naji haushi ba, sannan ni danake gidana ta ina zansan baki ci ba, muna hira ne fa zancen ya ratsa.�?
Ibty kanta na kasa dan ta kula inta hada ido da ita bata iya maida murtani yanda ya kamata, tace “Allah sarki, amma dai duk da haka nasan ke kika mai zancen dan shi baima san kin kawo abincin ba, kinga maganin mata dama bai kamata ya sani ba, sannan na jiya kuma da aka kai ance Ummy balle yasan daga nan ne�?
Hajiya tadan yi dariya sosai tace “Kinsan kn girma ya kama mutum sai yai ta maganar shirme, ni banmasan ya akai muka fara maganar ba.�?
Itama Ibty tai murmushi tace “Nayi tunanin haka dama dan nasan haka kawai bazaki hadamu fada dashi ba, tunda dai ke a matsayin uwa muka daukeki.�?
Hajiya rasa abin cewa tai wato lalai yarinyar nan ba kanwar lasa bace, lalai sai ta tashi tsaye ta ci kwal uban yarinyar nan.
Ibty ta mike tare sa yi mata sallama ta fito, da wata muguwar harara tabi Ibty, lalai wannan tsinaniyar yarinyar wuyanta yayi kwari.
Kallan kwanon tai a fusace ta wuce kitchen ta zuba abincin a shara, tace “ta rasa abinda zata jefenk dashi ma sai awara? Da alama maganine a tsakiyar waken suyan.�?
Ibty kam tana fita ta kama bango dan jitai kafafunta na rawa, ajiyar zuciya tai sannan ta koma gida, ko ba komai ta rage takaicin dake ranta sannan inma da biyu take kawo mata abinci itama yanzu zata dinga kai mata sai taga me zai faru.

*******
Umar ne ya kalli wani dalibin da ya fito daga makarantar yace “kenan sai wani satin za’a fara registration?�?
Saurayin yace “Eh gaskiya.�?
Shiru yai sannan yai dan kwafa ya wuce gida ransa a matukar bace.
Takaici ne ya kamashi ganin Bilkisu a kwance akan kujera tana kokarin mikewa, wata muguwar tsana da takaici ne ya rufeshi, babban burinsa bai wuce ya shigo gidan auransa yaga Ibty ta taho da gudu ta rungumeshi ba, yanzu wace banzar rayuwa yakeyi?
Bakinta na rawa tace “Yaya ka dawo? Sannu da dawowa.�?
“Bandawo ba, tunda aljani kika gani bani ba, ni wai dan Allah kwakwalwar dakikai gareki ko me? Wace irin ‘yar iskar tambayace wannan? Wai Ka dawo? Ban dawo ba ina waje.�? Yaja tsaki sannan ya zauna akan kujera ya dau remote ya kuna music, jiki a sanyaye ta hau kan kujerarta, batada lafiya tun jiya take fama, abinci ta daukomai ta ajiye a gabanshi.
Wani kallo ya watsa mata yace “dan Allah inkin ajiye ki matsa daga nan, sam banasan ganinki.�?
A hankali taja kekenta ta wuce daki, ya kara zabga wani tsakin sannan ya lumshe idanunsa, fuskar Ibty yake hangowa tana mai murmushi, hannunsa ya dunkule ya dan naushi kujera, wallahi sai Allah ya sakamai, kuma dole ne ya dawo da Ibty gunsa.

*******
Bayan yara sun tafi islamiya wajen karfe biyar da kwata Aminu ya dawo, hannunsa dauke da manyan ledoji na fruits, yaba Bala karamar ledar yace yakai bangaren Hajiya sannan ya wuce ciki.
Tunda ya shiga yake juyo kamshin turare, lumshe ido yai dan tabbas yanasan kamshin nan, bangarenta ya nufa, bakowa a cikin falan, kitchen ya wuce ya ajiye ledar sannan yadan kalli dakinta.
Kamar zai wuce sai kuma ya nufi dakin, sam a rayuwarsa bayasan shiga hakkin mutum shiyasa tun jiya abin ke damunsa.
Knocking yai, ba’a amsa ba hakan yasa yadan tura kofar dakin, Ibty ta gama wanka kenan saboda jinin al’ada daya zo mata dazu, dataji kwankwasawa yasa ta daura towel ta fito tana mamakin har lokacin tashinsu Islam yayi ne?
Fitowa tai sanye da towel din ta iya gwiwa, turus ta tsaya shima ya kalleta, haka kawai yau baisan dalili ba yaji wani abu yadan tsirgamai.
Ibty kamar zata koma toilet din sai kuma ta dake tace “Sannu da dawowa.�?
Gyaran murya yai sannan yace “Na shigo naji shiru ashe wanka kike.�?
Kai ta daga kawai batace komai ba, juyawa yai yana tunanin da alama da saninta take mai wulakanci, tun jiya inya mata magana sainta dinga amsamai kamar bataso, ya dauka ya bata hakuri? Ita tace kayi hakuri shima yace kema. Wannan bai isheta ba take nufi ko me? Shifa ya tsani a dinga neman juyashi.
Ibty kam kaya ta saka sannan ta danyi kwalliya sama sama, sai yanzu take fahimtar meyasa mata suke zama ‘yan duniya a gidajensu, wato wasu mazan sai su dinga nuna kallo ma baka ishesu ba, bawai so take ya sadu da ita a dole ba amma a kalla mijinka ya nuna maka kaima macece.
Lalai ko saboda Hajiya dole ne ta shawo kan Aminu yasota, dan ta tabbatar da yana santa bazai rufeta da fada jiya ba tare da bincike ba.

🏌🏻‍♀�?
2/25/22, 18:36 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

24
Ganin yayi shiru yasa tai shiru tana tunani, juyawa tai cikin ranta tana cewa “In har na danne tsoron tsohuwar nan dan me zan zauna Umar na ban tsoro?�? Jan idanunsa ta tuno da yanda yake tsareta a daki, hala tai ta tunane tunane har bacci ya dauketa. A bangaren Aminu kuwa abinda ya shekara biyar baiji ba shine ya taso mai yau, dan wata irin muguwar sha’awa ce ta rufeshi, haka yai ta juyi shima kafin baccin ya daukeshi.

****
Ran Juma’a suna tafiya school ta hau aikin gida tai wanka ta dauko wani dankakareren lace mai tsada ta saka, dinkin an mata shi mai kyau dan asali dama shi ta ajiye zata saka washe garin daurin aure to sai kuma aka samu matsala, tayi kwalliya sosai dan dama ba laifi ta iya kwalliya, Ibty ta fito das da ita kai kace ranar auranta ne, turaren wuta ta kunna wanda ya kara kama kayanta.
Sha biyu da rabi yara suka dawo daga skul nan suka ci abinci sannan ta musu wanka suma ta dauko kaya iri daya mai kyau ta saka suma lace sukasha an musu doguwar riga, tana daura musu dankwalli sukaji alamar bude gate. Wani irin dadi ne ya kamata yau dai xata gida taga Ummanta.
Fitowa falo sukai, shi kuma ya shigo kenan hannunsa dauke da leda, tunda ta shigo falan yake kallanta a sace, tayi kyau sosai da sosai gashi tun ranar da sha’awa ta tasomai abu kadan kesa yaji yana bukatarta. Har ta karaso yana tsaye yana dan satar kallanta, cikin murmushi tace “Sannu da dawowa.�? Tai maganar tare da sa hannu tana kokarin amsar ledar, hannunsu ne ya tabu a hankali ta dago ta kalleshi, shikam kasa janye hannunsa yai yanda ya saba, amsar ledar tai sannan ta juya ciki, ajiyewa tai a kitchen sannan ta dauko abincinsa, haka kawai takejin tunda ta tabashi bai janye hannunsa ba yanda ya saba ba ta samu kanta da murmushi a cikin ranta.
Ajiyemai tai a dinning sannan ta nufi dakinsa dan sanar dashi, ya cire rigarsa kenan tai sallama, juyowa yai ya kalleta, ta dauka zai maida rigar sai taga ya karasa cire ta daga jikinsa tare da kallanta. Ibty tai kasa dakai tare da yin shiru tana dan wasa da hannunta.
Sam batasan ya tako ba sai ganin kafafunsa tai yana nufo ta, gabanta ne yadan fadi kadan bata matsa ba haka kuma bata dago ba, daf ya matso da ita tana juyo numfashinsa, hannayenta tadan matse saboda yanda ta tsinci kanta, idanunta ta lumshe dan ta dauka rumgumeta zaiyi, ganin jikinsu ya hadu da juna, hannu yasa bayan ya matsota suna gogan juna, kofar data bari a bude yasa hannu ya rufe, sannan yadan kalleta, gefen kunnenta ya matso yace “A dinga rufe kofa saboda akwai yara a gidan, in kika shigo kika manta dasu su kuma suka taho nan fa? So kike suka babansu a haka?�?
A hankali tadan bude idanta daya tare da dan rike kunnenta tace “Sorry!�?
Matsawa yai daga jikinta sannan ya bude wardrobe ya dauko wasu kayan, tace “Dama kiranka nazoyi kazo kaci abinci.�?
Kai ya daga alamar to, juyawa tai kamar zata tafi sai taji yace “Duk kwalliya da zumudin zuwa gidan ne?�?
Tadan rufe fuska saboda kunya, murmushi yai yadau towel ya nufi bandaki, haryaje zai shiga yace “In Umar yaga kwalliya kuma ya hanaki dawowa to.�?
Yanayin fuskarta ne ya canza, kamar mai shirin kuka tace “Yaya baza dai ka daina ba ko?�?
Juyowa yai ya kalleta yace “Sai randa kika bar tsoron sa.�?
Tana kokarin magana taga ya shigo toilet baki tadan turo kafin tadan rufe fuskarta alamar kunya sannan ta fita.
Aminu kam a toilet shiru yai yana hadiyar wani abu, shikam meke damunsa? Taya zai bari sha’awar yarinya ta fara damunsa? Dan tabbas dazu rungumeta yaso yi ya wayance, iska yadan furzar lalai inya biya zuciyarsa tofa zai gabza abin kunya.
Haka ya fito yasa yadi fari sun mai kyau sosai sannan ya fito falo. A waje ya jiyo muryarsu da alama su Ilham ana keke ne, zama yai ya bude abincin, kamshin butter ne ya dan bigi hancinsa, vegetable soup ne wanda akai amfani da butter a maimakon mai, abinci yasa yana ci yana dan murmushi dan yana juyo hirarsu daga waje. Ba shakka Ibty tasan takan yara, har mamakin yanda ta shaku dasu daga zuwa yakeyi.
Yana gamawa suna shigowa, nan ta kwashe kwanuka suka kara gyarawa kafin su fito. Suna shiga tadan kalli bangaren Hajiya sannab ta tuno leken dataga tanayi ranar, cikin murmushi tace �? Yaya ko zamu shiga muyima Hajiya barka da juma’a kafin mu wuce.�?
Cikin jin dadi ya kalleta, wanda har ita kanta ta fahimci yaji dadin maganarta, nan yai parking a waje suka fito.
Hajiya kam tana kishingide a falo takaici duk ya isheta, tana juyo muryarsu Islam dazu suna wasa, yau kwana biyu kenan ko keyarsu bata gani ba.
Wata ajiyar zuciya ta bakin ciki ta saki sanda taji ana bude gate din gidan. Mamaki ne ya kamata dataji kwankwasa kofa yanzu, kafin ta mike har tajuyo murya da gudunsu Ilham.
Da sauri ta bude kofar ashe ba tare zasu fita ba? Da alama kawo mata su zaiyi ya fita. Kofa ta bude da sauri tana dariya tare da tafa hannu.
Da gudu suka karaso suka rungumeta, dadi ne ya kamata. Jin alamun bude kofa yasa tadan dago, Aminu ne ya shigo, haba wani irin dadi ya sake rufeta, ta bude baki zatai magana kawai taga Ibty ta biyo bayanshi.
Yanayin fuskarta ne ya canza lokaci daya, daurewa tai ta fara lale lale.
Nan suka koma ciki, suma suka karaso, Aminu ne ya zauna a kasa daga gefe, ga mamakinsa yaga Ibty ta karaso ta zauna gefensa, Hajiya ta kalleta ta dau wanka, wata tsana ce ta sake turnuke ta, lalai itakam mutuwa ta cuceta, banda mutuwa ina Aminu ya isa ya kawo mata wannan karamar karuwar?
Gaisheta sukai ta amsa, tana kallan Ibty tace “Amarya irin wannan kwalliya? Ina za’a haka?�?
Aminu yai dan murmushi yace “Gida zata ta ziyara saboda makaranta da zata koma.�?
Takaicin amsarsa ne ya kamata, wato harya fara bada amsa a maimakon ta? Ko batada baki ne?
Kallansu Islam yai yace “Ku tashi mu wuce saboda inaso na saukeku na wuce gun aiki.�?
Hajiya na kokarin magana taga harsun mike, Ibty ce ta kalleta tace “Hajiya mu mun wuce sai anjima.�?
Murmushin yake tai sannan ta rakosu, haka tana tsaye a kofa taga sun shiga mota, suna tafiya ta kwararo wani dogon ashar ta zabgawa Ibtisam tare da maimaita kalamanta, Hajiya mu mun wuce? Ko ubanwa ya tambayeta oho. Da karfi ta makonkofa sannan ta koma ciki, zama tai ta baza tagumi tana tunani kodai ta canza malami ne? Dan da alama wannan malamin ya fara sanyi, ba abinda yai aiki tun bayan auran nan.

********
A kofar gidansu yai parking, mamaki ne ya kamata ganin ya bude boat ya dauko ledoji guda biyu, karasowa tai tace “Yaya na menene?�?
Mika mata daya yai yace “Haka ake zuwa gidan da ba komai?�?
Amsa tai ta bude, turaruka ne ne da irin body wash din nan na kwali, ya mika mata daya shi kuma kayan kwalliya ne, yace “Kya rabawa su Iman ko?�?
Tayi mamakin jin yanda ya rike sunan Iman, kallansa tai tare da cewa “Angode Allah ya kara budi, Yaya ni sai yaushe zaka kira nawa sunan?�?
Boat din ya maida ya rufe yace “Randa kika bar tsoro?�? Ya kamo hannun Ilham sannan ya mata alama dakai akan su shiga.
Baki tadan turo tanasan yin magana gashi a gaban yara ne, ganin yanda ta maida maganarta yasa yadanyi murmushi kasa kasa.
Shiga sukai, ba kowa a harabar gidan, har saida suka isa ciki.
Kwankwasawa tai daga cikin aka amsa sannan Iman ta karaso ta bude, idanu ta zaro ta saki wani wawan ihu tare da rungumo Ibty iya karfinta, sam Ibty bata kawo irin rungumar nan ba ga hannunta dauke da ledoji, baya tai tana neman faduwa, da sauri Aminu yasa hannu daya ya taro bayanta, Iman sai a lokacin ta kula da abinda ta aikata, saketa tai tana dariya tare da yin alamun kunya na Aminu tace “Yaya kayi hakuri ai bankula tare kuke ba.�?
Ibty ta juyo ta kalleshi a hankali wani murmushi ya bayyana a fuskarta, hannunsa ya zare sannan yai gyaran murya yace “Da alama batada karfi ne shiyasa ta kusa faduwa.�?
Iman tai dariya tace “Ah to mutum kullum jiya iyau ai dole ya fadi.�?
Nan suka shiga ciki Ibty tana yima Iman rada na masifa a kunne.
Zama yai kafin Umma ta fito suka gaisa, farinciki ne a fuskarta sosai tace “Yanzu shine zakuzo Ibty bazaki sanar min na shirya tarbar siriki ba?�?
Kallanshi tai tare damai alama ya taimaka yai magana, kai ya kauda yanaji Umma na cewa “Kedai wlh naga randa zaki daina wannan zurfin ciki? Da kunzo bama nan kuma fa?�? Ibty ta sake kallansa kamar mai shirin kuka, daurewa tai tana neman abin cewa taji yace “Ninace karta fada saboda banasan daura muku wahala.�?
Wani irin dadi ne ya kamata dan da ta dauka bazai kula ba, nan aka kawomai juice da ruwa, itakam tana makale kusa da Ummanta.
Iman ta fita da sauri dan sanar da Yaya Bilkisu.
Umar na mimike a falo yana kallan TV yanayi yanacin dubulan din ta na gara, dama duk sanda zai zauna a falo to fa ita sai dai ta koma daki, haka ya kafa mata doka dan yace ganinta kusa dashi tasar mai zuciya yake.
Iman kam cikin zumudi tana shiga falan cikin daga murya tace “Yaya Bilkisu kizo ku gaisa da mijin Yaya Ibty, sunzo tare yanzun nan.�?
Ai garin durowa daga kan kujera baisan sanda ya fado ba, mikewa yai da sauri ya matso kusa da Iman yace “Da gaske?�?
Kallansa tai cikin mamakin yanda ya fado, badai haryanzu bai hakura ba?
Bilkisu ce ta turo keke tace “Iman da gaske?�?
Jikin Iman ne yai sanyi dan idanun Umar kadai zaka kalla kasan a rikice yake, daki ya koma ya canza kaya ya dau turare ya fefesa, sukam tare suka fito bayan Bilkisu ta rufa mayafi.
Comb ya dauka yana taje kansa yana wakar Babe ina kwana yanayi yana dan takawa. Fitowa yai yana cewa “Da alama daga nan bina zatai muyi wucewarmu.�?
Falon ya nufa, suna zaune duka anata hira, yana isa yai sallama, gaban Ibty ne ya fadi da sauri ta kalli Aminu. Shima kallanta yai tare da yi mata magana mara sauri yace “Uwar tsoro.�?
Baki tadan turo tare da dakewa ta dauke kai daga kan kofar ta maidashi kan Yaya dake kusa da ita.
Umar na shigowa idanunsa akan Ibty suka sauka, gani yai kamar ta kara wani irin kyau, kaunarta ce ke kara mamayemai zuciya, ji yake kamar ya mamake mutanen falan ya karaso ya rungume ta jikinsa.
Muryar Aminu ce ta katseshi wanda yana zaune yana kallan irin kallan dayake ma Ibty.
“Malan Umar ashe kana gida?”wani irin mugun kallon tsana ya makawa Aminu, shikam duk duniya ba wanda ya tsana sama da mutumin nan, kallansa yake yana wani huci, Aminu ya kalleshi yana daga zaune ya mika mai hannu.
Umar a ransa yace badai nufinsa na karaso na mika mai hannu ba?
Kallan Umma yai wacce itama take kallansa, kamar zaiyi ihu haka ya karaso ya mikawa Aminu hannu, matse hannun Aminu yai iya karfinsa, haka ya kalleshi yace “Karfi kakeji ne?�?
Sakeshi yai cikin takaici, Umma ta koma ciki dan dama ta sake fitowa ne jin Bilkisu ta iso.
Umar ya sake kallan Ibty yace “Ibty?�?
Dan kallansa tai sama sama tace “Ya Umar ina wuni?�?
Yanda ta gaisheshin ya bashi mamaki kamar irin taga wanda bata sani ba a waje?
Kasa amsawa yai sai ido daya kafeta dashi…�?

{Nikam na lalabo na fito dan na sha ruwa na koma ina tsoron kar a hada dani a makure}
3/3/22, 16:14 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

23⛹🏻‍♀�?

Su Islam an dawo bayan sunci abinci sunyi sallah ta zauna dasu ta koya musu homework, suna zaune tana dubawa ko sunyi daidai ya leko falan, dan yana zaune a falanshi yaji shirunsu yayi yawa. Shine ya leko yaga ko harsun kwanta ne.
Ganinta zaune tana dudubawa tana sake musu gyara yasa yai shiru tare da dan jingina da bango yana kallansu, shifa ko homework in sukace anbasu ce musu yake bashida lokaci suje suyi da kansu, shiyasa shi sam baisan ma me suke a skul ba, sai jarabawa tazo in aka kawo result basuyi kokari ba ya hausu da fada. Kallansu yake sosai cikin tsananin sha'awa abinda ya sake birgeshi sam babu alamar bacin rai a fuskarta in bash gane ba sake koya musu take.
Jin kamar ana kallansu yasa tadan juyo, ganin tana kokarin juyowa yasa yai saurin dagawa daga jikin bangon yana neman wayancewa, hannayensa yadan harde tare dayin gyaran murya yace "ku cigaba, dama naji shiru ne na leko inga ko sun kwanta ne."
Bata amsa ba sai dai idanunta na kanshi, haka kawai ta kasa yakice kalaman daya fada mata a ranta.
Islam cikin jin dadi ta dau book dinta ta nufeshi tace "Dady kalla kagani, wannan ne kawai banyi daidai ba shima yanzun nan zan gyara." Tai maganar cikin tsananin farinciki.
Murmushi yai tare da shafan saman kanta yace "Lalai Aunty ta iya koyarwa ko?"
Kai ta daga cikin jin dadi, yace "wannan kokarin dole nayi kyauta, tunda akwai sauran time kafin ai bacci ko muje dominos?" Ai nan Ilham ma ta taso tana tsalle, suka hau murna suna eh Dady.
Kallan Ibty yai yace "In a shirye kike muje?"
Cikin mamaki tace "Harda ni?"
Yace "Keda kikai koyarwa ai dole harda ke."
Dan murmushi tai sannan ta mike ta shiga daki, fuskarta ta gyara ta daura dankwali sannan ta sa mayafi, kayan lefenta ta dauko wani akwati ta dinga duba turaruka, jin kamshin wani yafi wanda take amfani dashi yasa ta dauko ta fefesa, dan dole ko kadan kadan ne ta fara jawo hankalin mijinta kanta.
Tare suka fito sun rike hannunta, bayan mota ta bude musu suka shiga sannan ta shiga gaba itama ta zauna. Kamshin turaren ta sosai yamai dadi, wanda harsai daya dan kalleta. Zama tai fuskarta haryanzu ba a sake kamar yanda ta saba ba, yana jinsu tanata hira dasu Islam shidai yai shiru dan ko wannan fitar saboda ita yayishi, yana fatan zai wanke laifinsa ta haka, shifa raini ne bayaso da alama ta kula yana neman bata hakuri ne shiyasa take dadaga mai kai.
Sun isa ya kalleta bayan yayi parking ganin bata da alamar fitowa, kallansu Islam yai yace "Muje?"
Nan suka fito suna murna, Ibty kam datake jira yace suje kawai taga sun fara tafiya, badai ta wuce gona da iri ba?
Fitowa tai itama tabi bayansu, ita datake neman karkato hankalinsa kanta in tun yanzu aka bangare ai ansamu matsala.
A ciki sai daya fara order sannan ya juyo yace "Akwai abinda kikeso?" Murmushi tadanyi tace "Kome aka siya yayi." A zahiri bata taba zuwa shagon ba, batasan ya abinsu yake ba, kartaje garin salo ta kwafsa shiyasa ma bata soma iyayi ba, dan Abba haka kawai bazai kawo su nan ya kashe kudinsa ba.
Sai da aka gama hada musu suka hada da ice cream sannan suka fito, inka gansu abin sha'awa, haka suka shiga mota suka koma gida.
*****
Hajiya kam tunda taji alamun fitar motarsu take leke ta gate, ina suka je bayan magriban nan? Bakin cikin duniya ya isheta da ta dauka shi kadai ne ya fita sai dai data tambayi Bala yace mata dukansu ne, sai suntiri take a tsakar gidan, jitai gwiwowinta sun fara amsawa, jingina tai da jikin gate din tana dan sake lekawa, jin alamun Bala zai bude gate yasa ta dan leko kanta tana lekensu.
Ibty dake zaune gaban mota ne idanunta yakai jikin gate din, mamaki ne ya kamata ganin ta hango kan mutum yana leke saboda fitilar motar daya kuna. Lalai matarnan takai makura gun sa ido, kauda kai tai kamar bata ganta ba ta juyo tanawa su Islam magana.
Hajiya ta koma ciki tai kwafa cikin tsananin kunar rai, wato Aminu baiji abinda tacemai ba kenan ko? Lalai yarinyarnan anyi tsinaniya tunda har ta iya wanke laifinta a kwana daya, sai dai intasan wata batasan wata ba, ta tabbatar da abinda malam yace mata inhar ta bari yarinyar nan ta shiga ran Aminu to fa ta shirya barin gidan, yanzu kam taga alama sarai, tunda dai gashi kiri kiri ta sanar dashi abu amma a kwana daya ya canza.
Komawa ciki tai hankalinta duk ya tashi, hangota take a cikin rumbum abinci tana kwance tana kyarmar sanyi.
A zabure ta mike tsaye tabbas bazata taba sabuwa ba.

*******
A falan Dady suka zauna, Ibty ta bude kwalayen ta dauko cup na shan juice din sannan ta kalleshi tace "Ya Aminu sauko."
Kallan mamaki ya mata yace "In sauko?"
Ta kalli su Islam tace "Eh mana, gwara ka sauko aci gaba daya."
Tab shi bayan Baffansa akwai wanda yakecin abinci dashi ne? Sai matarsa data rasu.
Ibtu ce ta katseshi jin tana cewa "Ilham matso nan, kinga Dady zai zauna agun."
Kallan yaran yai sannan ya kalleta, kamar yace bazai sauko ba sai dai kar yaransa suji ba dadi yasa ya sauko fuskarsa a daure sosai.
Gutsira tai ta mikawa yaran sannan ta turamai wani gabansa, hannu yasa ya dauka tare da jawo wayarsa yana daddanawa, fuskarnan a hade sosai yakeci kai kace cin dole aka sakashi, yana gama ci ya mike ya wuce daki.
Sukam bayan sun gama ta gyara gun sannan sukai sallar isha’i kafin ta kai su daki ta musu addu’a suka kwanta.
*****
Dakinta ta koma ta dauko d’aya daga cikin kayan baccinta wani mai shara shara, ita kanta kunyar ganin kayan tai da sauri ta maida ta sake dauko wani shima da sauri ta maida, jawo wata riga tai 'yar doguwa ce kadan bata kai gwiwa ba, kallan rigar tai tana tunanin ta yanda zata iya kwana da ita a gaban namijin da ko fuska bai sakar mata ba.
Dakewa tai ta saka rigar ta shafa turaruka sannan ta daura zani a kasa ta zura hijab. Dan itakam kunyar ma fita daga dakin take da wannan rigar.
Haka ta zauna a falo tai dan kallo tanata lissafin yanda zata shawo kan Aminu ya so ta, har internet ta shiga tanata dube dube, kunya da haushin kanta ne ya kamata tace “Wai duk yanda nakejin labarin soyayya a gidan amarya da ango ni nawa nice mai neman yanda zan sa a soni?�? Jitai idanunta sun ciko da kwalla nan gidan da zaman aurenta shine dahir dinta dole koma menene tayi. Haka ta mike ta duba su Islam sannan ta wuce dakin Aminu hannunta dauke da tire na tea data dafamai wanda yasha kayan kamshi.
Kwankwasa kofar tai daga ciki ya amsa sannan ta shiga da sallama, yana zaune yana duba abu a laptop dinsa ta karasa ta ajiye akan side bed dinsa, dagowa tai ta kalleshi tare da cewa “Aiki kake?�?
Tambayar tazomai a banbarakwai dan bai tabaji ta tambayeshi haka ba, kai ya daga sannan ta wuce ta inda take kwanciya, tunani ta fara ta yanda zata zare zanin ta kuma zare hijab gashi kwan wutar dakin a kunne.
Gaba daya gani tai bazata iya wannan abin kunyar ba, haka ta kwanta tadan ja bargo, daga cikin bargon ta dan zare zanin jikinta ta dan janye hijab din, shikam bai ma san tanayi ba, sai dai gaba daya hankalinsa na kanta. Ta hakura kenan? Da alama tunda dai yaga ta sauko. Ya zaiyi ya gane komai ya wuce?
Dan gyaran murya yai hankalinsa nakan laptop din yace “Me kike gani akan kije ziyara gida kafin ki koma school?�?
Sam ta manta shigarta ai cikin wani irin zumudi da yanayi ta yayi bargo ta juyo gaba dayanta tace “Gida?�?
Yanda tai maganar cikin zumudi yasa ya juyo ya kalleta, mamaki ne ya kamashi ganin shigar dake jikinta, gashi rigar irin mai hannun vest din nan ce, itakam sam ta manta ta sake kallanshi tace “Yaya da gaske?�?
Sake gyaran murya yai ya kasa sake kallanta yace “Eh ya kamata nima na gaishesu sannan su Ilham ma su je.�?
Wani irin dadi ne ya kamata, duk ta rikice tace “Yaya yaushe kake ganin ya kamata? Gobe? Ko jibi?�?
Juyowa yai jin lalai zumudin nata da gaske take, idanunsa ne suka sauka akan jikinta, da sauri ya dauke idanunsa.
Ganin yanayinsa yasa ta tuna shigar dake jikinta, da sauri taja bargo ta lulube jikinta sannan ta sulale a hankali ta kwanta, kunya duk ta gama kamata.
Haryayi shiru sai taji yace “Badai cewa zakiyi kunya kike bako?�?
Juyowa tai haryanzu tana cikin bargo tace “Allah na manta abinda ke jikina.�?
Wani murmushi yai wanda iya kacinsa lebensa yace “Hmm.�?
Da sauri tace “Allah dagaske na manta.�?
Kallanta yai yace “Taya mutum zaisa abinda yake kunya? Kedai kawai kice kinsa dan kija ra’ayina.�?
Haushi ne ya turnuketa, ta kalleshi cikin dan sakalci tace “Koma hakan ne Ya Aminu ba sai kai shiru ba? Sai ka fada?�?
Duk yanda yaso ya dane kasawa yai baisan sanda yai wata ‘yar karamar dariya ba, kallan mamaki tamai, bai bi takan dariyar dayai ba yace “Yanzu da na fada kinji kunya?�?
Ta dan shige bargo tare da dan fito da idanunta kadai tace “Allah ba sai kai shiru ba? Kuma ni wlh na manta, amma sai dai ka fadan sannan.�?
Kai yadan girgiza yana murmushi yace “Ranar juma’a insun dawo daga skul zan samu nazo lokacin sallah sai na kaiku can na gaishesu, in yaso sai na barku sai dare.�?
Dadi ne ya kara kamata tadan bubuga kafa ta cikin bargo tare da juya baya tana murna, zataje taga Ummanta, dasu Abba.
Aminu ganin yanda taketa murna yasa wani abu yazomai, ta gefen ido ya kalleta yace “Kin tabbatar ya kamata kiyi murna sosai?�?
Sake juyowa tai cikin mamaki take kallansa dan bata gane me yake nufi ba.
Kafada yadan daga yace “Dama ina jiye miki ne karkije wannan mutumin ya dan balla kafar da kike murnar da ita.�?
Sam ta manta da Umar, yanayinta ne ya canja ya dan guntse dariyarsa fuskarsa a daure yace “Gaki da tsoro? Ni karma yaje yayiwa su Ilham illa.�?
Kifta ido tai, lalai tasan haukan Umar tsaf zai nakasata, shi Aminu da alama wasa ya dauki abin ita kuwa tasan tsaf zai aikata.
Hannu tasa tadan riko hannunsa, hakan yasa ya kalleta sosai, cikin dan damuwa tace “Yaya dan Allah muje tare ka zauna acan bar lokacin da zamu dawo.�?
Yace “Ni? Inje gidan surukaina na zauna har sai kin gama yini sannan na daukoki?�?
Kai ta daga da sauri, kallanta yai sosai yace “A ina aka taba haka? Kuma ko an taba ma cemiki nai ni zan iya? Duk tsoron ne?�?
Tadan hadiyi yawon bakinta tace “Bawai tsoro bane, gudun magana ne.�?
Gudun magana?
Ta daga kai tace “Kaga mijin yayata ne bai kamata ayi husuma ba.�?
“Ohhhhh! Husuma ko?�?

⛹🏻‍♀�?
3/3/22, 16:14 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

24
Ganin yayi shiru yasa tai shiru tana tunani, juyawa tai cikin ranta tana cewa “In har na danne tsoron tsohuwar nan dan me zan zauna Umar na ban tsoro?�? Jan idanunsa ta tuno da yanda yake tsareta a daki, hala tai ta tunane tunane har bacci ya dauketa. A bangaren Aminu kuwa abinda ya shekara biyar baiji ba shine ya taso mai yau, dan wata irin muguwar sha’awa ce ta rufeshi, haka yai ta juyi shima kafin baccin ya daukeshi.

****
Ran Juma’a suna tafiya school ta hau aikin gida tai wanka ta dauko wani dankakareren lace mai tsada ta saka, dinkin an mata shi mai kyau dan asali dama shi ta ajiye zata saka washe garin daurin aure to sai kuma aka samu matsala, tayi kwalliya sosai dan dama ba laifi ta iya kwalliya, Ibty ta fito das da ita kai kace ranar auranta ne, turaren wuta ta kunna wanda ya kara kama kayanta.
Sha biyu da rabi yara suka dawo daga skul nan suka ci abinci sannan ta musu wanka suma ta dauko kaya iri daya mai kyau ta saka suma lace sukasha an musu doguwar riga, tana daura musu dankwalli sukaji alamar bude gate. Wani irin dadi ne ya kamata yau dai xata gida taga Ummanta.
Fitowa falo sukai, shi kuma ya shigo kenan hannunsa dauke da leda, tunda ta shigo falan yake kallanta a sace, tayi kyau sosai da sosai gashi tun ranar da sha’awa ta tasomai abu kadan kesa yaji yana bukatarta. Har ta karaso yana tsaye yana dan satar kallanta, cikin murmushi tace “Sannu da dawowa.�? Tai maganar tare da sa hannu tana kokarin amsar ledar, hannunsu ne ya tabu a hankali ta dago ta kalleshi, shikam kasa janye hannunsa yai yanda ya saba, amsar ledar tai sannan ta juya ciki, ajiyewa tai a kitchen sannan ta dauko abincinsa, haka kawai takejin tunda ta tabashi bai janye hannunsa ba yanda ya saba ba ta samu kanta da murmushi a cikin ranta.
Ajiyemai tai a dinning sannan ta nufi dakinsa dan sanar dashi, ya cire rigarsa kenan tai sallama, juyowa yai ya kalleta, ta dauka zai maida rigar sai taga ya karasa cire ta daga jikinsa tare da kallanta. Ibty tai kasa dakai tare da yin shiru tana dan wasa da hannunta.
Sam batasan ya tako ba sai ganin kafafunsa tai yana nufo ta, gabanta ne yadan fadi kadan bata matsa ba haka kuma bata dago ba, daf ya matso da ita tana juyo numfashinsa, hannayenta tadan matse saboda yanda ta tsinci kanta, idanunta ta lumshe dan ta dauka rumgumeta zaiyi, ganin jikinsu ya hadu da juna, hannu yasa bayan ya matsota suna gogan juna, kofar data bari a bude yasa hannu ya rufe, sannan yadan kalleta, gefen kunnenta ya matso yace “A dinga rufe kofa saboda akwai yara a gidan, in kika shigo kika manta dasu su kuma suka taho nan fa? So kike suka babansu a haka?�?
A hankali tadan bude idanta daya tare da dan rike kunnenta tace “Sorry!�?
Matsawa yai daga jikinta sannan ya bude wardrobe ya dauko wasu kayan, tace “Dama kiranka nazoyi kazo kaci abinci.�?
Kai ya daga alamar to, juyawa tai kamar zata tafi sai taji yace “Duk kwalliya da zumudin zuwa gidan ne?�?
Tadan rufe fuska saboda kunya, murmushi yai yadau towel ya nufi bandaki, haryaje zai shiga yace “In Umar yaga kwalliya kuma ya hanaki dawowa to.�?
Yanayin fuskarta ne ya canza, kamar mai shirin kuka tace “Yaya baza dai ka daina ba ko?�?
Juyowa yai ya kalleta yace “Sai randa kika bar tsoron sa.�?
Tana kokarin magana taga ya shigo toilet baki tadan turo kafin tadan rufe fuskarta alamar kunya sannan ta fita.
Aminu kam a toilet shiru yai yana hadiyar wani abu, shikam meke damunsa? Taya zai bari sha’awar yarinya ta fara damunsa? Dan tabbas dazu rungumeta yaso yi ya wayance, iska yadan furzar lalai inya biya zuciyarsa tofa zai gabza abin kunya.
Haka ya fito yasa yadi fari sun mai kyau sosai sannan ya fito falo. A waje ya jiyo muryarsu da alama su Ilham ana keke ne, zama yai ya bude abincin, kamshin butter ne ya dan bigi hancinsa, vegetable soup ne wanda akai amfani da butter a maimakon mai, abinci yasa yana ci yana dan murmushi dan yana juyo hirarsu daga waje. Ba shakka Ibty tasan takan yara, har mamakin yanda ta shaku dasu daga zuwa yakeyi.
Yana gamawa suna shigowa, nan ta kwashe kwanuka suka kara gyarawa kafin su fito. Suna shiga tadan kalli bangaren Hajiya sannab ta tuno leken dataga tanayi ranar, cikin murmushi tace �? Yaya ko zamu shiga muyima Hajiya barka da juma’a kafin mu wuce.�?
Cikin jin dadi ya kalleta, wanda har ita kanta ta fahimci yaji dadin maganarta, nan yai parking a waje suka fito.
Hajiya kam tana kishingide a falo takaici duk ya isheta, tana juyo muryarsu Islam dazu suna wasa, yau kwana biyu kenan ko keyarsu bata gani ba.
Wata ajiyar zuciya ta bakin ciki ta saki sanda taji ana bude gate din gidan. Mamaki ne ya kamata dataji kwankwasa kofa yanzu, kafin ta mike har tajuyo murya da gudunsu Ilham.
Da sauri ta bude kofar ashe ba tare zasu fita ba? Da alama kawo mata su zaiyi ya fita. Kofa ta bude da sauri tana dariya tare da tafa hannu.
Da gudu suka karaso suka rungumeta, dadi ne ya kamata. Jin alamun bude kofa yasa tadan dago, Aminu ne ya shigo, haba wani irin dadi ya sake rufeta, ta bude baki zatai magana kawai taga Ibty ta biyo bayanshi.
Yanayin fuskarta ne ya canza lokaci daya, daurewa tai ta fara lale lale.
Nan suka koma ciki, suma suka karaso, Aminu ne ya zauna a kasa daga gefe, ga mamakinsa yaga Ibty ta karaso ta zauna gefensa, Hajiya ta kalleta ta dau wanka, wata tsana ce ta sake turnuke ta, lalai itakam mutuwa ta cuceta, banda mutuwa ina Aminu ya isa ya kawo mata wannan karamar karuwar?
Gaisheta sukai ta amsa, tana kallan Ibty tace “Amarya irin wannan kwalliya? Ina za’a haka?�?
Aminu yai dan murmushi yace “Gida zata ta ziyara saboda makaranta da zata koma.�?
Takaicin amsarsa ne ya kamata, wato harya fara bada amsa a maimakon ta? Ko batada baki ne?
Kallansu Islam yai yace “Ku tashi mu wuce saboda inaso na saukeku na wuce gun aiki.�?
Hajiya na kokarin magana taga harsun mike, Ibty ce ta kalleta tace “Hajiya mu mun wuce sai anjima.�?
Murmushin yake tai sannan ta rakosu, haka tana tsaye a kofa taga sun shiga mota, suna tafiya ta kwararo wani dogon ashar ta zabgawa Ibtisam tare da maimaita kalamanta, Hajiya mu mun wuce? Ko ubanwa ya tambayeta oho. Da karfi ta makonkofa sannan ta koma ciki, zama tai ta baza tagumi tana tunani kodai ta canza malami ne? Dan da alama wannan malamin ya fara sanyi, ba abinda yai aiki tun bayan auran nan.

********
A kofar gidansu yai parking, mamaki ne ya kamata ganin ya bude boat ya dauko ledoji guda biyu, karasowa tai tace “Yaya na menene?�?
Mika mata daya yai yace “Haka ake zuwa gidan da ba komai?�?
Amsa tai ta bude, turaruka ne ne da irin body wash din nan na kwali, ya mika mata daya shi kuma kayan kwalliya ne, yace “Kya rabawa su Iman ko?�?
Tayi mamakin jin yanda ya rike sunan Iman, kallansa tai tare da cewa “Angode Allah ya kara budi, Yaya ni sai yaushe zaka kira nawa sunan?�?
Boat din ya maida ya rufe yace “Randa kika bar tsoro?�? Ya kamo hannun Ilham sannan ya mata alama dakai akan su shiga.
Baki tadan turo tanasan yin magana gashi a gaban yara ne, ganin yanda ta maida maganarta yasa yadanyi murmushi kasa kasa.
Shiga sukai, ba kowa a harabar gidan, har saida suka isa ciki.
Kwankwasawa tai daga cikin aka amsa sannan Iman ta karaso ta bude, idanu ta zaro ta saki wani wawan ihu tare da rungumo Ibty iya karfinta, sam Ibty bata kawo irin rungumar nan ba ga hannunta dauke da ledoji, baya tai tana neman faduwa, da sauri Aminu yasa hannu daya ya taro bayanta, Iman sai a lokacin ta kula da abinda ta aikata, saketa tai tana dariya tare da yin alamun kunya na Aminu tace “Yaya kayi hakuri ai bankula tare kuke ba.�?
Ibty ta juyo ta kalleshi a hankali wani murmushi ya bayyana a fuskarta, hannunsa ya zare sannan yai gyaran murya yace “Da alama batada karfi ne shiyasa ta kusa faduwa.�?
Iman tai dariya tace “Ah to mutum kullum jiya iyau ai dole ya fadi.�?
Nan suka shiga ciki Ibty tana yima Iman rada na masifa a kunne.
Zama yai kafin Umma ta fito suka gaisa, farinciki ne a fuskarta sosai tace “Yanzu shine zakuzo Ibty bazaki sanar min na shirya tarbar siriki ba?�?
Kallanshi tai tare damai alama ya taimaka yai magana, kai ya kauda yanaji Umma na cewa “Kedai wlh naga randa zaki daina wannan zurfin ciki? Da kunzo bama nan kuma fa?�? Ibty ta sake kallansa kamar mai shirin kuka, daurewa tai tana neman abin cewa taji yace “Ninace karta fada saboda banasan daura muku wahala.�?
Wani irin dadi ne ya kamata dan da ta dauka bazai kula ba, nan aka kawomai juice da ruwa, itakam tana makale kusa da Ummanta.
Iman ta fita da sauri dan sanar da Yaya Bilkisu.
Umar na mimike a falo yana kallan TV yanayi yanacin dubulan din ta na gara, dama duk sanda zai zauna a falo to fa ita sai dai ta koma daki, haka ya kafa mata doka dan yace ganinta kusa dashi tasar mai zuciya yake.
Iman kam cikin zumudi tana shiga falan cikin daga murya tace “Yaya Bilkisu kizo ku gaisa da mijin Yaya Ibty, sunzo tare yanzun nan.�?
Ai garin durowa daga kan kujera baisan sanda ya fado ba, mikewa yai da sauri ya matso kusa da Iman yace “Da gaske?�?
Kallansa tai cikin mamakin yanda ya fado, badai haryanzu bai hakura ba?
Bilkisu ce ta turo keke tace “Iman da gaske?�?
Jikin Iman ne yai sanyi dan idanun Umar kadai zaka kalla kasan a rikice yake, daki ya koma ya canza kaya ya dau turare ya fefesa, sukam tare suka fito bayan Bilkisu ta rufa mayafi.
Comb ya dauka yana taje kansa yana wakar Babe ina kwana yanayi yana dan takawa. Fitowa yai yana cewa “Da alama daga nan bina zatai muyi wucewarmu.�?
Falon ya nufa, suna zaune duka anata hira, yana isa yai sallama, gaban Ibty ne ya fadi da sauri ta kalli Aminu. Shima kallanta yai tare da yi mata magana mara sauri yace “Uwar tsoro.�?
Baki tadan turo tare da dakewa ta dauke kai daga kan kofar ta maidashi kan Yaya dake kusa da ita.
Umar na shigowa idanunsa akan Ibty suka sauka, gani yai kamar ta kara wani irin kyau, kaunarta ce ke kara mamayemai zuciya, ji yake kamar ya mamake mutanen falan ya karaso ya rungume ta jikinsa.
Muryar Aminu ce ta katseshi wanda yana zaune yana kallan irin kallan dayake ma Ibty.
“Malan Umar ashe kana gida?”wani irin mugun kallon tsana ya makawa Aminu, shikam duk duniya ba wanda ya tsana sama da mutumin nan, kallansa yake yana wani huci, Aminu ya kalleshi yana daga zaune ya mika mai hannu.
Umar a ransa yace badai nufinsa na karaso na mika mai hannu ba?
Kallan Umma yai wacce itama take kallansa, kamar zaiyi ihu haka ya karaso ya mikawa Aminu hannu, matse hannun Aminu yai iya karfinsa, haka ya kalleshi yace “Karfi kakeji ne?�?
Sakeshi yai cikin takaici, Umma ta koma ciki dan dama ta sake fitowa ne jin Bilkisu ta iso.
Umar ya sake kallan Ibty yace “Ibty?�?
Dan kallansa tai sama sama tace “Ya Umar ina wuni?�?
Yanda ta gaisheshin ya bashi mamaki kamar irin taga wanda bata sani ba a waje?
Kasa amsawa yai sai ido daya kafeta dashi…�?

{Nikam na lalabo na fito dan na sha ruwa na koma ina tsoron kar a hada dani a makure}
3/3/22, 16:52 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

25
Ibty tadan dago kadan ganin idan Umar kyar a kanta yasa tai saurin kallan Aminu, shikam yana gani zata juyo ya dauke kansa da sauri tare da kallan Umar yace “Zauna mana? Tunda ka gama nuna karfin?�?
Ibty ta kalli Bilkisu tace “Yaya mu shiga daki ko?�?
Tai maganar tare da mikewa, tana neman tura keken Bilkisu. Muryar Aminu taji yace “Ranki ya dade inaga zan wuce.�?
Gabanta ne yai wani irin faduwa ta juyo da sauri, kalmar ranki ya dade da zancen tafiyar ne suka sake dawo mata, cikin dauriya ta kalleshi tare da san shagwabe fuska tana mai alama daya taimaka karya tafi.
Umar ganin yanda ta shagwabe fuska tana turamai alamun da kana gani kasan tsakaninsu ne yasa ya daki tabirun gabansa da kafarsa, uban zafin da ya ziyarci kafarsa ne yasa yadan ciji lebe, Aminu ya kalleshi yace “Jarumi badai bigewa kai ba ko?�?
Wani mugun kallo yamai yace “Ko bigewa nai wannan karamin bugun zai min illa ne? Ko ba ka kula a gajiyar karfi na nake ba?�?
Kai yadan jinjina tare da daukan bottle din ruwa daya fadi kasa saboda bugar table din dayai, nunamai robar yai sannan yace “Hakan nada kyau ai, in mutum nada karfi ya nuna a gani.�?
Ibty kam tunda taga yanda ya bigi table din ta kara tsorata, zuciyarta sai dukan uku uku take, Bilkisu kam gaba daya kanta ta sadda kasa, idanunta suka ciciko da kwalla.
Itakam Iman wani irin kululun takaici ne ya kamata, ganin yanda Aminu ya mai magana yasa tai murmushin jin dadi.
Ibty ta kalli Aminu da sauri ta girgiza mai kai alamar ya taimaka karya tafi, Aminu ya kalli Iman yace “Iman wannan yayar taki da alama batasan nai nisa, duk zumudin san tazo gida da alama bataso taga na tafi na barta.�?
Iman cikin jin dadi tai dariya tace “Yaya ai da alama ka gama shagwabata tunda ta zauna ko minti daya na kula batayi sai ta kalleka.�?
Mamakin yanda Aminu mai ji da girma yau yake biyewa Iman suna irin wannan hirar ne ya kamata, Umar kam yazo wuya, ga azabar da kafarsa ke masa ga wani uban kishi dake nukurkusarsa, dan shi Kansa tunda ya shigo yaga yanda take kallan Aminu abin ya tsayamai a wuya.
Kallan Ibty yai idanunsa sunyi jaa sosai yace “Zuciyar mace ai batada amana, yanzu sai tai kicin kicin tace kai takeso anjima dan yaudara sai ta auri wani, shima daga ta gama yayinsa sai kaga tana neman tace ya saketa.�?
Kowa na falan ya fahimci inda kalamansa suka nufa, Ibty ta kalli Aminu wanda ya dauke kai da alama yanzu bazai tanka ba kenan, hannunta tadan rike cikin dauriya tana murmushi tace “Ya Umar kenan, ai in kaga mace ta canza ra’ayi to tanada dalilinta, sannan wasu mazan auren in Allah ya hadaka dasu ko na minti daya bakasan ku rabu balle har ka fara tunanin wani saki.�?
Aminu yaji dadin kalamanta sosai, kallanta kadan yai tadanyi raurau da ido tana jiran taga yabo a idansa, gani tai ya dau waya yana dan dannawa.
Kalaman Ibty sunyi matukar dukan zuciyar Umar, kafeta yai da ido yana sake jiyo kalaman a cikin ransa, yana ganin sanda tai raurau tanayiwa Aminu wani sign, ji yake zuciyarsa kamar zata fito, idanunsa suka kada sosai sukai jaa ji yake kamar ya tashi ya shaketa ta sake maimaita kalamanta a falan nan.
Aminu yana dana waya yana kallan yanayin Umar, jikinshi ya bashi tabbas inba kowa a falan wannan ba abinda bazai iya aikatawa Ibty ba, anya zainiya barinta a gidan nan kuwa?
Kallanta yai haryanzu kallansa take da alama batama kula da kallan da Umar ke mata ba “Hajiya in zuba juice din da kaina ne?�?
Abinda taji yace kenan, mamaki ne ya kamata ta sake maimaita kalaman a ranta, takowa tai ta karaso gun ta daga kwalin juice din daya fadi akan table din ta bude sannan ta zuba a cup tare da mikamai, hannu yasa ya amsa sannan yace “Thanks.�?
Tana kokarin tashi yadan mata alama data tsaya, tsayawa tai yana sha yana tunanin abinda ya kamata yai, dan tabbas barinta anan ba karamin hadari bane kuma bai kamata ya dauketa daga zuwa ba, shi kuma bazai iya dadewa a gidan surukai ba.
Harya shanye bai gama tsaida shawara ba, cup din ya mika mata sannan ya kalli Umar yace “Haka take ko a gida tafiso sai na gama abu kafin ta mike.�?
Ibty mamakin abinda Aminu yake aikatawa a gidansu yau take, anya Aminun data sanine kuwa? Umar kam bai ko tankashi ba idanunsa kyar akan Ibty.
“In ba abinda kake ko zamu fita tare? Mu basu guri suyi hira?�?
Idanu Ibty ta zare da sauri tace “A’a Yaya gwara ka tafi kai kadai.�? Sam batasan sanda ta fadi hakan ba dan itakam ta tabbatar Umar zai iya yiwa Aminu illa in suka fita tare mutumin da kallo aka mata yake neman duka balle?
Ganin yanda kowa ya kalleta ne yasa ta fahimci ta kwafsa, daurewa tai tace “Ahh naji dama kace zaka koma gun aiki ne to karka makara.�?
Ya fahimci abinda take shakka sai dai shima abinda yake shakka kenan, yana tsoron barinta a gida da wannan mutumin.
Umar ya kalleta cikin wata murya yace “Nine bakyasan na fita da mijinki ko me?�?
Tadan maida kai kasa dan batasan me zatace ba, Aminu ya kalleta tare da danyi mata karamin murmushi, itakam batasan wannan fitar.
Umar ya kalla yace “Muje?�?
Da Yayi niyar kin zuwa sai dai yanda Ibty tai magana yasa yaji ma dole ya fita, kodan ya nunawa Aminu danyan jini ne.
Mikewa yai yace “Muje, dan dama ba abinda nake.�?
Ibty kamar zatai kuma haka ta bisu da kallo har suka fita, ko mikewa ta kasayi daga inda take.
Mota suka shiga Aminu ya ja suka fara tafiya, idanu Umaf yadan lumshe kadan dan wani dadi daya ziyarceshi daya tuna inda ya zauna anan fa gun Ibty ta zauna, inama shida ita ne suke tafiya a motarnan? Tunowa da Aminu dayai ne yasa ya bude idanunsa cikin bacin rai.
Murmushi yaga Aminu yadanyi, murtuke fuska yai tare da kallan gefe.
“Ango ango! Ranar aure ashe kaine kaba motata karfi.�?
Umar ya gane mai yake nufi takaici ya hanashi amsawa, shiru ne yadan sake ratsawa, can Umar yace “Tunda kasan abinda ke faruwa meyasa zakai sata? Da girman ka da komai baka kunyar abinda ka aikata?�?
Bai kalleshi ba yace �? Sata?�?
Umar cikin hargagi da masifa wanda dama kiris yake jira yace “Sata mana! Kana tunanin dakai da masu shiga gidan mutane ko masu yankan aljihu suna daukan kudin mutane kunada banbanci ne?�?
Kai ya jinjina kafin yace “Kumafa hakane.�?
Ai nan Umar ya kara hawa yace “Banda asarar zuciya da rashin imani ka taradda mutum nasan abu tun yana karami ka sace? Sannan dan asara ma kai ba yaro karami ba? Kai ko kunyar abun bakayi? A haka a fuska kamar mai hankali da sanin ya kamata amma a boye kai babban dakiki ne mugu azallumi…�?..�?
Karar burkin da aka taka da karfi ne yasa Umar ya kalleshi dan tabbas ya dauka hatsari zasuyi, kallansa Aminu yai yace “Right? Dakiki? Mugu ko?�?
Umar cikin kumfar baki yace “Eh mugu azzalumi mara imani, har duniya ta nade wallahi bazan yafe maka ba, kuma Ibty ce ko kanaso ko bakaso sai ta dawo hanuna.�?
Kai Aminu ya jinjina yace “Very good.�?
Jan mota yai da karfin gaske, hakan yasa Umar yace “Meye hakan kake?�?
Aminu bai kula shi ba tuki kawai yake, nanfa ran Umar ya kara baci yace “Meye haka? Kasan Allah karka kaini bango zan iya aikata abinda baka taba tunani ba?�?
Bashida alamar kulashi jan mota kawai yake, Umar gani yai sun wuce mariri sun nufi hanyar Wudil.
Yanzu kam ya fara jan jinin jikinsa gashi inyai kwakwaran abu zasu iya afkawa hatsari. Bai tsaya ba sai da suka shiga Wudil, da sauri Umar ya fito daga motar ya kalleshi yace “Kai dalla mahaukacin ina ne? Bakada hankali ne zaka ja mota ka kawomu harnan?�?
Mamaki ne ya kamashi ganin motar tana neman juyawa, cikin sauri ya rike window yace “Tsaya tsaya! Ina zaka? Ko hamsin ban fito da ita ba.�?
Hannu Aminu yasa a aljihu ya dauko 500 ya sa akan hannunsa yace “Wai da zalunci da dakikantar nake so ka tabbatar inadashi.�?
Kallan dari biyar din yai yana neman yin magana kawai yaga Aminu yayi gaba. Idanu ya zaro ga kafarsa haryanzu ciwo take mai, wani irin ihu yasa tare da naushin iska yace “Sai naci********** wallahi sai naga uban daya tsayama a duniyan nan.�?
Ibty kam tunda suka tafi tanaji Iman tanata kokarin jansu da hira sai dai daga Ibty har Bilkisu dukansu abin duniya ya taru ya musu yawa, gashi sai waya takewa Aminu taki shiga, itakam ta shiga uku, in aka karya Aminu fa? Sam tunani sun hanata ko sakewa tai, ji take dama batazo gidan nan ba daya fiye mata alkairi.
3/3/22, 18:16 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
26
Dukunkune dari biyar din yai cikin fishinya cillar da ita kasa, hannunsa yasa a aljihu ba komai a ciki dan ko wayarsa bai dauko ba, cikin hanzari ya sukunya yana san ya dauki kudi. Me zai gani? Yara ya gani wanda basufi shekara shida ba sun falfala a guje suna dariya, ya daga zai bisy da gudu yaji wani uban zugi a kafarsa, da sauri ya tsaya tare da maida numfashi yadan matsa kafar dake mai ciwo kadan, yana kiran kwalla musu kira akan su dawo da kudin amma ina? Abinka da 'yan gari da suka shiga wani lungun nemansu yai sama da kasa ya rasa. Haka yaja kafarsa yadan jingina da wani shago a bakin titi yadan zauna akan wata kujera yana matsa kafarsa dake mai wani azaba, ga bakin cikin dake zuciyarsa, lalai Aminu ba karamin tsinane bane, wallahi sai ya koyawa mutumin nan hankali, tunda har kamar shi zai wulakanta, a dakeshi a hanashi kuka? An sace mai mata sannan ya kawoshi nan ya cillar? Banda tozarci da wulakanci?
Yanzu taya zai soma komawa gida? Tambayar data fara zuwa mai kenan, tagumi ya baza tare da sauke ajiyar zuciya.

******
Aminu kam kai tsaye gun aikinshi ya koma, sai daya nutsu a office sannan ya dauko wayarsa, kiran Ibty ya gani guda goma, haka kawai ya samu kansa da yin murmushi, kamar zai kira sai kuma ya ajiye wayar yana kallanta.
Ko minti biyar baiyi ba ta sake kira, yanzun ma yana kallan wayar harta katse, minti biyu bayan nan sak ga sako.
“Ya Aminu? Dan Allah karka bari Ya Umar ya nemi fada dakai? Wlh zuciya gareshi kuma yanada karfi sosai.�?
Fuska ya daure sosai kamar tana gabansa yadan kifa wayar yace “wato rago kika aura kenan?�?
Alamar wani sakon ne ya sake shigowa, juya wayar yai “Ya Aminu? Badai abinda ya sameka ko?�?
Sake kifa wayar yai yace “Tunda rago kika aura sai ki shirya ganina da ciwo ai.�?
Aikinsa ya cigaba yanayi yana tuno kalaman Umar, ba shakka kalamansa sun kaishi bango, baisan dalilinsa najin zafin kalaman nan sosai ba. Harzai kalleshi a gabansa ya dinga zancen wai yayi sata? To ko satar matar yai ai akalla dai yanzu matarsa ce.

{Nikam nace Aminuwa ko dai kishi ne🤪}

******
Ibty a gida sam ta kasa nutsuwa, Iman sai dariya take mata wai lalai san Ya Aminu ya mata yawa. Itakam Yaya Bilkisu bangarenta ta koma dan gaba daya zaman ya isheta, haka kawai ta samu zuciyarta da jin zafin Ibty, balle dataga tanata neman Aminu sai taji zuciyarta ba dadi, ita tana nan zaman auranta yaki dadi saboda Ibth amma gashi ita Ibtyn hankalinta a kwance ita da mijinta.
Iman ta dan matso kusa da Ibty tare da sake daukan wayarta tace “Yaya dan Allah nidai ina kamu, duk sanda zaki canza waya ki ban wannan.�?
Harararta tai tace “Ni dagani na dubo su Islam, haka kawai waya tun tana sabuwa za’a fara kamun ta?�?
Iman tana dariya tace “Wlh Yaya Ibty yau ke da Ya Aminu kunsa naji aure nakeso.�?
Juyowa Ibty tai da sauri takai mata dundu a baya, Iman tadan gantsare tarw da sosa gun tace “Me kuma nai?�?
“Nawa kike? Da zaki dinga maganar aure?�?
Ta kalli kanta tace “Lalai ma, to ko madai nawa nake yanzu kunsa naji aure nakeso, ni gaskiya ina gama secondary aure zanyi, nima yanzu bansan yaro irinsu Ya Umar wanda hankalinsu baya aiki daidai nafisan matashi wanda yasan me yakeyi irinsu Ya Aminu.�?
Sake kokarin kai mata dundu tai da sauri ta matsa tana dariya ta dan danna wayarta, mikewa zaune tai tace “Ibty meye hakan?�?
Hartakai kofa zata fita ta juyo tace “Ke nifa bansan rashin kunya, yanzu kuma menene?�?
Iman cikin dan mamaki tace “Meye wani Ya Aminu?�?
“To ba sunanshi bane?�?
Iman tadan bigi goshinta tace “Gaskiya wlh anbani kunya, da na dauka zuba love kuke meye wani Ya Aminu? Kamar wani Yayanki?�?
Harara Ibty ta maka mata tace “To ba yayan nawa bane? Sannan ke har wani sanin sunan daya kamata a sawa miji kikai?�?
Iman ta goge sunan tasa Bae sannan ta nuna mata tare da daga mata gira tace “Ya kikaga?�?
Juyawa tai ta fita da sauri tana girgiza kai, lalai Iman ta rika, wato harta san wani Bae? Gunsu Islam taje tasa suka dawo ciki ta zuba musu abinci sunaci ta koma sama.
Wayarta ta fizga daga hannun Iman sannan ta sake kiran Aminu, Iman tasa dariya tace “Wai tsoron me kike? Badai kina tunani Ya Aminu zai zauna a dakeshi ba?�?
Ibty ta zauna bakin gado tace “Kinsan Ya Umar kamar wani dan kwaya yake, shikam Ya Aminu ba ruwanshi banaso haukar wancan tasa wani abin ya sameshi.�?
Baki Iman ta bude tace “Inyeee? Lalai soyayya manya……�?
“Assalamu Alaikum�? muryar Aminu ce ta daki dodan kunnenta dan harta dauka bazai daga ba yanzun ma.
Iman ta turo kunnenta jikin wayar tace “Ya Aminu ina ka shiga? Matarka duk ta rikice……�?
Hankadata Ibty tai tare da saurin mikewa daga kan gadon tai waje.
Toilet ta shiga tasa key sannan tace “Inata kiranka.�?
“Inata ganin kiranki.�? Abinda yace mata kenan.
Tadan yi shiru tace “Shine baka dauka ba?�?
“Jira nake naga sanda zaki gaji da kira.�?
Dan baki ta turo kamar yana ganinta tace “Allah hakan ba dadi, ni ina nan inata nemanka kai kana jiran kaga sanda zan daina nemanka?�?
“Eh! Yanzun ma na daga ne dan na kula bazaki iya hakuri ba, sai kinga na daga.�?
Takaici ya kamata tace “Kuma menene na fada tunda kasan hakan ne?�?
“Wai gaskiyar ce ba’asan na fada ko me?�?
Tadan shagwabe fuska batai magana ba, “kunkuni kike?�?
“A’a nidai bance ba, kana ina?�?
“Gadan asibiti?�?
Ido ta zaro da sauri cikin tashin hankali tace “Gadan asibiti? Meya sameka?�?
“Mema ya sameni?�?
Kafafunta tadan bubuga cikin shagwaba tace “Yaya dan Allah ka daina zolayata, da gaske kana gadan asibiti?�?
“Badai ke a ganinki wannan yaran ya isa yamin dukan da zan kwanta a gadan asibiti ba?�?
“Tadan jingina da kofar toilet din tace “Kaine fa kace haka.�?
“Ke kuma uwar tsoro harkin yadda ko? Sannan ni me kika daukeni? Dan shekara sittin ko me?�?
“Allah nidai bance ba.�?
Yadan ajiye takardun hannunsa yace “Gashinan kina nunawa?�?
Cikin magana mai kamar rada tace “Da yanasan girma yanzu kuma baisan girman dayawa.�?
Kunkunin kike ko?
Tadan wayance “Kun dabu da Ya Umar din ne?�?
“Tun awa uku da suka wuce.�?
Ajiyar zuciya tai wacce har yana juyo ta, “Zan kashe in ba wani abin.�?
Tana tunani ko da abin cewa taji wayar ta katse, hararar wayar tai tare da dan sa yatsa ta dunguri wayar tace “Ai dai kadan jira kaji ko da wani abin ko?�?
Sai kuma tadanyi murmushi dan ba shakka hankalinta ya kwanta jin komai lafiya.

*******
Ganin har la’asar bashida wata mafita yasa ya kalli mai shagon tare da dan sosa keyarsa yace “Malam taimakamin da dubu daya ko dari biyar dan Allah, wallahi in na koma Kano a daren nan zan turo maka ninkin kudin daka bani.�?
Wani banzan kallo mai shagon yamai, yace “Kai da dubu dayan waya ajiye wani?�?
Umar a fusace yace “mene?�?
Mai shagon ya kalli jallabiyarsa dadan slippers dinsa ga kafa daya wajen yatsarsa a kumbure yace “Mahaukaci ne ni zan baka kudi bayan banga alama ko dari ka ajiye ba?�?
Ai Umar a fusace ya shako wuyan rigarsa dan dama a sama yake, kafin mutumin yai wani yunkuri ya kaimai naushi.
Yana kokarin sake kaimai wani wasu dake kokarin shigowa shagon suka rike hannunsa, fizgeshi sukai daga gun mutumin nan fa mai shagon ya nufo Umar shima ya cakumoshi, dambe ne ya kaure gashi abin haushi kafafunsa na ciwo balle ya koyawa mutumin nan hankali sosai.
Haka suka hadu da wadannan mutanen suka mai tsinanen duka suka turoshi waje iya karfinsu.
Umar dakyar ya mike yana dudura musu ashar, haka yaja kafarsa da ta sake tsami, can ya nufi gun masu mota yana rokarsu su tafi dashi, sai dai duk inda yaje fada da masifa ne ke rabasu danshi bazaiyi shiru ba suma kuma bazasu yi shiru ba.
Ganin ba haza yasa ya tafi masallaci dan rokar limab dan magrib ta kawo kai gashi tsoro ya fara kamashi, yana tsoron kar kwana ya kamashi a nan garin, ga uban yunwa datake cinsa wanda har ta tafi da karfinsa.
Haka ya shiga masallaci ransa duk a bace, zagi da tsinuwa kam Aminu yashashi har ya gaji, ya kuma dau alwashin ko zai tafi tsirara sai ya rama abinda mutumin nan yamai.
Gun ladan yaje ya danar dashi yazo Wudil ne an sace wayarsa an kuma sace kudinsa, su taimaka mai da dari biyar ya koma Kano.
Ladan ya dauko dari biyar a asusun masallaci ya bashi, haka ya fito kamar zaiyi kuka wai yau shine yake roko? A mai sata dannan a barshi da roko?
Haka yaje gun mai kosai yadan sai na hamsin yaci sannan ya shiga bus, tunda ya shiga yai shiru yana tunanin yanda zaiyi ya wulakanta tsinanen mutumin nan mai kama da fulawa.

******
Abba ya dawo dab da magrib dadi agun Ibty ba’a cewa komai, haka ya zauna ya sake mata nasiha sannan suka fara hira yana bata labarin yanda suka hadu da Baffa mahaifin Aminu.
Bayan Magrib Aminu ya iso tare sukaci tuwon dare da Abban sannan suka shirya dan su taho. Aminu ne ya kalli Iman yace “Iman ko zaki biyo mu ne ki mata kwana biyu?�?
Cikin zumudi zatace eh sai kuma ta kalli Abba tare da kunshe baki.
Abba ya kalli Aminu yace “Ai ka barta kawai, kaga ba hutun makaranta sukai ba.�?
Aminu ya kalleshi yace “Basai su dinga tafiya dasu Islam ba? In aka saukesu sai a kaita ko in aka kaita a kaisu? Bata taba zuwa gidan yayarta ba sannan na tabbatar itama yayartata tanaso taje.�?
Ibty ta kalli Abba tace “Abba dan Allah ka barta, sati daya kacal, kaga nima Monday zan koma skul.�?
Murmushi yai ya kalli Aminu yace “Shikenan amma sati daya.�?
Wani tsalle Iman ta daka ta nufi daki da gudu dan debo kayanta.
Umma tana zaune tana kallan yanda abinsu ke tafiya abin sha’awa, sai dai tausayin Bilkisu ya hanata sukuni dan itakam kana gani kasan ba dadin aure takeji ba.
Haka suka fito suka shiga mota suka tafi, Aminu ko tambayar Umar baiyi ba, duk da ya dauka in sukazo tafiya zai nemi tada wata husumar, da alama ganin Abba na gida ne yasa shi jin kunyar fitowa.

*******
3/4/22, 07:33 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
27
Islam da Ilham ana shiga mota sukai bacci da alama sun gaji, Iman kam sai kallan Ibty take tana kallan Aminu, tunda aka shiga ba wanda yai magana a cikinsu.
Wayarta ta dauka tayiwa Ibty text tace “Kunyi fada da Ya Aminu ne?�?
Da sauri ta mata reply, “fada kuma kamar ya?�?
“Naga ne kunyi kus kamar masu gaba.�?
Sam Ibty ta manta ashe fa Iman tana baya, ga Iman da tsinanen sa ido, ai bata mata reply ba ta kalleshi tace “Iman na tambaya wai munyi fada ne?�?
Yadan kalleta ta glass yace “Iman fada kuma? Ni ba yaro ba?�?
Tadanyi dariya tace “Nagane kunyi shiru.�?
Murmushi yai kadan yace “Jira nake ta warware dazu tayi fishi dani.�?
Dan ido Ibty ta bude tace “Ni? Kaine fa kai fishi dani.�?
Yana kallan hanya yace “Taya kika san nayi fishi?�?
Shiru tai tana tunani, Iman ya kalla yace “Kingani? Yayarki tsokana gareta.�?
Iman tai dariya cikin jin dadi tace “Yaya kaine fa mai tsokanan da alama.�?
“Infadi me tace?�?
Ibty ta zaro ido da sauri batasan sanda tasa hannu akan cinyarsa ba tace “Rufan asiri dan Allah, wlh bakasan halin Iman bane.�?
Iman ta koma ta zauna tare da kallan waje tanajin dadin yanda suke rayuwarsu.
Shikam Aminu sa hannun datai a cinyarsa ne yasa yaji wani yadan tsirgamai, shikam me ke damunshi?
Kallan hannun ta yai wanda hakan yasa tadan zare hannun itama cikin kunya, dan matsowa tai cikin dan rada tace “Yaya ka taimakeni karkai maganar nan a gaban Iman, dan Allah.�?
Dariya taso bashi ya murtuke yana tuki yace “Bakisan yanzu ba’a aikin banza ba? Kin fi kuma kowa sanin ba damuwata bace in na fada ko?�?
Mamaki ya kamata itakam wai haka mutumin nan yake?
Da sauri tace “Naji! Koma menene zanyi dan Allah karka fada, wlh tsaf zata fadawa su Umma ba saiti gareta ba.�?
Yadan kalleta kadan daidai nan sunzo yin kwana, dan jijiga motar tai kadan hakan yasa tadan rike cinyoyin hannunsa dake rike da sityari, bai kalleta ba haka kuma baice komai ba, a hankali tadan zare hannunta tare da komawa ta zauna sosai akan kujera. Iman ce tai gyaran murya tace “Yaya Ibty akwai mutum a baya.�?
Kamar zatawa Iman magana sai ta fasa, haka suka isa gida yai parking sannan Iman ta fara fitowa, Ibty na kokarin fita taji yace “Kin gama wayan ririkenin?�?
Juyowa tai da sauri tace “Wayan rikeka?�?
Bai amsa mata ba taga ya fita daga motar, baya ya bude yana daga tsaye yace “Islam!�?
Ibty mamakin kalamansa ya hanata rufe baki, dakyar ta daure ta fito daga motar ta kalleshi tace “Yaya bacci suke bari zan dau Ilham, Iman ta dau Islam.�?
Kafada ya daga sannan ya wuce ciki. Da kallo ta bishi ta sake maimaita kalamansa wai dama haka yake ko kuma yanzu ne ya zama haka?
Daukansu sukai suka shiga dasu, Iman sai kallan gida take tana santi, kwankwasa kofa taji tana dakin baki tana kallo, fitowa tai falo tace “Yaya Ibty waye da daren nan?�?
Jin shiru yasa ta leka dakinta, karar ruwa dataji ne yasa ya fahimci wanka take.
Kofa ta nufa kanta tsaye ta bude, kallan kallo suka farayi da matar dake tsaye hannunta dauke da tire dake dauke da kuloli.
Iman tai murmushi tace “Me aikin gidan ce?�?
Hajiya wacce ke tsaye dauke da kosai a flask da kunu a jug tace “mai aiki?�?
Iman cikin ko in kula tace “Ko makota?�?
Cikin mamaki da takaicin kalamanta Hajiya tace “Ke din wacece?�? Tayo maganar ne bawai dan batasan amsar ba dan kana kallansu da Ibty zakasan ‘yan gida daya ne saboda kama.
Iman tai murmushi tace “Kanwar matar gidan ce.�?
Hajiya ji take zuciyarta kamar zata tsinke, dazu bayan tafiyarsu ta nemi wata kawarta ta hadata da wani saban malami shine ya bata magani yace tasa a abinci daga Ibty har Aminu suci ba ahinda zai shiga tsakaninsu sai tsana da kyama. Ganin Iman a gidan yasa gaba daya gabobin jikinta sun mutu, bama damuwar ta cin maganin ba a’a haryaushe Aminu ya auri yarinyar da har zata fara kawo ‘yan uwanta?
Iman ce ta katseta da cewa “Goggo in baki fadi ke wacece ba zan koma ciki, na gaji da tsayuwa.�?
Goggo? A gidan uwarki na tsofan da za’a kirani haka? Abinda ta fada a ranta kenan, kamar ta mika tiren tana kuma tsoron kar wannan fitsarariyar taci, to amma ko taci menene damuwarta? Itama tsana ce zata biyo baya.
Mika mata tiren tai tace “Kiba Ibtisam din kice gashi inji Hajiya ba Goggo ba.�?
Iman ta kalli kwanan tace “Kiyi hakuri Hajiya, nikam bazan amsa ba sai ta fito ta tabbatar da ta sanki, dama na dauka mai aikin gidan ce, duniyar nan ba gaskiya.�?
Hajiya ta zuba mata ido tana mamakin yanda ‘yar karamar yarinya ke zuba mata fitsara haka, wannan dabadan a gidan Aminu bane da tuni ta tsinka mata mari, bata kara shan mamaki ba sai dataga Iman ta maida kofar gidan ta rufe.
Dakin Ibty ta koma haryanzu tana toilet, drawer dinta ta bude tana kallan uban kayan da ke jere a ciki, lalai gobe zata dau kaya tai hotuna, dan hotunan ta suk sun tsufa, gaban madubi ta zauna tana ta shinshina turaruka masu kamshi.
Ibty ce ta fito daga toilet sanye da towel, pillow din kan gado ta dauka ta cilo mata ita karfinta, sai dai bata sameta ba, Iman ta juyo tana dariya.
Ibty cikin dan fada tace “Zaki fara ko?�?
Dariya sosai tai tace “Yaya Ibty dan Allah nima in zakuyi aurena ku hadomin kaya dayawa da turaruka, ni na yafe wasu abubuwan.�?
Kai ta girgiza tana goge jikinta tace “Wato dai zancen auren ne bazaki daina ba ko?�?
Kayan bacci Ibty ta fara nema, wata yagal yagal din riga ta daga da sauri ta maidata.
Ai Iman ta mike daga kan kujerar da gudu ta fizge rigar ta wareta, ido tadan rufe tace “Yaya Ibty wannan kika saka ai Ya Aminu sai ya kusa suma.�?
Duka takai mata a baya tace “Allah Iman ki fita idona.�?
Maida rigar tai tace “Allah kina abu kamar ba wayayyiya ba, ko ni yanzu akai aurena rigar datafi wannan fitsara ma sawa zanyi. Mazan yanzu sai kana jan hankalinsu.
Hannu Ibty tasa ta turata daga dakin tace “Lalai yarinyarnan, yaushe ta fitsare haka?�?
Rigar taje maidawa sai kuma ta kara kallanta, irin ‘yan kananan rigunan baccin nan ne shara shara gashi batakai ko gwiwa ba, da net akai rigar.�? Kai ta girgiza da sauri tace “Dazu daga tabashi yace da sanina, haka jiya da daddare yau in nasa wannan ai cewa zaiyi na matsu.�?
Riga ta dauko mai gajeran hannu sannan wandanta shima three quater ne, ta saka sannan ta fesa jikinta turare mai dadin kamshi, kanta ta tufke da ribbon sannan ta daura zani ta tada sallah.
Iman kam sam ta manta da batun matar dake waje, itama dakinsu Islam ta wuce tai alwala ta wuce dakin baki tai sallah, Ibty ce ta fito sanye da hijab ta bude dakin daidai nan Iman ta idar da isha’i, fitowa tai ta wuce kitchen ta kuna kettle tasan ruwan tea.
Iman ta fito da sauri ta shiga kitchen tace “Yaya Ibty? Na manta wata mata tazo wai ko Hajiya?�?
Gaban Ibty ne yadan fadi tace “Hajiya?�?
Kai ta daga tace “wlh na manta tun dazu tazo, amma na tabbatar yanzu ta tafi.�?
Yanda Aminu ya rufeta da fada ranar ta tuno, da sauri ta karasa ta bude kofar, bakowa a gun, fuska Ibty ta shafa shikenan yanzu gobe zata kara kai kararta gun Aminu. Itakam ya zatai da wannan bala’in?
Dawowa ciki tai tace “Iman meyasa baki kirani ba?�?
“Kina wanka lokacin, ni kuma na dauka mafa mai aiki ce, wai wacece?�?
Ruwan tea ta zuba a flask tace “Mahaifiyar matarsa ce data rasu.�?
Cikin rashin fahimtar yaren tace “Mahaifiyar matarsa?Ban gane ba.�?
Murmushin yake kawai Ibty tai ta dau kayan tea din tace “Hakan dai dana fadamiki.�?
Ta kalleta tace “Dan Allah kafin ki kwanta ki kai Islam fitsari.�?
Cikin mamakin da har yanzu bai saketa ba ta daga kai alamar to.
Wucewa Ibty tai jikinta duk yai sanyi, dakin Aminu ta nufa, sallama tai tana kokarin budewa taga anbude kofar daga ciki.
Kallan juna sukai, ya kalli kayan tea din yace �? Bakya tsoron wata rana ya zubar miki a hannu garin bude kofa da hannu daya? Yanda kike din nan ba karfi ba?�?
Tai dan murmushi tace “Yaya ramawa dai kai ko?�?
Falo ya fito yadau wayarsa ya koma dakin, kallanta yai ya zauna akan kujerar da take guda daya a dakin yace “Wai dai a yanda kike din nan na tambatar dakyar kike rike kayan tea din.�?
Ta dan fara karkade gadan tace “Allah Yaya kabar ganin mu sirara karfi garemu.�?
Yadan tabe baki kadan yace “Ko a kira Iman a tambayeta?�?
Kai ta girgiza da sauri tace “Dan Allah ka rabani da Iman, Allah dan baka santa bane.�?
Hannu ya mika mata, kallansa tai sannan ta tako a hankali zuwa inda yake zuciyarta cike fal da tunanin me yake nufi da miko hannu? Isowa tai wata zuciyar tace “ko so yake ya tabaki yaji karfinki?�? Wannan tunanin shine ya tsaya mata, hannunta yaji a cikin nashi, hakan yasa ya kalleta tare dadan murza hannun kadan, ajiyar zuciya tai kadan da alama yau ta canka daidai.
Dagowa yai ya kalleta yace “In nayi magana ace nace.�?
Ta kalleshi cikin kunya tace “Mene?�?
Hannunta ya juyo da cikin tafin hannunta yace “Do you like me to hold you that badly?�?
Hannunta ta zare da sauri tadan zauna a bakin gado cikin wani yanayi tace “Wai Yaya meyasa kake min haka dan Allah?�? Tai maganar kamar me shirin kuka.
“Lipton dina dake kan madubi nake nufi ki bani.�?
Jitai kamar tasa ihu, ta mike ta dauko ta mikamai cikin fishi, tana neman juyawa taji ya riko hannunta. Juyowa tai idanunta sun ciko da kwalla, kiris suke jira su zubo, kallansa tai batai magana ba.
“Okay, yanzu na rikeki da kaina, happy?�?
Hannunta ta shiga fizgewa wasu hawaye suka zubo mata, duk yanda taso ta kwace ta kasa, shikam Aminu baisan meke damunshi ba haka kawai tun randa yasan abinda ke faruwa tsakaninta da Umar ya samu kansa da san zolayarta, har mamakin kansa yakeyi, dan bai taba jin yanasan tsokanar mutum ba sama da ita.
Ganin tana hawaye ne yasa ya dan jata kadan yanasan yi mata magana ganin ta juya, kasancewar bata kawo zai jata ba kawai ta fada kan cinyarsa, wani yanayi ya tsinci kansa a ciki, tare da dan hadiyar wani abu dake makoshinsa.
Saitin kunnenta ya matso yace “Yanzu fa? Gashi har cinyata kin samu kin zauna, am sure yau zakiyi baccin dadi.�?
Kallansa tai cikin hawaye tace “Yaya Allah ka daina min haka, yaushe na…�?.�?
Yatsarsa yasa akan labbanta alamar tai shiru, kwarjininsa ne yasa ta kasa magana, sai wani yanayi data tsinci kanta a ciki, itakam ta tabbatar tana san Aminu, sai dai shi ta tabbatar ba santa yake ba.
“Kina cewa wani abin zan sanar da Iman me kika ce akanta dazu a mota.�?
Tadanyi kasa dakai saboda nauyinsa dataji, gashi yanda sukai daf da juna tana kan cinyarsa kunya duk ta rufe ta.
Gyaran murya yai yace “Sai yaushe za’a daga ni? Ko so ake kafata tai tsami?�?
Mikewa tai da sauri tace “Kaifa ka daurani.�?
Yadan matsa inda ta zauna yace “Dama gun ne da jarumin saurayinki ya nemi min illa kinga yanzu kin sake�?..�?
Cikin sauri yaga ta tsuguna tasa hannunta agun tace “Dukan kafar taka yai? Inalila.�? Tai maganar tana taba gun, duk ta rude.
Gyaran murya ya sake yace “In kin gama tattabani inasan nasha tea kafin ya huce.�?
Da sauri ta mike ta wuce gun kwanciyarta taja bargo da sauri ta rufe har fuskarta.
Baisan murmushin daya bayyana a fuskarsa ba yadau tea yana kallanta, haka yara age dinta suke ko itace haka? Sake murmushi yai yana kallan wayarsa.

*******
A galabaice ya sauka daga cikin motar, dan an matseshi yaji jiki sosai a motar, dan kosan dayaci duk ya gama tafiya daga cikinsa.
Adaidaita ya tara ya nemi taimako akan ya kaishi Tarauni in ya shiga gida zai dauko kudi ya bashi.
Mai adaidaita ya kwashe da dariya yace “Kai yanzu malam banda ka rainani in daukeka sai naje gida ka gudu? Sannan in tambayi gidan da ka shiga ace ba’a sanka ba?�?
Umar saboda yunwar dake damunsa yasa bashida karfin masifa yace “In na gudu ina zani? Ka taimaka ka kaini.�?
Ai kafin ya karasa magana mai adaidaitan ya tafi. Haka ya dinga takawa dakyar duk adaidaitar daya tare in yaji sai yaki amincewa da uzurinsa, ga uban yunwa ga gajiya, ga dukan dayasha ga kuma kafarsa dake azabar ciwo.
Haka ya dinga jan kafa inya gaji ha zauna ya huta sannan ya tashi ya cigaba da tafiya, tun daga kundila haka ya karasa cikin Tarauni da kafa, kallo daya zakamai ka san lalai yasha wahalar da ya dade baisha ba a duniyar nan, tsinuwa kuwa Aminu yashata harya gaji, ya dau alwashin tattaro abokansa sumai tsinanen duka inya warke. Dan wallahi bazai bar wannan cin kashin ba, a kwace mai Ibty a wahalar dashi haka ba.

🏌🏻‍♀�?
3/6/22, 11:08 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

28
Hartai bacci bai daina shan tea yana kallanta ba, shikansa har mamakin kansa yake a 'yan kwanaki kalilan yana neman canzawa daga Aminunsa zuwa wani Aminun? Bayan ya gama abinda yakeyi yazo ya kwanta, hannu yasa yana neman gyara mata bargon data luluba dashi, idanunsa ne suka kai kan shigar dake jikinta, wani abu ne ya sake dan tasomai da sauri ya maida mata bargon ya rufe sannan ya mike yadan fara tafiya a cikin dakin alamar dan karamin exercise, yafi minti sha biyar yanayi sannan ya samu ya kwanta tare da juya mata baya, dan shikam kwanan nan baisan meke kansa ba.

*******
A bangaren Hajiya kuwa jiya tana shiga gida ta zauna a falo ta baza uban tagumi, can ta miki tana huci tace "Kamar ni? Yarinya karama ta kirani mai aiki sannan ta shanyani a waje?" Kwafa tai tace "Kin taimakamin dan dama ina neman hanyar da zan wulakanta yayarki, kin bani dama kin kuma kawo min abu ta sauki." Duk yanda bacci yaso ya dauketa taki yarda, haka tasa gishiri a ruwa ta hau kwankwada, ranar haka ta kwana cir ba bacci, kafin asuba kuwa kanta yayi gingirim saboda uban ciwo na rashin bacci datai, ana sallar asuba ta fito waje dakyar tana tafe kanta na uban ciwo ta nufi gun Bala dake zaune a waje yadan kunna radio. Tana kama bango ta karaso, kasancewar rana bata fito ba sai data zo kusa dashi sannan ya gane ta, da sauri ya mike yana gaisheta. Cikin hakki da magana irinta marasa lafiya tace "Bala! Taimaka ka taremin adaidaita saho in sun fito ina san naje asibiti."
Hankalinsa a tashe yace "Hajiya ba lafiya?"
Tadan daga kai cikin irin yanayin nan na tsananin jin jiki tace "Da alama dadewar danai a waje jiya da daddare ne yasa jinina yahau. Ga sanyi daya sake shiga jikina."
Cikin rashin jin dadi da tausayi yace "Ki koma ciki Hajiya zan samo adaidaita sai na miki magana."
Haka ta juya tana tafiya dakyar, a kuma hankali takeyi dan tanaso Aminu ya sameta.
Cikin sa'a kuwa sai gashinan ya dawo daga masallaci, daga nan nesa ya hangota sanda ta shiga ciki, da sauri ya karasa gun Bala yace "Kamar Hajiya ce na gani ta shiga ciki yanzu ko?"
Bala cikin hausarsa yace "Eh itace, adaidaita tace na tsaidamata zata asibiti."
Hankali a tashe yace "Batajin dadi ne?"
Hajiya dake bakin gate tanajin muryar Aminu sama sama saboda safiya, da sauri ta koma ciki ta dauko tire din abincin jiya ta ajiye akan table sannan tai saurin sa kwallin maganinta ta dawo falo ta kwanta a irin galabaican nan.
Aminu ya kalli Bala rai a bace yace "Ba tambayarka nake ba? Meya faru?"
Nan Bala yace "Jiya ta shigo bayan kun dawo da alama abinci ta kawo to awaje aka barta dan tafi minti talatin a waje tana jiran a barta ta shiga kafin daga baya ta fito tana share kwalla, ina ganin shine ya tada mata ciwo."
Yanayin Aminu ne yai matukar canzawa, fuskarsa ta canza sosai haka idanunsa suka canza kala, bangaren Hajiya ya nufa cikin sauri, tana kwance a falo tana rike da kanta dake ciwo, kallan abincin yai, cikin tsananin takaici yace "Hajiya tashi ki shirya zan dauko mota mu tafi asibiti yanzu."
Tunda ya shiga gidan kamshin turaren ke kara hasaso bacin ransa, zuciyarsa na sake tafasa. Kallansa tai tace "Aminu karka damu, zanje da kaina, banaso a adalilina kai da matarka ku dinga samun matsala."
Fuska a daure yace "Matar da batasan darajarki ba nima bazata samu matsayi a gurina ba, ki shirya zanzo yanzu."
Fitowa yai a fusace ya shiga cikin gida, tana zaune tana karatun qur'ani, idanunsa ya runtse yace "A haka kamar matar arziki" kofar dakinsa ya bude tana kai aya ta tsaya sannan ta kalleshi tace "Yaya Ina kwana?"
Wani kallo ya mata ya wuce ya dau key sannan yasa a aljihun jallabiyarsa, mamaki ne karara ya bayyana a fuskar Ibty ganin jiya ana raha da tsokana sukai bacci, da sauri ta mike ganin yana kokarin fita, hannu tasa ta riko rigarsa ta baya. Juyowa yai ya kalleta, yanda yake kallanta kadai tasan wani babban laifin tai. Bakinta nadan rawa tace “Yaya wani abin nai?�?
Yatsa ya nunata dashi kamar zaiyi fada, dan har jikinta ga gama yin sanyi ta tsorata da yanda ya nunata da yatsa, idanunta ne suka dan fara neman canzawa ya sauke hannunsa yace “Why are you pretending?�?
Kallansa tai tace “Pretending?�?
Rigarsa ya dan janye daga hannunta yace “The worse people I despite are those with two face, a gabanka su nuna maka wani hali a bayan idanka su nuna maka wani.�?
Bata gane meyake nufi ba, ganin ya fito daga dakin yasa tabi bayanshi da sauri tace “In laifi nai a matsayinka na babba yaya fadamin zakai menai sai kamin fada ko?�?
Bai kalleta ba sai gani tai ya fita daga gidan, da sauri tabi bayansa tana kallo ya shiga mota ya fita, hawaye ne suka gangaro saman idanunta, jiya da farinciki ta kwana yau kuma meke faruwa haka?
Tunowa da Hajiya tai, idanu ta zaro da sauri ta bi gate, Bala wanda yake sa kwado a gate din bayan fitan Aminu ta kalla tace “Bala? Ina Ya Aminu yai?�?
Ya gaisheta sannan yace “Hajiya yaje kaiwa asibiti.�?
Idanunta ta runtse sannan ta furzar da wata iska, Alhamdulila matsalar ta Hajiya ce dan ta dauka wani abin ne ya sake bullowa, indai Hajiya ce Allah na tare da ita kuma insha Allahu sai yanda taso hadata da Aminu kwanaki yanzu bata isa ba.
Bala ta kalla tace “Ciwon nata sosai ne?�?
Yace “Dazu dai dakanta ta fito da alama bawai ya hanata motsi bane.�?
Jin haka yasa ta juya ciki, zama tai a dakin Aminu tana kallan hotonsa wanda sukai shida Na’imah dake kan madubin dakin, ko tunanin ya kamata ya dauke hoton bayan auransu baiyi ba.
Ta dade ta a tunanin abinda ya kamata tai, ca. ta mike kawai ta shiga kitchen ta hau yin abinci, kasancewar weekend ne su Islam anata bacci, Iman ma dasan baccin safe tana can tanata baccinta.
Ta dade tana shirya abinci kafin ta gama, wanke wanke tai sannan ta fito ta shiga toilet. Wanka tak ta dauko wani doguwar material ta saka, dinkin ya mata kyau haka kalar material din ta amsheta. Batai wani kwalliya ba ta dau wayarta ta duba lokaci. Karfe tara na safe.
Saman goshinta ta dafa tana tunanin abinyi, can ta kira wayar Ainah.
Ainah na cikin bacci taji vibration, cikin abin bacci ta dauka. Ibty tace “Ainah taimaka ki turon number Hajiya.�?
Ainah jin muryar Ibty yasa tadan bude ido sosai tace “Ibty?�?
Murmushi tai tace “Turomin yanzu dan Allah, sai ki koma kiyi ta bacci harsai Ummy ta gaji ta watsa miki ruwa.�?
Ainah tai dariya sannan tace “Me zakiyi da numberta?�?
“Kawai dai gani nai banida numberta gashi muna daf da juna.�?
Ainah tadan tabe baki tace “Kardai ki sakewa matarnan dayawa wlh bazaki iya yakiceta ba.�?
Murmushi tai na yake tace “Turon please.�?
Ainah tana turo mata number ta kashe sannan ta kira number Hajiya.
*****
Kwance take akan gadan da aka bata ba’a dade da fara saka mata ruwa ba, Aminu na zaune yana tunanin hukuncin daya kamata ya dauka, tabbas Ibtisam ta bashi kunya, wancan karan yaji harda laifinsa amma wannan fa? Ai Hajiya uwa ce taya zata barta a waje?
Wayar Hajiya ce ta fara kara, mikewa yai ya karaso kan saman drawer ya dau wayar, ganin number ne ya kalleta yace “Number ce.�?
Gabanta ne ya fadi kodai malamin ta ne? Wani irin faduwar gaba ne ya kamata, tana kokarin cewa ya kashe kawai taji yace “Assalamu Alaikum!�?
Idanu Hajiya ta runtse shikenan in yaji muryar namiji zai yi zargin wani abin, ita kuma da saninta taki yin saving din numbersa saboda tsautsayi, gashi ba karatu tai ba bataso asa abinda zai rikitata.
Ibty kam jin muryar Aminu yasa tadan runtse ido, tace “Yaya! Nayi mata abincin safe ne shine nake so naji jikinta? Sannan na kiraka naji ko zaku dawo yanzu ko kuma zaka turo Mamman yaxo ya dauka?�?
Duk da akwai jin haushinta mai karfi a ransa sai dai bayanda zaiyi, zai hana Hajiya cin abinci ne saboda bacin ransa?
Kallan Hajiya yai ya sanar da ita sakon Ibty, mamaki ne ya rufe Hajiya wato yarinyar nan makirace? Murmushi tai tace “Allah sarki mun sata wahala, ka duba abinda kake gani ni duk daya ne.�?
Aminu fuska a daure yace “Zanzo na dauka yanzu, Mamman sun fita da Baffa.�?
Tana kokarin sake magana taji ya kashe. Kallan Hajiya yai yace “Ki kwanta ki huta ance harda rashin bacci, bari naje na dauko.�?
Haka ya fita daga dakin, gida ya wuce kai tsaye.
Su Islam sun tashi daga bacci, Iman ta kamasu ta musu wanka, Ibty tana dakin Aminu tana gyarawa taji motsin motarsa, turaren wutan data sa a dakin ta fito dashi zuwa falo, daidai nan shima ya shigo falansa.
Kallan juna sukai da sauri tace “Sannu da zuwa.�?
Bai amsa ba ya fara kokarin wucewa daki, da kallo ta bishi harya shiga ciki, ajiye kaskon tak ta nufi dakinsa, ya zare jallabiya sanye yake da vest da gajeren wando hannunsa dauke da towel da alama wanka zaiyi.
Har tana neman juyawa sai kuma ta koma tace “Ya jikin nata?�?
Yadan rufa towel a saman kafadarsa yace “Kin damu da lafiyarta ne kika barta a waje jiya?�?
Ibty tadan sadda kai kasa tace “Haka kawai sai na barta a waje? Bayan nasan matsayinta a gunka? Ko wace bansani ba nayiwa wannan wulakancin bazakai mamakin dalili na nayin hakan ba?�?
Wani abu yadan hadiya yace “Sometimes I feel like wannan face din nake akwai abinda kike boyewa, yanzu kinasan cemin akwai hujjarki na barin babbar mace a waje? Da daddare? Sannan cikin sanyi?�?
Hawayenta tadan share tace “I thought mun fara fahimtar juna, kasan abinda zan aikata da wanda baxan aikata ba, at least ko bakasan duka ba na dauka xaka fahimci bazan wulakanta babba ba……�?
Hawaye ne suka dan fara neman cin karfinta, da saninta tadan rufe fuskarta tana kuka sosai, me makon tai hanyar kofa sai ta nufi bango wai a dole batasan ina take nufa ba.
Cikin hanzari yasa hannu ya rikota hakan yasa ta dan fada kirjinsa, yana neman dagata kawai yaji tana kuka harda shesheka. Idanu ya runtse dan sam bayasan a dalilinsa mutum ya dinga kuka haka, kamar ya zareta ta karfi sai kuma ya kasa, samun kansa yai da dan shafa bayanta, can ya tuna abinda tai yadan dagota yana neman yin magana yaga yanda hawaye duk suka bata mata fuska, idanu yadan runtse sannan yadan juya baya, Ibty ta dan riko hannunsa da sauri, juyowa yai ya kalleta. Kwarjini da shakkarsa fal take a zuciyarta, ga rashin riga yasa saman kirjinsa a bude, kashin dake kirjinsa ya bayyana. Dakewa tai tana hawaye tace “Wlh bansan tana waje ba, ina wanka sanda tazo, kafi kowa sanin girman gidan nan in mutum yana toilet ba yanda za’ai yaji. Yau Hajiya ta fara zuwa ko jiya? Meyasa ban taba kin budewa ba? Sannan dana fito nai sallah muka zauna a falo banji kwankwasawa ba balle na bude, daga nan kuma na taho gunka�?
Idanunta ya kalla dake zubar da hawaye, da alama gaskiya ta fada, dan koshi baiji kwankwasa kofa ba.
Shiru yai yana tunani, muryarta ce ta katseshi, Hajiya mahaifiyar matarka ce data rasu, batada hakkin zama dakai, ba muharramarka bace, ba kuma aikinka bane kula da ita, nice matarka nice hakkinka, amma na taba nuna maka banasan xamanta dakai? Duk kuwa da bansan da zamanta ba sai bayan aurena?�?
Jikinsa ne ya sake yin sanyi, kara matsowa tai tana hawaye tadan kwantar da kanta a saman hannunsa tace “Kayi hakuri in har na bata maka rai.�?
Lalai san Ibty ya fara shiga jikinsa, dan tabbas ji yake kamar ya jawota sosai ya rungumeta, sannam ji yake kamar ya bata hakurin fishin dayai da ita.
Shiru suka danyi, can yace “Kin tabbatar ba kirana kikai dama ki kwanta a jikina ba?�?
Dagowa tai tace “Ni?�?
Yace “Umm humm kalli, tunda na shigo kike ta wayan ririkeni.�?
Badai ya gano yau kisisina tadan yi bajintar yi ba?
Sakeshi tak da sauri tace “Allah Yaya ka daina min haka kaifa ka jawoni jikinka.�?
“Ya akai ban tuna ba?�?
Tace “Allah kaine, naji bigewa ka jawoni……�?
Then?
Kunya tadan kamata, sai dai wani irin dadi ne yake kasan ranta yau ta tabbatarwa kanta inhar tanasan jin dadin aure to dole ta cire kunya ta kwaci mijinta da kisisina.
Aminu ya wuce toilet har zai rufe bandakin sai taji yace “Rainane ya baci jin an barta a waje, banyi tunanin baki sani ba.�?
Kallansa tai ya maida kofar ya rufe, murmushi tai tare da dan rufe fuskarta, dole ta sa Iman ta siyo mata littatafai na kisisina a kasuwa, sannan ta tabbatar akwai wasu online, tunda Aminu nada saukin kai da rauni, da alama dashi Hajiya take amfani.

******
A bangaren Umar kuwa dakyar ya shiga bangarensu, a kwance a falo yaga bilkisu tana bacci da alama jiransa take. Wani dogon tsaki yaja sannan yasa kafa ya zunguri kafarta iya karfinsa, a razane ta farka, dayake ba wuta fitila suka kunna, ta kalleshi tana kokarin mikewa duk ta rikece, garin sauko da kafafunta ta fado daga kan kujerar, kafa yasa ya kara hankadata da karfin gaske, wani irin azaba ce ta ratsata tadan saki kara tare da rike kafafunta, tsugunowa yai yadan shako wuyanta yace “Wato na tafi kinajin dadi har bacci kike kina sakin munshari ko?�?
Kai ta girgiza da sauri tana hawaye, hankadata baya yai ta sake faduwa yasa kafa ya tsallaketa sannan ya wuce kitchen, fitowa yai yace “Tashi kiban abinci kafin ranki yai mugun baci.�?
Dakyar ta mike ta nufi kitchen shi kuma ya wuce daki. Man zafi ya shafa a kafarsa sannan ya dau wayarsa, tabbas sai Aminu yasan shiya wulakanta wlh.
Abinci ta kawo ta ajiyemai, hannunta ya matse da karfi, ya kalli kafarsa yace “Kinga menene nan?�?
Idanu ta firfito dashi tace “meya sameka? Ko bigewar dazu ce?�?
Ya yarfar da hannunta yace “Ba sai kinji ba sai dai ina sanar miki duk sanda aka kai wani asibiti akan an kusa kasheshi ki tabbatar kin sanar da iyayenki shine ya fara bani ba.�?
Bata gane me yake nufi ba sai dai babu fuskar sake tambaya.
Nan fa yasa abinci a gaba sai daya cinye tas ya saki wata katuwar gyatsa sannan yasha ruwa.

******
🏌🏻‍♀�?
3/8/22, 08:04 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
29
Tana tafe tana dan waka a ranta nadan nishadi, bangarenta ta wuce daga falo ta juyo musun Islam da Ilham nan ta karasa dakin fuskarta duk alamun tayi kuka amma farinciki ne karara a bayyane a fuskar.
Iman dake zaune tana zabga dariya saboda itace ta jawo musun daga tambayarsu wanene babba. Ganin Ibty ta shigo yasa ta guntse dariyarta. Ibty da sauri ta karaso ciki jin muryar Islam harta fara canzawa tana neman yin kuka. Kusa da ita ta karasa ta kalli Iman tace "Allah kece."
Iman ta dan dafa kirjinta da hannu tace "Ni nai me? Kina dai kallo na a zaune."
Harara ta maka mata tace "Ko a kwance kike nasan kece, duk da nasan suna fada tsakaninsu amma tunda har musu ya nemi sa Islam kuka nasan kece."
Iman ta kalli Ilham tace "Ilham daga cewa wanene babba na sake magana?"
Da sauri Ilham ta girgiza kai alamar a'a, sannan ta daura da cewa "Itafa Islam neman kuma take dama, Kawar Aunty ba itace karama ba? Wanene ke fitsarin kwance? Wanene bai iya homework dinsa ba? Wanene inzai sa kaya sai an tayashi?"
Ai nan Islam ta harzuka tace "Kema ai baki da wayau kuma duk mara wayau shine karami."
"Surutu shine wayau?"
Ibty ta kalli Ilham tace "Ilham ya isa haka nan kinji?" Nan ta fara rarrashi tare da dauke musu hankali akan insuka shirya zasuyi keke.
Fitowa tai daga dakin, Iman ta biyota tana dariya. Dakin Ibty suka shiga, kallanta Iman tai yanzu ta daina dariyar tace "Ya Ibty wani abin ya faru ne? Naga idanki kamar kinyi kuka."
"Kukan me? Kedai kin fiya sa ido, to ba kukan danai." Ibty tai maganar tana bude wardrobe dan kar Iman ta sa mata ido. Iman ta zauna akan gadan tadan kishingida sannan tace "Ya Ibty gadan nan in aka juyashi ya kalli nan bazaifi kyau ba?"
Ibty ta dan kalli dakin sannan tace "Haba?"
Iman ta mike ta fara nuna mata tace "In akasa daga nan dakin ma zaifi space."
"To shikenan, anjima sai ki tayani mu gwada juyawa."
Fitowa tai daga dakin, ta tabbatar su Islam sunci abinci sannan ta nufi bangaren Aminu.
Tana shiga falansa kamshin turarensw ya tabbatar mata daya shirya, idanunta tadan lumshe kadan itakam tabbas tasan kaunar Ya Aminu ke yawo da ita, kuma ta daura damarar kwatar mijinta. Sallama tai daga ciki ya amsa sannan ta tura kofar dakin, yana tsaye a gaban madubi yana kokarin sa agoggon hannunsa, kai tsaye ta nufi gun gani yai tana neman riko hannun dayake sa agoggon, da sauri ya daga hannunsa sama yace "Me kike shirin yi?"
Tadan kalleshi kadan tace "Dama...." Sai kuma tai shiru saboda kunyar abinda zata fada dataji, itakam meyasa kunya ta mata yawa?
Aminu yadan matsa kadan yana gyara agoggonsa yace "Su Islam fa?"
"Suna tare da Iman wai keke zasuyi."
Bai amsa mata ba hakan yasa ta fara tunanin abinda zatace dan sudanyi magana.
"Zakizo muje tare?"
Da sauri ta dago ta kalleshi, tun dazu take tunanin ta yanda zatai taje ta duba Hajiya, sai dai bataso yai tunanin wani abin daban.
Cikin jin dadi tace "Eh Yaya!"
Hularsa ya dauka gani tai ya mika mata, bata amsa ba sai kallan hular datai tana tunanin karta amsa ya fada mata wata bakar maganar.
"Na dauka tunda kin damu ki samin agoggo yanzu kwatar hular zakiyi ki samin?"
Kallansa tai tace "Allah ni ba kwata zanyi ba." Tai maganar cikin 'yar karamar shagwaba.
Sa hular yai yace "Ki fadawa Iman zakije ki dawo, sai ki taho mu wuce."
"Abincin ka fa?"
"Tunda kai mata zamuyi in na dawo naci."
Bai jira me zatace ba ya dau key da wayarsa ya fita, bayanshi ta biyo itama ta nufi bangarenta, suna zaune a falo suna kallo "Iman zamu dan fita da Ya Aminu yanzu zamu dawo."
Haba Iman ta rike tace "Ah oh ni abin ba kunya? To ai da kin sani cemin kikai zaku fita da Habiby dinki. Sai infi fahimtar ki."
Pillow ta dauka tadan kwada mata tace "A gaban yara kike wannan maganar?"
Gwalo ta mata tai magana kasa kasa "in kun tafi karku dawo sai dare kuje can kusha love."
Daki ta wuce ta gyara fuskarta sosai ta daura dankwalin material din sannan ta dauko mayafi light purple wanda akwai kwalliyar material din dashi ta yafa, tayi kyau abinda das.
Nan ta dauko abincin a basket sannan tace “Iman in na dawo ma gyara dakin.�?
Haka ta fito ta nufi mota, dan taji alamar tada motarsa dayai, a baya ta ajiye abincin sannan ta bude ta zauna. Kallanta yai yanzu ma abinda ya saba ji ne yaji yadan tsirgamai, kansa ya dauke da sauri sannan ya maida kansa gaban mota.
*****
Hajiya kam tun fitarshi daga asibiti ta kasa kwantar da hankalinta, ya kamata tai bacci saboda ruwan da ake karamata amma dan bala’i da masifa har wage idanunta takeyi dan kar bacci ya dauketa. Ganin tunani ya hanata sukuni yasa ta kira saban Malaminta. Ya tabbatar mata da yana nan yana aiki dan haka itadai ta tabbatar tayi abinda yace mata.
Kwantar da kanta tai tana tunanin yanda zata tirsasa yarinyarnan taci magani, batada matsala daba Aminu dan ko a kunu zata iya damawa inyazo gaisheta tasashi yasha matsalarta daya wannan tsinaniyar yarinyar data fara jawo kanwarta dan suci zarafinta.
Tana kishingide tanata lissafi har bacci yai gaba da ita.
Kofa Aminu ya tura hannunsa dauke da basket din, shiga tai itama ganin tana bacci yasa tadan kalleshi.
Ajiye basket din yai ya kalli kujerar daki wace take kwaya daya ya mata alama da kansa akan ta xauna. Kai ta girgiza tadan mai alama dashi ya zauna. Hannu yasa yadan rikota ta dan ja hannunta kadan tare da nunamai bakin gado, alama ya mata da in bata zauna ba zai kinkimeta ya daurata. Garin dan kokarin zama tadan taba kafafun Hajiya, wanda hakan yasa tadan bude ido kadan cikin mayen bacci. Me zata gani? Gani tai Aminu na murmushi yana yi ma Ibty alama in ya zauna wai karta mai complain tace ya tashi.
Kallan hannunsu tai dake rike da juna, tashin hankalin da ba’a misaltawa, wato har Aminu ya fara hada jikinsu tare? Shikenan kila ma ya kusanceta. Itakam ta gama yawo.
Aminu ne ya zauna akan kujerar cikin maganar rada yace “Da sauki yanzu, da na dauka cewa zakiyi sai dai mu zauna a kujera daya, saboda san ki zauna kusa dani.�?
Me kunnenta sukeji?
Ibty tadan turo baki kadan tana dan magana mara sauti “Duk sanda na kamo bakin nan dake zagina a sirrance tun farkon haduwarmu sai na dinkeshi da zare da allura.�? Yai maganar idanunsa nakan wayarsa daya dauko.
Dan matsawa tai kadan tace “Inka dinke min baki, dame zaka samu damar zolayata?�?
Dan gyaran murya yai yace “Yaushe na zolayeki?�?
“Kullum mana, gashi nan yanzu ma kanayi.�?
Dan kafada ya daga ba tare da ya kalleta ba yace “Ji duk abinda na fada I mean it, kece kawai kike daukansa a…�?..�?
Tarin da Hajiya ta farane yasa yadan mike tare da dan matsowa, kafadarsu ce ta hadu shida Ibty, Hajiya kam ji take kamar ta rusa ihu.
Cikin dan kokarin mikewa tace “Amarya kece da kanki?�?
Ibty ta gaisheta, Hajiya ta amsa fuska a sake. Itama fuskar Ibty a sake tace “Kiyi hakuri jiya wlh bansan kina waje ba.�?
Kallan Aminu tai wanda takejin haushinsa ji take kamar ta zabgamai mari saboda takaicin saukowar dayai cikin sauki haka. Murmushi tai tace “Haba karki damu ai nasan da kin sani zaki fito.�?
Ibty ta kalli Aminu tace “Yaya kaji ko? Itama Hajiya tayi shaidata.�?
Mamakin kalaman nan ne ya rufe Hajiya lalai yarinyarnan makira ce.
“Hajiya ga abinci nan in zubo miki?�?
Ta dan girgiza kai tace “in an gama sa ruwan naci, kedai ki koma gida ki huta dan Allah.�?
Ba wani ja Ibty ta kalli Aminu tace “Yaya mu wuce?�?
Aran Hajiya tace “Sai dai ya kaiki ya dawo dan in banda lafiya to fa Aminu baya barin asibiti sai dai in aikin dole ne�?..�?
Batagama yin tunaninta ba taji yace “Hajiya zan dawo wajen azahar ko la’asar in jikin yayi sauki sai mu nemi sallama.�?
Tsananin mamaki ya hanata amsawa sai kai kawai data daga.
Haka tana kishingide galala tagansu sun fita.

*******
Gida suka wuce, Bala na kokarin bude gate din gidan Umar dake jingine da bango ya taho, Ibty tadan runtse ido cikin takaici, wato bayan waccen ga wani dake neman kawo musu matsala a rayuwa, itakam mutanen nan biyu bazasu barsu suji dadi ba?
Aminu kam kallan Umar yai dake nufosu ya dan kalli Ibty, yace “Gafa dodonki.�?
Tace “Ni Allah na dainajin tsoronsa.�?
“Really?�?
Ta daga kai, okay bari yazo muga me zakiyi.
Kanta ta kawar dan itakam ko ganinsa batasan yi ji take kamar zai cafketa.
Umar ya karaso yana dingishi, Aminu yadan karkatar dakai ya dan kalli kafarsa kadan wacce babbar ‘dan yatsan harya kumbura.
“A haka kake yawo?�?
Umar fuskarnan tasa a murtuke yace “Dadin saurayi mai jini a jika kenan.�?
Aminu yadan jinjina kai yace “Gaskiya, sai dai me ya kawo saurayi mai jini a jika inda ba’a nemansa?�?
Umar ya cilo dari biyar cikin motar, sabuwa yace “Kudinka na dawo ma dashi dan samun kwanciyar hankalina.�?
Aminu ya sunkuya ya dau dari biyar din yace “Ba laifi dan dama taimako ne nayi kuma tunda kanada halin dawo dashi ai ba laifi.�?
Umar ya kalli Ibty wacce ta kawar da kanta, lalai yarinyar nan wato ganinshi ne ma batasan yi?
Ganin kallan da Umar ke mata haka kawai Aminu yasamu ransa da baci, hannu yasa yadan tabota yace “Hajiya! Bakiga yayanki bane?�?
Kallan Umar tai fuska a daure tace “Ina wuni?�?
Baiko amsa ba sai kallanta kawai dayake, Aminu ya kalleshi yace “Saurayi matsa mu wuce in kuma kana bukatar wani ciwon ne to.�?
Hucci Umar yai kamar bazai matsa ba sai kumabya matsa, meyasa yakejin kamar Aminu ya kara wulakantashi? Bayan har gwada acting din yanda zai wulakantashi da dari biyar din nan yai a gaban madubi? Bakomai ai wannam masomi ne yajira haduwarsa da abokansa.
Haka yaja kafarsa yabar gun.

Aminu ana shiga ya kalleta bayan ya kashe motar yace “Jaruma na dauka zaki kori yayanki.�?
Kallansa tai tadan murza ido kadan tace “Ni fa gyangyadi nai ban masan mun iso ba.�?
“Ohhhhh! Gyangyadi ko?�?
“Wani sa’in in ina bacci har magana nake amma bansan me nake cewa ba.�?
“Yanzu fa? Kin tashi ko a tasheki?�?
Kai tadan girgiza tare da dan rufe ido, “Bacci nake haryanzu.�?
“Umar meka dawo yi?�?
Idanu tadan bude, Aminu ya girgiza kai “Ya kikai da rayuwarki na shekaru masu yawa kina tsoronshi haka?�?
Tadan maida kai kasa tace “A haka na tsinci kaina bansan yaushe na fara shakkarsa ba. Amma Allah yanzu in kana kusa bana shakkarsa so…�?..�?
Ganin yanda yake kallanta ne yasa tadan hada labanta biyu alamar yin shiru, “Na dauka kina ganin saurayin mai jini zai wahalar dani?�?
“Nagane ba hankali ne dashi ba.�?
“Hmmm�?.. kenan nine bakyasan a taba?�?
Kunyar kalamansa ne ya kamata, tace “Tunda ka sani sai ka tambaya?�?
“Zaki shiga ciki ko fita ki shiga ne bakyaso?�?
Hannu tasa ta dan bude kofa da sauri tana fita tace “Allah nima zan fara maidawa.�?
“Zaki iya?�?
Kallansa tai, kwarjininsa ne yasa tai saurin wucewa ciki saboda kunya, sai dai harga Allah tanasan yanda yake zolayarta ita a ganinta shakuwa suke sakeyi hakan.

🏌🏻‍♀�?
3/10/22, 08:07 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
30
Ciki ta shiga cikin jin kunya sai dai fuskarta dauke da murmushin farin ciki, a falo ta taraddasu suna zaune suna wasa, Iman ce shugabar tsaramusu yanda zasuyi.
Suna jin alamun bude kofarta suka nofota da gudu suka rungumeta suna mata oyoyo, cikin jin dadi itama ta rungumesu suka shiga ciki. Kitchen ta wuce kai tsaye ta yi warming din abincin Aminu sannan ta nufi bangarensa.
Yana zaune a kujera a falo ta shigo ta wuce gun dinning ta ajiye kayan abincin, "Yaya abinci."
Kallanta yai sannan ya zare hular kansa ya wuce ya zauna, "Ke kinci?"
Kai ta daga alama eh tace "Tun dazu."
"Su Ilham fa?"
"Naga zakaci abinci shiyasa ban fada musu ka dawo ba, inka gama zasu shigo."
Dan kallanta yai a hankali taga murmushi ya bayyana a fuskarsa, cikin sauri tace "Yaya murmushi kai?"
Fuska ya maida ya daure kamar yanda take, da sauri tace "Allah yanzu nagani murmushi kai."
Zama yai akan kujera yace "Bansan murmushina zai saki farinciki haka ba."
Kai tadanyi kasa dashi tace "Zaka fara ko?"
Kafada yadan daga sannan ya fara zuba abinci, fitowa tai tana tafe tana wasa da yatsun hannunta, abincin rana ta daura, Iman ta shiga tana tayata, su Islam agun Dady dinsu sukaci abinci sannan ya kaisu Islamiya.
Ganin sun gama komai Ibty da Iman suka nufi dakinta dan canza gado kamar yanda suka tsara, Ibty ce ta dan daga katifar, ita kuma Iman ta kamo gefe suka sauketa, dawowa Ibty tai ganin wani abu a bakar leda tasa hannu ta bude, tana cewa “Menene wannan?�? Karasa budewa tai tana ganin layar nan taji kanta yayi wani irin sarawa. Baya tai sai ji kake tim ta fadi a kasa, Iman ta dauka wasa takeyi tace “Wlh in ma zaki tashi ki tashi niba Ya Aminu bane balle nazo na lallabaki. In kuma shi kikeso na kira miki basai kin langwabe ba, naji motarsa da alama ya dawo daga kaisu Islam�?..�?
Ganin dai ba alamun magana yasa ta nufota, kafa tasa tadan zungureta, ganin ba motsi yasa tsoro ya kamata, da sauri ta fara jijigata, ganin da gaske ta kasa mikewa yasa Iman ta fito a guje ta nufi bangaren Aminu.
Yana kokarin shiga daki ta afko bako sallama, “Ya Aminu!�? Ta kwalla masa kira duk a rikice.
Da sauri ya juyo dan yanda yaji kiran, “Ya Aminu kazo Yaya Ibty�?.�?
Ai bai tsaya jin me zata ce ba ya taho cikin hanzarinsa, dakinta suka nufa tana kwance yanda Iman ta barta, cikin tsananin tashin hankali ya karasa ya dagota ya fara girgizata, ganin bata tashi ba yasa ya dagata cak ya fito da ita daga dakin, kan kujera yasata sannan ya kalli Iman dake tsaye a rikice yace “bani ruwa.�?
Nan tai kitchen ta debo ruwa a cup ta mika mai, ya yayyafa mata, a wani firgice ta mike jikinta na karkarwa, hannunta ya kamo ya dan jijigasu kadan yace “Ibtisam!�? Yauce rana ta farko daya taba kiran sunanta haka, itakam batama ji sanda ya kirata ba, haryanzu jikinta rawa yake tana fitarda wani irin numfashi, gaba daya ya rikice bai taba sanin ya damu da yarinyar nan ba kamar yanzu, badai mutuwa zatai ba itama? Gaba daya jiyai ya rasa abinyi, kawai yasa hannu ya rungumeta yana shafa bayanta, Iman kam daki ta koma tai tsuru tana tunanin meya faru?
A falo Aminu ya dade yana shafa bayanta yana tofa mata addu’a kafin jikinta ya daina rawa sai dai haryanzu numfashinan tana fitar dashi cikin sauri kuma akai akai.
Ganinta a jikin Aminu yasa mamaki ya kamata, meya faru? Kanta taji yayi wani irin sarawa mai azaba, cikin dan daurewa tace “Yaya kaina!�?
Dagota yai yace “Ciwo yake?�?
Idanu ta lumshe dakyar sannan ta daga kanta, da sauri ya mike ya wuce daki ya dauko paracetamol ya dauko ruwa ya mika mata, baya iya bude idanunta sosai haka sai shi ya taimaka mata tasha.
Kwanciyarta ya gyara mata sannan ya nufi dakin. Kallan Iman yai yace “Na bata magani tasha, amma meya sameta?�?
Iman ta girgiza kai tace “wlh bansani ba Yaya kawai naji tace menene wannan? Daga nan kawai naji shiru.�?
Da sauri ya nufi gun sai dai sama da kasa babu komai a gun, falo ya fito ya kalli hannunta nan ma ba komai, to me ta gani?
Dan tabbas ya tsorata matuka, tunowa yai da mutuwar Na’imah tana numfarfashi daga nan komai ya tsaya.
Ko daya koma bangarensa kasa zama yai, sai leko wa yake yana dubata inyaga tana bacci sai ya koma.

****
Hajiya cikin bacci taji wayarta tana kara, dakyar ta dauka saboda baccin na mata dadi, jin muryar malaminta yasa ta bude ido sosai.
“Ke wace irin mahaukaciya ce zakibar layar da na baki inda za’a gani?�?
Hankali a tashe tace “Wace Laya?�?
Yai tsaki yace “Layar dana baki wacce nace kisa a inda yarinyar nan ke kwanciya, badadan layarmu nada karfi ba wanda daga an budeta za’a nemeta a rasa da shikenan kin jawo mana jidali.�?
Mikewa zaune tai cikin tashin hankali tace “wannan yarinya anyi tsinaniya, shiyasa na fada maka ka tura a sa mata ciwo, ko na hauka ne, ni wlh gaba daya ko wulgawarta bana sanyi.�?
“Abinda bata sani ba karfin layar ko ganinta kai to fa sai aljanunmu sun hukuntaka.�?
Cikin jin dadi tace “Dan Allah ku hukuntata sosai, dan wlh da alama Aminu ya fara san yarinyarnan.�?
Tsaki ya danyi “Kinsa munyi asarar layar dan da alama bata taba kwana akai ba, bayan layar ta dawo gun mu ina dubawa naga ba’a taba kwanciya akanta ba, yanzu sai ki samu kizo a sake biyan bukata dan aljanu su samu damar yin hakuri da abinda kikai su bamu wani abin.�?
Takaici ne ya kamata, dan itakam saduwar nan ba dadi takeji ba haka nan yakeyin abinshi shi kadai ya gaji, sai dai yazatai? In har tanasan zamanta da matsayinta dolene ta kauda tsinaniyar yarinyarnan.
“Zanzo gobe yau ina asibiti.�?
Bai bata amsa ba ya kashe, kanta ta dafa itakam ta tsani yarinyarnan, ta tsaneta kamar yanda ta tsani mutuwarta.
******
Ibty bacci tai tayi kamar wacce tasha maganin bacci, shikam Aminu sam ya kasa kwantar da hankalinsa, haka ya dinga wayancewa sai ya shigo inyaga ba kowa ya dan tsaya yana kallanta, in kuma Iman na nan sai ya wayance yace ruwa yazo dauka bayan akwai fridge da ruwa a falansa.
Yanzun ma ya shigo dan hankalinsa yaki kwanciya, ganin Iman bata falan yasa ya karasa kusa da ita, gani yai kamar tana dan sauke numfashi, dan sunkuyowa yai kadan yana san jin wani irin numfashi take saukewa, ya sunkuyo ta bude idanunta, zaro ido yadanyi sannan ya dan dago tare da yin gyaran murya, “lekowa nai naga ko su Islam sun dawo.�?
Mikewa tai zaune tare da dan dafa kanta, baisan ya zauna kusa da ita ba yasa hannu saman goshinta, “kan ne?�?
Kai tadan girgiza tana murmushi tace “Wani irin bacci nai?�? Tai maganar tana kallan agoggo.
Shima agoggon ya kalla, “Yanzu ya kikeji?�?
Kai tadan girgiza a hankali tace “Bakomai.�?
Kamar zai mike sai kuma ya kalleta yace “Meya sameki?�?
Tace “Abu na gani a bakar leda na dauka na bude daga nan bansan meya faru ba.�?
“Bakar leda?�?
Ta daga kai alamar eh, “Iman ta duba dakin bataga komai ba.�?
Cikin mamaki tace “Yana nan bari na dubo.�?
Tadan mike, kafafunta ne suka danyi rawa da sauri yasa hannu ya riketa, kallan juna sukai, ya dan tsaida ita sosai yace “Ki zauna in jikinki ba karfi, ba abin sauri bane.�?
“Su Islam sun kusa dawowa banaso su ganni a kwance.�?
Daki ta nufa yabi bayanta da kallo, idanunsa yadan rufe kadan, meke damunta? Da ya dauka tsoron Umar ne, sai dai nayau tabbas ba tsoro bane wani abin ne ya faru wanda ita kanta bata sani ba.
Iman harta gama gyaran dakin, yayi kyau sosai, ga fili ya kafa fitowa. Dayake ba wani zama ake a dakin ba sam ba wani datti, kallan kasa tai tace “Iman bakiga bakar leda ba?�?
Iman ta mike daga kwanciyar datai saboda gajiya tace “Yaya Ibty? Kin tashi? Kanki ya daina ciwon?�?
Kai ta daga a hankali, tace “bakiga leda baka ba?�?
Ta daga kai alamaf eh tace “Na duba ko ina banga komai ba.�?
Mamaki ne ya kama Ibty tabbas taga leda yaza’ai yanzu ace ba’a gani ba?
Haka tai ta abubuwa cikin daurewa, zuciyarta cike fal da tunani, ita kanta Iman ta kasa sake ranta saboda halin dataga Ibty dazu.
Bayan Magrib Aminu yakaiwa Hajiya abinci ko zama baiba ya fito dan gaba daya hankalinsa nakan Ibty gaji yake wani abin zai iya samunta bayanan.
Hajiya ganin ya juya daga ajiye abinci yasa ta tabbatar lalai Ibty ta gama rabata da Aminu, ta kuma tabbatar magani tamai ta kwace yaran da ko maganar iyayensa baji yake ba akan tata.

******
Biyawa yai ya siyo gasassub kaji ya kawo, Ibty ta hada musu nasu, tana kokarin daukan na Aminu taji Iman tace “Yanzu Yayan shi kadai zaici? Ke wlh Ya Ibty kina neman bani kunya, wayace miki Amarya nacin abinci daban da Ango? Dazu duk ina kallan yanda ya damu da halin da kika shiga, baiji kunyar rungumeki a gabana ba sai ke kamar wata ‘yar kauye.�?
Harara ta maka mata tace “Ce miki akai bamacin abinci tare?�?
“To in kinaci ki wuce kuje kuci mu ki barmu.�?
Ibty ganin Iman zata rainata yasa ta kara musu sannan ta dauka ta dau juice ta nufi bangarensa.
Yana zaune yana aiki a laptop dinsa, ta karasa ta daura akan centre table tare da matso dashi kusa dashi, kallanta yai yace “Yanzu ya kikeji?�?
Tace “Bayan nayi magrib na yi addu’oi sosai yanzu jikina komai lafiya.�?
Kai yadan daga yace “Bakiga abin ba kuma?�?
Ta daga kai cikin damuwa tace “Na kasa gane meke faruwa�?
“Kila ko ya shige wani gun, daga yanzu dai in kinga abu karkiyi saurin budewa.�?
“Wannan karan Allab ba tsoro bane yasani na suma, ina budewa naji kaina na juyawa.�?
Shiru yai yana tunani, baisan daga mata hankali hakan yasa yace “Insha Allahu ba komai.�?
Kallan naman yai yace “Duk ni kadai sai kace wani kura?�?
Wuyanta tadan shafa cikin magana kasa kasa tace “Iman ce tace insa mana tare.�?
“And ke kuma dama nasan hakan kikeso ba.�?
“Allah ni bani nace ba itace tace.�?
“Shiyasa dazu naga ina kwantar dake kina kara ririkeni.�?
Fuska tadan canza zuwa shagwaba kadan tace “Kaima ai Iman tace a gabanta bakaji kunyarta ba ka rungumeni………�?
Labanta ta hade da sauri saboda kunyar abinda tace, “kunyar me zanji? Bayan bakida lafiya?�?
Kallan mamaki tamai, ya dauke kai tare da daukan nama daya ya kai bakinsa, kallansa take haryanzu.
“In kallona kikesanyi ki bari in nai bacci sai ki sani a gaba kiyi tayi harsai ya isheki.�?
Fuskarta ta rufe, itakam ya zatai da mutumin nan.
Dakyar ta dau cinya daya shima dakyar taci, shikam yana gama ci yasha juice sosai, mamaki duk ya hanata sakewa, shifa yace bayacin abinci da mutane sai su Baffa.

*******
Da daddare sai dayaga tayi bacci sannan ya hau kan gadan, ido yadan zuba mata kadan yana tuno yanda hankalinsa ya tashi dazu, da halin data shiga.
Tabbas abin kunya ne ke neman afkuwa dashi dan tabbas ya fara san kasancewa da ita wanda a gunsa ba karamin abin kunya bane aure ko wata baiyi ba ace yarinya karama ta shiga ransa haka.

Ibty kam tayi addu’oi sosai kafin ta kwanta, sai dai cikin baccinta ta dinga ji kamar ana kiran sunanta, tsoro ne ya kamata ta dage tana addu’a tare da matsowa kusa da Aminu, hannu tasa ta rikoshi sosai ta shiga jikinsa, jinta a jikinsa yasa yadan bude ido, kanta nakan kirjinsa ta sa hannunta akan cikinsa, shiru yai tare da dan lumshe ido wata irin sha’awa na sake tasomai, yanzu kamar shi sha’awar yarinya kamar Ibty itace ke neman fin karfinsa?
Dakyar bacci ya daukeshi dan sam ya kasa yin baccin ya kuma kasa yin rufda ciki balle ya samu sa’ida.
Itakam jin mutum a kusa da ita yasa bacci mai dadi ya tafi da ita.
****
3/12/22, 12:17 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
31
Baccin nasa ma haka yayishi cike da mafarkai, bayan yayi sallar asuba ya zauna a falo kawai yadau wayarsa ya fara duba yanda miji zai nemi karamar matarsa. Kunyar kansa ne ya kamashi yai saurin rufe wayar tare da shafar fuskarsa, yana zaune yana jiyo karatunta mai dadi, sai data gama sannan ya mike ya shiga cikin dakin tana ninke sallayar.
Dan gyaran murya yai bayan yayi sallama, ta amsa cikin murmushi sannan ta gaisheshi.
A bakin gado yadan zauna tare da daura hannunsa akan cinyoyinsa yace "Kanki fa? Ya daina ciwon?"
Cikin jin dadin tambayarsa tace "Ya daina, garau nake jina."
Kai yadan jinjina yana kallanta, karasowa tai ta dan kishingida a inda take kwanciya, shiru ne yadan ratsa dakin kafin yace "Gobe zaki school din ko?"
Tace "Eh! Amma sai wajen 10 haka zamu tafi da Ainah."
Kai ya sake jinjinawa dan juyowa yai kadan yana tunanin tabota, da sauri ya juyo wannan abin kunya dame yai kama? Da sauri ya mike ya koma inda ya sana kwanciya ya juya mata baya yana tunanin shi yazaiyi ya nemeta? Na'imah dama soyayya ce ta hadasu sannan ba wani ratan shekaru bane tsakaninsu, daren farkonsa sai daya gwangwaje, amma Ibty ba auren soyayya ba, sannan gata yarinya sa'ar kanwar kanwarsa, in ya nemeta taje taba Ainah labari fa? Shikenan girma da mutuncinsa sun zube.
Itakam Ibty bata dade ba wani baccin yadan dauketa, sai dai yanzun ma ji take anata kiranta, bata amsa ba sai dai ta bude idanunta ta sake jero addu'oi tana tunanin wannan wani irin abu ne yake faruwa da ita tun jiya?
****
Wajen karfe takwas ta tashi ta nufi bangarenta, kitchen ta shiga ko minti goma batai ba saigasu Islam sun taso, nan fa suka fara hidima, Iman ma ta taso ta fara gyaran gida, ta gama abinci ta sa musu sannan ta nufi dakinta, gaba daya tsoron dakin take, haka tai wanka tasa kaya kwalliya ma kayan kwalliyar ta kwasonta shiga dakin da Iman take kwana tai, abincin Hajiya ta zuba a flask sannan tasa a basket.
Bangaren Aminu ta nufo dan ta duba tagani ko ya tashi, shikam yana zaune yana sake duba waya dan maganar gaskiya matsuwarsa ta fara kure tunaninsa, har haushin kansa yakeji, dan yanzu ma dayaje wanka ya dade yana zubawa kansa ruwa kafin ya samu salama.
Tana shigowa yai saurin ajiye wayar tare da lankwashe kafa yana dan girgizawa, sallamarta ya amsa yana kallanta baisan sanda idanunsa suka tafi kallan surarta ba, idanunsa ya kawar da sauri.
Iman tana daga bakin kofa tace "Ya Aminu breakfast."
"Okay!Ganinan zuwa."
Ya fada sannan yadan runtse ido kadan tare da shafar saman goshinsa, mikewa yai ya nufi falo, yanzun ma samun kansa yai da kallan yanda take ajiye kayan abincin, dan sunkuyawa tai hakan yasa dan saman kirjinta yadan fito, idanunsa ne ya sauka akan kirjinta wani abu yadan hadiya kadan, Ibty ta ajiye sannan tace "Hajiya yau za'a sallamota?"
Yadanyi yake yace "Inaganin yau zasu sallameta dan dama bawai serious bane, rashin bacci ne ya haddasa mata wanda shikuma am sure tunanin ahinda ya faru ne ya hanata, to tunda sun samata drip jiya nasan ta samu bacci so banaji akwai wani matsala kuma."
Kai ta dan jinjina a ranta tace "Tana so dai ta hadamu fada."
Wayarsa ce tadanyi kara hakan yasa ya daukota, daga gun aikinsa ne sai ta koma bangarenta.

*****
A bangaren Hajiya kuwa karfe takwas ya nemi sallama, ance ta jira Aminu yazo tace "Ai bayanan karsu damu."
Hakanan suka bata dan dama suna bata girma dalilin kuwa asibitin abokin Aminu ne, so kowa yasan matsayin ta na sirikarsa.
Tana fitowa ta fada adaidaita, tana tafe tana tunanin cin zarafin da Aminu ya mata, wato jiya tunda ya dungurar mata da abinci bai sake ko kiran waya yaji ya take ba? Lalai yau ta tabbatar Aminu bai dauketa a bakin komai ba kuma yanzu shima zata nunamai yayi babban kuskuren wulakantata.
A bank ta tsaya ta ciro dubu ashirin ranta duk a bace da account dinta dayake zama da kudi sama da dubu dari biyu yanzu tunda Aminu yai aure bai sake turo mata kudin cefanen da take tarawa ba, wai itace da dubu talatin kacal a bank? Ga kudin datake tarawa a gida suma duk sun kare, yanzu data cire dubu ashirin saura mata dubu goma kacal.
Wannan abu ya kara sa taji tsanar Ibty da shi kanshi Aminun ya mamayeta, lalai ko me zatayi sai tayi dan ta kwato martabarta gunshi. Ba uban daya isa ya maidata kauye ko ya maidata cikin wahala.
A kofar gidan boka tai sauka wata katuwar mota ta gani wacce kana gani kasan an kashe millioyin kudi gun siyanta. Shiga tai, ta tsaya a bakin kofa tana jiran na ciki ya fito.
"Hajiya shigo mana muma ke muke jira ai."
Yaye labulen tai, wani babba mutum ta gani wanda kana kallansa kasan kudi sun zauna mai. Hajiya ta zauna malam ya kalleta sannan ya dan bushe da dariya yace "Ai dakinyi sake bakizo da wuri ba wata ta rigaki zuwa da shikenan kinyi asarar babba."
Ta kalleshi tace "Anfara aikin ne?"
Ya bushe da dariya yace "Yau akwai sa'a a wannan lokacin domin babban aljaninmu yana nan kusa damu a shirye yake daya biya muku bukatunku, sai dai shima yana jiran a biyamai tashi bukatar."
Kallan mamaki tamai ita takaicinta meyasa bazasuyi magana a sirri ba? Ya ajiye wani mutumi anan?
Kallan mutumin taga yayi yace "Wannan wani babban dan siyasa ne wanda shima yazo a biyamai bukatarsa, basai kowa yasan bukatar kowa ba, sai dai aljani yana bukatarsa ya sadu da mace wacce ta wuce shekara 60 ni kuma nasan bukatarku tafi ta wasu, sannan kema kinsan naki maganin baya aiki sai kin bari na isar da sihirin jikina naki tukunna. To shine yanzu zan fara mika nawa sihirin sai shima ya mika nashi, daga kuma wannan lokacin zakiyi mamaki kwarai da aikin da zamu gabatar."
Kallan tsoro tamai yana nufin maza biyu ne zasu kusance ta? Sai dai in taki amincewa shikenan rayuwarta ta kare.
Hakanan ta shiga daki Malam ya biya bukatarsa sannan ya fito, shima wannan babban mutumin ya mike tare da kade riga ya shiga, tashin hankalin da bata taba fuskantaba a iya tsawon rayuwarta domin mutumin nan jinshi tai ya shigeta ta baya, wani ihu tasa ta fara kokarin tureshi, cikin karfe ya riketa ya shafa magani ta cigaba da abinda ya dameshi. Hajiya raban datai hawaye harta manta yau sai gashi tana zubar da kwalla saboda bata taba zatan wannan abun zai faru da ita ba.
Bayan ya gama da kyar ta ja jikinta ta fito nan Malam yace “Yanzu kije gida kwana biyu kacal zaki bamu zakisha mamaki.�?
Haka ta ajiye kudi ta fito dakyar ta shiga adaidaita, tana tafe tana share kwalla.
****
Aminu yayi mamaki dayaje asibiti akace ai an sallameta bayan Bala bai sanar dashi dawowarta ba, hakanan ya koma yana shiga ya ga kofarta kuma a bude, wannan ne yasa yai tunanin Bala bai kula ba da sanda ta dawo.
Haka ya duba jikinta, duk ya lura yanayinta ya canza, sai dai yasan rashin lafiya ba dadi yasa baice komai ba, haka ya fito bayan ya ajiye abincin sannan ya koma gida.

*****
Yau da daddare kamar yanda ta saba tai wanka tasa doguwar rigar bacci mai hannun vest, ta sa hijab ta nufi bangarensa. Iman tana tsorkanarta wai kamar wata matar malam, a gidanta ma sai tasa hijab?
Ibty ta harareta tace “Da agaban su Islam kikesan insa rigarnan?�?
Iman ta kalli rigar tace “Meye da rigar? Da ace irin sexy rigarnan kika saka shine ma za’ace kina kunya amma wannan? Ko Umma zata saka.�?
Duka ta dan kawo mata da sauri ta matsa tana dariya, Ibty ta dau kayan tea sannan ta wuce.
Shiga tai bayan tayi sallama, Aminu yana zaune yana dane dane a laptop, kallansa tai bayan ta ajiye itakam haka zasuyi ta zama suna kallan juna? Ummy tace ta dinga kwana dashi, to amma gashi sama da sati suna kwana tare ko rungumarta bai taba yi ba.
Haushi ne yadan kamata ganin yanzun harta ajiye kayan tea ko kallanta baiyi ba, da saninta tadan bige kafarta a jikin gado a hankali sannan ta rike kafar tare dayin kara.
Da sauri ya ajiye laptop din a rikice ya karaso tare da riketa ya zaunar da ita kan gado tare da dago kafarta, “Nan ne?�?
Ganin yanda ya rikice yasa dadi yadan kara kamata tadan fara abin mai kuka tace “Na ajiye ma kayan tea ban kula bane na bige.�?
“Seriously? Nikam sau nawa ne zaki dinga tafiya bakya kula?�?
Cikin dan shagwaba tace “Yanzun Ma yarinyar za’a cemin?�?
Yadan hade fuska yace “Then?�?
Tace “Allah tsautsayi ne.�?
Kallan yanda tai magana yai wani abin ne ya sake ratsashi, gashi dama ya riketa ya kuma irin runkufo din nan, zama yai a kusa da ita yasa hannu ya riko habarta yace “Tsautsayi?�?
Kai ta daga tanajin wani irin a jikinta saboda yanda ya matso da daf da ita haka, balle yanda ya rike habarta.
A hankali tadan daga kai alamar eh, kamar zai kai bakinshi cikin nata sai kuma ya saketa tare dayin gyaran murya ya koma ya zauna.
Itakam Ibty ta gama saduda yau mai afkuwa zata afku ganin yanda ya ke kokarin yin kiss dinta, jin ya saketa yasa ta kalleshi, me nake tunani? Menene matsayina? Haka ta mike kawai ta kwanta jikinta duk yai sanyi.
Shikam kasa aikin yai har lokacin kwanciyarshi yai ya kashe wuta ya kwanta, sam ya kasa bacci yau abin yafi jiya dan sam ya kasa maida sha’awarsa.
Wajen karfe daya na dare kawai yakai hannu kan cikinta, Ibty cikin bacci taji hannu, tayi tunanin ko cikin bacci ne shima bai sani ba, sai dai jin an jawota ta hadu da jikinsa yasa tasan idansa biyu, a hankali ya fara kai hannu saman kirjinta, sam idanunsa sun rufe wata muguwar sha’awa ke sake ratsashi, Ibty kam tsintar kanta tai cikin yanayin da bata taba tunani ba, gaba daya tayi lumu kamar jikaken tsuma sai dan lumshe ido take, hannu yasa ya juyo da ita rigingine sannan ya matso a hankali ya rabata da rigar jikinta, idanunsa a rufe suke jitai bakinsa cikin nata, nan fa komai ya kunce domin ita kanta samun kanta tai tana maidamai murtani.
Hmmmmm abin nema ya samu dan Aminu sam ya gama fita a hayacinsa, duk da haka bai mata karfi ba yabi da ita a hankali, sai dai tadansha wahala dan Aminu yana cikin bukata sosai.

Nikam Ayusher dama kunsan ana fara haka zan tattara kayana na basu guri abinka da sirrin ma’aurata🙈🙈

*******
Suna gamawa yadan kwanta rigingine yana maida numfashi, Ibty kam mikewa tai a hankali, ga jini duk ya bata bedsheets din, toilet ta nufa tana dingishi, nan ta tara ruwa a baho na na zafi sannan ta shiga ciki tana runtse ido saboda zafin da takeji.
Kunyar kanta ne ya kamata, da gaske Aminu shine ya nuna mata kulawa dazu? Ita dama batasa akanta ba, dan ko tana karanta novel intaji ance namiji yakai mace toilet daren first night ya gaggasa mata jiki gani take sai wanda suka mato akan san juna, itakam tasan Aminu bazai aikata hakan ba, shiyasa bata daurawa kanta ba, gwara ta mike kafin taga ya mike taji ba dade ya shareta…�?
Bata gama tunaninta ba taga an turo kofar toilet din, cikin sauri tadanyi kasa dakai saboda kunyar yanda take, daga bakin kofa ya tsaya yana sanye da towel yace “Are you okay?�?
Kai ta daga a hankali tace “Eh.�?
Dan shiru yai kafin yace “Banji miki ciwo badai ko?�?
Kai tadan girgiza alamar a’a duk da batasan ya ake gane jin ciwon ba sai dai bataso yaji ba dadi.
Dan murmushi yai sannan ya maida mata kofar ya rufe, daki ya koma ya dan zauna a bakin gado tare da dan shafar fuskarsa, shikenan girma kuma ya fadi yanzu kam.
Nace daga baya kenan🤣

*******
Sai data canza bedsheets din bayan yana toilet sannan ta kwanta, kunya haryanzu ta kasa sakinta, tanajinshi ya dawo ya kwanta shima, ji take kamar tadan shiga jikinsa ta rungumeshi suyi bacci a haka, sai dai yanda ya juya baya yasa tasan ba zata iya ba.

Cikin baccinta ta dinga ganin wani abu mai ban tsoro wanda bata taba ganin irin hallitarba yana biyota a cikin wani bakin daji, gudu take iya karfinta sai dai abin yaki daina binta, gaba daya zufa ta gama karyo mata ta ko ina, sai girgiza kai take cikin bacci.
Aminu cikin bacci yaji kamar ana motsi da karfi, gashi basu dade da kwanciya ba, juyowa yai ya dan kunna wayarsa, ganin yanda take gumi yasa ya jawo ta jikinsa ya na tofa mata addu’a.
Gaba daya tausayinta ne ya kara kamashi, badai karfi ya nuna mata ba har take zabura cikin bacci ba?
Idanu ya runtse lalai Aminu baka kyauta ba. Haka yai tadan shafa bayanta kafin bacci ya dauketa.

*****
3/13/22, 21:16 - Ummi Tandama😇: *SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣�?*

*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣️🗣️*

*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣️🗣️🗣�?*

*NUCEEYLUV😘 NA MUKU ALBISHIR DA DATA DINTA ME SAUKI AKAN FARASHI ME RAHUSA, MAZA KU GARZAYO SAUKI DATA A CANCARE KU DA DATA A BAGAS🤸🏻‍♀�?, TURAWA BABU BATA LOKACI 📤👌🏻*

*MTN*
50mb-50
150mb-100
500mb-200
1GB-300
2GB-600
3GB-900
5GB-1500
10GB-3k
20GB-5k

*Codes for check balance, *131*4#*
*1MONTH VALIDITY*

*AIRTEL*

100mb-150
300mb-250
500mb-300
1GB-600
2GB-1200
5GB-3k
11GB-4500

*Codes for check balance, *140#*
*1MONTH VALIDITY*

*GLO*
1.35GB-550
2.9GB-1200
4.1GB-1600
5.8GB-2200
7.7GB-2600
10GB-3200
14GB-4k

*Codes for check balance, *127*0#*
*1MONTH VALIDITY*

*9MOBILE*
1.5GB-1200
2GB-1500
3GB-2k
11GB-4k

*Codes for check balance, *228#*
*1MONTH VALIDITY*

CALL 09039118754 OR CHAT ME PRIVATE 09039118754�?

*YADDA ZAKI BIYA, ZAKI TURO KUDI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 1445626295. NUSAIBA MUSTAPHA ACCESS BANK*

*IYA KUDIN SIYEN DATA IYA SHAGALIN KU🤸🏻‍♀�? BANA AMSAR KATI PLS😁👌🏻, KADA KU BARI AYI BA KU WANNAN GARABASAR😍, ZAKU IYA SAVING NUMBER NAN 09039118754 DOMIN SIYEN DATA KAI TSAYE BABU BATA LOKACI KO BANA ONLINE KU KIRA KAWAI MASOYA💃🏻*

💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

32

Idanu ya bude jin alamun kiran sallah, wani irin bacci yakeji gashi yau Monday, dan gyara kwanciyarsa yai tare da sake rungumeta a kuma take ya tuno wacce ya runguma da abinda ya faru dasu a daren jiya, nan fa idanunsa suka dan firfito, a hankali yasa hannu yana kokarin zareta daga jikinsa. Ibty kam wani baccin dadi ne yake kara kamata nan ta kara makaloshi, hannu yasa yadan shafi goshinsa ya zaiyi ya janyeta? Banda abin kunyar daya tafka jiya yanzu inta ganshi a haka ai shikenan ya gama yawo.
Sake kokarin zare jikinsa ya sakeyi cikin sanda kamar irin munafikin nan, dakyar ya samu yadan janye hannunsa daga jikinta, yana kokarin zare gangan jikinsa ne itama tadan bude idanunta, da yake yadan kunna fitilar wayarsa yana san ganin yanda zaiyi dabarar janyeta. Nan fa idanunsu suka hadu da juna, cikin sauri ta nemi mikewa ganin yanayin da suke, shima cikin sauri ya nemi janye jikinsa ji kake kum sun mauje gushinsu, cikin jin azaba ta saki dan kara, da sauri yasa hannu ya toshe mata baku, idanunta ta sadda kasa tana neman mulmula gun dan taji zafi. Shikam idanu yadan runtse kadan, bayan ciwon daya ji mata yau yanzu ma ya sake wani.
Daurewa yai cikin maganar rada yace “Yi mana uzuri da ihun nan kar Iman taji.�?
Kai tadan jinjina, sake bakinta yai a hankali taji yace “Sorry!�?
Kallansa tai harya mike yai toilet, sannan ta hau shishitu tana sosa gun, garin ya suka kwana a haka?
Sai kuma ta rufe fuskarta da sauri tuno yanda jiya ya dinga sarrafata lalai jiya ya manta da shekarunta, dan san girma irin na Ya Aminu da yai yawa.
Nan tadan ja bargo ta shige ciki ita kanta kunyar abinda ya faru jiya takeyi.
Shikam a toilet bayan yayi alwala tsayawa yai yana dan sauke iska, dolene ya daure fuska ya nuna kamar wani abu bai faru jiya ba. Sai dai anya zai iya? Dan tabbas a yanda yake jinsa baiki yanzu ya jawota jikinsa ba.
Kai ya girgiza da sauri tare da sake zuba ruwa a fuskarsa lalai Aminu, wai kaine ka koma haka? Sa’ar Ainah ce fa? Banda girman daka zubar jiya yanzun ma neman zubar da wani girman kake?
Haka ya d’aure fuska ya fito daga toilet, ko kallan kan gadan baiyi ba ya fito daga dakin, itakam sai dataji alamun rufe kofarsa sannan ta fito daga cikin bargon tare da yin murmushi da kyar ta sauko daga kan gadan, ta dade tana sake yin tsarki da ruwan dumi dan haryanzu zafi gun yake mata.
****
Bayan ya dawo daga masallaci yana juyo karatunta, harta gama, yau bai nufi dakin ba ya dan kishingida a falon tare da rufe idanunsa. Ita ma ganin ta kammala karatunta ta fito zata wuce bangarenta dan shirya yara zuwa makaranta.
Ganin sa a falo yasa tana daga dan nesa kadan tace “Ya Aminu ina kwana?�? Kasa amsawa yai dan ji yake kamar yana bude ido zai ganta daf dashi tana mai kallan abinda yai jiya. Ita kuma jin shiru yasa ta dauka ko bacci yake, bata kawo komai ba ta wuce bangarenta tana tafiya a hankali.
Juyowa yai yadanbi bayanta da kallo, ganin yanda take tafiya yasa kunya ta sake rufeshi, idanunsa ya maida ya rufe, shidai kam tabbas ya tabbatar ciwo yaji mata dan Na’imah ba abinda tai, ko jinin da ake cewa anayi ita batai ba, daya mata magana tace ai ba kowace mace keye ba, sannan ya tafi da ita cikin soyayya ne shiyasa wai duk wacce tai jini to karfi aka mata. Wannan tunanin shiya sake tabbatar mai da abinda take nufi.

******
A bangaren Hajiya kuwa duk yanda taso tai bacci ta kasa, juyi kawai takeyi saboda takaici da zafin da takeji daga duburarta, lalai itakam dole ta nemo wata hanyar dan bazata yadda ta dinga kwanciya kowa yana hawa kanta ba, to me zai hana ta nemo karuwa? Ko irin ‘yan duniyan nan ta biyash kudi su aure Aminu? Bayan aure su hada kai su saci kudi mai yawa su gudu?
Wani murmushin jin dadi tai lalai ba shakka inada kwakwalwa, na kuma tabbatar ni ba jinin talaka bace ba kuma a kauye na cancanci rayuwa ba.
Tunowa tai da yanda suka ja Aminu itada Na’imah, sai kuma ta saki murmushi tace “Wato banaji za’a samu munafiki mai fuska biyu irin Na’imah!�? Tai ajiyar zuciya gashi yanzu ta tafi ta barni inata saka da warwarewa.
Wayar boka ce ta shigo wayarta karfe shida na safe, kamar bazata dauka ba sai kuma ta daga tana ayyana inda zuwa ne wlh bazatai ba.
�? Hajiya muna cikin matsala!�?
Tadan harari wayar tace “matsalar me? Bayan wacce ka sani jiya?�?
Yai tsaki cikin takaici yace “Jiya aljaninmu yaje dan a karasa farrakasu sai dai ya dawo ya sanar damu sun sake hadewa, dole dole yanzu akan Aminu kadai za’ai aikin, zamu turamai muguwar tsanarta cikin ranshi, in da yanda zakiyi ki hada da zargi ki hada, daga sanda ya tsaneta zai saketa ba’a hayyacinsa ba kinga shikenan komai yayi daidai, ita kuma dama mun fara aikinmu na hanata kwanciyar hankali a gidan.�?
Hajiya tadan mike tsaye tace “sun sake hadewa kamar ya? Badai sun sadu da juna kake nufi ba?�?
“Ni Allahn musurune da zan sani? Kwalbar da muka hada aljani ya nuna min kwalbar sun hadu, wannan saduwa da rashinta ya rage naki ki bincika.�?
Wani dogon tsaki taja tace “Dama yanzu na kula aikinka sam ya daina aiki, inba haka ba taya karamar yarinya zata tsaya tana wahalar dakai? Ni in har baka sa ya saketa ba to kasa ran bazan sake zuwa gunka ba.�? Bata jira mai zai ce ba ta kashe wayar tare da cillata kan gado. Goshinta ta dafa tana fitar da wani huci na takaici, dayan maganin da wannan malamin ya bata ta dauko ba shiri ta fara dama kunun kanwa dashi, ta gama ta juyeshi a flask, sannan ta fito waje wurin karfe bakwai, gun Bala taje tace “Bala dan Allah in Aminu ya fito kace ina san magana dashi.�?
Yace to sannan ta juya bangarenta.
Gidan ubanwa zata sa zargin Ibty aran Aminu bayan kullum tana gida? Sannan bataga alamar tana yawo ba balle tasa ran akwai wanda yake santa. Wani dogon tsaki ta sake ja, lalai bokan nan ya tabbatar mata aikinsa ya daina ci. To yanzu ita zata dau komai a hannunta.
****
Duk motsin datai idanunsa na kanta ta kasan ido, har suka gama cin abinci, sam idanunsa da nata basu hadu ba, ko alamu yaga tana san kallansa da sauri yake dauke kai, itama ya kula da hakan, sukam su Islam sai zuba labari sukeyi har aka gama suka fito, Iman ma ta shirya cikin nata kayan makarantar dan Aminu zai saukesu sai ya wuce gun aiki, saboda Mamman sunyi tafiya da Abba.
Har yakai bakin kofa ta daure tace “Ya Aminu!�?
Tsayawa yai yadan kalleta kadan fuskarsa a dan daure, harta karaso yana kallan yanayin tafiyarta, tadan matso tana wasa da hannunta tace “Anjima zamu makarantar da Ainah……�?
Cikin sauri ya katseta “A’a ki bari sai gobe.�?
Kallan mamaki tamai tace “Jiya da daddare na…�?.�?
Nan ma ya katseta yana dan sa hannu a aljihunsa yace “Ki dai bari sai gobe, bakiga yanayinki ba? Ko so kike kowa yasan�?..�?
Sai kuma yadan juya baya yace “Ki dai bari sai gobe, registration ne ai ba wani abin.�? Bai jira tace komai ba yai saurin fita.
Baki tadan turo sannan ta juya ciki duk ranta ba dadi, aikam Ainah dole tai hakuri tajirata suje tare dan sam batasan zuwa ita kadai ji take kamar Umar zai bita school din.

******

Suna fitowa Bala ya sanar dashi sakon Hajiya hakan yasa yai parking ya kalli Iman yace “Iman bari nadan shiga yanzu zan fito. Mamaki nenya kamata wai dama a jikin gidan take? Lalai itakam tunda Allah ya halliceta bata taba ganin wannan kwamacalar ba, yana zaune tana kallanshi harya shiga, kallan Ilham tai tace “Dama Hajiya anan take?�?
Islam tai caraf tace “A’a da cikin gidan mu take yanzu ne aka mata katanga da gate dinta.�?
Idanu Iman ta zaro tace “Cikin gida?�?
Kai ta daga tana cewa “Da mun dauka saboda Dady yayi aure ne aka maidata can amma Aunty Ibty tace ita kawar Aunty ce, ko Ilham?�?
Kallansu kawai Iman take tana mamakin kalamansu, cikin dan bugar ciki tace “Waye ya fara muku da saboda Dady yayi aure ne aka maidata can?�?
“Hajiya!�? Abinda Islam tace kenan tana kallan window.
Iman tai shiru tana tunanin wannan lamari, lalai ba shakka Hajiyan nan neman hada Ibty take da jikokin ta inba haka ba meya kawo zancen nan? Takaicinta daya Ibty sam ta fiya kawaici, balle tasa ran zata dau mataki. To wai ma uban me matar take anan bayan ‘yarta ta rasu?
*****
Gaisheta Aminu yai sannan ya tambayeta jikinta, ta amsa cikin jin dadi, tace “dama da safe ne naji sha’awar shan kunu to dana tashi damawa sai na manta na dama dakai dan nasan yanda kake san kunu sosai, to kuma banasan na mika ma cikin gida saboda kar Amarya taji ba dadi, shine nace ama magana ko office ka wuce dashi.�?
Cikin jin dadi ya dau flask din yace “Nagode sosai Hajiya sannan Ibtisam bazata ji haushi ba dan kin kaimin, kun dan samu sabani ne amma tanada fahimta da zurfin tunani.�?
Kallansa tai cikin ranta tace “Tabbas Aminu ya fara zaucewa akan tsinaniyarnan.�?
A fili tace “Ai da alama kayi sa’ar mata, bandauka akwai masu tunani a shekarunta ba. Sam batada rawar kan yaran xamani.�?
Murmushi taga yayi yace “Ni kaina wani sa’in mantawa nake da shekarunta saboda hankali da tunaninta.�?
Daukan flask din yai yace “Bari mu wuce kar muyi latti.�?
Ko magana ta kasa yi haka ta saki baki tana kallansa harya fita, Lalai Aminu ya zama asarare akan yarinyarnan, ta kuma tabbatar asiri sukamai dan ko sanda yake gigin san Na’imah saboda karfin magani yana kunyar yabanta a gabanta, amma yau ko kumya yake yaban yarinyarnan?
Iman tana zaune taga ya fiyo da flask ya ajiye sannan sun tafi, mamaki yabi ya isheta, gashi abin takaici an hanasu zuwa da waya makaranta tabar tata a gida balle ta sanar da Ibty abinda wannan matar keyi.

******
Saukesu yai ya wuce office yana aiki sai dai jefi jefi yana tsintar kanshi da tunanin Ibty, wannan karan shine karo na hudu daya dau wayarsa yana san kiranta sai ya ajiye, kunun nan ya jawo ya cika cup ya zauna yana sha.
Sako ya tura mata ganin hankalinsa ya kasa kwanciya.
“Kin warware?�?
Kallan sakon tai sannan ta turamai da reply “Eh, ya aikin?�?
Kamar zaiyi reply sai kuma ya ajiye wayar tare da kifata.
Ganin yakiyin reply yasa ta kirashi.
Dagawa yai tare dayin gyaran murya, “Ya aikin?�?
“Alhamdulila! Sai ke kadai?�?
Ta daga kai kamar yana ganinta tace “Na saba ai baya damuna.�?
“Keda gidanku keda mutane ta ina kika saba?�?
Tadan gyara kishingidar datai tace “Dayake banasan zaman falo saboda kar…�?.�?
Sai kuma tai shiru, murmushi yai yace “Saboda kar mai karfin jini ya shigo ya zaneki?�?
“Ya zaneni kamar ya? Sai kace ‘yarsa?�?
“Dake da ‘yar tasa menene maraba? Tunda ko fita baki isa kiyi ba sai da saninshi?�?
Tadan turo baki kadan, “baki kika turo ko?�?
Kallan gefe da gefe tai da sauri tace “Umm?�?
“Harda kunkuni ma hala kinyi? Da na hanaki zuwa makaranta.�?
Ta girgiza kai da sauri tace “A’a banyi ba.�?
Shiru suka danyi kai kace wasu kurame, ganin ba abin cewa yasa yace “Ina aiki ne later.�? Bai jira me zata ce ba ya kashe wayar, yanasan ya cigaba da zolayarta amma inya tuno da abin jiya sai yaji kunyar kansa da kansa.
Yasha kunu yafi kofi daya sannan ya cigaba da aikinsa.

******
Hajiya sai safa da marwa take a falo tabbas dole ta samu yarinya ‘yar duniya mai kyau da cikar zati sannan dolene tayi abinda zata dasa zargin Ibty a zuciyar Aminu dan ba shakka yanda yau ya nuna mata tabbas Aminu ya gama fadawa san Ibty ta kuma tabbatar nan bada jimawa ba zatasa a koreta.

{Nace wannan mata anyi tsinaniya mara imani🤧}
3/14/22, 21:46 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bankima

33

Iman tana dawowa daga school ko zama batai ba ta ja Ibty cikin dakinta, a bakin gado suka zauna ta kalli Ibty cikin kulawa tace "Yaya dama matarnan a jikin gidanki take?"
Yanayin fuskarta ne ya canza ta danyi murmushin yake batace komai ba, "hauka kike Ya Ibty? Taya zaki bar matarnan a kusa dake haka? In taimako yake san mata ya nemar mata gida a wani gun mana dole sai daf dake haka?"
Shiru Ibty tai dan itakam batasan me zatace ba, hannu Iman tasa tadan riko hannunta tace "Ki cire wannan sanyin naki ki kwaci mijinki, wlh in bakiyi wasa ba sai tasa an sakeki, yanzu yau zamu tafi ta ba Ya Aminu abu a flask, kina zaune a gida tana doramai abu, kinsan da wace zuciyar takeyi?"
Kallanta tai idanunta suka dan ciciko da kwalla, maidasu tai tare da daga kanta sama tace "Karki damu, Allah yana tare dani sannan Ya Aminu yasan me yakeyi sanda ya fahimci halinta shi da kanshi zai sallameta."
Tsaki Iman taja tace "Zama zakiyi tayi kenan harsaj sanda yasan halinta sannan zai dau mataki? In kuma kafin yasan halin nata ta gama yi miki sharri fa?"
Shiru tai tare da dan dafa kanta, Iman ta dan juyo da ita tace "Wlh koni akawa aure sai na fiki iya kissisinan jan miji, ke kenan kamar wata matar liman, bakya janshi a jiki, ga mata a kusa dake tana neman shiga tsakaninku?"
Mikewa Ibty tai tace "To ya kikeso nai? So kike inje ince ya koreta ko me?"
Iman ta mike itama tace "Wai ke dan Allah kamar wata mara wayau? Ki ja Ya Aminu a jiki yanda zai manta da komai sai ke, daga sanda ya mato a kanki kisamu ya canza mata gida, shikenan."
Murmushi tai a ranta tace "Gani kike kamar jan nashi sauki gareshi."
Kamar Iman ta shiga ranta sai jitai tace "Ki cire wata kunya da wani shekaru ki tarerayi mijinki, duk shekarun namiji tareraya tana sa ya ajiyeshi ya koma yaro."
Baki ta bude tace "Tashi ki fita! Lalai karatun novel yasa gaba daya kinzama fitsarariya."
Iman ta fita tana cewa "Nidai wlh na fada miki, wannan wani irin abu ne banbarakwai?"
Tana fita Ibty ta zauna a bakin gado, tabbas dolene ta cire wannan shirmen kunyar tata taja Aminu a jiki, wayarta ta dauko ta kira Ainah sukai maganar sanda zasu makaranta gobe, suna kokarin yin sallama taji Ainah tace "Wai ga Ummy."
Amsa tai cikin girmamawa suka gaisa, Ummy tace "Ibtisam sannu da kokari Aminu yace ashe har abinci kika yiwa matarcan da batada lafiya."
Kai tadan yi kasa dashi tace "Ummy to ya zanyi?"
Tausayinta ne ya kamata tace "Allah dai ya miki albarka, nasa anata sauka insha Allahu duk wani kadarin matarnan ya kusa zuwa karshe, kedai ki kara hakuri ki kuma rungumi mijinki."
Cikin girmamawa ta amsa da to sannan sukai dan hira sukai sallama.
Kallan wayar tai tare da sauke ajiyar zuciya, dole fa ta mike tsaye da alama kamar yanda kowa ke sanar mata.

*****
Aminu kam lokacin tashi yanayi ya mike bai kara lokaci ba kamar yanda ya saba, gaba daya hankalinsa yau yini yai yana tunanin Ibty, sam ya kasa manta yanayin daya shiga daren jiya, anya badan ya dade bai kusanci mace bane? Dan ji yake kamar bai taba jin dadin mace ba irin jiya.
In wannan tunanin yazo mai da sauri yake kawar dashi da cewar ya manta saboda shekararshi biyar da rasuwar Naimah.
Jakarsa ya dauko da flask din Hajiya kasan ransa murmushi ne fal, shikam yanzu yanaji bazai iya hakuri da Ibty ba dole zai ajiye duk wani girmansa ya koya mata sanshi, dan shikam yanzu ji yake yana bukatarta a kusa dashi.
Da wannan tunani ya shiga mota, yana tafe yana dan murmushi shi kansa har mamakin kanshi yakeyi, yana kokarin shan layin gidansu yaga samari guda biyar a tsaye kamar jiransa sukeyi, yana neman wucesu yaga sun nunamai sanda daidai saitin glass din motarsa ta gaba. Ja yai tare da yin parking, nan idanunsa suka sauka akan Umar wanda yake sanye da riga da wando na jeans, saman goshinsa yadan shafa lalai mutumin nan kanshi ba daya ba, glass din motarsa yada zuge sannan ya dan sa hannu yamai alamar yazo irin kiran da akewa yara.
Umar ya kalleshi sannan ya kalli abokansa, ya nuna kansa da yatsa yace “Kana nufin ni nazo?�?
Kai Aminu ya daga mai tare da sake mai alamar da hannunsa, Umar wani irin zazzafan takaici da zuciya ne ya debeshi a fusace ya amshi sadar goraf sake hannun abokinsa ya daga sama zai makawa motar, “Kana sauke gorar nan ka tabbatar zakai kwana cell.�?
Juyowa yai ya bugawa Aminu wani kallo yace “Kana tunanin ina tsoro?�?
Wayarsa ya fito dashi ya danna kiran wani dake jiki an rubusa DPO nunawa Umar yai yace “Bismillah.�?
Umar a fusace ya sake dagawa zai maka wani abokinsa daga ciki ya rike gorar yace “Kai nifa wlh inada yaro karami a gida bazaka sani zuwa jail ba.�?
Umar ya kalleshi tare da fincike jikinsa cikin bacin rai, Aminu ya kalli abokan yace “Nawa ya baku kuka zo aikata abu haka? Duk wanda ya bar wannan wasan shirmen zan bashi dubu ashirin.�?
Ai kallan juna sukai basu tsaya yin wani tunani ba suka matso suna dan rusunawa Aminu, “Yallabai tuba muke wlh muma ba’a san ranmu ya kwaso mu ba.�?
Aminu ya kalli Umar wanda ke wani irin huci, cikin fishi ya daga gorar nan zai sake makawa ai nan abokansa suka hankadashi gefe iya karfinsu ya fadi kasa, ga dama kafarsa haryanzu a kumbure take, idanunsa sukai jaaa ya kafesu da ido yana muzurai yama kasa magana, yana tsaye Aminu ya turawa kowa kudi sannan yasa sumai alkawari akan bazasu kara aikata hakan ba, nan suka juya suka tafi suna tafi suna murna.
Aminu ya kalli Umar dake yashe a cikin kasa, kai ya girgiza yace “Yauma kana san bashin na motar ne?�?
Umar ya mike cikin zafi yace “Na rantse da Allah in baka shiga hankalinka ba zan yi aika aika.�?
“Aika aika? Wadanda suka aikata bakaga ya karshen rayuwarsu ta kasance ba? Wai kai in tambayeka, aikin yi ne bakadashi ko kuma gaba daya rayuwarka akan matata ka daurata.�?
A zabure yace “Matarka?�?
“Taka ce da?�?
Huci ya fara yi cikin kunar rai, “Ka koma gida ka kula da matarka kabar cusa hanci gun matar wani wacce ko sunanka basanji take ba.�?
Kafin Umar yai magana Aminu yaja motarsa, kai ya girgiza cikin bacin rai, yana murnar zuwa gun matarsa wacen dakikin na neman batamai rai.

******
A can gida kuwa Ibty yau ta dage tai kwalliya sosai cikin riga da skirt na atamfa, dinkin ya kamata sosai, yauce rana ta farko datasa kaya ba ko dan karamin mayafi a gidan, ta gyara gashinta tadan daura dankwalli irin wanda ake yayin nan, bayan kanta gashinta ya kwanta tayi kyau sosai.
Kallan kanta tai anya zata iya fita a haka? Su Islam suna Islamiya ga Iman ta fita wai zata gidan kawarta, jin alamun motar Aminu yasa tadan sauke ajiyar zuciya dolefa ta jajirce ita ba kidahuma ba bakuma mara ilimi ba gwara ta nuna wayewarta.
Fitowa tai daga dakin ta nufi falanshi, shima cikin jin dadi ya fito daga mota, duk da ya boye jin dadin amma tabbas zaka fahimci farinciki a ransa.
Kofarsa ya bude tana tsaye, kallanta yai daga sama har kasa, wani irin sanyi da kwanciyar hankali ne ya ratsashi, itama kallansa tai cikin jin dadi tace “Sannu da dawowa.�?
Karasowa ciki yai yace �? Yauwa.�?
Tana tsaye harya karaso inda take, hannu tasa za ta amshi kayan hannunsa “Kin warke ne da kike neman daukan kaya?�? Tambayar daya mata kenan, cikin maganar rada.
Kanta tai kasa dashi tace “Tun dazu nacema na warke ai.�?
“Taka na gani.�?
Dagowa tai cikin murmushi zatai magana, idanunsu suka hadu da juna, bakinsa ya motsa yanaso yace tayi kyau sai dai baisan taya zaice mata ba.
Kanta tadan sauke tare da cewa “Allah Yaya nidai zolayata kawai kakesanyi.�?
Kayan ya mika mata yace “Ungo tunda wahala kikeso.�?
Hannunta ta maida baya tace “Aikuma yanzu na tuna ashe banda lafiya.�?
Murmushi yai yace “Yanzu?�?
Kai ta daga tace “Kaifa ka tunamin.�?
Murmushi taga ya sakeyi, wani irin dadi ne ya kamata, tabbas tanaso taga Aminu na murmushi, shikam ji yake kamar ya rungumota jikinsa amma taya zai jawota? Kartai tunanin wani abin daban.
Idanunsa yadan rufe ya bude, ayi komai a hankali Malam karka tsoratata lokaci daya.
Abinda yazo mai kenan ya wuce ciki bayan ya ajiye flask din, kallan flask din tai da alana shine wanda Hajiya ta bashi, budewabtai ta leka ciki, kunu ne, cikin kunar rai tace “Wannan matar in an bibiya abu ta hada a kunun nan.�? Addu’a ta shiga yi akan Allah ya tsaresu ita da Aminu daga sharrin matarnan.
Kai flask din kitchen tai ta zubarda ragowar kunun sannan ta fito ta nufi dakinsa bayan ta jeramai abinci akan dining.
Ya sa riga kenan ta shiga, “Kinyi missing dan na kula burinki ki shigo ina sa kaya.�?
Da sauri tadan juya baya tace “Nidai Allah bance ba.�?
“Kingama kunyar tawa?�?
Tadan kalleshi kadan ta dauka bazaiyi zancen jiya ba, “Ba kunya ta kike ba tun safe?�?
“Kaima ai kunyata kake yanzu ne ka ware.�?
Kallanta yai ya tako zuwa inda take, tadan sauke kanta harya matso inda take, daf da kunnenta ya matso jitai numfashinta na neman daukewa “Yaushe nace ina kunyarki?�?
Tadan dago tanasan yin magana sai dai yanda ya matso daf da ita yasa ta kasa magana sai dan kif kif da ido datai, jiyai kansa yadan wani sara kadan da sauri yadan matsa kadan daga inda take.
Matsowa tai tadan rike hannunsa cikin kulawa, kallan hannun yai jiyai kamar an doramai garwashin wuta, da sauri ya fizge hannunsa daga hannunta, sannan ya xauna a bakin gado.
Mamaki ya sake kamata tace “Ya Aminu?�?
Kansa yadan dafe ya dan daure yace “Karki damu, bani paracetamol, da sauri ta mikomai ya amsa ta bashi ruwa, ya hadiya.
Dan kishingida yai yace “Jeki zan dan huta maybe zai lafa.�?
Gaba daya jikinta ne yai sanyi matsowa tai tadan dauko pillow ta dan fara kokarin daga kansa, jiyai yanzun ma kamar garwashi na tabashi, bai san sanda yadan tureta ba, baya ta danyi mamaki ya hanata ko magana, shikanshi mamaki ne ya kamashi, kallanta yai jiki a sanyaye “Sorry bansan hanuna ya tureki ba.�?
Kallansa tai jikinta duk yai sanyi ta fito daga dakin, yanzun nan suke hira kamar gaske me kuma ya faru?
Jitai gabanta na faduwa da sauri ta zauna akan kujera tana addu’a itakam meya samu Ya Aminu?
Abinda yabashi mamaki tana fita daga dakin kansa ya daina ciwo, meyasa ya tureta? Bayan tun safe yake kewarta? Meyasa inta tabashi yakeji kamar garwashin wuta?
Idanunsa yadan rufe da alama aikin dayai ne ko kuma bacin ran Umar ne yasa yakejin ba dadi, dan da in Umar yayi abu a hauka yake daukanshi.

********
A bangaren Hajiya kuwa deban maganin nan tai tana tunanin intai kunu gobe dashi tabbas batasan ta yanda zata bashi ba, to meya kamata tai? Tea ya kamata ta hada dashi sai ta nemi yazo suyi magana da daddare inyaso sai tasan yanda tai tasashi yasha.
To amma maganar me zasuyi?
Ko tamai maganar tsohon mijinta mahaifin Na’imah? Tamai sharri akan yanasan ta bashi kudi? Kenan intai haka ta daki tsuntsu da dutse biyu gashi zata samu kudi ga kuma ta bashi tea.
Dariyar mugunta tai, tabbas duk abinda kake nema a duniya indai da kudi da kuma Malam to komai mai yiwuwa ne, wannan maganar ita Na’imah ta fara fada mata sanda ta daukota daga kauye, murmushi tai tace “Kin tafi kin barni ganinan inata amfani da shawarwarinki.�?

*****
{Hmmm nikam wannan tsinaniyar matar ta isheni🤧}
3/16/22, 20:41 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004
2083371244
Zenith Bankima

34
Ibty gaba daya ta kasa gane meke damun Aminu, yanzun ma da yake zaune yanacin abinci a dinning ko kai yaki dagawa ya kalleta, hankalinta ya tashi ko dai shigar datai ne baisan kalla? Amma ai ba haka ya nunaba farko daya ganta, mikewa tai tadan matso kusa dashi tace “in karama salad din?�?
Yana dagowa suka hada ido yaji kansa ya wani sara, cikin dan zafin murya yace “Please dan kyaleni, in inaso zan kara da kaina.�?
Kallansa tai jitai gaba daya idanunta na neman kawo ruwa, jiki a sanyaye ta matsa daga gun ta wuce bangarenta.
Zama tai akan kujera tana tunanin abinda ke faruwa, menene wannan? Canji lokaci daya?
Wayarta ce ta fara kara, jawota tai tana kallan sunan Yaya Bilkisu a jikin wayar, ba shakka Iman ko Umma ne wani ya bata number dan dai itakam sanda taje bata ba taba.
Dauka tai tare da yin sallama.
“Ibtisam na rokeki da Allah ki dawo gareni, wallahi in har na rasaki gaba daya rayuwata zata iya salwanta, ni na amince mu gudu daga garin koma ina ne na baki xabi ki zaba……�?
Gabanta ne yai wani irin faduwa jin muryar Umar na wannan sharhin, cikin fada tace “Ya Umar bakada hankali ne? Ka amshi wayar matarka ka kirani? Sannan ka dingamin zancen hauka na marasa tunani?�?
Abinda tace kenan ta fara kokarin zare wayar daga kunnenta zata kashe, “Wallahi inhar baki dawo gareni ba ki shirya ganin ‘yar uwarki a gadan asibiti, in nan ma bakiji ba to ki shirya ganin ta a kabari.�?
Kamshin turaren data juyo ne yasa tai sauri sauke wayar ta kashe, tana maida wani irin numfashi na ban tsoro, dagowa tai tace “Ya Aminu, nikam inaji Ya Umar ba kalau yake ba, tsoro nake karya yiwa Yyata wani abin.�?
Yanda taga Aminu na kallanta ne yasa tadanyi shiru, gabanta ya fara wani irin faduwa, dan kallan daya mata kallo ne na wanda bai taba yi mata ba a iya xamansu, tsanarta ce karara a idanunsa.
“Dama ni nayi mamakin tareni dayai, da alama ke kika sanar dashi lokacin dawowa ta.�?
Cikin rashin fahimtar kalamansa tace “Wana sanar?�? Dan ita batamasan sun hadu da Umar ba. Matsowa taga yayi cikin karfi yasa hannu ya finciki wayarta ya kalli sunan Yayarta, ya cila mata wayar yace “Bravo! Kenan sunan yayarki ko ince a wayar yayarki kuke waya dashi?�?
Mikewa tadanyi tace “Yaya nikam meya sameka lokaci daya? Wace irin magana kakeyi?�?
Yatsa ya nuna mata cikin matukar bacin rai, idanunsa sunyi wani irin jaa “in kika kuskura kika kusamin wallahi zaki fuskanci tsananin bacin raina. In har mijin yayarki kikeso ki tafi gunshi mana.�?
Baki ta bude sam kwakwalwarta ta kasa daukan kalaman da Aminu ke jefanta dashi, juyawa taga yayi. Aminu kam yana shiga dakinsa ya dafe saman goshinsa, meke damunshi? Hakuri fa yaje ya bata na abinda ya aikata mata yaji tana waya, taya zai zargi alakarta da Umar bayan yasan komai, bayan shine yake zolayarta dan kawai yaga bacin ranta? Gefen kansa yasan buga, Aminu kanka daya kuwa? Meya sameka lokaci kankani? Yanzu gashican na tabbatar kasa yarinyar nan kuka.
Mikewa yai da sauri dan jiyai bazai jure ganin tana kuka akan abinda ya aikata ba, dan har hangota yai tana kuka da shesheka.
Yana daf da shiga falan yajuyo kukanta, jiyai zuciyarsa na tafasa da tsananin tausayinta, kofa ya bude ya shiga a durkushe ya ganta a kasa tana kuka sosaj, da alama kalamansa sunyi matukar kona mata rai, haryasa kafa zai shiga yaji sam baisan ganin ta, juyawa yai da sauri tare da komawa dakinsa.
Ibty kam kalaman Aminu sun tsaya mata a kwakwalwa, da ace zolayarta yake bazataji haushi ba amma wannan yanayin nashi har ransa yake magana.
Haka ta gaji da kukanta ta daure ta mike, wayarta ta kashe gaba daya ta wuce kitchen kawai ta hau yin wanke wanke.
Sai daf da magrib Iman ta dawo tare dasu Islam, kallo daya ta mata tasan tayi kuka sai dai a cewar Ibty ciwon kaine yake damunta.
Har dare yai yara suka kwanta tai wanka tasa kayan bacci ta nufi bangaren Aminu dauke da kayan tea dinsa, zataje in laifi tamai ma ta bashi hakuri dan bazata iya jure bacin ran nan ba, hartakai bakin kofa tace “Kodai dama budurcinta kawai yakeso? Ya gama yanzu baya bukatarta?�?
Kai ta girgiza da sauri dan Aminu ba irin mazan nan bane, sannan jiya soyayya tsantsa ya nuna mata bawai kawai saduwa yake so ba.
Shiga tai jiki a sanyaye bakinta dauke da sallama, lumshe ido yai cikin jin dadi a zuciyarsa, da alama ta ware dan sam hankalinsa yaki kwanciya.
Yana juyowa zai amsa sallama yaji kansa ya dan sara, wata irin muguwar tsanar ganinta ne ya shigeshi, kai ya kauda cikin kunar rai ya amsa sallamar kamar bayaso.
A hankali ta karasa ta ajiye tire din tace “Yaya in laifi na maka dan Allah ka…�?..�?
Hannu yasa a saman kunnensa ya kalleta yace “Can you please leave me alone? I just hate it! Dan Allah ki kyaleni naji da abinda ke damuna.�?
Kallansa tai a hankali ta mike kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, tana neman kwanciya yace “Please fita daga dakin nan.�?
Juyowa tai da sauri tana share hawaye tace “Yaya na fadamaka nawa Ummy alkawari akan kwana anan kullum.�?
“Okay! Ki zauna ni zan barmiki dakin.�?
Kallansa tai mamaki ya hanata magana, Inalilahi wa ina ilaihi raji’un ya Allah ka dubeni, meke faruwa?
Bata gama tunani ba kawai taga yabar dakin, zama tai a bakin gado kawai ta fara hawaye, can ta share tace “Koma menene am sure in aka tashi daga bacci zai huce, sai na bashi hakuri.�?
Aminu kam falo ya fito ya zauna ya fara aikinsa, wajen karfe goma Hajiya tamai waya akan wai maganinta batasan ya kare ba sai yanzu datazo sha.
Hankali a tashe ya fito ya shiga mota, Ibty sai jin alamun fita da mota ta fito a guje, kafin ta karaso ya fita, ina zaije a daren nan? Baiko fada mata ba? Bayan ko masallaci zaije yana ce mata ya wuce masallaci? Zama tai a bakin gado ta zuba uban tagumi, yau itakam meke faruwa? Jiya sunsha soyayya yau kuma kiyayya?
****
Hajiya kuwa mikewa tai ta dafa tea da maganin nan ta ajiye a falo da cup.
Tana jin sallamar Aminu tadan mike a hankali tace “Aminu kai hakuri na tasoka da daddare.�?
Ajiye ledar maganin yai yace “Haba Hajiya! Ko tsakar dare ne bana tashi na siyo ba balle yanzu?�?
Murmushi tai ta amsa tana godiya, kallansa tai tace “Kasha tea dan nasan kaunarka da shan tea.�?
“Kinsan bansha ba yau, dazu Ib�?..�? sai kuma yai shiru jin bama yasan ya ambaci sunanta, ita kuwa dama so take ta tabbatar da iya aikin da maganin yai, tace “Lafiyarta dai kalau ko?�?
Kai yadan girgiza ya zuba tea yace “Auren yarinya ko bacin rai, nidai banaji zanyi sa’ar mace bayan rasuwar Na’imah.�?
Wani sanyin dadi ne ya rufeta tace “Ka daure kasha tea din, sannan ka dinga mata uzuri kaga yarinyace sai hakuri.�?
Tea ya hada ya fara sha yace “Bazaki gane bane Hajiya.�?
Itakam wani dadi ne yake kamata ganin yana shan tea din nanfa ta far janshi da ‘yar hira harya shanye sannan tace “Kayan abinci nama sun danyi kasa.�?
“Subhanallah Hajiya kiyi hakuri yanzu zan tura miki kudi.�?
Nan ya tura mata 100k yace “Kiyi hakuri gaba daya bansan meke damuna ba harna manta.�?
Murmushi tai tace “Karka damu ai sai ana uzuri.�?
Haka ya taso ya nufi gida, yana shiga falo itama ta bude kofar ta fito daga daki dan dama tunda taji motsinsa ta mike, yanzu ta zare hijab dinta sanye take da rigar baci mai hannun vest da wando three quater, ta dan sa hula a kanta. Tayi shiga najan ra’ayi sosai.
Idanunsa ya runtse dan sam bai kaunar ganinta ji yake kamar yaga wani dodo mai mumunan halitta. Kansa ya dauke da sauri ya wuce doguwar kujera ya mike, tare da sa kansa akan throw pillow din kan kujerar.
Dan kusa dashi taje, kamshin turaren datasa mai dadi sai dai a gunsa ji yake yafi komai wari, tace “Yaya dan Allah ka shiga ka kwanta, kar tsautsayi ya kawo Iman�?..�?
“Dan Allah matsa daga kaina.�?
Abinda yace kenan ya rufe idanunsa, matsawa tai kamar zata juya sai kuma ta dawo tasa hannu a cikin sumarsa, ai a zabure yasa hannu ya hankade hannunta yace “Ke wai ana dole ne? Meke damunki ne?�?
Bakinta tadan motsa tana sanyin magana sai dai hawayen dake kokarin fitowa ya hanata, juyawa tai jiki a sanyaye ta koma daki.
Duk yandabtaso bacci ya dauketa ta kasa, sai juyi kawai takeyi, ganin ba dama kawai ta mike tai alwala ta fara kai kukanta gun Allah, dan itakam batasan metayi ba bakuma ta fahimci me ke damun Aminu ba.
Sqi wajen karfe biyu tadan kwanta akan sallayar anan bacci ya dauketa. Harya shigo yin alwala bataji motsinsa ba, tsayawa yai a jikin kofa yana kallanta cikin dan hasken dake shigowa ta window kadan, tausayinta ne ya kamashi, haushi da tsanar kansa ne suka rufeshi, ji yake kamar yaje ya rungumeta ya fara aika mata da sakonin so da kaunar daya tabbatar yana mata, to amma an taba so da tsanar mutum lokaci daya? Meke damunshi?
Kusa da ita ya karasa yana tunanin maidata kan gado, idanunsa ne suka sauka akan fuskarta da sauri ya dauke kansa ransa a bace ya tsallaketa ya wuce toilet.
Yana fitowa ya sake tsallaketa ya wuce masallaci.
Ibty kam tunda ya shiga toilet ta farka, tana kallansa ya tsallaketa ya tafi masallaci, jitai wasu zafafan hawaye sun sake zubo mata.

*******
Har sukai breakfast in kaji yayi magana to dasu Islam ne, ko kallanta baiyi ba, kallansa tai tace “Yau zamu makarantar da Ainah.�?
Ai kamar ta taboshi, “kije kiyi me? Banace ki jira ba? Keni meyasa sam bakida hakuri ne? Ko kuwa so kike kije ku hadu da wancan sha sha shan mijin yayar taki?�?
Kallansa tai tanasan magana sai dai a gabansu Islam? Shiru tai, nan taji yace “To ni nace ki jira koma menene ba yanzu ba.�?
Haka suka fito tana kallanshi ya wuce ko bi takanta baiyi ba.
Ainah ce tai waya akan zatazo anjima, jin muryar Ibty yasa tace “Ibty lafiya?�?
Jiki a sanyaye tace “Ainah kije kawai ni zanje daga baya.�?
Mamaki ya kamata tace “Yau ma bazaki ba kike nufi?�?
Murmushin yake tai tace “Banajin dadi ne shiyasa, kije ni in na warke zani.�?
“Meya sameki?�?
Zazzabi ne kawai na tabbatar zuwa gobe insha Allahu zan samu sauki.�?
Sam Ainah bata yarda ba dan muryarta ta nuna kamar wacce tai kuma ta gaji.
Kashe wayar tai ta nufi falo ta sanar da Ummy akan Ibty wai batada lafiya, hankalin Ummy ne ya tashi tace “Subhanallah! Bari Mamman ya dawo sainya kaimu mu dubata, ke kuma kibar zuwa makarantar zuwa jibi inta warke sai kuje tare.�?

*******
Sam Aminu ya rasa abinda ke mai dadi yau aiki har mistake yai sai da aka dawomai dashi ya sake, abinda tun shekararsa ta farko a aiki ba’a taba dawomai da aiki ba inya gama.
Gaba daya hankalinsa nakan Ibtisam ya rasa meke damunsa, ji yake gaba daya so yake ya ganta kusa dashi ya lalasheta akan abinda yai, sau hudu yana daukan wayarsa yana ajiyewa.
Tabbas wannan laifin daya mata ya wuce waya dolene ya bata hakuri sosai, taya zai yi mata haka bayan yanzu ya tabbatar yana san yarinyar? Ya kuma sha alwashin koyar da ita kaunarsa, to me kuma yakeyi haka? Me makon kauna kuma yana koya mata tsanarsa?
Yauma ana tashi ya fito, yana kokarin shiga mota Baffa ya fito, da sauri ya karasa suka gaisa, Baffa ya kalleshi yace “Aminu yau kaine da wuri haka zaka wuce?�?
Dan bayan kansa ya sosa yace “Inada abin yi ne a gida shiyasa.�?
Dadi ya kama Baffa yace “Ya kamata kam, ai tunda kai ango ne sai anamaka uzuri.�?
Mota ya shiga dan yasan halin Baffa sarai da tsokana.
Yana kallansa harya wuce dadi ya kama Baffa da alama Aminu yanzu yana kaunar matarsa, dolene yanzu su cigaba da addu’a akan Allah ya kara hada kansu.

******
Tsayawa yai a shago yasai wani turare mai tsada wanda yake hade da lotion dinsa, aka saka mai a gift bag, murmushi yai wai yau shine yake abinda samari keyi? Dan birge budurwa? Dan yanzun ma sai daya shiga internet yaga yanda ake ba mace hakuri, nan yaga wai asai gift akai mata sannan a bata hakuri.
Kai ya girgiza lalai Aminu kayi nisa.
A gida iyakam Ibty zazzabin gaske ne ya rufeta tsabar damuwa, dakyar ta daure tai abinci sannan ta koma dakinta ta kwanta.
Bayan su Islam sun dawo ta fito ta tabbatar sunci abinci sannan Iman ta kaisu Islamiya ita kuma ta koma daki ta kwanta. Da Iman ta dawo itama ta shige dakinta tana latse latsen wayarta har bacci ya dauketa.
Harya shigo gidan ba motsin kowa, murmushi yadanyi ai ba laifi da alama nunamai taji haushi tai, bangarenta ya nufa ya rike jakar a bayansa da hannun hagu.
Yana bude kofar dakinta tana zaune agaban madubi tana gyara fuskarta dan ta tabbatar ya kusa dawowa.
Juyowa tai nanfa suka hada ido jiyai gaba daya tsana da kyamarta sun tasomai, fuskarsa ce ta canza lokaci daya.
Ibty kam ganin yanayinsa yasa tadan runtse ido da alama haryanzu ana gidan jiya, mikewa tai jiki a sanyaye ga zazzabi tace “Yaya sannu da……�?
“Kun shigo ciki kun zauna gida ba kowa, in sata ma ko wani mugun abin akazoyi har ayi a tafi bakusani ba.�?
“Nasa key a kofofin gida ai.�?
“Musu kedai kullum musu bakya taba daukan laifinki, sam bazakiyi abu ace kinyi ba? Wannan wani irin taurin kaine?�?
Kanta kawai tai kasa dashi, juyawa yai rai a bace, dakinsa ya shiga ya cila jakar cikin wardrobe, tsaki yaja, laifinane ko wanaso birgewa?
Yaja wani tsaki tare da dafa kansa.

Ibty kam da kyar ta fito daga daki, dan tun ruwan tea datasha da safe haryanzu ta kasa cin komai, saboda zazzabi da bacin ran dake damunta.

******
Ummy ta dauko mayafi ta yafa tana kwallawa Ainah kira, “Kin fito munje munga jikin Ibtisam ko so kike dare yai? Dama gashi Mamman bai samu zuwa ba sai yanzu ke kuma kin tsaya kalula.�?
Fitowa tai tana gyara dankwalinta Ummy kefa kikace nai mata abinci? Da ace masu aiki ne sukai da yanzu nima na shirya.�?
“Sai kace wacce aka saki sirfe, dan abincin da kikai nawa yake?�?
Ainah tana dariya suka fito, “Sai san jiki kamar mage.�? Ummy ta fada.

*****
3/18/22, 20:36 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004
2083371244
Zenith Bankima

35
Haka su Ummy suka fito suka shiga mota, a dan shago suka tsaya suka sai drinks sannan suka dau hanya, Ummy a ranta tana ta fatan Allah yasa ciki ne?m, can kuma sai tace amma ciki ya fara wahalar da ita tun yanzu? In wannan tunanin yazo mata sai tace ai kuma ko wace mace da yanda take laulayin cikinta, itadai ta tabbatar ciki ne kadai zai tabbatar mata da kusantuwar Aminu da Ibtisam, abinda kullum ke ranta take kuma addu'a akai kenan.

****
Ibtisam kam tana kwance a daki dan dakyar ta iya kaiwa Aminu abinci, gudun samun matsala ga ciwon kai da zazzabi dake damunta yasa tabar falan ta koma daki ta kwanta, tana juyo sanda su Islam suka dawo amma sam ta kasa mikewa, haka suka shigo dakin da Iman ganin yanda take yasa sukasan batada lafiya, murmushin yake tai tace "Kaina ne ke ciwo daga nadan huta zan warke."
Haka Iman ta jawosu dakinsu suka cire kaya ta zuba musu abinci sannan ta nufi dakin da Ibty ke kwance, kusa da ita ta zauna tace “Ya Ibty dazu matsala kuka samu da Ya Aminu?�?
Gabanta ne yai dan karamin faduwa ta bude ido ta kalleta, Iman ta kara kallanta tace “Dazu ina kwance a daki am sure naji muryar Ya Aminu a sama kamar yana fada, to na mike zan fito naga kamar bai dace ba.�?
Murmushin dauriya tai tace “Kawai dan kinji muryar mutum a sama sai akacemiki fada ne? Yana daga bakin kofa ne ina daki shine yake magana, yaji gidan shiru.�?
Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki tare da danyin dariya tace “Kai Alhamdulila har hankalina ya tashi wlh na dauka har kun fara samun sabani.�?
Maida idanunta tai ta rufe tace “Shine kika wani damu?�?
Mikewa tai tana dariya tace “Harda na fara tsoron aure dan ganin Ya Aminu yasa yanzu naji inasan aure inhar naga ko wata ba’aiba ya canza ai kinga ba kanta.�?
Ibty bata tanka mata ba dan kanta dake ciwo sosai, tasha magani amma kamar batai ba.
Ana kiran sallar magrib taji ihun yara sun fita waje a guje, gashi ba karfi jikinta sam balle ta musu magana tace magrib tayi su dawo ciki, wayarta ta jawo tana kokarin kiran Iman taji kamar daga sama kuryar Ainah tana cewa “Ina Kalbin tawa?�?
Dakyar ta mike zaune ta dan ja mayafi ta yafa ta fara kokarin mikewa, kofar dakin aka bude Islam sai tsalle take, ta kalleta tace “Aunty kinga??�?
Ainah ce ta tsaya bakin kofar ta dan daga mata gira sannan ta karaso da sauri ta rungumeta, tana “Wayyo kalbina ashe file dinki aka binciko.�?
Ibty tadan tureta kadan tace “Ba wata kalbi kina magana kina dariya?�?
Hannunta tasa akan kuncinta, kallanta tai da sauri tace “Zazzabi haka?�?
Jin muryar Ummy a falo yasa ta mike da sauri, bata ko kula Ainah ba.
Ummy dake kokarin zama ta hango Ibty na tahowa, cikin kulawa ta mike da sauri, Ainah ta dan rike Ibty dan tafiyarta kadai zaka kalla kasan ba karfi a jikinta, tana kokarin zama a kasa Ummy tace “Zauna kan kujera�? nan Ainah ta zaunar da ita, karasowa tai ta zauna kusa da ita tare da taba jikinta, cikin tsananin damuwa wanda ya bayyana kiri-kiri a fuskarta tace “Ibtisam? Kinsha magani kuwa? Zazzabi haka?�?
Dan gyara zamanta tai tana tattaro dauriyarta tace “Nasha Ummy! Sannan bawai sosai yake wahalar dani ba.�?
Sallamar Aminu ce ta dan katseta dan Islam yanzu ta sanar dashi zuwan su Ummy, yana daki baiji ba.
Fuskarsa dauke da fara’a sosai yace “Ummy! Irin wannan zuwa ba sanarwa?�?
Kallansa tai tadanyi murmushi tace “Ba dole nazo na dubiya ba, banmasan zazzabin ya kamata haka ba.�?
Bai kawo komai ba yace “Wani ne ba lafiya?�?
Yai tambayar yana kallan mutanen falan, Ummy ta daure fuska sosai, mamaki ya rufe kowa na falan banda Ibty da batama dago ba, Ainah ta kalla tace “Keda Ummy ku shiga dasu daki.�?
Nan yaga anja su Islam cikin mamaki ya karaso ya zauna yana gaisheta tare da cewa “Wanene ba lafiya?�? Ya karasa maganar yana kallan Ibty, da sauri ya dauke idansa dan sam ji yai bayasan ko ganinta.
“Kanasan cemin bakasan matarka batada lafiya ba kenan ko me?�?
Kallan Ibty ya sakeyi da sauri, nan fa wata kiyayga ta sake ruruwa yai murmushin takaici yace “Karya kika koma kuma? Ko kuwa neman hadani da iyayena kike?�?
Mamakin kalamansa ne ya rufe Ummy baki a bude tace “Mene?�?
Ya kalli Ummy rai a bace yace “Banda munafurci Ummy ina zaune da ita a gida bata fadamin batada lafiya ba amma gashi can tana sanar dake batada lafiya?�?
“Munafurci? Aminu? Kanka daya kuwa? Kai dana sani baka fadar munanan kalamai yau hankalinka daya kake abu haka?�?
Wani banzan kallonya mata ya kalli Ummy tare da dafa goshinsa yace “Ummy yarinyarnan ta isheni wlh, shiyasa tun farko nace muku banasan auren nan, sam ko ganinta banasanyi.�?
Gaban Ummy ne ya fadi, tabbas Aminu ba kalau yake ba, nan fa ta fara Inalilahi wa ina ilaihi raji’un a ranta, anya batai sake ba?
Cikin dakewa tace “Fadamin menene laifinta?�?
“Batada kunya sam, gashi ta iya musu bazaka taba fada mata abu tace to ba, sannan ga karya na kamata tana abu amma sam tabure batasan zance ba.�?
Ba shakka Aminu ba’a hayyacinsa yake ba, uta ta haifeshi a cikinta ko a mafarki tasan idansa bazai rufe ya dinga kushe mutum haka ba.
Kallan Ibty tai wacce hawaye kawai ke gudu akan kuncinta, tsananin tausayinta ya kamata. Maida idanunta kan Aminu tai tace “Naji na kuma fahimta yanzu fadamin kalma daya datai na rashin kunya?�?
Shiru yai da alama wai tunani yakeyi, sai can yace “Batadai da kunya Ummy, tamin rashin kunya ta kuma yiwa Hajiya, in ni ta rainani ai ita uwa ce.�?
Idanunta tadan runtse, ta fara addu’oi a ranta tace “To yau yau cikin daren nan matarnan zata bar gidan nan.�?
Fuskarsa dauke da murmushi yace “Gwara ta koma gidansu inda wannan mahaukacin dake jiranta yake.�?
Dagowa Ibty tai da sauri tana hawaye rabuwar aure ko wata da aure ba’ai ba? Itakam ta shiga uku.
“Ba matarka nake nufi ba wacce bakada hadi da ita nake nufi. Yau ko me zai faru kafata kafarta a gidan nan.�?
Wani dan zabura yai yace “Wai Hajiya ce zata bar gidan? Ummy sai yaushe zaki fahimci matarnan amana ce a gareni?�?
Yanayin fuskar Ummy ne ya canza zuwa damuwa sosai, da alama zurfin ciki gareta tunda har take kokarin boye abinda ke faruwa.
Tai wani banzan dariya tace “Amana? Ta wuce ni dana dauki cikinka na wata bakwai na kuma haifa?�?
Fuskarsa a hade sosai yace “Saboda wannan ta zugaki yasa kika fadi haka Ummy?�?
“Ya Allah! Na rokeka ka kwatomin d’ana daga wannan bala’in.�?
A fusace Ummy ta mike ta fito daga falan, biyota yai da sauri yana bata hakuri akan kar ta kore Hajiya, ai bata tsaya ta kanshi ba tana tafe tana addu’oi akan yau Allah ya bata nasara. Kai tsaye ta bude kofa ta nufi ciki tana bubuga koga.
Aminu na kusa da ita yana bata hakuri, Hajiya daga ciki duniya ta mata dadi dan tsire ma ta gama ci tasha yoghurt tana kallo a tv.
Tana bude kofa sukai ido hudu da Ummy, hankalinta ne yai mugun tashi gashi batasa kwallinta ba wanda ke hana Ummy yi mata musu.
Ummy ta cusa kai cikin falan, kallan ledar dake kan centre table tai ta danyi murmushi tace “Duniya ta miki dadi, sai dai am sorry to say yanzu zata juya miki baya.�?
Hajiya ta dake tace “Nikam Asma’u mena tsare miki a rayuwa? A iya sanina ban miki komai ba, Aminu shiyasa a koda yaushe nake ce maka mahaifiyarka batasan zamana a nan……�? ta karasa maganar tana wani matsar kwalla, aifa nan hankalin Aminu ya tashi ya kalli Ummy yace “Ummy wai dan Allah meyasa kike haka? Ga wacce ya kamata kiwa fada can kinzo kina yiwa Hajiya? Menene laifinta?�?
“Laifinta kake tambaya? Ina uwar arziki zata zauna a karkashin mijin ‘yarta? Bayan rasuwarta? Ki tashi tun muna mu biyu ki tattara kayanki mu wuce dake goben nan ki tarkata ki koma kauyenku, gidan da nake neman a sai miki ma yanzu na fasa, tunda babban burinki a rayuwa bai wuce ki hana Aminu zama cikin kwanciyar hankali da matarsa ba.�?
Kuka ta fashe dashi tace “Aminu na taba magana akan matarka? Nikam bazan iya wannan bakin cikin ba ka barni kawai na tafi.�?
Aminu yakai karshe gun bacin rai, yace “Inhar Hajiya tabar gidan nan to itama yarinyarcan yau auranta xai mutu zata koma gidan su.�?
Mamaki ne ya rufe Ummy tace “Ni kake fadawa haka Aminu?�?
Ya dan kauda kai yace “Ummy na kasa gane meke damunki, akan me zaki dinga bin bayan yarinyarcan kina wulakanta Hajiya?�?
Bacin rai ne karara a fuskar Ummy tace “Ni kakewa magana haka?�?
Shiru yai baice komai ba, Ummy tace “To sai ta bar gidan nan yau, Ibtisam ni na kawota ko? To zan tafi da ita yanzun nan.�?
Hajiya ta dauka zataji Ummy ta sauko sai dai jin kalamanta yasa ta dago a zabure, ya zatayi tasa kwallinta? Wannan tsinaniyar mata me take shirin yi mata tana murna komai ya fara tafiya daidai?
Aminu ya zubawa Ummy ido yace “Wai Ummy…�?.�?
Hannu ta dagamai, yau kam sai godiyar Allah bata taba tunanin zata samu damar magana haka ba, dan haka dole ta tabbatar matarnan ta fita daga gidan nan kafin ta kasa komai.
“Idan ka sake magana wallahi sai ka fuskanci bacin raina. Malama ke kuma tashi ko? Muje zan biya miki kudin hotel ki kwana yau gobe ki dau hanya. Sannan kar kiyi tunanin dawowa gidan nan domin a goben nan zan nemo masu zama a ciki koda kuwa kyauta zan basu gun zama.�?
Gaba daya Hajiya ta sususuce, zubewa tai a kasa ta dan hade hannaye tace “Asma’u naji koma menene zanyi amma ki bari sai zuwa gobe yanzu dare yayi.�?
Ummy tai wani banzan murmushi tace “Dame dame kikayi kafin ki cimma burin raba Aminu da matarsa?�?
Hajiya tadan dafe kirji tace “Wani saban sharri ne wannan? Nikam mena miki kike min kazafi haka?�?
Ibty dake waje dan ta biyosu ganin maganar ta dau zafi yasa ta tsaya a waje, jin kalaman Ummy yasa hankalinta yakai kunun da akaba Aminu, tabbas daga shan kunun nan ne ya fara canzawa, lalai matarnan bala’i ce.
Aminu ya dan dafa goshi wata tsanar Ibty na sake tasomai, tabbas komai saboda ita ne yake faruwa.
“Koma me kikai Allah na tare damu, yanzu tashi ki hada kayanki, na tabbatar kinada magungunan da kikesan boyewa in kuma kin ban dama inje ni in hada miki kayan.�?
Hajiya ta kalli Aminu, tace “Aminu?�?
Kallan Ummy yai wacce ta nunamai yatsa tare da tamke fuska sosai tace “Wallahi ka kuskura kasa baki ka shirya daina amsa gaisuwata har nabar duniya.�?
Idanunsa ya runtse baice komai ba sai kawar dakai dayai kawai ya fito daga gidan cikin kumar zuciya.
A waje yaga Ibty ta dan hade hannayenta biyu alamar tana addu’a, kallansa tai tare da sauke hannu, matsowa yai ya sa karfi ya riko hannunta sosai, zafin matsar taji idanunta na hawaye tace “Yaya hannuna.�?
“Hannunki? Ni kinsan halin da kika jefani? Ke ko kunyar munafircin da kika hada bakiji ba?�?
Ta daure tana dan motsi da hannunta dake zafi tace “Komai laifinane kenan?�?
Yace “Yanzu fadamin laifin waye? Haka kawai ina zaune zaman zamana daga auranki kina neman ruguzamin farinciki.�?
“Ka tabbatar da can a farinciki kake?�? Tambayar datamai kenan ita kanta batasan dalili ba.
Jikin bango ya dan karasa da ita haryanzu hannunsa na rike da nata, idanunsa sunyi jaa sosai yace “Me kike nufi?�?
Kai tadan girgiza tadan sauke kai kasa saboda azabar ciwo da kanta yakeyi, dago habarta yai da karfi yace “Tambayarki nake?�?
Tace “Na tabbatar sanda na aureka ba fara’a a fuskarka, ba jin dadi na kwanciyar hankali, aiki kawai kake sai kula da abinda ya zama dole.�?
Yarfe hannunsa yai yace “Yanzu fa? A kallanda ina aiki cikin kwanciyar hankali yanzu fa? Kin ruguzamin rayuwa.�?
Idanu tadan runtse kadan tace “Daga baya zaka fahimci ban taba neman ruguza maka rayuwa ba.�?
Sauke hannunta yai cikin karfi ya juya ya fita daga gidan, a waje ya tsaya ya kira Baffa ya sanar dashi abinda ke faruwa yana rokarsa akan yawa Ummy magana, Baffa yace “Shi dakanshi zai karaso a tattara Hajiya dan ya tabbatar Ummy tanada kwakwaran hujja.�?
Jin wannan kalamai yasa zuciyarsa ta sake tafasa, cikin bacin rai ya shiga gida ya bude motarsa ya zauna yana tunanin abinyi.
Ummy kam tana tsaye akan Hajiya duk yanda Hajiya taso ta sa kwalli ta kasa, haka ta hada kaya da niyyar wallahi goben nan zata dawo dan bataga mai korarta ba.
Haka Ummy ta sata gaba suka fito, Hajiya yau kam ji take wannan ranar tafi kowace rana bakin ciki, lalai in ta tashi yiwa Ummy magana wanda yafi ko wane muni zata aikata mata.
****
Suna fitowa waje Ummy taga Ibtisam, Hajiya ta kalleta wato itace ta sanar da Ummy abinda ya faru kenan? Wani murmushi tai a ranta tace “Kema ki shirya ganin bala’i da masifa.�?
A waje sukaga Aminu da mota, Ummy ta kalleshi tace “Ina zaka?�?
“Zan kai Hajiya hotel din dazata kwana.�?
Tai wani murmushi tace “Bansaka ba ni da kaina zan kaita, kace Mamman da Ainah su fito mu tafi.�?
Takaici ne ya kara kamashi ya zabgawa Ibty wani kallo yace “Ita kuma yaushe zata barmin gida?�?
Wannan karka damu, zan zo na dauke abata goben nan, ai dai bakabar yaranka ba kowa bako? Xan zo na dauketa na kuma dauke jikokina kai sai kai zamanka kai kadai.�?
Ciki ya juya cikin kunar rai, Ummy ta kalli Ibty tadan dafa kafadarta a hankali tace “Karki damu, yau ranar farinciki ce a rayuwata sannan ba wanda zai rabaki da gidanki.�?
Ta kalli Hajiya tace “Duk tsubun mutum Allah yana tare damu, kuma ke da Aminu mutu ka raba, kafin wani abu ya faru insha Allahu sharrin wacan mara imani da tsoron Allahn ya karye, kedai kiyi kokarin ci gaba da addu’a sannan kija mijiki a jiki.�?
Kanta ta sunkunyar tare da daga kai, cikin sanyin murya tace “Ummy sai yanzu na tuna tunda ta bashi kunu ya tafi office dashi ya canza halayensa.�?
Murmushin takaici tai tace “Ai ni ina kallan d’ana nasan ba kalau yake ba, Aminu ko ya tsani mutum baya nunawa kiri kiri haka.�?
Kallan Hajiya tai tace “Yau ko zaki mutu kin bar gidan nan kenan, addu’ar shekara biyar bata fadi ba.�?
Hajiya ta kallesu zuciyarta na wani tunzura, lalai ko zata koma a sake kusantarta koma ta ina ne sai taga bayan mutanen nan guda biyu.

{Nace Hajiya ko na d’auko ragowar tsiren ki tafi dashi?🤭🏃🏻‍♀�? tunda ba’asan sanda za’a sake gamuwa ba🤭?}
3/20/22, 12:02 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004
2083371244
Zenith Bankima

36
Hajiya gaba daya ta kasa yin wani, duka ya kamata tawa Ummy ta koma ciki? In tai haka kuma ai ta kara lalata alakarta da Aminu, ‘yar iskan yarinyarcan wai harta samu baki tana fadawa Ummy ta ba Akinu abu, lalai dole ta tozarta yarinyar nan.
Ummy ce ta kalleta tace “Ke banda ma dai ba kunya a harkarki ki hau adaidaita ki bar nan mana? Ko gidan d’anki ne?�?
Hajiya ta kafe Ummy da ido tana mata wani kallo, Ummy tai dan karamin tsaki tace “Yau baki samu damar yimin maganin ba? Ko kuwa wanda kikai da ne ya karye?
Hajiya takai makura, Ummy ta kalli Ibtisam tace “Ki koma ciki ki kwanta a gidan mijinki, gidanki, in zaki wuce kicewa Bala yazo ya siyomin kwado dan dakaina zan rufe gidan da kuma kaina zan tafi da makulin saboda irin wadannan mutanen da basa tsoron Allah bakasan me zasu aikata ba.�?
Ibtisam duk da ciwon dake damunta hamdalla da sake addu’a kawai take akan Allah yasa matarnan tabar gidan kenan har abada.
Tana kokarin wucewa taji an jawo rigarta ta baya iya karfi, wanda yasata yin kakari.
Ummy ta kalli Hajiya wacce ta jawo Ibty gabanta kafin suyi wani yunkuri Hajiya ta tsinkawa Ibtisam wani gigitacen mari, da alama neman inda zata huce takeyi dama.
Ummy a fusace ta matso ta rike hannunta data rike rigar Ibty tace “Malama kanki daya kuwa?�?
Hajiya ta daga hannu tana neman sake zuba mata Ummy ta hankadeta da karfi, Ibty mamaki ya rufeta ga wani azabar zafi da kuncinta yakeyi, ai Hajiya kamar jira take nan fa ta balle, “Allah idan har yarinyarnan bata bani hakurin abinda ta aikatamin ba ta shirya fuskantar bala’i da masifa.�?
Ummy ta bude baki zatai magana kawai taji Ibtisam tace “Allah na tare dani, kuma duk wanda ke neman d’an uwanshi da sharri to ya shirya fuskantar wannan sharrin a kansa.�?
Baki Hajiya ta bude tace “Ni kike fadawa haka?�? Ta nufo Ibty kamar wata bijima, kofar gate aka bude nan suka maida kallansu kan kofa, me zasu juyo su gani? Hajiya ce yashe a kasa tana kuka.
Ummy ta kalleta ta kauda kai dan ko batai magana ba tasan sharri take shirin yi, Ibty kam mamaki ne ya rufeta tace “Lafiya?�?
Ai Hajiya bata kulata ba sai kuka kawai da take tana sa hannu akai, Aminu cikin sauri ya nufi har yana neman yin tuntube, ya karaso yace “Hajiya? Meke faruwa?�?
Ta girgiza kai tana kuka tace “Aminu matarka da mahaifiyarka ne suka hadu suka dakeni, daga nace da Na’imah na duniyar nan na tabbatar baza’a tozartani haka ba, Aminu banda kowa a duniyar nan sai kai to dama Na’imah ce ta hadamu gashi yau sun ra…�?..�? ta kwace da kuka, ai Aminu a zabure ya dago yana neman shararawa Ibty wani marin, cikin tsawa yaji ance “Kana sauke hannu a fuskar nan wallahi zai kayi dana sani mai karfi.�?
Ibtisam ta kalleshi kawai ta juya ta wuce tare da sanar da Bala sakon Ummy na kwado, nan ya taho ya amshi kudi ya wuce siyowa.
Aminu nan fa ya tsuguna yana lalashi Hajiya ita Ummy abin ma dariya yaso bata, suna nan tsaye itadai Ainah tana tsaye tana kallan ikon Allah.
Bala ne ya dawo da kwado, Ummy da kanta ta datse gidan tasa kwado daya a ciki daya a gate, sannan ta kalli Hajiya tace “Ko mantuwa kikai ki sanar dani zan zo na aika miki kauyenku.
Suna kokarin shiga mota sai ga Baffa ya iso, da sauri Aminu ya karasa kamar wani zarare yana rokar Baffa akan ya taimaka ya ba Ummy hakuri, ai Baffa hannu kawai ya dagamai bai tsaya mai magana ba ya nufi gun Ummy.
Murmushi tai tace “Yallabai an taso ka?�?
Ya kalli Hajiya yace “Ina zata da daren nan?�?
Kafada ta daga tace “Dama hotel nake tunanin nema mata ta kwana gobe ta tattara ta nufi inda ya dace.�?
Kai Baffa ya daga yace “Hakan yayi, mu wuce?�?
Ta girgiza kai alamar a’a tace “Ina bukatar mu wuce dasu Islam ne daga gida su dinga zuwa makaranta, na sati biyu, sannan inda hali Ainah kicewa kanwar Ibtisam ta biyomu mu wuce tare gobe zan sa a maidata gida.
Baffa bai nemi jin dalilinta ba dan ya tabbatar tanada hujja, haka suna nan a tsaye Hajiya tun tana kokan karya har ta fara zuge jaka tana neman kwalli ko turare.
Hankalin Ummy ne yakai kan abinda take, Ummy ta kalli Ainah tace “Kwashe kayan kisa a bayan mota.
Hajiya ji take kamar ta shake Ummy dan takaici, haka suna tsaye aka kwashe suka jira har aka hado kayan su Islam itama Iman ta hado nata suka shiga motar Baffa, ita kuma Ummy daga ita sai Hajiya suka shiga motar Mamman.
Haka Ibty na jikin gate har suka wuce, addu’a ta sakeyi sannan ta kalli Aminu wanda ya dafa goshinsa gaba daya kana kallansa kasan yau ankaishi makura gashi bashi da wata mafita.
Waigowa yai fitilin gaban gidan suka haske mai Ibtisam wata irin tsana ta kara kamashi, juyawa tai ta koma ciki ba tare da ta tankamai ba.
Shigowa yai a fusace, yana neman tarar mata, kafin ya karaso ta wuce falanta, nan ya nufi falanta yana neman ta ganin batanan ya nufi daki, yana hankade kofa ya ganta zaune da Al-qur’ani tana karatu, to kodai bashi da imani ai bazai je ya finciko ta tana karatu ba, ya kuma tabbatar munafirci ne yasata daukan qur’ani a wannan lokacin, da karfi ya banko kofar kai kace ballata zaiyi.

*****
Sukam su Ummy suna tafe Hajiya tana zazzagawa Ummy magana “Yanda kika tozartani kema sai Allah ya tozartaki dama batun yau ba nasan kin tsaneni amma ban dauka tsanarki takai ki tattaroni cikin dare da mutuncina da kimata ba, wato Na’imah ta mutu bakwa ganina da daraja, ai ko baku daukeni a bakin komai ba kwa duba jikokin dake tsakaninmu.�?
Ummy tana jinta ta kwantar dakai tare da lumshe ido tana godiya ga Allah daya nuna mata wannan rana.
Hajiya ganin da gaske fa Ummy take ta waigo ta kalleta tace “Naji na bar gidan yanzu ku kamamin gidan da tunda kukai niyya, badai kusa da Aminu bane bakwaso na zauna? To na hakura ku nemamin wani gun……�?
Ummy duk yanda taso ta daure batasan sanda ta kwashe da dariya ba, ta bude ido tace “Gida? Yanzu? Sanda nake rokarki ki zo mu baki wani gun kin kula mu? Yanzu kuwa ai korar kare muka so yi miki akuma dalilin me zamu baki gun zama?�?
Hajiya ta juyo tace “In baku bani ba ina kuke so na zauna? Ni ba kudi ba?�?
“Wannan damuwa tace? Ki wuce can kauyenku a taimaka a baki gun zama ko da can ba’a kauyen kike ba?�?
Hajiya gaba daya zufa ce ta fara karyo mata, tunowa tai da dubu darin da Aminu ya bata harta cinye dubu biyar, yanzu me ta ba mai magani sannan ina zata samu gun kwana na kwana biyu kafin ta dawo gidan ta? Dan ko za’a mutu bamai rabata da gidanta.
Ummy bata ko bi takanta ba sai da suka isa wani dan karamin hotel wanda kana gani kasan na wanda yake da dan rufin asiri ne.
Wani kallan kyama tawa hotel din tace “Badai anan zaki ajiyeni bako?�?
Ummy balle jakarta ta ciro dubu goma, ta mika mata tace “kwana daya dubu biyar ne, ragowar kyaci abinci kiyi kudin mota. Sannan zan kara sanar dake makulin gida na gurina kuma goben nan zan sa mutane a cikin gidan, in ma kina tunanin zuwa gun Aminu ne dan ya taimaka miki ki har wahalar da kanki.�?
Huci kawai Hajiya takeyi, Ummy ta dan mika hannu tace “Kawo wayarki nasa miki sabuwar numberta ko zaki kira ki fadamin kin isa riga?�?
Kamar bazata bada ba sai dai gwara ta bada yanda in boka ya nemi wani abin zatai amfani dashi.
Tana mikowa taga Ummy ta balle bayan waya ai nan Hajiya ta fusata ta fara kokarin kwace wayarta, Ummy ta cire sim din kamar masu kokarin dambe ta cila jakarta ta sa a kasa sannan ta mika mata wayarta, Hajiya ta hau zage zage tana tsinewa Ummy akan wallahi sai taga bayansu yanda suka mata itama sai ta ninka musu abinda suka aikata mata.
Nan ta fito ta kalli dan iskan hotel din kawai tahau adaidaita tabat gun dan ko za’a mutu bazata kwana anan ba.

Ina zata? Ko ta koma gidan Aminu? Kai ta girgiza da sauri in har tai hakan me Aminu zai dauketa? Ko ba shiba ina zata zauna bayan tsinaniyarnan ta rufe mata gida? Ai gwara taje ai magani a rufe bakin Ummy ko a haukatata yanda zata dawo da karfinta.

******
Ibty ce ta fito daga daki dan yunwa ta fara cinta dayawa har bata gani sosai, ga mari da tashin hankalin data fuskanta yau kala kala, ga tun ruwan zafin safe ne a cikinta.
Mamaki ne ya kamata ganin Aminu zaune a falanta ya hade kafa daya kan daya, fuskarsa ba annuri sam, kai ta dauke kawai ta fara yin hanyar kitchen.
“Bakiga jiranki nake ba?�?
Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta nufoshi, karasowa tai ta zauna daga dan gefen kujera, cikin muryar mara lafiya tace “Gani.�?
Kallanta yai sannan ya kawar dakai saboda rashin san ganinta dayake, “Wato ke munafuka ko? Yanzu hankalinki ya kwanta?�?
Ibty takai makura duk hakurinta ta rasa me tai, kallansa tai kawai yaga ta daga kai.
Yace “Eh?�?
Ta sake daga kai tare da dan kauda kai, hannu yasa ya rikota tare da jawota kusa dashi, dayake ba jiki ne da itaba daga ansa karfi sai kaga ana fincikota, balle yau da ba karfi sam a jikinta, yanda ya jawota ne yasa ta fada jikinsa, kokarin dagata ya farayi zafin jikinta ne ya ji a jikinsa, kallanta yai tausayinta na ratsatsi sai dai sam bayasan ganinta.
Dagata yai ta mike zaune tana dan maida numfashi kadan, kanta na wani irin ciwo ga jiri dake dibanta a zaune.
“Meye hakan kike?�? Yai tambayar ganin tana wani langwabe kai.
“Banasan iskanci da munafirci, magana nake miki ko? Ko kuwa rashin kunyar kikesan nunamin?�?
Bata tanka mai ba dan sam batada karfin magana, kwantar da kanta tai jikin kujera tanadan fitarda numfashi kadan kadan.
A fusace ya mike yabar gun saboda takaicin yanda kasan zuciyarsa ke tsananin tausayinta.
Bangarensa ya nufa sai dai sam ya kasa zama, yawo ya shiga yi yana tuno zafin da yaji a jikinta da kuma yanda tai luuu, karfa yarinyar mutane ta mutu a gida daga shi sai ita?

******
Hajiya hotel hudu tana shiga daga taji uban kudi sai ta fito, dan kudin nata da ba yawa ne dasu ba bazata karar dasu a kwana daya ba.
Haka nan taja uban kayanta ta nufi inda Ummy ta ajiyeta asali, kamar zatai kuka haka ta shiga ciki, babban tashin hankali bai kara afkuwar mata ba sai da taga an dauke wuta wai an kuna solar amma wai ba fanka ba Ac haske kawai solar din take badawa, ga uban sauro dan ma lokacin sanyi ne.
Tagumi ta baza lalai bata taba tunanin za’aci zarafinta haka ba, ta dauka yau rana ce mafi farinciki a rayuwarta amma an juya mata ita zuwa bakin ciki. Dole gobe da asuba ta nufi gun boka dan bazata iya jira ba.
Kanta tadan dafa ta tuno fadan da sukai dashi, haka nan zanje na bashi hakuri ya zanyi?

**
3/21/22, 20:59 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004
2083371244
Zenith Bank
37*

Aminu gaba daya baccin sa na ranar ragage ne kuma mata dadi, zuwansa sama da bakwai bangaren Ibty sai dai haryanzu tana nan a kwance a falo, daga ya nemi ya karasa gunta sai yaji sam bayasan ganinta sai ya juya, haka ya dinga zirga-zirga daya ya kwanta tunaninta zai hanashi bacci ya mike, sai yazo yaji ya kasa karasawa ya juya. A haka har asuba tai itakam wanni baccin wahala take mai cike da yunwa da rashin karfin jiki sai dai tayi bacci sosai.
Mikewa tai dakyar ta nufi toilet dakyar dan har wani jiri takeji, alwala tai ta tada sallah a dakinta, kawai datakai sujjada ta fashe da wani irin kuka tana rokar Allah ya daidaita tsakaninsu da mijinta, kuka take sosai tana rokar Allah�?.
Shikam Aminu bacci sai wajen asuba ya kamashi, a firgice ya tashibyai alwala sannan ya fito zai tafi masallaci, jiki a sanyaye ya nufi bangarenta batanan harzai juya yaji alamun kuka, gaba daya jikinsa ne yai wani irin sanyi ya nufi dakinta, hannu yasa kamat zai bude kofar sai kuma ya fasa dan ya tabbatar inya bude ma maimakon lalashi kara bata mata rai zaiyi. Ya dan dade a tsaye a bakin kofar zuciyarsa na wani irin tafasa dan yanzu kam ya tabbatar yana tsananin kaunar Ibty baisan yaushe santa ya kamashi ba amma yanada yakinin wannan so ne.
Haka ya nufi masallaci dan yasan an idar da sallah yai tashi sannan ya juyo. Yana shiga ya zauna a bakin gado kenan yaji sallamarta, amsawa yai jiki a sanyaye tare da dan zuba mata ido, harta rame kwana daya sa alama jiya bataci abinci ba sam. Idanunsa yadan kawar, karasowa tai ta gaisheshi, idanunsa na gefe ya amsa mata, mikewa tai zata fito, kallan bayanta yai da sauri yace “Ya jikin naki?�?
Juyowa tai jiki a sanyaye, sai dai suna hada ido ya juyar da kansa da sauri, yanzu kam ta fara fahimtar kamar ganinta ne bayasan yi. Hakan yasa itama ta juya baya da sauri sannan tace “Da sauki.�?
Ga mamakinta sai jiyai yace “Ki koma ki kwanta inda wani abin da kikeso ki fadamin sai nasa a siyo.�?
Tabbas abinda akai akan fuskarta akai dan tunda ya fara abin nan baiyi mata magana mai dadi ba sai yanzu.
A hankali tace “Nagode.�?
Tana kokarin fita taji ya daga waya yace “Mamman bazaka fadamin inda kuka kai Hajiya ba?�?
Gabanta ne yadan fadi kamar zata juyo sai ta fasa kawai tai waje, ruwan tea ta hada ta zauna tasha, dakyar tadan ci wani karamin bread sannan ta mike ta nufi toilet dan tai wanka.
Tana wanka tana tunanin yanzu in Aminu ya dawo da Hajiya ya zatai? Dole tai wanka ta sanar da Ummy dan ta dakatar dashi daga neman ta, tana fitowa ta bude wardrobe dinta bangaren inda aka jera mata english wears dinta ta kalla, ba sababbi bane dan nata ne data siya gwanjo tun tana gida, tanasan sakawa a gida sai dai shakkar Umar da abinda zai aikata yasa bata taba sakawa ba, sai dai ko t-shirt shima in zata sauko sai ta zura hijab.
Wata riga da wando ta dauko wanda duk a ciki dama tafi ji dasu, milk colour ne sai dai anyi kwaliya da orange, a jikin rigar, wandon mikk ne irin mai budewa daga kasa din nan, sun amsheta dan sun mata kyau kwarai da gaske, ta dauko orange din mayafi ta dan yafa a kanta sannan ta fesa turare, husnul muslim ta dauko ta fara yin azkar.

******
Acan hotel din Hajiya kuwa wajen karfe biyu na dare ta farka a zabure, mikewa tai ta zauna tana kallan dan dakin, jitai idanunta na neman cikowa da kwalla, lalai bazata taba kyale Ummy da Ibty ba sai sun san ita suka tozarta, haka ta zauna ido biyu har asuba tai, ko sallah batai ba ta zari hijab ta fito daga hotel din ta nufi titi, ta dade sosai a tsaye kafin tai sa’an samun dan adaidaita.
Kai tsaye ta wuce gun Malam sai dai abin haushi yau dakin nasa a kule wai bai karaso daga gidansa ba, haka ta zauna a bakin barandar dakin ta baza uban tagumi, batasan sanda ta dan fara gyangyadi ba.
Sai karfe takwas sannan ya iso lokacin bacci ya mata dadi ta jinginar da kanta a jikin bango tana shan baccinta harda minshari.
Malam ya kalleta jiyai kamar ya sheke da dariya, wato matar nan jiya ta gama zazzagamai masifa sannan yau ya ganta wai har jiransa take? Kamar zai kulata sai kawai ya wucewarsa cikin dakin, nan ya fara shirin sana’arsa sannan ya kira wannan alhajin ya sanar dashi gafa Hajiya tazo da alama ta matsu ne dan anan ma ya sameta.
Dadi ya kama mutumin cikin hanzari yace gashinan zuwa.
Hajiya ta bude baki tanata makar bacci taji abu ya wuce mata makogaro ai a zabure ta mike ta fara kakarin amai dan tabbas ta fahimci kuda ne, kakari take iya kakari dakyar kudan ya fito da dan karamin amai wanda bakomai a cikinta irin yalan nan.
Ajiyar zuciya tai sannan ta fara gyara kanta, lalai tasha bacci, jakarta ta jawo da sauri ta bude, me zata gani? Dubu goman da Hajiya ta bata jiya babu su a ciki, bama wannan ba ‘yar wayar tata an sace.
Ai fa nan hankalin Hajiya yai mumunan tashi ta hau sintiri kafin ta shiga gun Malam hankali a tashe.
Kallansa tai tace “Malam anmin sata wlh.�?
Kamar ya kwashe da dariya sai kuma ya dake yace “Sata? Aljanunmu basa bari ai sata anan in har an dauke miki abu to lalai ba anan aka dauka ba, ko kuwa kina so kice aljanunmu ne suka daukar miki abu?�?
Hankalinta ya kara tashi ta zube tace “Ba haka nake nufi ba, sai dai…�?.�?
“Na dauka mun rabu dake mun kuma gama magana jiya? Meya kawoki yau?�?
Ta dan sake zubewa tace “Ka gafarceni jiya sam ba’a hayyacina nake ba.�?
Yai dan dube dubensa yace “kinci sa’a babban aljani na kaunarki dan haka yace ya hakura yanzu meya kawoki?�?
Nan ta zayyane mai duk abinda ke faruwa ta karasa tana hawaye tace “Yanzu bansan ina zan zauna ba sannan ni wlh koma menene zan iya yi akan in koma kauye, Malam ka taimakeni ka taimaki rayuwata ka sa Aminu ya kasa zaune ya kasa tsaye sai ya nemoni, sannan wannan tsinaniyar uwar tasa ka daura mata jinyar da zata kasa ko motsi balle ta iya aikata wani abu. Ita kuma matarsa ka daura mata ciwon hauka.�?
Dariya ya bushe dashi yace “Indai wannan ne mai sauki ne a gurin mu amma wai ke meyasa kika nace sai kin zauna da sirikinki?�?
Kallan mamaki tamai tace “Inada wanda ya fishi ne?�?
Yai ‘yan dube dubensa ya sake dariya yace “Akwai wanda zai baki jin dadi ya kuma baki gida ki zauna in har zaki dinga yanda da duk sanda ya kawo bukatar da aljani yazo mai da ita.�?
Kallan mamaki tamai me ya ke nufi?
Ya dan sake dariya yace “Mutumin rannan, a shirye yake tsaf ya baki muhali in har zaki amince da bukatunsa.�?
A zabure ta mike tace “Badani ba, naji ni dama can mai saban Allah ce amma a ciki banda in bada gurin nan da girma na a dinga surfata.�?
Boka ya jinjina kai yace “Shikenan sai ki jira sak sanda magani yaci amma inaso ki sani matarsa tafi karfin aljanun da muke turawa, sannan uwarsa ta tashi tsaye akansa itama bata baci tana mai addu’oi mu kuma kinsan bama san a dinga mana addu’a ana ruguzamana shirin mu.�?
Hajiya tadan ciji yatsa tace “koma menene ka taimaka yanzu kamin.�?
Ya dan kalli dakin da suka saba shiga yace “To mu shiga?�?
Kanta tadan dafa sannan ta mike, haka suka shiga tana shiga yau taji kanta na juyawa kafin tai auni ashe ta suma.
Mutumin ne ya shigo ya shafa magani sannan yahau aiki ta bayanta, yau yafi awa daya yanayi kafin ya kammala.
Fitowa sukai suka sheke da dariya, Malam yace “Karka damu zansa ta dawo gunka, gaba daya hankalinta ba’a kwance yake ba, wanda take takamar dashi ya koreta.�?
Dariya suka sakeyi cikin jin dadi ya dauko bandir din dubu daya guda biyu ya ajiye mai yace “Ka tabbatar an kawota saboda wadancan mata daka hadani dasu duk sun gama yagwalgwalewa ga ciwuka shiyasa duk na fatatakesu, yanzu ita wannan ita nake hari.�?
Nan ya fito yana murmushin mugunta, matansa hudu sai dai ba wace yake kusanta domin umarnin boka ne, dole haka yake samo manyan mata ya dinga badala dasu ta baya, da zarar ciwo ko wani abin ya samesu ko kuma ya dainajin komai a tattare dasu sai ya koresu. Babban mutum ne dan yanzu ma ubangidansa ne ke neman takarar gomna na jahar Kano.

*****
Hajiya bata farfado ba sai da Malam shima ya kara mika nashi sakon, tana farkawa taji ko zama ta kasayi, samun kanta tai kawai da fara hawaye dan ta tabbatar Malam yau ta baya ya nemeta itakam ta tsani abin nan.
Haka ta fito tana tafiya dakyar, Malam ya daure fuska sosai yace “Yanzu ki koma zan kammala aikinki zan nemeki�?
Tace “Ka taimakeni Malam inba Aminu bazan taba jin dadin rayuwata ba.�?
Wani kallo ya kara yace “Wani in yaji abinda kikeyi dauka zaiyi kece matarsa ba ‘yarki ba.�?
“Wani irin zance kake haka?�?
“Ban manta sanda Na’imah wato ‘yarki ta kwato kansa dakyar ba, sannan itace tw hadamu dake, sai dai in kina wani abin sai naga kamar san mijin ‘yar taki kike.�?
A fusace tace “Malam wani kazamun zance kake haka?�?
“Haryau ina mamakin meyasa bakyasan yai aure? Naji ni nace inyai aure matar zata koreki amma ai zaki iya neman maganin da za’a rufe mata baki ko? Sai dai sam baki nema ba kullum kedai burinki ya rabu da matarsa.�?
Mikewa tai cikin takaici tace “Sai naji daga gareka.�?
“Kudin aiki fa?�?
Kallansa tai tace “Kayi hakuri anmin sata amma zan turo gaba daya.�?
Haka ta fito yabi bayanta da wani kallo…�?..

*******
Tunda ta shigo falan yake kallanta ta bayan ido, yau ko hijab batasa ba? Anya Ibty ce kowa?
Haka yai ta satar kallanta harta gama shigowa da kayan abincin, ji yake kamar ya jawota tsam ya rungume, bata bari sun hada ido ba idanunta nakan kayan abincin tace “Yaya abinci.�?
Gyaran murya yai sannan yace “Kedanace in kinasan abu kiyi magana? Baki da lafiya meye na dagewa sai kinyi abinci?�?
“Daga kai sai Bala shiyasa naga abincin ba yawa zan iyayi.�?
“Kefa?�?
“Banajin yunwa maybe in muka je school da Ainah na samu naci.�?
Cikin hanzari yace “Baki da lafiyan zaki skul?�?
Har zata juyo sai ta fasa tace “Yaya kaga tun yaushe nake cewa zamuje registration din nan, inhar kaban izini gwara in daure in je muyi.�?
“So kike kije ki fadi a skul? Sannan makaranta zaki kikai wannan shigar?�?
Dan karamin murmushi tai duk da bai fada ba taji dadi a kalla ya damu da ita.
Kamar zatace a’a sai tace “Riga da wando ne fa kawai in nasa after dress shikenan.�?
Fuska ya daure sosai yace “Inji wa yace shikenan?�?
Ta dan dake tace “Haka na dauka zakace.�?
Ya kara hade rai yace “Bance ba sannan banda jiyar cewa, sannan ki jira sai wajen azahar inhar jikin naki yayi sauki sai kuje.�?
Kai ta daga sannan tace “Shikenan.�?
Gani yai ta juya cikin ransa yace “Ko kunya wai ta dauka haka zance? Ce mata akai bansan darajar matata ba ko me? Sannan meyasa ma taki kallo na? Ganina ne batasan yi saboda abinda na mata ko me?
Goshinsa yadan shafa to in ma hakan ne ai batada laifi tunda koshi kunyar abubuwan daya mata jiya yake, haryanzu haushin kansa yakeji da tsanar abinda ya aikata mata.

Itakam magani ta karasha ta zauna akan kujera tana tunanin wannan abu, meyasa wasu mutanen basuda imani? Metawa matarnan da zata rabata da mijinta?
Wayarta ta dauka ta kira Ainah bayan sun gaisa ta sanar da ita sai bayan azahar in Ya Aminu ya yarda, sannan ta sanar da ita neman da Aminu yakewa Hajiya.
Ainah tace “Karki damu Ummy ta gama jawa Mamman kunne.�?
Ajiyar zuciya tai tace “Iman fa?�?
Ga wuce makaranta daga can wai zata wuce gida.�?
Kai ta jinjina sannan sukai sallama.

*******
Cikin magiya Bilkisu tace “Ya Umar dan Allah kaban wayata, tun jiya nakesan nai waya amma ba�?..�?
Cilo wayar dayai da karfi ne yasa gabanta ya fadi ji kake tas ta bugu da bango ta fadi kasa, ai basai ta duba ba screen din ya gama fashewa.
Kallansa tai kawai taji hawaye sun zubo tace “Yaya nikam me na maka dana cancanci wannan wulakancin?�?
Wani kallan tsana ya mata yace “Tambaya kike? Ai har abada indai dani zaki zauna to wallahi bazaki taba jin dadin aurenki ba, yanda kika rabani da masoyiyata nima sai na rabaki da duk wani jin dadi na duniya.�?
Ta share hawayenta taja kekenta tabar dakin, wani irin kara ya saki kai kace mai aljanu ne, ya cilo pillow da karfin gaske shikam ya tsani yaga keken guragun nan, ya tsani yarinyar nan kamar ransa.
Abinda Ibty tamai daya kira ya tuna, idanunsa sukai jaa yace “Ni mutumin daya ke tanadinki tun kina yarinya ni zaki tozarta? Ni zaki wulakanta saboda wancan jan mutumin? Nunar rana? Wanda na tabbatar kudin nasa ma daga sata ya hadasu?�?
Yai kwafa�?.

Nima kwafar nai nace {Malam Umar kai dai kace kana kishi🤪 ya fika komai}
3/22/22, 23:54 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*n

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004jiki
2083371244
Zenith Bank
38*

Harya shiga toilet yai wanka gaba daya ya rasa meke damunsa, taya zai kula da ita bayan sam baya san ko ganin fuskarta? Ga damuwarsa halin da Hajiya ke ciki.
Surar ta da shigar datai ne ta fadimai ya runtse ido sannan ya kara karfin ruwan shower din, yana jika kansa sosai, wannan wani irin abu ne? Kanasan kasancewa da matarka amma daga ka ganta sai kaji tsanarta? Ya dade yana zuba ruwa kafin ya gaji ya fito, gaban madubin bandakin ya tsaya wanda nason ruwan zafi duk ya sa baka ganin komai, hannunsa yasa yasan goge saman madubin tare da kurewa fuskarsa kallo, wannan kaddarar ce ko me? Kanasan abu wanda yake mallakinka amma ka gagara nunamai?
Yadan shafi sumar kansa, dole ko ma me zaiji ya daure yaja matarsa, dan shikam har mamakin yanda zuciyarsa ta kamu da yarinya karama yakeyi.
Ya fito cikin dakiya ya kira gun aikinsu ya sanar dasu matarsa ba lafiya, dayake gun aikinsu ne shida Baffa ba wani matsala da ya samu.
Fitowa yai ya zura jallabiya ya dan fesa turarensa sannanya fito, kai tsaye bangarenta ya nufa, yana shiga tana fitowa daga kitchen, yana kallanta yaji wata muguwar tsana da kyama sun rufeshi balle in ya tuno abinda ta aikata mai jiya, fuska ya daure sosai kamar wanda aka bashi mumunan labari, Ibty jikinta a sanyaye ta taho zata wuce daki dan yanayin fuskarsa kadai ya isa tasan bayasan ganinta.
Aminu ya runtse ido sosai sannan ya dake a ransa yace “Dole inje kusa da ita naga meke faruwa, in bata kusa dani sai naji kaunarta kuma daga naganta sai naji ba wanda na tsana a duniya sama da ita?�?
Ibty bataji takowarsa ba harya karaso ta bayanta, hannu tasa zata bude kofar dakin kawai taji an sakalo hannu ta kugunta, wani irin yanayi ta shiga wanda yasata dan lumshe ido.
Aminu bai juyo da ita ba yace “Meyasa kika aikatamin abu jiya har kikasa nakejin tsanarki haka a raina?�?
Idanunta haryanzu a lumshe suke duk da yanzu bawai yanayin data shiga bane yasata barin idan a rufe ba. “Haryau bansan mena aikata ba, naji in har kace nayi laifi to na dauka, ko wani iri ne ka yafemin.�?
“Meyasa banga alamun kina neman yafiyar ba?�?
“To Yaya me kake so nayi na nuna maka ina neman yafiya?�?
Hannunsa ya sake matsowa dashi saitin cikinta sosai hakan yasa tadanyi wata karamar ajiyar zuciya, shi kansa wani yanayin yake neman shiga, kokarin kwantar da kansa yake a kafadarta kawai yaji kansa ya fara wani irin sarawa, dan kansa ya girgiza saboda yanda ya fara jin abun na damunsa, da karfi yadan turata hakan yasa ta buge da jikin kofar, ji kake kum.
Idanunsa yadan bude ganin yanda ta bige yadan matsa da baya da sauri yana kallanta, Ibty ta juyo ta kalleshi kamar zatai magana kawai ta bude daki ta shiga.
Zama tai a bakin gado kawai sai jitai hawaye sun zubo mata, wannan wani irin masifa da bala’i ne? Haka kawai dan burin duniya sai ka juyar wa mutum kwakwalwa ka maidashi ya dinga abinda ba halinsa ba.
Qur’ani ta dauko kawai ta hau karantawa tana neman Allah ya kawo musu sauki cikin wannan bala’in da aka jefasu.
Shikam Aminu bangarensa ya wuce cikin sauri ya zauna a kan kujera tare da dafe saman kansa, tabbas akwai abinda ke damunshi, to ko dai akwai wani ciwo ne a jikinsa? Wannan tunanin yasa hankalinsa yai mugun tashi ba shiri ya kira abokinsa wanda yake doctor ne yasanar dashi yana bukatar yazo a dubashi.
Cikin kulawa yace “Kazo sai muji menene matsalarka.�?
Shida yake tunanin zaman gida dan ya kula da matarsa to zaman nashi ma sam ba amfani dan baisan ganinta, ita kuma ba lafiya ba, da alama kara mata ciwo yake saboda munanan abubuwan da yake mata.
Wayarsa ya dauka kawai ya rubuta mata sako akan zai fita.
Ibty tana dan kishingide a daki taga sakonsa da sauri ta mike ta fito, a falo ta ganshi daidai haryar fita ya canza kayansa zuwa manyan kaya na shadda.
Bakinta nadan rawa tace “Yaya muje makarantar?�?
Bai kalleta ba yace “Ki kira Ainah ta biyo kuje, ni zanje wani gun ne. Sannan ki tabbatar kin canz�?..�?
Sai kuma yai shiru, cikin dauriya tace “Dama taya zan fita a haka? Nima ai……�?
Bai jira ta gama magana ba taga yayi waje, da kallo ta bishi sannan tadan hadiye abunda ke makogoronta, tanasan sanar da Ummanta halin da take ciki ko zata tayata addu’a sai dai sam bazata iya ba, haka nan ta taso bata iya fadan matsalarta ba, sannan yawanci iyayenmu nada ba ruwansu da tambayar matsalarka, wannan dalili yasa a haka ta taso, har mamaki take in taga Iman ko Yaya Bilkisu na sanar da Umma abinda suke so da wanda basa so, ko dayake saboda ciwon Yaya Bilkisu ita kafin ma ta fada Umma ke tambayarta, Bilkisu me kikeso? Me za’a miki? Akwai abinda kike so? Meya sameki? Me ya faru naga kin canza? Sau da dama in taji ana irin wannan tambayar murmushi kawai takeyi dan tasan ba mai mata irin wannan tambayar, a haka a haka abin ya zama jikinta shiyasa ko matsalar Umar ba wanda ya sani a gidan.

*****
Hajiya dakyar ta koma wannan dan iskan hotel din, tana shiga sukace ta kawo kudi inba yau zata tafi ba, bakin ciki ya isheta haka ta sake fitowa ta nemi atm ta ciro kudi ta basu na kwana biyu dan tabbas kwana biyu kawai zatai ta koma gidanta.
Zama tai a dan iskan dakin ga uban yunwa ta isheta, cikin bakin ciki ta fito ta nemi gun saida abinci ta siyo waina da miya.
Ga ba waya balle ta dan yi tunanin abinyi, tana gama ci tadan kishingida dan azabar datakeji haryanzu yaki barinta.
Cikin baccinta banda mafarke mafarke ba abinda ta dinga yi, a zabure ta farka ta sauke ajiyar zuciya ta bakin ciki sannan tai kwafa, bari dai maganinta yaci wallahi wannan karan kwatar kudi zatai sosai yanzu ina amfani ace duk shekarun nan ko kudin gida bata tara ba?

******
Acan gidan Ibty kuwa Wajen karfe biyu na rana Ainah ta iso, nan Ibty ta saka abaya doguwa ta yane kanta da mayafi sannan suka shiga mota aka fara tafiya.
Shiru Ibty tai tare da dan sa kanta a jikin window din motar, Ainah tadan jawota ta zaunar da ita daidai tace “Matarcan bata dawo bako?�?
Murmushi tai tare da daga kai, “Yaya fa? Ya dawo hayyacinsa?�?
Murmushin yake tai tace “Ji wani tambaya, sai kace wanda hankalinsa ya gushe?�?
Ainah tadan sauke ajiyar zuciya tace “jiya Ummy kusan kwana tai akan sallaya tana addu’a insha Allahu komai zai dawo daidai.�?
Ibty hartayi shiru sai kuma ta kalli Ainah sosi tace “Ainah dan Allah tambaya, nikam ya akai Yaya ya hadu da matarshi marigayiya? Nadaiji kina labarin yanda yake tsananin santa.�?
Ainah tasa dariya tace “kishi ne?�?
Dan dungure kafadarta tai tace “abinda yafi kishi.�?
Ainah tadan gyara zama tana dan dariya kafin ta dan dake tace “Hmmm abinda aka kusa tafka abin kunya?�?
Kallan rashin fahimta ta mata tace “Abin kunya?�?
Ainah ta dan matso kusa da ita cikin rada tace “Baffa da yayarta zai aura yayarta wace suke uba daya, abin mamaki da al’ajabi wai kawai sai Ya Aminu yazo da labarin yanasan kanwar?�?
Idanu Ibty ta zaro tace “Me?�?
Ainah tadan tabe baki tace “Ai kishiyar Ummy da yanzu yayarta ce to tunda Aminu yazo da maganar yana san Aunty Na’imah shi Baffa ya janye, gashi lokacin wace yakeso ance tana bala’in sanshi wai hardasu kwanciya a gadan asibiti.�?
Gaba daya mamaki ya kama Ibty tace “Ikon Allah! To shi Yayan bai sani ba? Itama Na’iman bata sani ba?�?
Baki Ainah tadan tabe tace “Haka dai tace amma ita Ummy ta dage akan ta sani, gani take sai dama taga Abba sannan ta nemi dansa, dan a lokacin Ya Aminu fa baifi sati biyu da dawowa daga karatu daga kasar Canada ba, har yaushe ya ganta harya mutu akan santa? Da har a lokacin yake tunanin ba mai iya rabasu?�?
Shiru Ibty tai, Ainah tadan yi murmushi tace “Saukinta daya dai ita Na’iman ba ruwanta sannan tanada kirki gasan mutane ba kamar Mahaifiyarta ba.�?
Ibty bata amsa ba sai shiru kawai datai tana sake mamakin wannan abin, har suka iso skul suka fita suka shiga cikin friends dinsu kowa na mata iskanci akan taci amanarsu bata sanar dasu auranta ba, Ainah ta shiga tana kareta wai su daina damun matar yayanta…�?

*****
Duk wani bincike likitan yayi amma baiga komai ba, kallan Aminu yai yace �? Babu wani matsala kawai dai ka dage da exercise dan naga cholesterol dinka yadan hau kadan.
Aminu ya kalleshi sannan ya sanar dashi abinda ke damunsa, shiru abokin nasa yai yace “To dai gaskiya ba abinda ke damunka ka tabbatar kuma haka kawai kakejin tsanar?�?
Aminu ya jinjina kai yace “Bansan meke faruwa ba kwanan nan abin nan duk ya hanani sukuni.�?
Dan shiru ya sakeyi yace “To ko za’a duba islamic chemist? Ko harkar jinnu ne?�?
Dariya Aminu yai yace “Kai dai daga likita kana neman komawa wani abin, karka damu zan duba meke damuna.�?
Mikewa yai ya fito gaba daya yana sake mamakin wannan abin.
Yana shiga mota Baffa ya kirashi nan ya dauka yana tambayarsa jikin Ibty, cikin rashin damuwa yace ai tana makaranta shima ya fito.
Baffa yai shiru kafin yace “Aminu kadai san amana ka dauka ko? Dan daga sanda iyayenta suka amshi sadakinta to fa sun salama maka komai, hakkinka ce ya zama dole ka kula da ita.�?
Jikinsa ne yai sanyi yace “Na sani Baffa amma nikaina bansan meke damuna ba.�?
“Sakaci da addu’a shike damunka.�?
Mamaki ya kama Aminu yace “Sakaci?�?
Baffa cikin dabara yace “Aminu ita rayuwa da kake gani inhar ka fara karancin addu’a da karatun qur’ani sai kaga abubuwa suna neman dagule maka. Dolene mu dage dan kara kusanci da Allah.�?
“Insha Allah! Amma yanzu Baffa haka za’a bar Hajiya? Nayita kiran wayarta a kashe…�?.�?
Jiyai an katse wayar yabi wayar da kallo sannan ya tada motarsa.

🏌🏻‍♀�?
3/26/22, 17:02 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*n

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004jiki
2083371244
Zenith Bank
40*
Mikewa Hajiya tai ta dan kwantar da kanta akan gado, lissafi takeyi menene zai ceceta? Ko dai ta yadda da abinda boka yace? Inyaso da zarar ta dan tattara kudi a gunsa sai ta san yanda zatai ta nemi wani babban malamin da zai halaka Ummy da Ibty? Kai ta girgiza da sauri dan itakam bazata yanda ta zama inji ba.
Yanzu ita kadaice a duniya dole ne ta kwaci ta kanta ta kuma mori duniya iya san ranta yanzu meya dada? Na'imah ta gama saita rayuwarta gashinan bata mori duniya ba? Dole taje taga halinda Umar yake ciki dan ta tabbatar yana nan yana cigiyarta ta ko ina.
Mikewa tai cikin karfin gwiwa gwara taje ta lalabashi ya sai mata gida a boye da dai ta yarda a dinga lalata da ita haka kamar wata injin taliya.
Fitowa tai sanye da hijabin ta kai kace mutuniyar arziki ce.
Adaidaita ta fada ta nufi umguwar.

********
Aminu kam bayan ya samu nutsuwa yana daga gefenta ta baya hannunsa sakale a kugunta akan kujerar, ita kuma ta juya baya saboda bataso ya ganta.
Kansa na kan wuyanta sun dade a haka ba wanda yai magana, a hankali yace "Ke ba lafiya ba na sake wahalar dake."
Haryanzu bata juyo ba tadan girgiza kai a hankali tace "Indai zaka sauko kamar da wake zancen wahala? Sannan ni ba wahalar ma danasha."
Gyara kansa yai yace "Kema kin fahimci ba kamar da nake ba?"
Saura kadan ta juyo sai tai saurin tunawa, murmushi tadanyi tace "Bayan ni kadai ka canzawa? Taya zan kasa sani?"
Saman goshinsa ya shafa yace "Bansan meke damuna ba sam, gashi kasan raina nasan gaskiya amma sai naji kawai wani abu na tasomin kamar garwashi a raina."
"Yaya kaima wasa wasa kana sakaci da addu'a bance bakayi ba amma dai......"
Meyasa kowa ke cewa ina sakaci da addu'a?
Tadanyi shiru tana tunanin abin cewa kafin tace "addu'a makamin mumuni, inhar kana aikata abinda ba'a san ranka ba kakeyi kaga kuwa kana bukatar dagewa da addu'a."
Shiru yadanyi ya matso da labansa kusa da kunnenta yace "Malama an samu bakin magana?"
Dan kasa tai dakai saboda wani yanayi data tsinci kanta a ciki "zaki iya tashi ko na taimaka miki? Dan na tabbatar rannan kinji haushi na daban taimakeki ba." Yai maganar yana kokarin juyonda ita, kara dukunkunewa tai ya dan kalli saman kanta yace "Kunya? Na dauka daga sanda kika sumbaceni da kanki kin nunamin kin daina kunya ta."
Sake cusa jikinta tai jikin kujera cikin kunyar kalamansa, itakam Ya Aminu batasan ya zatai dashi da zarar magana ba.
Mikewa yai yaja vest da wando ya zura ya sa hannu ya dagota cak, kanta tasa a cikin kirjinsa saboda kunyar yanayin da take da kuma rashin san hada ido dashi.
Toilet dinta ya nufa da ita ya sauketa sannan ya ajiye mata towel yaja kofar ya fita, shower ta kunna tana wanke jikinta kawai ta samu kanta da fashewa da kuka, sai yaushe ne zataji dadin rayuwa? Gashi kiri kiri ta fahimci mijinta ya damu da ita amma an shiga tsakaninsu? An hanasu nunawa juna kulawa? Haka tana wanka tana share kwallarta.
Shima Aminu toilet dinsa ya nufa ya sakarwa kansa ruwa yanajin wani nishadi na tasowa daga kasan ransa, tabbas zuciyarsa na san Ibty sosai babu tantama a ciki sannan yana samun nutsuwa tare da ita amma meyasa sam wani sa'in yakejin tsana da kyamarta?
Dole ya dage da addu'a yana babba amma yarinya ita ke bashi shawara akan abinda ya kamata ya dinga yi?

*****
Acan bangaren Umar kuwa yana isa gida ya wuce bangarensa da niyyar zuwa yajawa Bilkisu kunne akan karta fadawa Abba komai in ba so take ya bata takardar sakinta ba, me zai gani? Jakar kayansa ya gani a wajen gidan mamaki ya kamashi ya sa hannu zai bude yaji kofa a kulle, cikin zafin rai ya bubuga kofar yana kiranta ransa a matukar bace.
"Idan ka gama bige-bigen ka dauko jakarka ka biyoni." Abinda yaji an fada daga bayansa kenan, basai ya duba ba muryar Abba ce, nan fa hankalinsa yai mugun tashi, cikin sanyin jiki ya dau jakarsa yabi bayan Abba har bangarensu.
A falo Abba ya zauna shi kuma yai sum-sum ya zauna a kasa kai kace mutumin arziki, Abba ya kalleshi yace "Na sa an rufe shagonka dan dama me makon riba kullum kara kankancewa yake na rasa ina kudin suke shiga. Sannan na rufe gidanka na d'auko 'yata dan ba baiwa na baka ba, sai abu na karshe ga takarda nan da biro ka sauwake mata ka tattara ka koma gida dan na kira Yaya na sanar dashi zaka dawo."
Cikin sauri Umar ya dago yace "Abba!"
Abba ya kalleshi cikin takaici sannan yai murmushin bacin rai yace "Na fahimci nama laifi na baka Bilkisu da take nakashashiya akan Ibty da take da lafiya, sai dai wannan ba hujja bace da zaka wahalar da mara lafiya saboda burinka bai cika ba, sannan ka hana ita Ibtyn kwanciyar hankali a zaman aurenta, banda rashin sanin darajar addini a ina ka taba ganin anabin mace mai aure? Wannan abinda ka aikata ya nunamin bazan iya barinka kacigaba da zama anan ba inhar ina bukatar kwanciyar hankalin Bilkisu da Ibtisam."
Shiru Umar yai sai dan hucin bacin rai da yakeyi, Abba ya kalleshi ya ce "Na kuma tabbatar tunda Aminu ya fadamin ba wannan bane karanka na farko na bibiyar matarsa."
Cikin fishi ya dago dan ya tsani a dinga cewa matarsa, ganin yanda Abba kenkallansa yasa ya kauda kai gefe kafin yace "Amma Abba ni da kuka cuceni kuka kwacemin abinda nakeso fa? Duk hakurin danai baku gani ba? In har tanine wallahi dauke Ibty zanyi muje wani garin muyi rayuwarmu, amma nai haku........."
"Ka rufemin baki ko sai na fasashi? Mahaukacin banza da wofi." Cikin tsawa Abba ya fadi haka tare da katseshi, Umar ya dunkule hannu cikin tsananin bacin rai.
Abba ya nunashi da yatsa yace "Bansan mahaukaci na raina ba sai yau, sauwake wa Bilkisu ka fitarmin daga gida."
Cikin gadara ya jawo takarda, da sauri Bilkisu ta turo kekenta da alama tana bakin kofa tana jin duk abinda suke cewa, tana hawaye ta karaso.
"Abba banda saki dan Allah."
Cikin tsawa Abba ya nuna mata ciki yace "Wuce ciki."
Komawa tai tana kuka, Umar ya kalli Abba yace "in rubuta naga kamar inta rabu dani wani hali zata shiga."
Mamaki ya kama Abba ya dake yace "Ko ta shiga ko karta shiga ba damuwarka bace, kaidai ka sauwake mata.�?
Umar ya ajiye biro din yace “Zan sauwake mata in Aminu ya saki Ibty.�?
Abba ya bude baki yana mai kallan mamaki yace “Amma bakada hankali ko?�?
Umar ya kauda kai sannan ya mike ya dau jakarsa yace “Taita zama da igiyar aurena, in har anaso in saketa to nima a saki Ibtisam.�? Ya fita yabar Abba da baki a bude.
Yana fita ya duba aljihunsa yaga yanada dubu daya nan ya wuce tasha dan tafiya kauyensu, a ransa yace “Tunda sunasan Bilkisu dayawa na tabbatar zasusa Aminu ya saki Ibtisam su nemini, dama ban taba kusantar nakashashiyar nan ba balle ta haramta min aure tsakanina da Ibty.�?

Nikaina Ayusher mamakin Umar ya hanani magana, lalai wannan kan bakomai sai…�?.🏃🏻‍♀�?

******

Daga can nesa Hajiya tasa aka sauketa, takowa tai tana bin bango dan haka kawai bata yadda da Ummy ba, kartaje tasa a dinga kula da zuwanta.
Harta iso kofar gate din ta dan kwallawa Baka kira daga gefe, yana zaune yanajin radio ya dago, ganin Hajiya yasa ya taso da sauri yazo yana gaisheta, tana dan yake tace “Bala! Aminu fa?�?
Yace “Dazu ya dawo da shi da matarsa suna ciki.�?
Gabanta ne ya fadi tace “tare suka dawo?�?
Ya daga kai cikin fara’a yace “Kin dawo ne?�?
Fuskarta ta tsuke sosai tace “Kana san cemin tare suka shiga mota daya?�?
Yace “Eh tana gaba shi da ita, menene?�?
“Baisa anyi cigiyar inda nake ba?�?
Bala yai dariya yace “Inda kike Hajiya? Na dauka ai tafiya kikai dan shikam tunda ya shiga baifito ba.�?
Kai Hajiya ya dafa shikenan magani ya karye, ta ina Aminu zai zauna kusa da Ibty? Ita ta dauka yana can yana nemanta ashe yana ma tare da matarsa?
Kasa magana tai sai tafiya data fara, Bala yace “Hajiya?�?
Daurewa tai ta kalleshi tace “Karka fadawa Aminu nazo dan Allah.�?
Kai ya daga cikin rashin damuwa ya juya abinsa.
Wani jir jiri Hajiya ta fara ji, dakyar ta rike bango tana yafiya, ta hau adaidaita ta wuce gun Malam.
Malam kam ana cemai tazo ya kwashe da dariya dan tabbas yasan dole tabi abinda yake so.
Hajiya ta shiga gaba daya ba laka a jikinta, gwiwowinta tasa a kasa ta hada hannayenta tace “Malam na rokeka ka taimakeni ka taimakeni ka sa Aminu ya nemini, naji yanzu na hakura da matarsa nidai ya dawo dani gidana.�?
Malam yai ‘yan dube dubensa yace “Wannan aikin babba ne dan yanzu rabin ayukanmu sun karye sai mun sake yin komai daga farko.�?
Hajiya ta jinjina kai tace “Naji dan Allah nidai ka taimakeni.�?
“To zaki kawo dubu dari uku in an gama ki kawo dubu dari biyu.�?
A zabure ta kalleshi tace “Ina naga wannan uban kudin?�?
Yace “To gaskiya ba abinda zan iya miki sai kin kawo wannan kudin.�?
Hakiya ta sake hade hannu tana rokansa, yace “Sai dai in zaki amince da abinda nace in yaso shi sai ya biya kudin, sai ki zauna a gunsa na sati biyu kacal, daga komai ya kammala zaki bargunsa ki koma gun Aminu.�?
Shiru tai sai dai yanzu kam batada wata mafita, fuskarta ta shafa tace “Shikenan, na amince.�?

{Hmmmmmm…�?..}
3/28/22, 21:00 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*n

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004jiki
2083371244
Zenith Bank
41*

Abba yai shiru a falo gaba daya kansa ya dau zafi, koda wasa bai taba tunanin Umar zai kwabamai magana haka ba. Umma ce ta fito daga dakin fuskarnan tata ba annuri sam, tana daga tsaye tace "Yanzu Abba abinda ka aikata yayi daidai?"
Juyowa yai ya mata kallan mamaki, tacigaba " A wani dalilin zamu yadda Ibtisam ta wargaza rayuwar Bilkisu? Shikenan ita baza'a barta taji da rashin lafiyarta ba sai an kara mata da bakin cikin kanwarta? To in har auran Bilkisu ya mutu itama Ibty a kashe nata susu su zauna tare Allah ya basu wasu mazajen."

Idanu ya ware sosai yana kallanta dakyar ya daure yace "Me kike cewa?"
Ta kara tsuke fuska tace "Haryanzu ban sauko daga abinda Ibty tawa Bilkisu ba, wani irin san kai kake nunawa? Taya zata ruguza rayuwar 'yar uwarta sannan ita taje tai rayuwar da takeso?"
Kai ya jinjina cike da jimami yace "Sai yanzu na fahimci dalilin dayasa yarinyarnan sanda yaran nan yake takura mata ta kasa sanar da uwar data haifeta, to tana kula da wannan uwar tata bata damu da ita ba, bata damu da matsalar ta ba, me zaisa ta tareki? Wani irin rashin hali da rashin kirki ne zaisa ki dinga nuna banbanci tsakanin 'ya'yanki?"
"Kai ma ai banbancin kake nunawa, taya zaka manta da halinda Bilkisu take ciki? Da dalilin daya jefata? Haba! Dame yarinyarnan akeso taji? Da rashin lafiyarta ko da abinda ake mata."
Mikewa yai ya kalleta a fusace, kamar zai cigaba da fada sai kuma ya fasa kawai ya fita daga falan yai ya wuceta ya shiga daki, kana kallan fuskarsa zakasan ransa yayi mugun baci.
Zama yai a bakin gado yana sake takaicin abinda kunnensa suka jiye mai, hankalinta daya kuwa? 'Ya'ya duk naki ne amma kiri kiri san kai yasa idanunki su rufe?
Umma kam ko a jikinta, dakin Bilkisu ta wuce cikin kunar rai itama.
Bilkisu na kwance a kan gado kuka kawai takeyi kai kace an rabata da wanda yake tsananin kaunarta ne.
Zama tai a kusa da ita tadan bubuga bayanta alamar lalashi tace "Ya isa hakanan, ke kukan me kikeyi? Bakiga Umar ba sanki yake ba? Me zaisa ki cigaba da wahalar da kanki akanshi?"
Kuka kawai takeyi dakyar tadan daure cikin kuka tace "Umma dan Allah ki roki Abba yai hakuri ni wlh bazan iya zama da wani ba inba Ya Umar ba, na sani ba sona yake ba amma ni ina sanshi kuma a hakan nake sanshi, na kuma tabbatar a hankali shima zai canza zai dawo ya soni ya manta da Ibtisam."
Saman kanta ta shafa tace "Bilkisu haka kikeso ki cigaba da rayuwarki da wanda baya sanki?"
Tana kuka tace "Ya Umar fa abin tausayi ne, rana tsaka an rabashi da wacce yakeso na tabbatar shiyasa yake abubuwan nan daga sanda ya fahimci nice matarsa kuma ji ke tare dashi duk runtsi Allah zai daina."
Shiru Umma tai tana tsananin tausayinta, itakam bazata yarda a lalatawa yarinyar nan rayuwa ba ga jinya ga bacin rai, ita Ibty a kalla lafiyarta kalau ai.

*******

Ibty kam bayan ta fito daga wanka ta bude drawer dinta, dole fa ta tattaro hankalin dan mijinta, ga asiri ga shi tana kunya ai abin sai yai yawa, yanzun ma kamar dazu riga da wando ta saka, sun mata kyau sosai sai dai wannan sun kamata sama da na dazu, ta tufke kanta, ta fesa turare bata ko daura dankwali ba ta fito ta nufi kitchen, me zata dafa maidan sauki? Dan haryanzu bata gama ware wa ba gashi dama su biyu ne a gidan.
Farar talliyavta daura tare da miyan cabeji wanda yasha kayan hadi. Kamshi ne kawai yake tashi, har dinning ta kawo sannan ta nufi dakinshi ganin baya falan.
Aminu kam yana zaune hannunsa rike da waya yayi shiru yana kallo, sai dai a zahiri addu'oi ya bude yaketa karantawa a ciki.
Sallama tai kanta na kasa bakinta dauke da addu'ar neman tsari, dagowa yai ya kalleta da sauri ya juya kansa gefe yana maida wani abu dake taso mai, tabbas ya kula abin baya tashi sai ya kalleta.
Gaban madubi ta dan tsaya, ta juya baya tace "Abinci Yaya."
Jikinsa ne yai sanyi badai itama ta fahimci baya san kallanta ba? Da bai kula ba amma yanzu yaga alama tabbas ganinta ne bayasonyi.
To kawai yace taje juyawa ta fita hannunta ya bigi hotonsu wanda yake kan madubi shida Na'imah.
Ji kake rasss glass din hoton ya fashe, gaba daya hankalinta ne ya tashi ta dago ta kalleshi, a tsorace take dan ta gama shirya fadan da zatasha yanzun nan.
Saman kansa yadan dafa da yaji kamar baya gani sosai, hannunsa ya murza a idanunsa yadan lumshesu, magana yakesanyi amma sam ya kasa saboda dum din dayaji a kanshi.
Da kyar ya mike tana nan tsaye ya wuce ya nufi bandaki, Ibty kam gaba daya dana sani da haushin kanta ya isheta, haka ta dauko abin shara, tana daga takardar hoton wani abu ya fado a jiki, kamar takardace sai dai an yi mata wani nadi mai kama da la ya, kamshin da dakin yakeyi wanda ta dauka daya daga cikin turarensa ne shine taji yana tashi daga jikin wannan takardar.
Mamaki ne ya dan kamata ta bude takardar tare da kallan wani rubutu a jiki duk ya dan koke baka ganin abinda aka rubuta sosai, sai dai rubutu ne mai kamada na larabci, sannan kamshin har hawa kan mutum yakeyi, tsoro ne yadan shiga ranta nan ta fara addu’a tana kallan takardar sosai, sake hude ta ciki tai shima rubutu ne a jiki sai dai wannan karan kamar da biro akai shima ba’a gani sosai.
Ido ta kura tana san ganin me aka rubuta sai dai bata gane komai ba sai sunan Aminu da hakuri dataga ansa a jiki.
Shiru tai tana kallan takardar tabbas wannan takardar tayi shekaru anan, sannan bataji Hajiya tana shiga dakin Aminu balle hartai wannan ajiyar, badai Na’imah…�?
Kai ta girgiza da sauri tare da cewa zato zunubi sannan Na’imah banaji irin mahaifiyarta ce.

Dauko abin shara tai ta gyara gun sannan ta kalli toilet wanda haryanzu Aminu bai fito daga ciki ba, kamar zata nufi toilet din sai tace “in kuma bayan gida yake ba?�?
Nan ta fita daga dakin ta tafi bangarenta dauke da takardar tana ta sake kura ido dan san karanta me aka rubuta.
Ganin har magrib Aminu shiru yasa ta nufi dakin, mamaki da tsoro ne ya kamata ganin haryanzu baya dakin, cikin dan hanzari ta nufi bandakun ta tsaya tare da kwankwasawa.
“Ya Aminu?�?
Shiru kakeji ba magana, “Ya Aminu?�?
Nan ma shiru, cikin tsoro tadan bude kofar, zabura tai tare da sakin wani ihu ganin Aminu a kwance a kasan bandaki, da gudu ta karasa ciki ta dan dadage karfinta ta dago kanshi, dan jijigashi tai cikin tashin hankali take kiran sunansa sai dai sam baya motsi.
Wayarta ta fito ta dauka ta kira Ummy tana kuka ta sanar da ita, dan itakam ta dauka ma mutuwa yai ganin ko motsi bayayi.
Ummy tashin hankalin data shiga mara musaltuwa ne, nan ta fito sanye da hijab din datai magrib, Baffa na falo ta tasoshi suka fito cikin tsananin tashin hankali.
Tun a hanya kawai addu’a takeyi duk tsoro ya gama kamata, gani take kamar abinda ya faru ne Hajiya tamai wani abin ko kuma raine yai halinsa, gashi basu daidaita da d’an nata ba.
Ibty kam kuma kawai take tana xaune a bandaki sam ta manta a inda suke, kuka kawai take tana jijigashi.
Gaba daya tama rasa me akewa mutum a cikin wannan yanayi, buga kofa taji cikin rawar jiki ta mike ta nufi kofa, tana budewa Ummy da Baffa suka shigo duk a rikice, nan suka dungume bandaki, Baffa ya dagoshi ya dawo dashi daki sannan yace ta kawo ruwa.
Sai a lokacin ma kwakwalwarta ta bata ashe ana suma, itakam tsabar tsoro sam ta manta da komai.
Abba ya sawa Aminu ruwa sai dayai sau uku sannan yaja wani dogon numfashi ya bude idanunsa a zabure yana salatin annabi kai kace mumunan mafarki yai.
Ibty tayi shabe shabe tanata hawaye ya sauke idanunsa a kanta. Kallan ta yai sosai sannan ya kalli Ummy da Baffa sannan yasan akwai abinda ya faru.
Shiru sukai Ummy ta daure tace “Meya faru Aminu?�?
Kai yadan girgiza yace �? Yana yana na fara gani a idona sai naga bana gani sosai, na shiga bandaki ina wanke fuskata daga nan bansan meya faru ba.�?
Ummy cikin damuwa tace “Inalilahi wa ina ilaihi raji’un Allah dai yasa ba wani ciwon bane?�?
Yadanyi yake yace “Dazu fa da safe naje ganin likita ba komai da alama kawai abin ne yazo.�?
Ummy tai shiru sannan ta kalli Ibty dake hawaye tace “Ibtisam kefa? Ba abinda ya faru?�?
Tadanyi shiru hakan yasa Ummy tace “fadamin.�?
Kallan Aminu tai shima kallanta taga yayi, sai dai yanzu ba kallan tsana tagani a idansa ba, ta daure tace “Hotoncan ne ya fado ya fashe daga nan ya shiga toilet.�?
“Hoto? Me zaisa dan hoto ya fadi ya suma?�?
Aminu yadan girgiza kai yace “Nima nasan da faduwan hoton amma me zai sameni saboda hoto?�?
Kallan Ummy tai idanunta sunyi raurau dama gasu sunsha kuka, tace “Akwai abinda ya fado a bayan hoton. Duk da dai zargi nane.�?
Ummy ta kalleta tace “Daukomin na gani.�?
Nan Ibty tai bangarenta ta dauko takardar nan ta mikawa Ummy, kallan takardar Ummy tai sannan ta mikawa Baffa shima ya duba ya mikawa Aminu gaba daya hankalinsu ya tashi sai dainahi Aminu cewa yai “To me nene hadin takardar nan da faduwa ta?�?

******
Hajiya ganin kiran Malam sau biyu yasa ta dane zuciyarta ta dauka dan dama itama zata kirashi sai dai ganin kiransa yasa tsoron rayuwar da zata jefa kanta ya shige ta.
Tana dauka taji yace “Kina ina? Komai na Aminu ya wargaje?�?
Da sauri ta mike tsaye tace “Mene?�?
Yai wani dogon tsaki yace “Ina nasan meke faruwa nima? Sai dai kwalbar da muka kulle komai nashi a ciki itace ta fashe, aikin da akamai tun daga shekarun baya an budeshi sannan duk wanda muka mai yanzu komai ya tafi dama abinda yasa muke samun sauki gun mai magani saboda mun riga mun rike gudan tsorkar dake zuciyarsa ne to yanzu komai ya bale.�?
Jikinta ne yahau rawa tace “Yaushe akai wannan aikin?�?
Yace “Aikin dai da aka faramai tun na farko ai samun nasara a kanshi shine yasa muke komai cikin sauki.�?
Batasan sanda tasa farcenta a baki ba saboda tsoro tace “Nashiga uku yanzu ya za’ai?�?
Ya girgiza kai kamar tana ganinsa yace “Ai wannan aikin banaji yanzu zai sake yiwuwa kedai ki gaggauta amincewa da abinda muka nemeki dashi kila in mukai sa’a a saku dacewa.�?

Tana kokarin magana taji ya kashe wayar, zama tai dabas a kan gado gaba daga jikinta yahau rawa, sai gutsirar farce kawai takeyi, shikenan taga ta kanta, shikenan itakam ta gama yawo. Rayuwa tana neman juya mata baya�?..
5/3/22, 21:48 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*n

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004
2083371244
Zenith Bank

42*

Cikin sanyin jiki ta shigo dakin bakinta da sallama, ta kalli inda suke zaune taga idanun Aminu a kanta. Da sauri ta mayar da kai kasa taje ta durkusa kusa da Ummy tare da mika mata takardar dake hannunta.
   Jiki a sanyaye Ummy ta amsa sannan tai bismillah, bude tarardar tai wacce ta fara yin wani kaushi-kaushi sakamakon danshin jikinta da ya fara bushewa.
Duk yadda Ummy takaiga san gane rubutun kasawa tayi, ta dinga kankance idanuwa dan ta karanta amman ta kasa. Baffa ta kalla wanda ke rike da Aminu ta sauke numfashi tana cewa. "Sai dai ka duba dan ni bana gane komai wallahi." Baffa yasa hannu ya karba, yana sake kai takardar wajan haske sannan ya zaro glass dinsa dake aljihu ya saka, shiru yai yana sake bin takardar da kallo a hankali.
   A hankali suka ga yanayinsa ya fara canzawa, gani sukai jikinsa ya fara rawa, jijiyoyin goshinsa suna tashi sai wani cicije lebe yake yi, ransa ne a matukar bace, ya kalli Aminu tare da cewa "Inalilahi wa ina ilaihi raji'un! Wannan wace irin jaraba ce?" Ummy dake gefe a zaune tace dashi. "Jaraba kuma?" Yaja numfashi cikin wani yanayi yace "Kinsan me yake jikin takardar nan?" Yai maganar tare da runtse idanunsa, ya zare glasses din cikin wani yanayi yace "Haba mana shi yasa yaro gabaki daya ya kasa karawa kansa yanci, wannan hoton da akaga takardar nan tun yaushe yake a gurinka?" Cewar Baffa yana kallon Aminu cikin huci. Aminu ya kalli ibty dake tsaye wacce itama shi din take kallo dan jin abinda zai fada. "Ya dade Baffa tun aure na da Na'ima." "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun kaji wata masifa." Duk sukayi shiru suna sauraran Baffa na fada kafin yace.
   "Zuciyar Na'ima da Aminu ta kasance tamkar ta rai da mutuwa da ikon n..nai..n." Bansan me suka rubuta a gurin ba saboda ya dan goge." Cewar Baffa da ya gama karanta abinda ya gani. "Kenan anyi wannan aikin da sanin Na'ima?" Ummy ta tambaya tana kallan Aminu wanda gabaki daya jikinsa yai sanyi ji yake kamar mafarki yakeyi. "Waye ya sani. " sannan ya sake kallan Ummy yace "Asma'u Ina Uwar Na'iman take?" Ya tambaya yana kallan Ummy wace gaba daya kanta yai gingirin ta daure tace "Ni tun da na sauketa ban sake bi ta kanta ba.
Baffa ya shafi saman goshinsa yace " Da ansani ba'a koreta ba sai yanzu dole mu nemo Hajiya ta sanar damu abinda yake faruwa." Ummy ta tabe baki kafin tace "Wannan munafukar matar ce zata gaya maka gaskiya? Kasan sharrin matar nan kuwa? Kila ma ita tasa akai wannan asirin."

Ibty kam gaba daya jikinta ya gama sanyi, hawaye ne kawai suke zubo mata. Dakin yayi tsit Duk sunyi shiru, Ummy ta janyo ibty zuwa kusa da ita, lallashinta ta shiga yi. Aminu kam yana tsaye yanayinsa kadai zaka kalla kasan yana cikin mumunan tashin hankali, idanunsa sunyi ja sosai, lebensa ya ciza kawai ya juya baya. Kukan da yaji tana yi har cikin ransa yake jin abin kamar ya janyota ya lallashi abarsa.
  "Babban aikin da zamuyi yanzu shine neman inda Hajiya take, duk inda take a kawo ta dan sai nayi maganinta wallahi, sai ta sanwa ta tabo." Ummy ta tabe baki dan tasan da kamar wuya Baffa ya dauki hukunci, amman dai tasa a ranta koda kowa beyi hukunci akan Hajiya ba, ita kam sai tayi. Baffa ne ya kalli Ummy yana cewa.
"Mu tafi gida, ina san yin wani aiki." kallon Ibty Ummy tayi tare da cewa. "Allah yai miki albarka Ibtisam, inai muku fatan alkairi. Insha Allahu komai zai daidaita kuci gaba da addu'a."  Ibty ta rintsa ido tana jin wani iri, ita kam da zata iya da tace a sake musu gidan da suke a ciki. Amman ba zata iya magana ba saboda nauyin baki da kuma kunya, Aminu ma batajin zata iya gaya masa ballanta kuma su Ummy.
  Aminu befito rakasu ba, Ibty ce kawai Ummy ta rike hannunta cike da karfafa mata guiwa tace.
"Ibtisam ke rahama ce a gurin Aminu, Allah shi kadai yasan dalilin yin auranku tare. Kici gaba da kulawa da kanki da kuma mijinki, karki kuma barin wata bakuwar fuska tazo miki, wannan Hajiyar dai ta cuce mu da yawa. Tsakaninmu dasu sai dai Allah." Ibty gyada kai kawai tayi ba tare da tayi magana ba, har suka shiga mota suka tafi.

Rasa abin yi tayi, sai kuma ta kalli ƙofar shiga falo, ganin babu kowa yasa ta kalli bakin gate, Bala ta hango taji tana son zuwa gurinsa amman tana tsoron kar Aminu ya fito. da wane kwarin guiwa zai iya tashi? Kawai kije kiyi abinda zakiyi' ibty taji zuciyarta na bata kwarin guiwa.
  "Allah yasa kisamu abinda zaki tambaya" taji zuciyarta na taya ta addu'a. Bala na zaune yana wankin kayansa, ganin ibty yasa shi saurin mikewa ya isa wajanta.
  "Ai da kin kirani daga can ranki ya dade zanzo ba sai kinzo da kanki ba." Ibty tayi dan guntun murmushi tana sake duba bayanta, ganin Aminu befito ba yasa ta kalli Bala tana cewa.
  "Bala kasan inda Hajiya ta koma?" Yayi dan jim kadan kamar yana nazari, sannan yaja numfashi. Ibty na sake ware kunne dan jin inda Hajiya take. "Ranki ya dade har yanzu bansan inda ta koma ba." Ya sake yin jimm tare da kallan ibty yace "Kwanaki dai tazo." Da sauri Ibtyn ta ware ido, cike da tsoro tace. "Kwanaki kuma? Yaushe ne kwanaki Bala?" Bala ya shiga tunanin tare da rike baki alamar wanda ya manta abu. "Ka gaya min yaushe Hajiya tazo gidan nan?" Yana kame da baki yace. "Wallahi na manta ne tace karna gaya muku." Ibty na jin haka ta samu kanta cikin hade rai, harar Bala tayi kamar zata shake shi tace. "Bala! kana aiki a karkashin mai gidan nan, tsawon shekaru be taba yi maka kwangen albashi ba, ashe zaka iya munafuntarsa?"
  Hankalin Bala ya tashi ganin yadda Ibty ke magana shi daya ke ganinta kullum cikin sanyi, ya shiga rantse-rantse yana cewa. "Wallahi ranki ya dade ban taba bada kofar cutar da yallabai ba, ina jin ko shekaran jiya ne, ko rannan ne na manta ranar, tazo kofar nan take tambaya yallabai ya dawo? Nace Eh, tace shida waye a cikin gidan nace shidake." Yayi shiru, Ibty da kirjinta ke bugawa ta kalleshi. "Sai tace me?" Yaja numfashi yana kifta idanu. "Da na tambayeta nace kin dawo ne? Sai tace a'a za dai ta dawo. Nace to yanzu tana ina sai tace min karna damu, daga nan kuma ta juya ta tafi."

Ibty taja numfashi tare da dafe goshi, wannan wacce irin masifaffiyar tsohuwa ce? Lallai Aminu ya dade a cikin masifa. Ta sake juyawa tana kallon bayanta, babu kowa ta kalli Bala. "Idan Hajiya ta sake zuwa, in ta tambayeka Aminu yana ciki? Kace mata eh, idan tace nifa? Sai kace bana nan. Ka kuma barta ta shigo indai ta bukaci ganinsa kaji?" Cikin ladabi yace. "Angama ranki ya dade." ibty ta juya, har ta fara tafiya sai kuma tace. "Bala."
   Da sauri ya amsa, tana rike da hannayenta tace dashi. "Sai ina gidan sannan zakace mata bana nan, idan shi kadai ne a gidan tazo karka bari ta shiga." Yace. "To ranki ya dade."  taja numfashi sannan ta juya zuwa cikin gidan. Sai dai kuma mene? Tsaye taga Aminu a bakin kofa ya hade rai, kasa tayi da kanta tana wasa da hijab din jikinta. Aminu ganin yadda tai kasa da kanta ne ya kuma bashi haushi, takowa yayi har inda take, ibty ta rintsa ido tana jiran tasha mari. Hannu Aminu yasa ya kamo kafadunta murya a sanyaye yace.
  "Meya hadaki da Bala? Kinje gabansa kin tsaya hira kukeyi?" Ibty tai saurin kallansa kafin ta maida kanta kasa da sauri, ya sake wurga mata harara. "Nayi karya ne?"  shiru batace komai ba. "wato saboda ni bana yin hira dake shine kika fara zuwa gurin Bala? Daman kila wannan mahaukacin saurayin naki kila shike hira dake, gashi na hanashi kulaki." Ibty ta fara hada hawaye ta rintsa ido tana cewa, "Yaya." Aminu ya kuma matse mata kafadunta ta saki yar kara tana turo baki.
  "Gaya min abinda kikayi wajan Bala, dan nasan da wane ido zan ringa kallansa." Ibty ta kasa gane abinda yake nufi, ta kawar da fuska gefe tace. "Kana zargina ne?" Yai saurin dago mata da fuska, tana dagowa  su ka hada ido. Kanta ta maida kasa tana sake mamakin kalamansa.

"Kin bani abinci ma kuwa?" Ya canza maganar dan yaga tamkar taji haushinsa. Bude ido tai ta kalleshi. Aminu ya kifta mata idanuwa, "Naji ina jin yunwa shi yasa nake ganin kamar baki bani komai naci ba."
  Ibty ta kuma kawar da kai. "Nace kazo kaci abinci, a lokacin ne kuma hoton nan ya fadi, idan ka shiryaci yanzu gashi can akan dining." Tayi maganar muryarta na ɗan rawa. Sam bata gane meke faruwa ba, taya zai jefeta da wannan kalmar? Bayan yanzu ta gama hawayen taysaya mai? Sannan shi da baya san ganinta me yake shirin yi yanzu?
  Aminu ya juya kai yana kallo saman table din, ji tai ya janyo hannunta suka nufi gurin. "Kina so naci sosai?" Kallan mamaki kawai takemai, mafarki take? Dan yanda yai tambayar kanaji kasan ba cikin bacin rai bane, zolaya ce wace ya saba yi amma a da.
Cikin sanyin jiki ta daga kai, ya dan sakar mata hannun yana cewa. "Sai ki bani da kanki."  saurin bude ido tai tana kallansa. "Idan bakya sonaci sai ki tafi kawai." Ya fada cikin daga kafada. Ibty a ranta tace 'lallai mutumin nan' kallanta ya cigaba dayi hakan kawai yakeji kamar an saukemai wani gagarumin abu daga zuciyarsa, ji yake kamar ba shi bane, san da yake jinsa sama sama yanzu jinsa yake da karfi, sai a yanzuma yakeji zuciyarsa na mata kallan da yake ta fata kuma cikin hayyacinsa.
  Abincin ta zuba cikin plate hannunta nadan rawa, karfa ta nemi bashi ya hankadeta? Karfa ya ci zarafinta? Wadannan tunanin sun rike mata kai, haka ta bude miyar gaba daya wajan ya dauki kamshi, cike da jin dadi Aminu ya lumshe ido. Ibty ta janyo kujera ta zauna, kafarta na gogar tashi, kamar tana yiwa dan karamin yaro magana tace dashi. "Haaaaa." Aminu besan lokacin da ya tuntsire da dariya ba, karo na farko da ta taba ganin dariyarsa sosai kenan. Ido ta dan kifkifta tana motsa baki.
  "Kin rainani yarinyar nan ko?" Shikenan abinda take tsoro ya tabbata, dama tasan wani abin yake shirin yi.
Jiyai ya kai bakinsa kan taliyar da ta nado masa jikin fork.
  Kallan mamaki kawai takemai, sai da ya dade da cinyewa kamar bazata sake bashi ba sai kuma yaji tace. "Haa." Ya kuma sakin murmushi a haka ta dinga bashi har yaci da dan yawa. Yau itakam ta tabbatar mafarki take sai dai bataso a tasheta daga wannan dandaddan mafarkin.

******

Hajiya gabaki ɗaya ta rasa abinyi, banda safa da marwa da takeyi a gaban hotel tana kuma jan numfashi babu abinda takeyi. Tunda boka yace mata kullin da akai tun zamanin Na'ima ya warware taji hankalinta gaba ɗaya yaki kwanciya.
  Ya akai haka? Wane shegen ne yai mata wannan danyan aikin? Sai da akaga ta kusa samun Aminu a hannunta sannan za'a ruguza mata komai? Duk yawan shekarun data dauka tana juyashi ana neman tarwatsa mata rana tsaka?
Aikuwa bazai sabuba, duk yadda zatayi sai ta yi wajan karkato da hankalin Aminu. Babban tashin hankalinta ma yanzu shine gurin kwana, masu hotel din sun koreta wai dakin wari yake saboda sun raina mata hankali. To wai ita yanzu ina zataje?
  Gidan Aminu ko gurin boka da yace mata sai an sake shiri sannan komai zai koma yadda yake? Taja tsaki yafi ashirin saboda rashin mafita ga batada kudi.
Bari dai taje gurin bokan taji abinda zai yi mata shima tsohon dan iskan, gabaki daya batasan yadda zatai dashi ba akan harkar da yake sata dole, ita dama da Aminun aka ce zata yi sai ta fijin dadi dan shikam namiji ne dan camas a kalla ta huce takaicin dadewa datai ba aure.
  Kuma a kalla taci riba dan ko a baya da ta fara ganinshi sai data san lalai Na'ima tayi sa'a, jinta dingayi inama itace? Kawai dai ta hakura ne dan tasan ba za'a yarda suyi aure ba tayi masa girma.

Juyawa tayi tana kwafa tana zagin mutanan hotel din, ta janyo ma'ajiyar kudinta wanda yanzu gaba daga dubu hudu ne a ciki, oh yanzu idan suka kare ba'a gama yi mata aiki ba ya zatayi? Ko kudin zuwa gun bokan batadashi kenan? Kodai gidan Aminu zata fara zuwa ta gani ko zata dace ya bata wasu?
  'Karki soma Hajiya, kinaji boka yace komai ya ruguje, kinga kila yanzu ma nemanki sukeyi.' Kuma yin kwafa tayi, tana tarar napep, yana tsayawa ta shiga ta sanar dashi inda zai kaita. Jin unguwar da zata yasa yace "Hajiya gidan karbar magani zakije ne?" Taji mai napep din yana tambayar ta bayan sun hau hanya sosai. Ko ina ruwansa? Ta fada cikin ranta ba kuma ta bashi amsa ba.
  "Zaki karbo maganin mallakar wani ko wata kike so tabi duniya Hajiya?" Gabanta ne ya bada wani irin ras. Karfa turo shi akai yasa mata ido. Zuciyarta ta shiga kitsa mata hakan. Waye zai turo shi? Ummy! Hajiya taji zuciyarta na sanar da ita, a tsorace tace dashi.
"Turoka akai kasa min ido?" Yace, "A'a mafi akasarin mata idan sunce a kaisu unguwar da kika fada, to gidan wani boka suke zuwa." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ganin ba sa mata ido aka turo yayi ba. Karamin tsaki ta saki tana cewa.
  "Ni wazansa tabi duniya yaro? Ai ni na iya zama da mutane ba tare da boka ko malam ba. Ko yana bada maganin ciwon daji?" Hajiya ta masa tambayar cike da rainin hankali. "Ya za'ai na sani Hajiya? Nifa ban ma taba ganin fuskarsa ba, wani ne yake ciwon?" Dadi ya kama Hajiya taji yace besan shi ba. "Yatace take fama dashi muna ta neman magani har yau bamu dace ba. Ko zaka fara ajiyeni a gidan na tambaya ko Allah zaisa a dace yana badawa, sai na karba." mai napep ya dan sai ta madubi yana kallo Hajiya ta ciki, karaf suka hada ido ta yatsina fuska.
  "Yaro na fadi wani abu na rashin dadi ne?" Ya cigaba da tuki. "A'a gani nayi nace miki boka ne kuma kina cewa a kaiki. Keda yanzu ya dace kuyi ta istigfari kuna tuba harta Allah ta kasance."
Hajiya ta rintsa ido, kaji tsinannan yaro. Cikin hade rai tace.
  "Ai zaka rigani mutuwa dan ba a girma da shekaru mutuwa take ba." mai napep najin haka ya fara tangal-tangal dasu, aifa nan Hajiya ta fara ihu tana surfa masa zagi, ta ririke napep tana cigaba da zunduma ihu, ganin bashida niyyar bari ta fara bashi hakuri tana rokarshi akan yayi hakuri ya taimaka ya daina.
Ta madubi ya kalleta yaga yanda idanunta suka firfito yai kwafa tare da murmushi....

(Anya Hajiya Nason mutuwa? To ba ruwa na ita da mai napep😂)

Ayusher ce⛹🏻‍♀�?
5/4/22, 21:04 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌️‍♂�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Na Kudine ki Bada 500 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku*

2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
+447894142004

*43*

"Tsaya na sauka, idan baka tsaya ba zanyi sanadin mutuwar mu harda kai." Mai napep na jin abinda Hajiya ta fada, cikin ransa yace, 'daga wasa? Afili kuma sassauta tukin yayi yana cewa.
  "Allah ya baki hakuri Hajiya, irin wasan nan ne na kaka da jikanta." Ware ido tayi tana kallansa hannunta dafe a kirji. "Karka raina min hankali kaji, Kaga nayi kama da kalar kakarka ne da zaka min wasa da rai? Yata dana haifa bata kai ka ba bare har ta haifo min jika kamarka."
  "Allah ya baki hakuri." Ya fada yana shan kwanar da tace ya sauketa. Sai ta ya gaba parking sannan ya juyo yana kallanta yace. "Hajiya kudinki dari hudu."
   "kace mene?" Ta tambaya cikin jin karin bayani.
  "Kudinki dari hudu zaki bada." Tace, "Ai da yake daga Lagos ka dakkoni ko? Ni na zatama cewa zakai na barshi." Da sauri yai wata irin juyowa, kallan juna sukayi yace.
  "Tab four hundred naira zaki miko Hajjaju, fetur tsada yake." Ta zaro ta mika masa tana cewa. "Kayi hakuri ita kadai garan." murza kudin ya shiga yi cikin bacin rai yace, "Haba Hajiya dari biyu?" Ta fice daga napep din tana cewa.
  "Ko na tsaya ka maidani inda ka dakkoni ne?" Haushi ya kama mai napep sai dai kuma babu yadda zai yi da ita, ya burga napep din tare da bula mata kura yabar wajan. "Shegen dan sa ido, gobema ka sake dakkoni kayi min maganar da bance ba." Hajiya ta juya ta nufi gidan boka ranta duk babu dadi.

*******

Yana rike da jakarsa ya rasa abinyi, tunani kawai yake wacce makoma zai fada? Ya rasa Ibty wacce ta zamemasa tauraruwar zuciyarshi.
  Tabbas Aminu ya dace da samun mata mai kyau, Abba ya bashi ibty abagas tunda yana can inuwa yaji an bashi mata. Shi kuwa yayi rainonta ya bata kyakkyawar kulawa amman karshe ya kare a nakasasshiya.
"Bilkisu ina san yayarki, hakika bake nake so ba amman ya zanyi?" Umar ya fada a fili yana furzar da iska a bakinsa. Jin wata mota tana tambayar inda zashi ne ya fara tunanin kodai ya koma? Dan shi yanzu ba komawa kauyen ba a'a rashin ganin Ibty kadai ya isheshi, ga kuma noma dan shikam yafi karfin yin noma yanzu.
  Idan ya koma kauyen mezai yi acan? Bilkisu. Yaji zuciyarsa ta ambaci sunanta tana sake sanar dashi.
Ka koma wajan Bilkisu tunda tana sanka da yawa. Ibty fa? Zuciyar shi ba zata taba yarda ta dinga ganin ibty tare da wani kato bashi ba. "Ina sanki Ibty, me yasa ke bakya so a?" Ya fada yana rike kafadun kwandasta, jin an saki tsaki yasa Umar kallansa.
  Da sauri ya dauke hannunsa ganin kwandasta. "Wai kai a haka soyayya ce ta ratsaka? Wato baka gane wuta da aljanna ko? Ware ka bamu waje muna da aikin yi." Kwandastan ya fada yana ture Umar gefe.
  Akan idanunsa suka ja motar su, Anya mutane sun san yadda yakeji akan ibty? Shifa yana ji a cikin zuciyarshi ake hada duk wata wuta a duniya saboda radadin rashin Ibty.
  Banda rainin hankali kuma an barshi da wata nakasashiya, gashi ta nace masa itama kodan tasan ba wata moruwa zatayi ba?
  Yaja tsaki yana kuma kallon gefe da gefensa kamar mai jiran wani.
Shawara ya yanke kawai tafi koma menene ya faru. Yana tsaye har wata motar tazo ya tara ya hau zuciyarshi cike da tunani.

********

Kwance tayi akan gado tana faman kuka a hankali, duk zuciyarta babu dadi ta rasa dalilin da yasa take masifar san Umar gashi shi batatata yake ba.
  Amman me yasa baya santa? Kamar tana magana da wani a kusa sai ji tayi ance mata. Ke nakasassa ce, ibty kuma lafiyayya ce. Ta fashe da kuka a fili ta fara magana ba tare da tasan da hakan ba, ji kawai tayi tana magana cikin girgiza kai.
"Kaddara ce, wallahi kaddara ce Allah ya doramin. Please Ya Umar dan Allah ka soni koda bekai na wacce kake so ba. Ina sanka zan kuma kasance da kai a cikin kowanne irin yanayi, dan Allah karka rabu dani Ya Umar, idan kayi hakan ka ruguza duk wani ragowar farin cikin da nake tare da shi."
  Cikin tausayawa Islam ta goge kwallar data zubo ta bata mata fuska, tabbas Ya Bilkisu tana cikin jarabawa. Babu abinda ya fi ciwo irin kana so ba'a sanka, halin da Bilkisu take ciki kenan.
"Dan Allah Ya Bilkisu kiyi shiru, ki nemi zabin Allah. Idan har Ya Umar alkairi ne agareki zai dawo, idan ba alkairi bane Allah ya hada kowa da rabansa." Bilkisu kallon Iman tayi cike da mamakin kalamanta, batayi magana ba ta maida kai gefe tana dafe da saitin zuciyarta.
"Kizo kici abinci inji Umma." Kai Bilkisu ta girgiza tana cewa. "Nakoshi." Iman ta sauke numfashi "Kina jin yunwa ya kamata kici abinci, karki sawa kanki damuwa, in har kika rame Ya Umar zai kuma tsanarki. Amman idan yaga kinyi fresh dole zai rage wani wulakancin."
Maganganun Iman gaskiya ne, sai dai taya zata iya cin abinci bayan Umar din ta ya bada sharadi akan auran su. Aminu ba zai taba sakin Ibty ba bare harta sanya ran cigaba da kasancewa dashi. Kuma idan Ibty ta bar Aminu kenan aurenta da Umar ya tabbata tsinkakke, tunda tasan sai ya rabu da ita ya auri Ibty tunda ba abin aure daya shiga tsakaninsu balle.
"Ki tashi dan Allah Ya Bilki kidena damun ranki, addu'a zamuyi Allah ya dawo da hankalinsa gareki."
Bilkisu ta mike zaune ta kamo hannun Iman, cikin wani yanayi tace. "Kiyi min addu'a karya rabu dani, wallahi ina jinsa har cikin jinina." Iman ta kuma matse hannun Bilkisu cikin na ta "Karki damu kullum kina cikin addu'a ta." Daga haka ta janyo kekenta, da taimakon Iman ta hau suka fito, Iman tana mamakin wannan mahaukacin san, tabbas da Bilkisu kanwartace da dukan tsiya zata mata a dakin nan.

******

Sai da ya gama cin abincin kafin ibty ta gyara wajan ta maida komai kitchen ta gyara. Lalai yanzu kam ta tabbatar ba mafarki take ba. Amma Ya Aminu a hayyacinsa yake kuwa? Yana zaune duk inda tai sai ya bita da kallo. Sai da ta gama komai sannan ta tsaya a wajan kitchen tana tunanin abinyi. Kota koma wajansa? Idan taje me zata yi? Ko hira? Toh tace masa mene?
  Yana hangota shima a nashi bangaran yana ta tunanin me zai yi mata yanzu?
Dawowa tai ta tsaya tsakanin falanshi da nata tana dan lekensa ta labule.
"Idan kin gama leken kizo." Ibty taji Aminu ya fada. Saurin komawa ciki tayi tana zaro ido. Ya akai ya ganta? Kai wannan mutumin yana da ido sosai.
"Bazaki zo ba?" Ibty taji yana kiranta, rintsa ido tayi tana murmushi. Kunyarsa takeji sosai, yanzu menene abinyi? Taje ko ta zauna a falanta tace bataji shi ba?
Bata gama tunani ba sai kawai ganinsa tayi tsaye a bakin kofar, suka hada ido tai saurin kawar da nata tana dariya kasa kasa. "Ya haka madam?" Ibty ta tsuke baki. "Muje." Ya fada yana mika mata hannunsa. Ibty ta mika masa nata a hankali ya mikar da ita, yana rike da ita suka shiga fallonsa sannan suka nufi dakinsa. Itadai da kallo kawai take binshi.
A zahirin gaskiya Aminu neman maida hankalinsa da tunaninsa yake kokarin yin gun Ibty dan sam bayasan ya zauna shi kadai saboda ya tabbatar tunanin abinda ya faru ne zai dinga dawomai, matar daya dauka duk duniya ba kamarta lokaci daya ya fahimci ba haka ba? Uwar 'ya'yanshi? Sam bayaso ya cigaba da zargin abubuwan data aikata a kanshi, gwara ya maida hankalinsa kan matarsa kila hakan ne zai samar mai kwanciyar hankali.

**********

Tunda ya sauka a bakin titinsu mai jar kasa yake ta yatsina fuska, ya juya tare da hango yadda maza ke zazzaune a inuwa sun kishingida, daga masu shan rake sai masu fushe gyada suna jefawa a baki, yaja tsaki tare da gyara jakar bayansa ya fara tafiya. A da dayake hutu yake zuwa bai damu da komai ba amma fa yanzu da yaga alamar zama ya ganshi sai yake ganin mutanen garin wasu kucakai kauyawa.
  "Umaru ya dawo." Yaji wani yaro daga can gefe yana fadawa abokan wasansa. Wai Umaru gatsal, yaro dan karami yana fadar sunansa saboda raini. Gasu Ibty can su Bilkisu Ya Umar a gayance suke fada amman nan kamar suna kiran wani dabba. Ko takan yan majalisar bebiba ya wuce yana ta wani kwambo shi a dole ya dawo daga birni.
  Yana shiga cikin gari kuwa yan matan kauyen nan suka fara yi masa caaa kamar sunga gasasshen nama,  dan wannan abin yana daga cikin abinda ke sashi jin wani girma in yazo kauyen nan, ya tabbatar dan sunga dan gayu ne. Kota kansu beyi ba ya shige gida yana zaginsu shi a dole yafi karfin su.
"Wallahi duk wanda aka cewa dan kauye an cuce shi." Wata mace dake karya kara tana turawa cikin murhu ta kalleshi. "Umaru? Mazan fama, saukar yaushe kenan? Waye ya tabo mana kai a hanya?" Yaja tsaki tare da naushin wata akuya dake gabansa.
  "Su Hansai ne, yadda kika san basu sanni ba, banzaye gajoji kawai." Cikin sanyin jiki matar tace. "Haba mazaje, ya kake yi musu wannan maganar? Ko babu komai su Hansai yan uwanka ne." Umar cikin sauri yace. "Yoni menace? Abu daya kawai na sani ba wacce zan aura saboda ina da mata a can birni. Kima gaya musu dan wallahi zan iya fasawa yarinya baki." Dama ya dawo da bacin rai ga ana neman sake batamai rai.
  "Dama basu ce suna sanka ba ai, kai daga dawowarka sai jaraba da neman fitina."
Umar bai koma cewa komai ba ya bude wani dan daki ya shiga. Bango ya dafa yana karewa dakin kallo, wanda yake dauke da 'yar tabarma da wani filo duk ya kare, dakinsu ne shida yayansa, tsaki yaja yana tuno yadda ya baro narkeken gadon Bilkisu da lumtsuma-lumtsuman kujerun da aka zuba, nan da nan ya fara jin kamar ya cuci kansa. "Anya bazan koma ba?" Ya tambayi kansa yana sosa haba.
Ai daga waje ya fara jin ana cewa "Umaru ne da gaske?"
Jin muryar Babansa yasa gabansa ya fadi, tabbas zaici duka in mahaifinsa yasan abinda ga aikata, ita kanta mahaifiyarsa bazata yarda ba.
Sum sum yadan leko yana washe baki ya tsuguna yana gaida mahaifinsa.

*******

Gyara mayafi Hajiya tayi tana kuma waigawa baya, ji take tamkar ana binta idan ta juya kuma bata ganin kowa. Rai a bace ta shiga sai faman jan numfashi take, Allah dai yasa kar yace sai ta bashi kanta, idan yai mata haka tabbas zai ilatata, sakamakon wani irin zugi da takeji gurin nayi mata tun wancan zuwan nata.
  Yana ganinta ya fara dariya yana kuma dukan cinya, tai masa kallon mamaki batace masa komai ba har ta samu wajan zama. Ji tayi yace.
"Daman nasan dole zaki zo Hajiya, akan Aminu na tabbatar zaki bar duk wani abu kizo wajena. Sai dai k..." Cikin takaici ta dakatar dashi tace. "Menene abin yi?"
Shiru yai yana kallanta yace "na fadamiki sai kin samu macen da zata dauke hankalinsa daga kan matarsa, a da can abu bai yiwu ba balle yanzu da komai ya wargaje."

Shiru tai tana tunani, cikin bacin rai tace "Kafi kowa sanin banda kowa a duniya banda Naima ina......."
Sai kuma tai shiru ta kalleshi ta dan kauda kai tana motsa baki, kallanta shima yai kafin ya bushe da dariya yace "Badai ke kanki kike tunani ba ko?"
Wani kallo tamai tace "Me kake san cewa? Ai ko da ba auransa ba zan iya dauke hankalinsa daga kan tsinaniyar 'yarnan, na kai makurar da ba abinda bazan iya aikatawa ba.
Dariya ya bushe dashi wanda ya kasa dainawa har abin ya fusatata, yau na tabbatar da abinda na dade ina zargi.
Ta hade rai sosai tace "Me?"
Na dade ina tunanin meyasa bakyasan Aminu yai aure? Bayan zaki iya neman maganin mallakar matarsa ki zauna lafiya? Sai dai yau kin nunamin dalili.
Ni babu wani dalili da nake nema ka bani magani da mafita  wacce zatasa Aminu hankalinsa ya kasa kwanciya sai ya bani gida da motar hawa, ni yanzu su nake san ya siya min sai na barshi  da wannan figaggiyar matar tashi." Yayi dariya yana nuna mata kusa dashi, tayi kamar bata gane ba yace.
"To tunda dai kin dage a barshi. Yanzu kizo nan dan dama Shine dalilin da yasa nace kizo din. Wannan aikin da za'a yi miki babba ne, kedai kawai kibi umarnin abokan aiki wato aljanun da suke yi." Hajiya ta kama baki, ta kuma kallan inda yake tace.
"Menene umarnin nasu?" Boka ya matsa kusa da ita, Hajiya kamar ta fashe da kuka yace. "Zaki kwanta dani, kiyi min abinda ko a mafarki bantaba jinsa, karkiyi korafi ko ki dinga jin haushin abin, yin haka zai sa aikin da za'a yi yaki yin kyau." Ranta ya sake baci tace.  
"Wannan aikin kam ya isheni, gabaki daya kun ruguza min guri kun maida shi kamar wani bakin kofi kowa yazo yasha ta wajan. Ni kam babu wata hanyar sai wannan ne?"
Mamaki ya kamashi, ta gaji kenan? Yanajin dadin matar nan gashi ta fara nuna gajiyawarta. Kodai yai mata asiri ta yadda komai yace mata ba zatai masa musu ba? "Nace babu wata hanya sai wadda ka fada?" Muryar Hajiya ta katse masa hanzarinsa.
  "Idan har kina san Aminu yai miki abinda kike so, dole sai kin kasance da mutumin nan dani na kwanaki bakwai." Hajiya ta rintsa ido tanajin wani irin bakin abu a wuyanta, haushi da takaici yasa tace masa, "Sai kai tayi." Murmushin jin dadi yai tare da janyo wani ruwa ya mika mata. "Fara shan wannan, ruwan farin jinine. Idan kika sha muka gama tarayya aka gama sauran aiyukan zakiga aiki, Aminu da kanshi zai nemoki." Banda tana san aikin nan da ba zata taba yadda tayi wannan aikin bakar wahalar ba.
  Dakyar ta shanye maganin saboda tsananin baurin da yake yi, ga wani wari kamar na kwata.....

Ayusher ce🏌️‍♂�?
5/6/22, 12:03 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌️‍♂�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Na Kudine ki Bada 500 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku*

2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
Call.... +447894142004

*44*

A can bangaren Umar kuwa tunda ya shiga cikin dakin ya kasa fitowa, ya zauna sai zabga tsaki yake tamkar wani karamin yaro.
  "Ga tuwon dawa nan miyar kuka, sabuwa ce ma Larai ta kawo min ita kyauta."
Umar yabi langar tuwon da ido, ganinsa bakikirin yasa shi kawar da kai. Shifa dama in yazo kauye da kudinsa yake tahowa ya dinga siyan abinda ransa ke so sai dai wannan karan ya taho ba kudi saboda Abba bai barshi ya shirya ba, gashi ya saida abubuwan kasuwarsa ya tattaro kudin ya boye a daki yana so in ya sace Ibty su gudu da kudin, sam ilimin maidasu banki baizo mai ba.
Kallan Goggo yai yace "Gwaggo bakuda fried rice? Ko 'yar shinkafa? Naga da ana kokarin yin abinci mai dan dadi?" Ya tambaya yana sauke numfashi. "A ina take mazan fama? Mace ce ko namiji?" Umar ya kuma jan tsaki dan yasan tasani sarai tsabar ya kona mai rai ne take wannan zancen, sau nawa tana zuwa gidan Abba tana ci? Cikin jin haushi ya dago tare da cewa. "Abinci ne fa." Gwaggo ta bude ido. "Ai kaji, ni ina nasanshi banda kinibibinka? Idan zakaci tuwo kaci shi garemu, idan bakaci ka barshi akwai mabukata."
Umar ya sake bin tuwon da ido tare da cewa. "Kai haba ina! ni gaskiya bazanci wannan bakin tuwon ba wallahi."
  "Iyyy ba shakka, to karkaci mana." Gwaggo ta dauke ta fita da kayanta sai fada take yi. "Karyar banza karyar wofi, indai kana cikin kauyen nan kuwa sai dai ka mutu da yunwa dan banga inda zaka samu irin abincin da kukeci ba a birni. Ai ni tunda naga rashin darajarka a biki nasan lalai jin dadi da rashin godiyar Allah ne ya maka yawa.
Umar naji ya dafe goshi tare da tuno abinda yake yi, cikin isa da iko zai ce da Bilkisu ta dafa masa abu, tana rawar jiki take masa kuma mai dadi. Dan in yaso mugunta ko an dafo abinci daga bangaren Umma sai yace shi bayasan wannan abincin sai dai ta sake wani.

  "Anya zan sakeki Bilkisu? Na rasa hasken zuciyata Ibty, wannan shegen mai kama da aljanu ya rike ta kam. Allah ya isa ban yafe ba, nasha wahalar kulawa dake amman aka cuceni. Har abada bazan yafe maka ba dan banza mai kan agwagwa."
Har aka yi sallar isha Umar yana daki yana shakar bacci, tun Gwaggo na zuwa lekashi harta kwanta abinta ta rabu dashi. Wajan karfe goma sha daya na dare ya farka da wata masifafiyar jin yunwa.
  Alwala yai yaje daki, sallah yai ya fito yana ta raba idanu da alama neman inda aka ajiye tuwon dazu yake. Wajan girki ya karasa yanata bude-bude, karar motsi yasa Gwaggo fitowa daga daki tana haska wajan.
"Wace irin fitinace wannan? Mekake nema a wajan?" Cikeda rashin damuwa yace. "Tuwon." Gwaggo ta rike baki, "Tuwo! Aikuwa babu." Ta fada tare da komawa zata shiga daki yace. "Tuwon ne babu?" Tace "Kwarai ma kuwa, ko kana shakka ne?" Kafa yasa yai shuri da murfin tukunya yana masifa.
"Ya za'a ce babu tuwon bayan ansan banci ba? Wannan ai ba daidai bane wallahi. Haba Gwaggo ya zaki cinye?" Mamaki ya kamata. "Wai dama zakaci? Bana kai maka ba ka tsaya kana cewa wai kai kafi son menene? Toh tuwo dai ya kare sai kasan abinyi."
  Tana kaiwa nan ta shige dakinta, Umar kuma yai kwafa ya koma daki. Kenan yau da uwar yunwa zai kwana, dama ba wani abu yaci ba. Duk ya rasa abinyi dan ko kudin siyan awara bashi dasu ballantana yace zai siya, kodama yana da kuɗin yanzu babu kowa a gari saboda dare ne duk antafi gida.
"Idan ka gama kunkunin kazo ka karba, ai da na zata balangun Dan Bale zakaje ka siyo tunda ba zakaci tuwon dawa ba." Umar yaga Gwaggo na miko masa langar yai saurin karasawa zai karba ta rike. "Bazakai min godiya ba?" "Nagode Gwaggo." Ya fada yana cizon lebe.
  "Ato gobe ma kace min bazakaci tuwo ba kaga karyar banza." Umar yaki magana ya koma ya zauna tare da faracin tuwon yana lumshe ido saboda dadi.
Tas ya cinye tuwon ya kura da ruwan sanyi na randa tare da sakin katuwar gyatsa yana faman hura hanci.
  Saboda baccin da yai hakan ya hanashi yin na dare, ga duhu ga sauraye sai kuka suke wasu kuma suna gasa masa cizo yana ta buge-buge da riga. Haba malam birni lafiya ne, idan babu nepa ga inji, idan babu kuma ga sola duk dan kar a zauna cikin duhu. Gashi zuciya ta kawoshi kauye yazo sai wahala yake sha.
Haka yai kwanan zaune gashi ko tunanin yin nafila da istigfari beyi ba, sai tunanin yadda ibty take mannewa jikin Aminu yake, daya rintse ido zai hangesu kwance kan gado suna soyayya a zabura zakaga ya mike yana sauke huci sai kuma ya jawo filo ya nausa yace "Allah ya isa tsakanina dakai mugu, azzalumi dan bakin ciki."
  Babu ruwanshi da yadda ya baro Bilkisu bare ya tausaya mata, yasan dai kawai zai bar auransu ne saboda shima yaci gaba da morar arzikin da yakeci.

**********
Aminu ya zaunar da ita kan gado kallansa kawai take itakam mamaki duk ya isheta, gani tai ya koma gefe ya zauna, cikin sanyin jiki ta dan sunkuyar da kanta kasa, ita dama tayi mamakin yanda ya canza ashe ba gaba daya ba......"
Jin an jawota ya kwantar da ita akan cinyarsa ne yasata kallansa cikin wani yanayi, hannu yasa yadan zare hijab din kanta sannan ya cire hularta ya sa hannu asaman gashinta, kallan mamaki kawai takemai sai wani irin faduwar gava da takeji akai akai, shiru ne ya ratsa dakin saboda abu ne da basu taba yi ba, itakam lumshe idanu tai kawai tana addu'a Allah karya kawo abinda zai sake shiga tsakaninsu.
Cikin wannan yanayi taji yace "Kiyi hakuri ki yafemin."
Idanunta ta bude a hankali ta saukeshi akansa, dan murmushi yai cikin sanyi yace " I don't know what happens to me, gashi kiri kiri zuciyata nasan tausaya da baki kulawa sai dai jikina baya iyawa, haka kawai in na kalleki sai inji duk duniya ba wanda na tsana irinki, sai zuciyata tai ta fadamin abubuwa daban daban."
Idanunta ne suka dan ciciko tana kallansa, ganin ya kalli idanunta yasa tadan sauke idanta kasa, sunkuyowa yai wanda hakan ya kara sa kata faduwar gaba, a hankalinya sumbaci idanunta, sannan yace "Wannan yayan ya saku kuka sosai ko?"
Cikin wani yanayi tace "Eh."
Murmushi yai yace "Madam yaushe na tambayeki?"
Dan baki ta turo tace yanzu mana."
Ya dan girgiza mata yatsa yace "ni ga wanda na tambaya nan bake ba.."
Ta kalleshi tadan juyo ta ciki saitin cikinsa tana san yin magna sai dai haryanzu kwarjini yake mata "Ya ya? Har an gama maganar dani? Bayan ina kallan yanda kika dage kina magana da Bal......"
Batasan sanda ta dago tasa hannu ta rufe mai baki ba, dan baya ta turashi hakan yasashi kwanciya akan gadon ita kuma ta dan daneshi da hannunta a bakinsa, kallansa tai da sauri ta cusa kanta cikin kirjinsa cikin kunya, "Ni dama nasan abinda kike san aikatawa kenan."
Dagowa tai cikin mamaki tace mene?
Yanda ta dadaneshi ya nuna mata yace "Gashinan, so kike ki kwanta a jikina.
Kokarin mikewa ta fara yasa hannu ya rike kugunta, yace "Daga baya kenan, yanzu wayancewa kike shirin yi."
Kallan shagwaba tamai tace "Allah ni....."
Kai yadan karkatar alamar ko?
Hakan yasata yin murmushi, a hankali ya kwantar da ita a kirjinsa shiru suka sakeyi, can cikin wata murya yace "Me kike tunani akan abinda aka gani a bayan hoton can?"
Shiru tai bata dago ba sai dai tace "Banida kwakwaran hujjar dazan bada akan abinda banida masaniya a kai."
Yanayinsa kadai xaka kalla kasan lalai yanacikin wani yanayi mai wuyar fassarawa.
Murmushi yai, dakin yai dan shiru kowa da abinda yake sakawa a ransa, "Abinda ya faru dazu yana nuna san da Na'imah ke min da wanda nake mata ba tsakani da Allah bane?"
Ibty ta juyo tana kallansa dan ya bata tausayi sosai yanda yai maganar, mikewa zaune yai ya dan yi ajiyar zuciya yace "ina tunanin na girma nasan duniya, ni babba ne ashe babu wanda ya kaini kankanta."
Ibty ta bude baki zatai magana taga ya mike kallanta ya juyo yai yace bari nai meeting, karfe uku ne gashi ban kula ba har ukun tayi."
Kai ta dagamai a hankali tare da binshi da kallo harya fita, komawa tai ta kwanta rufda ciki s kan gadan tace "Wannan wani irin bala'i ne?"

*******
Washegari.....
Abin duniya duk ya ishi Hajiya, alakarta da boka ya fara isarta musamman da yanzu take jin idan beyi ba kamar ana tsunkulinta a sassan jiki, ga wancan tsinanen mutumin da yafi boka danshi inya fara ganayin kusan awa biyu kafin ya gama, takaicinta ma sam ta kasa sanar dashi bata so ta gaji. Dan karamin daki ko ince dan karamin gida wanda daga daki sai bandaki suka ware mata daga kusa da gidan Malam ya take zaune a ciki suna abinda suke so da ita, gaba daya ta kasa nuna rashin san da takewa wannan rayuwar, duk ta rame ya jeke, wai kuma duk cikin nemo kan Aminu ne.
  Tana zaune tayi zugum kamar wacce taiwa sarki karya, wayarta tai ringing jiki na rawa ta dakko. Dan dazun nan mutumin nan ya kawo
Mata sabuwar waya ya kuma sa an mata welcome back na sim dinta, dan tun jiya take rokonsa akan ya taimaka mata, sai daya sadu da ita sau biyu s lokaci daya wai kudin yin welcome back da waya.
Ganin Aminu yasa zuciyarta harbawa, haka kurum taji yau bata san daga wayarsa, dan haka harta tsinke bata samu damar dagawaba. Gefe daya na zuciyarta yana gaya mata aikin boka ne ya fara aiki.
Kiran ya sake shigowa ta dauka jiki na rawa kamar tana gabanshi muryarta har tawa takeyi.
"Waalaikas salam." Tana fada ta sa kuka cike da makirci. Aminu dake zaune a falo bayan ya
dawo daga aiki, da sauri ya dafe goshi, gaba daya haushinta yakeji, abu daya yasa shi nemanta dan yanasan jin meke faruwa sannan dazu Islam da Ilham suka tambayeshi tana ina? Dan suna dawowa dazu suka nufi bangarenta suka ganshi a kulle. Wai Suna san ganinta.
"Ina wuni Hajiya?" Hajiya ta hadiye kukanta, mamaki ya kamata a da idan har yaji tana cikin damuwa rudewa yake balle kuka, amman yanzu tana kuka yana miko mata gaisuwa.
  "Dama tambaya zanyi kina ina?" Hajiya ta zaro ido 'Mezai mata? Ko gidan ya siya mata ne? "Hello." Taji ya fada tai saurin dafa bango.  "Ina gidan wata kawata, ince dai lafiya ko Aminu?" Aminu yace, "Ina so nasan inda kike yanzu." A razane tace,
"Lafiya dai ko?" Yace, "Zanzo gurinki ne." Ta zaro ido tamkar tana gabansa, Toh me zai yi mata? Gabanta ne yai wani mumunan faduwa badai maganin da akace an bude komai ya karye yake kokarin Tuhumar ta akai ba? Ya san Na'ima ta aikata ne? ko kuma sha'awar ganinta kawai yakeyi? Tana san tasan mezai kawoshi dan tasan abin fada masa.
  Muryarsa ce ta katseta yace "Hajiya kinyi shiru." Tace "Wallahi ina fama da ciwon ciki ne, sai dai ka bari wani lokacin sai mu hadu. Kaga ba dadi nace kazo bayan matar batasan zakazo ba, ni kuma bazan iya fita ba saboda ciwo."
Kafin ya bata amsa tayi saurin cewa "Ina su Ilham? A gaishe min dasu."  Kafin Aminu yai yunkuri magana yaji ta kashe wayar, abin yai matukar bashi mamaki, ya kuma sake tabbatar da cewa Hajiya tasan da wadannan layun ta kuma san dalilin dayasa yake nemanta sarai.
Tsaki yaja cike da haushi ya ajiye wayar, yana jin tsananin kunya da tsanar kansa yanzu a kalli Hajiya ace surukarshi ce, shi kuwa mai ya kaishi hada zuri'a da wadannan mutanen? sannan su Islam su kalleta suce kakarsu ce, wannan abin yana ci masa zuciya.

**********

Da kallo Abba ya bita, Bilkisu kuwa kamar ta sani taki yadda da dago kai sai wasa tske da wajan key din kekenta. Umma ce ta fito daga kitchen ganin Bilkisu yasa ta saki murmushin jin dadi, saboda bata san ganinta cikin damuwa.
  "Kin fito kici abinci?" Bilkisu ta daga kai batace komai ba dan har lokacin ranta babu dadi.
"Zonan Bilkisu." Cewar Abba yana ajiye wayar hannunsa. Ta gungura keken zuwa gurinshi bata kallesa ba yace.
Yadan ja numfashi yace "Kina tunanin Umar zai yadda da aure tsakaninku? Ada ina yiwa Umar kallon mai hankali da sanin yakamata.
Amman yanzu tunanina ya kauce daga wannan kyawawan zuwa akasin su. Kina ganin zakici gaba da zama tare dashi har tsawon rayuwarki?"
  Shiru Bilkisu tayi dan ji take ko hauka Umar yake zata iya zama dashi, ballanta kuma yana da hankali kawai soyayya ce ta rufe masa ido kamar yadda ta rufe mata duk wani aibunsa. Kuma yanzu ma maganganun da Abba keyi akan shi, ji take kamar ta mutu saboda aibata mata miji da yakeyi.

Cikin sanyin jiki tace, "Abba lokacin da kuka yiwa ibty aure batasan waye mijin ba, kunyi mata an kai ta gurinsa, ya taya har ta janyo suka fara kula juna duk bamu sani ba. Abba nima ina so ku bar aurena dana Ya Umar har zuwa lokacin da zai manta da wacce ke cikin ransa."
"Muna so mu karbar miki yancinki ne Bilkisu, barin Umar a haka ba zai sashi ganin mutunci da darajarki ba. Ki bari mu nuna masa ko wacece ke a gurin mu ta yadda nan gaba zaiji tsoran takaki yadda yakeso. Hakan zai yiwune idan har kin bamu hadin kai Bilkisu." Tayi shiru tana share hawayen da suke bata mata fuska.
"Shikenan Abba amma dan Allah karkuyi yadda zai sakeni, idan Ya Umar ya rabu dani zan shiga damuwa dan Allah Abba."
Tausayinta ya kama Umma, ta karasa wajanta tana lallashinta cikin kulawa "Ya isa kukan, Insha Allahu yadda kike san yaran nan haka shima zai soki wata rana, zanci gaba da yi miki addu'a Insha Allahu ba zaki kuma rasa wani abu ba, kiyi shiru ki kuma yi hakuri." Abba ya amsa da "Amin ya Allah."
Shiru Abba yai cikin wani yanayi yace "Iman fa?"
Tace "Tana gidan koyan dinki."
"Kin kira Ibtisam din?"
Tace "Ita da hankalinta yake a kwance? Kana ganin gidan da aka kaita ga mijinta na santa, zan kirata gobe, tunda kaji shiru bata kira ba ai lafiya ce, bakaji hausawa sunce inka ji shiru lafiya ba ce?"
Kallanta yai kawai baice komai ba, yana mamakin yanda sam take nuna banbanci karara akan 'ya'yanta, sam bata nunawa Ibtisam kulawa, haka ma Iman to anyi sa'a ita Iman da kanta take nemawa kanta abinda takeso ba kamar Ibty ba.
Daga haka suka samu Bilkisu taci abincin sannan suka samu ta fara walwala ana ta hira da ita sama-sama, duk da haka zuciyarta na wajan Umar da kuma ina zashi? Wannan abun yana damunta sosai, tana so tasan yana wane wajan ko hankalin da yake ciki.

*******
A kwana a tashi asarar mai rai.....
Yau sati biyu kenan Hajiya na zaune cikin wannan dakin kwani irin ciwon ciki take fama dashi wanda in har ya motsa mata duk irin maganin da zai bata batajin dadi har sai mutumin nan yazo yayi mu'amala da ita ta baya kamar yadda ya saba yi.
  Kwananta goma a gurinsa saboda ciwon da yake damunta yasa bata tafi ba, kuma ko ya bartama bata da wajan zuwa. Hajiya kwance tana ta faman murkususu abin har ya fara bawa bokanta tsoro, yace ta shirya zata bar musu gida saboda yana tsoran ta mutu a gurin shi ace ai shine ya kasheta tunda kowa yasan wannan dakin da take nashi ne. Cikin azabar ciwo tun abun na cinta a hankali yanzu ko zama bata iya yi saboda wajan ciwo yake sai dai tayi goho. Babban tashin hankali mutumin da yake zuwa safe da rana da daddare yau kwana biyu kenan ko lekota baiyi ba, dan kayan dadin dayake kawo mata suma duk sun kare, ga yunwa ga azaba ga babu kudi.

**
Tana kishingide gun sai uban zugi yake mata amma duk da haka dan bala'i neman mutumin nan takeyi ko shi ko boka wani yazo ya biya mata bukata.
A fusace ya bude labulen dakin da take a kwance ya kalleta cikin jin haushi. "Dama da nace ki shirya zaki barmin guri ashe bakiji ba?" Cikin wahalar ciwo Hajiya tace. "Ina zanje?" Ya rike baki "Da ina kike zaune? Koda a karkashina kike? Ni da ba mahaifinki ba bakuma mijinki ba ina zan dauki nauyin muhalinki?"
Cikin zafin rai Hajiya tace " To kai in bazaka kula dani ba ka sanar da wanda yake bukatata ai yanada kudi tunda har gida yaso sai min, ka fadamai ya sai min gida na koma, a wannan matsiyacin gidan naka kake cin zarafina?"
Dariyace ta kusa kwacemai lalai batasan har mutumin da take magana ya gama aiki ya manta ma da ita ba? Dan harya samu wata?
Jiyai tace " Wai ma naga ai yanzu aiki kake min ko har an gama? Dan banga Aminu ya susuce yana nemana ba?" Ta fada tana sake cije lebe saboda azabar da takeji. Wayarta ya hango yaje ya dauka ya fice tana ta kiransa Amman yaki kulata.
Lambar Aminu ya nemo, jikinsa har rawa yakeyi saboda san ya kirashi. Dan shikam tsoro yake gashi har an fara gulmar sa akan ya ajiye babbar mace yana bushasha, kenan kiris zai sa ace shiya kasheta.

Acan bangaren Aminu kuwa Ibty na zaune kusa dashi lokacin suna zaune a falo wai kafadarsa ke ciwo ta ce zatamai tausa, tana farawa ya jawota ya dawo da ita kan cinyarsa sannan ya kalleta yace "Shikenan kafada na ciwo itama kafar neman karyamin ita ake san yi."
Baki tadan bude tace "Yaya kaifa ka jawoni."
Ya danyi shiru sannan yadan girgiza kai yana dan kane ido irin mamakin nan yace "Oh ni yaran yanzu, ba kunya in su Islam suka shigo suka ganki a haka kuma kice musu me?"
A firgice ta nemi mikewa yasa hannu ya riko kasan cikinta, kallansa tai tace "Yaya Allah karsu shigo su ganmu a haka."
Kafada yadan daga yace "Wannan kuma laifinki tunda kece kikai fitsarar zama a jikina."
Zatai magana wayarsa tai kara.....
Bugu biyu ya daga tare da yin sallama, dama ya dauke kai akanta ne yana jira har duniya ta koya mata hankali sannan ya sata a gaba ta sanar dashi duk abinda ke faruwa.
A rayuwarsa bayasan zargi shiyasa gaba daya yake kokari kauda kai akan abinda ke faruwa, a koda yaushe ya tuna ji yake kamar zaiyi kwalla, ya yarda da Na'imah iya yarda bai taba tunanin zata aikata mai haka ba, har zama yake yana san yai tunanin wai wani irin so ya mata? Sai dai baya iya tunawa, wanda hakan ya sake tabbatar mai lalai wannan san bana Allah bane.
Sabanin muryar da yake tsammani sai yaji ta namiji.
A dan zabure ya mike yace "Lafiya dai ko? Ina mai wayar?" Yadda Aminu yai magana ne yasa boka zaro ido, sosai yaji tsoran su hadu a zahiri dan daga ji zai yi matuƙar kwarjini.
"Batada lafiya munga sunanka ne na karshe wanda sukai waya da ita shi yasa muka kira mu sanar dakai." Aminu ya shiga mamaki kafin yace " Batada lafiya?"
Cikin dauriya yace "Ina Hajiyar yanzu?" Bokan yaja numfashi, yamai kwatancen can wani guri sannan ya katse.
****

Kallansa Ibty tai cike da sanjin bayani, riko mata hannu Aminu yai yana dan matsawa yace.
"Babu komai." Ibty ta kalleshi sosai, ganin kamar tana masa kallan makaryaci ne yasa shi yin murmushi tare da cewa "Hajiya ce wai bata da lafiya." Cikin sauri tace "And?" Yaja numfashi ya sauke tare da cewa. "Ana jiran naje inda take."
"Bazaka ba, trap ne, wannan matar Allah akwai abinda ta shir......."
Labanta ta hade saboda tuna kalaman da takeyi, a cikin ranta tace Banda rainin hankali meyasa tun lokacin da ka kirata ba'a ce kaje ba sai yau? Bazakaje. Yanda ta dage kan cewa bazai je ba ne ya bashi mugun mamaki ta dauke tace "Allah nidai A'a haka kawai su sake rikita ka, daga rashin kallo a koma tsana mai karfi, dan Allah ni nasan kunun da aka baka ne yaja ka tsaneni lokacin, yanzu wa yasan me za'a baka?"
Kallanta kawai yake tana fada yace
"Madam calm down! Zanje ne saboda su Islam." Zuciyar Ibty tayi sanyi amman dai bata san yaje gani take tamkar munafuncin Hajiya ne. "Karki damu Insha Allahu babu abinda zai samu mijinki kinji?" Sunkuyar da kai tayi tana wasa da gefen rigarta da hannunta.
Tashi Aminu yai tsaye yana gyara maballin riga. Ganin ya dauki mukullin mota yasa Ibty tai saurin tashi ta dauki hijab dinta tana turo baki. Aminu ya kalleta da mamaki yace. "Yah?" Sai da ta kawar da kai sannan tace dashi "To nidai muje tare, ni gaskiya bazan bari kaje gurin wannan matar kai kadai ba."
  Aminu ya janyota a hankali ya sanya ta a jikinsa, ya dan sumbaci goshinta tare da bubbugawa bayanta alamar lalashi tabbas ta damu dashi tana kuma san kare masa lafiyarsa, daidai kunnan ta yai maganar cewa. "Karki damu, kici ba da min addu'a Insha zanje lafiya na dawo." Babu yadda ta iya dole ta kyaleshi ya fita ya shiga mota.....
Da kallo ta bishi idanunta kamar zasu kawo kwalla, nan danan ta koma ciki tai alwala tadau Qur'ani, bataso wani abu ya sake shiga tsakaninsu, dan yanzu rayuwa suke mai cike da sha'awa tana san Aminu har cikin ranta ji take kamar bazata iya rayuwa yanzu babu shi ba.

*Ayusher ce🏌️‍♀�?*
5/8/22, 21:51 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*46*

Tunda ya shiga daki ta koma ta zauna akan kujera dabas gaba daya mamaki ya hana Ibty yin motsi, tasan za'ayi haka tabbas dan tunda yace gurin Hajiya zashi tasan da wahala ba'a sake hargitsa mata shi ba. Haushi duk yabi ya kamata saboda ita ta barshi ya tafi, inda ta dage akan cewar tare zasu tasan zai yadda. Wai har sai yaushe ne Hajiya zatabar Aminu yai rayuwar jin dadi? Daga auran yarki shikenan sai abu ya zama masifa da bala'i? Kodama auran ai ba dasaninsa ba.
Ibty kam ganin zancen zuci bayi mata zai yi ba yasa ta koma daki, wajan madubi ta nufa tana kallan kanta. Ko har sai yaushe zasu samu kwanciyar hankali kamar ko wane ma'aurata?
Kwana biyu ta huta da matsalar Umar, amman ta kasa rabuwa da matsalar Hajiya. Ibty ta kuma matsar da fuskarta tana karewa kanta kallo tace "Ada ta dauka uwar miji itace matsala sai dai a nata bangaren ta rasa da me zata kira Hajiya, wannan bala'i dame yai kama" Kanta ta dafe, ada ta bari Umar ya takurawa rayuwarta, nan ma Hajiya ta takura ma rayuwar auranta sai dai tana ganin yanzu bazata bari a kara shiga tsakaninta da Aminu ba, shine farincikinta, turare tasa hannu ta janyo ta feshe jikinta dashi sannan ta fito. Dakin Aminu ta nufa, cikin shahada ta dan murda tana fatan Allah yasa ya bude kofar, jin kofar ta bude yasata yin wani ajiyar zuciya, a hankali ta tura kofar gani tai bakowa a kan gadan, dan tura kofar ta sakeyi yi sosai, me zata gani? ganin kasan dakin tai duk kaya hakan yasa tai saurin shiga.
Turarukan kan madubinsa ne duk ya watsosu kasa, sannan takardar hutansa shi da Na'ima wanda glass din ya fashe Aminu duk ya yaga shi, yana tsaye rike da kai alamar ya rasa mai zaiyi. Ibty ta kalli Aminu zuciyarta na bugawa dan tana tsoran ya juyo ya ganta yai mata wulakanci. Amman duk da haka sai da ta nemo juriya ta dake sosai ta karaso ciki ta tsaya a bayansa tayi masa magana cike da kulawa.
"Zuciyar da aka ginata da hakuri babu abinda ya kamaceta a koda yaushe sai hakurin, Abban Islam kana cikin jarabawa mai matukar wahala, sai addu'a da fatan Allah ya baka ikon cinyewa. Kayi hakuri ka fitar da kanka daga jikin Hajiya shine kawai zai sanya ka samu lafiya da nutsuwar zuciya."
"How?" Ibty taji ya fada cikin juyowa a fusace, kafin ta kuma magana yaci gaba da cewa.
"Taya zan yi nesa da ita bayan akwai Ilham da Islam a tare damu? Meyasa Hajiya zata min haka? Ta cuceni ta cuci yarana da zasu yi mata kallon kaka. Wallahi nayi da..." Sai kuma ya kasa karasawa ya kalli ibty yana cizon labansa.
Taku daya ta kara ta kwantar da kanta a gadan bayansa, dan yanada tsayi duk da itama tanada tsayi amma bata kaiwa samansa, idanunta tadan kumshe ta daura hannu a gefen kanta tace "Kayi hakurin daka saba yi, Habibty........." Kalamanta sun matukar sanyaya masa zuciya har besan lokacin da ya juyo tare da kamo kafadunta ya rike ba ya rungumeta a jikinsa tsam.
"Thank you." Ya fada, dagota ya sake yi yadan karkatar dakai yace "A tabbatar an cigaba da kirana da wannan sunan."
Labanta ta hade jitai ya sunbaci saman goshinta. Tadanyi murmushi tace "Ni kunya nakeji in kiraka haka a gabansu Islam."
Kunnenta ya matso yace "Ya zakiyi?"
Tace "Dame?"
Yai wani murmushi "Dole ki kira ni haka, dan in bashi ba bazan amsa ba."
Baki tadan turo, yatsarsa ya dan hade kamar sai rankwashi goshinta hakan yasata runtse ido da sauri, ji tai ya jawota jikinsa ya rungume, "Gobe kinada skul ko?"
Kai ta daga, ya jinjina kai yace "Yara fa?"
Suna daki suna wasa, yadan daga kai, sannan ya juya kallansa tai taga yanda yanayinsa ya canza, jiki a sanyaye ta kalleshi dan yaki sanar da ita abinda yake faruwa da Hajiya ita kuma batasan tambayarsa, shikam a ganinsa shi kadai ya dace yaji wannan abin.

********

Sanye take cikin riga da skirt na lace maroon color, tayi kyau sosai, Iman ce dake koyan kwalliya ta fente mata fuskarta, ta fito das da ita, sai murmushi takeyi ita kadai. Kekenta ta gunguro har zuwa falo ta tsaidashi a inda ta saba, wayarta ta ciro a gefen wani aljihu dake jikin keken ta fara daukar selfie, tana juyar da wayar zuwa wajan kofa sai kawai ta ganshi ya daga labule. Cikin tsananin zumudi ta juya gabaki daya, suka tsaya kallan juna kowa da abinda yake sakawa a ransa.
Umma ta fito daga kitchen dauke da robar alayahu xata yanka a falo tagansu, Umar yai kasa da kai jiki a sanyaye. Ganin haka yasa Umma tayi saurin karasawa inda Bilkisu take. Gungura keken tayi zuwa hanyar daki ranta fuskarta a hade. Bilkisu kuma hankali ya tashi, ganin Umar a yanzu ba karamin taso mata da miken daya fara warkewa yai mata ba.
Suna shiga daki ta rufe kofa tare da kallanta tace "Ina so idan kinga Umar ki dinga kama kanki Bilkisu, saboda har zuwa yanzu hankalinsa yana wajan yar uwarki. Ke ko zuciya baki da ita? Daga dawowarshi yau kike neman bada kanki?"
Umma na kaiwa nan ta fice zuwa falon tana faman hade rai.
"Umma barka da rana." Umar ya fada yana sosa kumatu. Taki tanka masa bare yasa ran magana mai dadi, zama tai ta jawo robarta ta fara yankan alayahunta.
Ganin batada niyyar kulashi yasa ya tsuguna yana gaisheta, nan ma ba amsa, ya daure yace "Umma! Abba baya nan ne?" Yaji ta kuma yin shiru sai aikin ta kawai takeyi.
"Dan Allah Umma ki kulani." Kamar ya tunzura ta nan ta juyo tana masa kallan wulakanci tana cewa.
"Umar ka matsa min da tambaya fa, idan na goya Abban ai zaka ganshi a bayana ko? Ni abinda ya bata min rai ma shine mekadawo yi gidan nan? Bakace sai Ibtisam ta kaso auranta ta dawo ba sannan hankalinka zai kwanta? Bari kaji in gaya maka wani abu, IBTISAM tana gidan mijinta, sakamakon biyayya da tayi na karbar zabin da aka yi mata yanzu haka babu wanda Aminu yake matukar so da kauna sama da ita. Kai kuma an baka ka raina ko? Toh ba zaka bar gidan nan ba sai da takardar sakin Bilkisu a hannuna."
Umar ya kalli Umma cikin wani irin yanayi, har zai ce su kwada Bilkisu su cinye, sai kuma ya tuna kauye da sauri ya durkusa kasa kamar zai mata kuka yana magiya.
"Umma dan girman Allah karku rabu mu, nifa na hakura zan zauna da Bilkisu har mutuwa wallahi. Naso Ibtisam amma yanzu da Bilkisu zan zauna."
Hannu ta daga mai tace "Kaga Umar bana san shirme da shiririta kaji ko? Idan har dan zama ne ai ba guri Bilkisu ta rasa ba a gurinmu."
"Umma ina nufi ina san Bilkisu."
"Karya ne, nasanka sarai Umar. Ko ka manta rashin albarkar daka dinga gabza mana saboda kana ganin mun rabaka da rabin ranka?"
"Wallahi da gaske nake Umma, dan girman Allah ku sake bani dama na kasance tare da Bilkisu." Umma ta yatsina fuska tace.
"Zanyi shawara tukunna." Tana kaiwa nan ta shige daki tabarshi a inda yake. Umar ya cije lebensa ya tashi ya fita dan jiran Abba ya dawo ya karbi mukullin bangaransa. Wai akan wacen nakashashiyar ake wani juyashi? Tsaki yai ya zauna akan benci yana tunanin yanda yasha love dinsa da Ibtisam, lalai duniya ta juyamai baya dole ne ya lalaba Bilkisu.
  Koda Abba ya dawo da daddare yaga Umar ba karamin mamaki yai ba, amman saboda yasan haukansa yasa Abban kin kula yasan da zamansa a bakin gate din. Abba na fitowa Umar ya zube a kasa yana rokansa akan ya yafe masa, sannan yayi hakuri ya bashi Bilkisu su koma bangaransu. Abba yaki kulashi ya shige gida Umar yabi bayansa.
"Wai Umar bakace sai IBTISAM ta baro gidan auranta ba? Ka zauna har randa zata fito din, amman ba zan baka Bilkisu ba dan bansan mekaje kauye ka kullo mata ba. Wulakancin daka mata da yanzu bazan bari a mata kwatan kwacinsa ba.
"Haba Abba." Cewar Umar yana turo baki.
"Nayi karya ne?"
"Abba meka maidani?"
"Oho maka."
Tashi Umar yai kawai sukaga ya wuce zuwa dakin Bilkisu, babu wanda yabi ta kanshi ganin fitina yakeji da ita yau din. Zaune ya sameta tana ninke kaya, tunda ta kalleshi sau daya bata kuma ba duk da cewa ba haka zuciyarta taso ba. Shima Umar karewa dakin kallo yai wanda ke faman kamshi. Nashi dake kauye ya tuno banda warin akuyoyi da kaji babu abinda yake yi.
Zama yai a bakin gado kawai ya baza wani uban tagumi, kallan Bilkisu yai kamar mai shirin kuka yace "So kike ni dake mu zama zawarawa?"
Bakinta tadan motsa tanasan magana sai dai tasan tana farawa zata kwafsa, yadan ja hanci yace "Naji na miki laifi amma ai ke mai fahimtace, kinfi kowa sanin ba halina bane, abinda ya faru ne yazomin cikin ba zata koni abinda na miki baimin dadi ba....."
Yadan rike hanci kamar mai neman yin kuka, jikinta ne yai sanyi, ta kuramai ido tana tunanin abinyi, jitai ya jawo kekenta ya rungumeta wai shi a dole kuka yake, rikicewa tai tace "Na hakura Ya Umar dan Allah karkai kuka....."
Ya dade sosai a dakin shida Bilkisu, abinka da miji da mata akace sai Allah Abba da Umma sukaga Umar yana gunguro Bilkisu, babu wanda yai magana har suka karaso falon, Umar yace.
"Abba mukullin." Wani kallo Abba yamai, Bilkisu tace "Abba dan Allah."
Babu musu ya dakko keyholder dinsa ya ciro ya mika masa yana mai wani kallon tuhuma.
"Zamu tafi bangarenmu tare da matata." Umar ya fada kai tsaye. Suka hada ido da Umma ganin batace komai ba yasa Abba yi masa sallama da hannu. So hana ganin laifi, kiri-kiri soyayya ta rufewa Bilkisu ido ta yadda bata ganin komai sai Umar koda kuwa zai kaita wuta.

*********

Hajiya kam jiki yayi tsanani, anata yi mata magani amman da ta farajin sauki sai wani ciwon ya bullo. Hajiya duk lokacin da take cikin sauki bata da zance sai na tambayar likita yaushe Aminu zai zo? Likitan ya sanar da ita cewa shima baisani ba. Shi kuwa Aminu yau tsab ya shirya tana dawowa daga makaranta yace da ibty ma ta shirya zasuje unguwa.
Murna ta cikata dan tasan gida zai kaita, bayan ta fito daga wanka tsayawa tayi gaban wardrobe yatsanta a cikin bakinta sai ciza takeyi, tunanin kayan da ya dace tasa takeyi, amman duk wanda ta kalla sai taji be dace da yau din ba. Tafi minti biyar kafin idanunta ya tsaya kan wata doguwar riga ta atamfa golding brown an jera stones sosai a jiki, Ibty ta janyo ahankali ta warware tasa.
Murmushi tasaki ganin tayi kyau sannan ta daura dankwalin tabi jikinta da turaruka. Tana cikin saka lipstick da wayarta cikin handbag Aminu ya shigo, ta dago tana kallansa sukai ido hudu. Wani irin yanayi Aminu ya samu kanshi, zuciyar shi ta shiga cikin wani irin shauki. Yana mamakin yadda a hankali yar yarinyar nan take sake mallakar duk wani sashe dake jikinsa, yana mamakin yadda karamar yarinya kamar ibty take neman sarrafa duk wani tunani da yake dashi.
"Ka gama na fito ne?" Aminu ya kasa magana sai matsawa da yai gab da ita, ta kawar da kai saboda yadda kirjinta yake bugawa.
Hannunsa yasa a kan kugunta hakan yasata dan sakin wata karamar ajiyar zuciya.
"Wai kin dauka lunch zamuje wani gurin?" Ya fada yana dan matso da ita kusa dashi. Ibty ta zaro ido.
"Ina zamuje to? Nazata gida zaka kaini mu gaisa dasu Umma?" Aminu ya bude ido.
"Gida kuma? Ba gida zamu ba unguwa zaki rakani."
"Daga unguwar fa sai ina?" Tayi maganar tana shagwabe fuska. Murmushi yayi tare da sumbatar saman lebenta yace.
"Sai mu dawo nan gidan."
"Kai Yaya."
"Dagaske nake miki." Ya saketa yana juyawa.
"Idan kin gama ki taho ina mota."
Ibty ta bubbuga kafa a kasa irin na yan yara, yana jin ta amma yaki waigawa sai dariya da yake yi har ya bar dakin. Mayafinta ta dauka tasa takalmi tabi bayansa. Tunda ya hangota tana tahowa ya kasa dauke ido daga kanta har sai da ta iso wajan, yasa hannu ya bude mata kofar ta shiga ta rufe sannan yaja suka fice. Sai da suka dauki hanya sosai yaga bata kallansa sannan yai murmushi dan abin nata dariya yake bashi yace
"Baby Wai duk fushin na menene?"
"Ni ba fushi nayi ba." Ya dan kalleta.
"Kikai shiru kuma?"
"Me zance to?"
"Labari zaki bani."
"Kai Yaya ni fa banda labari." Ibty ta fada tana sake turo baki.
"Yaya? Wa kenan?"
Baki ta sake turowa batace komai ba.
"Ahhh sai yanzu na tuna ashe dazu abu biyu nazo fada miki kika sa na manta."
Dan kallansa tai kadan, ya dan gyara zaman glass dinsa yace "Tunda fishi ake dani banaji akwai anfanin fadar."
Kamar bazatai magana ba sai kuma tace "Ni fa ba fishi nake ba."
Murmushi yai kadan yace "to me?"
"Habibty...."
Tai maganar cikin wata murya wacce tasashi kunshe dariyarsa.
Aminu yaci gaba da tuki jefi jefi ya kan kalleta a haka har suka karasa asibiti. Ya samu guri ya ajiye motar suka kalli juna yayi murmushi, itakam kallan asibitin take tana tunani waye ba lafiya?
"Fito muje." Babu musu ta fito ya rufe suka jera. Tun daga bakin dakin din suke jiyo ihun Hajiya, hakan yasa Aminu saurin murda kofar yaga nurses suna ta kokarin riketa gashi tayi kaca-kaca da gurin da kashi da fitsari. Su kansu a dole suke ajiye da ita a asibitin kowa ya tsani zamanta, gashi da alama kudi ake bawa mai asibitin shiyasa shi ko haushin abin basuga yanaji ba.
  Ibty jikinta ne ya fara rawa ganin Hajiya a cikin wannan yanayin, babban abinda yazo mata shine meke faruwa? Menene yake damunta? Wannan wane irin ciwo ne yasa duk ta fige ta lalace? Kallo daya zaka mata kasan lalai tana cikin tashin hankali mara misaltuwa.
Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, cikin sauri Aminu yace da ita ta koma waje. Hankali a tashe ta fita, jikinta na wani irin rawa, tsugunawa tai a jikin bango tana addu'a dan gaba daya kwakwarata ta kasa fahimtar abinda ta gani.

Wayarta ce tai kara hakan yasa ta zarota, nunber Ainah ce hakan yasa tazaro wayar ta daga gaba dwya jikinta rawa yake "Ibty wato miji dadi ko? Shiyasa kika gudu kika barni a skul ko?"
Shiru Ibty tai dan batama san me zata ce mata ba, Ummy dake zaune kusa da ita ta dan bige kafadarta tace "Auntyn taki kikewa magana haka? Sannan ba Aunty sai wani Ibty gatsai?"
Baki ta turo tace "Kawatace fa akan me...."
Ummy ce ta amshi wayar tasa a kunnenta tace "Ibtisam."
Dakyar ta daure tace "Ummy!"
Jin muryarta yasa tace "Lafiya?"
Bakinta na rawa tace "Hajiya ba lafiya, ciwon ba dadi......"
Hankalin Ummy ne yadan tashi tace "kuna ina?"

Babu bata lokaci kuwa sai ga Ummy da Aina, mamaki ya kama Aminu ya kalli Ibty wacce ke gefe tare da Ainah wacce ta rike hannunta ganin yanda yanayinta duk ya canza.
Hankalin Ummy ya tashi itama ganin halin da take ciki "Fadamin meke damunta haka?" Yayi shiru yana neman abin cewa.
"Da alama karya kake son yi min ko?"
"A'a Ummy."
"Kai nake sauraro, kar kuma kayi min karya kasan dai matsayina a wajanka. Sannan nan asibiti ne zan iya neman likitan ya sanar dani."
Aminu ya dafe kai shi gaskiya besan asan abinda yake damun Hajiya, gashi yanzu sunce masa har tana dauke da cutar nan mai karya garkuwar jiki wato HIV  ga kuma ciwon koda wanda da alama shi kuma girma ne ya jawo mata shi. Kai ya sunkuyar kasa yana tunanin abin cewa.
Cikin dan daga murya tace "jiranka nake ko?"
Badan yaso ba haka ya bawa Ummy labarin abinda ya faru da Hajiya. Ba karamin tashin hankali ita kanta ta shiga ba, tasan matar shaidaniya ce amma batasan shaidancinta yakai haka ba.
Inalilahi wa ina ilaihi raji'un abinda Ummy ta fada kenan sannan ta kalli Aminu cikin fada ta fara magana.
"Wai a ina ka hadu da Na'ima ne har ka jajibowa kanka wannan masifaffiyar matar? Wannan wace irin jaraba ce? Tunda nake a rayuwata ban taba cin karo da bala'i irin na mutanen nan ba."
Ta sauke wani huce tacigaba "Duk saboda su mallake min kai shine har takai kanta wajan sabawa ubangiji? Zanji matukar kunya a nuna wannan matar a ce surukatace, gashi harda zuri 'a a tsakanin mu da ita."
Ta kalli Hajiya dake runkufe akan gado an mata allurar bacci tace "Ka bude kunnanka da kyau kaji ni, duk yadda za'ai sai matar nan ta koma kauyensu, taje can su samar mata lafiya."
"Amman Ummy k..." Da sauri ta dakatar dashi.
"Umarni ne ba shawara ba, kayi yadda nace maka, ban hana ka bada abinda za'a kula da ita ba, amman dai bana bukatar ka sake kusantar inda take indai ba da sani na ba."
Ummy na kaiwa nan ta juya ta kalli Aina tace "wuce mu tafi, zuciyata bazata dauki ganin wannan matar ba."
Suna fita Ibty ta karasa wajan Aminu wanda yake dafe da goshi ya rasa ma abinda zai yi.
"Yaya!"
Kallanta yai cikin dan bacin rai yace "Meyasa zaki kira min Ummy? Tunda kikaga ban kawo ta ba ai nasan abinda nakeyi." Yai maganar ba tare da ya kalleta ba.
Ita kanta batasan mai ya kaita fadawa Ummyn ba, cikin dana sani da sanyin jiki tace "Kayi hakuri."
Yayi shiru kafin ya dago su hada ido, Ibty tai saurin maida nata gefe saboda kwarjinin da yai mata.
Sake waigowa tai ta sake kallensa yanzun ma kallanta yai, a hankali ta daura hannu ta dan rike kunnenta alamar tayi laifi, idanunta sukai jaa tana neman yin kuka, kai ya girgiza mata da sauri alamar kartamai kuka, ta kallo Hajiya wacce tausayinta duk ya rufeta, kara kallansa tai ta dan rike rigarsa, dan murmushi ya mata hakan yasa hankalinta ya kwanta.

Tana kusa da Hajiya aka turo kofa, Ummy ce ta kuma dawowa wannan karan da wasu maza suna bin bayanta, ta kalli Aminu.
"Ga bus nan na taro shata, kaje ka karbo sallama yau ba sai gobe ba matar nan zata koma kauye."
Mamaki ya rufe Aminu yace " Amma Ummy......"
Ummy tai saurin katse shi tare da dagamai hannu
"Karka sake ka rokeni, wallahi matar nan sai ta koma kauye kaji na rantse. Sanda take yawon badalarta ta tuna dakai? Ta tuna da darajar jikokinta?"
Ido yadan runtse "Tun kafin asan me ta aikata ayiwa 'ya'yanka lamba matarnan zata koma inda ta fito."

Babu yadda zai yi dole yabi umarninta yaje ya karbo takardar sallama, ma'aikatan gun sai dadi sukeji dan damw sun gaji da ita. Nan aka janyo Hajiya har mota aka sanya ta Ummy ta bawa masu bus din kudinsu sannan Aminu ya kwatanta musu garin da unguwar da zasu kai Hajiya.
Sai da Ummy ta gama tabbatar da cewa sun tafi sannan ta tasa keyar su Aminu suka tafi. Ibty kam gabaki daya ta dinga baya-baya da Aminu dan tasan tabbas haushinta yakeji, da ya sauko amma abinda Ummy tai ta tabbatar ya kara hawa.
Suna isa gida yai hanyar daki fuskarsa a daure, dan tunda suka shiga mota ba wanda yai magana, da sauri ta karasa da gudu ta rike rigarsa ta baya, bai waigo ba yace "Dan sakeni toilet zan shiga."
Jikinta a sanyaye ta sakeshi tana kallo ya wuce, tabi bayansa da kallo.....

******
A can kauye kuwa ana kai Hajiya gidan sukace fir bazasu amsheta ba, wai mayya ce da alama kuruwar wani taci aka kamata, sukam masu bus suka ajiyeta a waje sukai tafiyarsu.
Kan kace me? An cika taf a kofar gidan ana kallanta, Kawu wato yayanta ne ya dawo daga gona cikin sauri saboda wayar da Aminu yamai sannan ya turo kudi masu yawa akan a kula da ita.
Nan ya shiga da ita ciki a ka gyara kata dakin awakai aka sakata a ciki, gaba daya bata gane kanta sai ihu kawai take tana cewa "Amaidata gun Aminu...."

  Yau Kwana hudu kenan da maida Hajiya kauye aka turo musu sakon cewa jikin nata ya matsa kuma babu sunan da take ambata irin na Aminu. Da kyar Ummy ta barshi suka tafi shi,Ibty,Aina dasu Islam.
Koda suka isa Hajiya suka tarar cikin wani daki dako kare basu tsammanin zai iya zama a cikinsa, tana ganin Aminu tayi murmushi mai zafi.
Dazun nan jikinta yai dan sauki tadan sa a taimaka mata ta gyara jikinta jinsu Aminu na hanya, bayan sun gaisa ne ya kalleta yace  "Hajiya ya naga bakya shan magungunan?" Ganin da yai musu a ajiye da alama tunda ta dawo kauyen bata sha su ba.
"Babu komai Aminu, bana iya sha." Islam ce tace"Sannu Hajiya."
Ilham ta matso gunta tace "Hajiya in kika warke da kaina zan kawo miki chocolate dayawa dayawa/"
Hajiya ta kalleta tare da yin murmushi, kallan Ibtisam tai kamar zatace wani abu sai kuma tayi shiru.
"Kuje waje ina zuwa." Suka hada ido da ibty ya jijiga mata kai, babu yadda zatai dole ta fita ta basu waje.
"Aminu."
"Na'am Hajiya." Suka yi shiru na dan lokaci.
"San zuciya ya kawoni wannan yanayin da nake ciki, kayi min komai amman na kasa hakura gashi inda na kai kaine. Aminu ka yafewa Na'ima dake kwance a cikin kabari. Allah ne kadai yasan azabar datake sha a dalilin abinda ta aikata. Nima ka yafe min dan Allah."
Aminu yai shiru yana sauraranta harta gama, ya sauke numfashi.
"Allah ya yafe mana baki daya. Amman ya kamata ki dinga shan maganin saboda wahalar ciwo ake gudu bawai mutuwa ba."
Hajiya tayi shiru ita kadai tasan halin da take shiga idan tana shan magungunan, shi yasa kwatakwata ta dena shansu.

Ayusher 🏌🏻‍♀�?
5/9/22, 20:54 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀�?

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

*47*

Dakin yadanyi shiru kafin Hajiya cikin sheshekar kuka tace “Duk abinda ta aikata nice sila, tun tana karama nake hure mata kunne nake nuna mata ‘ya’yan kishiyoyina ba ‘yan uwanta bane, kudi sunw gatanta da darajarta. A haka aurena ya rabu da mai gidana saboda ya gaji da mugayen halayena, da sharrin da nake yiwa kishiyoyina ina hadasu husuma.�?
Aminu ya kalleta sosai yace “Ni kuma mai na muku? Mai na muku daga ke har ‘yarki kuka tarwatsa min rayuwa?�?
Hajiya ta girgiza kai da sauri tace “San zuciya ne kawai irin namu amma ba abinda ka mana, ahasalima bamu sanka ba mu muka bincikoka da kanmu.�?
Kallanta yai mai tattare da alamar tambaya, ta share kwallarta tace “Mahaifinka ne yake san ‘yar kishiyata Zainab da aure, Na’imah tunda taga kudin mahaifinka ta rikice, balle ita duk samarin dake santa babu mai ko mashin, ita kuwa gashi mai jibgegiyar mota yazo yana santa. Nan ta bazama neman samari masu kudi sai dai kowa yai amfani da ita sai yace bazai turo ba.�?
Kan Aminu ne yai wani ginginrin jin wannan kalmar, ko kallan Hajiyar ya kasa saboda nauyin da zuciyarsa tai, Hajiya tai kasa dakai tace “Allah ne kadai yasan yanda akai ta shiga gun malami taje ne akan a juyo da hankalin mahaifinka kanta, ya bata umarni ta kawo hotonsa ta kuma yi bincike a kansa, anan ne tasan yanada babba ‘ya wanda ya isa aure, bata sanka ba saboda baka kasar, nan malamin yai maka asiri wanda ya karkato da hankalinka ka dawo Nigeria.�?
Gaba daya kallan Hajiya yake yanzu yana mamakin wai matar dayai shekara uku da ita ashe duk zaman karya tai dashi?
“Tundaga lokacin take ma asiri harka mato akanta wanda babu wanda kake gani sai ita, a haka kuma tasa ka daukoni nan muka kara shiga dan rufe bakin ka dana mutane…�?.�?
Hannu ya daga mata da sauri yace “Ya isheni haka, to daga ke har Na’iman ribar mai kuka ci? Ita ta rasu ba tare da ta moreni ba yanda ta shirya ke kuma kalli yanda Allah yai dake.�?
Kuka ta fashe dashi sosai, nan danan tari ya riketa, Aminu ya kalleta cikin takaici yace “Ni duk abinda kukamin na yafe muku sai ku shirye gamuwarku da wanda ya haliceku, ‘ya’yana bazasuzo nan garin da sunan ganinki ko wani naki ba, wannan shine hukuncin dazan muku daga ke har ‘yarki. Basu da dangin uwa daga yau na musu iyaka daku.�?
Yana kaiwa nan ya mike ya fito daga dakin wanda ba abinda ke tashi sai warin kashi na dabobi da kuma warin tusar Hajiya.
Hajiya kuka take sosai tana rokar yafiya tana kiran Aminu, daga baya ta koma kiran Ibtisam sai dai Aminu kallo daya ya mata tasan bai amince ta shiga ba.
Kafin su tafi Aminu ya bawa wata mata kudi yace ta dinga kula da Hajiya, daga haka suka tafi.
Kwanan su biyu da zuwa kauyen suka sake samun mummunan labari na rasuwar Hajiya, tun dare ta mutu dayake tana xaune ne a bangare guda basuma san ta cika ba, sai da safe anzo kawo mata dumame akaga ta mutu.
Babu wanda yaje gaisuwa daga Kano sai Aminu, gaba daya gidan kamar ba gidan mutuwa ba, mutane ana zaune anata hira da shewa, ana sanar dasu labarin zuwan Aminu kowa yai kasa dakai wasu harda dauko carbi, ya shigo ya ajiye musu kudi bayan kayan abinci da aka shigo dashi, yana zuwa ya dawo ko minti talatin baiyi ba ya juyo.
Abin mamaki tunda Hajiya ta rasu sai yaji tamkar an cire masa kaya a cikin zuciyar shi, kamar yau aka haife shi haka yakejinsa cikin walwala da nishadi, dama yana tsoran yadda zai yi rayuwa bayan Hajiya na da manyan tabbuna a jikinta, duk da yaji mutuwarta sai dai ga yaransa yan mata da in har mutane suka san sirrin kakarsu aure zai yi musu wahala.

(Allah yasa mu cika da imani ka kuma mana kyakyawan karshe)
****
Yana shiga karin kano ya wuce ta wani mall, bangaren kayan mata ya nufa, english wears yadan dauka gaba daya kamar wanda ke sata haka yakeyi saboda kunyar kar aganshi da girmansa yana daukan kaya irin wannan, wata rigar bacci ya gani irin mai net din nan shara-shara, ta gefe ya dinga kallan rigar yana tunanin yanda zata zauna a jikin Ibtisam, gefe da gefe ya kalla ganin ba mai kallansa yasa yadan zaro rigar ya dukunkune yasakata a kasan cart din ya rurufeta da wasu kaya, shi a dole baisan a gani.
Gun mai biyan kudi ya nufa, gaba daya kunya ce ta rufeshi, da aka daga rigar, wayarsa kawai ya dauka ya kira kaninsa dake kasar waje suka fara waya, kallan mai biyan kudin yai yace “Eh duk na sai maka abinda kake bukata.�?
Cikin mamaki kanin nasa yace “Me nake bukata?�?
Bai tankashi ba ya kalli mai biyan kudin yana murmushi ya kashe wayar yace “Haka nan suke, sune yara amma ba dama suji zaka shiga siyayya sai su fara cewa sunasan kaza da kaza.�?
Shidai dariya kawai yai dan baisan me zaice ba, haka Aminu ya fito ya shige mota yana hawa kan titi kawai ya girgiza kai tare da sa dariya, lalai Aminu yaushe ka zama haka?
(Ni kaina abinda nake san sani kenan🤪)

******
Da wani irin farin ciki Aminu ya shiga gidan, hannunsa dauke da kayan shopping din da yai, yau bayan tayi wanka ta saka wani lace dinta da aka mata dinkin buba, ya mata kyau sosai, tayi dan makeup kadan sannan ta daura dankwallinta nan fa ta kara fitowa fes, dama kwanakin nan wani kyau da fresh take karawa, ba shakka kana ganinta zakasan hankalinta a kwance yake, dan a skul ma kawayenta tsokanarta sukeyi Ainah sai tai dariya tace “Yayana ne da alama ya iya kiwo.
Tana zaune a falo tana juyawa su Islam taliya wacce tai fara da vegetable soup yasha kayan ciki sai kamshi hake, nan sukaji sallamarsa. Atare duk suka waiga ganinsa yasa Islam da Ilham rugawa da gudu suka rungume shi, yana murmushi yana kallansu, ya kasa shafa kansu saboda kayan da ya riko. Ibty ta karaso ta karbi na hannu daya, tana neman zame hannunta taji ya rike hannun, cikin kunya tamai alamar su Ilham da ido, saketa yai tare da shafar saman kan su.
"Inyeee me za'aci haka.?"
"Taliya." Ilham ta fada tana dariya.
"Uhmmm da alama kuna so ko?"
"Mune mukace a dafa mana, Dady daga yanzu wannan shine best abinci na.�? Ilham ta fada tana dariya.
Ya kalli Ibty yace “Da alama Mumy ta iya abinci ko?�?
Kallan sa sukai sannan suka kalli Ibtisam da sauri.
Mumy? Suka tambaya
Ya kalli Ibtisam yace “Bakwa santa a matsayin Mumy dinku?�?
Kallan juna sukai, yace “shikenan bari ta koma gidansu inyaso ku sai ku cigaba da zama daga ku sai ni.�?
Kai suka girgiza da sauri suka karaso suka rungume Ibty, Islam tace “A’a dan Allah Dady.�?
Yace “Gashinan ku zaba in ba Mumy bace ta bar muku gidan.�?
Ilham ta kara kankameta tace “Mumy!�?
Idanun Ibty ne suka danyi raurau ta sunkuyo ta rungumesu a jikinta tace “Ilham!�?
Itama Islam ta dago tace “Mumy!�?
Kam ta rikesu a jikinta bata fargaba sai kwalla taji, Aminu ya kallesu cike da sha’a.
Mikewa tai suka kalli juna sosai kowanne da abinda yake ransa.
"Sannu." Cewar Ibty tana kallansa cikin wani yanayi.
"Maza kuje kucigaba dacin abincinku, bari na kai kayan nan kitchen." Ibty ta sake daukar ledar kan table tayi kitchen, shi kuma ya nufi dakinsa da dayar ledar, ganin haka yasa batace zata karba ba tasan kayan bana kitchen bane. Sai da ta gama ware komai tasa a inda ya dace kafin ta dakko wanda zata bawa yaran ta aje gefensu sannan ta nufi dakin Aminu.
Bata ganshi ba sai dai taji alamun zubar ruwa a cikin toilet, ta dinga baza idanu ko zataga inda ya ajiye ledar amman babu, ta daga kafadu ta fice da nufin ta dawo bayan yan mintuna.
Aminu yana fitowa jallabiya ya janyo maroon yasa, sannan ya hau kan sallaya yagabar da sallar la'asar, yana addu’a yaji sallamarta yana kallanta ta sake shigowa ta zauna a bakin gado tana jiransa har ya shafa sannan ya juyo ya kalleta.
"Ban rokar miki kishiya ba dan naga kinki shafa addu'ar da nai." Zaro ido tai tace “Ni cewa nayi ka roki kishiya? Kuma ko ita ka roka ai bana tsoranta tazo mana." Aminu ya tashi daga kan sallayar ya karasa inda take ya zauna gefenta.
"Ina da budurwoyi fa karki cika baki naje na zabo daya." Nan da nan ta hade rai ta kauda kanta gefe, hannunsa ya shiga irgawa kafin yace “Acikinsu na tambatar kowace nawa magana…�?
Yanda ta sake kallansa fuskarta kamar wacce aka turowa sakon mutuwa ne yasa shi yai murmushi yana kamo mata hannu tare da lankwasa yatsun ta, tadan daure dan batasan magana, jin zafin yana ratsata yasa ta fara yar kara.
"Ashh! Ahhh!! Washhh...!!!" Hannu yasa ya janyota jikinsa yana cewa.
"Kina ihu sai yaranki sunji? Kuma idan suka ganki anan ai ni zasu zarga, ko suce na bugar musu Mumynsu.�?
"Gaya musu kuma zanyi ba." Ibty ta fada cikin shagwaba tare da yar harara.
"Kice musu mene?"
"Zance zaneni kayi mana, ince ma da bulala…�?
Ido ya zaro yana kallanta, nan ta juyar da kai tana dariya a hankali.
"Shikenan tunda sharri zaki min, yanzu anyi abincin dani ko kuwa naje naci a waje? Dan naga yau fitina akeji.�?
Juyowa tai tare da turo baki tace. "Salan kaja min zagi, ace kana da mata amman kana fita waje cin abinci?"
"To ai gani nayi baki min tayi ba, shi yasa na kama kafa biyu nace in babu na fita waje."
"Taya zanyi abinci bakai?�? Cewar Ibty cike da jin haushi.
"A falo za’a bani? Konan zaki zo ki ban?" Kasa cewa komai tai sai tashi da take kokarin yi, hannunsa ne a sakale a kugunta, tadan sake yunkurawa nan ma ta kasa kwacewa. Ganin yanda take fizgewa yasa shi sakinta ta fita shi kuma ya dafe goshi. Kodai be iya soyayya bane? Shin menene ya fada na rashin jin dadi a maganarsa? Sai ya tuna Na'ima itama haka take fushi idan yace zaije gidan Ummy yaci abinci bayan kuma yasan tana dashi a gurinta, amma shi ai zolayarta yake.
Tashi yai tsaye ya cire jallabiyar yabar singlet da three quater a jikinsa, gefen gado ya zauna bayan ya dakko laptop ya kunna. Ibty ta shigo rike da tary kallo daya tai masa ta dauke kai sakamakon yadda taji zuciyarta ta harba, wani irin yanayi na bazata yai mata. Sosai ta lura da cewa tsarin halitar Aminu kadai kan iya sanya mace fadawa tarkonsa musamman irinta da take da feeling akanshi.

Fuskarta a tsuke tace “Yaya ga abincin nan." ya kalleta shima sai ya tsuke fuska yace.
"Nan zanzo naci ko kawo min kusa dani zaki yi?" tayi shiru kamar mai nazari, sai kuma ta dauka ta karasa kusa dashi ta ajiye “Yaya�?..."Ta kira sunanshi tana dauke hannunta daga kan tire din, yana ji yai mata banza saboda yaga alamar zata fara rainashi, haka kawai daga dan zolaya sai wani hade rai take? So take hala yai ta lalabata tana wulakantashi.
"Yaya." Ta sake kiranshi, Aminu ya dago daradaran idanunsa ya zuba mata su, tai saurin dauke nata ta maidasu kan gado.
"Wai ni me nai maka kake fushi dani?�? Mamaki ya kamashi, lallai yarinyar nan ta mugun raina masa wayo, har ta manta ita ta fara yin fushi ya gani.
"Yaya nidai to ka ajiye aikin kaci sai ka karasa idan ka gama."
Ya rufe laptop din ya tsaya yana kallanta. Matsawa tayi sosai ta zuba a plate sannan ta fara bashi a baki, yana ci yana kare mata kallo, ita dai tunda ta fuskanci idanunsa yana kanta sai taki bari su hada ido har yazo spoon din karshe sannan ya rike hannun ya juyar dashi saitin bakinta yace.
"Cinye shi." Da yake sulhu take so sai batai gaddama ba ta bude bakin yasa mata.
Cikin dan shagwaba tace “Ka huce?�?
“Shiru yai kamar mai nazari sannan ya nuna kansa sannan ya nunata yace “Nine nake fishi ko kece kike fishi?�?
Tadan rufe ido sannan ta bude idonta daya ganin yana kallanta yasa tace “To ai kaine wai zakaje kaci a waje.�?
“Kinga dai kece mai fishin bani bako?�?
“To ai na sauko.�?
“Aka ce min Yaya?�?
Labanta ta rufe a tare tace “Sry Habiby Allah mantawa nake saboda su Islam, ni dai dan Allah kabarninnace ma Yaya.�?
Kuncinsa ya nuna fuskarsa a daure ajiyar zuciya tadanyi sannan ta sumbaci kuncin nasa, tana kokarin zama ya nuna mata daya kuncin, sake dawowa tai ta sumbata, zata sake zama ya nuna kan lebansa, kamar zatai kuka ta sumbata, gani yai ta tsaya bata xauna ba, ya kunshe dariyarsa ya dau glass dinsa ya saka yana neman shan ruwa.
“Aikin soja kika koma?�?
Ta xauna tace “Wai shi wannan punishment din sai nazo zan zauna ake yinsa?�?
Ajiyar zuciya yai yadan kalli glass din hannunsa yace “Dazu kin kusa karyamin hannu gaba daya banajin hannun nan na aiki.�?
Tasan ruwa hannunsa yakeso ta amsa, amsa tai sannan tace “Yaushe na taba maka hannu amma?�?
Kin manta sanda kika sani lankwasa miki yatsu?�?
Dariya ta kwashe dashi tace “Kenan ai hannuna ne zaiyi ciwo ko?�?
Kai ya girgiza yace “Nawa dai da nai aikin.�?
Tana kallansa tace �? Kaifa kai bani na saka ba?�?
“Still dai�?.�?
Yaya kenan, shi gaba daya zamansa zolaya ne, shiyasa yanzu gaba daya ya gama shiga zuciyarta sam intana tare dashi bata tunanin komai…�?

*Ayusher ce*🏌️‍♀�?
5/12/22, 14:23 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀�?

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

*48*

Ajiyar zuciya tai ganin yadan mike tsaye, ina zaka?
Yadan dau glass dinsa dake gefenta yace “Gida zanje, amma bazan dade ba.�?
“Muma zamuje dan Allah!�?
Kallanta yai yadauko riga yana sawa yace “Yawo ko?" Ibty ta sunkuyar da ido.
"A'a ba yawo bane ba rakiya zamuyi please." Aminu ya juyo tare da sa hannu yadan dagota, samun kanshi yai da rungumeta, yau jinsa yake tamkar wani sabon ango, ga wata muguwar sha'awa da take bijiro masa tamkar be taba kusantar mace ba.
"Ku shirya amman ba gidan Ummy ba." Kallansa tai tare da lumshe ido.
"Jeki shirya su Islam kema kisa hijabi." Ya saketa ita kuma ta fito tana hadawa da gudu dan tasan idanunsa yana kanta.
"Kids maza kuzo na shirya ku." ta fada tana tattare gun da suka ci abinci.
"Aunty Ina zamu?�? Ilham ta tambaya cikin zumudi.
Kallan Ilham tai tare da dan yin wani iri da fuskarta, dariya tasa tace “Mumy ina zamu?�?
Cikin jin dadi tace “Idanunku zasu gane muku, oya ku tashi muje daki, kafin ace an fasa zuwa damu.�?
Da gudu suka tashi da sauri tabi bayansu. Kaya ta zabo musu iri daya riga da skirt masu kyau, ta saka musu ta gyara musu fuska kowacce ta dauki handbag din ta sannan tace su jira itama taje ta shirya. Doguwar riga tasa purple ta zauna a jikinta das sai tai wani irin kyau na musamman. Mayafin rigar tasa akanta ta yafa sannan ta janyo farar jaka tasa abubuwanta, ta dakko sneekars tasa tayi kyau sosai.
Tunda ta fito Aminu yake kallanta, shi kansa yasa yanzu ne yai aure ya matsa kusa da ita yana jin kamar ya sakata a cikinsa.
"Watabarakallahu ahasanil kalik." Aminu ya fada, Ibty ta kalleshi.
"Yaya! Magana kayi?" Hancinta yaja tare da girgiza kai.
"Nace duk wannan kwalliyar fitar ce?�?
Tadan yi raurau tace “Ace nayi kyau ne ba’a san fada?�?
Hannayensa biyu yasa a aljihu yace “Muje ko?"
Su Ilham ta kira suka fito tare, baya ta bude suka shiga ita kuma ta koma gaba, Aminu ya shiga yaja mota suka wuce.
Gani tayi sun dauki hanyar gidan su, tai saurin kallan Aminu cike da farin ciki ta dafa cinyarsa.
"Gida?�?
Kai ya rangwafar yana tukinsa, dadi ya kara rufeta tace “Wayyo dadi yau zanga Umma."
"Is for you."
Kunya tadan kamata tace “Nagode�?
Tadan rage magana cikin alamar rada tace “Habiby.�?
Sun isa gidan yai parking farinciki ya kasa boyewa a fuskarta.
Umar ya fito da alama fita zaiyi ya hango mota, basai an fada ba yasan motar waye, yana tsaye yana kallansu har sukai parking. Shi kuma Amin tunda ya hango Umar sai ya hana Ibty fita, ya kalli su Islam yace su shiga ciki, shi kuma ya fito ba tare da ya kalli inda Umar yake ba.
Kofa ya budewa mata tare da mika hannunsa alamar ta kama, sarai tasan saboda Umar yai hakan, kunshe dariyarta tai a hankali itama ta dora hannunta saman tafin hannun Aminu ta fito cike da takama da kasaita. Umar na ganin haka ya zabura a fusace zai nufi inda suke yaji ya dunkule hannu kamar mai shirin dambe, ya nufo gub kai kace an taba matarsa.
Daga gefensa yajiyo muryar Abba, da sauri ya fara dan fifita da hannunsa alamar zafi da alama so yai yaje ya naushi Aminu.
"Juya min mota zan fita." Abba ya fada yana mika masa key din hannunsa.
Hannu yasa ya amsa cikin ladabi kamar gaske, Abba ne ya hada ido dasu Ibty nan danan ya fadada murmushinsa, da sauri Aminu ya saki hannun Ibty tare da san matsawa daga jikinta yana shafa bayan kansa, murmushi tai dan yanda yai ya bata dariya sosai, Abba ne ya karaso ya mikawa Aminu hannu suka gaisa, Ibty itama ta gaisheshi.
"Kushiga ciki mana? sannunku da zuwa." Umar ganin yanda Abba yake kishi ya kara kamashi, tahowa yai kamar yana waya ya bugi kafadar Aminu ya wuce. Abba na gani sai dai be ce komai ba hakan kuma ya tabbatar masa da cewa Umar na rike da Ibty a ransa sabannin abinda yace masa.
Bayan sun shiga sun sake gaisawa Abba yai musu sallama yana sane yace da Umar ya tuka shi su fita tare, dan yasan indai ya barshi za'a samu matsala a gidan.
Aminu kam a gidan ya barsu, sai da akai sallar isha sannan yaje ya dakko su suka koma gida. Da yake sunci sun koshi hakan yasa yaran yin bacci da wuri.
Tunda suka dawo ya kule a daki yana kallan youtube da karatu akan yanda ake soyayya, duk abinda ya gani sai ya girgiza kai yace Da girmana? Wannan abin yara ne, sai ya canza ya fara duba wani. Ganin dai bazai iya ba kawai ya kashe wayar ya dauko ledar dazu ya fito.

Bayan tayi shirin kwanciya sai kawai taga Aminu ya shigo rike da leda, mika mata yai ta karba tana jiran karin bayani taji yace
"Kisa fararen kizo bedroom dina." Yana fada mata yabar dakin. Ibty tai saurin zazzage ledar ta fara daga kayan a hankali, duk na bacci ne kuma babu na mutunci a ciki.
"Wayyo Allah na wannan zansa? Nashiga uku." Ta fada tana zama a bakin gado. Taya zata iya zuwa ya ganta cikin wannan arnayen kayan? Waye ya bashi wannan shawarar ta siyan su? Wayyo ita kam kunya takeji.
Ta dade tana shawara ganin lokacin yana korewa dare yana kuma yi yasa ta ritsa ido ta dauki fararen tasa, riga ce half vest da dan mitsitsin skirt wanda ko mazaunanta ba zasu rufe ba, tana gama sawa ta isa wajan madubi yadda kasan kareena Kapoor a beach ko ince irin ‘yan duniyan nan ansha bikini.
Zani ta janyo ta daura akai tasa hijabi ta nufi dakin nashi.
Tana murdawa ta ganshi a tsaye a bakin kofar, sai dai yana ganinta ya tsuke fuska, fuskarsa a hade yace
"Islamiya zaki?" Tai saurin kallansa taga yana mata up and down.
Tace “Islamiya?�?
Juyawa yai ya wuce gado ya kwanta tare da janyo laptop da alama ta bata masa rai. Ibty ta hadiyi yawu a hankali ta kashe wutar dakin tabar wutar dake kunne a gefen gado, ta rufe ido tare da cire hijab din tana kiransa.
"Yaya.." Aminu yai mata banza, ta bude ido taga ko kallanta bayayi idanunsa ma a rufe suke kamar mai bacci.
Zanin ta cire tare da fashewa da kuka ta tsugunna a kasa ta rike kafa.
"Habiby please..." Jin sautin kukanta yasa shi saurin mikewa ya nufo inda take riketa yai cikin tsananin kulawa zaiyi magana yaga tana kallansa tana dan murmushi, kallanta yai sosai nan ya ganta cikin kayan. Saurin kawar da fuska yai sakamakon wani irin abu da yaji yayi masa yawo lokaci guda.
Daurewa yai a hankali ya dago fuskarta, idanunta a lumshe taji yayi mata wata kyakkyawar runguma a faffadan kirjinsa. Sake dagota yai yana kallanta kafin ya maida fuskarsa saman kirjinta, luf tai, tanajinsa ya daga ta ya kawota kan gado kafin a hankali ya sa fuskarsa kan hancinsa, nan ya karaso ya kai bakinsa cikin nata…�?
(Mukam daga nan mukai waje🤸🏼‍♂️🤸🏼‍♂️🤸🏼‍♂�?)
******
A can gidansu Umar kuwa basu dawo ba sai magrib lokacin har Ibty ta tafi, haushi duk ya kamashi dan ko kwakwaren kallo bai mata ba.
Bangarensa ya nufa, yana shiga yaga Bilkisu akan kekenta tana zaune a falo tana kallo, tana ganinshi ta fadada fara’a wani takaici ne ya kamashi amma ya zaiyi? Haka ya washe baki kamar gaske yace “Amarya.�?
Murmushin jin dadi tai ta jawo keken tana cewa “Dazu su Ibtisam sukazo sun dade anan.�?
Ya waske yace “Haba dai? Ba raban zamu gaisa.�?
Jin haka yasa Bilkisu jin wani dadi lalai Ya Umar ya canza.
Abinci ta kawomai ya shiga daki ya fito ya zauna, yau kuma me muka samu?
Ya tambaya yana lankwashe kafa, bude kular yai, fried rice tai da soyayyen naman kaza, dadi ya kamashi, tabbas ko saboda wannan dole zai lalaba nakashashiyarnan, gashi daga gidansu ake kawo kayan abinci ba ruwanshi dayin cefene sai dai yaci ya koshi, wani sa’in ma daga gidansu akeyin abincin.
Nan fa ya cika katan plate ya juye duka naman, ya hau ci.
Wannan abin ne haryanzu bai mata dadi yanda in yazo baya tambayarta ko taci ko bataci ba kawai juye naka yake ya cinye. Sai dai gani take zai daina daga baya.
Sai daya cinye tas sannan ya nufi daki ita kuma ta gyara gun, sallar isha’i yai dan yanda ya koshi ko masallaci bayajin zai iya zuwa, danewa kan gadan yai ya bubude kafa yana tuno yanda yaga su Ibty sun wani rike hannu.
Kwafa yai ya runtse ido jin alamun hannu yai akan nashi hannun, ya dauka mafarki yake, yadanyi murmushi tare da rike hannun, lalai yanasan Ibty wato ma mafarkinta yake shima ya rike hannun da akamai gori dazu.
Hannu ya jawo yadan sumbata yadan bude idanunsa cikin sha’awa.
Idanunsa ne suka sauka akan Bilkisu tana murmushin kunya.
Wani abu ne ya tsaya mai a rai, ya daure yadan saketa a hankali yace “Banasan takura miki ne tunda ba lafiya gareki ba.�?
Matsowa tai ta riko hannunsa tace “Yaya dan Allah ka daina fadar haka, matsalar kafar nan bawai ta hanani rayuwa bane, taya zanki baka hakkinka bayan zan iya?�?
Yanda yake rike da sha’awar Ibth gaskiya dole ya huceta akan yarinyarnan.
Nan fa ya rikota babu soyayya babu wani lalabawa ya biya bukatarsa, itakam tasha kuka sai dai gani take haka akeyi tunda dai ba sanin kan abin tai ba.
Kasa ko zama tai gashi shi babu alamar yana da niyyar taimaka mata, ya wuce dakinta wai ya barta ta shirya shi bari yadan kwanta, nan fa ya baje ya shari baccinsa hankali a kwance, lalai yau ya rage abinda ke ransa.
Itakam ta kasa tashi duk yanda taso hakanan ta kwana, da safe ma tayi tayi ta mike ta kasa wayarta ta dauko ta saka a gaba tana tunanin wanda zata kira, duk wanda ta kira ta tabbatar zaisan sirrinsu, haka tai ta jan jiki tana kwalla harta wuce toilet, dakyar tadan gasa jikinta taba rike da bango ta dawo daki.
Haka taja kekenta ta leka dakinta, yana ta sharar baccinsa, jitai hawaye sun zubo mata, anya wannan auren zai yiwu kuwa? Abu babu tausayi sam? Kusa dashi taje, dan tabashi tai tana kwalla.
Cikin zafin rai ya bude ido zaiyi masifa sai kuma ya wayance, “Amarya ya akai?�?
Ta goge kwallarta tace “Ya Umar jiya bakasan a yanayin dana kwana ba?�?
“Yanayi? Ohhhh ai nasan zakiji daban tunda abinmu na farko, badai yanzun ma so kike a kara ba?�?
Sai yai dariya yace “Ba laifi abinka da sabun shiga daga ni har ke.�?
Fuskarta a hade take sosai dan bata taba tunanin abinda zaice mata kenan ba, lalai wannan na nuna rashin so da yake mata.
Hawayenta ta goge, mamaki ne ya kamashi badai yayi laifi ba? Karfa su koreshi dan Kawunsa yace “Inhar Abba ya koroshi tofa ya nemi wani gidan�? banda wahalar dayasha zuwan dayai, Goggo ta dinga dannamai tuwo ba ruwanta da abinda yake so.
Da sauri ya riko kafadarta cikin sanyin murya yace “Wani abin na miki?�?
Ta girgiza kai kawai tana neman fita, sake rikowa yai cikin sauri yadan rungumeta yace “Amarya kiyi hakuri kinga ni sabin shiga ne ba komai nake ganewa ba, in banyi daidai ba ki dinga hakuri dani.�?
Tausayinsa ne ya kamata ta girgiza kai cikin jin haushin kanta, ai ta tabbatar baisan ya abin yake ba shiyasa inba haka ba mezaisa ya barta.
Cikin sanyi tace “Kayi hakuri Ya Umar bansan me ya sameni bane.�?
Murmushi yai yace “Nima kiyi hakuri kinji.�?
Ta daga kai cikin jin dadi…�?..
(🤧Bilkisu)

*******

Su Islam na islamiyar Tahfiz saboda yau asabar ta wuce kitchen tana hada musu abincin rana.
Aminu ne ya shigo kitchen din yana kallan kitchen din kamar mai neman abu, cocumber din da take yankawa na salad ta ajiye ta kalleshi, shima kallanta yake hannunsa a baya yace “Naji ance mata suna so a dinga dubasu in suna aiki ne.�?
Murmushi tai tace “Bawai a duba muba a tayamu muke so.�?
Ido yadan ware yace “Me?�?
Ta juye cocumber din ta dauko lettuce tace “Ehen.�?
Ya koma jikin kofa yace “Shikenan sai mu cigaba da zaman mu basai mun leko mun duba ku ba.�?
Tadan turo baki tace “Na yafe tayin ko lekowar a dingayi.�?
Takowa yai yazo ta bayanta yadansa hannu ya zagayo dashi ta cikinta ya kansa akan wuyanta wani abu ne yadan ratsata tadan lumshe ido kadan, cikin dan rada yace “Haka kawai an sani karatu bayan na gama skul.�?
Karatu? Ta tambayeshi cikin mamaki.
Yadan gyara kansa yace “Eh ni kaina bansan ya akai na dage da karatu haka ba.�?
Juyowa tai tana mai kallan mamaki, ya dan rungumeta kadan yace “Bakyajin kunya in babban namiji kamar ni yana abu kamar yaro?�?
Ido tadan jujuya tace “A’a!�?
Ya saketa yana murmushi kadan kadan, tadan riko hannunsa tace “Ni banga yaushe kai abu kamar yaro ba.�?
“Kalleni fa a kitchen? Gani inata nemab janki a jikina.�?
Wasa da hannunta ta fara cikin kunya tace “Ni hakan ai dadi yakemin.�?
Ya dan sauke ajiyar zuciya yace “Ya zanyi? Tunda dai inaso in dauke hankalinki akan kowa sai ni? Gashi ina tsoron kar kiga da yaro kika aura da yafi kula dake?�?
Duk yanda taso kartai dariya kasawa tai, ganin yanda take dariya yasa yace “especially wannan kidahumin saurayin naki.�?
Ya juya kamar zai fita daga kitchen din, da gudu ta taho ta tsaya jikin kofar tana dariya haryanzu.
Fuskarsa cike da mamaki yace “Wai wannan ma abin dariya ne?�?
Ta girgiza kai tana hadiye dariyarta tace “Farin ciki ne ya sani dariyar ba komai ba.�?
Kallo mai dauke da tambaya ya mata, tace “Wannan alama ce ta kana sona.�?
Ya tako ya dan rike kuncinta yace “Ke sai yanzu kika sani?�?
Tana murmushin jin dadi tace “Tunda kake karatu akan yanda zaka kula dani kenan kafi sona akan……�?
Sai kuma tai shiru, hannu yasa a aljihu yace “sai ma kin hada?�?
Mamakin kalamansa ne ya kamata ta kalleshi cikin wani yanayi, mai kalamansa yake nufi?
Tana tunani taji yace “I can’t remember yanda naso ta sai dai yanda nakeji yanzu abu ne daban taba ji ba a rayuwata, hankalinki ya kwanta?�?
Hannu tasa da sauri ta rufe fuskarta, sumbatar hannunta yai ya fito daga kitchen din yana shafar fuskarsa.
Lalai Aminu lamarinka ya fara karfi, yaushe ka zama haka? Ya sake shafar sajensa lalai anyi girman kwabo. So ba ruwansa da girma.
Ya fada a fili yana murmushi.

Itakam gaba daya aiki take tana murmushi kamar wata wawiya, hannu tasa bayan ta gama miya tanaso ta dandana taji ko komai yaji, tana kaiwa bakinta taji tana neman yin amai, dan kirjinta ta bubuga lalai tsabar yanayin da ta shiga ne har taji batasan kamshi da dandanon abincin? Tabbas yau ita kadai tasan dadin da takeji saboda kalamansa

Ayusher 🏌️‍♂�?
5/16/22, 07:43 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)
   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki🤸🏻‍♀�?
*TURA 500 Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004

Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*50*
Karshe.....

Duk da zuciyarta ba haka taso ba, ba zata iya bude masa ba saboda kamar yadda Umma ta fada ne Umar bazai ga darajarta ba in har bata nuna masa kuskurensa ba.
Yadda yake mata magana kamar zai yi kuka shine yasa ta toshe kunnanta tana rintsa ido cike da zafin rai, ta jawo pillow din dake kan gado ta rufe kunnenta dashi da karfi tana zubarda kwalla, yanzu kenan laifinta ne yai sanadiyar zubar cikin ta, dan da ta kira Umma tun farko bata tsaya jiran Umar ba kila da bai zube ba.
Tana juyo shi daga waje yana cewa “Billyna zoki bude min dan Allah, wallahi bansan kin kirani ba dan Allah ki bude min yake abar kaunata. Kinfi kowa sannin yanzu zuciyata a mamaye take da kaunarki, dan Allah Billyna.�?
Gaba daya ta rasa abin yi a hankali Bilkisu ta taho wajan kofar saboda zuciyarta tana neman fin karfinta, har ta kama handled din da nufin budewa sai taji kiran wayarta, haka ta gungura kekenta taje ta dauka, ganin Umma ce yasa tai saurin dagawa inda tace.
“Kada ki sake ki budemai kofar nan kinji na fada miki, idan ba haka ba zai daukeki babbar banza kuma sakarai, ki bari ki karbi yancinki wannan fadan naki ne ba nawa bane ba kuma na Abbanki bane. Da alama tun farko dan ina shiga fadanki ne yasa kika saki jiki bakya nemawa kanki ‘yanci da kanki.�?
Hawayenta ta share tace “Umma yana ta hadani da Allah na rasa ya zanyi." Tai maganar cikin kara sakin wani kukan.
Umma cikin dan kakkausa murya dan ta shiga hankalinta tace “Nadai fada miki Karki kuskura ki bude, ke ko haushin abinda ya samu jaririnki bai isa ki nunamai kuskurensa ba? Allah yaga zuciyarki yaga tashi, dan haka ki dena ma sauraransa."
Bilkisu ta jijiga kai sannan ta ajiye wayar tana dora kai saman cinyarta.
Ganin taki budewa ya tabbatar masa da cewa itama taji haushin abinda ya faru, hakan kuma ya sake tabbatar masa da cewa Bilkisu zata iya rabuwa dashi. Ya matsa kusa da kofar yana mata magana cikin magiya
"Shikenan Sahibata tunda ba zaki bude min ba zanje kan titi na kwanta har katuwar mota tabi ta kaina tunda kema kin tsaneni yanzu." Umar na gama fada mata haka yabar wajan jiki babu kwari.
Da sauri Bilkisu ta nufo kofa ta bude sai dai bata ganshi ba alamar yabar wajan. Wani ihu ta saki wanda yasa su Umma fitowa da gudu suna tambayarta.
"Lafiyar ki Bilkisu? Menene haka?"
"Umma! Na shiga uku Umar zai kashe kanshi, dan Allah Umma kubarshi yai min duk abinda yaga dama, wayyo Allah Umma wallahi ina sanshi."
Tsabar takaici yasa Umma kasa yi mata magana, ji take kamar ta shaketa saboda haushi. Harara kawai ta zabga mata tare da wucewa ta koma daki tana ta masifa. Iman ma tsayawa tai tana kallan Bilkisu wacce ta gunguro kekenta ta rike hannun Iman cikin kuka tace “Iman ku tausaya min, ku gane cewa Allah yayi Umar a haka ne, koda Ibty ya aura halinsa ne a haka, dan Allah ki bishi kice ya dawo." Saboda ta kyalesu yasa Iman cewa.
"Bari naje." Ta fita can bayan wasu lokuta sai gata ta dawo inda ta samu Bilkisu a falo tace.
"Na sameshi a bakin gate yace shikenan amman ki bari Umma ta huce sai a sasanta." Bilkisu ta sauke wata nannauyiyar ajiyar zuciya tana lumshe ido.

Umar kam yana waje yana safa da marwa yana kallan wayarsa tare da leken ko zaiga wani yazo bashi hakuri.
Ganin Iman yasa yai kwafa tare da yin wani murmushi yace “Ai nasan bazata iya rayuwa bani ba.�?
Yana kokarin bude kofa cikin kasaita da isa kawai yaga Iman tayi shawaginta ta koma ciki.
Mamaki ne ya rufeshi kamar ya kirata sai kuma ya tsaya yana kallan abinda take ko komawa tai ta dawo?haka ya karashi zamansa ya koma ciki, kitchen ya shiga ya dinga bude drawers yana neman abin ci, wannan wani irin iskanci ne? Ace ko abinci babu dafafe?
Bai iya ko kunna gas ba sai abokinsa ya kira a video ya koyamai, haka yai haukar dafa farar taliya ya zuba mai da yaji ya zauna yana ci yanda kasan ya samu nama, wannan wani irin masifa ne? Yanasan fita yaje ya sai abu amma yana tsoron karya kashe dan kudin hannunsa a zo amai korar kare. Ai dai ance abinci ya kare ko? Gobe dai dole a kawomai in kuma baso ake a kasheshi ba.

Washe gari har wajan karfe goma yaga ba'a kawo mishi abinci ba, ga yunwar ji yake kamar zai mutu, yaso dafa wata taliyar amma babu, ita kenan ya samu ‘yar kadan jiya, yana mamakin dama Bilkisu kullum w gidansu take amso abin dafawa kenan ko me? Rai a bace, ya tashi ya fita zuwa sashen su Umma. Yayi sa'a Abba ya dawo da alama jiya da daddare ya dawo, cikin jin dadi ya kalleshi ganin yana karin kumallo, sum-sum ya shiga ya duka yana gaishe, Abba bai tanka mai ba karahe ma yi yai kamar baisan da zaman sa a gun ba.

Yadan sassauta murya kamar mutumin arziki, yace “Abba kaima fushi kake dani?" Abba ya ajiye kofin shayin hannunsa.
Kamar bazai amsa mai ba sai kuma yace “Ba dai ni kake yiwa wannan maganar ba ko?�?

Umar yai kalar tausayi yace “Abba ina san Bilkisu na rantse da sarkin dake busa numfashi ina santa, duk abubuwan da suka faru tsautsayi ne, bada sanina bane wlh Abba inaji a jikina asiri akamin, sam bansan sanda nake aikata wasu abubuwan ba.�?
Ya dan nisa cikin sanyin murya yace “Idan har kuka raba auran nan Abba rayuka ne zasu baci."
"Anzo gurin, daidai wajan ma kuwa, Umar dan Allah wane rai ne baka gama batawa ba a cikin gidan nan? Ashe akwai ragowa ban sani ba?" Umar yai saurin cewa “Ba haka nake nufi ba Abba, wallahi baka fahimceni bane."
"Tashi kabani guri, ba ance Bilkisun tace ta hakura da auran ba? Inaga ai an hutar da kowa ko? Allah ya hada kowa da nashi rabon."
Lallai mutanan nan sun shirya raba su da Bilkisun shi, bema san yanacin arzikinta ba sai yanzu da yaga tabbas za'a rabasu. Ya zauna ya dinga bawa Abba hakuri har Umma tazo wajan, ya hada da ita yana ta magiya kamar makahon da ya rasa hanyar gida. Umma na shirin magana ta hango Bilkisu a can gefe tana hawaye, hakan yasa ta hadiyar yawu mai daci, babu yadda zatai dole ta hakura kafin Bilkisu tawatsa musu kasa a cikin ido.
Umma ta daure cikin halin ko in kula tace. "Ni babban bakin cikina yadda kake mata kamar ka samu dabba, Umar ka manta wacece Bilkisu a wajan mu? Bilkisu ‘yarmu ce ta cikin mu, ƴar uwa a gurin IBTISAM idan har kana da mutunci zaka lallabata fiye da yadda zamuyi, in har da gaske san Ibtisam din kake ai bazakaso abinda zai illata yayarta ba ko?�?
Yai shiru yana sauraren Umma, jikinsa duk yadanyi sanyi.�?
Umma ta kalli Abba sannan ta kalli Bilkisu tace “Zan sake baka Bilkisu a karo na karshe, idan har ka kuskura tayi kuka ko ranta ya baci kasan da cewar sai ka bar gidan nan koda kuwa shine karshen rayuwar Bilkisu." Tana kaiwa nan taja tsaki tare da barin wajan.
Abba yai masa nasiha sosai sannan yace zai bashi jari yai sana'a ya rike Bilkisu da kuma kanshi saboda halin rayuwa karya saba ana bashi randa Abban ya mutu yazo su rasa yadda zasu yi.
Farin ciki ya lullubeshi tare da daukar alkawari zai riketa kamar kowane miji a gurin matarsa.
Yana kokarin mikewa sukaji muryar Bilkisu tace “Abba ko ka bashi ni bazan koma ba, takardata nake jira.�?
Gaba daya mamaki ne ya rufesu suka kalleta cikin mamakin abinda ta fada, tabbas tana san Umar kamar ranta sai dai gani yanda iyayenta ke lalabashi suna kashemai kudi saboda ita, kuma duk da hakan babu alamun so a tattare da shi yasa taji ko zata mutu yanzu kam zata hakura dashi, ta tabbatar iyayenta basa farinciki da wannan auran, gashi a dalilinta ta rasa ‘dan cikinta.
Cikin mamaki Abba ya kira Umma wacce ke zaune a bakin gado rai a matukar bace.
Fitowa tai cikin kunar rai, sai dai jin kalaman Abba yasa gaba daya ta tattare hankalinta kan Bilkisy.
Cikin dauriya ta kalli Umma sannan ta kalli Umar tace “Ya Umar dan Allah ka bada takardata kafin ka fita, in kuma kana bukatar biro da paper ne yanzu Iman sai ta kawo maka.�?
Ta maida kallanta kan Abba tace “Abba dan Allah in ya rubuta aba Iman ta kawomin.�?
Bata jira mai zasu ce ba ta shiga daki ta kulle, kuka kawai tasa tana dukan kirjinta ita kadai tasan irin masifar san da takewa Umar a rayuwarta.
Gaba daya falan yayi tsir kowa mamakin abinda ya faru yake, Umar a firgice ya sa gwiwowinsa a kasa ya hade hannaye yace “Abba wallahi Allah na tuba dan Allah ku yafemin.�?
Mikewa Abba yai ya nufi daki, Umma tabi bayanshi.
Hankalin Umar yayi mugun tashi tabbas yanzu abin ba wasa bane, ya shiga uku? Ya zaiyi?
Duk yanda yai magiya Bilkisu taki yarda, gashi Abba ya kule bangarensu, dakyar Abba ya yarda ya koma dakinshi nada, haka kullum zaizo yana bada hakuri amma Bilkisu ta dage tace sun gama zaman aure, ita kanta duk ta canza ta rame amma ta kafe tace bataso.

********

IBTISAM kuwa a nasu bangaren cikin yazo mata da laulayi sosai, Aminu kuma ya sake zurmawa cikin shafin kaunarta, gaba daya ya kasa sukuni saboda rashin lafiyarta, in ya tafi aiki yana kira sama da sau biyar ya dinga jin ya jikinta da sauransu.
Ibty gaba daya ba ta iya cin abincin da ta dafa sai na gurin Ummi shima daga danwake sai tuwo da kunun gyada. Kullum driver yana hanyar gidan Aminu kai abinci, idan sukaji shiru kuma sai Aminu yaje da kanshi ya amso mata in yana gida, ita kuma takan jure wajan yiwa Aminu da su Islam girki amman ita ba zataci ba.
Yau aka samu matsala Ummy sun tafi gaisuwar wata yar aminiyarta ta rasu, ibty na gida kamar zataci babu saboda yunwa. Aminu ya shiga dakinta ya tarar da ita sai juyi take akan gado, cikin sauri ya isa wajanta ya dagota zuwa jikinsa.
"Habibty ya akai? Me yake damunki?" Hannu ta saka ta riko shi tasa idanunta cikin nashi kamar zata fashe tace “Ummy bata gida, gashi yunwa nakeji wallahi kamar zan mutu haka nakeji." Gyara zamansa yai tare da kwantar da ita saman kirjinsa, bayanta da gashin kanta ya shiga shafawa cikin lallashi yace “To ko ni zan zake dantse na daure na dafa miki ko indomie ce kici? da kaina ma zan dafa miki, am sure zakiji dadinta."
Kallan mamaki tamai tace “Kai din?�?
Ya dan hadiyi yawon bakinsa shi kansa fada kawai yai dan bai san ma ya ake ba, kawai dan zolayarnan ne.
Mamaki ne ya kamashi dayaji tace “Banacin indomie, taliya ma bana so sai dai kaimin danwake." Aminu ya zaro ido yana kallanta yace “Danwake?�?
Tadan shagwabe tana daga kai, yanzu ne lokacin da zaki dan moreshi ko ruwan tea tunda akai aurensu bataga ya dafa ba, Aminu fa an shiga tunani. Yanzu ina yasan yadda ake danwake? Abu daya ya sani ana saka kuka itama besan a wane lokaci ake amfani da ita ba. Ibty da taji yayi shiru sai ta juyo ta kalleshi, ya sakar mata murmushi kamar gaske, cikin wasa kai yace.
"Wanda zan miki sai yafi na Ummy dadi, zaki sha mamakin dadinsa, kwanta ina zuwa." Ya kwantar da ita shi kuma ya fice daga dakin. Yana shiga dakinsa ya sauke numfashi yana furzar da isa daga bakinsa. Kodai ya kira Aina ne ya sata ta dafa sai ya amso ya kai mata? Amman kuma idan ya kirata shi kuma cikin yace baya so dole fa shi din ne zai yi ko? To idan shima yayi cikin yace baya so fa?
"Kai ya subahanallahi." Ya fada yana dafa bango. Wayarsa ya janyo ya kunna data, YouTube ya shiga ya nemo yadda ake danwaken, cikin sauri ya tashi ya nufi kitchen din duk abinda yaga an fada a hadin sai da ya dakko a ajiye a gefe, wanda be gani ba zaije ya tambayota inda ta ajiye, Allah-Allah yake ya gama tun kafin yara suzo su ganshi dan baisan me zai ce musu ba.

Ta YouTube video Aminu ya kalla yai mata danwaken, shi kansa sai da ya burge kanshi ganin yadda komai ya kammala, sai dai fa ya bata kwanuka sunfi nawa gaba daya kitchen din yayi kacha kacha ko ina flour da kuka.
Ya zubo a cikin dan bowl ya dakko tire ya dora yaji da mai da ruwan sha ya dauka ya nufi dakin. Lalai Aminu wai mantawa kake da shekarunka? Abinda zuciyarsa tace kenan, ya dan yi murmushi in banyi ba yanzu sai na tsufa zanyi? Da wannan ya shiga dakin, ya tarar da ita ta fito daga wanka saboda tunda cikin nan ya sameta buni-buni tayi wanka ta zama tamkar wata kifi. Sai da ya ajiye tire din a kan gado sannan ya karasa ya taho da ita ta zauna.
Kallan bowl din tayi mamaki ya bayyana saman fuskarta dan ta dauka ma wata hidimar ya shiga ko kuma kila fita zaiyi ya siyo mata ya kawo mata, daga karshe ta yanke tunani akan lalai Ainah zai turawa tayi yaje ya dauko, dan Ummy tace zatasa a yi amma ita Ibtyn tace a barshi tanada ragowar, sam batasan daurawa su Ummy wahalar nan.
Baki ta saki tana ta kalleshi kafin ta kuma kallan danwaken ta janyo shi gabanta tasa yaji da mai tana cewa.
"Wai dagaske Habiby kaine kayi wannan?�?
Hanaye yasa a aljihunsa ya dan zauna tare da harde kafa yace “Ce miki akai shekarun danai a banza nai?�?
Ta sake kallanshi cike da mamaki, ya dan daure fuska yace “Wai ke kin dauka ban iya ba?" Ya fada cike da kuri.
"Wallahi nasha mamaki, Ummy fa tace bata taba ganin ka soya koda kwai ba bare abinci. A gida in an ganka a kitchen to tea ka shiga hadawa.�?
"Af yo komai nawa ta sani ne an gaya miki? Kinga yanzu sai kije ki basu labarina." Tana motsawa tace dashi “A’a fa karfa ka cika baki, ka bari baki ne zai bada amsar girkin naka ba wai ido ba." Ta diba shi kuma yai saurin rintsa ido yana shafa tafukan hannayensa kamar mai shafa mai. In baiyi dadi ba ai ya bada kanshi.
Shiru beji tace komai ba hakan yasa shi kuma rintsa ido yasan an samu matsala.
Ya juyo cikin dakewa da rashin san nuna abinda ke ransa yace “ya akai?" Ya tambayeta yana bin yanayinta da kallo.
"Me aka yi?" Ta fada tana kallanshi tana kokarin boye abinda ke ranta.
Ido ya kankance yana mata wani kallo, fork tasa ta sake dauka takai bakinta, bata ko sake magana ba sai dataci spoon hudu, ai Aminu besan lokacin da ya saki murmushi dan ya tabbata komai yayi.
"Habiby gaskiya ka iya wallahi, ni daga yanzu ma kai zaka dinga yi min yafi na Ummy dadi."
"Ke! Me zan dinga yi?" Kallanshi tayi cike da marairaicewa tace masa.
"Danwaken." Aminu yace.
"Tab kin maidani kuku? Hajiya sorry bazanyi karya ba dan bazan iya ba.�?
"Allah ba ruwana babyn ciki na ne yake so bani ba.�?
Suna ‘yar hirar nan ta cinye tas da yake waya yake yi sai ta tashi ta kai kayan kitchen anan ta tarar da aika-aikar da yayi.
Goshinta ta dafe lalai taci dan wake da wahala, dan dacin wannan dan waken da wannan uban aiki ai gwara ba’aci ba.
Nan ta shiga tattare kwanukan da aka bata sannan ta shiga wanke-wanke, sai datai wajen rabi ya shigo tare da kamo kugunta ya rike sannan ya kwantar da kansa a kafadarta yace “yaushe aka tara kwanuka haka? Dazu fa da na shigo babu kwanukan wanke-wanke.�?
Kallansa tadanyi kadan tace “Dan wake ne ya tara mana.�?
Baki yadan bude yace “Wai nine na tara kenan?�?
Murmushi tadanyi “Madam karfa kice in tayaki dan bansan ya akeyi ba. Nadaiyi sanda ina karatu a kasar waje amma ban iya ba.�?
Ta dan yi kasa dakai tanayi yana tsaye a jikinta suna ‘yar hira kafin daga baya ya tayata kifa kwanuka har suka gama.
Yadan kalleta yace “Sai muje yanzu kuma a bani ladan aiki." Ya fada yana jan hannunta ya nufi dakinsa.
Suna shiga daki tana dariya tace “Nawa ne kudin?" Ta cigaba da dariya kasa kasa.
"A'a wallahi ni bana kudi nai miki ba, zuwa zaki nan gurin." Ya nuna kusa dashi yana gyara mata filo.
"Yaya an kusa kiran sallah fa." Ya shafa kai saboda gabaki daya yasawa ransa dan haka ya mike ya kamota.
"Dama ance ‘yan yaran nan sufi jan aji gurin shimfida.�?
Suka saki dariya tare da hawa kan gadon. Daga nan fa suka ci gaba da farantawa juna rai, Aminu gaba daya yayi laushi a hannun ‘yar yarinyar da ya raina, a koda yaushe in suna tare har mamakin kansa yake, sai dai fa in suna cikin mutane yana nuna fa shi namiji ne babba, ita abin ma dariya yake bata wani sa’in in gaga ya daure a gaban mutane.
Lalai ba shakka su Hajiya ne suka juyar mai da hankali dan mutum ne mai saukin kai da yiwa mutum uzuri in yai laifi.

***********

Dawowarta daga makaranta kenan ta baje a parlor ta kwanta tana ta bacci, gajiyar da tayi ne ya hanata ko cire hijabi bare ta nemi abinci. Cikin bacci taji tamkar ana sallama amman ta kasa tashi, duk a tunaninta ma mafarki takeyi.
"Ibtisam." Umma ta kira sunanta tana bugun kafarta. Ibty ta bude ido a hankali, wa zata gaji? Ai da sauri ta tashi ta rungume ta tana murna.
"Umma sannunku da zuwa, Yaya Bilkisu hardake?"
Umma ta girgiza kai tace “Yanzu in barawo ne ya shigo har sata sai yai kina baje kina bacci.�?
Sai a lokacin ta dan rufe baki tace “A bude nabar kofar?�?
Umma ta harareta hakan yasata yin murmushi tace “Zan kula nan gaba.�?
Bilkisu tadan tura kekenta bayan ta gama dan zagaya falan dan yau ne zuwanta na farko tace “Ke kuma a haka kike sha'awar kwanciya? Kinga a yadda muka tarar dake kuwa? Ke a takure babynmu a takure?�?
Kai ta sunkuyar dakai cike da jin kunyar Umma yanzu fa kowa yasan mai tai ta samu cikin ko?
Bata san ana magana akan cikin nan saboda kunya takeji sosai.
"Nima dawowata daga makaranta kenan na kwanta sai bacci, bari na kawo muku ruwa."
"A'a bashi wucewa zamuyi Iman ta dage sai mun biyo." Cewar Umma tana sake kallan Ibty.
"Ina kukaje?"
"Asibiti." Iman ta fada tana shiga kitchen.
"Waye ba lafiya Umma?"
"Ba kowa Bilkisu muka kai, tunda tai barin nan take ciwon mara shine mukaje saboda ina tunanin ko be gama ficewa ba, munje kuma an duba lafiya lau."
Suka hada ido da Bilkisu, nan da nan na mata sannu. Hira suka taba dan Umma yanzu tana ta kokarin jan Ibty ta fahimci lalai duk abinda ya faru itace sila da ta ja Ibty a jiki to fa da duk hakan bata faru ba.
(Iyaye dan Allah mu dinga kokarin jan ‘ya’yan mu a jiki especially ‘ya’ya mata dan sai kin jasu a jiki ne zasu iya sanar dake matsalarsu.)
Bayan sun gama hira ne su Umma suka tashi suka tafi ita kuma taje tai wanka.
Assignment din da aka basu tai shiga yin browsing tana yi Aminu ya dawo, ya zauna sukayi a tare ta rakashi dakinsa yai wanka sannan suka fito falo.

******

A bangaren Umar kuwa gaba daya yanzu Allah ya jarabceshi da mugun san Bilkisu, ga sha’awa dake damunsa kullum in zai kwanta, tabbas yaji dadin saduwa da ita gashi yanzu duk yanda ya bata hakuri ta kafe ta tsare tace a’a.
Gaba daya ba wanda yake kulashi yanzu a gidan, abinci wannan a bakin kofarsa Iman ke ajiyemai tai tafiyarta, Abba kuma ya hanashi shiga cikin gidanshi.
Rayuwa tamai zafi yanzu har letters yake rubutawa Bilkisu ya sa a kwanon dayaci abinci, text kuwa kullum sai ya mata amma ba reply, gaba daya ya canza ya maida hankalinsa gun aiki dan ba wanda ke kulashi, kauye ma Kawunsa yace in har zaizo ta ya tabbatar ya daidaita da matarsa, ita kanta Goggo taki kulashi.
Wannan abu yamai yawa abokan ma yanzu duk sun daina harka dashi.
Watansu biyar da rabuwa zazzabi ya kamashi cikin dare, ya turawa Bilkisu sako tare da sanar da ita halin da yake ciki, kamar bazata kula ba sai kuma ta tuna halin data shiga a dalilin kin zuwan dayai, haka ta fito va tare da sanin kowa ba ta nufi bangarensa, a hankali tadan kwankwasa yana daga ciki ya mike dakyar dan ko abincin rana baici ba, yana tafe yana fatan Allah yasa itace, a hankali ya bude kofar nan suka hada ido, fuska ta daure tana neman juyawa, da sauri ya rikota yana cewa “Billy ki yafemin dan Allah!�?
Tsayawa tai bata juyo ba, hannu yasa a kan kafadarta zafin dataji ne yasa tadan juyo, bakinta nadan rawa tace “Da gaske bazaka rubuta takarda ta ba?�?
Ya girgiza kai yace “Ko a haka zamu dawamma bazan sakeki ba, ki tuna ni mijinki ne, nayi iya kokarina na ganin kin hakura, to amma tunda kinki zan umarceki a matsayina na mijinki ki koma dakinki gobe.�?
Yanayinta ne ya canza ya dawo gabanta ya tsuguna yace “Billy please…�?.�?
Tausayinshi ne ya kamata ta rike hannunsa tace “Kasha magani?�?
Ai bai jira komai ba ya rungumeta yace “Dan Allah ki dawo, wallahi Allah bazan sake wulakantaki ba in har na kuma duk hukuncin da kika ga dama ki dauka.�?
Nan suka daidaita washegari ta sanar dasu Abba ta koma dakinta.
Umar gaba daya ya canza, tunsanda yaji Ibtisam nada ciki ya tsani kanshi, ita gata can tana rainon cikinta amma shi dan asara ya jawo sanadiyar zubar da cikin datai.
Wannan dalili yasa ya kara kaimi gun kula da Bilkisu yana kuma fatan Allah ya basu wani cikin.
Hankalinsu Abba yanzu ya kwanta dan Umar ya canza banda zafin rai wanda haryanzu yake dashi.

*****
Cikin Ibty yakai wata tara haihuwa yau ko gobe, ta ajiye karatunta a level 3 akan in ta haihu zata dawo ta cigaba, Aminu da kanshi ya nemi alfarma aka kawo Iman gidan ta zauna da ita, sannan duk weekend Ainah na zuwa tai kwana biyu sai ta koma.
Kulawa ta ko ina tana samu sau da dama takan yi kuka sai taga anya ta cancanci wannan farincikin kuwa? Ilham da Islam na tsananin santa ita ma tana iya kacin kokarin ta, har addu’a take a ranta akan kada Allah ya bata damar nuna banbanci tsakaninsu da ‘ya’yan da zata haifa nan gaba.
Alhamdulila nakuda ta zo mata suka nufi asibiti inda ta haifi danta namiji, Aminu ya sa mashi sunan Abdullahi dan yana san sunan.

Aminu bai kara waiwayar zuri’ar Hajiya ba bai kuma sake bi takansu ba, mahaifin Na’imah dai suna gaisawa wani sa’in har gida yake zuwa ya gaisheshi banda shi bai bi takan kowa a cikinsu, a koda yaushe yana godewa Allah daya kawo Ibtisam cikin rayuwarsa, yanzu hankalinsa a kwance yake sai dan abinda ba’a rasa ba wanda dukanmu dani da ke mai karantawa munsan rayuwar aure dole in ana tare wani sa’in za’a samu matsala�?..

Allah ya kara daidaita rayuwar auranmu da mazajenmu, wanda basuyi ba kuma Allah ya kawo miji na gari.

****
Alhamdulila ina godiya ga duk wanda ya sai novel dinnan ya karanta, wadanda kuma suke san siya su min magana ta number dake sama☝�?
Ku biyoni a cikin wani saban littafin kar ku damu free zanyi 🤪

Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.