Bakon Lamari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: BAƘON LAMARi By Haseenatu.txt
Chapter 9 of 26
Minti kaÉ—an ta dawo da akwatin Æ´an kayan gaba É—aya wanda mamaki ya cika Amatullah haka ta zazzage kayan waÉ—anda ba yawa gare su ba Matan gidan ko wacce tabi kayan da kallo banda Mama data É—auki Riga mai kyau ta sanyi ta Sinke Æ´ar.
"Amatu bakya bata Nono hala?"
Da sauri Amatullah ta É—ago tana Bin mama da kallo kamar su da Ahmad har tai yawa sannan taji ta gaya mata sunan da É—anta yake gaya mata.
Batai magana ba tai ƙasa da kanta.
"Amsheta ina zuwa"
Mamar ta faÉ—i.
Da kanta ta miƙe ta haɗowa Amatullah tea mai kauri nan da nan ta rufeta da faɗa tana ce mata.
"Gidan ki babu abin da zaki nema ki rasa cikin sa baza ki ci abinci ba Laifin Hadiza ne ( ummah ) tunda ita ba zata tsaya ta lura dake ba haihuwar fari ce in bata tsaya akanki ba zaki lalace shiyasa nacewa Mijin Hafsa ya kawon abata in watan haihuwarta ya kama"
Amatullah ta amshi tea É—in ta kafa kai tana sha wanda Anty ta amshe maganar.
"Ai mama yaya hadiza sam ta gyara halinta ace mu ta mayar damu ababan gaba fisabilillahi rayuwar haka zata tafi Ace kaf matan gidanmu sai tazo da kanta taiwa Amatullah wanka"
Mama tai murmushi tace.
"Rabu da maganar Lami bata da amfani Allah dai ya ganar da Hadiza kawai"
Daga haka taja bakinta tai shuru bata bawa Anty ƙofar taba da haka zata ja gulmar Ummah ai tayi da matan gida.
Har la'asar suna gidan anan suka ci abinci ban da mama da take azumin alhamis.
Haka har ranar suna tazo ƴan uwan Amatullah basu yanke ba umma tai mitar zuwan nasu amman Amatullah tace mata arziƙine kuma tun daga wannan Dubarar shan tea da mama ta nuna mata shikenan ruwan Nono ya kawo yarinya ta sami abinci.
Anyi suna lafiya Yarinya taci Sunan Ummah Khadijatul Iman amman Iman É—in za'a ke ce mata.
Kuma har lokacin Babu wani daga cikin ahalin imran daya zo gidan Amatullah bata sami fuskar tuhumar shiba a daddafe umma tai zuwan sati bayan suna.
Daga nan kuma Amatullah ta koma cigaba da kula da yarinyarta.
Lokacin datai kwanaki ashirin agidan Imran ya soma Tsiro mata da wasu halaiya na daban Son kusantarta acikin Jinin Biƙi ji wani jahilci ƙin amincewar da tayi shine ya tsiri hanata abinci tare da Kulleta a ɗaki tun safe har sai ya dawo zai Buɗeta..........
_EKEJA BARRACK LAGOS STATE_...........
*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*
*Ina masu kananan nono?*
*Ina masu yaye?*
*Ina yammata da ake shirin aure?*
*Ina matan gida masuson gyara?*
*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*
*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*
*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko uwargida ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*
BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MOREÂ @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679
IG Bintus-spa-nd-more..
*BAƘON LAMARI...!*🌹
{ Eternal love }
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*007*
Juyi kawai yake a saman kujera hannun shi riƙe da wayar shi yana duba posting Ɗin da aka turo mishi yanzu na zuwa Kano wanda zai ɗauki watanni kusan uku acan, Shine zai jagoranci rindunar sojoji ta farko da zasu shiga wasu daga cikin ƙauyukan Kano waɗanda ake tunanin wasu mutane da ba'a san ko su waye ba suna haurawa cikin dare suna kwashe musu dabbobin su tare da ƙona musu Gidajen su wannan tasa Aka buƙaci sojoji kusan Rinduna Biyar don ta shiga ƙauyukan ta bawa mutanan dake ciki kariya.
Duba Map É—in Æ™auyukan ya shiga yi wanda suke Cikin Æangareron Kano maso kabashin Gudu Batare da wata shakka ba ya tura shaidar Gani tare da aje wayar tashi yana Cike wata takarda dake gaban shi.
Tura Ƙofar Office ɗin nashi akai tare dayin sallama Abokin Aikin shi Captain Khalil ne ya shigo sanye Cikin kakin su na soja Miƙa masa hannu yayi suka gaisa sannan ya nuna masa Kujerar dake kallon Shi.
"Khalil yanzu nake ganin Wani posting letter ko kai ma ka gani?"
Captain Khalil yaja tsaki tare da cewa.
"Kai dai Bari Makama nagama Shirin tafiya zamfara kasan Gida ce amman Mutanan nan suka sauya mana rinduna"
Murmushi Ahmad yayi tare da cewa.
"Au kaifa gida aka tura ka ko? to ka sani Ko kanon ce alheri gare mu?"
Khalil bai yi magana ba ya janyo wayar shi yana nunawa Ahmad cikin ta.
"Kaga nan zamu sauka a Bakabo barrack fa na can janguza wannan posting sam bai min daÉ—i ba wallahi"
Ahmad yace.
"Na gani mana Allah ya zartar mana da alheri haka kwanakin Baya Nai shirin katsina naga an mayar dani Barno haka na tafi kasan a rundunar mu ni kaÉ—ai nayi rai"
Haka suka ɗan tattauna akan tafiyar tasu wadda Shida Abokin aikin sa Khalil sune zasu jagoranci Rindunar sojojin ɓangaren su, sauran tawagar ukun daga wata tawagar ta daban take.
Bayan gama maganar tasu Khalil ya tashi ya koma office É—insa.
Bayan sallar azahar suka soma training da tawagarsu sai wajan yamma ya koma gidan shi duk ya gaji haka ya watsa ruwa ajikin shi ya kwanta agado yana mai jin wayar shi tana ringing!
Idanun shi a rufe ya ɗaga wayar yana sakin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya.
"Tunda mukai magana rannan Shikenan ka share ni ka manta dani wato dani da Babu duka a É—aya a rayuwar ka Ko Baby?"
Muryar Zee wadda take maganar cikin shagwaɓar da take masa a koda yaushe idan suna waya.
Ya janyo pillow ya matse a kirjinsa ya gaji Hutu yake buƙata amman yasan idan yace mata haka wata rigimar ce zata kuma tashi.
"Kiyi haƙuri zainab wallahi ayyuka ne suka sha kaina yanzu ma haka".....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.