Complete Hausa Novels

Dingishin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Dingishin Kwado Book 1.docx

Chapter 1 of 2

[9/[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya bugo mini waya ya ji ya jikina ma bai yi ba, watakila ma ya mance da ni. Duk yadda ya kyamaci Amrah ta dawo ita kadai. Na lura tunda ya fada soyayya da yarinyar nan haka yake bata umarnin ta dawo da kanta.

A kullum sai na tuna Abida sama da sau ashirin. Don kuwa kullum sai na ci karo da abin da yake na gaskiya a cikin hasashen da ta dinga yi akan Sahal. Zamanmu na nisa matsaloli na sake girmama.

Ya mike yana fadin "bari na yi wanka gabadaya na gaji."

Bai jira abin da zance ba ya shige dakinsa da saurinsa domin kaucewa kallon da nake masa mai kaifi.

Tsawon lokaci ina zaune ina ta sake saken zuciya. Duk da ban taba yi masa magana akan kudaden da yake fitarwa ba, wannan kam ba zan iya yin shiru ba.

Kwanaki kadan da suka shude ya cire sama da 150 kuma shima store ne suka cire, tabbacin shopping suka je ya yi mata, yau ma ya cire kusan hakan duk a cikin sati guda bayan wanda ya fitar da ya je siyo mana kayan amfanin gida, yauma ya sake cirewa ban da kananun da yake cira yana yin alheri da su ga ahalinsa da duk wanda ya so.

A sanyaye na nufi dakina na watsa ruwa dan na samu na sake wartsakewa.

Na shafa lotion (coconut na oriflame).

Wanda na farare ne irina Aisha lame ta zaba mini, sosai nake jin dadin amfani da shi mussaman yadda ya sanya na yi tas fatar ta yi mulmul. Na gasgata products din da lame take sayarwa na kuma gamsu an mata baiwar sanin dukkan rabe raben skins, tare da sanin naui'in man da zai dace da kowa. Don kallon ka kawai zata yi ta gane irin man da zai dace da fatarka.

Tuntube ta a wannan layin dan samun kalar naki man da zai gyara miki fatarki ko da ta fara yamushewa saboda tsufa ko rashin samun kulawar da ta dace.

*Lame Nig....07036662633.*

Rol on kawai na saka na zura rigar barcina cotton wacce cikin siyayyar da na yi ne a wajen Umm Asalah +201121544627

+2349162662750 kamshin turarena ya kamata.

Na sanya dogon hijab din gunis na fita.

Na leka dakin Amrah na tarar da ita tana kallo a wayarta. Na mika mata hannu, ba ja in ja ta miko mini domin doka ce karfe goma zata kawo mini wayar ba dan makarantar da take zuwa sun màtsa kowanne dalibi sai an siya masa waya ba da ba zan amince ta rike waya ba sai ta kammala sakandire domin hadarin da yake cikin wayar a wajen yara masu shekaru irin nata yafi alkhairinsa yawa. Kana tarbiya kana ta boye musu abubuwan da basu kai su gane ba ashe su kam kallon fanko suke mana domin da wayar hannunsu babu iyashegen da basa ga ni ko ji.

Na tsani na ga ta bude tiktok din nan tana ganin yaran mata suna sakin maganganun rashin da'a da kunya hadi da shigar banza tamkar dai basa tuna watarana zasu koma ga ubangiji ga kuma doguwar kwanciyar kabari da take gabansu.

Na leka Farha da take kwance a kan gadonta da shine na farko.

Barci take yi cike da nutsuwa. A duk sadda take barci ko ta yi murmushi sai na ga tamkar Abida ce. Duk da ba kammaninta a tare da ita.

Na kalli Amrah na ce "kin sa ta yi addu'ar barci?"

Tana daf da shigewa bayi ta ce "Ta yi Mahmah, sai da safe".

Ta shige bayin ni kuma na ja musu kofar na nufi dakinsa.

A kishingide na iske shi da waya a hannunsa. Na isa na zauna a gefen da nake kwanciya.

Kafin na yi magana ya kashe wayar ya ajiye a kan durowar gefen gadon.

Ya juyo ya kalle ni. Ya ce "Ya jikin dai?"

Na amsa da ce wa "Na ji sauki Alhamdulillah!

Muka kalli juna abin mamaki sai ban ji wannan dinbin soyayyar ta taso mini mai tsanani ba. Amma kuma duk haushinsa da nake ji bai saka na ji na tsane shi ba illa iyaka soyayyarsa ta fara samun tawaya.

Ya janye idanuwansa dan kauce wa kallon da nake binsa da shi wanda ya kunshi al'amura masu nauyi.

Ya numfasa ya ce "Wannan kallon fa? Tunda na dawo kike ta tsare ni da idanuwa, ya ya haka ne, gabadaya a kwanakin nan bana gane yadda kike mu'amala da ni fa!

Na sake zuba masa ido kirr ban tanka ba.

Ya kufulo ya ce "Oh yau ai Basma ta zo gidan. Komai kika yi babu laifi, sai dai na fada miki duk abin da kuke nufi nima na shirya masa."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Na hadiye takaicinsa na ce "Ai na ga alamun hakan tun dazu".

Na gyara zama na ce "Da na ga sako daga H.M.H. store sun cire kudi daga asusun ajiyarmu na zaci ma kayan dubiya ka siyo mini, na adana yunwata ina dakon ka sai kuma na ganka hannu na dukan cinya".

Ya kadu kwarai da gaske da furucina. Ya ce Bilkisu ke nan. Dama an sha fada mini zan fuskanci haka, sai ga shi kuwa na fara ga ni. Ki fito ki ce kin gamsu da hudubar da take yawan fada miki na ce wa ki daina hada aljihunki da nawa saboda naki mai nauyi ne."

Karon farko da ya fadi hakan ban ji gabana ya fadi ba, ban kuma ji fargabar bai fahimce ni daidai ba. Na yi gajeran murmushi tare da ce wa "Ba dan nawa yafi nauyi ba ne. Watakila tana jiye mini tsoron faÉ—awa yanayin nan na k'ato da shan bugu kura da cinye wa."

Ya zuba mini ido sosai cikin son ya fahimci azancina.

Nima din na zuba masa dukkan nawa idanuwan cikin rashin tsoro ko zullumim kada ya yi fishi.

Ya ce "Kina nufin ina shanye romon wahalar ki ne Bilki?"

Jin ya fadi Bilki nasan yana cikin rashin sukuni.

Dan haka kaitsaye na ce "Kusan hakane domin kuwa kana yiwa wadanda basu cancanta ba hidima da wahalata. A tunanina baka da son zuciyar da zaka yi haka, sai dai da yake kai din dan Adam ne kuma jinsin namiji ba abin mamaki bane idan ka yi fiye da hakan."

Ya fusata ya mik'e ya dauko walet dinsa ya fito da ATM dina ya jefo mini. Ya ce ",Ga shi nan matukar ina shakar numfashi ba zan sake taba abin da yake na ki ba ne. Mafi munin kuskurena shine yadda da na yi imanin zan yi yadda nake so da abinki kaitsaye domin na dauka mun riga mun zama abu guda. A sadda nake da dama ba abin da ban miki ba mai asalin tsada ba garabiti irin wanda kike yi mini ba."

Na kada kai na ce "Tafi nono fari domin kuwa ban yi lalacewar da zaka yiwa budurwa hidima da abin da yake nawane ba alhalin ni tuni ka y'anta kanka da ga yi mini hidima kowacce iri tun shekaru masu nauyi da suka shud'e."

Ya fusata ya ce "Tabdi jam! Wato halittar mace da gori take da kuma manta alheri take!

Cikin nutsuwa na ce "Namiji kuma da son kai da zalunci yake ba.! Na fada a matukar zafafe.

Ganin na fara fusata sai ya sassauta fishin ya ce "Dan na yi aure a yanzu ai na yi miki adalci. Shekaru sha biyar zuwa sha shida dan zan k'ara aure sai ya zama zalunci?"

Na hadiye na ce ba zalunci bane. Amma a sanin da na yi maka baka da lafiyar da zaka iya gamsar da mace biyu. D'ayar ma ya ya ne? Sannan aljihunka ma bai cudi bayanka ba."

Nan da nan ya muzanta ya ce "A da duk hasashe kike yi da tsananta bin diddigi a kaina. A yau kuma ina mai tabbatar miki ina neman aure, wanda zai tabbata a kusa kusa".

Na kafe shi da kallo mai tsananin gaske murya babu amo na ce"Sai yanzu ne ya kamata na sani Sahal?"

Kaitsaye ya ce "Tunda ban bari sai bayan na yi auren kika ji ba, ai kuwa na mutuntata ki"

Gabana ya fadi sosai murya na rawa na ce "Tsakanin ka da Allah kana da lafiya da halin kara aure?"

Ya murmusa ya ce "Ba ki da hurumin wannan tambayar. Domin ba matsalar da ta shafe ki bace "

Murya babu amo na ce To ba zan lamince na cigaba da zama a gidana alhalin ka samu sukunin bani muhalli ban sani ba".

Ya girgiza kai ya yi kwafa. Can ya numfasa ya ce "Kamar d'azu na na yi ta jaddada miki cewar duk abin da kuke nufi da ni na shirya masa. Kin sani Abida ma ta hak'ura ta bar ni da dukkan nak'asun da take jigina mini, bare kuma yar karere irin Basma!

Na hassala na ce "A da ba Sahal, a lokacin ina sonka, ina ganin adalcinka".

Ya rausayar da kai ya ce "Shike nan lokaci zai fayyace komai."

Daga haka ya juya ya yi kwanciyarsa cikin nutsuwa.

Yayin da ni kuma hawaye ya balle mini. Na kasa daina kukan nawa duk da marar sauti nake yi. Irin na sharbe mai sanya nauyin kirji.

Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, ya fara sakin munshari tabbacin yana cikin nutsuwar zuciya.

Na zura masa ido sosai. Ina ayyana al'amura masu yawa a kansa, sashin zuciyata har ce mini yake yi na dauki filon na danne masa kansa har sai ya daina numfashi. Nan da nan na zabura na mike ina ta'a'uziya tare da istigifari. Ina neman a tsare mini zuciyata da hankalina mummunan kishi da tunzurin zuciya mai sawa a halaka a kuma kafirta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Na doshi kofa na fice na doshi dakina. Na zauna a bakin gadon. Idona a bushe yayin da da zuciyata ta yi nauyi kwarai da gaske.

So nake na yi kuka ko zan samu sassaucin yadda nake jin kishi na babbako mini tare da bin dukkan ilahirin jikina yana soke ni.

A fili da kuma k'arfi nake ambaton Innalilahi wa inna ilaihir rajiun.!

Duk yadda na kunna a c da fanka basu yi tasirin da zufa ta daina yanko mini ba.

Na dinga safa da marwa a tsakiyar dakin.

Ina ta kokarin karfafawa kaina guiwa ta hanyar yin tunani na gaskiya tare da son na tursasa zuciyata k'aranta mata damuwa. A fili na ce "Bai kamata na bari k'aramin tashin hankali ya sake tarwatsa zaman lafiyar zuciyata ba.

Domin na yi amanna na shiga wanda ya wuce shi tsanani. Abin da ya faru a gidanmu ya fi k'arin aurensa firgici a gare ni. Ya kuma wuce, duk da ba'a samu daidaito ba har yanzu. Dan haka ba abin da zan ga ni na jarabawar rayuwa yafi wanccan al'amarin tashin hankali.

Tunda kuma har zuciyata bata buga ba a wanccan lokacin, to kuwa ba abin da zai sa na bari ta buga a yanzu.

Na fada bandaki na doro alwalla. Sallah nake yi ba tare da wata nutsuwa mai yawa ba. Amma a kalla na yi raka'a goma. Na kasa addu'ar komai. Kawai nasan ina ta ambaton Innalilahi wa inna ilaihir rajiun, Hasbinallahu wa niimal wakil.

Har tsakiyar dare ina zaune kan sallaya ina ta lazimin da ya zo bakina. Yi nake yi domin na samu sukunin zuciyata domin na kasa rokon Ubangiji komai. Sai goshin asuba barci ya fara fizgata, na sanya jarumta na tashi na sake alwalla dan na wartsake sosai, ban zauna ba sai da na sallaci asubahi.

Na samu saukin tunanin da ya yiwa kwakwalwata k'awanya. Amma gabadaya na sake tsunduma wajen son sanin inda zai ajiye amaryar da ya kudiri niyyar yi.

Zuciyata ta harba da tsananin gaske a dalilin na tuna muna daf da kammala gini. Tabbas fili nasa ne sai dai kuma kaso casa'in na kudad'en da aka yi ginin daga lalita ta suka fito, filayena guda muka siyar aka fara aikin ginin, bayan kudin sun kare, kullum cikin zuba kudade masu nauyi nake har muka kai da fenti da k'ananun aiyuuka ne suka yi saura.

Tirk'ashi na furta a fili tare da hasashen girman dabarwar da take gabana.

Da na ga kaina ya dau caci sosai sai kawai na hau hailala a fili.

Cikin ikon Allah sai nutsuwar zuciya ta same ni domin akan sallaya barci mai nauyi ya yi gaba da ni .

Na ji dad'in barcin nan domin rabon da na yi barci mai nauyi kuma cikin nutsuwa na mance. Ban farka ba sai wajen tara saura na safe. Na yi matuk'ar mamakin yadda ko motsin shige da fice yara ban ji ba. Tabbas na tabbatar sun shigo, Amrah da Alti ne zasu hanasu tashina. Na sa ni kuma ba k'aramin lallaba Farha aka yi kafin ta yarda ta tafi ba tare da ta gan ni ba.

Na yi salati na yunk'ura na fad'a bayi

Kaitsaye wanka na yi. Na fito na shirya cikin riga marar nauyi. A haka Alti ta turo kofa a hankali ta leko, ganina a tsaye har na yi wanka ya sanya ta shigo dakin gabadaya. Da kuzari tare da walwala ta ce "Kin tashi Mahmah? Na ji dadin barcin nan da kika samu. Da kyar dai yarki ta yarda ta tafi makaranta".

Na murmusa na ce "Farha duniya. Ni da kaina na tabbatar ba karamin wahalar da ku ya yi ba."

Cike da kulawa ta ce "Na miki kunun gyada. Na soya miki awara ne? Na dafa miki tun dare na saka a firij".

Na murmusa na ce "Sannu da kokari Alti. Allah ya taya ni gode miki".

Walwalar fuskarta ta karu. Tare da ce wa "Ameen Hajiya Mamah. Allah ya ninka miki walwalar zuciya da ta fuska."

Na amsa da fadin "ameen ameen, zan yi walaha yanzu, wajen goma saura sai ki fara soyawa".

"To "

Ta fada da azama sannan ta juya ta fice tana fadin "Alhamdulillah!.

Bayan na kammala karyawa da kaina na kwashe kayan na kai kicin. Na zauna a falo yayin da Alawiyya ta shiga dakina dan ta tsabtace. Gabadaya tamkar wanda aka cire mini Sahal a raina domin ko ganinsa ban ji ina son yi ba.

Na cigaba da zama a falo har ta kammala ta bazawa dakin daddan turaren air freshener.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Jimawa kadan na koma dakin, akan kafet din na zauna ba akan gado ba. Sai dai na dauko filo guda daya daga kan gado.

Haka kawai nake na jin d'okin cigaba da hakaito rayuwarmu ta baya dan na sake nisanta kaina da tunanin Sahal da kudirinsa na karin aure wanda yake ganin zai iya muzanta ni matukar na ce zan yi adawa da hakan.

Na numfasa na janye filo na jingina da shi.

Na lumshe ido na sake kutsawa tiryan tiryan ina hakaito abubuwan da suke zaune daram a kwakwalawata da wanda bayyanasu zai zama darasi da gargadi.

Tunda na ga Abida ta hau nazarin karatu ya sanya na mike na shiga kicin dan na dora mana abin da zamu ci domin ba zata sake yi mini magana na har sai ta kammala al'amuran gabanta.

Washagari ta juya Katsina ta zarce kaitsaye.

A lokacin goyon Yaya Faruok Sahal ya samu budi sosai. Dan har Umra ya biya mana ni da shi tare da yaranmu gabadaya. Haka ya biyawa iyayensa duk da sun je. Bayan shekara da zuwanmu kuma ya biyawa su Baban Zaria da matarsa takwarar Amrah.

Gata da tattali ba wacce bai mini ba, komai zai ajiye mini tamkar ba da kudi yake siya ba. A haka na yaye Faruk tuni kuma Amrah ta shiga makaranta.

Hankalina ya koma kan rubuce rubuce akan abubuwan da suke Gina ciki. Misali zan dauka Apple na yi rubutu akansa da irin alfanunsa a jikin Dan Adam da sinadarin da yake bayarwa da nauin mutanen da suka fi bukatarsa a jikinsu. Wani lokacin Kuma sai na yi bayani akan mangwaro. Duk Kuma a kafar sadarwa ta Facebook tunda itace a lokacin kawai. Kafin na ankara sai na sake tara mabiya. Ina kuma sake fadada business dina na snacks.

.

Gabadaya na zama babbar mace da ilimi da gayu suka ratsa tunda miji ya tsaya mini sana'a kuma ta yi k'arfi. Iyayenmu kuma masu hali don ko da suka aurar da mu hidima suke yi mana kan hidima basa saka ran mu yi musu. Sai dai muna yi don neman albarka. Na zama big madam mazaunai sun fito sosai Dan haka na bude ta kasa na bada shape mai daukar hankalin masu kallona. Fata tana samun mayuka da sabulan da suka dace da ita kwarai da gaske. Haka nan kamshina na mussaman ne domin kuwa turare designer nake amfani da shi. Wadannan dalilai suka sanya na sake makalewa a zuciyar Sahal yana al'amarin kasancewata matarsa, shi da kansa yasan nafi dacewa da manyan masu kudi da suka zarta shi komai da koami dan kuwa shi din gabadaya nai bani shekaru uku cikakke ba ta bakin Abida. Sai dai har wannan lokacin da muke shekaru biyar da aure ba zan ce ina cikin rashin nutsuwa a dalilin aurensa ba. Kawai matsalar daya ce. Tabbas bashi da sha'awa mai yawa, wannan ne kawai tasgado domin ina kwaruwa sosai. Amma ba yadda na iya dan haka na saka rashin samun biyan bukata shine jarabawar aurena. Kuma abin mamaki zaman namu na nisa al'amarin na sake yawa. Dan yanzu kam sai mu kwashe kwanakin wata bai nema ba. Sai dai idan ya ga mutsumutsuna ya yi yawa zai yi romancing d'ina har sai na samu na fitar abin da ta takura ni. Na fara tunanin ko lafiyar makarfafarsa ce ta yi kadan. Na fara nazarin abubuwan cima da zasu taimaka masa wajen motsa masa sha'awarsa. Kullum cikin nazari tare da gabatar masa duk wani nauin abinci ko kayan marmari da suke taimakawa amma babu wani sauyi. Na fara magana da likitoci ana rubuta masa magani amma kuma da ya sha daya biyu to ya bar mini su kenan. A wanccan lokacin da shekararuna basu da wani yawa sai nake jin tsoron irin na gagajiya wanda ake zubawa miji a lemu ko a shayi don ina jin tsoron kada ya gane ya ce asiri nake yi masa.

Ga shi al'amarin mai matukar nauyin ka tattauna da wani ne. Kan dole na hakura nake ta kokarin na danne abin tunda haka kaddara ta zaba mini.

✏️

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Contact me 08032773332 what'sapp only*

*For all your kayan mata gangariya*

*Bridal package*

*Maijego package*

*Uwargida package*

*Bazawara package*

*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*

*Ciccibin garari*

*Tsumin saiwowi*

*Hakkkn daka emergency*

*Gumbar ridi*

*Gumbar saiwowi*

*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Yaya Faruk ya isa shiga makaranta aka saka shi wacce Amrah take yi.

Har zuwa lokacin kuma Abida bata yi aure ba. Watanni uku da kammala resident dinta a jamiar kasa ta Lagos (Uni Lag).

Burinta kuma ta wuce da karatunta har sai ta zama kwararriyar likitan mata.

Ta fada mini ta riga ta gama cike ciken tafiya kasar Uk dan ta zama gynecologist, sai komai ya kankama kafin ta bari gida su sani dan kada ma a hana ta tafiya, domin matukar ta samu gurbin karatun to ba za'a hanata ba tabbas.

Bayan haka kuma ta nemi gurbin karatun a jamiar Ahamadu Bello, ma'ana raba kafa ta yi, tsakanin guda Nigeria da Kasar England.

A matukar sanyaye na yi mata murna da fatan alheri, tare da addu'ar Ubangiji ya zaba mata mafi alheri.

Tana shirin shiga shekaru ashirin da bakwai amma bata maganar aure sai dai neman ilimi tamkar alhuda alhuda.

Autar gidanmu gabadaya ta kammala sakandire a bana. Bata damuwa da yadda aka aurar da kannemu ita tana zaune.

Da yammaci ina zaune a falo ya dawo, na tashi na karbi jakar hannunsa tare da yi masa barka da zuwa.

Ya jani jikinsa yana shinshinar kamshina jikina tare da tab'a gashin kaina da ya sha gyara yake tufke cikin katon ribbon.

Ya dan shafi mazaunan da suke tsole masa ido da tare da yin spanking dinsu. Maimakon na ji dadin hakan sai takaici ya nemi taso mini domin daga hakan shike nan. Ba komai zan samu da ya wuce hakan ba.

Kaitsaye dakinsa muka wuce na adana masa jakar na ce "Wanka zaka fara ko abinci?"

Ya ce "Bari na watsa ruwa tukun".

Na juya tare da ce wa "To a fito lafiya".

Na ja masa kofar na nufi kicin na shiga fito da abincin ina shirya masa a dining table.

Tuni mun bar gidan da muka fara zama da muka dawo Kano.

Gida mai kyau na bada labari ya kama haya, kuma na shekaru uku ma ya biya, bamu jima da tarewa ba. Shi kuma cikin kaddararsa ko maganar ya sayi gida ba ya yi, don na tabbatar zai iya siyan gida ko da ba irin wanda yake hari ba. Ko maganar ya sayi fili na yi masa sai ya ce "so yake ya samu kudin da zai saya a unguwa mai daraja. Tunda ya siya a katsina sannu a hankali ma zai siya a Kano.

Ni kam jinsa nake yi, domin ban gamsu da dabararsa ba. Ni a tawa dabarar ya siya a koina mana, sannu a hankali idan ka sake samun wani kudin sai ya siyar ya hada ya sayi irin wanda yake so, domin na tabbatar samun irin wanda yake so a cikin manyan unguwannin birnin Kano zai yi masa wahalar gaske tashi guda.

Ya fito sanye da jallabiya ruwan toka sai kamshin turaren() ke tashi. Cikin nutsuwa nake zuba masa. Na zauna yana ci yana yi mini hirar yadda ma'aikatarsu ta Nigerian airways kullum take fuskantar kalubalen rashin samun tallafin da ya dace daga gwamnatin tarayya.

Na zuba masa ido na ce "Ni fa na dauka gwamnatin na bada kulawa ta mussaman ga ma'aikatar tunda harkar sufurice ta kasa da kasa "

Ya ce "Hmm al'amarin dai sai kurum cin hanci da rashawa ta shiga ko ina. Ko muma da aka buda mana muke samu ai kinsan hanya ne tunda shugaban ma'aikatar gabadaya abokin Baban Mashi ne. Idan ba haka ba ai albashina bai isa komai ba.

Duk wata ma'aikata ko kamfani mai muhimmaci gwamnatin nan sai ta yi shagulatin bangaro da shi har sai ya durkushe ko sai sun cefanarwa yan kasuwa sannan hankalinsu yake kwanciya."

Na numfasa na ce "Baban Amra ya kamata ka yi himma ka mana gini ka kuma saka hannun jari a kamfononi domin tsaron ko ta kwana. Ranar da aka ce babu shugaban wajen fa?"

Ya ce"Kin fini tsinkaye Billy! Zan fara dan gaskiya albashi kadai ba zai rike mutum ba".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Yana kammalawa ya tafi dauko su Amrah tunda sai biyar da kwata suke tashi a dalilin har da islamiya a makarantar suke yi.

A daren wannan ranar bana mantawa da kaina na ballo masa magani da ruwa ya karba ya sha bai yi musu ba. Sai dai kuma yana gama sha ya kwanta barci mai nauyi ya yi gaba da shi. Sai da asuba ya bukace ni, ya yi iya abin da zai yi, ya samu gamsuwa shike nan ya tsallake ya yi wankasa ya hau shirin tafiya ofis. Ya kalle ni ina kwance tamkar ruwa ya cinye ni domin ni gabadaya ban ma gane komai ba. Wani irin abu na mamayata tare da tambayar kaina shin ita mace bata da hakkine a wannan fagen? Komin bukatarta matukar namiji baya da muradin haduwar sai dai ta yi hakuri ta yi ta fama da ciwon zuciya da kukan cikin dare?

Haka nan ita mace bata da hakkin idan an hadun a tabbatar an gamsar da ita?

Namijine kadai yake da hakkin ya gamsu a cikin al'amarin?"

Ba ni da mai warware mini wannan tambayoyin, amma kaina ya yi matukar daukar caji.

Ya ce "Ba zaki tashi ki shirya yaran ba ne?"

Cikin dabara na dauke hawayen idona. Cikin nauyin jiki na sauko na nufi bayi. A gurguje na yi wanka. Na fito na saka riga na fita kicin ganin har shida da rabi. Kaitsaye na dora doyar da na fere tun daren jiya.

Kafin ta dahu na je na tashe su, na yi musu wanka. Na shirya Yaya. Yayin da Amrah take shiryawa da kanta. Na tafi kicin bayan na ce su yi sallah.

Na fasa kwai na hau soyawa. Na zuba musu a lunch box dinsu yayin da na hada musu cornflakes suka sha. Shi kuma ganin zasu makara sai na shirya masa doyar da tea a basket, ya karya a ofis.

Ya fito yana daura agogo ya ce "Da alamun idan na tsaya karyawa zamu yi latti da yawa.

Ganin na fito masa da basket ya sanya ya yi murmushi ya matso kusa da ni ya karba ya jani jikinsa ya yi mini sumba a goshina da kumatuna.

Ya ce "Allah ya yi miki albarka. Daga haka ya tisa yaran suka fice. Na bisu bakin kofar falon ina yi musu addu'ar dawowa lafiya.

Ba wani kuzari na hau aikin gyara kicin, din, sannan na dawo falo na gyara. Yau kusan sati kenan da tafiyar yar aikina garinsu akan Babanta ba lafiya. Kafin karfe tara na gama komai na kintsa ko ina har dakin barci da na su Amrah.

Sai da na yi wanka sannan na karya. Na yi wanka na shirya so nake na yi rubutu akan tasirin da garin k'irya take da shi da yadda ake sarrafata ta yiwa mata maganin dukkan naui'in cutar daji(kansa). Tunda kan kansar mama, ta mahaifa, ta fata da dukkan naui'in ciwon daji. Amma zuciyata babu sukunin yin rubutun domin matsalar da nake fuskanta kullum sake mikawa take yi, ba ni kuma da halin da zan yi korafi ko na tattauna da wani tunda a wanccan shekarun abin kunya ne mace ta bude baki ta yi irin wannan korafin sai idan tura ce ta kai bango.

Kan dole na kwanta ina fatan na samu barci ko na huta da kunan rai. Na jima ban samu barcin ba, sai dai da ya sure ni ban farka ba sai wajen karfe uku.

Da azama na duro daga kan gado bayan na kalli agogon bangon da ya fada mini karfe uku saura mintina takwas kacal.

Da na idar da azahar lazimi na zarce da yi har sai da na sallaci la'asar. Sannan na shiga kicin dan yin abincin da zamu ci.

Domin na riga da na saba girki daya nake yi.

Kwanaki suka yi ta shudewa suna haifar da makwanni, da haka a samu kwanakin wata, watanni su haifar da shekaru. Rayuwar aurena da na yi a Kano itace rayuwa mafi dadi a gare ni, domin cikin nutsuwa na yi zaman. Miji na cikin wadata, shi kuma bai mini kwangen komai ba. Ba ruwansa da samun kudina, baya kuma taba sakar mini wahalar gidansa. Komai yi mana yake yi ni da yara a wadace, ko hidimar bikin dangina ne ya taso zai bani gudunmawa mai nauyi, shima kuma zai je ya bada nasa. Dan haka kowa yake mini kallon na taki sa'a. Don hatta Abida ta yi matukar mamakin yadda Sahal yake da halin girma. Gaskiya ba ni da matsalar zahiri da za'a iya nunawa. Domin ni kaina da ace yadda yake sauke nauyin ciyarwa da tufatarwa tare da kula da lafiya haka yake sauke hakkin auratayya da na ce ba ni da matsalar komai a aurena.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Amma da yake dukkan aure da irin nasa kalubalen ni cikas din nawa mai girmane, dan har rayawa nake yi inama a abinci nake da tasgado tunda ina da kudin da zan siya mana abinci.

Kan dole na cire matsalar a raina tunda tana da nauyin a fayyaceta na mayar da hankalina kan abubuwan da nake samunsu.

Na tara kudade sosai a asusna domin kwarai da gaske sana'ar bakery tana kawo mini kudi mussaman shekarun baya da sana'ar bata yi yawa irin yanzu ba.

Mun yi murnar cikar aurenmu shekaru takwas (wedding anniversary). Kwanaki uku a tsakani muka tashi da wani tashin hankali na rushe kamfanin Nigerian airways aka kuma sallami ma'aikatan daga aiki babu garatutu bare a je ga batun fensho.

Mun shiga rudani kwarai da gaske.

Amma da yake yarda da kaddara wajibine a sharadin zama mumini. Muka hakurkurtar da zuciyarmu mu karbi wannan kaddara da hannu biyu.

Na taka muhimmiyar tawa wajen kwntar masa da hankalinsa a wannan lokacin.

Haka aka yi ta zuwa mana jaje tare da fatan Allah ya kawo masa wata mafitar mafi alheri.

Bamu shiga matsalar a farko ba domin shi mutum ne mai tara kayan abinci da yawa sosai, sannan a duk sadda zan yi cefanen kayan su samosa, spring rolls, meat pie, pizza da sauransu, cefanen ne na sosai dan haka a ciki muke diba mu yi amfani a gida.

Kudin hayar gidane ya nemi daga mana hankali domin mai tsadane sosai, amma dana runtse ido sai kawai na cire a asusuna na biya. Farinciki kan farinciki Sahal ya yi tare da yaba mini. A yanzu da yake zaman gida komai tare muke yi, sannan ya ninka soyayyarsa a gare ni tare da kulawa da yaranmu, zai kaisu makaranta, idan lokacin tashi ya yi zai je ya debo su. Baya wani fita ya jima sosai.

A rubuce rubucen da nake yi a kafar sadarwa ta Facebook ya ja hankalin mahukuntan hukumar lafiya ta duniya(W.H.O.) Suka gayyace ni ofishinsu, suka tattauna da ni, suka bukaci sanin matakin ilimina. Na tabbatar musu na yi karatuna na firamare har zuwa matakin digiri. Sannan na karanci ilimin abincin da ya dace da kowanne rikunin Dan Adam.

Suka ce washagari na koma tare da dukkan takarduna.

Na fito na tarar da shi a mota.

Na shiga ya ja muka tafi.

A hanya ya kalle ni ya ce "Ya ake ciki?"

Da walwala na ce "Sun bukaci na kawo credentials dina gobe".

Ya fadada murmushinsa ya ce "Alhamdulillah! Ina ji a jikina Ubangiji zai sake kawo mana dauki"

Na taya shi murna tare da ce wa "Allah ya biya bakinka".

Washagari tare muka fita da yara. Sai da muka fara ajiye su sannan muka wuce.

Cikin sa'a kuwa bayan mun shafe awanni biyu na fito dauke da takardar daukata aiki na tsawon shekaru uku. Abin burgewa sau biyu zan fito a sati, sai na yi musu rubutun da zasu dinga dorawa shafinsu cikin harshen Hausa da turanci sau daya a sati. Ba karamin murna muka yi ba domin albashina mai tsoka ne matuka da gaske.

Dan haka bamu wani shiga zullumin rashin aikinsa ba. Ba wani abin da ta canja mana.

Sai dai shi tunda mai son ya yi alherine sai ya takura, duk da ban shata masa layi da komai nawa ba. Ko biyan kudin makarantar yara na shekara na biya musu dan haka komai lafiya lau.

Watanni takwas da rashin aikin Sahal. Mun je hutu gida Funtua ni da yara zamu yi sati guda, domin na kwana biyu ban je ba.

Na tarar da Abida da su Baba ana artabu domin kuwa daga Baba babba har Baba karami sun hade mata kai sosai akan ba yadda za'a yi su bari ta tafi uwa duniya babu aure da sunan zurfafa ilimi. Dama ace digirin farkone da sauki, amma yanzu tana da aikinta tunda likitace a babban asibitin Funtua tun shekarar da gabata take aikin. To matukar sun isa da ita aure suke so ta yi idan tana da auren ta tafi birnin Sin ma ba Ingila ba.

Ba Abida ba, ni kaina mamakin yadda Baba babba ya shafawa idonsa toka ya yi nake yi, domin kuwa kowa yasan baya iya takure ta. Watakila kuma ya yi hakane don Baba karami ya kafe ba zata tafi uwa duniya babu aure alhalin tana da shekaru ashirin da bakwai tana shirin cika da takwas.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Cikin fishi sosai na tarar da ita, bata shiga shirgin kowa, kullum tana dakinta, ruwan shayi kawai take sha. Amma ganin Amrah yasa ta dan sauko take hira da ita.

Yanayin da take ciki sai ya sanya ban ji dadin hutun ba. Domin tun filazal ita da Yaya Munira sune cikon farincikina a gidan, nafi shakuwa da su akan yayan mahaifina.

Tun Mami na mini sababi har ta hakura ta kame bakinta mussaman da a yanzu duk cikin yaranta babu wanda yake gatantata Irina. Yaya Sulaiman ne yafi ni dama a cikinmu shi kuma ba'a kasar yake ba, yana Germany. Tunda ya kammala karatunsa ya zama likitan ido gwamnatin Kasar Germany ta rike shi na shekaru uku dan ya yi mata aiki. Amma ya dawo sati hudu da suka shude, dan haka zuwan nawa ma har da yi masa barka da zuwa. Dan da ya kammala wa'adin shekaru ukun sun so ya sake zama amma ya bijire tunda ya nemi aiki a nan Nigeria. Ya kuma samu da gwamnatin jihar Katsina. Yana cikin likitocin asibitin cikin gidan gwamnatin Katsina. Haka nan Yana da ofis a cikin babban asibitin Katsina.

Dan haka idan zai mata aike kudi yake turo mata.

Ni kuwa komai take so yi mata nake yi, haka bana raba ta da kayan ciye ciye kala kala, domin a kai, akai akai nake yin samosa da da meat pie na aiko mata ta saka a firij tunda a wanccan lokacin babu matsalar rashin wuta a Funtua. Na dauke mata gudunmawa, haka nan ina mata dinkuna sosai. Ina hadawa na yi musu da Momi amma dai na Mami ne sha kundum, dan haka na samu sassauci sosai a wajenta, ta daina tsananta mini akan sha'anina da su Abida, ta daina mini shagube, ta daina bagarar da lamarina. Tunda ya gamsu lamarinta shine gaba a wajena har mahaifina kuwa.

Daren ranar da muka je muna dakinmu na sashen Mami.

Na kalli Abida na ce "Yanzu Abida menene abin fishine har haka? Ki huce ko kuma ki fitar da mijin tunda idan har mijinki zai barki ai kuma ba sauran ace za'a hanaki yin abunda kike so".

Ta ja k'aramin tsaki ta ce ",Ban samu wanda nake so ba. Ni dai kawai su Baba sun takaice ni. A wannan marrar wanne namijine zai yarda da ga yin aure na tsallake na tafi na bar shi? Su sun kasa fahimtar aure fa ba wajibi bane matukar mutum zai kame akan me za'a mini dabaibayi irin hakane?"

A tausashe na ce "Suna son ke ma ki yi naki iyalin, aure ai sutura ne, rufin asirine ta hanyarsa kadai zuria take yaduwa" .

Ta kaurara murya ta ce "Kun haifa mini, naku sun ishe ni".

Na ce "To tunda kin samu a A.B.U din ki yi anan din mana"

A takaice ta ce "Nan din ma sun ce sai na tsayar da miji sannan zan yi. Ni kam gaskiya an takure ni, ni fa jina nake yi dakila ce don kuwa yana wahalar gaske na ji sha'awa bare har na gundura da zamana haka. Menene a cikin aure ne ban da jidali, haka kawai ina cikin zamana na jefa kaina a garari. Ba dama kuma ka zo gida a saurare ka sai dai ace ka yi hakuri, suma hakurin suke yi. "

Dariya ta so subuce mini wai tana zaton ita dakila ce. Amma na maze domin a halin da take ciki idan na yi kuskuren yi mata dariya zamu hau sama mu fado ne.

Na cije na ce "Ke ba dakila ba ce Abida! Dan dai kin kulle zuciyarki ne akan rijalu amma da zarar kin samu wanda ya yiwa zuciyarki kutse na ban mamaki zaki tabbatar ke din ba haka kike ba"

Ta zuba mini ido ta ce "Sannu Maigado masaniyar komai akan mace da namiji".

Na tuntsire da dariya domin gabadaya a kufule take, kuma so take sai na gasgata ita bata cikin jerin mata masu sha'awa.

Washagari har azahar ban ga Yaya Sulaiman ba. Na kalli Mami da muke zaune a falo na ce "Yaushe zai zo na gan shi ne? Na kasa samun wayarsa".

Mami ta muskuta ta ce "Ina ganin gobe alhamis su dawo tare da Babanku".

Na ce "To Alla ya kaimu ya kuma kawosu lafiya".

Ta amsa da "ameen".

Washagari kuwa tare da Baba karami suka dawo. Na jima ina karewa Yaya Sulaiman kallo domin ya zama zabgegen saurayi na k'asaita .Kammanina da shi sun sake bayyana karara. A tsaye yake cak tamkar dai Yaya Asad, banbancin yafi Yaya Asad haske. Ba farine kamar ni ba, amma kuma ba za'a shi a sahun bakake irinsu Baban Bilkisu ba.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Hoton fuskata na ga ni a fuskarsa sai banbancin gemu da kuma hasken fatata da sauran abubuwan da zasu banbanta jikin mace da na namiji. Amma tabbas muna matukar kama da juna.

Na tafi lissafin shekarunsa domin shekaru shida ya bamu. A lokacin shekarunsa talatin da uku. A wanccan lokacin gani ake yi ya zama tuzuru domin dukkan sa'aninsa da ma wanda ya girma sun yi aure har sun haihu.

Tun filazal Yaya Sulaiman dan gaye ne kuma dan bokone na gaske. Amma da ya dawo na fahimci ya samu cigaba mai yawa, ya goge da ilimi da kuma wayewar rayuwa.

Sadda suka iso ni da Abida muna farfajiyar harabar wajen adana motoci, gidan Yaya Faruk zamu je yini.

Da girmamawa muka gaida Baba karami.

Ya kalli Abida ya ce "Maryam kin huce, kin daina fishin?"

Ta dauke kai i tana fishi fishi kunya kunya ba tare da tanka ba.

Ya ce "Ato gara kisan matakin dauka dan kuwa tabbas babu maganar wata makaranta kuma sai a dakinki. Ke ko sha'awar yanuwanki da kike ganinsu da yaransu ba kya ji?"

Da shagwaba ta ce "To Baba sun duk sun samu mazan ni kuwa fa?"

Ya zabura ya mata dakuwa tare da yin kanta zai kai mata bugu.

Ta yi maza ta goce ta falfaala bata tsaya ba sai da ta bada tazara, sannan ta tsaya tana dan haki.

Ya ce "Mutane nawa suna zuwa wajenmu da sunan sun gan ki suna so, kina yin tsallen albarka kina fadin ba da yawunki suka zo ba?"

Ta kasa amsa masa. Ya yi kwafa ya ce "wannan karon kam ko ni ko ke na gaji da iyashegen ki, inma jinnul ashuq ne akanki zasu ci iyayensu dan kuwa na shirya yin arangama mai zafi da su".

✏️

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Daga ni har Yaya Sulaiman muka kwashe da dariya domin yadda Baba ya furta jinnul ashuq akwai ban dariya kwarai da gaske, yayin da ita kuma ta sha mur.

Haka muka tafi gidan Yaya Faruk tana ta gungunin ita bata da mashanshani, don kuwa duk wanda ake lissafin sun zo da sunan suna sonta ba jarumai bane ba kuma mijinta a ciki. Don ta yi imani da akwai mijin da kaddara ta zaba mata a cikinsu da tuni ta yi auren ai.

Muka isa gidan Yaya Faruk muka tarar yana shirin tafiya gidan gona. Ya dinga marabtarmu cikin barkwanci.

Haka ma matarsa domin a yanzu kam gaisuwar girma da arziki muke yi ta daina tsananta mini.

Ya zauna ya ce to ku gaisa da matar gidan ku sha ruwa sai mu tafi gidan gonar mu yini a can ko sarauniyar shaiba?"

A duk sadda ya ce hakan har cikin raina nake jin sunan. Tare da tasowar al'amura masu yawa a kansa.

A sanyaye na ce "To Yaya Faruk".

Ya saka hannu ya dauki mai sunansa da ya yi barci tun a hanya. Yana fadin my name sake tashi ka ga Yaya Faruk senior."

Na murmusa ba tare da na ce komai ba.

Ya kalli Abida ya ce "Autar momi wai har yanzu ba ki huce ba ne?"

Ta sake zumbura baki amma bata tanka ba.

Ya sassauta ya ce "Indai kin san akwai wanda yake sonki ki ba shi dama mana, ba fa wacce su Baba suka daga mata kafa irin ki. Ina jiye miki kada ki yiwa kanki sanadin da zaki ji sun bada aurenki ga wanda suka ga ya dace"

Ta murmusa ta ce "Ba maganar a mini auren dole Yaya Faruk. A wannan karnin? Da ilimina?"

Ta girgiza kai tabbacin ba mai yiwuwa ba ne.

Na zuba mata ido ba tare da na furta komai ba. Wato Abida asalin feminine ce.

Ya Farook ya kalle mu ya ce "Rigunan jininku sun mini kyau. Ban cika ganin abayas irin haka ba anan".

Abida ta ce "Bilki ta siya mana a wajen Umm Aslan &Asalah. Egyptian abayas ne kasan sune original. Ya ce gaskiya sun yi kyau sosai nima zan baki ki siyowa Jamila irinsu ".

201121544627 da +2349162662750 Kawai ta tuntube ta a WhatsAp sai ta zaba da kanta idan kun tura kudin, sai na karba muku a Kano tunda anan kayanta suke sauka.

Haka muka rankaya muka nufi gonar ladi farms da kwandon abincinmu matarsa ta hado mu da shi.

Yadda muka zo a motar Abida haka muka shiga ya ja muka yi gaba yayin da ya shiga tasa ya bimu a baya.

Gabadaya gidan gonar ya sake habaka, dukiyar dabbobi kala daban daban a ciki iya ganinka. Haka nan an gyara ta gyra na mussaman domin har zuwa ake yi da sunan yawon bude ido. Sosai ake hada hadar kasuwanci a ciki. Madara da yogurt din da ake sarrafawa a ciki na manyan kudade ne masu matukar nauyin gaske. Hatta kwai a kullum ana diban sama da dubu talatin ban da wanda suka fashe, shiyasa ma'aikatan wajen suma yawane da su tamkar me, an samu cigaba ta hanyar samarwa matasa masu yawa aikin yi

Yaya Faruk ya sake zama babban mutum kudi ya zauna masa duk da shi kadai ne a Funtua cikin yayyanmu. Amma yana cikin daula don idan kana gidansa ma sai ka zaci kana Abuja ne cikin rikunin uguwanni masu daraja.

Duk yadda nasan ladi farms girmanta ya kai kurewa amma a wannan ranar da na shiga cikin shekaru na hankali, ina kuma cikin nutsuwa sosai, na tsorata da irin girmanta da tarin dabbobi da shuke shuke. Don yanzu har 'katon runbun abinci an gina ta yadda ake adana kayan amfanin da aka nomawa a ciki.

Jikin mangwarori suka yi parking muka yi shimfida muka zauna. Gabadaya wajen yabanya ce ga danshin k'asa a dalilin duk safiya da maraice sai an jona tiyo a duk inda aka yi shuke shuke ko inda koriyar ciyawa take.

Duk yadda shekarun nan suke tafiya Yaya Faruk bai canja ba. Zama yake cikinmu a rak'ashe duk mai matsala ta zano masa, shi kuma zai saurare ka da kunnen basira ya kwantar maka da hankali ya kuma baka shawara ta gaskiya.

A yau kam Abida ce ta dinga jero masa laifukan Momi. Ashe duk yadda soyayyar Abida bata boyuwa a wajen Momi yanzu zaman nasu ya fara tsami bisa dalilai guda biyu. Ita Momi aure take so Abida ta yi, dan haka ta matsa lambar sai ta fito da miji, bayan haka mafi yawa bata bari ta yi dinkuna ko saka kayan alatu bisa hujjar wai maza zasu kasa dunfararta da sunan aure tunda suna ganin matsayin aikinta da matsayin gidansu, kaya masu tsadar gaske kuma zasu sake kaita kololuwar

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: matsayi.

Ya yi dariya ya ce "Hakuri za ki kara yi, lamarin iyaye dole a bisu yadda suke so. Sannan ni kaina so nake ki yi auren Abida! Menene ya rage miki ne? Aure kuma shine suturar mace. Duk zurfin karatun da zaki yi, matukar ba ki da aure kin rasa wata kariya ta mutuntaka da aure kadai ke bawa mace shi. Ki nutsu ki sassauta burinki, ba yadda za'a yi ki samu irin teste din ki, domin no body is perfect a cikin wannan rayuwar."

Ba walwala ta ce "Aure lokaci ne fa yaya Faruk. Kuma ni ba wani dogon buri ko wani tsatssauran ra'ayin na dauka ba. Kawai wanda zuciyata ta nutsu ne ban samu ba, amma ko yanzu idan na samu wanda na aminta da shi zan gabatar da shi. Akan me za'a matsa mini har sai na je na auri wanda ba mijina ba ne?.

Muka kwashe da dariya. Na kasa ce wa komai domin yanzu zata sauke mini fishinta da take fama da shi, na sani. Yaya Faruk ne ya ce "Dama ana auren mijin da ba naka ba ne autar momi?

Da dukkan zuciyarta ta ce "sosai ma domin idan na auri wrong person ai ban auri mijina ba domin na fada cikin garari da talajaurar duniya".

Ya gintse dariyarsa ya ce "Da ikon Allah na gari za ki aura albarkacin adalcin da iyayenmu maza suke yiwa iyayenmu mata ba za ki yi aure inda za ki wulakanta ba. Fatana ki kwantar da hankalinki. Ki bude zuciyarki ki fahimci manufar iyayenmu ".

Anan muka yi sallar la'asar.

Wajen karfe biyar sai ga Yaya Sulaiman ya iso akan machine.

Yaya Faruk ya kalle shi ya ce "Baka son yin tuki ne?"

Da walwala ya ce "Da kafata na yi rabin tafiyar.

Sai kuma na hau machine domin daga bakin gate din nan ma shigowa ciki ba karamin tafiya ba ce mikakkiya".

Yaya Faruk ya ce "Ka yi kokari, ka kuma motsa jikinka.

Na kalle shi na ce "Yaya Sulaiman sannu da zuwa dama na k'osa mu hadu".

Ya zauna yana ce wa "Ga ni "Bilkisu sarauniyar shaiba in ji Yaya Faruk ".

Muka murmusa gabadayanmu ban da Abida da dama ba wani jituwa suke yi ba tun filazal.

Ya kalle!ta ya ce "Autar momi saboda Allah har yanzu ma da kika girma ba zamu shirya ba? Tunda na dawo sau uku kika bude baki kika mini magana fa".

Yana rufe baki ta ce "To ai sau ukun muka hadu."

Ya ce" yau fa?"

*Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke da kyau da nagartar.*

*Gunis hijab ado cikin wayewar addini da rayuwa*

*08163761797*

Kaitsaye ta ce "Dazu bamu gaisa ba? Yanzu kuma daga zuwanka sai na ce make me?"

Ya girgiza kai tare da ce wa "Ho Abida! To sannu da yammaci ".

Ta amsa da fadin"Sannunka dai Yaya Sulaiman".

Daga haka ta tsuke bakinta yayin da ni nake ta fadin "Allah Yaya Sulaiman ya kamata ka yi aure tun baka bari Ansar ya kutso da maganar aure zai yi ba".

Ya galla mini harara tare da ce wa"Ya yi mana an fada miki ni ina da gaggawa ne duka ma shekaruna nawa ne, haka kawai kun damu da maganar society akan aure aure, to wai idan mutum ya ce ba zai yi ba, shike nan ba zai shiga aljanna ba ne kome kuke nufi?"

Nan da nan Abida ta fashe da ce wa "Yauwa Yaya Sulaiman gara ka zo ka taya ni fahimtar da su. Wacce irin masifa ce haka da mutanen da suke da ilimi amma suke runtse idanuwansu da fahimtar komai lokacine. A yi ta damun mutum ya yi aure, ko ma ace ya ki yi gabadaya wai a dole sai sun barranta mutum daga shiga inuwar ma aikin Allah. Haba haba na gaji da ra'ayin hausawa akan aure. Zamana a Lagos shine mafi dadi a rayuwata domin ba yadda za'a yi a tsangwame ka akan aure."

Yaya Sulaiman ya tausasa harshensa ya ce "Yo ke ma da kike daka ta tasu kina bata ranki a banza. Ba ki samu wanda ya dace da ke ba, ba kuma zaki yi auren dole ba, shike nan ki tsaya akan ra'ayin ki fak'at!

Yaya Faruk ya ce "Kai kuma kalar na ga girman ke nan Sulaiman? Ana shawo hankalinta akan ta bawa masu sonta dama su kwankwasa kofar da ta kulle zaka sake ingizata akan ra'ayinta?"

Da dukkan gaskiyarsa ya ce "Ba zugata nake yi ba. Amma ban son a saka ta yi rushing."

Daga haka ya ce "Yogurt nake son sha".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Nan da nan aka mika masa gabansa domin tun dazu an kewaye mu da shi.

Wajen karfe shida na yamma muka bar gidan gonar.

Yaya Sulaiman ya karbi mukullin motar Abida ya shiga mazaunin direba.

Na yi maza na shige baya domin a yanzu ban cika son na zauna gaban mota ba matukar ba ni zan ja ko Baban Amrah ke jan motar ba.

Na san Abida kuma tun filazal bata kaunar zaman gaba tafi gane ta hakince a owner's corner ana janta, dan haka na rigata shigewa baya.

Kan dole ta shiga gaban motar tunda ta sani a shekarun baya ma Yaya Sulaiman bai yarda ya zame mana direba ba, bare. kuma yanzu da ya sake wayewa ainun.

Maimakon ya bi ta cikin gari sai kawai ya bi ta bayan gari wanda nisan tafiyar ya sake nunkuwa. Sannu a hankali yake tukin. Ni da shi sai hira muke yi yana ta mamakin yadda Amrah ta yi tsawon kafa tamkar ba yar shekaru shida ba. Da kansa kuma ya ce ko da yake Babanta ai dogone na gaske, ke ma kuma ba'a magana ".

Na yi dariya tare da ce wa"Ga uwarta nan a kusa da kai, ni uwar Yaya Faruk ce kawai".

Ya ce "Hakane, amma idan an zo maganar kama ai dole a jinginawa Sahal ita don kuwa kamar ya yi kakinta ne".

Na yi shiru ban ce komai ba.

Jin haka sai ya yi gyaran murya ya kalli Abida da tunda ta zauna ba ta ce kala kanzil ba.

Ya ce "Dr ya ya dai?"

Ba sukuni ta ce "fine".

Ya murmusa tare da ce wa "Amma ba kya cikin yanayi mai dadi. Duk sai na ji nima am not in the mood."

Ta muskuta ta ce "Akan me za'a takura ni sai na yi aure akan dole? Bana son kowa. Ni hana ni tafiya karatun nan ma basu san sun sake nesanta zuciyata da son auren ba ne gabadaya ".

Da wata irin murya ya ce "To yanzu Autar momi kawai ki yi hakuri ki tsayar da miji a yi auren, ana yi sai ki tafi karatunki".

Murya a dashe ta ce "Ni ba wanda zan tsayar, duk zugugun da ake yi mini na ki tsayar da miji alhali ina samun masoya, ai duk basu cancanta ba ne. Ba wani jarumin gaske a cikinsu mitisew..! Ta ja dogon tsaki mai nuna kololuwar takaicin da ke zuciyarta.

Ga mamakina sai jin Yaya Sulaiman na yi cikin wata kankanuwar muryar da zata kai sako cikin zuciya ya ce "Autar momi ina ganin zan shiga sahun yan takara ko zan yi sa'a na zama jarumin kawai".

Gabana ya fadi sosai don kuwa nasan Abida sarai ba amince wa zata yi ba.

Ga shi na lura da gaske ya fada sonta ba kadan ba.

Tsawon lokaci muna dakon amsarta daga shi uban gayyar da ni yar tsurku.

Ya numfasa ya ce "Kin yi shiru autar momi."

A takaice ta ce "To me zan ce ne? Baba babba ne ya ce ka neme ni ko kuwa Baba k'arami?"

Da azama ya ce "Ko kadan Wallahi Abida! Zuciyatace ta harbu da son ki tunda na duro k'asar, har yau ban samu sassauci akan lamarinki ba. A farko na karaya da na ga yadda ake dauki ba dadi da ke akan aure. To amma zuciyata ta kasa jarumtar hakurin da na yi niyyar yi, don bana son na takura ki".

Ta numfasa tamkar zata yi magana sai kuma ta tsuke bakinta ta ki tankawar.

Cikin taushi da lallashi ya ce "Son ki nake yi tun ma ban gama fahimtar hakikanin son ba. Tun kuna Bakori. Idan za ki tuna ranar da Yaya Asad ya zo tare da y'ansanda suka kakkame muku ke da Baba da Bilki tun ranar na kamu da son ki. Ki bani dama, mu tattauna mu fahimci juna, idan akwai alheri Allah ya amintar da zuciyoyinmu, ba tsayawa zamu yi soyayyar shiririta ba, don kuwa dukkanmu ba yara ba ne, fatana dai ace mu dan fahimci juna".

Ga mamakina sai jin Abida na yi cikin murya marar amo ta ce "Allah ya tabbatar mana da alheri"

Murna ta kama shi ya ce "Ameen Ameen na gode."

Gabadaya kaina ya kulle. Me Abida take nufi? Ta amince ne ko kuwa amsa mai harshen damo ta bayar?

Na sani tana iya ce wa dan ta ce Allah ya tabbatar da alheri, ba shine nufin ta amince ko zata amince din ba.

Ya juyo kadan ya ce "Bilkisu ki taya ni fadawa kanwarki ina sonta da dukkan zuciyata, idan ta mini alfarma ta saka ni a zuciyarta to zan zame mata masoyi mai wuyar samu a yau".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Cikin karaya na ce "To Allah yasa ta amince domin lamarin nata kam babu sauki akan aure gabadaya."

Ya numfasa ya ce "Ni kuma ban fara sonta dan na daina, ko na fasa bisa karamin dalilai ko hujja marar k'arfi ba".

Na nisa na ce "Ubangiji ya tabbatar da alheri".

Ya amsa da fadin ameen ".

Har muka iso gida janta yake yi da zantuka da suka shafi karatunsu na likitanci. Sai ya yi magana uku sannan ta ba shi amsa d'aya a dunkule.

Ni dai na zuba ido ina nazarinsu, sun dace da juna sosai. Amma cike nake da zullumin yadda zata iya ce wa kyaunsa ya yi mata yawa. Domin kyakkwan gaske ne dogo mai cikken jiki. Kamarmu daya da shi sai dai na fi shi fari yayin da shi kuma ya fita haske tunda ita tana da duhu.

Da ya yi parking tana shirin bude motar ya tausasa harshensa ya ce "Tsaya mana ai bamu gama ba."

Ta koma ta zauna babu musu.

Ni kuma sai basirata ta toshe maimakon na fita na basu waje sai kawai nima na fasa fitar na gyara zama.

Ya juyo ya kalle ni ya ce "Saboda Allah Bilki sai na bude baki na ce "Ki dan yi excusing d'ina?"

Na diririce tare da bude murfin kofar ina ce wa "Afuwan!"

Na fita na yi sashen Mami tunda Yaya Faruk na can wanda shekarunsa hudu a lokacin.

Ban san ya suka kare ba, basu rabu ba, sai da aka yi kiran magariba, na ga yaà fito ya tafi Masallaci ita kuma ta shige shashinsu.

Ana idar da sallar ya shigo. Kaitsaye dakina ya wuce yana fadin" zo mana Bilkisu ".

Na tashi na bar su Ansari tare da Mami. Ya rike kunnena alamun kashedi ya ce "Kada ki sake na ji kin furta maganar nan a gaban mami ko yaran can. Sai mun gama daidaitawa zasu ji a bakina".

Na ce "In sha Allah kuwa! Amma ka ga alamun zata amince kuwa? Sannan sai ka yi hakuri da Abida domin tana da wani irin tsatssauran ra'ayi".

Ya murmusa tare da yin juyi sannan ya ce "Handsome guy kamata bata isa ce wa ban yi ba" .

Na yi dariya na ce "To ai ita bata son maikyau fa!.

Ya zabura ya ce karya take yi, kawai bata samu tsayayye irina ba ne, tunda kuma jarumi take so ai magana ta kare domin ni din jarumine ko cikin jarumai".

Na yi dariya na ce "Yabon kai dai babu kyau Yaya Sulaiman".

Ya fita yana fadin "Gaskiya na fada, ke ma kuma kin sani. Ra'ayinta kuwa idan akan gaskiya take ai ba ni da matsalar hakan, idan kuma na ga wanda ba zan daukesu bane ai tuni zan taka mata birki, don ba zan yaudare ta bare kuma na yaudari kaina".

Cikin doki na tafi sashen Momi. A dakinmu na tarar da Abida ta fito daga wanka tana zaune tana tsane jikinta da tawul. Amrah na gefenta tana cin Cheese wadda na ga ta siyo mata dazu a hanya, tunda sadda zamu tafi Ansari ya fita da ita gidan Yaya Usman.

Na zauna na kalle ta sai na ga ta yi kicin kicin da fuska. Jikina ya yi sanyi domin hakan alamace na ba zata tattauna komai a yanzu ba.

A hankali na ce "Abida ya ya batun Yaya Sulaiman kuwa, shi din ya yi?"

Na tambaya cikin tararrabi.

Ta matso manta ta hau shafawa tamkar ba magana na yi mata ba. Sai kuma ta numfasa ta ce "Kyaunsa ya yi mini yawa, inka cire wannan ba shi da wani nakasu, ya yi ".

Na saki ajiyar zuciya cikin kwantar da murya na ce "Ba shi da wani kyau fa Abida! Kin fi shi kyau ai".

Ta girgiza kai ta ce "Kin sani yana da kyau Maigado."

Na ce "amma ai kyaun bai yi wani tsananin a zo a ga ni ba Abida!

Ta dauke kai tare da ce wa "Kin san Allah kada ki nemi ki wani zake a harkar nan. Domin ba irin kamfen din da ban yiwa Yaya Asad ba kika shafawa idonki toka. Shine yanzu zaki zo kina mini wani rawar jiki?"

Na zabura na ce "Ai dai bai zo gabana ya furta mini soyayya ba. Haka ma Yaya Faruk din da nake so bai zo da nufin gaskiyar magana ba. Ki daina wannan maganar Abida!.

Ta numfasa ta ce "Na barta adalcin da nake yi miki ba wani wanda ya nuna jarumtar tunkarar ki da maganar soyayya sai kame kame. Nima kuwa duk wanda suke son nawa duk haka suke yi hannunka mai sanda shiyasa na ce babu jarumi a cikinsu ".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Na kyakyale da dariya tare da ce wa ki ce "Yaya Sulaiman ne jarumin tunda ya dunfare ki kaitsaye."

Kafin ta ce uffan muka ji ana kwankwansa mana kofar dakin.

Ganin Abida babu kaya a jikinta ya sanya na tashi na nufi kofar.

Kawai sai ganin Yaya Sulaiman na yi a tsaye ya yi wanka ya sauya kaya, sai kamshi yake yi"

Na murmusa na ce "Da alama dai sosai muka shake wuyanka yayanmu".

Ya murmusa ba tare da ya ce kanzil ba. Ya yi baya ya ce "ki ce mata ina jiranta".

✏️

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Na dawo dakin na tarar tana zaune ba wani alamun motsin a tare da ita. A hankali na ce "Ya ce na fada miki yana jiran ki."

Kai kawai ta daga tabbacin ta ji abin da na ce.

Amma shudewar mintina talatin tana faman busar da gashinta da hand dryer, ba wani sauri ko gaggawar ana jiranta. Zuciyata sai tsallen badake take tare da fargabar Yaya Sulaiman bai samu karbuwa a zuciyarta ba.

Murya ba amo na ce "Abida Yaya Sulaiman fa na jiran ki".

Kafin ta bani amsa wayarta ta hau kuwwa. Amrah da take game a wayar ta mika mata da hanzari.

Ba walwala ta amsa. Ban ji me aka ce mata ba.

Na dai ji ita ta bada amsa da ce wa "Rigar da na yi nufin sakawa yau ashe na mance ban karbo a wajen matar Yaya Faruk ba".

Ta yi shiru tana sauraronsa.

Ta numfasa ta ce "Ina da wasu kayan da yawa ma kuwa, sai dai ba wacce nake son na saka a yanzu sai waccar da bata gidan nan."

Tsawon lokaci tana rike da wayar da alamu suka nuna magiya yake yi mata da rarrashi.

Ta numfasa ta ce "Tom!.

Tare da kashe wayarta ta kalle ni ta ce "Ya ce ki kai masa mukullin motata don wacce yake hawa fitilunta duka sun lalace."

Na zuba mata ido tare da mamakin yadda ta zabi ta aike ni alhalin ko Amrah zata iya kai masa tunda ta shekara shida.

Na dauki mukullin motar na ce "Amrah maza sauri ki kaiwa Uncle key ga shi can a kofar shigowa nan".

Wayar na hannunta ta yunkura.

Amma sai Abida ta zuba mini ido sosai ta ce "Ke ya ce ki masa, kuma nima ke nake son ki kai din".

Ganin ba wani wasa a fuskarta ya sanya na mike ina fadin "Idan na kai din Abida ba abin da zan ragu da shi".

Na fice da sauri. A bakin kofar shigowar sashen na gan shi yana tsaye cak da shi. Idan har da gaske bata son kyakkwan namiji to zai yi wahalar gaske ta karbi soyayyar Yaya Sulaiman.

Na murmusa na ce "Oh Yaya Sulaiman!

Da hanzarinsa ya miko mini hannu ya ce "Ba ni dan Allah sauri nake yi."

Na ba shi cikin madaukakin mamaki domin ban yi zaton yadda yake matukar kamewa a gabanmu zai so Abida irin haka ba.

Na juyo ina jinjina sha'anin Ubangiji don babu wani shiri ko jituwa a tsakaninsu asali Yaya Sulaiman irin mutanan da suka fi son rayuwa a wajen da babu hayaniya, amma aka jarabce shi da son murdaddiya kuma yar hayaniya irin Abida.

A fili na ce "Gidanku akwai kallo kuwa.

Na zabi na zauna a falon momi cikin shauki nake sosai domin na jima ban ji faricinciki irin wanda nake ciki a dalilin wannan lamarin ba.

Momi ta fito dauke da tiren da baba Babba ya ci abinci.

A tausashe ta ce "Maigado ke kadai a nan?"

Na fara kunkuni ina fadin "Gaskiyar magana Yaya Asad ya bata mini suna!

Ta murmusa ta ce "ban da Bilkisu wa ce ce mai gadon zinare duk duniya?"

Ta bawa kanta amsa da fadin "Babu sai sarauniyar shaiba".

Na murmusa na ce "Ai ina ga ba shii da lambata yanzu, tunda aka fada mini an masa karin girma zuwa A.C.P na jihar Oyo nake ta nemansa bana samunsa, sau daya dai ta yi ringing amma har kusan wata guda bai biyo ni ba".

Ta ce "Ki yi masa uzziri ayyukan da suke kansa masu nauyine kin san shi da kazar kazar ganin hakan ya sanya shugabanninsa suke sakar masa aiyyuka masu nauyi da yawa ".

Na ce "Hakane cikin gaskata ta domin tabbas Yaya Asad ya zama babban mutum ya yi kudi na gaske tun shekaru uku baya, ya samu manyan kudade na bada labari.

Matarsa da yayansa sun zama zarra duk da mu din ba talakawa ba ne. Amma dai shi kam ya yi kudi irin danyen kudaden nan ta bakin Abida.

Momi ta fito ta sake ganina a tukure a falon tunda na kasa na tsare ina dakon dawowar Yaya Sulaiman na ga yadda zata kaya.

Yayin da momi ta ce "Hala yar sababin ta rufe miki kofar?"

Na girgiza kai tare da fadin "ko kadan momi waya na yi".

Ta wuce tana ce wa "au to ba laifi ".

Ba'a wani jima ba ya shigo a gaggauce rike da leda a hannunsa, waya a kunnesa, sai dai duk da hakan sai da ya yi sallama, na amsa ina binsa da idanuwa.

Kaitsaye ya miko mini tare da ce wa "Ga ta nan zata kawo miki. Pls Abida mintina goma sun ishe ni. Ina son ganin kine kawai."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Mamaki ya sake mini k'awanya dama Yaya Sulaiman zai iya doguwar magana haka?"

Ya katse wayar ya kalle ni ya ce "Da alamu dai Abida ta koya miki son jin kwakwaf ko?"

Na fadada murmushin da nake yi na ce "mamaki nake yi akan lamarinka da Abidan Baba".

Ya ce "oya wuce ki kai mata ban son tsurku"

Na wuce da azmaa ina faman kyalkyala dariya.

Na tarar da ita a tsaye da alamu dakona take yi. Na mika mata, ta karba ba tare da ta ce mini uffan ba.

Ta shige bayi bata wani bata lokaci ba ta fito sanye da riga.

Na bita da kallon tu'ajjibi, domin rigar irin ta shan iska ce, tabbas doguwace har kasa amma ba yadda za'a yi a fita da ita, domin irin yadin nan ne mai rawa a jikin mutum bayan haka hannun rigar irin armless din nan ne. Na zuba ido ina son ganin yadda zata fita da rigar a haka.

Ba zato na ga ta zaro katon hijab dinta mai matuk'ar kyau da ya sha guga ta dora a kan rigar, ya rufe ta ruf.

*Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke dacewa da amsu jiki ko sirara.*

*08163761797*

da ke mun riga mun saba da kanbasa, mun saba sai mun yiwa kayanmu kafin mu shiryasu a wadirof, kamshin hijabin ya iso har hancina.

Amrah ta kalleta ce "Ammi kin yi kyau".

Ta murmusa tare da fadin "Thank you Amrah dear.

Ni dai ido na bita da shi, ko menene hujjar tura shi karbo rigar da ba za'a yi ado a fita da ita ba?

Asalima ta rufe ta da hijab, na numfasa ina dada bin ta da ido.

Na kasa hakuri na ce "Ni kam Abida dan Allah menene hujjar karbo wannan rigar duk zatona ta alfarma ce kwalliya za ki yi ta mussaman da ita ".

Ta galla mini harara ta ce "Bilki ki kame bakinki akan sha'anin nan, kinsan dai ke ba ki isa ki mini kanzagi ko taya shi neman yardata ba kamar dai yadda kika nuna ban isa na taya Yaya Asad neman yardarki ba".

Nan da nan na diririce na ce "me ya taso da wannan maganar kuma Abida? Ba ki ga rabon ya'yan da na haifa ba na Yaya Asad ba ne? Ashe ke har yanzu kallona kike yi da abin alhalin shi ya mance ma gabaya da ni?"

Ta ce "Hmm idan bai manta da ke ba, za ki aura miji biyu ne?"

Na ce "To ko dai shima a kullace yake da ni ne? Dan idan har lissafina daidai ne rabona da na amsa wayarsa tun haihuwar Amrah. Duk sadda na kira da nufin na gaishe shi kuwa wayar zata yi ta ringing amma ba zai dauka ba, ba kuma zai biyo bayan kiran ba! Na jijjiga kai na zarce da fadin "Ashe shata layi ya yi da ni, alhalin ni ya kamata na masa irin haka tunda ya yi mini sanadin rasa Yaya Farouk."

Na fitittike ina zayyano asarar da ya janyo mini ban da dai ina da taushin zuciya har na sake nemansa da nufin yin zumunta da shi. Amma lallai kina da son kai har ki kullace ni tsawon lokaci irin haka Abida? Babu damuwa na gode sosai amma ki sa ni, ni ba zan taba miki son kai ba. Idan zuciyarki ta amince da Yaya Sulaiman fine. Idan bata amince ba fine, don ba ni zan zauna miki ba, bare na nade kafar wandon tallata miki shi by fire by force ba"

Ganin da ta yi na dan motsa kwanjina ya sanya ta hadiye komai don tasan yana wahalar gaske na bude baki na kare kaina idan tana mini sababi, idan kuwa har na yi to ta kure ni ne, hakan kuma dabi'ata ce kowa ya sani kafin na yi korafi sai tura ta kai bango kwarai da gaske. Ba tare da ta sake ce wa kanzil ba tasa kai ta fice tare da janyo kofar sai dai bata rufe gabaya ba, na tabbatar kuma bata yi zaton ba zata rufu ba don ta tsani a bar kofar a bude.

Sai da na shiga bayi na fito na kalli Amrah barci ya sure ta ga wayar Abida na gefenta. Na girgiza kai domin nan duniya Amrah kadai ke da lasisin taba wayar Abida ba yaron da ya isa ma ya tunkarevta da nufin ta ba shi wayarta, ko ni bata yarda ta ara mini tunda can bare yanzu.

Na tabbatar da dukkan zuciyata take son Amrah.

Na nufi falo a hankali tamkar munafuka.

Na tsaya ina sauraraon Abida na ce wa "Na kyautar da abin da zan fara haifa tun shekaru goma da suka shude ga Bilki".

Na ji Yaya Sulaiman ya yi guntuwar dariya ya ce "Funny girl! Yanzu ki yi kyautar da d'a babu yardar babansa, kuma wa ya ba ki tabbas din za ki haihu ne?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Na kasa kunne ina murmushin jin dadi.

Ba wani kunbiya kunbiya ta ce "Na dai sanar maka ne dan ka sani akan wannan alk'awarin nake rayuwa".

Yadda kike so haka za'a yi Abidan Baba."

Yaya Sulaiman ya fada a takaice.

Daga haka ta ce "To gobe ka je wajen Baba k'arami ko baba Babba ka ce a daura auren".

Na kasa gane nufin Abida daga zance daya sai aure, na tabbatar ba sonsa ta afka mai nauyi ba.

Ilai kuwa sai jinsa na yi ya ce "Aure Abida! Ban hango soyayyata irin soyayyar da nake miki a idanuwanki ba, ban gan ki cikin shaukina ba, sai ki ce aure kamar wasan yara?"

Yana rufe baki ta ce "oh bata mini lokaci ka zo yi ke nan?

Ka ce kana sona, kana son aurena, na fada maka cewar abin da muka haifa a farko ba namu bane, ka ce ka amince babu matsala, na ce to ka fito sai kuma ka ce baka ga soyayyarka a tare da ni ba? To shike nan nemi wacce zaka ga soyayyar ". Ta mike tsaye da nufin tafiya.

Ya yi maza ya mike shima ya ce "Ba hakan ba ne Abida wai da so nake mu dan fahimci juna ko ya ya ne, sai maganar auren ta biyo baya."

Ta juya da nufin barin falon ya yi maza ya sha gabanta ya ce "Ba fa abin fada bane Abida ki fahimce ni mana"

Ba walwala ta ce "Na fahimce ka da kyau amma gaskiya ba ni da lokacin yin soyayyar da zaka ganta a idanuwana a yanzu dai, is better ka nemi wacce zaka gane hakan."

Ya ce "Abida kamar dai kora kike mini da hali. Harshenki babu laushi a kaina ko kad'an"

Kafin ta ba shi amsa baba Babba ya shigo don tunda ya tafi sallar Isha bai shigo ba.

Ganinsu tsaye cirko cirko ya sanya ya ce "A a Sulaiman da Abida yau a tsaye babu fada?"

Ta zabura ta ce "Ai kuwa fadan zamu yi da yafi na baya muni Baba".

Nan da nan baba ya ce Assha Abida ba za'a yi hakan ba da ikon Allah ".

Shi dai Yaya Sulaiman ya kasa ce wa komai.

*Kun tuna Umm Nihla mai yadinkan Yan gayu da Yabin Bulkacuwa ta yi ta kece raini da su?*

*Tana nan tana kawo muku Su Zuka zuka, na alfarma, amintattu, akan farashi mai rahusa*

*Malaysianfabricsng*

07020695644.

Baba ya zauna ya ce "Ku zauna na ji ba'asin fadan da zai barke bayan yanzu kin yi hankali".

Abida ta yi fit ta ce "Tunda ya dawo yake bina da kallon da yake takura ni, na so na kawo kararsa sai na hakura tunda ba ni da hujjar kawo karar. Kwanaki biyar da suka shude ya tsananta bin diddigina tare da fara yi mini magana, yanzu kuma tunda ya ga Bilki ta zo ya sake tsananta shiga shirgina na yi hakuri ban ce komai ba. Yau sai ya zo ya ce yana sona, yana son ya aure ni. Na fada masa na fa kyautar da abin da zan fara haifa ga Bilki, ya ce ya amince da hakan .

Sai na ce to ya zo wajenka, ko wajen Baba karami a daura auren."

Ba murna bare godiya sai kawai ya hau sarhutun wai bana sonsa, bai hango soyayyata a idanuwana ba da sauran maganganu masu nauyi har da ce mini bai ganni cikin shauki ba. Wato yaudarata zai yi a cikin gidanmu Baba?"

Baba ya tuntsure da dariya tare da fadin "Ho Abida!

Yayin da Yaya Sulaiman ya zama gunki ya kasa cewa komai.

Ta fara tafiya tana ce wa "To kada ya sake mini wani kallo na daban sannan tunda ba aure za'a yi ba, to ya rabu da ni,da zancen wata soyayya ban iya ba ".

Baba ya ruko ta ya ce "Ba haka za'a yi ba, ba ki fahimce shi daidai ba, yana nufin ku fahimci juna, ku dan tattauna har ku sami daidaito sannan ya sanar mana."

Nan da nan Yaya Sulaiman ya samu kwarin guiwar ce wa "Thank you Baba that is exactly what I mean".

Baba ya juya ya ce "kin ji ba? Zauna ku cigaba da tattaunawar ai ba za'a yi rikici ba, ahalin Allah yana shirin gwada karfin ikonsa a kanku, ko a mafarki a ka nuna mini hakan zai faru zan yi kokwanto bare a zahiri. Amma ikon Allah yafi ga hakan."

Yana rufe baki ta ce "Allah Baba ba zan iya ba, ban son kallon da ya tsiri yi mini irinsa, sannan idan ya kira ni a waya baka ji yadda yake yin kasa da murya ba, tamkar ta sabon mashayi ko mai shekarariyar mura. Na yi ta fadin ban ji ba, ban ji ba, kai abubuwan dai da bazan iya daukarsu ba ".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Yayi kasa da kansa yayin da baba ya rasa me zai ce.

Da kyar ya ce ,"Wai ke wacce irin yarinya ce ne haka? Kin doshi shekaru talatin amma kina abu tamkar yar shekaru goma. Likita ce fa".

Ta ce "Da karatun likitancin zai dinga mini sai mu fafata. Amma ban da karya murya da kallo na daban mai tsanani, haba haba gaskiya Baba ni bana son a yi ta yin soyayyar nan ta masifa".

Dariya ta sosai ta kwacewa Baba ya ce"Allah ka taya ni son Maryam Abida!

Ta murmusa ta ce "Ameen Baba".

Ya wuce yana fadin "To kai Sulaiman sai ka je ka gaida Baba karami idan ya amince da nagartarka, ni da Asad sai mu nema maka aurenta a gabansa, Allah bar shi ka nemi soyayyarta idan an kai ta gidanka, tunda haka take so".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Bojuwa herbs*

*Oder your kayan mata for women of class*

*Our products are healthy and original*.

*Tested and trusted*.

*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.

*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.

*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*

*Sanyi flusher kuwa best seller ne*

*Just DM for your order @08033773332*.

Baba na gama fadin haka ya wuce yayin da Abida ta yi wuf ta matso tsakiyar falon ta yadda zamu ga juna sosai.

Idonmu ya hadu nan da nan na diririce na kasa ce wa komai.

Ta bude murya sosai ta ce "Na rantse kin banu Sola. Tuni jikina ya bani kin biyo ni. Oh na ga ranar da za ki daina gana mini azaba matukar muna cikin gidan nan."

Na yi sukuri na kasa tanka mata.

Ta juya ga Yaya Sulaiman da yake fadin "Abida zo mu gama idan na tafi sai ku dora a inda kuka dakata"

Kan dole na ja jikina na shige daki ba tare da na jiyo matsayar da suka dasa aya ba.

Kamar wasa karamar magana ta zama babba don kafin na bar Funtua magana ta nuna har an saka aure watanni biyu masu zuwa a dalilin za'a yi gyara a sashen Hajiya kakarmu a nan zasu fara zama kafin a samu a mayar da Abida aiki asibitin cikin Katsina tunda a can angon yake aiki.

Amma sam Abida bata sauya ba don kuwa ba kasafai take ba shi dama su yi hira ba, idan ya kira waya nan ma bata yarda su yi doguwar hirar da ta zarta mintina goma.

Ni dai na zuba ido ina kallo tare da mamakin yadda Abida take kan sharafinta tare da gasgata dinbin soyayyar da Yaya Sulaiman yake yi mata. A duk sadda na kalli lamarin ko na tuna yadda aka yi auren sai na gasgata karfin kaddara da rabo. Domin ba dan karfin rabo ba, ban ga ta yadda suka dace ba, gabadaya hasashen yadda zaman nasu zai kaya nake yi matukar na zauna ko na kwanta da nufin na yi barci ba ni da wani lissafi ko hasashe sai mamakin lamarin Abida da Yaya Sulaiman nake yi.

Ba dan na ce a takaice zan hakaito muku rayuwarmu ta baya da komai da komai akansu zan binciko, idan kuwa na yi hakan to lamarin nasu zai mamaye labarin ba tare da mun nausa cikin alamarin da nake son ku fahimta ku kuma yi mini alkalanci ba.

A takaice kafin na bar Funtua an tsayar da lokacin aure watanni biyu masu zuwa. Mahaifiyarmu bata soki lamarin ko kadan ba, bare kuma baba karami da ya kambaba lamarin. Duk yadda na so mu tattauna da Abida akan wannan murdaddiyar soyayyar ta sha mur ta ki ba ni damar hakan. Amma na kulle tarin tambaye tambayen da nake son yi mata a hannun zanina don ba zai yiwu ta gama kushe kyawawan maza snanna rana tsaka ta tsayar da tsalelen saurayi na garari da sunan ta aminta su yi aure, ni na kuma kasa yi mata raddi duk sababinta kuwa.

Ana gobe zan koma Kano muka yi waya da Sahal nake fada masa gobe ya zo ya dauke mu. Ya gabatar mini da uzzirin gobe zai taro Baban zaria a airport zai dawo daga umrah. Na ce "To ka zo jibi, bai ce komai ba. Ni kuma na kudire goben dai zan tafi tunda na kwashe sati 2 maimakon 1 da muka zo da niyyar yi, dan haka na yi shiru ban ce masa zamu biyo motar haya ba a kokarina na yi masa bazata. Washagari na yi harama duk da ban samu an kai ni har Kano da motar gida ba, bisa hujjar Yaya Sulaiman na Katsina da motar gida da ake amafani da ita. Yaya Farouk kuwa ya je taron inganta saraffa Madara da kiwon kifi wanda yake gudana a birinin tarayya Abuja. Abida ta kai mu tasha,.sit din baya ta biya mana gabadaya ta biya kudin sannan ta wuce asibiti.

Na dawo Kano cikin matsanancin farinciki da zumudi.

Sai dai faricincikina ya koma ciki ne a dalilin tarbar da Sahal ya yi mini. Mun saba shi yake kai ni ya kuma koma ya dauko ni, amma jiya da na ce Zan dawo gobe sai ya ce mu shigo Mota ba zai samu zuwa ba baya jin dadi ba zai iya tuki na lokaci mai yawa ba.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Zuciyata daya na ce to tare da fatan Allah ya ba shi lafiya.

Muna daf da shigowa Kano na masa waya akan ya zo ya taremu a tasha nan ma ya ce mu hau A daidaita sahu.

Jikina ya yi sanyi na shiga zullimin ko dai jikin nasa ya yi masa tsananine boye mini kawai ya yi.

Cikin sanyin jiki na isa gidan sai dai ga mamakina ba shi ba kuma motar da yake hawa.

Zuciyata ta dan yi rawa tare da tunanin wato ba a kwance yake ba, zuwa dauko ni ne ba zai iya ba, nan da nan na kore wannan zaton tare da fadin "To ko yana asibiti ma?"

Cikin kasala na kwantar da Yaya Farouk da yake ta faman barci. Na hadawa Amrah complex tare da kunna mata katoon na yi daki.

Na dauki wayata da nufin kiransa sai na ji karar bude gate tabbacin ya dawo.

A sukwane na dawo falon na zauna.

Sai da ya rufe gate din sannan ya shigo bakinsa dauke da sallama.

Amrah ta ruga wajensa. Ya dauke ta cak yana fadin "Ai da yau na yi nufin na daukoku ke da Farouk".

Kalamansa suka alamta mini yana fishi da ni a dalilin na kara kwanakin akan sati da ya ce mu yi. Abin da ya ba ni mamaki sai da na fada masa zamu kara kwanakin tunda hutun makarantar yara bai kare ba.

Haka nawa hutun bai kare ba. Bai yi inkari akan hakan ba.

Ya zauna ya kalle ni fuska ba yabo ba fallasa ya ce "Na yi zaton ba za ki dawo ba ne, har na fara tunanin zan je na debo yarana".

Na kalle shi cikin kasala na ce "Ban yi zaton zan maka abin da ranka zai sosu ka boye mini ba, ban taba hakaitowa hakan ba Baban Amrah".

Ya dauke kai ya ce ",Nan muka yi sati guda zaku yi na zo na daukoku, amma ana gobe za ki cika satin kawai kika ce mini kina ganin ba gobe zaku dawo ba ,kada na taho zaku kara kwanaki! Ya juyo da fuskarsa gare ni ya ce me kike so na ce miki tunda kin zartar da abin da kika ga ya kamace ki, sannan fada mini kika yi ba wai izini ko alfarmar hakan kike so na yi miki ba".

Na ce "To ka yi hakuri ban yi da gayya ba, wani alamarine yake faruwa da ya sanya ni farinciki da zumudi tare da tsurkun komai ya wakana a gabana ".

Ya daure fuska ya mike ya ce"Ko dai kina ganin yanzu ke kike da abin duniya, bana iya wadata ki da komai dole na yi biyayya akan abin da kika zartar a zamantakewarmu!

Gabana ya yanke ya fadi na kafe shi da manyan idanuwana na ce "Baban Amrah haba dan Allah wacce irin bahaguwar maganace haka?"

Ba damuwa ya ce "Maganar gaskiya kenan idan har ba hakan ba me zaisa ki mini irin wannan wulakancin?"

Na hadiye komai na sake ce wa "Ka yi hakuri, tunda wannan ne karon farko da na saba maka akan zuwa gida to daure ka yafe mini hakan ba zai sake maimaituwa ba ".

Ya saki ajiyar zuciya tabbacin ya huce.

A hankali ya ce "Ya wuce".

A hankali na furta "na gode".

Na tashi na shiga kicin don samar mana abinci tunda yamma ta yi sosai. A nutse nake aikin tunda akwai kayan miya a freezer da duk abin da zan bukata.

Amma kasan zuciyata ta ya yi nauyi.

Menene hujjar Sahal na ce wa "Don ba shi da shine ya sanya na yi masa abin da na yi din?"

Na furta hakan a bayyane ba tare da na shirya ba.

Bamu zauna cin abinci ba sai da ya dawo daga sallar magariba, duk da zucoyoyimu a jagule suke sosai muka ci abinci a dalilin kowannenmu yana da dauke da yunwa don ni dai tun karin kumallon safe ban sake kai komai bankina ba.

Ban saka ran zan samu tagomashi a shimfida ba tunda na riga na gane sha'awarsa mai raunice ainun.

Sai dai kuma ya nema din ya yi iya abin da zai iya, da ya samu nutsuwarsa ya bingire yana haki ba jimawa na fara jin saukar numfashinsa tabbacin barci ya murkushe shi.

Na yi lamo. Duk da a cikin duhu nake haka na tsurawa saman saman cilin ido, gabadaya idanuwana sun cika da k'walla, Ni kam haka auren yake ne ko kuwa dai ni kadai ce?

Kowanne namijine yake yin haka ko kuwa nawane kawai a hakan?

Na dinga kukan sharbe, hawaye ya dinga keto mini yana kwaranya a kan filo.

Tsawon lokaci na kasa barci don na fara gane matsaloli masu nauyi sun yi mini kawanya a gidan aurena sannu a hankali. Nauyin gida ya dawo mini, sannan kuma babu samun biyan bukata wanda wannan matsala ce da take tun farkon zuwana illa girma da take yi, kuma itace matsalar da tafi damuna don kullum ina k'ara fahimtar cutuwa nake yi sosai.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Washagari na tashi sukuku, na gyara gidan a daddafe don gaskiya bana iya aiki sosai. Ina aikin ina tunanin dole na samo mai aiki tunda dai wanccan tawa bata dawo ba, sai daga baya nake jin labarin an tura ta Abuja.

Alti kuma da aka kawo mini ita lokacin haihuwar Farouk ta tafi garinsu wacce ta aurar da ita ce take jinya, shine ta tafi jinyarta.

Mun kai sati kafin ya warware ya dawo mini sak yadda yake. Na ba shi labarin soyayyar da ta kullum tsakanin Yaya Sulaiman da Abida. Yana bude baki sai ce wa ya yi "Tabdi jam! Wacce irin karfaffar kaddara ce haka? Yarinyar da bata ganin kowa da gashi kuma mai kafirin isgiline yaya Sulaiman zai so har ya aure ta?"

Na kalle shi na kasa ba shi amsa domin dai tabbas dole ya yi mamakin amma kuma har cikin zuciyata ban ji dadin yadda ya kausasa harshensa akan Abida ba, duk da nasan tsakaninsu da tsakuwa amma ita tunda ya aure ni bata sake aibata shi a gabana ba. Asalima yanzu yabonsa take yi tare da ce wa ya zama raina kama. Ashe dattijone a zuci ba yaro yadda yake a gangar jiki da shekaru ba.

Sanin ba zai taya ni farinciki ba sai na kame bakina na bar murnata a ciki tare da bin lamarin da adduar alheri.

Har yara suka koma makaranta nima na koma bakin aikina.

Kullum shi muke bari a gida ya bar mini kai yara da daukosu. Duk safiya zan fice da yara bayan na tanadar masa abin karyawa yayin da shi yake nade a gado yana sharar barcinsa kaitsaye babu damuwar komai.

Kwanci tashi asarar mai rai har bikin Abida ya zo. Tuni kuma na aika mata ingantaccen sanyi flusher da Bojuwa herbs (08032773332 what'sapp only)suke yi da ingantattun saiwowin da suke dagargaza sanyin mara ya wanko dattin mahaifa. Bridal package na siya mata cikin zullimin ko zata yarda ta yi amafani da su. Tuni na tura mata kayan, kazar sababi ta amare ce sai zan tafi zan kai mata na tisata a gaba har sai ta ci.

Fadin irin rawar ganin da na yi a bikin ma kauyancine da asarar lokaci.

A cikin gidanmu aka tsantsara mata jere a bangaren kakarmu wanda aka yi masa gyara na mussaman ya koma ire iren gidajen Germany.

Ginin mai ban sha'awar gaske.

Haka nan Yaya Asad ya fitar da mahaukatan kudade wajen yi mata kaya na garari har lefe ma shi ya yiwa Yaya Sulaiman. Takanas ya turasu Dubai ita da matarsa suka siyo komai, tunda ya hana Yaya Sulaiman yin lefe ya ce zai masa.

Gidan Yaya Sulaiman da Abida na cikin jerin gidajen da na ga ni na alfarma a tsawon rayuwata gabadaya.

Murna kan murna nake yi musu tare da fatan mutuwa ce zata rabasu.

Biki ya yi kyau duk da iya rana daya aka yi domin ko kamu sai ranar yini aka fesa mata nono da turare. Amma komai yar raayin ta ce na za'a yi ba.

Dan haka yinin da iyayenmu mata suka shirya ya isa bata son bidia da tsokanar shari'a a matsayin bikin murnar aure.

Ni da Yaya Munira da ta zo bikin daga Spain uwar y'ay'a biyu mata.

Mun zubawa hakimar ido don mun riga mun san halinta na ra'ayin rikau.

Rabon da na saka Yaya Asad a idona gaskiya idan har lissafina daidai ne tun aurena shekaru kusan tara don ko aurerarakin da aka yi bayan nawa bamu hadu ba duk da ya kan zo daurin auren rana daya. Wannan bikin ma daga shi sai matarsa suka zo a dalilin ba'a yi hutun makaranta ba, sun bar yaran da kanwarta da take ruk'onta tunda mahaifinsu ya rasu. Da yarinyarta Noor mai shekaru biyu kad'ai suka taho, zuwa yanzu y'ayansu shida.

A lokacin da na gan shi sai da zuciyata ta buga da karfin gaske. Yana nan kamar yadda na san shi ba wani alamun shekaru sun ja, a tsaye yake cak, ko da yake tun filazal shi mai motsa jikine sai kuma ya zama sadaukin jami'in tsaro.

Da girmamawa na gaishe shi, ya amsa gaisuwar ta hanyar sara mini tamkar yadda ya sha yi mini a shekarun baya. Dadi ya kama ni na murmusa cikin kunya kunya na ce "Anya kuwa zan karbi gaisuwar nan Baban Bilkisu?"

Ya yi waiwaiye ya ce "A a Maigado ai ba zamu yi haka ba, daure dai ki karba kada ki sace mini iska mana, wannan gaisuwar ai ba a yiwa garabitins mutane."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Na kwakkwabe fuska na ce "Ba dama na kira ka dan na gaishe ka, ka dauki wayata? Ba dama a yi maka haihuwa ko k'arin girma ko wani abin jaje ya same ka, ko iyalinka na kira ka amsa mini, ba kuma zaka biyo ni daga baya ba tabbacin ka manta da ni, ka shafe ni gabadaya a zuciayrka da tunaninka alhalin ina da hakkin zumunta a kan ka!

Na fada idanuwana na tara kwalla.

Ya dan diririce ya ce "Oh no Maigado kin sani, ba yadda za'a yi na manta ki bare na shafe ki, asalima ke ce kadai a kullum nake tunawa sau ba adadi kullum yaumin, ko kin manta ina da Maigado junior a gidana? Kullum sai ance Bilkisu sama da sau goma a gidana. Kin tabbatar kuma ba yaudara ko dadin baki zan miki ba, sunanki na sanya mata. To a duk sadda aka kirata Wallahi sai na tuna ki, wani lokacin na murmusa, wani lokacin na tausaya".

Na yi kasa da kaina don na gasgata shi. Murya ba amo na ce "To amma me yasa ka yanke hulda da ni Baban Bilkisu?"

Kaitsaye ya ce "Na yi kuskure ki mini uzziri zan gyara, amma ki sa ni ba wai yadda kike so haka zan miki ba domin kowa da yadda yake managing abubuwan da suka dabaibaye shi a wannan rayuwar."

Na saki gauron numfashi na ce "Amma dai ni ce kawai ka takaita yadda zaka mu'amalance ni, ko na na ce ka datse mu'amalar bakidaya"

Nan ma ba ja in ja ya ce "Hakane kada kuma ki dauka tsana ce ko wani abune a raina marar dadi, kawai haka na tsinci kaina amma zan yi iya kokarina na gyara din kamar yadda na yi alkawari."

Hawaye ya zubo mini na goge da tissue na ce "Na gode ".

Ya kasa ce wa komai kawai sai na ga ya yi gaba ya bar ni cikin karfaffan takunsa amma bai iya furta kalma ko guda ba.

Washagarin da aka kaita kuwa sai ga shi sun shirya kasaitaacciyar walima ta abokansu da mu ahalinsu da bamu tafi ba.

Kana ganin yadda aka shirya walimar da nau'ikan abinci da nama da kifi hade da lemuna kasan sun shirya abinsu tuni.

Cikin nutsuwa da walwala aka gudanar da walimar, an ci, na sha, aka yi nasiha taro ya tashi, suka tafi gidansu, muma muka shige namu gidajen wadanda suka zo daga waje ma'ana abokan arzikinsu suka tafi nasu gidajen suma.

Ni dai na kasa daina mamakin wanna kasafi na Abida da Yaya Sulaiman. Kallo d'aya zaka masa ka gane ya gama rasuwa a kanta, yayin da ita baka isa gano alkiblarta ba. Kawai abin da nake kallo daya ne, da bata sonsa ba zata yi alkunya ko Kawaicin aurensa akan dole ba, ba da Abida za'a yi kawaicin cutar kai ba.

Surayya Dee

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Na kammala wannan shafin na ji rasuwar da ta girgiza ni, ban san shi ba, amma nasan Haj Rabi Sani madakin Gini*

*Allah ka jiqan Hon Mamuda Sani madakin Gini! Allah yasa aljanna makoma*

*Taaziya ga Anty Rabi Sani*

*16/06/25*

Washegari har azahar basu bude sashinsu ba. Mun so zuwa ni da Yaya Munira amma muka hakura.

Again washegari ina ta son na je amma na kasa tunda angon bai fito ba, ga shi da yamma Sahal zai zo mu tafi.

Yaya Hamida sai mita take yi akan bare baren da nake yi na son sai na je ganin kwakwaf. Ban tanka ba domin itama na ga a cike da ni tana mini kallon na fi son su Yaya Munira a kanta. Wanda ba hakan ba ne ko kadan illa shakuwa da muka yi da su, tunda tare muka taso.

Ana fara kiraye kirayen sallar azahar ta karfe daya na ga fitowarsa da ke sashinsu ne a kusa da tsakiyar tafkekekiyar harabar gidanmu. Na yi maza na fito tare da ce wa mami bari na yi sallama da amarya na ga maigidan ya tafi masallaci.

Cikin sauri nake tafiyar tamkar za'a dakatar da ni.

Yaya Munira ta kwalla mini kira tana daga sashensu. Na daga mata hannu tare da ce wa yi mini hakuri Yaya Munira yanzu zan zo".

Na murda kofar da ba'a rufe da mukulli ko jamlock ba.

Kamshi turare da na spice's din Amreesh spicy kana.... Ya bugi hancina. Na zauana a falo ina kallon aljannar duniya. Kafatalin ya'yan gidanmu ba wacce ta samu rabin kayan Abida duk da mu din ma kowa an mata na ke ce raini tunda iyayenmu masu wadata ne kwarai da gaske basa yi mana kwange kuma.

Na dinga jin karar hand dryer, sanin baya nan ya sanya na doshi dakin nata kaitsaye. Na yi turus a dalilin daga ita sai tawul ga gadon a yamutse kayan barcinsu a waste a kasa.

Ta zuba mini ido ta bude baki zata yi magana sai kuma na ga ta yi maza ta hadiye ta cigaba da taje gashinta.

Na ce "Amarya kina sha'aninki, kin ga irin annurin da yake fita a dukkan jikinki kuwa?"

Daidai lokacin ta kammala ta zare dryer daga jikin soket ta dauki comb tana kara taje wa, sannan ta saka ribbon ta kame shi daga kasa ba'a tsakiya ba. Na sake ce wa "yanzun ma ba za ki kama gashin a tsakiyar kai ba ta yadda daurin kallabin zai fi tafiya da yayanmu?"

Ta rausayar da kai ta ce "Hmm Maigado zan ga ranar da za ki daina nausa mini kuttu. So kike na tufke gashi a tsakiyar kai na siffantu da matan da Annabi ya siffanta masu tozo a kansu ya kuma tsine musu albarka. Dan ina son na burge shi, ko dan na yi kyau sai na yarda na shiga sahun matan da Annabi ya kwashe musu albarka shekaru dubu da y'an kai da suka shude ko?"

Na ce "Ai na ga mijinki kawai za ki yiwa kwalliya ne".

Da sauri ta ce "Idan sai na yi artificial abu da na burge shi, ko na yi masa kyau to tabbas ba zan taba burge shi ba. Na riga da nasan ko karkashin tsinuwar babanka ka shiga ko ta limamin unguwarku ai ka gama lalace wa bare ta ma'aikin Allahu."

Na yi maza na ce "hakane Abidan Baba."

Daga haka ta mike na zuba mata ido a bubbude take tafiya, ta bude wadirof ta fito da kaya, ta shirya a gabana. Sannan ta kwashe kayansu da nake da tabbacin gogan ne ya watsosu kasa. Ta gyara gadon tsab. Na kalle ta na ce "sannu Abida."

Ta murmusa ta ce "Kai Bilki sake ce mini sannu, wato abin nan da yake zama sanadin samun baby's babu sauki fa, bare idan ka hadu da karfaffan namiji mai jarumta kwanaki uku kacal har na gundura ina tunanin zan iya kuwa?

Amma da zarar na tuna na hau turbar da zan haifo miki da ko diya sai na yi maza na hadiye komai na kara jarumta".

Da azama na isa gare ta, na rungume ta ina jin sonta na huda duk wani sashe na jikina. Aurenta da Yaya Sulaiman sai ya sake ninka soyayyarta a zuciyata da gangar jikina gabadaya, a wannan ranar na gane manufarta na son na auri wani cikin yayunta don ta yi mu'amala da gidana sosai.

Ta dago ni tana share mini kwallar idona ta yi murmushin gaske ta ce "Yadda kike sona haka nake son ki Maigadona!

Na murmusa na ce "Na dade ban ji farinciki mai yawa irin yau ba Abida na gode sosai Allah ya zaunar da ke lafiya a dakinki, Ubangiji ya ninka soyayyarki da tausayin ki a zuciyar mijinki ya baku lafiya da zuria mai albarka ".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: A hankali ta ce "Ameen dear. Amma fa idan ya so ni fiye da hakan zai susuce ne, a dai kara masa tausayina da hakuri da ni kawai Maigado"

Muka kyalkyala da dariya gabadaya.

Can ta tsuke fuska sosai alamun ba wasa zata yi ba, ta ce "Idan kin tafi ki aiko mini da sanyi flusher din nan, na Bojuwa herbs, na rantse miki na ji dadinsa sosai na gamsu da shi."

Wannan karon ni na kwashe da dariyar na ce "Ni wacece ta dinga sababin ba zata sha ba? "

Kaitsaye ta ce Abida ce amma ai kinsna a likitance bamu yarda da shan maganganuwa gargajiya barkatai ba, to shi sanyi flusher din na gamsu da tsabtarsa an riga an dafa shi duk wani bakteriya da ido ba zai iya ga ni ba ya kone. Haka nan kaza da ciccibi suma sun dahu sannan tare ake dafasu da saiwowin maganin dan haka suma na yi accepting dinsu da dukkan zuciyata."

Na murmusa na ce "To da su da kazar sababi din za'a hado ke nan?"

Ta dauke kai ta ce "Idan kin so ki hado da ita".

Na tsananta kallonta na ce "Tsumin saiwowin fa? Shima ai ya dahu don shi sai ya kwana ma a kan murhu yana shan wuta ".

A takaice ta ce "Hado da shi Bilki!

Na dinga tuntsura dariya sosai, don kuwa ba karamin sababi ta yi mini ba da na aiko mata da bridal package akan wai ita nake nufin za ta sha maganin gargajiya?"

Sai ga shi da kanta ta nema tun ba'a je ko ina ba. Na sani kuma yadda ta ga sabbin robobi da containers ake zuba magungunan ya yi matukar nutsar da zuciyarta mai kyankyami.

Da yake tana bukatar kayan da gaske sai ta k'i yarda ta hasala ta ce "Na ji dadin marata ne da na sha sanyi flusher din sosai, yanzu kuma da ake zuba maka abu kullum, bayan idan ya je Katsina yana shiga toilet din da ba shi kadai zai shiga ba, dan haka dole na dinga yin rigakafi. Har antibiotics zan tanadar mana".

Na murmusa na ce "Na fahimce ki Dr matar likita".

Na kankance murya na ce "Da dukkan alamu dai Abidan Baba ba dakila ba ce, sannan yayana jarumine a komai".

Ta yi maza ya dauke kai tana fadin "Kin banu da son irin wadannan zantukan sola".

Na kwashe da dariya don da gaske kunya ce ta yi mata k'awanya.

Daga haka muka fita zuwa dayan dakin muka yi sallah.

Mun fito muka zauna ta ce "Maigado tashi ki lalubo mana abin kusa da baka mana".

Na ce "Wai yaushe zaki fara ba ni girmana ne Dr Abida?".

Ta yi murmushin nan nata mai burge kowa ta ce "Yaya Maigado wai da yake ke din y'argidace a zuciyata da gangar jikina ba zai yiwu kuma na mayar da ke bakuwa a gidana ba" .

Nan da nan ta kashe ni da dadin kalamanta na ce "Kin yi gaskiya Abidan Baba".

Na ajiye mayafin na shiga kicin, girman kicin din ya kai kurewa haka nan kayan da aka zuba mata sun sake mayar da shi na garari.

Shauki ya debe ni kawai na ji so nake na yi musu snack da girki.

Dan haka na fara aiki sosai tunda duk abin da nake bukata akwia tunda ga kan kifi da nama da kaji shake suke a freezer.

A shekarun baya kowa yasan yadda Funtua take da isasshiyar wutar lantarki.

Na fito da naman saniya na debi iya tsoka na ajiye a gefe, na ciro kaji biyu tare da kifi.

Da yake tana da na'ura kala kala nan da nan aikin nawa ya tafi, na yi grinding nama don samosa da meat pie zan yi masu dama na yi musu frozen, gefe kuma na dora ferfesun kaji, kifi kuwa na cikin oven ina gasawa. Jollof rice kuma tana daf da kammala a rice cooker.

Ina cikin kwashe shinkafar na ji shigowarsa. Zuciyata ta buga da na ji ya shigo da wakar you're my queen.

Na sandare a tsaye cikin mamakin Yaya Sulaiman.

Na tsinci kaina da lekensu, ya zauna daf da ita ya jata jikinsa yana tambayar ta shafa maganin ko su je ya shafa mata tunda dazu ta ce sai ta yi wanka.?"

A hankali ta ce "Na shafa tun dazu har yanzu kuma bai daina zugi ba, ga tafiyata a bude".

Ya shafa bayanta yana fadin sorry zuwa gobe za ki zama normal, nima zan daure na yi hakuri har zuwa goben".

Ta ce "zuwa gata dai gaskiya".

Cikin wata kalar murya ya ce "A a ban yi alkawari ba, mu bar shi dai zuwa jibin ".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Daga haka ya dagota ta zauna sosai ya mike yana fadin ""me kike yi ne ya cika gidan gabadaya da kamshi mai taso da dukkan tsohuwar yunwa?"

Bai jira cewarta ba ya doso kicin din na yi maza na kauce daga saitin da nake lekensu.

Ya tsaya a bakin kofar da ya ganni ina faman nadin samosa.

Ya murmusa ya ce "Well-done Bilkina".

Ya yi maza ya yi waiwaiye don shine kalmar da shekarun baya take saka Abida ta hassala da shi.

Ta ce bari waiwaiye na jika sai dai ai ka tabbatar mini ni ce taka ba ita ba".

Ya fadada murmushinsa bai ce komai ba.

Yayin da na bishi da da wani irin kallon farinciki. Ina ta mamakin wai Yaya Sulaiman ne yake baza soyayya ni ban yi zaton ma zai iya kula mace ba, bare ya lalace mata irin haka.

Na ce "Oh Yaya Sulaiman ashe dai dama Abida ta dade da kanainaye mini kai"

Ya juya yana fadin "Ban son shiririta yi maza ki kawo mana abin da kike girkawa pls,".

Na shirya shinkafa da gashasshen kifi na kai musu. Na dawo à kalle ni tare da ce wa "Oya zo ki yi joining dinmu".

Na rausayar da kai na ce "a a ban kammala aikina ba".

Ban bar gidan ba sai kusan la'asar, da na kammala sai da na shirya musu a cikin leda sannan na saka a firiza.

Da zan tafi muka rungume juna muna hawaye sai na tuna haka muka yi lokacin aurena. Duk yadda auren Abida ya yi jinkiri da Allah ya kawo lokacin an yi an wuce wajen. Na tsinci kaina da yiwa matan da suke fuskantar jinkirin aure adduar Allah ya yanke musu ya kawo mijin aure na nagari.

A bangaren momi na iske Yaya Munira tana dakinmu. Zaune take dirshan kan gadon Abida na kyalkyale da dariya na ce "Kina son hawa gadon nan dai Yaya Munira! Ga naki ko kewarsa ba kya yi?"

Na fada ina zama akan gadon da shine nawa.

Ta murmusa ta ce "Gadon yar sababi ai tunda bata tafi da shi ba soyayyarta gare shi bai kai ba

Na ce "Ai ta ce zata dauki abinta ba zata rabu da shi ba har tsufanta".

Muka yi dariya gabadaya.

Daga haka na yunkura na ce Yaya Munira bari na je mu yi sallama da Yaya Hamida anjima zan wuce."

Ta ce ai kuwa sun fita da Yaya Salaha cikin gari".

Na koma na zauna ina ce wa "To bari na baki soyayyar da Abida suke barza ita da take fadin bata son soyayya ba kuma zata yi ba"

A yammacin ranar na koma Kano. Shi ya zo ya dauke ni.

Muna tafe ina ta yi masa hirar soyayyarsu Abida. Ya ce "sai suke burge ki ko?"

Da azama na ce "Sosai ma Baban Amrah!

Ya numfasa ya ce "Mun yi soyayyar da tafi tasu k'arfi, har yanzu ma ban yi zaton zasu kere mu ba, sai dai sabon abu sabone akwai wannan shaukin."

Na yi yake na kame bakina ina rasa ta yadda zan masa bayanin halin da nake ciki ya gane ya dauki mataki.

Lafiya muka isa Kano. Na cigaba da harkokin sana'ata haka aikina. Sannu a hankali Sahal ya daina fita ya yi dan bugebugensa sai ya yini a gida a kan gado sallah take fita da shi.

Idan na dawo na gan shi akan gado ko a zaune yana kallo ko karatun jarida sai na ji gabadaya kunci ya mamaye ni, sai dai ba halin na nuna tunda a wanccan lokacin ina jin tsoron kada ya ce dan ina aiki, ina masa hidima shiyasa nake yi masa gatsali.

Karshen wata kuma haka zai bini mu yo shopping din kayan masarufi da komai na bukatar yau da kullum kamar sadda muke yi da yana aiki. Haka zai kwasowa kansa inner wears da turaren da yake sanyawa har ma da abin yin askinsa (sheving stick).

Ban taba gajiya ko jin wani abu ba. Don ni da kaina nake siyo masa shadda da yadika masu tsada su yi anko da Yaya Farouk, haka na siyo namu ni da Amrah.

Bai gama rufa shekara da rasa aikinsa ba komai na dawainiyar gidansa ya dawo kaina, ya sakar mini gabadaya. Bana damuwa da hakan tunda yana yawan yaba mini tare da gode mini, a duk sadda na yi hidimar da ya kamata ace shi ya yi sai ya ce "Allah ya ba ni damar da zan jiyar da ke dadin da ya zarta wanda na jiyar da ke a baya, ina son na samu damar da zaki gane ni din namijine da yasan alheri."

A duk sadda ya ce hakan kuwa na kan yi murmushin da nake jinsa tunda ga zuciyata dan haka kullum nake sake yi masa hidima kan hidima da karfina da aljihuna. Kullum ina cikin mm lissafin abinda zamu ci da wanda zamu yiwa y'ay'anmu hidimar makaranta da sauran dawainiyar yau da gobe.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Shi kuma ya sake nadewa ya bar mini dukkan wahala babu tausayi, ga shi duk wahalar da nake kwana da yini wajen rike masa gida, ba zaisa da daddare na samu nutsuwar da ta dace da ni ba.

A haka har aka shafe watanni takwas da auren Abida sai dai shiru bata da ciki ta dai yi bari, watanni biyu da bikinsu har yanzu kuma wani bai samu ba .

Yanzu suna shirin komawa Katsina da zama gabadaya don a watan jiya ta samu sauyin aiki zuwa cikin babban asibitin Katsina.

Zaune nake a falona hannuna rike da kofin da na zuba masa sanyin flusher don tunda na shiga wani toilet da muka je wayar da kan mata masu juna biyu akan muhimmancin shan folic acid, matsuwa ta kama ni na shiga bayin duk da na kwara ruwan kafin na tsugunna amma sai nake ta jin marata ba daidai ba, haka nan na fara ganin farin ruwa na fito mini, shiyasa na yi maza na yi order dinsa don na gasgata kyaunsa, na kuma gamsu da ingancinsa tunda Dr Abida ta yaba shi. For your order 08032773332.

Ya shigo ya zauna kusa da ni ya ce "Ina son na gan ki sanye da wadannan material din na Malaysia suna yi miki kyau suna kuma dacewa da kowanne yanayi ga taushi ga rashin nauyi abin birgewa basa kodewa duk sadda za ki saka tamkar ranar a dinkasu."

Na murmusa na ce "Ai Malaysianfabricsng siyan kayansu ribace babba, ga sauki sannan Kano take turosu kai tsaye daga Malaysia Idan kuma ba a kano kake ba ma za'a tura maka kaynaka duk inda kake ka karba cikin aminci."

Ya ce "na gasgata ki Billyna!

Na ce kin sanya yadin yangayu irin na Yabin Bulkacuwa da Maigado ko kuwa? Idan ba ki taba sanyasu daure ki jarraba siyansu zaki mini hodiya saboda yadda zaki ji dadin sanyasu.

Materials ne masu aji, masu class, na masana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu. Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basuda zafi basuda nauyi.

07020695644.

Ya mika hannu ya ce "me kike sha?"

Na mika masa ya ga ni ya kurba kadan ya mike mini ya ce "Dadina da maganin nan babu dacin da za'a ce wai ka zuba zuma shiyasa nake shansa".

Na yi murmushi don kuwa sanyi flusher kadai yake sha amma duk sauran maganganuwa da nake karba masa har da na karfi da kuzari da ya sha sau daya to ba zai sake sha ba, sai dai ya barsu sai na gaji da ganinsu raina na tafasa zan kwashe na zubar.

A haka dai rayuwarmu ta cigaba da gungurawa, tun yana dan fita yana y'an harkokinsa ya samo ko ba yawa har ya tsike ya daina fita da sunan neman kudi tunda kudadena sun wadacemu ba kuma na yi masa iyaka ko na jira ya ce mini yana bukatar kudi, don duk watan duniya sai na cika mana moticinmu da mai, sannan da hannuna na dauki daya daga cikin ATM dina na bashi tare da fada masa lambobin sirrin. Duk da dai a lokacin ce mini ya yi an turo masa kud'i.

Wani zuwa da Abida ta yi Kano daga Zaria zasu yi seminar a asibitin Murtala na kwanaki biyu, duk da an basu masauki sai ta taho gidana, bata sauka a inda aka basu ba cikin kwanakin biyun ta fahimci halin da nake ciki duk yadda ta so dauke kai ta kame bakinta kasawa ta yi. Ni kuma cike nake da zullimin kada Sahal ya yi mata abin da zaisa ta tunzura ta yi masa wulakancin da ni zata bari a cikii. Amma ga mamakina sau daya tak ta bari suka gaisa.

Sai da ta bari ranar da zata tafi, muna tafe zan kaita asibitin inda zasu hadu da abokan tafiyarta.

Ta kalle ni ta ce "Maigado duk yadda na so na makance na kuma kurmance daga rayuwar gidanki na kasa wannan jarumtar. Yanzu haka kika zabarwa kanki? Kullum ke ce kai yara sassafe ko da sai da rana ko yammacin za ki wajen aiki, shi kuma gogan ba inda za shi amma yana nade a gado! Haka nan tunda ya rasa aiki sai kika yi sanadin da ya rasa jarumtar zuci? Dole aikin gwamnati ne kadai namiji zai yi ya rike iyalinsa?

Wato ke kina da kudi zaki rike kan ki, ki rike y'ay'anmu, sannan shima ki rike shi da dukkan lalurarsa?"

Ta tambaya idanuwanta na kan fuskata da nake tuki sannu a hankali.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Na numfasa na ce "A a Abida ba haka bane, ke da kan ki kinsan sadda yake da hali ba abinda da bai yi ba, mai kokarin kyautatawa iyalinsa ne. Yanzu kuma sai nake ganin bai kyautu dan babu ta same shi na boye masa wadata ko na yi masa kwange ba. Mussaman da a kullum yake yaba mini tare da jadda ba zai taba mantawa da alherina ba, ba shi kuma da burin da ya zarta ya samu damar da zai jiyar da ni dadi ya kuma yi mini halacci".

A wannan karon murmushinta ta yi, tsawon lokaci kafin ta ce"A takaice dai na fahimci ke kika sanagarta shi gabadaya. Sannan kika kasa nuna masa komin kashin sana'a ya fita ya yi da ya zauna ki yi masa komai a gidansa. To saurara ki ji da kyau!

Allah da ya halicce shi yafi ki sonsa, ya kuma fiki tausayinsa, ya kuma fada mana a cikin alkuraninsa mai girma ce wa ba ya dorawa rai sai abin da zai iya. Haka kuma cikin hukunce hukunce da ya gindaya a cikin aure ce wa ya yi "Namiji ko shine yafi kowa talauci ya ciyar da matarsa gwargwadon ikonsa, ko da kuwa matar itace tafi kowa arziki a lardin! Dan haka idan dan Allah kike wannan hidimar to ki sani ba shi ya dora miki ba, asalima sarayar da hakkunanki masu yawa kika yi, yana kwance ke kuma kina tafe kullum a titi da sunan kai yara makaranta, da kuma kuma daukosu ko da ace ba zaki je wajen aiki ba, ya zame miki wajibi ki yi hakan, wannan ke kika dorawa kanki babu wata sakayya da Allah zai miki. Kazalika idan kina yi masa hidima da tunanin nan gaba idan ya samu dama zai miki halacci to ki yi maza ki farka daga barcin yaudarar kai da kika jefa kan ki a ciki don kuwa tabbas zai shayar da ke mamakin gaske, yadda bai wani girme ki da yawa ba, lokaci zai zo da zai ga sa'anin Amrah ne daidai da shi at that time kuwa komai zai kubuce miki ne sai an yi sa'a zai tuna da yanzu da kike ta wahala da rike masa gida ba tare da kin yiwa kan ki tanadin gobenki da ta y'ay'anki ba. Na taba fada miki wannan maganar, yanzu ma na maimaita miki and it will be the last time da zan sake furta miki. Time will tells you the real fact".

Daga haka ta fito da gilashinta ta saka ta hau dube dube a wayarta.

Duk da nasan ta riga ta kammala bayaninta zai yi wahalar gaske ta sake jan maganar. Na yi kundunbala na ce "Na gane Abida in sha Allah komai zai daidaita, zan gyara in sha Allah!

Na fada da wata kalar murya marar amo.

Tare da tunanin ta ina zan fara ce wa zan janye daga yin abubuwan da take korafinsu? Alhalin duk yadda yake yaba mini idan na kuskure ce mini yake dole ya ga komai tunda ni nake da dama a yanzu, ni kuma tashin hankalina ya furta mini wannan kalmar.

Tun watanni shida da ya yi zazzabi na hutar da shi kai yara da daukosu kafin ya warware shike nan ya sallama mini har yau bai karbe ni ba.

Ni gabadaya ma mamakinsa ne yake dabaibaye ni ta yadda kullum kullum kirkinsa da tausayina yake raguwa a maimakon ace ya ninka, saboda yadda nima ban gaza da dawainiya da shi ba.

*Contact me 08032773332* *what'sapp only*

*For all your kayan mata gangariya*

*Bridal package*

*Maijego package*

*Uwargida package*

*Bazawara package*

*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*

*Ciccibin garari*

*Tsumin saiwowi*

*Hakkkn daka emergency*

*Gumbar ridi*

*Gumbar saiwowi*

*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.

Surayya Dee

✍️✍️

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Har muka isa inda na kaita bata yarda mun sake maganar Sahal ba. Da na matsa da son sai ta kula ni ma a gajarce ta ce "To ban da kina da mantuwa bana fada miki ba zan shiga shirginki da mijinki ba? Yanzu ma kasa jure wa na yi ta yadda kika k'arantawa kan ki tunani da hangen nesa. Amma Allah yasa ki gane tun komai bai gama kwace miki ba."

Kwanaki biyu ina ta bitar kalaman Abida, amma na kasa samun mafita don na kasa fad'a masa ya dinga kai yara makaranta ya kuma dinga fita ko yaya ne, tunda a farkon rasa aikinsa yana fad'i tashi yana samun ana daukarsa yana tsayawa masu rangwamen gata suna biyansa yadda zasu iya. Amma yanzu kam da muka yi shekaru daya da rabi da rashin abin yinsa ya daina fita gabadaya da sunan yin sana'a kullum yana gida a nad'e akan gado, ko kujera kamar wani hamshakin basarake in ji Abida.

Ban san me ya saka Sahal da Abida basa ra'ayin junansu ba har yanzu da muka kwashe kusan shekaru goma da aure. Don bayan tafiyarta da kwanaki biyu bana mantawa, na dawo daga office k'arfe uku na yammaci gajiya da yunwa suka sababa mini ciwon kai, a falo na zube iskar fanka na kada ni. Yayin da yake zaune kan kujera yana kallon labarai a tashar C.N.N.

Hankalinsa ya raja'a akan yak'in da Saudiyya take yi da k'asar Yamen. A gaggauce ya kalle ni ya tausasa ya ce "Sannu Billy, alamu sun nuna kin gaji".

A hankali na ce "Ga yunwa ga ciwon kai".

Ya mik'e ya ce "Bari na kawo miki cake da tea ki rage karfin yunwar, sai ki sha paracetamol Ki dan huta kafin la'asar."

Bai jira absata ba ya nufin kicin ya hado mini shayi mai kauri a katon mug din da nake sha, ya zubo mini cakes guda hudu a cikin bowl. Bai zauna ba sai da ya dauko maganin hade da pure water mai rangwamen sanyi.

A tausashe na ce masa "Thank you Daddy".

Bai amsa ba ya cigaba da kallonsa ni kuwa na tsani kallon wannan tashin hankalin, domin alamun ne na musulunci ya fad'a cikin garari da fitinar gaske. K'asa mai tsarki da duniyar musulmai suke kallonta a uwa wai itace ke yak'ar kasar musulunci ta Yemen. K'asar da Annabi ya yi nuni da sashen yankin da take ya ce imani na can, ya sake ce wa imani na Yemen!

Yemen din da kaso casa'in da tara na alummar musulmai ne. Har menene abu mai dadi wajen kallon wannan masifa da ta fadowa alummar musulmai bakidaya?

Na fara cin abinci na kammala na yi gyatsa, zufa ta yanko mini. Na balli maganin na sha. A wajen na kishiginda, k'arar bude kofar da ya yi ya fita zuwa masallaci ya saka na farka, na sani kuma bai tashe ni kaitsaye ba ya bari na dan huta ko kan zai sauka. Na zauna ina jin babu ciwon kan dama nasan yunwa tafi yawa don yau ban karya ba , ruwan Lipton kawai na sha a gurguje saboda yara zasu yi latti.

Sai da na yi wanka na saka guda cikin material din Malaysianfabrics don bana gajiya da sanyasu saboda da taushi da rashin nauyinsu, ga kyaun da yake mai daukar idon mai ganinsa07020695644 order ur Malaysiaanfabrics.

Sannan na tada sallah.

Ina idarwa na fada kicin na hau aikin abinci. Ba ni da mai aiki mace. Amma akwai almajirin da muka yi sabo duk safiya da yammaci zai zo ya share mini gida ya yi moping, ya gyara kicin, ya mini wankin kayan yara ya yi guga. Amma bana ba shi wanke wanke, wannan ni nake yin abina, na yi girki na gyara dakunan barcinmu da bandaki. Amrah kuwa tuni na koya mata wanke bandakinsu da panties dinta.

Har wajen biyar bai shigo ba, ga shi bana son na sake fita.

Ina ta wasiwasin dauko yara, ya shigo ina kwashe abincin daga tukunya zuwa filas.

Ya biyo ni kicin din ya tsaya daga bakin kofar ya ce "Sannu har an sheka mana girki haka?"

Na ce "Yanzu babu ciwon kan, shiyasa na yi girki kada su dawo babu abin da zasu ci".

Hakane to sannu da kokari".

Na tausasa harshe na ce "A gajiye nake ka daukosu mana"

Ya kalli agogon hannunsa ya ce "Daure dai ki kwasosu ball zan kalla kin kuma sani biyar da rabi ake farawa".

Na girgiza kai na ce "Kallon k'wallone tafi hidimar ya'yanka? Me yasa kake son barina da dukkan nauyin da kaine wajibi a kansu, yanzu ace bana jin dadi ba zaka kwaso ya'yanka ba, saboda kallon kwallo?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya girgiza kai ya ce "Daga nan har wata guda komai za ki yi nasan ba ra'ayinki ba ne, tunda ta zo gidan nan ai dole komai na ga ni. Babbar godiyar da nake yiwa Ubangiji a lokacin da nake da dama ba abin da ban yi miki ba, kowa sha'awar ki yake yi. Idan har jarabawar da na shiga ne sanadin da zaisa ki raina ni, ko ki dinga neman yi mini iyaka a zamantakewarmu kawai ki bude baki ki yi magana" .

Nan da nan na ce "Dady me ya kawo wannnan maganar?"

Bakina har harde wa yake yi.

Ya zuba mini ido ya ce "Ke menene sanadin fadin na bar miki nauyinkan da nine a hakku na yi su? Kin sani, na sani daga bakin uwar iya wadannan kalaman suka fito ba a bakinki ba. "

A sanyaye na ce "Mu bar maganar haka nan, ban cika son idan muna magana ka dinga shigo da wata ko wani ba".

Ya juya yana fadin "Duk yadda nake dauke wa yarinyar nan kai sai ta kai ni bango na shata mata layi da shigo mini gida!

Haka na shirya na fita daukosu.

Ina mamakin daga ya yi jinya na karbe shi kai su da dauko su shike nan sai ya zame mini wajibi ni zan kai su na daukosu alhalin shi ba abin da yake yi? Kasan zuciyata na fara ganin k'amshin gaskiya cikin hasashen Abida. Amma da yake sonsa nake tsakani da Allah sai ban wani zurfafa ba na watsarke da tunanin na cigaba da hidimomin da nasaba.

Kwana biyu yana mini yar shariya kafin ya warware domin bai iya dogon fishi ba, tunda ni din zan yi ta takalarsa da magana har ya huce.

Akan dole na tattara komai na ajiye na cigaba da harkokina tare da adduar Allah ya cigaba da sakawa nemana albarka, kuma Alhamdulillah komai na taba sai Ubangiji ya saka albarka ya zama kudi sosai.

Lokacin biyan kudin hayar gida ya zo, na biya na shekara guda sabanin shi da yake biyan na shekaru biyu.

Abin farinciki da W.H.O. da nake aiki da ita ta sake kara mini wa'adin aikin da zan mata daga shekaru biyu zuwa shekaru uku.

Dan haka a cikin wadata muke sosai. Ga kasuwancina da yake ta habaka don yanzu ma'aikata ne da ni masu kama mini dan sosia ake yin snacks. Don ban cika ma yin dari ba sai dai ka ji ana fadin kowanne a yi guda dari biyar ko dubu.

Sai da Abida ta yi watanni goma sha hudu sannan ciki ya samu. Bana mantawa da murna ta kira ta ce mini "Bilki ki fara shirin tarban d'a ko diyarki nan da watanni takwas masu zuwa".

Da karadi na ce "Kai madallah da Abidan Baba! Allah ya raya ya sauke ki lafiya".

Ta amsa da "amin !

Har mun yi sallama ta ce "Kinsan Allah kada ki fadawa kowa nan duniya ke kadai kika sani har Yaya Sulaiman ma bai sani ba."

Dadi ya sake kama ni ina jin lallai ina da matukar muhimmanci a zuciyar Abida tamkar yadda take a tawa zuciyar.

Duk yadda nake cikin zumudi haka na kama bakina na tsuke ban fadawa kowa ba, tunda tafi so a ganta da shi. Na dinga yi mata addu'ar samun lafiya. Kullum sai na kira na gaishe ta, ta yi ta mini tsiyar ta gane nafi son unborn a kanta domin kafin hakan ai sai na kwana biyu ban neme ta ba, yanzu kuwa na fitine ta da yawa.

Dariya kawai nake yi ban kuma fasa gaishe ta kullum safiya ba. Idan abin ya ciyo ni ma har da yammaci sai na sake kira, da dukkan zuciyata nake jin son abin da Abida zata haifa mini.

Da yake a Katsina suke ba'a gane me take ciki da wuri ba, sai da cikin ya yi kwari, aka dinga murna da fatan alheri, domin itace kadai aka yi aurenta ta zarta shekara bata haihu ba.

Wani zazzabi da ta yi na je dubo ta na yini guda, na dawo da zullimin ko Abida zata iya cika alkawarin da ta yi mini a lokacin da take cikin shekarun kuruciya? Ga shi bata samu aure da haihuwar da wuri ba, har sai da aka fara jajensu. Ko Yaya Sulaiman zai amince a yadda ya sake ninka rawar kai a kanta?

Ina tafe ina wannan tunanin. Kasan zuciyata kuma sai tunani nake ban taba ganin Sahal a yanayin da nake ganin Yaya Sulaiman idan Abida na gabansa ba.

Na yi karamin tsaki tare da kore tunanin da ke son sababa mini Shubuha don kuwa nasan yana sona ai. Kawai he is not romantic ne yadda nake so da ace he is da na fi kowa dace. Duk da a yanzu ma kowa kallon daula yake yi mini a cikin ahalinmu. Abida ce kawai tasan hakinanin halin da nake ciki. Duk da taki bari na fada mata hakinanin matsalar da ta fi damuna a gidan aurena.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Yau da gobe har watan haihuwarta ya tsaya cikin ikon Allah ta haifo yarinyarta lafiyayya mai kama da Yaya Sulaiman sak.

Cikin sa'a cikin hutun yara aka yi haihuwar kuma abin farinciki ranar birthday din Yaya Farouk wato ranar ya cika shekaru shida.

Kwana biyu da haihuwar muka isa, murna kan murna yake yi ya samu birthday mate kuma itace matarsa, ya ganta fara mai gashi. Kaitsaye yarinyar tafi kama da ni akan Abidan.

Daga ita, har jaririya lafiyarsu kalau Yaya Sulaiman sai kanzagi shiga goma fita goma sai ya leko ya mata sannu.

Na dauki yarinyar na tsura mata ido sonta na keta ni tamkar yadda na dinga jin son Amrah a ranar da na haife ta. Na dago da idanuwana da suka cika da kwalla na ce "Sannu Abida Allah ya baki lafiya ya raya mana ita akan sunna".

Ta murmusa ta ce "Ameen.

Can na numfasa na ce "Shin kyautar tana nan ko Abida? Wannan tawa ce ko?"

Ta murmusa ta ce"Annabi ya ce munafikine yake saba alkawari, Duk yadda na sha wahalar nakuda ba zai saka na fasa baki abin da tuntuni naki ba ne. Cikin dalilan da yasa na amince da auren Yaya Sulaiman har da ba ki kyautar da ba za'a kwace miki ko nuna miki iyaka ba. Don idan ba shi ba, ba lallai burina ya cika na ba ki kyautar halak malak ba."

Na matsa na rungume ta na kasa ce wa komai domin wani irin rauni ya shige ni, tare da wata irin soyayyar da ba abin da zai shafe ta ila yaumil kiyama.

*

Ranar suna Yaya Sulaiman ya sake shayar da mu mamaki da ya ce sunan yarinyar Bilkisu alhalin da ya ce sunanta Aisha. Sosai Abida ta yi murna tamkar sunan momi aka ce an saka.

Basma Maska aminiyarmu da itama cikin Katsina take aure, uwar Abdul, Ayra da Iman.

Da ita aka yi shagalin sunan Bilkisu. Yaya Salaha da Yaya Hamida sai fadi suke suna manya ba'a yi musu takwara ba sai ni?

Ga takwarata ta gidan Yaya Asad ta cika shekaru goma a jiya.

Yaya Munira kuwa ta what'sapp aka yi vedio called da ita ta dinga fadin yadda ta yi missing dinmu gabadaya, ta kuma ce ta gode da son kan da suka yi, domin kamata ya yi a sakawa jaririya Munira ba Bilki ba.".

A wannan lokacin nima dauke nake da karamin ciki na watanni uku. Gabadaya cikin ya zo mini a bazata ban so ba, mussaman da nan ba da jimawa zan karbi y'ata da Abida ta haifa mini.

Amma haka na hakura na yi godiya ga Ubangiji na fadawa Abban Amrah ya yi murna. Na dinga mamakin ikon Allah. Don na shaida samuwar cikin haihuwa ikon Allah ne kawai, ban da haka yadda Sahal yake Mr 2minutes sannan sai an dauki lokaci kafin ya bukace ni, dole na yi mamakin yadda ciki ya shiga, dariya ta kwace mini a dalilin na tuna abubuwa masu yawa a kansa sam ya gaza a wannan fannin na kasa fitowa na fada masa har lokacin. Kunya da tsoron fassarar da zai mini suka mini dabaibayi. Duk yadda nake cire kudi na siya masa magungunan k'ara k'arfi masu tsada da supplement bai sa ya gane manufata ba, bai kuma taba mayar da hankali wajen shan ba, da ya sha sau daya tak to kuwa sauran sum zama asara shiyasa na hakura na daina siya suna zame mini na takaici tunda da hannuna zan zubasu a shara komin tsadarsu kuwa.

Kwanci tashi har su Abida suka yi arba'in.

Ina kwance a dakina ina sauraron littafin *Ta fita zakka* daga tashar Tsakar gida ta mai sanyi bayan na kammala jin *Abdul Qadir na Lubna*

Kiran Abida ya fado wayar. Na dauka ko gaisawa bamu yi ba, ta Fara korafi da ce wa ",Yanzu Maigado ace har yanzu baki turo mini maijego package din ba?"

Na ce "A a Abida ya ya muka yi ne? Ba ce wa kika yi sanyi flusher big galon za'a fara turo miki, idan kin kammala sai a turo sauran kayan gyara din?"

"Hakane! To Ki yi maza a turo mini nan da gobe?"

Na ce "Tom ina little?"

Ta ce "Ga ta can a hannunsa a falo".

Bata jira komai ba ta yanke wayar tunda ta riga ta isar da sakonta.

Ban ajiye wayar ba sai da na tuntubi Surayya Bojuwa@08032773332 na saka order ta bani tabbacin jibi dan sassafe za'a tura mini kaya Katsina. Na bada lambar Yaya Sulaiman don nasan shi zai je ya karbo kayan.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Muka yi sallama bayan na yaba mata kan nishadin da ta sanya ni cikin labarinta na Sabo da kaza. Abida sai ce mini take yi na samu lokaci na karanta HALIN YAU da Bakar Ta'ada lallai zan ji dadinsu. Amma na kasa karatun sai dai tunda na k'ulla abota da jin audio zan saurare su d'aya bayan d'aya da zarar na samu lokaci da nutsuwa.

*

Watan Abida shida da haihuwa nima na haihu bayan na sha kafirar wahalar gaske. Lafiyayyar yarinya mai kama da Amrah. Sai dai kwanaki biyu tak ta koma. Alhini sosai muka yi mussaman da ba wani ciwo ta yi ba, haka na hakura na cigaba da kula da kaina cikin dangana. Kowa ya zo ya gaishe ni.

Wata biyu da haihuwar Sahal ya tubure Katsina zai koma ya gaji da zaman Kano, tunda dama Mahaifinsa ya rasu watanni uku da suka shud'e.

To wai Hajiyarsu ta ce ya koma gida tunda ba aiki yake yi ko wata harka mai k'arfi ba. Tunda akwai wajen zama a cikin gidansu.

Na yi kasake ina kallonsa lokacin da yake yi mini wannan jawabin, tare da tunanin bai fada mata ni harkokina masu k'arfi ba ne a Kano?

Amma na hadiye ban yi inkari ba, kawai na ce "Allah yasa arzikinka a can ne"

Na dinga zullimin yadda zan yi da aikina da sana'ar da na kafu akan ta.

Sai dai cikin sa'a W.H.O din da ta ce babu damuwa sai na cigaba da yi mata aikin a ma'aikatrsu ta jihar Katsina.

Haka muka tattara muka koma. A wannan zaman na sake ninka hakurin da nake yi, domin a lokacin na fahimci dangin Sahal kallon mai farar k'afa suke mini. Zasu zo gidan sai ta kure da su shigo inda nake mussaman ace sun hadu da shi a cikin gida ko a waje sun gaisa.

Ranar wata Talata na dawo daga wajen aiki na shiga sashen Hajiya na tarar da kusan duka ya'yan gidan da yake akwai wanda babarsu ta rasu duk sun girma ga kuma 'yanmata wadda babarsuce amarya.

Ba laifi Hajiyarsu Sahal din ta rungumi dukkan ya'yan gidan nata da ba nata ba cikin hakuri da kyautatawa

Sai dai kamar kowanne gida baka rasa tsuguri tsoma irin na y'an ubanci. A zahiri kansu a hade yake amma a badini kowa da yan dakinsu yafi mu'amala.

Yar kanwar babansu ce ta haihu yau ake suna. Shine duk suka hadu a gidan daga nan sai su d'unguma su tafi gidan maijegon.

Na saba matuk'ar zan fita zan je na gaishe ta, haka idan na dawo sai na je mun gaisa ta ga

dawowata.

Ba ni da matsalar komai da Hajiya don mace ce mai addini da tsoron Allah.

Ina dosar bangaren na jiyo muryar Yaya Turai wacce itace babbar gidan, kuma dakinsu daya da Sahal diyar Hajiya ce.

Fadi take yi "Yo dama ai tsaurin ido ya yi, wannan yarinyar ai tafi karfinsa yadda yake salau salau ta ya ya zai iya da ita?

Dirarriyar mace mai zati, komin k'yashi ai ba matar yara ba ce. Amma da ya kwasowa kansa ai ga shi nan a tsugunne. Iyayenta matansu daya, kaf sisters dinta babu mai kishiya. To shi kuma ya gaji k'arin aure dukkan iyayenmu babu mai mace d'aya sai baba na Zaria shima ai ya yi mutuwa ta yi amaryar wajen haihuwa har yanzu kuma bai k'ara ba .

Gabadaya ban yarda da ita ba shiru shirunta ba na alheri ba ne. Tana da saka hannu wajen zamansa haka, ku duba ku ga irin tashen kudin da ya yi. Amma daga rasa aiki ace komai ya k'are ta kankane ta rik'e komai tana juyawa ta hana komai wai ita mai sana'a kuma ma'aikaciya. Na riga na gano makircinta, a hakan kuma idan rabo ya tsaga sai ya yi auren ko tana so ko bata so, ko kuma rabo ya kawar da ita da k'arfin tuwo dukiyarsa ta dawo hannunsa ya samu y'ar yarinya ya aure".

Ummu wacce take bin Sahal ta ce ", Wallahi kuwa Yaya ni fa ga ni nake yi ma ta girme masa".

Ragowan suka ce "Haba dai sai dai su yi sa'ani ko ya fita kad'an".

Hajiya ta ce "kai kuna da shiga sha'anin da bai shafe ku ba, tunda yana zaune lafiya da iyalinsa menene damuwarku ne? Sannan ai mace bata fin k'arfin namiji. Ni dai ban ga laifinta ba yarinyar akwai hakuri da mutunta babba"

Yaya Ture ta ce "Ga ungo ko Hajiya?"

Gabadaya suka kwashe da dariyar iyashege.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Zuciyata ta buga ashe haka suke mini kallo?

Ina fama da wahalar d'anuwansu su suna mini kallon nice sanadin tsiyacewarsa, sannan na danne komai nasa? Menene da shi da na danne? A wanccan lokacin ba yadda ban yi ya sayi gida ko na raianwa ne amma ya k'i. Wanne irin son kai ne haka? Da ransa ba mutuwa ya yi ba har na hana shi abin da yake nasa ne, kuma yana kallona? Allah na tuba, ba dan shi ba, da tuni bansan adadin dukiyar da zan tara zuwa yanzu ba.

Wato duk kokarin kyautatawar da nake yi musu, shima ya yi musu da nawa kudin ashe basa mini kyakkwan zato?

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!

Na furta a hankali. Da k'yar na ja kafufuwana da suka yi mini sanyi na isa kofar falon. Na yi sallama na shiga. Kusa da Hajiya na durkusa ina gaishe ta, ita kuma ta amsa cikin sakakkiyar fuska tare da yi mini barka da dawowa. Na juya muka gaisa da su cikin walwala sun shanye haushina suna ta fadin sannu da dawowa.

Yaya Turai har da tambayar yara wai idan an yi hutu na bari suje Su mata kwanaki.

Maimakon na ji dadin hakan sai raina ya sake bak'i domin Hausa ta yi mini. Wato idan ban amince ba, ubansu bai isa ya kai mata ba.

Na sake hadiye komai na yi yake na ce "Ko yanzu ma kike so sai ki tafi da su, sai su dinga zuwa makarantar daga gidanki, indai kin fada masa ba zai tankwabar da buk'atar ki akan ya'yansa ba".

Na juya ina fadin "Bari na je na yi salla.".

Har na isa bangarenmu zancen zuci nake yi tare da tunanin yadda mu'amala da fuska biyu ta zama ruwan dare a wannan duniyar.

Haka nan son kan da dangin miji mata suke yi akan matar d'anuwansu kullum k'ara hau hawa yake yi tamkar Wutar* jeji( littafin Salaha Abubakar Zaria).Mai bukatar littafin da tsofin littafanta na baya za'a same su in soft copy in sha Allah. 08033773332.*

Haka na sake daure wa ban fada masa abin da na ji suna tattaunawa ba. Amma dai nasan inda na ajiye su, don yadda yake sanyi kalau ko na fada ma ba komai zaice ko ya yi ba, to hakurin shi yafi don nasan a karshe zai iya ce wa zama da sune bana so.

Komai na tafiya mini daidai ta fuskar aikina domin albashina da ake ba ni mai tsoka bai samu tasgado ba, sana'a ce ta samu tawaya domin na fi karfafa a Kano. Amma nan din ma ina dan yi kullum kuma abin gaba yake yi ba baya ba.

Dawowata Katsina ya kara kusanta ni da Abida da kuma Basma Maska Maman Abdul. Duk weekend Abida take turo mini d'iyata da nany dinta su yini a wajena. Tana girma kammaninmu na sake yawa, banbancina da ita na fita haske duk da ba bak'ace irin Abida ba tana da d'an haske irin na Yaya Sulaiman.

Sam bata mini k'iwa lafiyayyar yarinya mai cike da kuzari rarrafe take yi, komai ta kama sai ta mik'e.

Bamu cika wata biyar da komawa Katsina ba aka musu rabon gado. Inda muke zaune ya fito a na kaninsa da suke ciki daya autan Hajiya.

Shi Baban Amrah inda Hajiyarsu take zaune ya gada.

Wata daya a tsakani aka mai waje ya sanar masa watanni biyu masu zuwa aurensa kuma a nan yake son zama.

Duk da nasan sharrin Yaya Turai ne amma dadi ne ya lullube ni domin tamkar akan k'aya nake zaune haka nake jina a cikin gidan.

Na tabbatar ba yadda zai yi ya tashi uwarsu kamar yadda kaninsa ya tashe shi. Gara na yi nesa da su tun basu k'ure hakurina mun fara tashin hankali ba.

Su ko tunanin inda zai samu muhalli cikin k'ankanin lokaci basu yi ba, na yi murmushi don tozarcin dai ba ni suka yiwa ba d'anuwansu suka jefa cikin cankacakare.

Sai dai cikin ikon Allah auren ya fasu dan haka tashinmu ma ya fasaya.

Duk da ni so na yi na kama mana haya mu tashi din din na gaji da gutsuri tsomarsu.

Ni dai na dinga mamakin yadda zartar da hukunci na gaskiya irin na Hajiya baya tasiri akan ya'yan cikinta domin haka take kamar agwagwa duk abin da y'ay'anta suka ce ko suke so bata tursasa musu. Wannan duniya cike take da kalubale kala kala ko ina ka buga babu dad'i.

Don ba dan auren ya watse ba da tabbas zuba ido zata yi a tashi Sahal.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: da Abida, Allah ka hana ni kunyata, Allah ka taya ni rikonta Ubangiji ka sanya soyayya da tausayi a tsakanina da wannan yarinyar, Allah ina neman tsari da son da zada zai

hana na yi mata cikakkiyar tarbiya, Allah ka so Abida ka so Yaya Sulaiman, na gode sosai Allah ya saka muku da alheri ."

Duk taurin ran Abida sai da ta yi hawaye yayin da Yaya Sulaiman ya yi shiru idanuwansa sun fito sosai.

Tunda na saka hannu na karbi Farha ta kwanta a kirjina barci ya sure ta. Basu wani jima ba suka tafi jikinsu a sanyaye.

Sai me ba sai Baban Amrah ya tada sababin dan me zan karbi rik'o babu yawunsa?

Na sassauta na ce "Ni dai nasan ba zan iya tuna adadin sau nawa nake fada maka Abida ta bani abin da ta haifa tun shekaru masu yawa da suka shud'e watakila ma tun kan mu yi aure."

Da kumfar baki ya ce "Saurara baiwar Allah ai ni duk dauka na yi labari ne irin na k'anzon kurege."

Na yi yak'e tare da ce wa "Yanzu sai ka gane gaskiyar lamarin da girman sha'aninsa."

Ya tunzura ya ce "Ki mayar mata da 'yarta da ranta da lafiyarta ba zan rike mata y'a ba alhalin ba mutuncina take ga ni ba, ita idonta da kwalli ta kawo mini d'iyarta gidana? Ko yanzu na girmane a idonta?"

Haka kawai na kufula na ji zuciyata ta yi nauyi tare da wani irin fishin da nake neman tsarin Allah a kansa.

Na dago muka hada ido. Na ce "Farha d'ya ta ce da Abida da Sulaiman suka haifa mini. Za ta zauna da ni a duk inda zan rayu ko da kuwa cikin ramine. Idan har kana da matsala akan zamanta cikinmu to kawai ka dauki mataki amma ba zan mayar da ita ba, domin ni zan rike ta ba kai ba, ka sa ni!

Ganin na tunbatsa da fushi sai ya yi maza ya sassauta ya ce "Yi hakuri Billy gabadaya an shafe mini ce war d'iyar Sulaiman ce. Nima ai d'iyata ce zan sakata cikin ya'yana zan taya ki sonta, huce uwar Amrah! Amma idan ta uwar iya zan daka ko kallon inda yarinyar nan take ba zan yi ba.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Watanni uku*

Gabadaya hankalin musulmai ya koma kan shirye shiryen wata mai alfarma na azumi. Ni da Abida muka had'a kud'i kamar yadda muke yi muka yiwa su Baba hidimar neman albarka.

Muka yiwa iyayenmu mata d'inkuna.

Farha ta warware kamar ba ita ba, bata yi mini kuka sai da dalili, sai kuma idan har ta ganni bata yarda da kowa sai ni.

Mai aikina ita take kula mini da ita idan zan je wajen aiki. Ranar da ba zan jima ba na saka ta a gaba mu tafi.

Tun kafin azumi ya kama na kammala yi mana d'inkuna ni da yara har da shi ogan na yi mana ankon shadda.

Karon farko da na fara jin haushin suturar da nake siya masa. Don kuwa rabon da ya shigo mini da wani abu a leda da zummar ya siyo ya kawo gidansa ko da kuwa karas ne ko yalo na manta don kuwa shekarun da yawa. Bare maganar sutura. Shi ya ji a jikinsa ko y'an gwanjo ya siyo ya kawowa yaransa zan ji dadi suma su ji dadi amma sam baya yi, ban da Maman Zaria da take aikowa takwararta Amrah kayan sallah ba wanda yake yiwa ya'yansa kyauta da sallah duk danginsa. Dukkan kayansu daga ni sai dangina. Kuma ko d'ar baya ji, ya riga ya sanagarce ta bakin Abida. Don sai nake ganin tamkar yana ganin hak'kin kula da iyalinsa ya sauka daga kansa ne. A kullum na zauna mamakinsa ke kama ni, ta yadda baya damuwa ya tashi ya nema, ba kuma ya jin kunyar taba kudina duk da hidimar rik'e masa gida da nake yi tsawon lokaci. Abida kadai ta fahimci halin da nake ciki , a cikin dangina sai ko Yaya Sulaiman ban taba jin kuma sun fadawa kowa ba.

Na zama abin misali a wajen su Baba. Duk wacce ta je da gidan da sunan bacin rai sai an buga mata misali da ni.

Fadi suke yi "Bilki ce tunda muka aurar bata taba zuwa ta kawo mana matsalar miji ko ta danginsa ba, shekara da shekaru tana zaune lafiya da dadi ba dadi dai tana zaune abinta, ku dinga koyi da ita mana."

Sannu a hankali ido ya dawo kaina ana mini kallon na n taki sa'a mijina ba sawa ba fitarwa yasan alheri, ni kam na dace ba ni da matsalar miji da ta danginsa.

A duk sadda suke irin wannan washin yake nake yi domin ni kadai nasan me nake fuskanta a aurena. Kawai hakuri nake yi kan hakuri. Allah ya sani ina son Sahal da dukkan nak'asun da yake da shi. Dan Allah nake sonsa shiyasa ban gajiya da zamana da shi ba.

Watan azumi ya kama dukkan alummar musulmai aka tsunduma ibada tare da kankan da kai wajen mahaliccinmu.

Ana jibi sallah Yaya Asad ya dira a Funtua tare da iyalinsa akan zasu yi sallah a gida.

Haka Yaya Usman.

Dan haka Abida da Yaya Sulaiman ma suka tafi ana gobe sallah.

Ni kaina so nake ace na tafi sai dai ba zai yiwu ba.

Amma washegarin salla na tafi ni da yara.

Gida ya cika aka yi ta dabdala cikin jin dad'i.

Uku ga salla kusan kowa na gidan an hadu idan aka cire Yaya Munira da bata K'asar.

Yaya Salaha da Yaya Hamida sun iso don yau ake taron da muke yi duk sallah tunda a gobe su Yaya Asad da Yaya Usman zasu juya garuruwan da suka fito.

Wannan yinin da muka yi na cikin ranaku masu dadi da ba zamu manta ba. Don kuwa itace ranar karshe da muka hadu cikin walwala da begen junanmu, kafin ibtila'in da ya fado cikin zari'ar ya tarwatsamu gabadaya.

Tare da dukkan iyayenmu hudu aka yi walimar cikinmu suka zauna suka ci abinci tare da mu.

Baba Babba ya dinga nasiha Yana fadin "Ku kadai kun ishi junanku, ku yi hakuri da sha'anin rayuwar nan, duk halin da kake ciki ubangiji ya sani, ku yi juriya ku zama masu afuwa! Ku yi kokarinku ku zama masu yin hakuri dan Allah. Idan masifa ta same ku to ku yi hakuri na gaskiya ku barwa Allah. Idan kun k'i yi kuwa to ku sani zaku yi hakurin dole wanda babu lada a cikinsa tunda mutum bai isa ya canjawa kansa k'addararsa ba.

Tamu ta zo k'arshe ku ninka hak'uri da junanku, ku kula da y'anuwanmu ku sada zumunta da su. Kunsan dai goggoninku kune masu gaishe su, ba sune zasu dinga gaishe ku ba. Allah ya muku albarka gabadaya ".

Jikin kowa ya yi sanyi Baba k'arami kuwa ce wa ya yi ", Yadda muka hadu a nan ubangiji ya hadamu a aljannarsa kamar haka! Muka had'a baki wajen fadin "Ameen Baba".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya numfasa ya ce "Sulaiman kamo mana Munira ita kad'ai ce bata wajen nan."

Nan da nan kuwa Yaya Sulaiman ya ce "To Baba!

Ya fito da wayarsa ya kira ta, bugun farko ta dauka hotonta ya bayyana

Tana zaune tare da ya'yanta da mijinta, cikin nutsuwa ta gaisa dasu Baba. Sannan aka bamu wayar muka cure guri kowa na yi mata magana. A sanyaye ta ce "Yanzu saboda Allah idan ba so kuke na yi kuka ba, menene na wannan hayaniyar bana fahimtar kowa. Ina Bilki da Abida?"

Muka ce "Ga mu Yaya Munira!

Ta ce "Bilki Abida ta kawo miki d'iyarki?"

Na hasko mata Farha da take gefena na ce "Tuntuni, ki ga yadda ta girma kammanina na sake bayyana a tare da ita".

Ta yi dariya ta ce "Kunsa na matsu na zo gida, baku ji dad'in da na ji da na ganku dukkan ku a tare ba". Abida ta ce"Oh Yaya Munira ga ni kike zan kasa cika alk'awari ne? Ko kuwa so kike yanzun ma ki nuna kin fini son Maigado? Ki daina shigoa tsakaninmu don ke ce da kunya!

Aka kyalkyale da dariya gabadaya. Daga nan ta gaisa da Su Yaya Salaha aka mikawa Yaya Asad wayar, haka aka dinga bawa y'an mazan d'aya bayan d'aya sai da ta gaisa da kowa. Daga nan aka yi sallama da Yaya Munira da ahalinta.

Anty Rukayya matar Yaya Asad tana cikinmu tamkar ba suruka ba, Khadija da Aysha sun kammala sakandire a wannan shekarar. Yayin da Hafsina take aji biyar na sakandire sai kuma takwarata Bilki a aji uku na k'aramar sakandire.

Amal ta kammala primary, sai kuma Noor mai shekaru uku.

Kallo d'aya zaka yiwa ya'yansa da matarsa ka gane kud'i na amo a jikinsu domin ba ya yiwa iyalinsa k'wange, ado suke yi na alfarma k'warai da gaske.

Dukkanmu kowa na cikin wadata da rufin asiri.

A wannan zama aka yi maganar auren Ansari da yake so iyaye su shiga maganar.

Yaya Farouk yaransa biyar na Yaya Usman uku. Su Saddiqa da Anisa kowa da nata yaran.

Na kalli yadda muka cika harabar gidan namu mu da ya'yanmu mun zama gayya guda.

*Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke da kyau da nagartar.*

*Gunis hijab ado cikin wayewar addini da rayuwa*

*08163761797*

Washegari Yaya Asad ya fara tafiya don Kaduna zasu je su hau jirgi zuwa Lagos don shine (D.P.C)Deputy police commissioner na jihar. Saddiqa da take Kaduna ta shiga motar da aka turo masa.

Kud'ad'e masu nauyi ya turawa kowannenmu a cikin asusun da sunan barka da sallah.

Kafin yamma kusan kowa ya tafi ni da su Abida ne muka rage akan sai gobe zan bisu mu tafi. Farha tunda ta ga Abida ta makale mata, idan kuma bata ganta ba to tana makale a jikina. Yayin da Abida take kawaicin kin daukarta har sai na ce "A a dauke ta mana kada ki saka mini yarinya kuka".

Washegari muka tafi muka bar iyayenmu da kewa.

Har gida suka kaimu sannan suka tafi nasu gidan.

Ga mamakina Farha bata yi kukan zata bisu ba.

Ranar alhamis da yammaci muka riski mummunan labarin da ya gigitamu gabadaya.

Baba Karami ya zo taron da ma'aikatrsu ta shiryawa tsofaffin Daraktocin da suka rike maaaktarsu. Yaya Farouk ne ya kawo shi tunda tuni ya yi ritaya ya koma gida Funtua gabadaya.

Sun kammala zasu koma juyin duniya motar ta k'i tashi. Ganin haka Yaya Sulaiman ya ce "Bari ya kaisu sai ya dawo, idan dare ya yi masa ya dawo gobe. Sun zo daidai... daf da Funtua Yaya Farouk ya sauka akan zai yi magana da masu yi masa aikin cire albasa, zai hawo mashin ya k'araso.

Ba jimawa da saukar Yaya Farouk wani mai amalanke ya taho a guje ya shigo musu take motar ta dinga walankeluwa bayan ta daki bijimin sa da k'arfin gaske. Motar bata tsaya ba sai da ta je ta bugi wata bishiyar mangwaro kafin ta hautsina gabadaya.

Kan ka ce kwabo mutanen k'auyen sun yi dafifi suna ta 'kok'arin ceton ransu. An ciro Yaya Sulaiman a sume jini na ta fita a hancinsa da bakinsa yayin da Baba karami aka kasa ciro shi. Ganin hakan ya sanya suka yi dabarar tarar wata mota aka sanya Yaya Sulaiman da wasu zuwa babban asibitin cikin Funtua.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Baba karami kam sai da aka sare gaban motar sannan aka fito da shi sai dai Babu rai ya amsa kiran mahaliccinmu.

Wannan mutuwar na tsaya hakaito muku yadda ta yi mana mugun bugu bata lokaci ne mai yawa. Amma mutuwar Baba ya zama tamkar tafiya da dukkan nutsuwa da walwalarmune gabadaya.

Daidai nan kuka mai tsananin gaske ya k'wace mini, dama lallaba zuciyata nake yi sai kuma na zo inda duk dauriyata dole na koka, dole hankalina ya tashi domin an zo gabar da bana fatan masifar da ta sauko mana ta sauka kan kowanne ahali.

Mutuwa da ciwo da tonon silili take. Allah ka jikan makabantanmu.

Da yake dab da magariba aka yi hadarin labarin mutuwar sai bayan magariba ya riskemu. Cikin tashin hankali na isa gidan Abida.

Kuka muke yi kan kuka ita kam ta tubure a lokacin zamu tafi tunda Yaya Sulaiman na asibiti rai a hannun Allah.

Da k'yar da sudin goshi Yaya Asad ya dakatar damu akan gobe da asuba zai saka a zo a kaimu Funtua.

Barci barawo a wannan ranar bai iya satarmu ba. Gabadaya ni da Abida a rikice muka ainun ba mai bawa wani hakuri. Sai dai na yi imanin Abida ta fini rikicewa. A fili cikin kuka take ce wa "Allah ka kaddara mini na ga Yaya Sulaiman da ransa, Allah na tuba kada a yi mana biyu innalillahi wa inna ilaihir raji'un!

*Bojuwa herbs*

*Oder your kayan mata for women of class*

*Our products are healthy and original*.

*Tested and trusted*.

*Sanyi flusher n zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta Ki*.

*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini later domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zata iya zuba kudi ta saro masu daraja irinsu ba*.

*Duk wadda ta ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*

*Just DM for your order @08033773332*.

Kuka nake yi mai tayar da hankali sosai amma da zarar na kalli Abida sai na ji tashin hankalina na sake rub'anya mussaman idan tana gunji tana rokon Ubangiji kada ya k'addara mata yin takaba a yanzu.

K'arfe shida na asuba motar y'ansanda ta zo ta kwashe mu.

Muka isa muka tarar da kofar gidanmu tamkar zai stage da jama'a.

Haka muka kutsa muka isa. Idanuwan kowa ya yi jajur tabbacin an sha kuka an gaji. Baba Babba kuwa gabad'aya ya rikice baya um baya umum ya zama wani iri k'arfin imani ya hana shi ya shiga cikinmu ya yi ta rafsa ihu, don tabbas an masa mutuwa mai gigitarwa. Mami kuwa sosai take sowa da k'yar aka samu ta koma yin na sharb'e.

Hankalinmu bai dawo ba sai yamma aka tafi asibiti wajen Yaya Sulaiman. A can muka tarar da Abida tana zaune duk ta fige ta lalace. Kasancewarta likita kuma ta yi aiki a wajen ya sanya ba'a shata mana layi wajen shiga wajensa ba. Jikinmu ya sake yin sanyi a lokacin da muka halin da yake ciki. Yana kwance bai san inda kansa yake ba.

Yanzu haka sun tura shi asibitin

K'ashi na dala. Don ya bugu sosai.

Tashin hankalin da muke cikinsa k'warai ya tsananta.

Ranar da aka yi sadaka uku aka tafi da Yaya Sulaiman asibitinn Dala cikin Kano.

Cikin k'ankanin lokaci gabadaya aka gigita mana nutsuwa da walwalarmu gabadaya, don Baba Babba ma a kwance yake ana ta kara masa ruwa.

Dukkan ahalinmu kowa ya bar inda yake ya taho gida. Daga Funtua kuwa aka d'unguma Kano nemawa Yaya Sulaiman da har lokacin ba'a san matsayin lafiyarsa ba, tunda asibitin dala ma sun ce sai an hada masa da ganin likitan kwakwalwa don ya bugu a kai. Ganin hakan Yaya Asad ya ce Farouk da Abida su shirya zasu tafi Germany ya ga likitoci a can, tunda a can ya yi karatu ya kuma yi aiki na shekaru zai samu kulawa ta mussaman.

Wata guda yana asibitin cikin coma sannnan aka samu visar tafiyarsu. Gabadaya bama cikin nutsuwa sai dai su Yaya Asad sun koma wajen aikinsu. Kan dole muka hakura muka bi Baba

da adduar rahama, aka mayar da hankali wajen neman lafiyar Yaya Sulaiman da a yanzu muke cikin tashin hankali ganinsa tamkar gawa.

*Dafatan zaku gyra zama don yanzu ne zamu kutsa cikin danbarwar labarin. Ku nutsu sosai, ku bi sannu a hankali har zuwa inda zn karkare don kuwa yanzune abin da labarin yake tafi da shi zai fara.*

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Su Abida sun isa ƙasar Germany tare da Yaya Sulaiman, sun dai yi waya damu sun sanar damu isar su amma tun bayan nan ba mu sake ji daga gare su ba, ni kaina idan na k'ira wayar Abida ba na samu, da man Yaya Faruku ne ya kira ni a lokacin da suka sauka a k'asar. Su suna can mu kuma muna nan amma zullumi bai bar mu ba, mun san ce wa mun rasa Baba ƙarami ya tafi in da har abada ba zai dawo ba, amma zullumin da fargaban halin da Yaya Sulaiman ke ciki ke nurƙurkusan dukkanmu, kowa ka yi waya da shi jikinsa a sanyayaye ba karsaashi ba farinciki.

Mami kusan ko da yaushe muka yi waya da ita cikin kuka take, haka muke ta kwantar mata da hankalin ce wa ta cigaba da addua in sha Allahu Yaya Sulaiman zai warke. Amma ita ga ni take yi kamar shima ɗin kamar Baba karami ne rasa shi za mu yi, ni kaina karfin hali na ke yi amma a yadda aka tafi da Yaya Sulaiman bai san wanda ke kansa ba kowa ma ya sare amma saboda kar na zama raunin Mami ya sa na ke daure zuciyata ina nuna mata da ikon Allah Yaya Sulaiman zai tashi da ƙafafunsa.

"Umh Bilki, shima rasa shi zan yi, rasa shi za mu yi kamar yadda muka rasa Babanku."

Kalaman Mami ke nan a duk lokacin da muka yi waya da ita shi ya sa in muka gama waya sai na zauna na ci kukana na ƙoshi ba mai lallashina. Domin Har da tausayinta ke nuk'urk'usata, mutuwar miji da rashin sanin makomar rayuwar d'a tashi guda ba k'aramin alamari ba ne.

Baban Amra lokacin farkon faruwan lamarin ya kula da ni, ya tausaya mini,amma tunda aka fara nisa da mutuwar shike nan ya janye tausayawar. Kullum sukuku na ke, ga ciwon mutuwar mahaifi ga zullimin makomar lafiyar Yaya Sulaiman.

Amma sai ya kalle ni ya ce

"Ki k'arantawa kanki wannan damuwar fa duk ba mafita ba ce, hakuri da addu'a shi ne mafita. Allah ya jiƙan Baba shi kuma Sulaiman Allah ya tashi kafaɗun sa."

Na sani gaskiya ya fada, kuma shi zuciyarsa d'aya yake fadin hakan. Amma ni so nake ace cikin taushi da laushi tare da kulawa zai dinga fada mini, ba wai ya fada ya cigaba da uzzirinsa ba.

Tun da na dawo ba na cikin sukuni da walwala, hakan bai hana shi kallo ko charting ba, har ga Allah na ji zafin sa ko dai bai taya ni kuka ba ai ya taya ni alhinin halin da na ke ciki ni da zuciyata amma bawan Allah nan da wuri ya wartsake.

Alhalin lokacin da nasa tsohon ya kwanta dama mun shafe fiye da wata ko talabijin bamu kunna ba. Ba Shi da sukunin yin kallo dan haka nima na haramta mana ni da yara dan taya shi jimami, amma abu ya zo kaina, na ga daban. Matsanancin mamakinsa kullum k'ara ara yi mini tsamari yake yi tare da tunanin mene matsalar ne?

Basmae kullum sai ta kira Ni a waya tana sake kwantar mini da hankali. Duk bayan kwana biyu sai ta zo ta debe mini kewa tare da ba ni hakuri tabbas ita ɗin ƙawar alheri ce.

Baba Babba duk dakiyarsa wannan lamarin ya raunana shi ya gaza, ko a waya na k'ira shi yadda na ke jin sa wani sanyi sanyi ba na jin daɗi, yana gida ba ya zuwa ko'ina lalle mutuwar Baba karami ta raunana kuzarinsa sosai Momi ce ma in muka yi waya da ita na ke jin karfin gwiwa domin ƙwarin da tabbaci ta ke bamu da cewa Yaya Sulaiman zai warke, mu ma kuma muna fatan haka in sha Allahu.

Tun tafiyar su ba a sake jin su Yaya Faruƙu ba, sai bayan kwana goma sannan Yaya Asad ya kira Baba Babba ya sanar da shi halin da suke ciki, ashe shi suna magana da shi, mune suka rufe hanyar sadarwa da mu, shi kuma da ya ke da aljihunsa ake yin komai, sannan a matsayinsa na babba suna k'iransa suna kuma sanar da shi halin da ake ciki.

Alhamdulillah likitoci sun yi gwaje-gwaje akan ƙwakwalwar Yaya Sulaiman jini ne ya taru a wani gefe in da aka gode ma Allah bai taɓa ƙwaƙwalwarsa ba, tuni an yi masa aiki

sannan in da ya ke da karaya sun É—ora shi sun kuma ba da tabbacin a kowani lokaci zai iya farfaÉ—owa, a bakin Yaya Muneera na fara jin labarin sosai n samu sassaucin zullimin da nake ciki ba ma ni kaÉ—ai ba dukkan mu wannan labarin ya wanke kaso mafi girma daga cikin damuwarmu. Sai bayan kwana biyu na samu mgana da Abida yadda na ji muryanta cikin sukuni ya sa na samu tabbacin labarin da muka samu gaskiya ne.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Maigado an gano matsalar Yaya Sulaiman na masa aiki a kansa sannan an masa na k'afa dazu!

Abin da ta fara faÉ—a mini ke nan ko gaisawa ma ba mu yi ba, farinciki ya cika ni na yi hamdala a fili da sarari, mun É—an jima muna hira, tana tambayana ya su Mami da mutanen gida?

Na ce "kowa lafiya da godiyar Ubangiji, a baya dai muna cikin zullimi amma yanzu sai godiya. Ta tambayi yara, na ce su suna nan lafiya, mun É—an jima muna hira ta ce mini za ta É—an kwanta tun zuwan su ba ta samu barci ba.

Ranar yini na yi murna da farinciki na kira Basma na faÉ—a mata itama sai murnar farinciki take yi. Baban Amra ma da rawan jiki na tare shi da labarin har sai da ya É—an rumgume ni yana faÉ—in" Alhamdulillah."

Nima na riƙe shi ina mai bayyana farincikina har fararen haƙorana suna bayyana tsabar murna.

Yara ranar kaf sun san Mahma na cikin farinciki saboda yadda na yini tare da su. Mutuwar Baba karami ta gigitamu k'warai da gaske mussaman da ba jinya ya yi ba. Sai kuam aka had'a mana da kila wa Kala na rayuwar Sulaiman dole dukan sai ya yi mana yawa, ace ba Baba ƙarami sannan ba Yaya Sulaiman, tabbas zukata za su raunana sai dai da ya ke Ubangiji ne mai yin abin da ya so, idan ma hakan ne ya so ya faru sai dai mu yi haƙuri ba mu isa mu ja da hukuncin Ubangijinmu ba. Labarin farfaɗowar Yaya Sulaiman ya zo mana da kwana ashirin da isar su ƙasar Germany. Yaya Faruku ne da kansa ya kira ni ya sanar da ni, bayan shi Abida ma ta sanar da Ni an kawo shi ɗakin hutu amma dai yana ta barci ne ba su samu shiga wajen nasa ba. amma tabbas ya dawo hayyacinsa. Na samu K'warin guiwar tafi ganin Mami tunda an samu cigaba sosai . Hakan ya sa na ce wa Baban Amra gobe ina son zuwa gida bai hana ni ba. Washegari na tattara yara muka zo Funtua kamar na sa ni gida cike da matansu Yaya Faruku da yara ana ta barka da arzikin da aka samu.

Baba Babba kuwa kofar gida ya fito aka tara masa almajirai ya riƙa rabon kuɗi sadaka domin godiya ga Ubangiji, mu kam mu a cikin gida kowa ka ga ni ya d'an samu k'warin jiki har Mami na ga ta d'an samu kuzari.

Yaya Asad daga can lagos ya nemi visa sai dai kawai da suka kira mu Video call suka haɗa mu da Yaya Sulaiman muka gan shi a can kwatsam ba tare da kowa ya san tafiyarsa ba. Allahu Akbar Allah mai gagara misali, sai ga Yaya Sulaimam zaune a kan gadon majinyata ga rigarsu ta asibitin kafafunsa da ya samu karaya an ɗora shi kansa da wani bandeji, amma yana zaune yana mgana kamar ba shi ne aka kai shi rai ƙwaƙwai ba, kowa ya gaishe shi kuma ya amsa sannan ya kira sunan kowa alamun dai ya dawo hayyacins sosai a Allah abin godiya.

Ni ina ganinsa sai kawai na ji kuka ya zo mini. Farha na jikina ta lafe. Abida ta leƙo da kanta tana kallona ina ta sharan ƙwalla, sai kawai ta kaɗa kai kafin ta ce" Sola ke wai me ya sa ba kya girma ne? Gaban ɗiyar ta ki, kike b'are baki kina kuka?

Ina jin ta ce haka sai na sake fashe wa da kuka don gabad'aya tausayinsa ya yi mini k'awanya Bai san mahaifinsa ya rasu ba.

Baba Babba ne ya kalle ni kafin ya ce" Bar kuka Maigado yi magana da É—ant'uwanki kin ji!

Na gyaÉ—a masa kai, kafin na yi magana Yaya Sulaiman ya murmusa kafin ya ce" Bilkkina ba ga ni kin ganni ba? Ki daina kuka kin j! Kar ki saka Farha ta fara gata nan idanuwanta ya kawo ruwa." Sai da ya faÉ—a na juya ina kallon Farha ta kusa kukan itama.

"Ya jikin ka Ya Sulaiman?

"Na ji sauƙi Bilkina. Alhamudulillah mun gode ma Allah"

Kallonsa kawai nake yi duk ya rame ya yi baƙi sai na tuna dr rasuwar Baba ƙarami kawai sai na sake fashewa da kuka kamae wata ƙaramar yarinya na ɗauka bai sani ba ashe ya sani sai ji na yi yana ce mini "Maigado ya ƙarin haƙurinmu!? Allah ya jiƙan Baba da gafara Allah ya kyautata makwancinsa"

Gabaɗaya muka amsa da Amin Yaya Usman ne na ji yana faɗa mini Yaya Asad ne ya sanar da shi bayan ya isa a jiya. Su Abida ba su samu wannan ƙarfin zuciyan sanar da shi rasuwar Baba ƙarami ba.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Har wayar ta gama zagayawa hannun kowa ban daina kuka ba, Mami da Momi suna ƙwalla amma na farinciki ne Baba Babba faɗi yake yi" Allah na gode maka da ka karɓi ɗan'uwana, sannan ka bar mini ɗana Ubangiji na gode maka."

Muryarsa ta karye mutuwar Baba ƙarami ta sake dawo mana sabuwa dama tana jika, ba ta gama fita ba, kuma har abada ba za ta fita ba, ba za mu manta ba, don da yanzu ina tunano abubuwan da suka faru amma ina jin kamar a yau ne muka rasa Baba ƙarami. Mutuwa tana da d'açi, sannan mutuwa mai tonon asiri mutuwar Baba ƙarami ce ta yi sillar ta tarwatsewar gidanmu, kaina na saka a cikin tafukan hannayena duka biyu na sake fashe wa da kuka ina jin wani irin nauyi a samam k'irjin irin nauyin da na riƙa ji lokacin da gidanmu ya hirgitse, Ubangiji na ke fata da roƙo ya daidaita kan ahalina

Na cigaba da hakaito rayuwarmu washegari muka koma gidajenmu cikin sukuni da salama, sannan yanzu muna mgana da su sosai, barin ma Yaya Faruƙu yana yawan kirana saboda har gobe Yaya Faruƙu nawa ne, ina girmama karamcinsa a gare ni. Abida ma muna waya sosai sannan Yaya Sulaiman ma suna haɗa mu da shi, kuma jikinsa sai godiya yana ta samun sauƙi.

Ya Asad sati ɗaya ya yi ya juyo zuwa gida Nigeria. Abida da Yaya Faruƙu za su cigaba da zama tare da shi har sai an sallame shi, Abida ko an ce ta dawo ba za ta yarda ta dawo ba. Baba Babba ya ce a barta ta zauna ta samu ladan jinyar mijinta, ban ɗauka haka Abida ke son Yayana ba sai a wannan lokacin aikin ta ta ajiye ta ta tafi jinyar Yaya Sulaiman kuma da aknsa ya faɗa mini da jikinta da zuciyarta take wahala da shi, kusan ita ke yi masa komai sai na ji tausayinta ya kama ni, shi da man Yaya Faruƙu Ladi farm ne kuma ba matsala akwai masu kula da wajen shi ya sa ba shi da wata matsala.

Gabaɗayanmu mun koma bakin aikinmu tunda hankula sun kwanta ni kuma a gida na cigaba da karɓan aikin snacks sannan a bangaren aikina na W.H.O, mun cigaba da wayar waa da mata kai wajen kula da cikin da raino da kuma muhimmancin yin rigakafi ga yara bayan haihuwa.

Ba tare da shawara da kowa ba Baba Baaba ya fara tattara dukkan wata dukiyarsu shi da É—an'uwansa idan a baya ba wanda ya san shiga da fitar dukiyarsu, yanzu mutuwa za ta yi sillar fallasar komai. Idan a baya dukiyarsu tana haÉ—e ne a waje É—aya ba wanda yasan tsakaninsu yanzu dalilin mutuwa yasa dole komai ya bayyana, ya shiga har bangarenmu ya yi magana da Mami da Ansari tun da Yaya Sulaiman baya kusa.

Ya ce 'an fara tattara dukan abin da Baba ƙarami ya mutu ya bari idan an gama tattarawa lokacin su Yaya Sulaiman sun dawo za a zauna a raba gado domin a sauke masa nauyi, wannan maganar rabon gado, wannan gadon shine silar dambarwan da ta faru a gidanmu dambarwar da ta yi silar da na rasa Abida na rasa Ya Munnera.

Bansan da mganar ba Mami ta kira ni da kanta a waya tana faÉ—a mini abin da yake faruwa.

Sai na ji hawaye ya goce mini, yanzu shike nan mun rasa Baba ƙarami, har ga shi ana mganar rabon gado Allah sarki rayuwa Allah ya kyautata makwancinsa ranar yini na yi kamar marar lafiya. Baban Amrah yana can bangaren Hajiyarsu sai da ya shigo ne ya ganni zaune a falo na shiga zurfin tunani ban san ya shigo ba sai da na ji hannunsa a saman kafaɗata sannan na dawo hayyacina.

"Lafiyarki kuwa?

Ya faɗa yana kallona cikin kulawa, na sauke ajiyar zuciya idanuwana suka kawo ƙwallah, gidan da ma ya yi mini shuru yara sun tafi islamiya, Basma ce ta ce mini za ta shigo to ta kira ni ta ce ta fasa zuwa Baban Abdul ya yi baƙi sai dai zuwa gobe.

"Na sha faÉ—a miki ki daina zurfafawa kanki tunani. So kike na rasa ki na shiga uku?

Kalamansa na ƙarshe yasa sai da na yi dariya, kusa da ni ya zauna ya ɗan rumgumo ni da sigan lallashi yana ɗan buga bayana.

"Komai mai wuce wa ne, Allah ya jiƙan Baba,. Shi kuma Yaya Sulaiman da ikon Allah sun kusa dawowa"

Na gyaɗa masa kai cikin gamsuwa domin na yi lamo a jikinsa na kuma karɓi lallashinsa, ban san me yasa ba sai gani ina bashi labarin wayar mu da Mami, ina ƙoƙarin mai da hawayen da suka cika mini ƙwarmin idanuwana, amma ga mamakina sai da ya ɗago ni cikin nuna murnarsa kamar na ba shi labarin wani abin daɗi.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Ma sha Allah."

Ya faɗa yana kallona, na yi kasaƙe ina kallon sa, faɗa masa fa na ke yi mutuwar mahaifina ta dawo mini sabuwa saboda an yi maganar rabon gado, amma yana kallona da farinciki a muryansa har ya bayyana a saman fuskarsa.

"Gaskiya Baba Babba ya yi tunani kuma ya cika ɗanuwa na gari, gwara a raba a bawa kowa haƙƙinsa haka addini ya tanadar"

Ni dai har ya gama magana ya tashi, ban sake wani motsi ba me ya sa yake murna? Saboda na ce za a raba mana gado, a kullum al'amuran Baban Amrah mamaki yake ba ni, ba ya gyarawa kuskuransa sai ma ƙoƙarin sake wasu yake yi, ajiyar zuciya na sauke amma abin da ya yi ya tsaya mini cak a zuciyata sai dai ban iya faɗa wa kowa ba sai washegari da Maman Abdul ta zo, ban yi mata wata magana ba, saboda na

san ko na faÉ—a mata sharhi da magana kawai zan jawowa kaina ita da Abida har gobe ba sa iya boye adawarsu akan Baban Amrah shi yasa na yi shuru da bakina amma dai na ji daÉ—in zuwan ta mun yini tare muna hira kuma ta saka ni na saki jikina har na manta damuwata.

Tun daga lokacin da na yi ma Baban Amrah maganar rabon gado ya dame ni bini-bini sai ya tambaye ni wai ya ake ciki ne har yanzu ba a kiramu ba? Tun ina mamakinsa har na daina na gama fahimtarsa kuÉ—in kawai yake hange, tun da ranar ma muna karyawa a gaban yara yake ce mini." Kai gaskiya za ku sha kuÉ—i Balki, ko gidan gonar nan kaÉ—ai ai sai ta yi miliyan dubu da doriya."

Kawai sai na saki baki ina kallonsa, au shi da man ya kwanta ne da gidan gona yana lissafin zan samu kuÉ—i ya sake komawa ya naÉ—e hannu ni kuma na sakin masa kuÉ—i ina masa hidima shi da Æ´aÆ´ansa da iyayensa, tun da na riga na sabar masa, a lokacin ban ba shi amsa ba sai da ya sake yi mini zancen kai tsaye na faÉ—a masa gaskiya.

"Gidan gonar da kake mgana ba ta Baba ƙarami ba ce shi kaɗai, duka dukiyar tare ne da na Baba Babba. Ko mu y'ayansu bamu san yadda dukiyar su take ba."

Tun daga nan na kashe masa baki amma duk da haka bai daina tambayata har yanzu Baba Babba bai kiramu ba?Ranar da daddare har mun kwanta ya sake yi mini mganar na harzuƙa na miƙe ina faɗin" Bai kiramu ba, don Allah Baban Amrah ka ƙyaleni da wannan maganar. Mu fa ba gado ba ne a gabanmu mutuwar mahaifinmu ta fi yi mana ɗaci, sannan lafiyar Yaya Sulaiman ta fi damunmu fiye da tunanin wani gado."

Ganin na buɗe masa wuta ina masifa sai ya yi ƙasa da murya yana faɗin" Sorry ni ma ai mutuwar tafi damuna amma ina so na ga an sauke ma Baba ƙarami nauyi, ai Allah ne ya ce a raba ko Bilkis? Kuma ke matata ce duk abin da ya shafe ki ai ya shafe ni."

Saboda haushinsa da ya kama ni ko magana ban yi masa ba na koma na kwanta na juya baya ya san ya yi laifi shi ya sa ya mirgino ta gefena yana kiran sunana, ta gefen kunina da dama yana yi mini raɗa, da ya ke ya iya kalamai sanyaya zuciya Idan ya so, tuni ya shawo kaina da azama muka tallafi juna sai dai kamar ko yaushe bai wani daɗe ba, ya matsa gefe ya fara barci ni kuma ya bar ni kwance cikin hawaye, na daɗe ina kallon shi ina tunanin wai haka sauran maza suke? Ba su damu da damuwar matansu ba sai kan su? Ban gane komai ba amma ba ni da yadda zan yi haka na ja jikina na shiga tiolet na yi wanka na tsarkake jikina na zo na sauya rigar barci na raɓe ta gefensa na kwanta ina tunanin makomar rayuwata, shike nan ni a haka zan ƙare, ba zan iya ɗorar da komai akan jin daɗin aure ba, a wajen ana mini kallon mace a cikin sahun matan da suka yi dacen samun gwarzon miji, kyakkwa Kuma marar hayaniys, ni kuma a cikin gida ni kaɗai na san inda ɗakina yake yi mini yoyo, na daɗe kafin barci ya kwashe ni cikin tunani da zullumi.

Tun da muka yi haka da Baban Amrah ya kiyaye ni da maganar rabon gado, nima jin Mami ba ta sake yi mini maganar ba, sai na cire abin a raina sai kwanaki biyu tsakani Ansari ya kira ni a waya yana faÉ—a mini wai Baba Babba shiru har yanzu bai ce komai ba? Takaici ya kama ni amma sanin da na yi Ansari da Mami bakinsu É—aya akan komai shi yasa ban É—ora komai ba amma sai na ce masa" Mu yi hak'uri mu ba shi lokaci watakila bai gama tattara dukiyar..."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Kawai sai Ansari ya tare ni da ce wa" To dukiyar me? Abu ga shi nan a bayyane ai ba a bukatar wani dogon zama."

Mamakin kalamanshi suka hana ni magana ban gama mamakin ba ya sake kwabo wata maganar.

"Wallahi idan ya sake ya cucemu ba za mu yi shuru ba, mun san komai babanmu na da kaso mai yawa a cikin dukiyar nan Mami ma ai ta faÉ—a.'

Ina jin ya ambaci Mami nasan daga bakinta maganar ta fara fitowa. Na yi maza na kame bakina tare da fadin "Allah ya kyauta "

Da azama ya ce "Malama saura a zo batun rabon gado wata magana ta taso ki waremu ki je kina marawa bare baya Wallahi kika yi kuskuren yin haka zamu cire ki a cikin jerin Æ´an'uwanmu. Tunda ba ki da wayo ko kadan"

Ni dai ban ce komai ba har muka gama wayar jikina a sanyaye abin da na yi ta gudun faruwansa shi ne ya zo ya faru daga ƙarshe.

*Na ce kuna karatun nazari ko kuwa iya na nishadi kuke yi?*

*Wannan labarin gabadaya fa ban gina shi dan nishadi ba!*

*Dan haka a yi hakuri a nutsu a gane me nake son a fahimta.*

Na daɗe ina tauna maganganun Ansari a cikin zuciyata amma ban iya mgana da kowa ba Yaya Sulaiman ne zai taya ni ga shi kuma ba ya kusa duk da yana ta samun lafiya. Har an kunce karayarsa guda ɗaya muna saka ran dawowarsu nan da wata ɗaya. Amma ni kaɗai ba zan iya ba da Mami ba, balle ga Ansari shima ba shi da sauƙi in dai ga lamarin yan gidanmu ne. Mami dama tun Baba ƙarami na raye take da wannan adawar, bata samu ikon fitowa da ita bane. Ballatana yanzu da ba ya raye zata iya aikata komai, ina ta tsoro amma sai na dake, nake ta adduar Allah ya kaɗe fitina duk wata guguwar da za ta taso ta dumfari zuru'armu Allah ya yi kare mu da ita. Ashe ba zamu tsira daga wannan guguwar ba.

Ana cikin haka ne gutsiri tsomar ƴan'uwan Sahal a kaina ya fara isa ta, yanzu har ta kai a kan fuskata ake shaguɓa mini magana da ce wa na babbake komai, na sakawa d'anuwansu mutuwar zuciya, kamar ni ce na hana shi ya fita ya nemi aiki, shi ya zaɓarwa kansa zaman gida, amma ni ba ruwana a ciki. Daga baya har Hajiyarsa ma na ga ta sauya mini idan na shiga gaishet a bayan gaisuwa ba ta sake ce mini komai saɓanin a baya zamu zauna mu yi ta hira. Na fara fahimtar ta fara ɗaukan zugar ƴaƴanta akan ni ce sillar rasa aikin ɗanta yana zaune a gida, sun manta Allah ne meyi, gutsuri tsomarsu bai bai dame ni ba, don ban fasa fita aikina da uzurorina kuma ban fasa hidima da gidana da yara na ba, tunda saba ya ma zame mini jiki. Na lura burinsu ya samu aiki ya ƙaro aure, don na gane ban gama da shi ba, ni ko a raina na ce ai ba zai iya rike gida biyu ba, gida ɗayan ma ba iya rike shi ya yi ba ballantana biyun amma su duk ba zasu san haka ba, tun da wani sirrin a lulluɓe yake ko an bayyana ba kowa zai iya fahimtar haka ba.

Wayar da Ansari sati É—aya ne tsakani Baba Babba da kan shi ya kira ni ya ce na nemi izini wajen megidana na zo Funtua ko kwana É—aya ne yana son ganina. Hankalina ya tashi amma tunda ya tabbatar mini da komai lafiya sai na samu natsuwa, in tambayan Baban Amrah ya amince washegari ni kaÉ—ai na taho funtua har Farha a gida na bar ta tare da Baban Amrah, sai da na isa gida na fahimci dukkan Æ´an bangaremmu ne Baba Babba ya kira ba makawa akan maganar gadonmu ne, ilai ko haka ne, a falon Mami ya tara mu gabaÉ—ayanmu, daga Yaya Hamida da a lokacin sun koma Kano da zama, sai ni da Ansari ne manya a wajen. Ko Momi bata shigo wannan zaman ba daga mu sai mahaifiyarmu sai Baba Baaba.

Bayan zama da addu'ar Rahma ga Baba ƙarami. Baba Babba ya fara jawabi kan dukiyarsu da take haɗe a dunk'ule.

Baba Babba ya sake tunasar damu basu raba gadon mahaifinsu ba, sannan ba su raba na mahaifiyarsu ba sun cure su waje ɗaya suna kasuwancinsu tare a lokacin kuma yarda da zumumci hadi da aminci ba su yi tunanin yin komai a rubuce ba, basu kuma taɓa tunanin wata rana mutuwa za ta gifta da har za a bukaci haka ba, to bayan zama da kuma ƙiyasun duka dukiyarsu ya yanke shawaran kawai za a

rabata gida uku ne, shi ya ɗau biyu tun da kason shi ya fi yawa a cikin duka samun su, sai sauran kashi ɗaya a barwa Baba ƙarami a rabata Ga iyalinsa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sannan kuma gidan da muke ciki bangaren da muke halas malak ya zama mallakinmu shi kuma zai riƙe bangaren da suke ciki sannan ladi farm kuma za ta fito a cikin na shi sauran kaddarorin ne a matsayin na Baba ƙarami.

A wajen sai da Mami ta ce ba ta gane ladi farm zai tashi a na iyalan Baba ƙarami ba, ni ce na riƙa taɓa kafarta sai ba ta ƙara magana ba Ansari ma bai yi magana ba saboda ƙwarjinin Baba Babba, daga ƙarshe ya cr za mu jira dawowar su Sulaiman kafin a sake zama, kafin lokacin zai yi magana da wasu lauyoyi da malaman addini da zasu yi kiyasin dukiyar sai a taru waje ɗaya a raba komai cikin adalci. Baba Babba na fita daga bangarenmu Mami ta mike ta ce ba zai saɓu ba.

Ansari ma ya miƙe yana faɗin" Haba ji wata tsatsuniya Mami, yana nufin saboda zalunci mu fitar da mu za a yi daga ladi farm? Wannan ƙatuwar gidan gonar ne zai ce tashi ce ita kaɗai wannan ma ai ƙarya ne'

Mami na kaÉ—a kafa ta ce" Daman na san za a rina. Ai zalunci ya shirya dole ya ce haka. To wallahi Tallahi bai isa ba ko da za a yi sharia ne bai isa ya mallake wannan gidan gonar ba.."

Ansari ya kaÉ—a kai kafin ya ce" Tabbas Mami, sai dai a yi sharia har mahadi ya bayyana amma ba za mu yi shuru a cuce mu ba."

Ina zaune gefe na yi tagumi gabana na tsananta bugawa, ina tsoron kar wannan mganar ta kawo mana rabon kai a gabana Mami da Ansari suka gama yiwa sauran yan'uwana famfo suka hau suka zauna, nima kuma Mami ta dawo kaina ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.

"Shashasha na san daman ai ba za ki yi mgana ba. To ko za ki mutu wannan karon ba zan yi shuru a cuce ni a cuci ƴaƴana ba. Tun da suma dangina sun ware ni ba ni da kowa sai ku gwara ma ku haɗe kai domin mu taru mu yaƙe su mu kwato dukiyarmu."

Sai kawai na fashe da kuka kafin na ce" Haba Mami, haba don Allah wannan abin da kike yi sam bai dace ba."

A lokacin hannu ta saka ta bige mini baki tana faɗin" Za ki ce haka tunda an taɓo ubanki da danginsa, to bari ki ji yadda shima bai yi abin da ya dace ba mu ma kar ya yi tsammanin za mu yi abin da ya ce. Idan yana son gaskiya a raba komai gida biyu ya ɗau na shi kason ya bamu namu kason shike nan sai a zauna lafiya.

"Faƙat"

Ansari ya faɗa sauran ma suka mara masa baya ni ko cikin sharan hawaye na ce" ku tuna fa mahaifinmu ne ya rasu Mami ko takaba ba ki fita ba amma kina hayaniya da faɗa kan dukiyar? Dukiyar da shima wanda yatara ta yau ya tafi ya barta, kar ku manta in da ya tafi yau ko gobe cikinmu wani zai iya tafiya, kuma tsakani ga Allah munsan cewa Baba Babba ya fi Baba ƙarami kuɗi to ba zai zama dukiyarsu an yi raba dai-dai ba in har za mu yiwa junan mu adalci Mami"

Na karishe faɗa cikin ƙanƙantar da kaina amma bai sa Mami ta gane ba sai ma zagina da ta hai yi tana ce mini da ace ba a gida ta haife ni ba sai ta ce Momi ce uwata tsabar yadda bana ƙishinta a matsayinta na uwata. Ansari kuma kamar ya kai mini duka yana faɗin bani da kishin yan uwana, wannan dalilin ya sa a ranar na juya zuwa Funtua ko Momi da na shiga gaishe ta ta fahimci na sha kuka da ta tambaye ni sai na ce kai na ke ciwo, ta yi ta yi na tsaya na kwana na ce gobe ina da fita wajen aiki. Baba Babban ma ban gan shi ba an ce ya shiga ciki ya ɗan kwanta nasan kuma duk damuwar furucin Mami ne, haka na koma gida ina cikin matsanancin damuwa, Baban Amra bai lura da haka ya fara mini wasu tambayoyin da ba su shafe sa ba wai me Baba Babba ya ce mana? Ko mganar rabon gadon ne? Tsabar haushi ko amsa shi ban yi ba sai ya fara faɗa wai ya fahimci yanzu na raina shi sai ya riƙa yi mini magana ina share shi tunda na ga yanzu ba shi kuɗi nike da shi ina masa hidima to ban isa ba har gobe yana matsayin mijina sannan ai kafin ni na fara yin hidima shi ya yi hidimar da ni ganin abin zai koma wata fitinar sai na bashi haƙuri saboda a halin da na ke ciki bana ma bukatar wata hayaniya amma shi ya kasa ganewa abin da ke gabansa kawai ya ke dubawa saboda ba shi da adalci.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Gabaɗaya ba ni da sukuni saboda duka suna bayan Mami da Ansari ne, ni ce kaɗai bana tare da su, shi ya sa suka ware ni jin daɗina ɗaya su Yaya Sulaiman sun kusa dawowa ina tunanin shi ne kaɗai zai taya ni wannan faɗan amma a yanzu kam Mami ta ja tun ga za a yi hatsaniyar da ba a taɓa yi ba akan wannan gidan gonar, ban san cewa shirin Mami ya fara fallasa ba sai da Ya Usman ya zo gidana ma'aikatarsu ta turo shi wani taron bita na kwana uku a garin a katsina shi ne ya kawo mini ziyara. Shi ne yake faɗa mini gida ba daɗi da na ke tambayan shi su Mami.

"Mami ta sauya Balki, ko ni kafin tahowata na shiga bangarenta na gaisheta tana ganina ta tashi ta shige ciki, abin ya É—aure mini kai ahalin na san Mami ta fi kowa zama mu yi hira mai tsawo tare da ita."

Zuciyata ta amsa, abin da na ke gudu ne yake neman faruwa.

"Ayya ka san zafin rashin nan na Baba ƙarami ga kuma rashin lafiyar Ya Sulaiman duk sune suka saka ta zama haka."

Sai ya kalle ni kamar yana so ya fahimci wani abu ni kuma sai na yi saurin kauda wannan zance kar ya fahimci ƙarya na ke yi amma bai bar maganar ba, faɗa mini yake yi Ansari ma yanzu ba ya masa mgana sun haɗu kafaɗa da kafaɗa ya wuce bai gaishe shi ba sannan Momi ma ta ce ta kasa gane kan Mami irin shigan nan da take yi mata da yamma ta ɗan taya ta zama in ta shiga Mami take tashi ta bar mata falon sai dai in ta gaji da zama ta koma bangarenta ta kuma tambayeta ko ta yi mata wani abu ne ta ce mata ba komai.

"Maigado Wallahi gidanmu ya sauya. Ba daÉ—i shi kan shi Baba Babba sai rama yake yi a tsaye yau lafiya gobe ba lafiya."

Cikin tashin hankali na furta" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."

Ya cigaba da faÉ—in" Tun bayan faruwan lamarin nan komai ya rikice, amma ina fatam idan su Abida suka dawo komai ya daidaita. Tun suna saka ran dawowa farkon wata mai kamawa Ya Muneera ma ta ce idan suka dawo za ta zo kasar sai a zauna gabaÉ—aya a tattauna domin magance matsalolin da suke tunkaro mu."

"Allah ya sa."

Na faÉ—a a fili amma zuciyata na rawa, na samu Ya Usman ya tafi ba tare da ya fahimci na san kan zancen ba, ina zance masa kan maganar gado ne, ina zan iya fada masa suna tuhumar mahaifinsu ne da ya yi musu rashin adalci wannan Magana tana da munin a ji daga bakin wani daga cikin mu.

Abin da na ke gudu ne shi ke yake faruwa. Maganganu har sun fara yawo kuma na tabbata Baba Babba shima mganar ta je masa Shi da Momi wataƙilama Yaya Usman har su Ya Asad duk ya sanarwa, kaina na dafe da na ke jin yana sara mini, irin wannan lamarin akwai sarkaƙiya duk yadda kaso ka warware shi cikin sauƙi ba zai warwaru ba. An samu matsala tun farko, an yi abin ba rubutu, idan sun aminta da junansu sun manta suna da mata da iyalai? Sannan sun manta akwai mutuwa, wata rana ƴaƴa za su taso su ɓukaci gadon mahaifinsu, su kuma gidanmu gadone kan gado tunda har na mahaifansu basu raba shi ba sannan ba su yi wani rubutu da zai iyakance ga na wane ga na wane ba, tabbas hakan babban kuskure ne shi yasa abin da Ubangiji ya ce a zarta gwara a zartar saboda gudun fitina.

Ni na ga ni a gidanmu da a ce sun raba gadon iyayensu da tun farko abin da ya faru bai faru ba sannan da ace sun yiwa dukiyar iyaka da rubutu da duk alamrin Bai cukurkude mana ba, kuskuren haka ya jawo mana gagarumin yaƙi, yaƙin da ya zo ya cinye gidanmu kaf, sannan wacce ta jagoranci yaƙin daga karshe ba ta ci moriyar kafiyarta ba.

Sai Allah ya kaimu Monday.

Ayi karatun Lafiya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ni duk a tunanina satin da muka shiga su Ya Sulaiman zasu dawo kamar yadda muka ji, ashe an sauya Yaya Faruƙu ne kaɗai zai biyo jirgi ya dawo sakamakon likitoci sun tabbatar ba zasu sallami Ya Sulaiman ba sai ya fara takawa da k'afafunsa, ba taimakon sanda ko keke, shi yasa suka ce zasu sake riƙe shi nan da wata ɗaya.

Shi kuma ya ƙosa, ya matsu sai ya dawo gida amma tunda Ya Asad ya ji labari ya ce ya zauna ya bi dokokin likitoci domin samun ingantarciyar lafiyarsa. Ya ce Abida za a bari da shi, Yaya Faruƙu kuma ya dawo gida, ko Baba Babba dawo, ya d'an warware tunda dama Yaya Faruk din ne a gari. Anisa ta fad'a mini hakan da muka yi waya tunda ni kaina mun kwana biyu ban yi mgana da Ya Faruƙu ba bai k'ira ni ba, nima ban kira shi ba, ina jin kunya da nauyi domin ina tunanin maganganun da suka fita daga bangaren Ansari shima sun isar masa. Bayan na ji maganar a bakin Anisa ne na yi waya da Mami itama ta sake tabbatar mini da sun yi magana mgana da Ya Sulaiman a cikin satin nan Yaya Faruƙu zai dawo za a bar Abida a tare da shi, fatan samun lafiya na yi masa jikina a sanyaye, na ji daɗi da har muka gama waya Mami ba ta yi mini batun gadonmu ba, nima ban yi mata ba, saboda kwata-kwata ma bana son yin maganar domin ɗaga mini hankali al'amarin yake yi. Har Ansari ban yadda mun sake waya ba, ban kira shi ba shima bai k'ira ni ba, kuma ina da tabbacin haushina yake ji shi ya sa bai neme ni ba.

A bakin Momi da muka yi waya na ji labarin dawowar Yaya Farouk. Na kira ta na gaishe ta sannan na ji yanayin jikin Baba Baaba hawan jini ya rafke shi, likita ne ke jigilan zuwa gida yana duba shi na musamman da Ya Asad ya É—aukan masa.

Jin ya dawo yasa na cire nauyi da kunya na kira shi na yi masa barka da dawowa, dama na tsammancin fiye da haka daga bangaren Ya Faruƙu domin shi karimi ne, haba haban da ya saba yi mini bai ragu ba, mun jima muna waya da shi na ji daɗin labarin da ya bani na Ya Sulaiman da cewa kaɗan ya rage kafar ta ƙarisa warke wa sai a kunce ɗorin wataƙila kafin ma su cike wata ɗaya za su iya dawowa, na ji daɗin bayanin nasa , na ji nutsuwa ta saukar mini,don ba almun ya samu labarin cecekucen da yake ta fita.

Kewa ta kama ni, kewar Abida, kewar wacce zan yi magana da ita na ji sanyi, ta kuma yi mini sassauci idan ta ga raunina ya bayyana. Sai dai duk yadda na matsu da dawowar Yaya Sulaiman haka nake cikin zullimin durowar Abida Funtua ta ji wannan bak'in labarin don kuwa na tabbatar Abida zata jagoranci y'an sashinsu wajen shata layi damu don a bayyane yake yadda Baba Babba ya jarabtu akanta itama haka take sonsa tare da kiyaye daarajarsa, na tabbatar aurenta da Sulaiman ba zai yi tasirin da zata gwada nata wulak'ancin ba.

A fili na furta "Allah mun tuba, Allah ka yafewa iyayenmu wannan gangancin da suka yi da sunan zumunta."

Tsorona Allah kar wannan fitinar da Mami take son jawowa ya yi silan baƙin cikin da zai iya kai Baba Babba k'asa, don kuwa mutuwar Baba ƙarami ta raunana Baba Babba matuƙa raunin da har a muryarsa ya bayyana, gangar jikinsa ya rasa k'arfi da kuzari gabadaya. Dan na rasa madafa sai na tsananta addu'a mussaman a cikin sallolina na dare ina adduar Allah ya daidaita komai kar sheɗan ya samu damar shiga gidanmu ya daidaita mana shi

Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya. Ina Katsina ban koma Funtua ba, amma ina kiran waya ina jin halin da suke ciki.

A

Jin za su dawo ya sa nima na fara shirin tahowa Funtua na yi ko da sati ne, sai aka ci sa'a ina tambayan Baban Amrah ya ba ni izini ya ce sai mu je tare ya duba Ya Sulaiman shi sai ya dawo ni kuma na zauna. Sai kuma a ka ci saa a satin yara suna hutun mirdterm break, shi ya sa na yi tunanin tafiya da su gabaÉ—aya.

Ina ta shirina cikin farinciki ana gobe za su sauka gida Basma ta zo mini yini, mun sha hira sosai muna tuna rayuwarmu ta makaranta muna dariya, sai yamma Baban Abdul ya zo ya ɗauke ta, itama da alƙawarin bayan su Abida sun dawo za ta je har Funtua ta gaishe da mai jiki.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Daran ranar da su Abida zasu sauka a lagos kasa barci na yi, a ranar wata asabar da safiya Yaya Sulaiman suka sauka a filin saukan jirage na garin lagos, kuma Ya Asad ne da tawagansa suka je suka tarbe su, na ɗauka a ranar za su taho Funtua amma sai muka ji shuru, su Anisa da Yaya Hamida duk suna can Funtua a gida suna jiran isowarsu ni ce dai na jira idab sun sauka sai na taho, amma ba su taho a ranar ba sai washegari da safe. Yaya Asad ne ya ce sai sun kwana sun sake hutawa, da safiyar lahadi nima na isa Funtua ni da yara da Baban Amrah. Misalin k'arfe ɗaya na rana ko minti talatin ba muyi da sauka ba sai ga motocin tawagar y'an sanda tunda reshen jihar Kaduna, tunda daga airport suka tarosu. Muka cika harabar gidan cikin murna da farinciki Allah sarki Baba Babba sai ga shi da kansa ya buɗewa Yaya Sulaiman murfin mota yana fitowa da kafafunsa zai ɗukawa Baba Baaba shi kuma sai ya tarairayo shi ya rumgume shi har hawaye suna zirarowa ta gefe da gefen idanuwan Baba Baaba, muma sai kuka muna share ƙwalla shi kan shi Yaya Sulaiman ɗin hawayen yake yi. Baba Babba na sakinsa Mami ta rike shi tana hawayen farinciki.

"Ashe zan sake ganin ka a kan kafafuwanka Sulaiman?

Ta faÉ—a tana mai sake kecewa da kuka sai ya rumgumo ta yana faÉ—in" Alhamdulillah Mami. Allah ya sa ina da rabon sake rayuwa da ku."

Kowa ta kan Yaya Sulaiman ya bi, ni ce kawai na yi ta kan Abida, wacce na ga ta yi kiba ta sake fari da cika kamar ba wacce ta je jinya ba, rumgume ta na yi ga mamakina nima sai ta riƙe ni, ina kuka ina faɗin" Sannunki da ƙoƙari ya ke masoyiyar yar'uwata."

Dago ni ta yi tana share mini hawaye tana kuma yi mini murmushi, yara ma haka ta riƙa rumgumarsu da'ya bayan ɗaya, mun daɗe a harabar gidan kafin a dumguma zuwa falon Mami can kuma sai mutuwar Baba ƙarami ya dawo sabuwa, shi kuka mu kuka Yaya Sulaiman kuka Yaya Asad ne mai ba su ba da bakin a yi haƙuri, sai da aka natsa suka yi wanka suka ci abinci sannan aka sake zama har Video call a ka kira Ya Muneera itama ta yi magana da su Abida kowa kaga ni yana cikin sukunin dawowar Yaya Sulaiman akan dugagunsa. Zuciya ta samu salama daga cikin tararradi. Baban Amra Zaria ya wuce a ranar ya kwana, sai washegari ya koma Katsina. Ni kuma ina gida domin gidan ya d'an yi daɗi kad'an. Don ina ankare da Mami da Ansari nake kada su ballo wata magana, sai kuma aka ci sa'a ba su yi ba. Jama'a ana ta zuwa duba Ya Sulaiman da yi musu barka da arziƙi. Baba Babba ma jiki ya yi kyau kamar ba shi ba.

Yaya Asad bai kwana ba a ranar ya juya saboda aiki, zai shiga jirgin k'arfe shida zuwa birinin Ikko.

Kwana na biyar a Funtua lokacin har Abida ta koma bangarensu ita da mijinta, na samu nutsuwar zuciyata da ban ga Abida ta birikice ba, tabbacin bata ji komai ba, sai hankalina ya kwanta ina shirin haÉ—a kayana na koma gidan mijina saboda yara sun koma makaranta Baba Babba ya ce na dakata za a yi general meeting tun da na ji haka na firgice saboda ban san abin da wannan zaman zai haifar ba.

Zama ya haÉ—a mana dukkanmu har da y'an bangarensu Abida, Ya Muneera ce kawai ba ta a wajen, kowa da kowa ya hallata. A bangarenmu a falon Mami aka yi zaman ita lokacin ta fita daga takaba da kwanaki biyu.

Sai dai zaman har da limamin masallacin unguwar. Dattijon arziƙi ne sannan malami ne sosai masanin Qur'ani da hadisai, mai wadar zuci da fayyace gaskiya komin d'acinta. Bayan buɗe taro da addua da yiwa Baba ƙarami addua Baba Babba ya fara kora jawabinsa.

Ya fito da wasu takardu na shaidar rukinin filayen Ladi farm gabaɗaya mallakinsa ne babu sisin Baba ƙarami a ciki.

Sannan dabbobin rukunin, dawakai ne da talo-talo, da dawisu na Baba ƙarami, amma sauran duk dabbobin dake cikin Ladi farm mallakin Baba Babba ne, sai dai Baba ƙarami ya kasance yana kula da su, masoyin dabbobine kuma likitansu ne.

Amma  bisa adalci Sai baba Babba ya ce za a raba amfanin gona kashi biyar shi kash uku, a bawa iyalin marigayi biyu duk da shi bai damu da noma ba, yafi son siyan dawakai da tsuntsaye.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bayan ya gama jawabinsa liman ya ɗora da tasa nasihar kan rayuwa da muka mutuwa, sannan ya gangaro kan haƙƙokin raban gado da waɗanda Ubangiji ya hallata ma samun gado.

Ya yi maganganu sosai jikin kowa kuma ya yi sanyi falon ya yi shuru ana sauraransa, daga karshe ya nuni da ce wa Baba Babba ya yi daddako, ya yi zumunci, domin bisa adalci irin nasa ne ya sanya ya ce a raba guda biyar, amma an sani akwai tazarar sosai a tsakaninsu.

Sannan ko da ya ce ladi farm tasa ce ya fadi gaskiyar abin da ba nasa ba a ciki. Dan haka liman ya umarci a zagaya da takardan filin kowa ya ga ni a cikinmu da kwanan wata da komai sama da shekaru talatin baya

Kowa ya yi na'am da wannan tsarin amma Mami bata ce uffan ba tabbacin bata gamsu ba ke nan.

Ya Sulaiman da ni hankalinmu ya yi tashin gauron zabi.

Tare da adduar Allah ya hana ta ikon magana.

Mami ba nauyin kowa ta ce" Wallahi ban amince da wannan tatsuniyar ba".

Ta faÉ—a tana babu ko d'ar.

Ya Sulaiman ya mike yana mata magana amma ba ta saurare shi ba, kuka ta saka na sosai ganin haka ya sa Baba Babba ya sallami liman domin ba zai so a yi wannan hatsaniyar ta cikin gida a gabansa ba.

Momi hankalinta tashe ta mike tana faÉ—in" Haba Mami! Alhaji kuwa idan bai yi muku ba, ba zai zalunce ku ba. Menene Bai yi muku ba sai yanzu da aka zo gargada ne kuma zai ci amanar shak'kin

d'anuwansa?".

Mami ta kalle ta da jajayen idannuwanta kafin ta ce" Ba zan yi mamaki dan kin yi mini gori ni da ya'yana ba. Don mamakin yadda za'a danne mana dukiyarmu ta fi komai girma a idona!

Yaya Sulaiman cikin rawan jiki da na murya ya ce" Mami kin ga shaida kin ga cewa filin nan na Baba Babba ne ".

Tsawa ta daka masa kafin ta ce" Dalla rufe mini baki, mara kishin kansa, don anzo da wata takarda duk ta tsufa sai ace shaidar ke nan, ba zan yi shuru a cuce ni ba, daga nan har gaban abada kuwa"

Na miƙe jikina na rawa ina kuka ina kiran sunan Mami amma ba ta saurare ni ba, daga karshe ma tsawa ta buga mini tana faɗin" Zan ci miki mutumci Balkisu."

Sai na yi shuru na koma gefe ina kuka su kuwa Baba Babba da su Yaya Usman sun yi shuru kamar ruwa ya cinye su, ina tunanin Baba Babba ne ya dakatar da su daga yin magana. shi da kansa kansa na ƙasa ya kasa magana. Abida kuwa kai kawai ta ke girgizawa Yaya Usman na cije baki, Ya Faruƙu ma ya yi shuru kamar baya a wajen.

Mami kuka take yi tana rantsuwan ba zamu amince ba

Ansari ya miƙe yana faɗin" Ina bayan ki Mami.

Ganin haka yasa Abida ta miƙe itama tana faɗin"Muma mu nan akan ce wa ladi farm ta Baba Babba ce.

Yaya Usman ya miƙe yana marawa Abida baya bayan shima ya ce "Komai zai faru sun shirya masa.

Yaya Faruku ne da Momi suka taimakawa Baba Babba ya mik'e suka bar mana falon Ya Sulaiman zai bi su Mami ta ce "Dawo! Ko kuma na yafe musu kai".

Wannan kalaman sune suka dakatar da shi daga bin bayan Baba. Amma yadda suka fita hankalinnsu a tashe sannan su harzuƙa sosai daga kalaman Ya Usman da Abida, amma bai saka Mami ta saduda ba sai ma ta cigaba da mganganu ita da Ansari suna yi ma su Aneesa famfo akan su mara musu baya, akan akilo da suke yi na ganin ba'a cucemu ba.

"Haba Mami don Allah ki bar mganar nan haka nan. Yau ko Baba ya dawo  duniya Wallahi ba zai yi alfahari damu ba".

Ya Sulaiman ya fad'a murya babu amo, shi yana kwalla ni kuma ina faman kukan sharbe, abin da na ke ta gudun faruwarsa ne ya faru, kuma ina hango kafiyar Mami kan iya haifar da hargitsin da ba mu taɓa tunani ba.

"Ki yi haƙuri don Allah Mami ki bar mganan nan haka don Allah ba don halinmu ba."

Na fad'a ina kuka Mami ta kalle mu ta sake kallonmu kafin ta koma ta zauna tana jijjiga k'afa ta ce" Na rantse da wanda raina yake hannunsa ba zan maganar nan ba. Sai na yi sharia da duk wanda zai tauye mini haƙkina ni da ya'"yana"

Ansari na gefenta ya ce" I support the motion Mami."

Anisa ma ta ce tana bayan Mami haka ma Yaya Hamida sai ya kasance daga ni sai ya Sulaiman ne a ware.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Mun kasa ce wa komai saboda kalaman Mami sun girmi tunaninmu  ban sake tsinkewa da cewa Mami ta yi nisa ba sai da ta furta wata magana mai nauyi.

Wai ba ta yarda da hatsarin su Baba Ƙarami ba ma, tana zargin maƙarƙashiya aka shirya saboda a kashe Baba ƙarami da Ya Sulaiman

Tana faÉ—in maganar jikina ya tsuma tashin hankali. Ya Sulaiman kam a tsawa bude murya ya yi sosia ya ce

"Mami! Na roke ki kada Ki sake furta wannnan mummunar kalmar ko da a zuciyarki ne "

Ta zaro masa ido kafin ta ce" Ai ba ƙarya na yi ba. Ka yi lissafi da kanka me ya sa bai faru da Faruƙu ba sai kai? Haba da akwai ayar tambaya akan wannan lamarin."

Ansari ya jinjina kai kafin ya ce" Uhm ni fa na daÉ—e da tunanin haka Mami kawai dai ban yi mgana ba ne domin ba ni da wata hujja."

Ina kuka da muryata a buɗe na ce" Haba Mami yanzu sai ki bari zuciyar ki na faɗa miki Baaba Babba zai iya yin wani abu na cutar da Baba ƙarami? Me yasa Mami? Me ya sa kike so ki jawo abin da bamusan iyakacin inda zai tsaya ba?"

"Kin ci uwarki Balki. Na ce kin ci

ubanki!

Mami ta faɗa a harzuƙe har tana yi mini daƙuwa.

Ansari ya kaÉ—a kai kafin ya ce" Dama kin kai mata hannu Mami kwata - kwata Bilki ba ta kishinki sannan mu ma y'an uwanta ba ta kishinmu"

Mami na huci ta ce" Idan suka ce za su kware mini baya sai dai na yafe su Wallahi. Kuma idan na yafeku ba zaku taɓa yin albarka ba idan kuma haka kuke so to ku bada himma."

Tana gama faÉ—in haka fuu ta bar mana falon Yaya Sulaiman ya bi bayanta yana kiran sunanta..

Ni kuma suka bar ni da Ansari yana ta gaya mini maganganu wai ba ni da kishi ni sakara ce mara wayau Abidan da na ke kuka saboda ita, ubanta zata kare, amma da ya ke ni sakara ce ba san nawa ba tamkar Dai ba nice gaba da shi ba.

Ina kuka na ce" Ansari kar ka runtse idanuwanka ka manta da mu Ahali É—aya ne. Kar ka manta Abida matar Ya Sulaiman ce fa?"

"To sai me? Sai ya sake ta tun da abin na su ba adalci a ciki.'

Cewar Anisa sai na fahimci gabadaya yanzu suna bayan Mami ne, ba wanda zai iya saurarata ballana ya gane ina manufata ta dosa.

Nima falon na bar musu na shige ɗaki ina ta kuka, mutuwar Baba ƙarami ta dawo mini sabuwa mutuwa ce ta kawo mu wannan bigiren yau da Baba ƙarami na raye, ba mganar gado ballanta asan asirin da suka rufe shi da Baba Babba.

Ranar haka gidan nan ya kwana ba lafiya, da safe da na je gaishe da Mami ƙin amsa gaisuwata ta yi, shi ya sa jiki a sanyaye na fita zuwa bangaren Ya Sulaiman saboda na kasa shiga bangaren su Abida. Sun yi tsit kamar ba su a gidan sai dai ina zuwa bangaren Ya Sulaiman na iske

Shi kad'ai wai ta je asibiti.

Kawai na jine amma ba wani asibiti. Baba ya hanata zama ya sata ta dawo gidanta akan dole shine sassafe ta fice da sunan zuwa asibiti. Nasan Abida za'a fafata don kuwa ba mai sassauci ba ce irin Yaya Munira.

"Balki, na yi iya bakin ƙoƙarina amma Mami ta ce tana kan bakanta ta saka Ansari ya nemo musu lauya za su shigar da k'aran Baba Babba."

Kai na dafe ina faÉ—in" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.

Idona ya soye hawayen ya kafe, kirjina ya yi nauyi ainun.

"Bilki muna cikin Tsaka mai wuya(Janafty )Mami ta ce idan muka bijere mata za ta yafe mu. Ya za mu yi?

Shima yana magana cikin k'unar rai, bamu da wata mafita Mami mahaifiyarmu ce idan ta tsine mana zamu bi duniya mu lalace, idan kuma muka goya mata baya dai dai yake da mun saka wuka mun gille zumunta.

Ya numfasa ya ce "Ga yarinyar nan ta murde, na ga take takenta ita zata jagorancin bangarensu wajen sake watsa zumuncinmu.

Muka gama zaman bamu samu mafita ko dabara ba.

Haka muka fito babu matsaya, kaitsaye muka yanke muje mu gaida Baba Babba.

Zamu shiga muka ci karo da Ya Usman ya rako likitan da yake duba Baba Babba ke nan jikin na shi ya tashi saboda hatsaniyar da ya faru jiya, jikina ya sake sarewa lokacin da na ga na gaishe da Ya Usman ya yi wucewarsa kamar bai ganni ba.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Jikina kamar ba nawa ba na ƙarisa shashen Baaba Babba Momi ce kaɗai a falo itama da na gaisheta sau ɗaya ta amsa daga nan ta tashi ta bar falo na yi tsaye ina kukan zucci da na sarari amma ba motsin kowa, kamar zan taka ɗakin da Baaba Babba yake sai na ji kamar muryan Ya Faruƙu sai na fasa na juya zan nufi ɗakinmu muryar Abida na ji tana waya.

"Ya Muneera sun ce za su kai Baaba Babba ƙara a kotu. Tunda bamu muka fara ba, to ba za mu juyawa yaƙinsu baya ba."

Ta yi shiru tabbacin tana sauraronta ne.

Sai Kuma na ji ta cigaba da magana cikin d'aga sauti ta ce "Na rantse da wanda raina yake hannusa Yaya Munnera za mu yi sharia da su kuma sai mun tabbatar da adalci ga Baba Baaba sannan za mu dakata."

"To Idan kinsan ba za ki kwafsa ba to sai ki zo ki tsaya masan".

Ban ji me Ya Munnera take faɗi ba, saboda yadda jikina ke rawa yasa bansan na k'arisa ƙofar ɗakin namu ba, kofar a buɗe ta bar ta.

Murya ba amo na shiga dakin bakina dauke da sallama.

Ta juyo tana ganin ni ce ta sake haÉ—e rai, itama idanuwanta sun yi luhu luhu alamun ta sha kuka.

"Zan kira ki Ya Muneera."

Ta faɗa sannan ta katse wayar ganin ta nufo ni sai na yi ƙoƙarin shigowa ɗaki amma Abida ta yi maza dakatar da ni daga bakin kofar dakin wanda hakan alamace na bazan shiga dakin ba ke nan.

Nan da nan na ji na muzanta idona ya ciko da kwalla.

Tana kallona ina hawaye ita ko saboda taurin zuciya ban ga kukanta ba akan fuskata Abida ta bugo mini kofa ta bar ni da radaÉ—in zucci da sarari, ina kuka wiwi da gudu na koma bangarenmu sai É—akin Mami tana zaune gefen gado tana magana a waya a yanayin yadda take mganar na fahimci da Ansari ne domin faÉ—a masa take yi cikin satin nan take son ta shigar da kara kan Baba Babba.

Gabanta na faɗi ina kuka na riƙe kafafunta ina faɗin" Don Allah Mami ki yiwa zumunci kara, ki yiwa Baba ƙarami alfarma ki yiwa Yaya Sulaiman karamci ki janye mganar nan don Allah"

Fizge kafarta ta yi, kafin ta miƙe tana fadin" Wallahi Balki yadda na ke jin takaicinki zan iya yi miki baki."

Na kalle ta ina kuka amma bai saka Mami ta saduda ba, cikin dakiyarta ta ce"idan kika sake ce wa tak a kan wannan mganar sai na yi miki Allah ya isa. Sannan zance ba za ki yi albarka ba Balki."

Kaina ya sara na durƙushe ina faman gunjin kuka ba ni da wani kalami da zan sake furtawa haka na ja jikina na fito, ranar a ɗaki na yini yarane ma suka debe mini kewa suna ganin ina kuka suka fara tambayata Mahma me ya faru da ke? Dan haka na hadiye kukan dan na Samar musu da nutsuwa.Tun jiya rabo na da waya komai na duniya baya yi mini daɗi Anisa da Yaya Hamida da safiyar nan suka koma gidajen mazajensu, tun ina tunanin Mami za ta sauka har na yi sarandar da ce wa bata fara domin ta daina ba. Gidanmu ya rikice gabadaya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ba zato ba tsammani kawai sai ga takardan sammaci daga babban kotun katsina, sammaci daga iyalan Marigayi Alhaji Isa Funtua(Baba karami) zuwa Alhaji Musa Funtua.(Baba Babba).

Wannan takardan sammacin ta yi silan ɗaga hankalin Baba Babba da ahalinsa, ashe dai Mami da gaske take yi, ashe Mami duk abin da take faɗa har zuciyarta ne? Hankalin Baba Babba yafi na iyalansa tashi, yana kuka yana faɗin" Bazan iya sharia da ƴa'ƴan ɗan'uwana ba, ba zan iya shari'a da iyalan Isa ba, bayan ƙasa ta shafe idanuwansa ba."

Momi ma hankalinta ya kai maƙura wajen tashi, tana kuka Baba Babba na kuka, bata taɓa tunanin Mami zata yi haka ba, ta ɗauka duk barazana ce ashe ita da gaske take yi? Wannan wani irin lalacewa ne ace saboda gado ƴaƴan Baba ƙarami zasu yi shari'a da Baba Babba itama tana goyon bayan Baba Babba shi ya janye, ya ba su duka gidan gona in dai haka Mami take so, zai fi mutumci da kuma yi ma zumunci kara, akan ayi ya yamimidin yana shari'a da ahalin k'aninsa bayan k'asa ta shafe masa ido.

Ga shi kuma zaman kotun ranar 20 ga watan da muke ciki ne, yau kuma biyu nan da kwanaki sha takwas ke nan masu zuwa.

Shi dai Baba Babba ba nan yake hango matsalan ba, shi ba zai iya sharia da ya'yan d'an'uwansa lamarin ne yake saka shi kuka da tunanin mutuwa ce duk ta jawo wannan tonon sililin yau in da ace Baba ƙarami na raye da duk haka bai kasance ba.

Gabad'aya komai ya ɗakule masa, a cikin zuciyarsa yake jin wani irin zafi zafin da ya kasa misalta misalinsa, tun bayan rasuwarp Baba karami yake fama da nauyin zuciya ga wannan rigimar da ta taso. Shima yana ji dama ace shi ne ya rasu ba Baba ƙarami ba, da yau bai fuskanci wannan tashin hankalin da damuwar ba, da shi ma ya huta kamar yadda Baba ƙarami ya huta da kwaramiyar duniya mai cike da rudani.

*

39

Ina katsina Ansari, ya kira ni yana faɗa mini za a fara sauraran ƙara ranar 20 ga wannan watan da muke ciki, na shiga ɗimuwa da tashin hankali Mami ba zata saduda ba, Mami da gaske take yi ke nan? Ya kuma sake ba ni tabbacin tuni takardar sammaci ya isa ga Baba Babba da iyalansa, na sake firgita nasan Mami da kafiya kuma tun da ta kafe sai ta cika muradinta, ba tare da shawara da kowa ba na yiwa Kawu Bala waya na sanar da shi halin da ake ciki ina kuka ina roƙon shi su zo su sami Mami wataƙila in suka yi magana ta ji su ta kuma janye kuɗirinta.

"Ashsha abu bai yi daÉ—i ba! Sai dai ba zan saka kaina a sabgarta ba, don kuwa kunsan yadda muma muke ciki da ita".

Kukana ya tsananta na kasa Magana.

Jin yadda nake kuka ya saka ya ce "Tausayinki ya kama ni! Share hawayenki zamu zo mu same ta Allah ya sa ta ji. Tunda kunsan halin uwarku muma ba jin dad'inta muke yi ba."

Cikin shassheƙan kuka na ce" Kawu ku taimaka ku daure, ku tursasata ta janye, wanne irin masifa ta had'a mana haka?"

Ya ce "Zamu yi Mata magana da nasiha Idan ta amince shike nan, amma ba zancen tursasa ta tunda bamu da kudade masu nauyi. Yanzu ma saboda ke da nema muku masalaha da mutunci ya saka Zan yi karfin hali na jarraba tunkarar ta. Don na yi alƙawarin daina shiga sha'anin mahaifiyarku saboda halinta. Amma tunda har lamarin ya kai ga haka zamu zo mu sameta idan ta ji nasiharmu shike nan, idan bata ji ba sai na ce Allah ya bata sa'a. Duniyace wanda ma ya tara dukiyar ai ya tafi ya barta. Itama bata fi ƙarfin Allah ya ɗauke ta a wannan yanayin ba."

Haka muka rabu da Kawu Bala bayan ya bani tabbacin zasu je har Funtua su samu Mami da maganar ni kuma a gida ina ta fata da addu'ar Allah ya

sa zuwansu ya zama alheri.

Kwana biyu tsakani ina ta fama da zullumi, na sake kiran wayar Kawu shi ya fada mini a jiya suka je suka yi magana da Mami kuma ta nuna ta ji nasiharsu amma dai bata ce musu komai ba, hankalina ya É—an kwanta a tunanina an samu nasara da karfin gwiwata na kira wayar Mami sai dai tuni ta ranfo ni ce na kai k'ararta wajen yayyen nata, ko gaisawa ba ta bari mun yi ba ta fara mini faÉ—a tana zagina.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Sakarya marar kishi, ai nasan dama ke ce kika kira su Yaya Bala kika kai k'arata. Bilki kina daukar lamarina da wasa? To bari ki ji na rantse da Allah bazan bar maganar nan ba sai an kwato mini haƙkina da na ƴaƴana gwara ma ki yi shuru da bakinki. Duk kuma wanda za ki turo kin daɗe ba ki turo su ba amma ina nan akan matsayata babu ja da baya."

Tana gama faɗin haka ba ta saurara ni ba, ta kashe wayarta na yi ta k'iranta daga baya ba ta ɗaga kirana ba. Na k'ira wayar Ya Sulaiman, shima ɗin ya ba ni tabbacin sun zo amma ko bayan tafiyar su Mami ta sake jadadda masa da ce wa tana kan bakanta ba kuma irin ban baki da nasihun da bai yi mata ba amma ta ce, babu gudu ba ja da baya, Ansari kuma yana bayanta tun da har shige da ficen, ƙaran ma Ansari ne ya yi a Katsina ya shigar da karan sannan ya ɗauki ƙwararan lauyan da zai tsaya akan sharian yanzu haka ma suna ta haɗa hujojinsu ranar shiga kotu kawai suke jira. Hankalina ya rub'anya tashi gabaɗaya duniyar ba ta yi mini daɗi har zazzaɓi ne ya kama ni da nake yinsa a tsaye saboda zullumi da tashin hankali.

*

Funtua.

Kwanakin shiga kotu, suna ta kara matsowa, duka duka saura kwanaki hud'u ne a fara zaman farko. Hankalin Ya Sulaiman ya tashi ganin har Ya Muneera ta samu Visa ta iso. Hakan ya alamta mana ita ce zata tsayawa Baba Babba.

Abubuwa sun sake ƙwabewa don kuwa barci kad'ai ke kawo Abida shashinsu Hakan ma yasan turo ta ake yi akan dole. Duk juyin da zai yi kuma bata yarda ta ce masa uffan. Gaba ta k'ulla a tsakaninsu mai tsananin gaske duk da itama fama take yi da zazzabi da rashin kuzari wanda take ganin bacin rai ne ya sababa mata.

Gari na waye wa take fice wa zuwa bangaren momi, tamkar akan k'aya take, da yake a cikin rudani yake sai Bai tsananta ba, don Shi tashin hankalinsa ba akan fishin Abida bane, gabad'aya hankalinsa da tunaninsa yana kan ya samu damar da zai hana yin wannan shari'ar da take k'aratowo, tun ba'a shiga kotu ba, gaba ta fara k'ulluwa a tsakaninsu da ya'yan Baba Babba. Ko Muneera da ta iso garin ba ta zo b'angarensu ba kuma bai ga laifinta ba, a irin abin da Mami ta yi musu suna daidai da irin hukuncin da suka É—auka a kansu.

Ya kudire zai sake tuntubar mahaifiyarsu a karo na k'arshe ko Allah zai sa zuciyarta ta yi laushi ta sauko a janye k'ararta tunda lokaci bai kure ba. Hakan yasa yau tun asuba bayan ya dawo daga sallar asuba a bangarenta ya sauka shima duk ya rame ya lalace ,shi da ya dawo daga jinya ya kamata ace ya samu natsuwa da hutu amma ina tun bayan dawowarsu bai samu natsuwa ba sannan bai samu hutu cikin salama ba tun da zuciyarsa babu sukuni.

Duƙurshewa ya yi a gabanta yana sake bata baki da lallashi nasiha yake yi mata cikin dubara wanda ba cin fuska ko raini a ciki.

"Haba Mami har kin manta mutuwa? Har mene ne a duniyar da ya fi miki Baba ƙarami? Wani daɗin duniya ne ya fi miki Baba ƙarami Mami? "

Shuru Mami ta yi ba ta yi magana ba, amma da alamu kamar jikinta ya yi sanyi ganin haka yasa ya sake gyara zama yana ƙara tusa mata mganganu domin zuciyarta ta raunana ta saka Ansari ya janye ƙarar Baba Babba da ya shigar.

"Amsar ita ce Babu Mami, ba wani daɗin duniyar da ya fi miki Baba ƙarami, kuma kin rasa shi kin haƙura! To mene ne a dukiya ko gona da ba za ki iya haƙuri da shi ba? Kar ki manta shi kansa Baba ƙaramin nan da ya tara dukiyar da guminsa yau ina yake? Ba shi a duniya ya tafi ya barki, ya bar mu ya bar kowa na shi da duka dukiyarsa ba domin baya so ba, sai don wa'adinsa ya yi ba shi da yadda zai yi Mami."

Sai ya ga ta dukar da kanta ƙasa har a lokacin ba ta ce komai ba.

"Mami ki yi hakuri, ki sake yin hakuri, ki yiwa zumumci kara, ki sake kallon karamci da kirkin Baba Babba a gare mu. Mami ba kya tunanin wata rana duk tafiya zamu yi inda ya tafi? Me kika nema ne a duniyar nan? Me ya rage miki ne? Yau ko da a ce ba a bamu ko sisi daga cikin gadon Baba ƙarami ba, ba zamu tagayyara ba Allah ya rufa mana asiri, mene ne ba zamu yi miki ba? Ina aiki, Bilkina na aiki Hamida na cikin rufin asiri, haka Anisa, Saddiqa Nurse ce, sannan ga Ansari yana harkokinsa yana samun rufin asiri sai godiya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Mami mene ne ba za mu yi miki ba? Wanne jin daɗin duniya kike bukata wanda ba za ki samu daga bangarenmu ba? Dan Allah Mami daure ki yi mana kawaici cikin zumuntar gidanmu.! Ko da ma cutarmu ya yi, Ubangiji ne alkali mafi adalci. Sannan albarkar da za ki dinga sanya mana kadai ta ishe mu arzikin duniya da lahira. Kada ki bari mu shiga cikin tarihi, kada ki janyo mu tozarta ki yi hakuri, ki k'ara hak'uri da sannu Ubangiji zai miki kyakkwan sakamako."

Ya ɗauka ta saduda ya dauka maganganunsa ya shige ta yadda ya ga ta yi shuru ba ta yi mgana ba ya ɗauka nasihar ya ɗauki kusan awa ɗaya yana yi mata tare da kalaman jan hankali sun shige ta ashe ba haka bane domin yana gama magana ta ɗago ta kalle sa sannan ta girgiza kai kafin ta ce" Sulaiman ke nan. Duk abin da za ka yi ba zan bar haƙkina ba. Cutarmu fa za su yi muna ji muna gani fa Sulaiman? Ko Annabi da kansa ya ce kar ka yadda a danne maka haƙkinka har sai idan lamarin ya fi ƙarfin ka, ni kuma bai fi ƙarfina ba shi yasa na tsaya kai da fata akan sai an ƙwato mana haƙkinmu."

"Mami!

Sulaiman ya kira sunanta cikin sarewa, sai kawai ta ɗaga masa hannu kafin ta ce" idan har kana so ka yi albarka kar ka sake zuwa dakina da wannan maganar. Wallahi Tallahi bazan janye wannan ƙarar ba sai alƙali ya kwato mana haƙƙinmu, su da suka yi zaluncin ba su yi nadama ba sai mu ne da suka danne wa haƙƙinmu? Ko kuwa haƙilon da kuke yi kai da Bilki na kar a ɓata musu, su kun ga suna yin haka akan ku? Sun fi ku wayo, domin kansu suka sani kafin ku. Idan ma za ku dawo cikinmu ku dawo, ni ɗin nan dai ni ce na kawo ku duniya ba Momi da Alhaji Babba ba"

Ta fada cikin sake jadadda masa, cewa ita ce fa mahaifiyarsu kar su manta da haka.

Cikin ƙasƙantar da kai Sulaiman ya ce" Mami ba kya tunanin yadda rayuwata za ta ƙare? Tunda na dawo ban sake samun natsuwa ba. Abida ta yi nesa da ganina, ba kya tunanin bayan yankewar zumunci har da taɓarɓarewar aurena da Abida a cikin yunkurinki?

Kai tsaye Mami ta ce" Sai dai in ba ta sonka. In tana son ka za ta zauna da kai ko da zumuncin ya yanke. Ko da yake ta fi ka sanin ciwon kanta za ta zaɓi ahalinta ne sama da kai. Kaima sai ka yi irin yadda ta yi."

Kasa magana ya yi, rauni ya mamaye shi hawaye sun kawo a ƙwarmin idanuwansa amma bai bari sun zuba ba, ya yi saurin mayar da su, haka ya miƙe yana layi kafin ya ce" Shike nan Mami. Shike nan ba zan sake ce wa komai ba."

Daga haka ya fice daga É—akin nata ta kara shi da harara tana mai faÉ—in" Sakarai kawai dama nasan akan shedaniyar yarinyar nan kake wannan kai kawon to sai Dai auren naku ya lalace a hakan. Ja'irar yarinya mai bakar fuska da bakar zuciya".

Fitarsa haraba ya haɗu da Ya Usman da Muneera zasu fita a mota ya yi ƙokarin yiwa Usman Sallama amma bai amsa shi ba sai Muneera ce har ta wuce sai ta dawo.

Yaya Sulaiman ya ƙarfin jikin?

A sanyaye ya amsa mata da ya ji sauƙi, sai ta kaɗai kafin ta ce" Allah ya kara lafiya."

Yana so ya yi magana amma ba ta tsaya sauraransa ba ta yi gaba Usman ya daɗe da barin wajen, ya daɗe a tsaye yana nazarin rayuwa har sabo ya yi zuciyarsa na kitsa masa me yasa ya dawo kasar? Ko me yasa ya rayu shima bai mutu kamar Baba ƙarami ba? Da ace bai rayu ba da yau bai ga wannan baƙin cikin da tashin hankali ba, yana jan ƙafa ya karisa bangarensu shi da Abida da ya kasance fanko tunda jiya da yau ma ko kwanan bata zo ta yi ba.

Yasan wace ce Abida ba zata tab'a sauraransa ba yanzu wataƙila sai an gama wannan shariar sai ta yanke hukunci. Kuma hukuncinta dai dai da yake da rabuwa da shi, in dai Abidar da ya sani ce mai tsauri da ra'ayin rik'au ce.

Bai san yana hawaye ba sai da ya ji suna sauka daga saman fuskar shi, ashe wai kuka yake yi, kukan rashin Baba ƙarami, kukan rashin bango kamarsa, komai ma ya yi masa tsaye cak ya kuma rasa tunanin da zai yi, ya riga ya gama sarewa da lamarin Mami tun da ta sake rantsewa to tana nan akan bakanta. A ranar ma lauyan da suka ɗauka ya zo gidan shi da Ansari sun yi magana da Mami ba fashi ranar 20 ga wata za a yi zaman farko kamar yadda aka rubuta a takardun ƙaran.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sai kawai ya sare ya yi saranda da cewa Mami sai ta cika muradinta kuma gashi ta ɗauki hanyar cikawa, ya daina mata magiya ya yi shuru da bakinsa ya koma zura musu ido ita da Ansari kamar yadda ya ce shike nan ba zai ƙara mganar haka ne ya faru bai sake ce musu komai ba.

*Dakin Baba Babba.*

Daga shi sai Munira zaune suke tsawon lokaci bai ce komai ba, duk da shi ya bukaci ta shigo har cikin dakin barcinsa, ya kuma ce da Momi ta basu waje. Munira kuwa bata ce komai ba, tana zaune tana dakonsa zuciyarta cike da tausayinsa, ta tabbatar yana cikin rudani da rashin sukunin zuciya mai yawa.

Da matukar rauni a zuciyarsa ya ce "Abin da tashin hankali Munira. Ace ni zan yi shari'a da ya'yan Isa? Hakan kuma bai isa ba sai na sake ba ki damar ki ba ni kariya su kuma ki barsu?".

Hawaye ya k'wace musu gabad'aya. Ya ce "Kaf ya'yan da muka haifa daga ku har su Bilki babu wanda Baba karami ya ja a jikinsa irin ki hatta sunanki shi ya zaba miki. Kin sani kin girma sosia bai daina yawo da ke ba. Yanzu da kika tafi wata k'asa duk taron da zamu yi shi yake tunowa da ke ya ce a lalubo ki a waya, a gaishe ki. Ko ya'yansa idan ya haifesu baya tab'a tsayawa wajen me za'a yi tunda yasan zan yi komai. Amma haihuwarki ba rawar jikin da bai yi ba. Dan haka ni ba zan je kotu ba, balle ki saka rigarki da rabin ilimin da ya ba ki damar sanyata daga aljihunsa suka fito.

Ta numfasa ta ce "Baba dole zaka je kotu domin a k'aida idan an yi k'arar mutum har kotu ta kawo masa sammaci sai ya girmama kotu ya je idan ya so sai ya gabatar da uzzirinsa sannan ya janye daga k'arar ".

Ya numfasa ya ce "To ku dauko wani lauyan Munira, bana son ki ba ni kariya bisa son zuciya, bana son iliminki ya yi mini amfani ni kadai ban da Babanku ".

Ta yi k'asa da kai domin tausayin mahaifinsa ya mata dabaibayi k'warai da gaske don kuwa jarabawar rashin Baba karami kadai idan an bar shi da ita ta ishe shi radadin zuciya bare kuma wannan bala'in da ya gitto.

A tausashe ta ce lokacin daukar wani lauyan ya k'ure, gobe ne zaman.

Ka kwantar da hankalinka komai za'a yi bisa gaskiya da k'aida, ina maka alakawarin abin da zai biyo baya wanda zaka gamsu ne".

Ya kada kai ya ce "Allah dai ya shiga lamarin kawai amma al'amarin ya b'aci. Sai dai na fahimci kuskuren da muka yi ne Allah ya bawa shaidan damar shigowa cikin zumuntarmu.16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Katsina.

Ranar ashirin ga wata ta kama ranar da za a yi zama akan shari'ar a babban kotun dake cikin garin Katsina. Tun asuba wayar Mami ta tashe ni daga barci faÉ—a mini take yi yau ne ranar shiga kotu na tabbatar da na samu hallata, ba ni da yadda zan yi na amsa mata.

Baban Amra dama yana sane da ranar tun da suna wayar da Ansari tun safen ya yi mini magana ban dai ce masa komai ba tunda ko na hana shi zuwa yasan hanya zai iya zuwa shi yasa ban ma tsaya b'ata wa kaina lokaci wajen yi masa bayanin ba sai ya je ba.

Na kira Ya Sulaiman a waya ya tabbatar suna hanyar tahowa Katsina shi da Mami da Ansari, sai na ji nima na gama sarewa dole kanwar naƙi na shirya bayan yara sun tafi makaranta na shiga bangaren Hajiya na yi mata sallama na ji tana mini zancen shariarmu da za a fara yau.

"Bilki ashe kuma haka gida ya rikice! Sahal ya faÉ—a mini na ce lamarin dai bai yi daÉ—i ba "

Sai ga ni zaune gaban Hajiya ina ta faman yaƙe, shi yasa ban so Ansari ya saka Baban Amrah cikin maganarmu, ga shi nan ya zo ya barbaɗamu wa ma ya sani ma ko duka ƴan'uwansa, sun ji labari tun da dai ga shi a bakin Hajiya.

"Allah ya kyauta na gaba. Amma shi ma dai wan baban naku ya so kansa duk uban gidan gonar nan da ake labarinta a garin Funtua da jihar Katsina gabad'aya ya ce tasa ce shi kaɗai? Yin shari'ar ma yana da amfani saboda a fiddo muku da haƙkinku"

Ni dai ba baka sai kunne, na kasa mgana kaina na kasa kunya duk ya kama ni ke nan komai da komai na sirrinmu Baban Amrah ya gama barbaÉ—a mu a gari amma ba laifinsa bane, laifin Æ´an'uwana ne su suka jawo mini wannan tozarcin.

Bayan na yi mata sallama zan tafi ta bi ni da faÉ—in" Allah ya ba ku sa'a Bilki. In sha Allahu kune da nasara."

Ta san ranar za mu fara zaman kotu ashe, ni ina can ina arowa kaina jarumta da sunan kar dangin mijina su fahimci akwai matsala ashe aikin banza na ke yi Baban Amrah ya gama kwance mini zani a kasuwa ban sani ba.

Tare muka tafi da shi, shi yasa ni ko magana ban yarda ta haɗa mu ba, shine yake ta maganganunsa yana faɗa mini In sha Allahu mune da nasara ya san lauyan da muka ɗauka Barrister Jibril Hadi, senior din su ne a makarata guri ne yasan kan aikin shi kuma ai muna da hujoji ni dai kala ban ce masa saboda a lokacin jin kaina na ke yi kamar ba ni ba komai, na duniyar nan baya yi mini daɗi, har muka isa cikin kotun nan da misalin goma da rabi na safiya lokacin su Mami ba su iso ba sannan ana gudanar da wata sharia ne, wanda daga shi sai tamu shari'ar, muna haraban kotun motar Ya Usman ta fara shigowa bayan ta kuma ta Yaya Faruƙu ce. Kafafuwana sun kasa ɗaukata daga in da nake sai da na jingina da bangon wajen.

Baba Babba tare da Momi da Abida a motar Ya Usman. Ya Muneera da take sanye da rigar ta lauyoyi a motar Ya Faruku. Babu Ya Asad watakila bai samu zuwa ba, sun ganni nima na gan su, ina son na ƙarisa na je na gaishe da Baba Babba amma kunya da nauyin sun k'i barina kuma ma kafafuwana ba za su iya ɗaukata ba rawa suke yi, Abida ma ta ganni ta ɗauke kai ta gabanmu suka bi suka wuce kamar ma ba su taɓa sanina ba. Baban Amra ba ya wajen yana can gefe suna mgana da wani lauya, shigar su ba daɗewa sai ga motar Ansari ta shigo wajen Mami da Ya Sulaiman suka fito. Mami fuskarta ba damuwa ita da Ansari Ya Sulaiman ne kamar ni mun yi zuru zuru. Wai ashe lauyan da Baban Amrah ke magana da shi lauyan da su Mami suka ɗauka ne sai da na ga sun k'ariso wajen ya gaishe da Mami yana sake gabatar da kansa.

"Barista. Kana da tabbacin za mu yi nasara?

Mami ta tambaya tana mai kallon Barista, ya karkace da rigar shi ta lauyoyi yana fadin" In sha Allahu Hajiya. Ai muna da hujojji masu k'arfi, kuma ma shari'ar bata da tsawo ba za ta É—auke mu lokaci mai yawa ba."

Mami ta jinjina kai Ansari ya dafa kafadanta yana mai ce wa" Ba ki da matsala Mami Barr Jibril ya san kan aikin shi."

Ni da Ya Sulaiman muna gefe kamar ruwa ya cin ye mu, lauyan ya fara shiga ba daɗewa aka sallami masu ƙara na ciki sai ya fito ya ce mu shigo mu ne akan layi, gamu ga su Abida amma ba wanda ya nuna yasan kowa a cikinmu sai dai ana kallon kallo kowa ya ɗauke kansa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: A wajen zaman kowa da rukuninsu, bayan an karanto k'ara da gabatarwa ga lauyoyin masu k'ara da masu karewa aka fara shari'a, ni tun da aka fara na ke shatatan hawaye ina kallon Baba Babba ma yana ta sharan k'walla da haɓan babban rigan shi, tun ballatana da Lauyan mu ya gayyace shi tsayuwa a ɗan akwatin nan na masu ba da shaida, ya yi masa tambayoyi akan dukiyarsu da take haɗe da ta Baba ƙarami. Nan ma ya yi duka jawabin komai kamar yadda yake a farko, yadda lauyan ke jifan Baba Babba da cuta garemu ya sake kunyata ni sai da Ya Muneera ta mik'e ta yi mgana sannan alk'ali ya dakatar da Barr. Jibril, an gabatar da dukkan hujojji. Sannan yaya Muneera ta gabatar da takardun shaidar cewa filin Ladi farm ta Baba Babba ce, mu ma daga bangaren mu Lauyanmu ya gabatar da cewa komai na dukiya tare ne, kuma har Baba k'arami ya rasu bai taba ce wa ladi farm babu guminsa a ciki, haka Mami ta ce da Lauya ya gayyace ta, bayan gama haɗa duka shaidu a waje ɗaya sai ya ce ya ɗaga sake saurara ƙara zuwa 21 ga watan gobe kuma zai zama ranar ƙarshe da za a yanke hukunci.

Har aka tashi zaman kotun nan kuka na ke yi, a gaban idanuwanmu su Abida suka shisshiga mota suka bar haraban kotun amma da alamu kamar Baba Babba jikinsa ya tashi, domin Yaya Faruƙu da Momi na riƙe da shi lokacin da zai shiga mota, daga kotun muka rabu da su Mami.

Ni da Baban Amra muka koma gida ina shiga gida na rufe kaina a É—aki ina ta faman kuka. Na shiga dimuwa mara misaltuwa, na shiga tashin hankali da yasa bana iya barci komai nawa ya tsaya cak, duk na rame na lalace saboda zullumi da tunani.

Ya Sulaiman ma a can Funtua komai ya dak'ule, domin ya sanar da ni cewa Baba Babba ba lafiya suna dawowa gida a ranar da aka yi zaman kotu yana zaune a kan kujera ya ƙame dumfara ta dinga fita ta bakinsa tare da karkacewa. An kai shi asibitin cikin garin Funtua kwana ɗaya ya yi Ya Asad ya iso suka ɗauke shi zuwa speacialist hospital Abuja.

Ni dai ba abin da nake yi sai Allah ya yayyafawa matsalar wuta. Ya huci zuciyarsu Abida, don kuwa a bayyane yake ita da Usman a shirye suke a yi yak'in basasa.

Ranar har sai da Baban Amrah ya farka jin ina cewa Allah ya sassauta fushin Abida!

Tsaki ya yi kafin ya ce" Mtsewww, ke yanzu ba ki damu da damuwar Mami ba sai na wata can Abida? An ya Bily haka Abidar nan ta bar ki? Ita fa bata ko damu da ke ba, ta bi bayan Æ´an'uwanta amma ke kina nan kin kasa sukuni saboda su."

Har ya gama maganarsa ban ce masa komai ba, ai tun da ba gidan su yake faruwa komai ma zai iya cewa, tun da ba zuruan Hajiya ba ne suka tarwatse ba ai ya ce haka, ba zai taba gane yanayin ba tun ba bashi ne a cikin tashin hankalin da nake ciki ba, daga karshe ma É—akin na bar masa ban sake yarda mun yi wata mgana da shi ba, ni kunyar fita ma na ke yi sai na ke ganin kowa yasan abin da ke faruwa za a dinga nuna ni a matsayin wacce mahaifiyarta ta tayar da hargitsi saboda gado.

A can ma Funtua an ce gari ya ɗauka ana ta mganganu marasa dadi tun da labari ya zaga ko'ina da cewa mun kai k'arar wan ubanmi saboda gado, kowa na kallon mu a waɗanda ba su kyauta ba wasu kuma suna ganin cewa ba a yi mana adalci ba ne shi ya sa abin ya kai zuwa gaban alƙali. Dama yanzu kowa albarkacin bakin shi zai faɗa, tunda sanin gaskiyan sai Allah sai kuma mu da muka san mafarin komai.

Har ranar zaman kotu ta zagayo ban sake barci cikin salama ba, daga Abuja su Abida suka taho Baba Babba a kan wheelchair, sannan wannan zaman har da Ya Asad aka zo, kamar ma wancan karon wannan ma lokacin kallon kallon kawai aka yi a tsakaninmu da ahalin Baba Babba kowa ya kauda kai, mu ma daga bangaren mu har da Hamida da Anisa, muka zauna a rukunin mu suma suka zauna a nasu rukunin Baba Babba duk ya rame ya lalace daga gani ya sha jinya yana zaune kan weelchair, gwanin ban tausayi, ni da man a raina ban taba jin za mu yi nasara ba har addua nake yi na ka da ya zama kotu ta bamu nasara ko yaya ne Baba Babba ya samu adalci.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Haka kuma ya faru bayan sake tattara hujojji da shaidu kotu ta tabbatar da Ladi Farm ta Baba Babba ce, fuskokinsu Ya Usman ya cika da farinciki .

Mami da Ansari kuwa kamar za su yi bindiga saboda bacin rai, jin an samu tabbacin gona ta Baba Babba ce a kotun Ya Muneera ta miƙe cikin sanyin muryanta ta ce" Alhamdulillah Allah mun gode! Cikin adalci kotu ta tabbatar ba'a zalunci kowa ba. "

Bisa adalci da zumunci had'i da biyayyar da marigayi Babanmu ya yiwa mahaifinmu mun sadaukar da Ladi farm da dukkan abin da yake cikinta ga iyalin marigayi Babanmu Alhaji Isa Funtua gonar da ake takaddama akanta halak malak. Mahaifinmu da ake k'ararsa ko mu ya'yansa bamu da alak'a da gonar Ladi farm ila yaumil qiyama."

Tana gama fadin haka sai da ta share ƙwalla ta kwashi takardun gabanta ta doshi mahafinsu.

Yayin da Abida da Yaya Usman suka yi kanta a harzuk'e, ganin duka zasu rufar mata da shi ya sanya Ya Asad ya shiga tsakani yana mai daka musu tsawa.

"Mene ne haka? A nan ne za ku yi mana haka? Kuma haka za ku yi mana?".

Ya fada idabuwansa sun yi ja sosai".

Ya Usman ya buɗe baki zai sake magana Ya Asad ya sake buga masa tsawa kafin ya ce" Usman ka yi shuru, mu ba dukiya ba ce a gabanmu gaskiya ne Munnera ta faɗa. Mutuwar Baba ƙarami da lafiyar Baba Babba ta fiye mana duniya da abin da ke cikinta."

Kalamansa suka sake sanyaya mana jiki, suma daga haka ba su sake ja in ja suka shisshige motoci suka bar haraban kotun aka bar mu cikin sanyin jiki, Mami ta yi sukuri ba magana amma ni na fahimci jikinta ya yi sanyi sosai.

"Mami kin ga ni? Mune ya kamata mu nunawa duniya cewa Baba ƙarami ya fiye mana duniya da abin da ke cikinta amma mun kasa. Sai ga shi su sun nuna mana karamci da dattako, sun bar mana gonar tunda mun nuna duniya ce a gabanmu ba mutuwar mahaifinmu ba."

Mami ta yi shuru kanta na kasa ta kasa mgana Ansari ma duk bakinsa ya kasa cewa komai.

Yaya Hamidaa ma cikin sanyin jiki ta ce" Wallahi na ji kunya. Na ji nadama ta shige ni."

Anisa ma ta amsa da cewa" Wallahi nima, sai na ji dama ba mu kawo ƙara, wannan fa shine sun watsa mana aniyar mu."

Mami ta saki gauron numfashi amma ta kasa mgana, wani abu ya yanke a kirjinta kamar nadama ne ya fara shiganta amma tabbas jikinta ya yi sanyi, kuma fuskarta ya bayyana haka, ni dai daga nan muka rabu da su suka kama hanyar Funtua sai da suka isa na k'ira Anisa take faɗa mini su Baba Babba gidan suka dawo amma sun ga ana ta haɗa kaya wataƙila ma har gidan gabaɗaya sun bar mana.

Ina sharan ƙwalla na ce" Sun yi daidai. Sun nuna mana idan kudi ne a gabanmu ga shi nan sun bar mana gabaɗaya."

Mami ma sun ce tunda suka koma jikinta yake sanyaye bata sake tayar da maganar ba. A raina na ce nadama marar amfani.

Baba Babba.

Murya a dakushe ya ce "Sannu Munira. Hakika Na gamsu da wannan shari'ar na kuma amince da hukuncinki da dukkan zuciyata na bar musu.

Allah ya rufa miki asiri Duniya da lahira.

Ina Usman, ina Abida?"

Ya fad'a muryarsa na rawa.

Suka amsa gamu Baba.

Ya ce "ku bude kunnuwanku da kyau, ku saurare ni, na amince da hukuncin Munira. Duk wanda ya tayar da maganar nan a cikinku lallai ni ya shirya yak'i da shi, kuma Wallahi idan na mutu wani cikinku ya tayar da maganar to lallai ban yafe ba".

Wannan kalamin shi ya sanyaya musu jiki suka hakura kann dole.

"Na fad'a miki ba za ki bisu Abuja ba Abida! Sulaiman ya fada cikin jarumta da son motsa mata kwanji.

Dariya marar nishadi ta yi masa tare da ce wa "Mutuwa kadai zata hana ni bin ahalina.

Ai tunda kuka kasa fadawa gyatumarku gaskiya ba sauran aminci ko Zama a tsakaninmu. Dama ni saboda kyautar da zan yiwa Bilki na aure ka, ba sonka nake yi ba. Yanzu kuma na gane had'a zuria ma da ku kuskure ne babba."

Ga mamakinsa sai ba hassala ainun ba domin zai Dade Bai ya abin da tayar masa da hankali ya Kona masa rai irin wakiar da take faruwa a gidansu.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya rasa mai zaice mata.

Ta sake ce wa "Ban yi zaton rashin kirkin mami ya kai kurewa ba. Tunda na gane nan duniya ba wanda ya isa da ita ai kuwa dole a guji hada zuria da ita. Yanzu haka ina da ciki na tabbatar a Germany na kwaso cikin nan wanda kaddara ce ta saka aka yi tarayyar. Sai dai ba zan haife ba, da ikon Allah sai na zubar da shi ya bi rariya"..

Ashe a lokacin ma bakinta dauke yake da maganin da ake sanyawa k'asan harshe wanda take tayar da nakuda bakatatan.

Karfin hali ya sanya take magana amma a cikin azabar ciwon mara take.

Ba zato kuwa ta fadi k'asa jini ya b'alle take ta suma.

Haka ya kwashe ta zuciyarsa ta bushe ga ni yake ma tamkar ya haukace tsananin bacin rai na dibansa.

Munira da Usman sun ga sadda ya fito da ita tamkar gawa ya saka a mota.

Dan haka suka fito sai dai tuni ya ja mota zuwa asibiti.

Haka aka bata taimakon gaggawa ta farafado aka daura mata ruwa da allurai na rage ciwo da zugi.

Kwanata biyu aka sallame ta.

Ta kuwa tubure sai ta bisu Abuja.

Shi Baba Babba tun jiya Yaya Faruk ya kai shi tunda zai ga likita washegari.

Munira kuwa zata bi momi ne daga nan ta shiga jirgi ta koma inda ta fito.

Kan dole suka tafi da ita. Sulaiman ya zuba mata ido don gabad'aya a rikice yake, hankalinsa ya rub'anya tashi akan kalamanta mussaman maganganun da ta fada akan mami sun masa tsauri na gaske a zuciyarsa.

✍️

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tafiyar Abida ta sanya Ya Sulaiman cikin ruɗani mai yawa, ya raunana duk da ya saka jarumtar dannewa da gudunmawa dakakkiyar zuciyarsa,amma abin da ke ɓoye a cikin zuciyarsa ya bayyana har a saman fuskarsa zuwa gangar jikinsa, a tsaye yake amma kana kallonsa za ka fahimci maza sun raunana sannan zuciya na ciwo.

A cikin zuciyarsa ya ƙullaci Ya Asad a matsayinsa na babba me yasa bai dakatar da Abida ba? Aure ne a kanta amma ta kama hanya ta bisu ba da izininsa ba, bayan ta gama faɗa masa munanan kalamai akan mahaifiyarsa, sannan har da Baba Babba ko da Abida ta bisu a lokacin da baya cikin sukunin da zai dakatar da ita, to a yanzu fa da ya warware yake samun saukin jiki da na zuciya? A ganinsa kamata ya yi su zaunar da ita, su sake jadadda mata daraja da ƙima irin ta aure, sannan idan har zasu yi masa adalci ai ba shi ya yi laifin ba, bai kuma kamata laifin Mami ya shafe shi ba. Mami uwa ce a gare shi ko akan bola take rayuwa ba zai guje ta ba, kuma tilas ne ya yi mata biyayyaa. Amma tsabar tsaurin ido har ta iya kallon idanuwansa ta kira sunan Mami ta jingina mata munan kalamai. Sannan mafi baƙin cikin abin da Abida ta yi masa shi ne ta yi sanadiyar lalacewar gudan jininsa, ashe bata son shi? Duk da yana ganin soyayyarsa a cikin idanuwanta. Amma tunda ta iya cewa had'a zuria da uwarsa abin kaico ne! Lallai dole ya nuna mata kuskurenta don bai yi lalacewar da zata furta masa wannnan k'azamar kalmar akan idanuwansa ba, sannan ta fi a iska. Cire masa ciki da ta yi ya sake harzuk'a shi tare da alwashin ko sonta ne ajalinsa ta yi kad'an ya neme ta da sunan sulhu. Haka nan ba zai sake ta ba, amma idan ta nemi ya sake ta da kanta, to la shakka take yanke zai sake ta din. Yanzu ma idan zata shekara dubu ba zai bi bayanta da sunan biko ba. Kuma ko sun dawo da ita matukar ba ta yi tuba kan kalamanta ba to kuwa babu ita babu sake jin dadinsa matuƙa da aniya ta ɓata masa rai kuma ya ƙullase su kwarai da gaske. A ransa yake ta sakesaƙe, me ya rage masa a wannan duniyar yanzu? Babu Baba ƙarami, babu Baba Babba da iyalansa, sannan babu mata babu ƴaƴa, ƙannensa kuma matan ne kawai. Ansari ya juya masa baya. Mami bata sauraransa to shi me ya rage masa a wannan duniyar ne? Ya so ana gama shari'ar nan ya zubawa Mami ido ta yi komai yadda take so sai kuma ya kasa ganin ta yi sanyi sosai kamar ba Mami ba, maimakon abin da take fata na mallakar ladi farm ta yi farinciki amma ba ta yi ba sai ma yake ganin ta cikin rashin sukuni kamar dana sani da nadama suka yi mata k'awanya amma ta kasa furtawa kowa. Shi kansa Ansari duk ya yi sanyi ya daina cika baki, tunda ga dukiyar ga gidan gabaɗaya an bar musu amma kuma sun kasa farinciki. Saddiqa da yaya Hamida dama tun ranar zaman kotu sun furta nadamarsu. Mami da Ansari ne ba su yi magana ba amma ko basu furta komai ba yanayinsu kawai ya isa ya bayyana suna cikin damuwa da nadama.

Ganin komai ya 'kare, dukiyar da Mami take haƙilo ta dawo tasu, to me za a jira kawai sai ya samu Mami ya ce a raba gado a ba wa kowa nasa kason.

Mami ta shiga tashin hankali cikin damuwa ta ce" Saurin me kake yi haka Sulaiman? Ka bari ko zuwa nan gaba idan mun sake samun natsuwa."

Kai tsaye ya ce" Wata natsuwa kuma Mami? Ai gidan nan tuni mun yi sallama da natsuwar zuciya har da ta gangar jiki. Gwara a raba a sallami kowa tunda dukiyar muke so kuma ga tanan an bar mana."

Mami ta kasa magana da Ansari ya zo ta faɗa masa shima dai bai ce komai ba, illa iyaka ayi abin da Ya Sulaiman yake so a raba a bawa kowa nasa kason sha'anin gado da komai ma ya ƙare.

Mami ba ta da cewa dole ta amince aka haÉ—a dukiyar waje É—aya Ya Sulaiman ya gayyato malamai aka zauna aka raba gado daidai yadda Addini ya hukunta ya tanadar.

Wurin da Ya Sulaiman yake zaune ya fito a nasa kason, sannan bangaren Mami ya fito ana Ansari. Mu kuma matan sai muka yi mubaya'a zasu fitar da mu a wasu gidajen na wasu garuruwa, ni na samu gida mai kyau a garin Katsina. Saddiqa da Anisa anan garin Funtua suka samu na su gidajen.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: In da ace Baban Amra yasan yadda na ke kwana na tashi da ƙunar zuciya kan rashin Abida da bai ce haka ba amma sanin ba zai gane komai ba yasa ban tsaya yi masa bayani ba ina cikin damuwa, damuwar da ta ke cin zuciyata sannan yana kassara gangar jikina amma shi duk bai lura da haka.

Kwanaki kadan sai ga sako wai kaninsa da muke zaune a bangarnasa zai fara gyaran wajen don aurensa watanni uku suka rage, a kuma wajen zai zauna. Hankalina ya yi tashin gauron zabi tare da tuna lokutan baya muna Kano da na dinga yiwa Sahal nacin ya sayi gida ko na rainawa ne ya zuba haya. Ga irin ranar da nake guje masa ta zo. Yanzu ina muka dosa ke nan? Don ko giyar wake muke sha ba zamu bawa Hajiya notis din tashi tamkar yadda k'aninsa ya bamu ba.

Na sake kutsawa cikin nazari tare da tunano Sahal bai ajiye komai ba ban da k'aton fegen da ya siya shekarun baya. Tabbas wajen ya zama unguwa mai daraja a yanzu. Tare suka siya da yayansa da shine babba a dakinsu. Dan haka filayen biyu a jere suke manya na sosai.

Shi kansa hankalinsa ya tashi, tunaninsa ya kulle. Ya shiga damuwa kullum da zullimin inda zamu koma yake kwana da tashi. Da na ga ya shiga rudani ainun sai kawai na yi masa tayin mu koma gidana da ya fito a gadona a maimakon mu je mu kama haya. A farkon kamar ba zai amince ba, amma da ya yi nazarin ba shi da mafitar da wuce hakan sai ya amince mini. Dad'i ya kama ni, dama a matuk'ar takure nake da zamana a cikin gidansu mussaman idan sister's dinsu sun zo. Ba k'aramin takaici suke guma mini ba, mussaman Yaya Tourai bansan me na tsare mata ba.

Da labarin komawarmu gidana ya iske su kuwa ba abin da basu ce ba. Ai yanzu zan sake d'agawa da izza. Na cinye masa arziki, nawa yana ta habaka. Amma da yake na gama da shi ya kasa fahimtar ni din ba alheri ba ce, don a lokacin da yake cikin arzikinsa ai a jere na dauko haihuwa saboda na tara magada. Amma tunda na tsiyata shi na kulle bakin mahaifa na k'i haihuwa. Dan kuma na nuna musu isa na dauko yar riko babu neman amincewar miji bare ta uwarsa. A sa'ilin da na ji suna furta wadannan kalaman murmushi kawai na yi, domin tashin hankalin da ya faru a gidanmu ai ya wuce ƙaramin abu ya zauna yana damuna.

Amma da Baban Amrah ya dawo na sanar da shi, na ce masa Idan bai gamsu da shawarar komawarmu gidana ba, to ya kama mana haya babu damuwa. Jin na ce haka ya yi maza ya ce shi ba shi da matsala yasan halina duk abin da na mallaka ai kamar nasa ne, kar na damu da masu magana. Yasan ni rufin asirinsa ce. Ashe shima yasan ƴanuwansa suna ta yamididi akan batun. Hajiya ma da na shiga gaishe ta sai da ta yi mini maganar komawarmu gidana na ce mata ina son mu koma ne tun da ko bamu zauna ba y'an haya zamu saka, sannan muma hayar zamu kama, to gwara mu koma ɗin. Ta ce "hakan na da kyau, ganin Baban Amra ya amince shi da Hajiya sai na fara shirin tarewa, bayan mun je mun duba gida lafiyayye ne, sai ɗan gyaran da ba za a rasa ba Baban Amra na barwa bangaren gyare-gyaren gidan, na kira Ya Sulaiman na faɗa masa ya ce hakan da na yi daidai ne. Mami ma da na kirata ba ta ce komai ba, yanzu ba ta cika doguwar magana ba, ni tsorona kar a ce haƙƙin Baba Babba ne ke bibiyar Mami, saboda yanayin da take ciki ya yi tsawo. Ya kamata a ce ta saki jikinta zuwa yanzu, amma kuma lamarin nata sai ƙara lalacewa yake yi, ba wanda yasan meke damunta amma mu munsan ba zai wuce nadama da girman haƙki ba.

Shiryen -shiryen tarewarmu na mayar da hankali, duka duka lokacin wata É—aya ne da rabon gadonmu, har mun fara parking din kaya tun da gidan an gama gyara komai ya yi fes kamar sabo, wata ranar jumma'a da asuba wayar Yaya Sulaiman ta tashe ni, wayar da ta tafi da numfashina na wani lokaci, wai faÉ—a mini yake yi na taho gida mun rasa Mami!

Mami fa, mamin da ko jiya da daddare na kira ta mun gaisa har ina jin daÉ—in ta saki jiki mun yi hira har na bawa yara suma suka gaisa da ita, ita ce wai Ya Sulaiman yake faÉ—a mini ta rasu? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Na faÉ—i kasa ina kuka, ina birgima ina faÉ—in na shiga uku na lalace! Baban Amrah ya kasa iyawa da ni sai da ya je ya kira Hajiya ita ta zo ta zauna da ni tana lallashina.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Bilki bar kuka, mamaci ba ya buƙatar wannan kukan na ki, addu'arki kawai take bukata a yanzu, ki yi hakuri, ta shi, bari na shirya, kai Sahalu shirya yaran yanzu mu kama hanya."

Kuka kawai nake ina faɗin "Na rasa Baba ƙarami, na rasa Mami, na rasa Abida na rasa Baba Babba na rasa kowa ina zan saka raina."

Lallashina kawai take yi tana ce mini ina da Allah na yi shuru kar na yi saɓo. Har muka kai Funtua kuka na ke yi ban sake tsinkewa da lamarin duniya ba tabbas ba sai da na ga gawar Mami lulluɓe cikin likkafani, a lokacin na sake tsinkewa da sha'anin rayuwar gabad'aya. Tabbas duniya zancen banza ce, yau ga dai Mami ta tafi inda Baba ƙarami ya tafi bayan duk faɗin tashin da ta yi akan dukiya yau itama ta mutu ta barsu ko sisi bata ci a ciki ba. Wallahi duk wanda bai ji tsoron Allah ba ya yi kaico a rayuwarsa, mutuwar Mami izina ce sannan wa'azi ne ga mai hankali. Mutuwar kwatsam, da daddare Ya Sulaiman ya ce ya shigo bangarenta suka yi hira ta ce mai za ta sha magani kai na sara mata suka yi sallama ta shiga ciki, da asuba ne ya kasa natsuwa kafin ma ya kai ga zuwa masallaci ya shiga bangarenta tuni mai ikon rai ya yi ikon shi sai dai ya tarar da gawa har ta fara sandarewa alamun ta jima da rasuwa wataƙila tun farkon dare. Allahu Akbar rai baƙon duniya sai ga ƴanuwan Mami da ta rayu akan cewa ba sonta suke ba, take adawa da su, sune suke zagayemu da ita gabaɗaya, muna kukan rasa uwa, su kuma suna kukan rasa y'aruwa. Mutuwar Mami ta kassara sauran kuzarina ta kuma tafi da kaso mafi girma daga cikin yaƙinin rayuwata.

Kafin a kai gawar Mami kushewa su Baba Babba suka iso, bawan Allah nan mai yakana ne da yiwa zumunci kara, kaf É—in su suka zo har da Abida da na ga ta yi wani kiba fuskarta ta kumbura ta zurma wani babban hijabi da na kasa gane wani yanayi take ciki. Ya Asad ne kawai bai zo ba, na ji Baba Babba na faÉ—awa Kawu Bala ce wa ba ya k'asar ne.

Baba Babba da Momi da su Ya Faruƙu har gaban gawar Mami suka ɗuka suka yi mata aduua.

Baba Babba ya kallemu kafin ya ce" Ku daina kuka, ku yi mata addu'a domin a wannan lokacin ita ta fi buƙata, Allah ya jiƙanki Habiba Allah yasa kin huta. Allah ya shaida na yafe miki, babu kullinki a zuciyata. Allah yasa ki shiga a sa'a."

Ya kammala fadin hakan hawaye na kawo masa, ya warke kamar ba shi ba, daga ganinsa yana samun kulawa sosai, yana hawaye, muna kuka sai na ji kamar na tashi na je na faɗi kan kafafunsa na fashe da kuka amma ba hali. Abida ta mini gaisuwa amma a takaice duk da na ga mutuwar ta buge ta ainun. Momi ta zauna tare da mu da kuma yanuwan Mami anan falon bayan an tafi kaita. Abida ma tana tare da mu sai wajen azahar sannan ta tafi bangaren momi ta kwanta kana ganinta kasan bata ma da cikakkiyar lafiya wataƙila ma akan dole ta zo. Duk da ina cikin zafin mutuwa sai nake ganin kamata ya yi ta bude bangarenta ta zauna ko dan hankalin mijinta ya samu daidaito. Gabad'ayanmu a firgice muke sosai da mutuwar nan ta mami. Amma Ansari ne kan gaba wajen firgici gwanin ban tausayi tunda Mami ta rasu yake zabura yana neman hanyar gudu kamar ya zare, mutuwar ta gigita masa tunani fiye da tunanin kowa, to ai dole. Ansarin Mamine. Shi ne abokin sirrinta duk wani abin da ta aikata da sahalewarsa, dole ya gigice gabaɗaya ya zare kamar wanda haukan dare ɗaya ya same shi. Aan dawo daga kai Mami an zauna ana karɓan gaisuwa. Baban Amra da Hajiya kwanan su uku suka juya da yara. Baba Babba da iyalansa kwana daya suka yi suka koma gabaɗayansu. Da za su tafi sun shigo har bangaren Mami sun yi mana sallama amma ban da Abida, ban ganta ba sai da na raka su haraba na ganta a cikin mota, ya Usman sabe da Farha ya leka ta bangaren da take zaune. Ina jin yana ce mata "Ko kina son tafiya da yarinyarki?"

Gabana ya buga da k'arfin gaske don kuwa raba ni da farha a lokacin ba karamin gigicewa zan sake yi ba. Nan da nan na ga ya Sulaiman ya zuba musu ido cikin hassala irin wacce na jima ban ga ya yi ba. Kafin mu yi magana, muka ji Abida ta ce "A a Ai ba yarinyata ba ce ta Bilki ce, munafikine mai yin alk'awari ya sab'a. Mik'a mata d'iyarta".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: A sanyaye ya dire ta, yarinya kuwa ta nufo ni. Na rike mata hannu ina ta hamdala don da ace sun yi gangancin ce wa zasu tafi da ita tabbas Yaya Sulaiman da Yaya Usman zasu yi kare biri jini sai dai idan Baba ne ya tsawatar. Don Yaya Sulaiman ya fuskata da su sosai. Haka aka shiga sallama da fatan Allah ya sauke su lafiya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya Sulaiman da Baba Babba suka yi maganar da ban ji me suka ce ba, sai su Ya Faruku da suka yi musabaha. Har suka tafi magana ta fatar baki ba ta haɗa shi da Abida ba, tun ranar da ta zo ta ce masa ya hakuri a cikin bainar nasi, shike nan ta'aziyar da ta yi masa. A tunaninsa ma a bangarensu zata sauka har su samu sulhu ashe ita da gaske take bata sonsa, ta kuma shirya rabuwarsu har zuciyarta. Duk yadda ya ƙullace ta, amma sai ya ji ya damu da yanayin da ya ganta na rashin lafiya da rashin kuzari. Amma ya riga ya kudire ba zai neme ta ba tunda dai bai mata laifi ba, bai kore ta ba. Sannan rashin ware shi ta yi masa ta'aziyar mahaifiyarmu cikin mutunci da tausayawa, ya sake tsananta fishinsa a kanta tare da lasar takobi lallai rigima yanzu aka fara tsakaninmu da ahalin Baba Babba tunda akan idon Baba da na Yaya Asad Abida take yi masa wannan rainin da kuma wulakanta masa aure amma basu taka mata burki ba, ya fahimci inda matsalar take akwai sauran jidali kuwa. Idan har zuba ido suka yi suna dakon ya je bikonta to kuwa ila yaumil kiyama ba zasu gan shi a gabansu akan batun Abida ba.

Daga ni sai Ya Sulaiman muka yiwa su Baba Babba rakiya. Ya Hamida har tana zagina wai ba ni da zuciya uwarmu ce fa ta rasu amma sun zo sun kwana ɗaya tal Abida ma saboda wulakanci tafi ƙarfin ta yiwa mutane magana. Ni dai ban ce komai ba ganin rasuwar Mami ta saka Ya Hamida ta koma masifafiya sannan ta gasgata yamididin da ake yi a gari cewar Baba Babba ne ya yiwa Mami Yasin shiyasa ta sururuce sannan dare d'aya ta yi bindiga ta mutu. Gabadaya Yaya Hamida ta tsanesu da gaske. Ni dai bana um bare um um. To ni me zai dame ni ballatana na kulata, bayan na rasa komai, duka duka kwanan Mami hud'u ne da rasuwa W.H.O ta turo mini saƙon sun sallame ni daga aiki sakamakon contract ɗina da su ya ƙare, dama shekaru uku ne, na yi biyu a Kano na zo Katsina na cike d'ayar.

Shi yasa har muka k'are zaman makoki, ban yarda na biye mata ba. Har ce wa ta yi ita da Asad har gaban abada tunda bai zo mana ta'aziyar uwarmu ba. Duk da Baba Babba ya hadamu da Shi a waya ya mana ta'aziyar smma hakan bai yi mata ba.

Ansari ne mai baki a baya amma yanzu ya yi sanyi tun bayan rasuwar Mami mutumin da sai da aka haɗa masa da rokon Ubangiji tare da ruwan rubutu. Tun lokacin Ya Hamida ta ɗauki ragamar nuna tsana ga ahalin Baba Babba da ni, kuma haushinta yafi yawa a kaina tunda ta ce ni ce ban daina ƙulafuncinsu ba. Ni dai ban biye mata ba, kwana goma na yi a Funtua na tattara na koma Katsina. Amma gangar jiki da zuciya sun raunana gani nan ne dai kamar wata mara lafiya sai da na koma gida ne Baban Amra ya san contract din aikina da W.H.O ya k'are yanzu sai dai na koma zaman gida. A wannan gab'ar Baban Amra ya tausaya mini ya kuma tsaya tsayin daka shi da Hajiya wajen kula da ni da lallashi, shi ya sa ko wani takaicin ya tusa mini idan na tuna da wannan karamcin nasa, sai na ji na yafe masa. Shi da Hajiya sun yi ƙoƙari a kaina ba don su ba da tuni depression ya kama ni.

Sannan Ya Sulaiman ma ya yi ƙokari a kaina shi ya sa har yau ban daina kuka idan na tuna da shi ba, da a ce yau yana nan da wataƙila kewa ba ta yi mini k'awanya da yawa ba. Saboda yanayin da na ke ciki ya sa maganar komawarmu gidan nan ya sha ruwa saboda ba na cikin natsuwata.

Ko wata ɗaya Mami ba ta yi a k'asa ba Ya Sulaiman ya ce za a raba gadon duka dukiyar da Mami ta mutu ta bari, saboda ba ya son a sake samun wata baraka daga bangaren gado, shi ya yi tsaye akan komai ga ruwan kuɗi ga kaddarori, kuma ya ce ba zai riƙe kudin kowa ba, dukkanmu ya damƙa mana haƙkinmu a hannunmu. Kayan Mami kuma an fiddo su an ce idan muna som wani abu mu ɗauka idan kuma bama so za a sadakar da shi da amincewarmu tun da haƙƙinmu ne gabadaya. A cikin kayan sai na ga wata sarkar azurfa da na taɓa siya ta nuna tana sonta na cire na bata, ina son sarkar nan sosai,ita kaɗai nake so a ciki kayanta. Na ɗauka na ce "ina son wannan Ya Sulaiman".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya ce na ɗauka Ya Hamida ta taso tace itama tana so, ni ko da naga na riga ta ɗauka sai na ce ai na riga ki, Aman ga wata na nuna mata wata ta azurfar wadda tafi wacce na dauka din ma girma. Nan da nan ta fara sababi tana faɗin na dai riga kai hannu amma dama ta faɗawa su Saddiqa sarƙar take so. Raina ya ɓaci na ce " sakarkar fa dmaa tawa ce, ganin ta nuna tana so me ya sanya na bar mata. Yanzu don na ce ina son kayata sai ya zama jidali ? Haka kawai na ambata Ya Hamida ta fara kuka tana faɗin na yi mata gori don na ga Mami da Baba ƙarami basa raye, dama tuni ta fahimci na fi son su Abida a kansu, to na je tunda su na riƙe itama ta zare hannunta daga mu'amala da ni, daga wannan lokacin zumumcin mu ni da Ya Hamida ya samu tawaya, tawayar da har yau bai koma daidai ba.

Kalubalen da ake fuskanta akan matsalolin rabon gado masu girma ne, faÉ—a tsakanin y'anuwan juna, faÉ—an tsakanin yan É—aki É—aya, faÉ—a akan kuÉ—i ko wani kadara, sannan yanzu gidan gandu da yawan mutane son rasa hakkunansu saboda haÉ—aka da rashin rabawa. Sai bayan sun rasu Æ´aÆ´ansu sun taso, sun nemi hak'kin iyayensu rigima ta taso da za ta yi silar rabuwar zumunci. A bar katon gida ba'a raba kowa ya yanki waje ya yi Gini ba tare da iyakance hak'kin kowa ba. Sun manta cewa bayan su akwai Æ´aÆ´an su da za su taso. Mata na fuskantar k'alubalen rashin raba hak'kin gidan mahaifinta da ita, za ta yi aure a wani gidan idan aka tashi rabon gado masu tsoron Allah me ke fitar da ita da kudi ko Sa wani fili, amma galibi Æ´anuwa maza da ahalinsu ke babakere a gidan. To idan aka bari aka cigaba da tafiya da sha'anin gado yadda Malam bahaushe yake yi to la Budda an dinga samun baraka a cikin zumuntarmu. Gidajen gandu a a k'asar Hausa yana wahalar gaske a iya raba shi saboda yadda ake zaune kara zube.

Ko babban wa ya yi babakere akan dukiyar k'annensa duk kuma wanda ya fito ya ce a bashi hak'kinsa sai ya zama abin tattaunawa abin zunde a kuma ware shi ace yana son tada fitina.

Muna rayuwane da mutanan da basu dauki dukiyar gado da tsantseni ba. Alhalin cikin abin da Annabi ya yi ta jan kunnenmu tauye hakkkin magada na kan gaba, tare da yi mana gargadi mai tsananin gaske don kuwa hadarin cinye dukiyar magada tamkar kana d'urawa kanka wutar jahannama ne a cikinka.

Sulaiman..

Shi kaɗai kawai ya ke tunanin yanzu me ya rage masa? Ba shi da uwa ba shi da uba, haka nan ba shi da mata ba shi da ƴay'a y'anuwansa da zumunci ya haɗa su sun tarwatse me ya rage masa a halin yanzu? Shi kaɗai ya fara wani tunani, tunda ya gama sauke nauyin gadon dukiyar Mami kuma ya damƙawa kowa nasa kason to lokaci ya yi da shima zai nemawa kansa mafita. Ansari an samu ya dawo hayyacinsa ya ɗau dangana. Saddiqa da Anisa suna cikin rufin asiri haka ma Hamida.

Bilki ce abin tausayi yanzu ba ta da kowa a kusa da ita duk da sun zama attajirai saboda yawan kuɗin da gado ya samar musu. Balki ta fi zama abin tausayi kuma marainiya ta sosai a wannan gab'ar, ga rashin aikin da yake rage mata damuwa. Da a ce za ta samu wani aikin da ya ɗebe mata kewa, matuƙa yana jin tausayinta ganin ba Abida a kusa da ita, don shine shaida Bilki da dukkan zuciyarta take son Abida, duk da ya gasgata Abidan ma na sonta. Babban abin da yake sake sa shi jin tausayinta shima zai yi nesa da ita na wani lokaci. Ga mijinta shima ba shi da wani aikin hi rayuwarta akwai tausayi a ciki, kuma idan ba'a kai mata dauki ba komai nata zai kare ne tunda yasan yadda zuciyarta take komai fitowa zata yi da shi su saka a gaba.

Shi kaÉ—ai ba tare da sanin kowa ba ya fara fafutukan nema mini aiki, ni dai ya kira ni ya saka ni na tura masa duka takarduna, kuma cikin ikon Allah lokacin ya yi daidai da n'ada Baban abokinsa Salim Buba da suka yi karatu a Germany tare sabon V.C na jamiar dama y'an jihar Katsina ne a garin Mashi. Da taimakon Salim ya samo mini koyarwa a jami'ar Umaru musa y'ar aduwa.

*MalaysianFabrics*

*Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.*

*Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.*

*7020695644.*

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Lokacin da Upper ɗin ta fito da kansa ya shirya ya zo gidana, na yi mamakin ganinsa amma sai murna ya danne mammakina, na yi ta rawar jiki da shi, na rasa ina zan saka shi na ji daɗi, ga shi yara ba sa gida baban Amra ma baya nan ya shiga cikin gari. Na share hawaye a ɓoye saboda shi kadai ya ke damuwa da lamarina a yanzu. Ya Hamida da gaske take ta yanke alak'a da ni, ba ta k:irana ko na k'ira ta sai ta ga dama take ɗauka. Su Saddiqa ba kasafai muke mgana da su ba, Duk ta zuge su. Ya Sulaiman ɗin ne kaɗai na ke gani na ji daɗi, lokacin da ya damƙa mini upper ɗina ta aiki bansan ya aka yi narumgume shi ina fashewa da kukan dan nake ta danne shi ba. Murna da tausayin kaina suka dabaibaye ni. Ina kuka ina faɗin" Na gode sosai Ya Sulaiman, na gode Ubangiji ya yiwa rayuwarka albarka, ya tsare ka ya sanya albarka a dukiyaka da ya'yanmu, Allah ya jiƙan iyayenmu."

Ya amsa da Amin kafin ya ce" Ba komai Bilkina ni dai fatana ki nutsu, ki yi haƙuri, ki rungumi mijinki da ƴaƴan ki, ki koyi juriya da yadda za ki iya tsayawa kanki ko da ba ki kowa a duniyar to ya zama kina da Allah kina da kanki!

Sai na ji maganganunsa masu kama da yana barin wasiyya ne.

Hankalina ya tashi kar ya zo shima mu rasa shi kamar yadda muka rasa Mami da Baba ƙarami.

"Yayw Sulaiman waÉ—anan mganganun fa? Ina za ka je?"

Na faÉ—a cikin damuwa da tashin hankali

Sai ya yi saurin ce wa" Ba komai Bilkina, wata yar tafiya zan yi amma kar ki tayar da hankalinki, idan da rabo za mu sake haÉ—uwa."

In jin ya ce haka na fara kuka ina faÉ—in" Na shiga uku Ya Sulaiman kai ma barinmu za ka yi! Don Allah kar ka tafi ka bar ni."

Hannayena ya riƙe cikin nasa kafin ya ce" Na ce ki kwantar da hankalinki ba zan daɗe ba, zan dawo, ke dai kawai ki koyi dauriya da jarumta, komai zai wuce, kina da ƴaƴa da mijin da wata rana za su iya zama garkuwa gare ki"

Duk yadda na so Ya Sulaiman ya faɗa mini k'udurinsa bai yi ba, ban dauka ganin k'arshe na yi masa idan a ce na san haka da ko za a mutu bazan bari ya bar gidan nan ba. Ganin yadda nake ta kuka yasa ya ɓata lokaci wajen lallashina har sai da ya ga hankalina ya kwanta.

Har abinci sai da na yi masa kuma ya ci mun d'ade muna hira yana ta mini nasihohi yana ce mini na kula da rayuwa, na kuma saka ido sosai akan yara. Ni kam na gama tsorata da jawabansa ya yi mini fatan alheri da fatan nasara sannan ya ce zai tafi.

Na ce ya É—an jira su Farha sun kusa dawowa.

Ya kalleni kafin ya ce" Farha kaÉ—ai sauran yaran fa?

Na yi shuru ban yi mgana ba.

Ya numfasa ya ce "Ki daina danganta Farha da ni Bilkina, d'aya take da su Amra a wajena, ba tawa bace ta kice tun kafin ta zo duniya kowa ya tabbatar da cewa Farha taki ce don kuwa na fi Abida cancantar na ba ki ita".

Na ba shi haƙuri ganin ransa ya ɓaci sai da na tabbatar da ya hakura sannan na sakoasa batun Abida tare da fatan ya dauke ta Su tafi inda zashi don na tabbatar hakane kadai zaisa hankalinsa ya nutsu. Ya girgiza kai ya ce "Bilkina ban saki Abida ba, amma matukar sai na nemi ta dawo gare ni to la shakka na haramtawa kaina ita. Bamu samu matsala da ita ba, ban mata komai ba, Baba da Yaya Asad suka zuba mata ido take yin yadda ta so, saboda kawai ba ni da Baba k'arami. Muryarsa ta karye. Ni kuwa kuka nake yi sosai don na gane ba k'aramin ciwo lamarin yake yi masa ba jarumta kawia yasa ciwo Bai kada slazzphi ba saboda tsananin damuwowin da suka yi masa k'awanya. Ya hadiye kukan dan ya so k'wace masa ya ce "Da ikon Allah sai na samu damar da zan tozarta Abida fiye da tozarcin nan da ta yi mini. Sai Allah ya ba ni dama na nunawa Asad iyakarsa. Saboda Yana da kud'i shiyasa ya shake Baba a maimakon ya tsaya ya daidaita komai a matsayinsa na babban wanmu"

Na yi shiru don ba ni da bakin magana don na lura Yaya Sulaiman'zfishinsa akan Yaya Asad fiye ma da Baba Babba akan batunsa da Abida. Na dinga ba shi hak'uri har ya d'an nutsu sannan muka yi sallama har harabar gidan na raka shi muka yi sallama cike da kewa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Baban Amrah ya dawo na nuna masa upper ya yi murna ya ce shima ya yi interview a makarantar tunda v.c din dan Mashi ne abokin Baban Zaria ne.

Kwana huɗu da zuwan Ya Sulaiman gidana ya turo mini saƙo da cewa ya yi nesa da mu na wani lokaci amma kar mu damu idan da rabo wata rana zai dawo.

Ashe ba ni kaɗai ya turawa saƙon ba dukkanmu ne, sai ga wayoyin su Ansari cikin tashin hankali. Ansari ya bani tabbacin Ya Sulaiman ya kwashe komai nasa kamar ma ya bar k'asar ne gabad'aya sanin inda ya nufa a yanzu sai Allah. Mun shiga matsannacin tashin hankali Ya Hamida ta k'ira ni a waya ta zage ni tas tare da cewa na ji daɗi wacce na ke karewa ga shi nan ta yi sanadiyar tafiyar Ya Sulaiman uwa duniya ina kuka ina so na kare kaina amma bata ba ni damar haka ba ta kashe wayarta.

Tafiyar Ya Sulaiman da rashin sanin inda ya nufa ya sake rauna ni, na shiga matsanancin damuwa. Baban Amrah ya samu lasisin zagin Abida tare da kusheta.

Duk halin da na ke ciki bai saka, ya hadiye abin da yake cinsa ba fada mini yake yi "Ai dama kallona kawai yake yi na hana shi ya je kotu ya karemu, saboda ba na so na yi laifi wajen Abida da Ya Muneera to ai ga shi nan sun nuna mini matsayina, daga karshe su sun cure kansu waje É—aya mu kuma sun samu nasaran tarwatsa mu, tunda ga shi Ya Sulaiman ya shiga duniya ba a san in da ya tafi ba, kuma yasan har da bak'in cikin Abida da ubansu ne ya sanya ya fantsama duniya. Ban da ma kaddara me zaisa Sulaiman kallon yarinyar nan da Sunan soyayya? Ta gama yin kwantai ta samu ya rufa mata asiri shine har take jin kanta ita wata tsiya ce. Kallon shi kawai na ke yi ban iya shuru ba sai da na ce masa" Baban Amra ban da karfin halinka ina ruwanka ne da zaka ce zaka shiga shari'ar gidanmu?"

FaÉ—in haka sai ya sake jawo mini ya dinga jefa mini maganganu da ce wa dama ya ga taketakena tunda na yi kuÉ—i na fara masa wulakanci to kar na manta shi É—in garkuwata ne. Bak'in ciki ya turnike ni wai fashe masa da kuka ba tare da na sake ce wa komai ba. Ganin kukana ne ya saka ya sauko ya shiga aikin lallashina da nuna mini ya damu da ni shi yasa ya damu da damuwata.

Ni ko na ce idan har ya damu da damuwata kar ya sake dago mini wannan maganar, ya ce ya yi alƙawari.

Da gaske kam ya bar maganar domin kwana biyu haka ya shiga ririta ni, har wanka ma da taimakonsa nake yi. Gidanmu na Funtua ba kowa a ciki gida ya zama kango, ita kanta Ladi farm din Ansari ya ce ma'aikata na ta sallaman kansu, ba kula abubuwa dai duk sun lalace a gidan gonar tun barin Yaya Farouk garin Funtua.

Idan na zauna ina hakaito lamarin gidanmu sai na ji kamar zan yi hauka saboda baƙin ciki da takaici, da zaran na tuna sai na samu kaina cikin kuka, kuka mai karfin da bana sanin ma lokacin da na ke zunduma shi da iyakacin k'arfina.

Tabbas mun yi rashi, gidanmu ya ruguje ya zama kango.

Mami da ta gama yaki akan dukiya ta mutu ta barta, mu kuma muna ji muna ga ni gidanmu na Funtua ya zama kango.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Lokacin da Upper ɗin ta fito da kansa ya shirya ya zo gidana, na yi mamakin ganinsa amma sai murna ya danne mammakina, na yi ta rawar jiki da shi, na rasa ina zan saka shi na ji daɗi, ga shi yara ba sa gida baban Amra ma baya nan ya shiga cikin gari. Na share hawaye a ɓoye saboda shi kadai ya ke damuwa da lamarina a yanzu. Ya Hamida da gaske take ta yanke alak'a da ni, ba ta k:irana ko na k'ira ta sai ta ga dama take ɗauka. Su Saddiqa ba kasafai muke mgana da su ba, Duk ta zuge su. Ya Sulaiman ɗin ne kaɗai na ke gani na ji daɗi, lokacin da ya damƙa mini upper ɗina ta aiki bansan ya aka yi narumgume shi ina fashewa da kukan dan nake ta danne shi ba. Murna da tausayin kaina suka dabaibaye ni. Ina kuka ina faɗin" Na gode sosai Ya Sulaiman, na gode Ubangiji ya yiwa rayuwarka albarka, ya tsare ka ya sanya albarka a dukiyaka da ya'yanmu, Allah ya jiƙan iyayenmu."

Ya amsa da Amin kafin ya ce" Ba komai Bilkina ni dai fatana ki nutsu, ki yi haƙuri, ki rungumi mijinki da ƴaƴan ki, ki koyi juriya da yadda za ki iya tsayawa kanki ko da ba ki kowa a duniyar to ya zama kina da Allah kina da kanki!

Sai na ji maganganunsa masu kama da yana barin wasiyya ne.

Hankalina ya tashi kar ya zo shima mu rasa shi kamar yadda muka rasa Mami da Baba ƙarami.

"Yayw Sulaiman waÉ—anan mganganun fa? Ina za ka je?"

Na faÉ—a cikin damuwa da tashin hankali

Sai ya yi saurin ce wa" Ba komai Bilkina, wata yar tafiya zan yi amma kar ki tayar da hankalinki, idan da rabo za mu sake haÉ—uwa."

In jin ya ce haka na fara kuka ina faÉ—in" Na shiga uku Ya Sulaiman kai ma barinmu za ka yi! Don Allah kar ka tafi ka bar ni."

Hannayena ya riƙe cikin nasa kafin ya ce" Na ce ki kwantar da hankalinki ba zan daɗe ba, zan dawo, ke dai kawai ki koyi dauriya da jarumta, komai zai wuce, kina da ƴaƴa da mijin da wata rana za su iya zama garkuwa gare ki"

Duk yadda na so Ya Sulaiman ya faɗa mini k'udurinsa bai yi ba, ban dauka ganin k'arshe na yi masa idan a ce na san haka da ko za a mutu bazan bari ya bar gidan nan ba. Ganin yadda nake ta kuka yasa ya ɓata lokaci wajen lallashina har sai da ya ga hankalina ya kwanta.

Har abinci sai da na yi masa kuma ya ci mun d'ade muna hira yana ta mini nasihohi yana ce mini na kula da rayuwa, na kuma saka ido sosai akan yara. Ni kam na gama tsorata da jawabansa ya yi mini fatan alheri da fatan nasara sannan ya ce zai tafi.

Na ce ya É—an jira su Farha sun kusa dawowa.

Ya kalleni kafin ya ce" Farha kaÉ—ai sauran yaran fa?

Na yi shuru ban yi mgana ba.

Ya numfasa ya ce "Ki daina danganta Farha da ni Bilkina, d'aya take da su Amra a wajena, ba tawa bace ta kice tun kafin ta zo duniya kowa ya tabbatar da cewa Farha taki ce don kuwa na fi Abida cancantar na ba ki ita".

Na ba shi haƙuri ganin ransa ya ɓaci sai da na tabbatar da ya hakura sannan na sakoasa batun Abida tare da fatan ya dauke ta Su tafi inda zashi don na tabbatar hakane kadai zaisa hankalinsa ya nutsu. Ya girgiza kai ya ce "Bilkina ban saki Abida ba, amma matukar sai na nemi ta dawo gare ni to la shakka na haramtawa kaina ita. Bamu samu matsala da ita ba, ban mata komai ba, Baba da Yaya Asad suka zuba mata ido take yin yadda ta so, saboda kawai ba ni da Baba k'arami. Muryarsa ta karye. Ni kuwa kuka nake yi sosai don na gane ba k'aramin ciwo lamarin yake yi masa ba jarumta kawia yasa ciwo Bai kada slazzphi ba saboda tsananin damuwowin da suka yi masa k'awanya. Ya hadiye kukan dan ya so k'wace masa ya ce "Da ikon Allah sai na samu damar da zan tozarta Abida fiye da tozarcin nan da ta yi mini. Sai Allah ya ba ni dama na nunawa Asad iyakarsa. Saboda Yana da kud'i shiyasa ya shake Baba a maimakon ya tsaya ya daidaita komai a matsayinsa na babban wanmu"

Na yi shiru don ba ni da bakin magana don na lura Yaya Sulaiman'zfishinsa akan Yaya Asad fiye ma da Baba Babba akan batunsa da Abida. Na dinga ba shi hak'uri har ya d'an nutsu sannan muka yi sallama har harabar gidan na raka shi muka yi sallama cike da kewa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ganin ya ruɗe yana ta wasu surutai yasa na s lalubo jarumta na yi ta masa nasihan da jan hankalin cewa tunda mutuwar Mami ta zame masa wa'azi ka da ya karaya, ya yi haƙuri ya cigaba da harkokinsa kowa iya kwanakinsa zai yi a duniya ya ɗauka ita Mami kwananta ne ya ƙare, da irin kalaman da na yi amfani kenan na lallashi Ansari ya bar kuka ya samu natsuwa.

"Allah ya jikan Mami da Baba ƙarami Allah ya sa sun huta."

Ya faÉ—a cikin karaya, na amsa mishi da Amin ina mai É—auke hawayen da suka zubo mini da yatsun hannuna.

"Ya Sulaiman har yanzu ba labarin shi Ansari??

"Wallahi babu, na bincika duk in da ya kamata da wajen abokansa da suka yi karatu tare a Germany amsar duk iri É—aya ce basu san in da yake ba sannan suma ba ya magana da su."

Ansari ya amsa mini cikin damuwa a muryansa.

"Shike nan. Idan yana raye Allah ya tsare shi a duk in da yake. Idan da rabon mu gana Allah ya haÉ—a fuskokinmu da alheri."

Na faɗa ina jin kamar na fashe da kuka Ansari ya amsa da Amin mun daɗe muna tattaunawa kafin mu yi sallama bayan mun gama wayar na zauna a ɗaki ni kaɗai na ci kuka na ƙoshi sannan na faɗa bayi na wanke idanuwana, haka nake yi idan na tuna da yau ba Mami ba Baba ƙarami, sannan ba iyalan Baba Babba. Ga Ya Sulaiman ya yi nesa damu sai na ji ina kuka wanda banma san ina yi ba, ƙarfin zuciya ne da tasirin musulunci ke rike da ni amma matuƙa zuciyata da gangar jikina sun raunana, ƙarfin hali ne kawai da karɓar kaddara tunda rubutattaciya ce daga littafan kaddarar rayuwarmu, kuma cikar kowani musulmi karɓan kaddara mai kyau ko akasin ta.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi haka nan bawa yake zirga-zirgarsa na yau da kullum tunda akwai rai har da lafiya mun godewa Allah. Ba laifi ina samun ƙudi sosai tunda gidajen da na samu duk haya na saka, sannan ga sana'ata ta snack ta karɓu sosai da dukkan zuciyata da jikina nake yin aiki tuƙuri domin idan tuna maganar Ya Sulaiman ta ƙarshe a gare ni akan na zama jarumace na tsaya akan ƙafafuwana saboda ni uwa ce domin zama garkuwan ƴayana wata rana. Bana ko tsayawa jiran Baban Amrah domin ɗaukan laluranmu ta riga ta zame mini jiki komai ni nake yi, mantawa ma nake yi nauyin hakan na kan Baban Amrah ne, tun kuma da hakan ta faru ban sake komawa Funtua ba, saboda ko na je wajen wa zan je? Gida na can a kulle babu kowa shi yasa ko marmarin zuwa ban taɓa yi ba. Ansari da ya dawo ya zo kwanaki da ya shigo garin kan harkokinsa duk ya rame amma ba laifi tun da ya kwantar da hankalinsa ya fara ɗaukan dangana, ya sanar mini ya samu aikin amma an tura shi Maiduguri babban birnin jihar Borno. Jikina ya yi sanyi tare da zullimin yadda Ansari zai yi nisa Ga shi a lokacin garin Maiduguri na fama da ta'adin yan tada k'yar baya. Amma na daure na yi masa kyakkwar adduar alheri. Ya mini sallama akan gobe zai tafi. Tafiyar Ansari ya sake kassara ni don gani nake yi tamkar shima ya tafi kenan. Da k'yar na hak'ura na cire al'amarin a raina amma bansan me yasa nake ji a jikina ƴaƴana kad'ai suka rage mini. Shi yasa na rike aikina da sana'ata da muhimmanci don duk ƙokarina da wahalata sabo da su ne, domin na ingata musu rayuwa ko da wata rana bana tare da su.

*BAYAN WATA SHIDA*

Bayan watanni shida da tafiyar Ya Sulaiman, ba wanda ya sake jin labarinsa, yana raye ko ba ya raye ba wanda ya sani sai Ubangiji.

Ni dai addu'ata kullum shi ne idan yana raye ubangiji ya karkato da hankalinsa gida idan kuma ta Allah ta kasanance da shi Ubangiji ya haÉ—a mu a darussalam.

Ashe Abida ta haihu ban sani ba, kuma ba na tunanin wani a cikinmu ya san da batun haihuwar nan, nima Ya Faruƙu ne ya k'ira ni kwana uku da haihuwar ya sanar da ni, sai na ji abin kamar a mafarki tambayar kaina na ke yi dama Abida na da ciki ne? Mamaki da al'ajabi suka sake mamaye ni da jin ikon Allah! Yafaɗa mini namiji ta haifa da uwar da abin da aka haifa duk suna lafiya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Duk da C.S aka yi maa Abidan a dalilin ba zata iya haihuwa da kanta ba, ban sani ba, sam bansan Abida na da cikin Ya Sulaiman ba wato shi ya sa da rasuwar Mami na ganta wani iri ashe lokacin ma tana cikin laulayi ne? Allah sarki! Kwalla ta zubo mini a dalilin na Kara fahimtar ya'yan Baba Babba gabaɗayansu sun rufe ni daga ganin status dinsu koma share lambata suka yi oho! Ya Faruƙu da na ke ganin yana yiwa zumunci kara bana ganin status dinsa Sai dai ina masa zaton bai share lambata ba, amma na gode masa domin ba dan shi bazan ji labarin haihuwar ba. zumunci ya riga da ya lalace gyaruwarsa zai zama wani abu ne mai wahalan gaske.

Amma na dinga mamakin yadda Baba Babba bai fada mini ba don kuwa ni ban daina gaishe shi ba, a kai akai ina k'iransa a waya na masa gaisuwar juma'a tare da tambayar jikinsa da iyalinsa gabad'aya.

Ni na kira su Saddiqa na faɗa musu haihuwarAbida suna ta mamaki, Ya Hamida ce sai da ta dama ta ɗaga kirana da nafaɗa mata haihuwan Abida ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce" Ta baya ta rago kenan. Ta yi nasaran koran shi daga k'asar gabaɗaya, sai ta zama uba da uwar abin da ta haifa."

Daga haka ta kashe wayarta sai na sake kiranta.

A fusace ta É—auka tana faÉ—in" Wai lafiya kike ta kirana Bilki?"

N tausasa harshe na a ce" ko za ta shirya mu je Abuja mu ga Abida da abin da ta haifa?"

Kawai haka na fad'a Ya Hamida ta fara zagina ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce ita kam ba in da za ta je idan ni zan je Allah ya raka taki gona tunda ban san kishin kaina da na y'anuwana ba.

"Ba haka ba ne Ya Hamida, kar ki manta ba saboda ba Abida za mu je ba. Saboda Ya Sulaiman ne."

Ko saurarena ba ta yi ba ta sake katse wayarta tana faÉ—in sai kuma na yi, tun da na ji haka sai na zare ta a ciki a raina na kudiri niyyar ni kaÉ—ai ma ya isa zan je na duba ta saboda zumunci da kuma Ya Sulaiman. Na kira Ansari mun yi magana ya ce shi Wallahi nauyi yake ji da ya raka ni amma na fara zuwa shima daga baya zai je, ko dai bai je ba magana ma mai daÉ—i sadaka ne na ji daÉ—in mgana da shi. Baban Amrah na dawowa na tare shi da maganar haihuwar Abida.

"Wace ce kuma Abida?"

Ya tambaye ni yana kallona, bai wani ba ni mamaki ba sanin dama ba ya son duk wata magana da ta danganci Abida yake yi ba.

"Abida dai tawa da ka sani y'aruwata"

Na ba shi amsa a takaice kuma a dake.

Ya jinjina kai kafin ya ce" ikon Allah, dama tana da ciki ne?

Na amsa masa da ce wa "ni ma ban sani ba sai da ta haihu."

Tabe baki ya yi bai yi magana ba, ni kuma ganin haka saboda bana son mu sake wata mgana daga baya da sauri na ce" Ina so ka yi mini izini na je Abuja na duba su."

Ya É—aure fuska kafin ya ce" Me yasa za ki je?"

"Saboda ya kamata!

Na amsa mishi kai tsaye, tuna Ya Sulaiman da na yi yasa kawai sai na fara hawaye ina faɗin" Baban Amra ka yi mini izini na tafi, zan je ganin abin da aka haifawa Yaya Sulaiman wanda ba mu san ko yana raye ba, ni ina ji a jikina wataƙila ba ya raye, domin idan yana raye ba zai kai wannan wattanin bai neme ni ba, k'ila ma a inda ya je ya haɗu da tsautsayi na ajali."

Na ƙarisa faɗa ina mai fashewa da kuka. Jikinsa ya yi sanyi ya taso zuwa gare ni ya rumgume ni yana lallashina.

"Daina kuka, in sha Allahu Sulaiman yana raye kuma cikin ƙoshin lafiya."

Ya furta hakan murya babu amo.

Na É—ago daga kan k'irjinsa ina faÉ—in" To idan yana raye yana ina. Me ya sa har tsawon wannan lokacin bai neme mu ba?

Na faÉ—a hawaye na sake kece mini! Shi ya share mini hawayen yana sake rumgume ni, a daran ya yi ta lallashina da kalamai sai ga shi na saki jikina tun ballanta ma da ya ce ya amince na je amma shi ba zai samu zuwa ba, za su je Zaria shi da Amrah su duba mai sunanta.

Na ce masa sai na tafi da Faruk da Farha. Ya ce to sai mu tafi gabaɗaya idan muka duba Maman Zaria ni da sauran yaran mu ƙarisa Abuja.

Da wannan shawaran muka tsaya washegari kasuwa na shiga na yo siyayyar kayan jarirai da su pampers kamar za a bude shago.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ni kaina sai da na ga kayan sun yi yawa Abida kuma na siya mata super wax da leshi mai tsada da mayafinsu masu tsadar gaske, ko ba za ta amsa ba ni dai na sauke haƙƙi da nauyi a matsayina na uba tunda ina makwafin yaya Sulaiman ne, tunda ba inuwarsa a wajen kuma babu wanda zai maye gurbinsa sai ni shi ya sa ban ji na sare ba.

Da na koma gida shi kan shi Baban Amrah da ya ga yawan kayan sai da ya yi magana, ni kuma na sake ba shi amsa da fadin "Abida ce ta haihu sannan d'an Ya Sulaiman ne, komai zan yi musu ban biyasu girman ƙaunar da suka nuna mini ba".

Jin na faÉ—i haka yasa sai ya yi shuru bai yi mini sharhin nasa ba".

Washegari tun safe muka d'au hanya, azahar muna Zaria salla kawai muka yi sai abinci da muka ci, ya kai mu tasha muka shiga mota cikin sa'a gurbin mutum biyu ya rage dan haka muka biya wajen ni da yara. Nan da nan muka kama hanyar Abuja ni da su Faruk, muka bar Amra da Babanta a Zaria sai washegari za su koma Katsina. Ni kuma dama na ce masa zamu dan yi kwanaki, daÉ—in da na ji, jiya mun samu hutun mid semester.

Sai da muka sauka a garin Abuja sannan na kira wayar Ya Faruku na ci sa'a ya daga k'iran ya sha mamaki da na ce masa ga ni a Abuja, addreshin gidan Baba Babba zai ba ni. Ya shanye mamakinsa, ya turo mini adreshin, mai taxi É—in da na tare na nuna masa ya ce ya san wajen tunda fitattaciyar anguwace ta masu hali.

Danƙareren gida Ya Asad ya saka iyayensa a ciki, har sai da na saki baki ina kallon gida.

Ba kowa a gidan daga Baba Babba sai Momi sai Abida, sai ma'aikata.

Kawai suka ganmu kwatsam kamar daga sama, tunda da na isa bakin gate din gidan Yaya Farouk na k'ira ya yiwa maigadin magana ya bude mana bayan ya kinkimi kayana.

Ya ce mu shigo zai dawo ya shigo mini da sauran kayan.

Momi ce a falo tare da Baba Babba.

Dukkansu bakinsu ya kasa rufuwa na murna da mamaki.

Momi ta miƙe tana faɗin" Lale marhaban Maigado ke ce tafe?"

Ina murmushin jin daÉ—i na ce" Ni ce Momi."

Su Farha suka nufe ta ta tarbesu cikin farinciki. Ni kuwa gaban Baba Babba na ƙarisa na rusuna ina gaishe shi.

"Barka da zuwa, lale da Bilkisu yayar Abida!

Nan da nan idanuwana suka kawo ruwa domin na tuna shekarun da suka shud'e a lokacin da muke hade, muke rayuwa cikin jin dadi da kaunar juna.

Kaina na kasa da rawar murya na ce " Sannu Baba mun same ku lafiya?"

Ya amsa da lafiya k'alau yana tambayata sauran yaran da sauran Æ´an uwana duk na amsa mishi da muna nan lafiya.

'To Alhamdulillah sannu mai gado. Allah ya yiwa rayuwarki albarka.'

Na amsa da "Amin"

K'wallah na taruwa a kwarmin idanuwana farinciki da alhini sun kewaye ni kamar na fashe da kuka haka nake ji.

'Sai kika ji yar uwar taki ta haihu ko?'

Baba Babba ya katse mini tunani.

"Ban ji ba Baba. Sai shekaranjiya ne Ya Faruku ya kira ni ya faÉ—a mini."

Ya jinjina kai kafin ya ce" Da ya ke sai jiya aka sallamo ta daga asibiti wataƙila ba ta samu natsuwar kiran ki ba ne maigado "

Ina kallon Baba Babba a cikin zuciyata sai ayyana har yau Abida ce raunin Baba.

"Maigado har yanzu baku samu labarin Sulaiman ba?

"E, Baba bamu samu labarinsa ba har yanzu."

Ya jinjina kai kafin ya ce" Ubangiji Allah ya bayyana shi cikin aminci"

Na amsa da Amin kasa kasa sai falon ya yi shuru, tunda Momi ta ja yaran zuwa ciki, ta gefen ido nake k'arewa Baba Babba kallo ya warware sai dai bai mayar da jikinsa ba haka nan tsufa sosai a tare da shi alamun har lokacin zuciyarsa bata nutsu sosai ba.

Mamakin Baba Babba nake yi a kullum shin wanne dalilin ne ya sanya ya zubawa Abida ido ta zauna a gida har hakan ya taimaka wajen b'acewar Yaya Sulaiman?

Duk da dai nasan itace rauninsa, amma duk da haka ina mamakin yadda ya iya zuba ido Abida take zaune a gabansa, idan a lokacin ba shi da lafiya ai daga baya ya ji sauƙi ya kamata ya mayar da Abida d'akin mijinta tunda bai sake ta ba. Bai kuma yi laifin da za'a kashe masa aure ba.

"Maigado tashi ki shiga wajen y'aruwar ta ki, ku gaisa ki yi salla ki ci abinci ki huta."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Muryarsa ta katse mini tunanina, na amsa masa da to na tashi na shiga dama kayan da na zo da su tuni Momi ta shigar mini da su.

A bedroom É—in farko na iske Momi da yara ta zuba musu abinci suna ta mata hira tana dariya.

Nan na fara shiga na duk'a har k'asa na sake gaishe ta.

"Lafiya lau Maigado, ya mutanen gidan ina me gidanki da amaryar Alhaji?"

Na amsa mata da duk suna lafiya, mun barta a Zaria tare da Babanta.

Na daÉ—e a wajenta muna hira itama sai da ta tambaye ni labarin Ya Sulaiman na ce mata ba wani labari cikin damuwa ta ce "Oh Allah ka bayyana wannan yaron alfarmar Annabi."

Na amsa mata da Amin.

"Za ki fara yin salla ne ko sai kin ƙarisa wajen y'aruwar ta ki?

Na ce bari na je can wajenta sai na yi, ita ta nuna mini dakin da Abida take ciki na shiga ciki na iske ta zaune a gefen gado tana shan tea ga Baby a cikin showel a gefenta yadda ta kalle ni na gane ba zan wani samu karbuwa daga gareta ba.

Ba ta yi mini mgana ba tun bayan da na yi sallama ta amsa mayafin jikina na yaye ina faÉ—in" Sannu "Abida."

Kai tsaye da muryata cikin dakewa ta ce" Yauwa Bilki"

Na kalle ta itama ta kalle ni, hawaye suka kawo mini amma ban bari sun zubo ba, itama ina ganin rauni a cikin idanuwanta sai dai ta yi saurin kauda kanta daga barin kallona.

Ganin haka yasa na ƙarisa wajen jariri na ɗauko shi zuwa jikina a gefen gadon na zauna, ina mai kallon yaron sai da na yi kabbara a cikin zuciyata yaron nan kamar ni ce na haife shi tsabar kammanina da ya debo, ni kuwa dama kaf ɗakinmu na fi kama da Ya Sulaiman hawayen da nake tarewa suka zubo har saman kumatun jaririn na saka hannu na share masa sai barci yake yi.

"Kai ma mu ka biyo?"

Na faɗa murya babu amo kamar shi da Farha a bayyane ba tantama, wannan jinin Ya Sulaiman ne! Da sauri na rungume jaririn ina mai fashewa da kuka har yana fidda sauti. Abida na gefe tana kallona amma ba ta yi mini magana ba sai da na sha kuka na k'oshi na share hawayena amma ina ƙankame da jaririn a hannuna zaman sama da mintina ashirin ba mu tanka ma juna ba sai ita Abidan ce da ta gaji da kanta ta kalle ni tana faɗin.

"Ina yaran ko ke kaÉ—ai kika zo?"

Ina shirin bata amsa sai ga su Farha Momi ta kawo su Faruk ya nufi Abida yana ganinta, ta rike shi a jikinta tana faɗin" Yayanmu akwai ƙauna ashe baka manta da ni ba? Ta faɗa tana shafa kumatunsa shi kuma yana dariya.

Jaririn da yake hannuna ta nuna masa tana faÉ—in" Je ka kaga k'aninka? Kana son shi?

Da sauri ya ce" E Ammi ina son shi."

Don kaf yarana Ammi suke kiran Abida, wajena ya nufo yana faÉ—in na ba shi jaririn na ce ba zan ba shi ba Momi ta ce ya zauna sai na rike masa haka ko aka yi jikin shi har rawa yake yi.

"Mahmah da shi za mu tafi?

Ina shafa kan shi na ce" A a Faruk a wajen Ammi za mu bar shi."

Abida kuma na ta kallon Farha itama tana ta kallonta kamar ta gane ta, kamar ba ta gane ta ba, sai ta miƙa mata hannu tana faɗin"Farha zo mu gaisa."

Ta mik'a mata hannu Farha ta tafi zuwa gare ta, ta riƙe ta ta daɗe tana kallonta kafin ta shafa kumatunta tana faɗin" Farhan Bilki ta girma!

✍️

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Bojuwa herbs*

*Oder your kayan mata for women of class*

*Our products are healthy and original*.

*Tested and trusted*.

*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta Ki*.

*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini later domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zata iya zuba kudi ta saro masu daraja irinsu ba*.

*Duk wadda ta ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*

*Just DM for your order @08033773332*.

Na kalle ta ina mai murmusawa, duk yadda soyayyar ɗa da uwa take Abida ta yi jarumtar bar mini abin da ta haifa shi yasa nake yi mata uzziri don ta nuna mini zahirin soyayyar da ta shafe dukkan iyashegenta a zuciyata. Nan duniya na shaida Abida na cikin jerin masoyana na haƙika. Duk da tana kawaici amma yanayin yadda take kallon Farha zaka san akwai soyayya irin ta uwa a idanuwan Abida.

Ta sake tambayar Farha da 'Ina yayarku?'

Farha ta ce "Mun barsu a Zaria tare da Dady".

Ganin har biyar ta gota ya sa na mike na kwantar da jaririn a saman gado, ganin na mike yasa Farha ta saki hannun Abida ta nufo ni tana faÉ—in" Mahma ina za ki?"

Ina kallonta na ce" Ba inda zan je Farha salla zan yi "

Ta sake ni jin ba tafiya zan yi ba.

"Je ki zauna wajen Ammmi ku kalli Baby kafin na idar da salla."

Ta gyada mini kai, ta tafi wajen Abida ni kuma na shiga tiolet.

Abida ta sauke ajiyar zuciya, tabbas a shaidar da ta yiwa Bilki ta san zata so Farha kuma zata fifita ta fiye da su Amrah ko da kuwa ba Sulaiman ne ubanta ba.

Sannan ganin Farha tsab cikin kayan alfarma ya sanya ta sake jin ba ta yi nadamar yiwa Bilki kyautar abin da ta haifa ba, sai ma take ganin yadda Balki ke kula da Farha inda tana hannunta ba lalle ma ta samu irin wannan kulawar daga gare ta ba.

Inda na barsu nan na iske su Farha da Faruku suna ta faman yiwa Abida surutu, ni na ɗauko sallaya da kaina na shimfida. Abida ta nuna mini gabas na tada salla ina idarwa Mami ta kawo mini abinci na ci kaɗan saboda cikina ya cushe, yaran kuma sun fita sun koma ina ga wajen Momi ne, kayan da na siyawa Abida da Baby na ɗauka na kai har gabanta na miƙa mata ba ta tambaye ni ba ta karɓa ta ajiye a gefenta.

"Abida sunan yaro Sulaiman" Na furta hakan cikin jarumta.

Ta kalle ni kafin ta ce" Baba Babba ya zaɓa masa suna tuni."

"Wanee suna?"

Na tambaya a hankali.

"Sunan Baba ƙarami. Isa."

Da sauri na ce" A a ba sunan Baba ƙarami zai amsa ba, sunan sa Sulaiman saboda Anisa ta haihu kwanaki kuma sunan Baba Ƙarami aka sanya masa."

Nan ma bata yi mgana ba tana ta dai kallona ni kuma ganin haka yasa na cigaba da faÉ—in"Sunan yaro Sulaiman. Allah ya raya mana shi. Shi kuma Ya Sulaiman idan yana raye Allah ya bayyana mana shi."

Sai kawai na kece da kukan da nake ta danne shi da k'arfin gaske saboda ba ni da ƙwarin gwiwa indai akan mganar da ta shafi Ya Sulaiman ne.

Jikin Abida ya yi sanyi ta yi sukutum tana jina amma ba ta yi magana ba.

Amma daga ga ni itama ta shiga tunani mai zurfi.

Dama ace, dama za ta iya mayar da hannun agogo baya.

Ikon Allah ne yasa ta rabu da cikin nan lafiya a sanadin Bp É—inta ya hau fiye da k'ima ta kuma tabbatar saboda rashin ji daga Ya Sulaiman ne. Kamar yadda ya faÉ—a menene na shi? Mami mahaifiyarsa ce ko akan bola take ba zasu guje ta ba.

Ta kuma tabbatar sanadin barinsa k'asar nan saboda ita ne, ta tabbatar ya nemi ya yi nesa da sune a dalilin ba zai nemi sulhu da ita ba, duk yadda take tak'ama da jin kanta ya dame ta ya shanye, ta san halinsa ba ya daukar reni ko kad'an abin da zai biyo bayan takaddamansu ba mai sauƙi ba ne, da a ce ba ta je gaisuwar Mami ba, da nadamar ta yi mata yawa domin da farko cewa ta yi ba za ta je ba. Baba Babba ya matsa mata akan sai ta je. Da a ce ba ta je ba da yanzu kunya da nauyin sun ishe ta, da ba ta je musu ta'aziya ba da yau ba ta san da wani ido za ta kalle su ba.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ni dai ina ta kuka, tana zaune gefe tana kallona ta kasa lallashina har sai da na gaji na share hawayena.

Sannan na sake kallonta ina faÉ—in" Allah ya raya mana mai sunan Ya Sulaiman."

Abida ta amsa a sanyaye amma ba fara'a a saman fuskarta.

Tana so ta ware su yi hira da Bilki, tana so komai ya wuce amma da zarar ta tuna yadda ta ga su Balki a kotu da yadda suka dunk'ule wajen kalubalantar mahaifinsu sai ta ji komai ya k'wace mata.

Ganin mun yi jugum jugum yasa na miƙe ina faɗin" Bari na je wajen Baba Babba."

Ta gyaÉ—a mini kai na fice na barta tana mai bina da kallo.

Mamakina take yi wai nice da wannan jarumtar? Yadda na ce sunan yaro Sulaiman ya bata mamaki sosai don tasan yadda nake kaffa kaffa da ita. Sannan na nuna a bangaren uba nake.

Ina fita falo na samu Baba Babba na zauna a gabansa ina fadin Baba ashe ka yiwa yaro huduba da sunan Baba Karami?"

A sanyaye ya ce"A tun ranar da aka haife shi".

Na yi k'asa da kaina cikin girmamawa na ce "Don Allah Baba ina neman alfarma a saka sunan Ya Sulaiman a kuma tayamu da addu'ar idan yana raye Allah ya dawo da shi gida lafiya."

Jikin Baba Babba ya yi sanyi, yana ta lallashina da ce wa" ki yu haƙuri Bilki. Allah zai bayyana shi. Sunan yaro kuma Sulaiman kamar yadda kike so ".

Na ce "Na gode Baba! Daga na zarce da fadin abin da yake cina a zuciyata.

"Bamu da kowa a yanzu Baba.

Baba ƙarami ya tafi ya barmu, mami ma haka, sannan ga Ya Sulaiman bak'in ciki da maraici ya saka ya fantsama duniya yana raye ko ya mace sai Allah!

Ga haihuwa an yi masa bai sani ba bare ya rungumi yaron ya yi masa addua irin ta uba. Ahalin Baba k'arami muna rayuwa cikin bak'in ciki tare da tunanin bamu da inda zamu dosa da matsalarmu."

Hankalin Baba Babba ya sake tashi, cikin karaya ya ce"Maigado haka kuka dauka?"

Na jinjina kai kafin na ce" E Baba. Abubuwa da dama sun faru da ya kamata ka tsawatar amma ba ka ce komai ba. Ana kallon Abida ta dawo gida aka zuba mata ido ta zauna alhalin ba sakinta mijinta ya yi ba. Na kuma san baku mana irin wannan tarbiyar ba. Ina tuna Yaya Salaha da Yaya Hamida sun sha tahowa gida idan sun samu matsala da mazajensu a ranar kake sakawa a mayar da su, ba don ba kwa sonsu ba, sai dan ku nunawa mazajensu daddako da kara. Amma ace Abida ta taho gida a barta ta zauna haka siddan. Yaya Sulaiman ba shi da wata alfarma ke nan?"

Na fada ina sharan hawaye.

Cikin sanyi Baba Babba ya ce" Ba ni da lafiya Maigado ba zan iya komai a lokacin ba. Da na ji sauki kuma na kyaleta ne dan zuciyoyi su sake hucewa kada a zo a samu sabani mummuna.

Na gyada masa kai shi kuma sai ya cigaba da faɗin" Abin da ya ba ni mamaki shi ne me ya sa Sulaiman bai zo ba? Da ya zo mun zauna da wataƙila an samu masalaha.

" Duk da haka Baba bai kamata a zubawa Abida ido ta zauna a gida haka ba, ba wannan tarbiyar kuka bamu ba, lokacin yaya Asad ai yana nan bai kamata a barta ta yi yadda take so ba."

Baba Babba ya jinjina kai cikin gamsuwa kafin ya ce" Na aminta da maganarki Maigado. Hakika kin hasko mini kuskuran da ni na kasa ganewa. Alokacin Abida ta nuna mini so take yi ta samu natsuwa idan ta zauna a can za a samu matsala tsakaninta da Mami da Sulaiman, ni kuma sanin halin zuciyarta ya

sanya na fahimceta na ce ta zauna har a samu natsuwa ban É—auka lamarin zai lalace kamar haka ba Mai mgado. Sannan k'arfin barinta don na bawa cikin jikinta da yake kokarin faduwa kariya.

Na fahimci Baba Babba ba shi da laifi lamarin ne ya kwace masa, ya yi ta addu'ar Allah ya bayyana Sulaiman cikin aminci na yi ta amsawa da Amin Amin.

Mun daÉ—e muna hira mai dad'i har sai da aka k'ira sallar mangariba.

Sannan na koma ciki na iske Abida da su Faruku suna ta mata hira, toilet na shiga na dauro alwala na yi salla bayan na idar na jawo jakata na kira Baban Amra da na ga ya yi ta kirana wayar na jaka, mun gaisa har ya ba ni Amra muka gaisa, ta ce Na bata Ammi. Na mika mata wayar. Ta saki fuska da murya ta yi hira da Amra sosai.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Yara tare da Momi suka kwana ni kuma a dakin Abida amma magana mai tsawo ba ta sake haɗa mu ba, washegarin Baba Babba ya sake yiwa yaro huduba da sunan Sulaiman.

Addu'a sosai momi da baba Babba suka yi mini a lokacin da suka ga kayan da na kawo.

Baba ya ce "Faruk ma ya ce Ansari ya turo kud'i wai a sayi raguna guda biyu. Allah ya yi muku albarka."

Duk yadda Abida bata sakar mini jiki ba, ban tafi ba sai da aka yi walimar suna da ni. Duk da ba gayya aka yi ba, iyakacin matar Yaya Asad ne da iso ana gobe suna ita da iyalin ta, gabad'aya na ga mata ta sauya mazaunai da kirji sun cika dam, fatarta ta goge ta zama tamkar wata half-caste. Na shiga tunanin dama Anty zata yi Kiba ne? Ni da nasanta siririya doguwar mace sannan bata da manyan mazaunai haka nan kananun nono gareta. Amma tsabar kudi da daula ne ya sanya tashi guda ta zama haka ko kuwa surgery aka yi mata? Ni sai na ga har k'uruciya ta kara. Don ba zaka ce ita ta haifi manyan yanmatan mata, alhalin da har gulmar mijinta ya fita k'uruciya muke yi ni da Abida. Ya'yanta su Aysha sun zama manyan y'anmata sosai hatta Bilkisu mai sunan tana aji biyar a sakandire ta dinga murnar ganina don duk salla sai na aika mata kayan sallah masu tsadar gaske.

Kan dole na kunshe mamakina akan sauyawar matar Yaya Asad tunda abokiyar gulmar ba wani sakewa ta yi da ni ba. Daga matar Yaya Farouk da ta Yaya Usman shikenan sai ya'yansu sai ni da nawa yaran muka yi walimar sunan cikin nutsuwa. Abida bata yi wata kwalliya ba gabadaya ma bata da kuzari duk y'anuwanta da matansu kamar zasu hadiye ta tsabar nuna kulawa da soyayya amma gata nan babu walwala wanda kowa ya gane rashin uban danta ke nukurƙusanta duk da bata furta ba.

Ni dai addu'ata da fatana idan Ya Sulaiman na raye Allah ya dawo da shi gida lafiya.

Anty Rukayya matar Yaya Asad ta zata je ganin sabon gidansu da ake kan ginawa ta ce 'Na shirya mu je tare, duk da bana son zuwa amma haka na daure na bita ban watsa mata k'asa a ido ba a lokacin na fahimci kamar anty Rukayya da Abida babu jituwa a tsakaninsu.

Unguwar Asokoro muka je, duk yadda ake labarin kuÉ—in Yaya Asad ban zaci sun kai haka ba. Don kuwa mallakar gida k'arami a Asokoro ma ai sai manyan masu kudi bare wani rafkeken gida na garari. Na daga kai ina kallon ginin wannan kam zai yi hawa hud'u zuwa biyar.

"Dankari mankari"

Na furta a fili.

Muka nutsa cikin gidan da masu aikin suke ta faman aikinsu mafi yawa masu jajayen kunnuwa ne suke jagorantar aikin.

Na ce "Anty Rukayya ina miki fatan a lahira ma ki samu dandasheshen gida a gidan aljanna, don a duniya kam kin samu".

D'adi ya kamata ta murmusa ta ce "Ameen Maigado ke ma ya miki fiye da haka anan duniya da kuma lahira"

"Ameen yayata in sha Allah idan zaku dawo ki fad'a mini takanas zan zo a yi tariya da ni ".

Da sauri ta ce "In sha Allahu kuwa zan fada miki Maigado duk da sai next year zamu bar fatakot, amma dai zan sanar miki idan lokacin ya zo"

Ko fenti ba'a yi ba da saka kofofi gida ya fito ya yi ras ina idan ya sha fenti da kaya na alfarma?

Bayan shekara muka yi bikin Ansari tunda yana aikinsa yana kuma juya kud'insa. Funtua muka yi bikin dangin Mami sune suka zama gatanmu, don kuwa sun zo sun cika mana gida basu barmu mu kad'ai ba. Baba Babba da Ya Farouk sun zo daurin auren shi ya yi walicci tunda har Abuja ya je ya gaishe shi ya sanar masa. Momi ma da ita aka yi bikin amma ban da Abida ba ta zo ba, wai tana fatakot tunda watanni biyar Kenan Yaya Asad ya zama kwamishinan y'an sanda na jihar River's. An yi biki lafiya an tashi lafiya ni ce na zama kamar uwa a wajen tun da ba Ya Sulaiman sannan ita kuma Ya Hamida duk abin da ta ga na saka hannu sai ta zare jikinta a ciki, ina can Funtua Baban Amra ya kira ni da albishir ya samu aiki a jamiar da nake koyarwa ta marigayi UMARU MUSA Y'AR ADUWA. A matsayin non acadamic staff, dama na ji ana ta batun zasu É—ebi sabbin ma'aikata a wannan shekarar na yi masa murna sosai. Ina komawa Katsina na sake yi masa murna baki da baki.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ina ayyana yanzu sai ƴan'uwansa su daina k'ullata na, har gida suka zo taya shi murna ni kuma na yi musu girke-girke da kayan Snaack, sai habaici suke yi a fakaice ban biye musu ba domin ni yanzu irin matsalolin nan sun daina ɓata mini rai. Baban Amra ya yi farimciki da samun aikin har hakan ma ya nuna a saman fuskar shi ni kaina na taya shi murna a matsayin magidanci zama ba aiki ba bu daɗi sam.

ÆŠan'uwan Baban Amra zai siyar da filinsa da yake jikin nasa sai ya kawo masa talla, shi kuma Baban amarah ba shi da kuÉ—in siya. Sai ya yi mini ta yin siyan filin ni kuma lokacin ba ni da kuÉ—i a hannuna sai dai kadarori. Shiyasa ban siya ba sai daga baya Baban Amra yake fad'a mini ai fili yanzu ya zama nasa tunda ya siyar masa da b'angaren Hajiya shi kuma sai ya bashi filin ya yi masa ciko, tunda filin yana da girma sannn unguwar ta yi daraja sosia shiyasa ma Baban Amra ya dage ya mallak. An yi rubutu da shaidu da komai kowa ya saka hannu tare da ajiye takardar shaida a wajensa.

Wani irin kwantar da kai ya fara mini a kwanakin nan ne, wani irin ji da ni Baban Amra yake yi, soyayyar da ko a farkon aurenku bai gwada mini irinta ba, hatta wanka ma sai ya ce tare zamu yi, ya cuda ni , na cuda shi. Duk dare ya cika ni da kalamai da ƙauna. A da sai mu yi wata wani abu bai shiga tsakanin mu ba amma kwanaki nan a akai akai sai ya nema abin nasa har mamaki yake ba ni, yana kokarinsa wajen ganin ya gamsar da ni. Hankalina ya Fara kwanciya nutsuwar da ta yi mini tustu na Fara samun sauki a zuciyata da gangar jikina. Sosai hankalina ya kwnaata har nake tunanin rashin samun attention din Sahal shine kan gaba a wajen wargajewar walwalata.

Wajen aikinmu daya amma Shi yawanci da safe yake fita yayin da ni ba kullum nake fita da safe ba sai idan ina da darasin safe. Idan mun fita tare shi yake É—aukar mini jaka, idan na ce ya bari kar a fara ce masa mijin Hajiya.

Murmushi yake yi ya ce ai ya daÉ—e da zama haka, ni ko farinciki ya cika ni na samu kwanciyar hankali ana cikin haka ya bijiro mini da maganar ya kamata mu fara gina wannan filin muyi kyakyawan muhallin da zamu nuna, kuma mu k'arishe rayuwarmu da ya'yanmu a cikinsa. Da kalamansa da soyayyarsa ya yi amfani ya ruÉ—e ni, na siyar da filina guda guda biyu, É—aya da shi aka zagaye filin kuÉ—in dayan kuma aka fara kafa foundaton É—in gini da shi, sannan akwai ruwan kuÉ—i a cikin account É—ina duk na tattara na bashi, tunda mu zai yiwa ginin domin farincikinmu shi yasa ban ji k'yashi ko kokonton bashi ba.

Da haka aka fitar da gini, mai hawa uku ginin ne na alfarma na k'asaita aka kai linta aka zuba dakin aka dora sama aka sake zuba dakin aka dora Hawa na uku kaso saba'in da kudadena ake ginin. Tunda aka yi rufi sai ginin ya tsaya amma a hankali a hankali ana cigaba da aiki ni da shi duk kudadenmu anan suke ƙarewa, barin ma ni duk dukiyata da wasu kaddarorina sun tafi a wannan ginin gumin sana'anata da albashina sun tafi anan sannan har gobe ni ce nake ɗaukar nauyinmu gabaɗaya.

Komai ni nake yiwaa kaina da Æ´a'Æ´ana ban damu ba. Don mantawa nake yi yana da aiki. Na sake shiriricewa da shi da na ga ya karbi car loan ana cirewa a albashinsa ya siyar da motarsa tunda ta tsufa ya sayi sabuwa mai kyau, sannan yana siyan wani abu a harkar gini dan haka nasan ba shi da wani kudi.

Sannu a hankali gida ya hattama fenti da tayals suak rage da kayan band'aki, murna muke yi sosai don kuwa yadda muka tanfatsa gini irin wannan munsan hucewar Ubangiji ce. Duk da muna ganin sauara ne kadan ya rage amma kafin a kammala din ba kananun kudi kudi zai sake had'iyewa ba. Sai dai kuma a hankali zamu yi har mu hattama.

Sannu a hankali sai nake ganin sauyuka tare da shi, ya fara kaffa kaffa da wayarsa, haka nan yana yawan wuce lokutan dawowarsa gida. Sannan É—an soyayyar nan yanzu duk babu magana É—aya biyu sai ya kulle bakinsa yafi mayar da hankali kan wayarsa. Tunda ya samu aiki sai muka yanke shawara ya dinga tafiya da Amrah tunda makarantar ta a hanyar makarantarmu take. Ni kuma na dinga kaisu Farha tunda Mafi yawa ba sassafe nake fita ba. Amma shi tun safe sai yammacin zai gama.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Dan haka sai yake tafiya da ita idan zai dawo sai ya daukota tunda itama sai yamma. Baya son ta dawo gida ita kad'ai . Duk sai runtsi ya daukota ya kawota sannan ya sake fita. Amma tunda ya k'ulla abota da waya da rashin zaman gida sai ya fara bata umarnin ta hau abin hawa ta dawo duk da ba kullum yake yin haka ba.

Sannan yanzu ungulu ta koma gidanta na tsammiya sai ya shafe satttika bai neme ni ba.

Kwata kwata hankalinsa da rayuwarsa, sun koma kan wayarsa na fara zargin akwai abin da ke É—auke masa hankali.

GabaÉ—aya na susuce na shiga damuwa, kuma ni daman damuwata na bayyana a saman fuskata.

Sannu a hankali na fara gasgata maganganun Abida. Na yarda da batun Basma a gare ni, da irin fadan da ta mini kamar ta dake ni lokacin da na ke faÉ—a mata duk kuÉ—aÉ—ena sun k'are wajen ginin da muke yi, ta yi ta mini faÉ—an cewa ni ce zan É—auki É—awainiyar miji sannan na yi na ya'yansa, na yi masa ginin gidan da zai zauna, na ga hakan ya kamata?

A lokacin duk ban hangowa kaina matsala ba, sai ma ce mata da na yi" Ni ban Ga abin damuwa ko rashin dacewa ba. Ni da ya'yana ne fa kawai to menene ribata dan ban taimake shi mun yi rayuwa mai kyau ba?"

A lokacin kasa magana ta yi, sai yanzu da nake ganin abubuwa na lalacewa maganganunta suke dawo mini a cikin kaina, na shiga damuwa ba mai rarrashina ku'ncin zuciya suka haifar mini da ciwon kai da jiri sai da na je na ga likita faÉ—a ya yi mini da cewa jinina ya hau sannan ina saka damuwa a raina deperession na neman ya kamani zan kashe kaina, jin haka sai hankalina ya tashi, daga asibiti gidan Basma na wuce na je mata da kuka Sai Dai na kasa bayyana mata halin da nake ciki sai ita ce ta zargi kukan da nake yi bana komai bane na kuttun mijine.

Takaici ya kama Basma ta rufe da faÉ—a" Ai da man na faÉ—a ki, ba ki da wayo ba ki yi shawara da kowa ba kika kwashe dukiyarki ki ka narkawa miji yana kwance kina masa komai ai dole ya yi miki wulakanci yanzu ba ki san me gobe za ta haifar ba? Ni dama nasan ba zaku kwashe kalau ba."

Na shiga tashin hankali ganin haka yasa ta sassauta ta shiga lallashina hakuri zan yi domin koma mene ne ya riga ya faru, tun daga lokacin Basma ke kula da ni tana yawan zuwa gidana ta duba ni a cewarta in ta k'yale ni takaicin namiji zai iya sakawa na hadu da stroke, kuma gaskiya ta faÉ—a Sahal na neman gigita mini duniyata k'warai da gaske. Haka siddan kuma ya d'ora mata karan tsana idan ta zo gidan ya dinga kunci ke nan. Har ta kai ya fara fad'in bata nufinsa da alheri Nima kuma ba sona take yi ba tunda tana son kashe mini aure.

Munafukace tana son raba aure.

Wulakanci iri iri ba wanda ba ya yi mini, amma ba wulakanci na kai tsaye ba, a a wani irin wulakanci mai susuta zuciyar yaya mata. Ba ruwansa da na yi kwalliya ko ban yi ba, baya daukar damuwata da muhimmanci, idan na masa magana zai kula ni, idan ban masa ba yana tare da wayarsa cikin jin annushuwa. Tunda ya samu aiki ba zance ga ranar da ya shigo da wani abu a leda a matsayinsa na maigidanci ba.

Duk da haka ban tab'a k'alubalantarsa ba.

Kashe kud'insa ya k'aru akai akai zan ga an cire mini kud'i wanda a da hakan ba d'ab'iarsa ba ce. Idan har zai cire to sai abu mai muhimmanci.

Muna cikin haka kwatsam aka mini waya ta biyu da ta kid'ima ni ta tayar mini da hankali komai ya tsaya mini cak.

Tsananin tsoron Allah ya sake kama ni. Oh rayuwa babu tabbas, idona ya soye zuciyata ta bushe na dinga jin bugawarta fiye da k'ima Allahu Akbar! Ikon Allah kafi ga haka. Kafin nan hawayen tausayi da dimuwa ya goce mini.

✍️✍️✍️

*Surayya Dee*

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: 32

*Bojuwa herbs*

*Oder your kayan mata for women of class*

*Our products are healthy and original*.

*Tested and trusted*.

*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.

*Dan Allah ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.

*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*

*Sanyi flusher kuwa best seller ne*

*Just DM for your order @08033773332*.

Na sake dubawa na tabbatar Yaya Farouk ne ya ya mini waya.

Na zauna na zabura na mik'e.

Anty Rukayya ta rasu?

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"

Na ambata da k'arfin gaske. Zuciyata ta dinga harbawa da k'arfin gaske.

Gabadaya sai yawo take mini, ba abin da ya dawo mini irin bara da na je haihuwar junior ta dauke Ni zuwa sabon gidansu da zasu tare.

Wata daya da ya wuce Allah ya ba ni iko na mata waya na gaishe ta, har ta had'a ni da Yaya Asad ya dinga mini gorin na zama yartsako samu ka k'i ii dangi. Har na dinga k'iranta amma shi bana k'iransa.

Ni kuwa fuskar da ta ba ni ne ya sanya nake girmamata. Yayin da shi ko na k'ira shi ba kasafai nake samunsa ba, yana kuma wahalar gaske ya neme ni dan kansa.

Na kalli agogon wayar na ga k'arfe shida saura kad'an.

Yaya Hamida na fara k'ira na sanar mata.

Ba wani alhini ta ce ", Ubangiji ya mata Rahma".

Murya ba amo na masa da amin. Na zarce da ce wa zamu tafi tare ne wajen ta'aziyar?"

Da azama ta ce "Ba zan je ba, idan kin je ki had'a ni da mijinta a waya. Uwata da rasu a waya ya mana gaisuwa dan haka nima zan yi masa ta wayar ya wadatar."

Na mararaice na ce "Haba Yaya Hamida baya k'asar ne fa. Kuma ai ba'a rama baƙi da baki. Ki duare mu je tare dan Allah ".

A harzuke ta ce "To uwar iya ni da bak'i k'irin zan rama! Ko momi ce ta kwanta dama ba zan yiwa Asad gaisuwa a zahiri ba."

Daga haka bata sake ce wa komai ba ta kashe wayarta tabbacin ta gama maganar ta.

Na k'ira Ansari na sanar masa ya ce 'Dazu ya ga N.T.A sun sanar mai dakin kwamishinan y'an sanda na jihar River's ta rasu.

Na numfasa na ce ya batun ta'aziya?"

Ya ce "Jibi in sha Allah zan bi jirgin safe na isa Abuja. Daga Maiduguri zuwa Abuja da tafiya ba zan iya zuwa a mota ba.".

Dad'i ya kama ni ganin na samu wanda zai je a cikinmu.

Na yi masa addu'ar ya iso lafiya.

Na kasa zaune na kasa tsaye tausayin Yaya Asad da na yaransa ya yi matuk'ar kama ni.

Yarana suna gidan Hajiya da yake a cikin hutu ake. Ban so aka tafi da Farha ba. Amma Amrah ta dage da ita zasu tafi ko su fasa zuwan suma. Kan dole na bari suka tafi da ita.

Sahal bai shigo ba sai goma saura na gabatar masa da abinci ya ce cikinsa a cunkushe yake.

Na ce "Rasuwa aka yi mana Baban Amra!.

Da hanzari ya ce"Waye?"

Murya ba amo na ce "Anty Rukayya Maman Bilkisu ".

Ya yi shiru da alamu nazarin wacece yake yi.

Da azama ya ce "Matar yayanku?"

Na ce "Ita fa Baban Amra. Ban ji tana ciwo ba sai mutuwa kawai na ji."

"Cike da alhini ya ce "Allah ya mata Rahma, ya shafe kurakuranta."

Cike da rauni nake amsawa da amin.

Ya shiga wanka ya fito ya yi shafa'i da wuturi.

Duk ina zaune ban iya motsawa ba.

Sai da ya hau gado ya zauna na tausasa harshe na ce "Baban Amra gobe nake son tafiya Abuja".

Ya yi shiru bai tanka ba. Tsawon lokaci ina dakon amsar sa.

Kafin ya ce "Ki yi mata addu'ar Allah yasa ta huta kawai. Amma gaskiya tafiya Abuja a yanzu bana so"

Na kalle shi sororo na ce zuwa ta'aziyar ne baka so na je?"

Ba ja in ja ya ce "Eh"a

Na rausayar da kai na ce "To kai zaka je a madadina?"

Ya girgiza ya ce "Ba zan sake na bi wannan hanyar ba don kuwa ina son rayuwata".

Na ce "To ni da bin hanyar ya kama sai ka lamince mini, zan bita idan kwana ne ya k'are Allah ya gafarta mini albarkacin zumuncin da zan je yi. Ni ba jiya ka ke fad'a mini an tattauna da y'an bindiga zasu daina addabar hanyar Kaduna zuwa Abuja ba?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Eh na fada miki tabbas, amma na ce miki an cimma matsaya ne da su?"

Na hurar da iskar b'acin rai. Na ce "To ko ba'a ci ba zan yi shahadar zuwa in sha Allah, Zan dawo lafiya".

A hassale sosai ya ce "Idan kuma tsautsayi ya sanya kuka yi arangama da su fa? Kinsan dai ko sun bar kowa suka kyalla ido suka ganki babu tantama jeji zasu wuce da ke tunda za ki dauki hankalinsu".

Na zuba masa ido takaici iri iri na cina na numfasa na ce "Ko mun yi arangama in sha Allah da masu raunin akan mace zamu yi kiliya ba jarumai akan al'amarin ba".

Nan da nan sai ya sha jinin jikinsa ya kasa furta kalma ko guda akan batun.

Ganin haka ya saka na ce "Gobe nake son tafiya Kano sai mu hadu da Yaya Hamida mu tafi".

Ya ce "Ki dawo lafiya amma ni dole kika mini, menene na zuwanki? "

Na zabura na ce "Ban gane menene na zuwana ba. Matar Yaya Asad fa na ce maka ta rasu ba wani kalen dangi ba".

Cikin ko in kula ya ce "Ansari ya ce mini zai je Bai isa ya wakilce ku ba. Ina ce nan da Mami ta rasu bai bar abin da yake yi ya zo muku gaisuwar mahaifuyarku ba, shine ke kike rawar jikin zuwa yi masa ta'aziyar matarsa?"

Bak'in ciki ya kawo mini wuya na tunzura ainun cikin fishi na ce "Baban Amra na roke ka fita a cikin sha'anina da dangina, ka daina saka bakinka a cikin duk abin da ya shafe cikin gidanmu tamkar yadda ban taba tsoma bakina ko yi maka katsalandan a tsakaninka da danginka ba. Ko bai zo mana ta'aziyar uwarmu ba to iyayensa da matarsa sun zo ya kuma yi mana a waya. Na tabbatar kuma baya k'asar ne, ko ma yana nan bai zo ba, to na yafe masa. Tunda rashin zuwansa ba zai saka Allah ya k'i yi mata Rahma ba".

Ya yi sakare yana kallona ya kasa furta kalma ko guda.

Na kwanta a gefen da nake kwanciya ba tare da tunanin yadda ya tunbatsa da fushi ba. Ni kuma na fara gajiya da yadda ba ya daukar damuwata da muhimmanci ko kad'an.

Washegari sassafe na shirya cikin tsaleliyar Egyptian abaya da na siya a wajen Umm asalan mazauniyar Eggypt(2349162662750, 201121544627).

Na shirya kayana da na yara a karamar jaka tunda a hutune. Ya kuwa tubure ba zan tafi da su ba.

Na cire kayan Amrah da na Yaya Farouk.

Na saka musu a wata k'aramar jaka tunda ya ce gidan Hajiyarsu zai kai su.

Ya ce "Ita Farha ba ni da iko akan ta ko Bilkisu?"

Yadda ya yi magana cikin rauni sai zuciyata ta nemi ta karaya. Amma na daure na ce "Ba haka nake nufi ba. Bana son na tafi ne ni kad'ai sannan nafi son duk inda kaddara zata wulla ni ta wullamu tare da ita. Idan aka yi rashin sa'a y'an tada k'ayar baya suka sace ni, tunaninta ne kad'ai zai fi saurin yin ajalina. Amma idan ina tare da ita zan samu sassaucin tashin hankali."

Ya ce "Saboda su ya'yan da kika haifa basu da haƙƙin akan ki ko?"

Na ce "A a saboda ita din itace zata fi zama abin tausayi idan babu ni. Don kuwa kasan ni din ce uwarta da kuma ubanta".

Cikin takaici ya ce"Abida da ranta haka nan Ansari da ransa idan ni ban ci arzikin rikonta a mini karar nima ubanta ba ne".

Na yi yak'en da babu nishadi na ce "Abida ai karimiya ce wajen magana d'aya tabbas ita ta haife ta. Amma har k'asa ta rufe mata ido ba zata jinginawa kanta Farha ba don kuwa tasan tawa ce."

Daga haka na ce "Zaka samu kaimu tasha ne ko mu je mu hau Napep?"

Ya ce"Mu je na ajiye ku"

Muka tafi tare da su Amrah suka kai ni tasha ya tafi da su zai kaisu wajen Hajiya na sani kuma ya hana tafiya da sune dan kada a sace su. Yaya Farouk sai kukan sharb'e yake yi. Haka Farha sai ta zama wata iri don gani take yi Yaya shine abokinta. Tafi sonsa akan yayarsu.

Sanin da na yi Yaya Hamida ba yarda zata yi mu je gaisuwar tare ba. Sai na tsaya a Kaduna gidan Saddiqa cikin sa'a ta gamsu zata bini mijinta kuwa bai hana ba, tunda ma a Abuja yake aiki. Don haka ya siya mana ticket din jirgin k'asa na k'arfe shida na yammaci. K'arfe takwas muka isa, muka tarar yana dakonmu.

Da kansa ya kaimu Wuse2 gidan da su Momi suke zaune anan kuma ake karban ta'aziyar.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Cike da alhini suka karbe mu.

Washegari muka gaisa da Yaya Asad duk da yana cikin gigita ya ji dadin ganinmu. A sanyaye ya ce "Sannunku Bilkisu da Saddiqa na gode Allah ya bada lada."

Haka ma Baba Babba da Momi.

Abida mun gaisa ba yabo ba fallasa. A wannan karon dakinmu daban Momi ta bamu. Duk inda Farha ta yi junior na binta na dinga mamakin hakan tasirin jini ne ko kuwa kammaninsa da yake ga ni a tare da ita ne? Ya dinga janta ta zo su je d'akin Ammi ko su yi wasa ita kuma sai da k'yar take binsa a cewarta ita ba yarinya ba ce kamarsa.

Da azahar Ansari ya iso.

Haka dai aka dinga karɓar gaisuwa ana sharar hawaye. Ya'yanta abin tausayi.

Ban sake tsorata da mutuwar ba sai da na ji sanadin mutuwarta.

Ashe wai allurar da ake yi a spinal cord take yi da take saka girman mazaunai da cikar kirji tare da fidda cikakkiyar sura mai dauakar hankali. Ashe hadarin da yake cikin irin wadannan alluran da magungunan bature da mata suke dirkawa kansu da sunan k'arin girman halittunsu ko ragewa yafi hadarin jirgin sama muni. Lafiya k'alau ta kwanta amma tashi ya gagare ta. Haka aka kwashe ta zuwa asibitin koyarwa na jamiar Fatakot. Sai dai gabad'aya wajen kugunta ya dagargaje a dalilin yadda ake mata allura a wajen da yake da had'arin gaske wato spinal cord. Ciwo bai bayyana ba sai da ya gama raraketa. Ko da aka je asibitin suka ce ba abin da zasu iya don hatta fatar ta da nake ganin tana glowing na mussaman ashe akwai sindarin hydroquinone a mayuka masu tsada da take tu'amalli da su.

Sinadarin da yake kwaile fata amma a wajen matan yau glowing ne. Tabbas da na ganta a haihuwar junior na ga halittarta ta sauya gabad'aya sannan fatarta ta zama ta alfarma jikinta ya zama rugu rugu tamkar tana cikin shekarun kuruciya, ta mini kyau ta burge ni, ni kaina mace, bare mijinta. Ashe da kuÉ—inta ta siyawa kanta lalurar da zata k'wamushe rayuwarta gabad'aya.

*

Hankalina ya rub'anya tashi tare da tunanin ta ina za'a bayyanawa mata illar kasassabar da suke yiwa kansu a dalilin maza?

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!

Sannan na sake tsorata da yadda mahaifiyarta take kuka tana fadin ita damuwarta yaran nan da ba wadda aka aurar duk da Aysha a lokacin ta kammala makarantar call to Bar a Enugu. Barrista ce ta gado Yaya Munira.

Sai fadi take yi a mayar da Laura kanwartta da take ruk'onta d'akin marigayiyar tunda ta saba da yaran, itama ta kammala jami'ar a wannan shekarar.

Na rasa me zan ce don na lura ita kubucewar Asad a matsayin surukinta yafi nukurƙusanta.

"Ke Duniya!

Na furta hakan cikin d'imuwa mai yawa.

A yammacin ranar Saddiqa mijinta ya zo ya tafi da ita inda yake akan gobe sai saka ta a jirgin k'asa na safe ta koma Kaduna. A dalilin Yaya Asad ya ce "Gobe mai d'akin gwamnan Katsina da wasu mukarraban gwamnati zasu yi masa ta'aziya a madadin gwamna da baya nan. Yana Saudiyya yana gabatar da umrah. Dan haka na bari sai na shiga jirginsu mu koma tare na huta da dogon zaman mota.

Ban yi masa musu ba na amince. Na zauna Sai dai basu zo washegarin ba. Sai da suka k'ara kwanaki biyu suka iso ranar sadakar bakwai da wuri.

Wanda mahaifiyarsu Anty Rukayya so ta yi daga taron sadakar bakwai a mayar da Laura d'akin yayarta. Na rasa gane wannan gaggawar da take yi. Ai ta bari a yi arba'in duk saurinta. Yayin da gogan ya yi biris bai tanka ba sai dai kallonsa kawai zaka yi ka gane bai gamsu da tayin da take ta yi masa ba.

Ranar da zamu tafi junior kuka tuburan Sai ya bi Farha. Na dinga mamakin yadda yake sonta kai tasirin jini yawansa ya kai k'urewa. Kuka sosai ya rik'e ta. Na kalli Abida na ce "Ko na tafi da shi idan hutunsu Farha ya k'are sai na dawo miki da shi?"

Ta girgiza kai tare da ce wa "Bar shi kawai Bilki Idan ya biki kafin gari ya waye zai dame Ki da kukan nemana ".

Na kalli Farha da take rike da hannuna na ce "Farha to Ki zauna nan da 7days sai a kai ki Kaduna gidan Anty Saddiqa daga nan sai Dady da yaya Amrah Su zo Su d'auke ki ku dawo gida ".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ta ce "Tare da ke zamu zauna?"

Na ce "A a ni yanzu zan tafi ke kuma zaki dawo nan da just 7days".

Ta make kafada tabbacin bata yarda ba.

Na ce "Ki ga fa junior na kukan bai so ki tafi".

Ta ce ",To shi ya zo mu tafi gidanmu mana ni dai ba zan zauna ki tafi Ki bar ni ba".

Ganin haka ya Asad ya sure shi ya kaiwa momy shi yana ta faman kuka sosai.

Kowa Sai da ya yi mamakin junior sosai.

Wannan karon har harabar gidan Abida ta rako ni. Ta k'asa hakuri ta ce "Bilki telan da yake yiwa y'ay'anki dinki ya iya sosia".

Na kalli leshin da na sanyawa Farha na tabbatar kyaun da ya yi Mata ne da yadda ya zauna cif ya saka Abida k'asa hakuri ta yaba a fili.

Na ce da junior mace ce da sai djnga yi mata. Mace amma Kano take. Indai dinkin yara mata ne da zannuwan gado to kawai kin je makura wajen samun waccyta kware."

Abida ta ce ", Gaskiya na gamsu. Amma zan karbi lambar na bawa ya'yan Yaya Asad tunda hasu Noor da Amal nan duk da sun fara girma".

Na ce "babu damuwa zata yi musu kuma ta aiko musu kayansu cikin aminci."

08080266674 ga lambarta ga masu son ganin y'ay'ansu cikin d'inkuna na garari da zannuwan gado na alfarma.

Haka na shiga cikin tawagar first lady muka juya Katsina.

Tun kafin mu tashi na fadawa Baban Amra a jirgi zamu dawo ya taremu a iyafot nan anjima.

Cikin sa'a kuwa a iyafot din na tarar da yara suna dakonmu.

Farouk ya ce "Mamah kinsan a jirgi zaku dawo kika tafiya da ni? Kinsan dai ina son shiga jirgi ko?"

Na murmusa na ce "Da ikon Allah yayana zaka hau jirgi zaka biyawa wasu ma Su hau in sha Allah ".

Dad'i ya kama shi ya ce "Ameen Mamah."

Amra ta ce "Amma ni fa Mamah ni Ki Abujan ma ban tab'a zuwa ba".

Na ce kema haka Amra duka ina yi muku addu'a. Abuja kuwa zaki je hae sai kin gaji".

Ta ce "To Mamah. Ammina mai ta baki ki kawo mini"

Na ce ",Sai mun je gida leda ne a daure ban bude ba, idan na baki sai ki bude da kan ki."

Ta murmusa tare da ce wa "Na gode ".

Ina gaba yara na baya. Ya kalle ni ya ce "Ya k'arin hak'uri?"

Na amsa da "Alhamdulillah!

Ya ce "Na ji dadin ganin ki sanye da hijab din nan ya rufe ki ruf sannan kuma ya miki kyau sosai."

Na murmusa ina jin dad'i har k'asan raina don zan iya cewa wannan ranar ta shiga cikin ranakun da ba zan mance ba don kuwa yana wahalar gaske ya yaba mini idan na yi kwalliya.

A raina na ce "Madallah da Gunis hijab. Hijabanta duniya ne don kuwa yankan hijabanta zama suke a jikin mutum daram a kuma sake sosai a cikinsu. Ga yadin masu dad'in sawa, ba masu saka jin zafi ba ne.

(08163761797 gunis hijab and more)

Muka isa gida Amra ta dauki jakar kayanmu yayin da Babanta yake rike da tawa. Shi kam Yana son rike mini jaka. Yana wahalar gaske yarana ko wasu mutane na waje Su gane yana musguna mini don yadda yake mini a gaban mutane ya saka danginsa suka washe ni. Kowa kallon sha'awar zamana da mijina yake yi amma a zahiri ni kad'ai nasan gashin kumar da yake yi mini.

*Bayan watanni hud'u*.

Sannu a hankali sauyawar Sahal ta cigaba da yawaita. Kamar yadda na fada ba wai fada ko sababi yake yi mini na kaitsaye ba, kawia shagulatun bangaro yake yi da ni. Matuk'ar waya na hannunsa ba shi da lokacin komai ko fahimtar komai. Sai dai kawai ka ga yana ta danne danne a waya yana murmushi. Sannan kaffa kaffa yake yi da wayar kamar me. A da baya dare a waje duk inda bakwai take ya dawo gida, ya ci abinci ya tafi sallar isha Idan ya shigo sai kuma gobe. A yanzu sai ya kai tara wani lokacin har goma bai dawo ba. Na fara damuwa sosai, ga rashin samun biyan bukata wanda na lura tamkar ya manta ina da haƙƙin akan haka. Sannu a hankali na shiga wani irin yanayi da likitoci suka tabbatar mini ciwon damuwa na (depression) ke son kama ni. Suka bani shawarwarin na k'arantawa kaina tunani da ragewa kaina damuwa. Aka d'ora ni kan magunguna.

Basma ta dinga fad'in "Idan ba ki shafawa kanki ruwa akan lamarin Baban Amra ba sai hawan jini ya kama ki Bilki. Ki tattara shi ki koma gefe ki rungumi ya'yanki ki bashi dama ya yi abin da yake so".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ina son na bude baki na fada mata abubuwan da nake fuskanta sai na kasa, sai na ji Abida kawai nake son farkewa damuwata ko da kuwa zata balbale ni da sababi ne. Amma dai Maman Abdul ta riga ta fahimci rayuwar da nake yi a gidana.

Shiyasa ta tsani Sahal, shima kuma ya tsane ta ainun.

Wata rana da daddare sai juyi nake yi a gado gogan yana kwance lamo da alamu ma barci ke shirin d'auke shi. Na daure na cire kunya na mirgina kusa da shi na saka hannu a kansa ina shafawa zuwa kunnesa a kokarina na isar masa da sakon gayyatar da nake yi masa.

Tsawon lokaci ina yi masa hakan ya k'i yin motsi sai ma lumshe idonsa da ya yi.

A hankali cikin rada na ce "Dady wake mana".

Murya ba amo ya ce "Wlh kaina ciwo yake yi mini, Ga gajiya da ta yi mini dabaibayi gabad'aya".

Ina jin haka na gane ba zai amsa gayyatar da na cire kunya na yi masa ba.

Na cije na ce "Anya Dady kana lissafin adadin watannin da muke kallon juna tamkar hoto kuwa?".

A takaice ya ce "Ki yi hakuri in sha Allah jibi zamu yi, ki shirya tarbata sosai '

Jiki na k'warai na matsa daga jikinsa. Amma zuciyata ta yi nauyi sosai.

Haka na hak'ura ina fatan Allah ya kaimu jibin lafiya tunda dai ina so, ba ni kuma da mai yi mini sai shi.

Da hantsi na yi magana da (Bojuwa herbs 08032773332 what'sapp only) na saka order din ciccibin garari da Tsumin saiwowi a kokarina na sabunta kaina a wajensa. Na tura kuÉ—in na tabbatar gobe sassafe zata turo mini Katsina. Ban ji ko d'ar ba tunda dukkan costomers din Surayya Halin yau mun tabbatar bata magana biyu, na shaida a gobe da safe zan karba na ci kafin dare ya bi jikina in sha Allah.

Na je saloon na wanke kaina. Nadinga bare bare tamkar me. Amma me da jinin ta zo sai bawan Allan nan ya yi barcinsa da na tashe shi sai ya sake ce mini ya sake d'agawa sai wata jibin a dalilin jikinsa na yi masa ciwo. Daren jiya ke nan wanda hakan ya sababa mini bacin rai da tsananin tashin hankali. Daga baya kuma na zo na gano soyayyar da yake yi da dalibata Hawwah. Da irin sababin da ya dinga yi mini. Har ya zama ba'asin da na shiga d'imuwa da tashin hankali. Da yadda Basma ta zo gare ni ta kai ni asibiti har zuwa lokacin da ya tabbatar mini yana neman aure.

Na ja gauron numfashi tare da goge hawayen da ya k'i yanke mini don kuwa na famowa kaina abubuwan da suke nauyaya zuciyata.

A fili na furta "Allah ka yaye mini nauyin zuciyar da ya dame ni.

Allah ka taimake ni ka kawo mini É—auki da kanka. Allah ka bayyana mana Yaya Sulaiman idan yana da rai, idan kuwa raine ya yi halinsa Allah ka masa rahama."

*Nan ne karshen hakaito labarin da Bilki ta bamu.*

*Sai a gyara zama don jin danbarwar da zamu sake kutsawa da kuma abin da zai biyo ba.*

*Ina baku tabbacin zaku nisahdantu a gaba.*

*MalaysianFabrics*

*Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.*

*Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.*

*7020695644.*

✍️✍️

Surayya Dee

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bilkisu ta gama hakaito duka tarihin rayuwarta, gabaɗaya jikinta ya mutu ba ƙwari. Tana zaune tana sauke tawagen numfashi lokaci ɗaya tana mai tsiyayar ƙwalla.

Kirjinta ya yi nauyi. Tarwatsewar gidansu shine mafi tashin hankali a rayuwarta. Sai dai nade k'afar wandon da Sahal ya yi yake shirin nuna mata ainihin shi namiji ne yana matuk'ar sakata zullimi da fargaba

Ba ta san iya lokacin da ta É—auka zaune tana kuka ba sai da Alti ta leko don ta yi mata sannu sai ta iske ta cikin kuka.

"Yanzu Hajiya ba ki bar wannan kukan ba?

Ashe ba zaki dangana ba?"

Jin haka yasa ta sake rushewa kuka ta ya ya za a ce na bar kuka ahalin abin kuka ne ya dabaibaye rayuwarta

"Na sha faɗa miki Hajiya, kuka ba shi ne magani ba addu'a zamu cigaba da yi. In sha Allahu komai ya kusa zuwa ƙarshe. Dazu har murna ta kama ni, ganin kin karbi rarrashin da na yi miki kin ware sai kuma ki sake rikice wa?"

Alti ta sake fad'a lokaci daya tana dafa kafaɗarta bayan ta ƙarisa shigowa cikin ɗakin ke nan.

"Alti kullum fa haka kika ce mini. Ga shi shekaru sai sake turawa suke yi amma babu wani abu da ya sauya."

Ta ƙarishe faɗa cikin kuka da har muryata ta dishe bata fitowa sosai.

"Kar ki cire rai ga rahamar Allah. Ubangiji yana sane da ke, ina da yaƙinin ya amsa addu'arki Nikawai mu jira lokaci Hajiya."

Ta tsinci kanta da share hawaye tare da gyaÉ—a mata kai.

"Na gode Alte kin kasance da ni a lokacin da ba kowa a kusa da duniyata. Ba zan taɓa mantawa da kasancewarki tare da ni ba."

Bilkisu ta fad'a cikin dauriya.

"Ba komai Hajiya mun zama É—aya."

Da daddare da Baban Amrah ya dawo bai neme ta ba. Itama bata neme shi ba, saboda ta riga ta shiga damuwar da ta zarce fishinsa takura, tana cikin wani yanayin da take bukatar kadaici. Ranar ita da shi kowa a dakinsa ya kwana sai da safe ne ya shigo É—akinta da shirin fita aiki.

Kallon kallon suka yiwa juna.

Kamar ba zata gaishe shi ba, saboda haushin faÉ—a in faÉ—an da suka yi da shi Har da ce fad'in ko yanzu kasuwa ta watse d'an koli ya ci riba. Maganar ta yi mata nauyi da yawa. Amma ganin ya biyo ta thar É—akinta sai ta daure ta gaishe shi a takaice.

Ya amsa da fad'in "lafiya lau, ya jikin na ki?

A ginshire ta amsa masa da cewa ta ji sauƙi daga haka shima bai ƙara tofawa ba, ya saka kai ya bar mata ɗakin. Ta bishi da kallon mamaki tana ayyana, shi yanzu jira yake yi ta ba shi haƙuri ahalin shi ne ya yi mata laifi! Murmushin gefen baki ta yi lalle ko sai dai su dauwama a haka abin da Abban Amrah bai sani ba, yanzu ba ɗaya ba ne da baya. Abubuwan da ta ɗauka a wancan lokacin yanzu ba zata iya kauda idanuwa a kansu ba.

Anya kuwa Bilkisu?

Amma dai mu cigaba da bin ta a hankali.

Sun shafe sama da sati duna zaman doya da manja. Yadda baya shiga harkarta itama bata shiga harkarsa.

Daran da suka yi sati basa kula juna ya biyo ta har É—aki ya ce "lokaci ya yi da zai ta shi daga gidanta ya yi saboda ya ga abin ya zo da cin mutumci tun da har 3na fara yi masa gori."

"Ni na yi maka gori Baban Amrah?"

Ta tambaye shi a gajarce.

Cikin gadara ya ce" E kin yi mini gori kin faÉ—a mini maganganu masu zafi saboda kin ga ina zaune a gidanki, to kar ki manta nima ina da nawa gidan saboda haka can za mu koma."

Har ya fice na kasa iya tanka masa. Dariya ma ya ba ni domin sai na ga ƙarfin halinsa ma, ya manta da ce wa ginin gidan kaso mafi girma da dukiyata aka yi shi? Amma yana faɗa mini cike da gadara wai na yi masa gori zai tashi daga gidana ya koma gidan shi. Lallai ma!

Sahal.

Zaune a cikin mota suna hira da budurwan shi a bakin hostel É—insu don ba yar Katsina ba ce karatu ne ya kawo ta amma asalin ta y'ar kaduna ce.

Tun bayan isha'i ya zo suna ta hira. Tuni kuma ya gana da mahaifinta tun farkon zuwansa gidansu a lokacin da suka je Zaria da Amrah Bilki ta wuce Abuja a wannan tafiyar ya je Kaduna gidansu tunda suna hutu ta je gida.

A wannan ranar sai ta gan shi duk wani iri a hargitse.To

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "My Dear me yske faruwa ne?"

Ta faÉ—a tana kallon shi, lokaci É—aya tana kashe shi da kallo da ita kaÉ—ai ta san yadda kallon yake tasiri a wajen Sahal.

Kamar yadda ta sani É—in ya yi tasirin domin nan da nan ya susuce ya fara mata sambatu.

"Zullimi nake shiga kada samarin zamani su mini shigar sauri, so nake ki ba ni dama gemu da gemu su zauna akan batunmu. Kin ga dai ni ba yaro bane dan zan yi ta jan doguwar hira a tsakaninmu ".

Cikin tattausan lazafi ta ce" To ai kai nake jira My Dear! Mun gama fahimtar juna, kuma ka nemi izini magana da ni wajen Baba. Na aminta da kai. Yanzu sai ka turo magabatanka gidanmu don magana ta nuna".

Da sauri ya ce" Na gode sosai in sha Allah ba za ki yi nadamr aurena ba "

Nan da nan fara'an fuskarta ya ƙaru ta shiga kashe Shi da kalaman da ta san suna kunna shi, shima yana mayar mata da martanin cikin soyayya da kulawa kamar ba shi ne ya ajiye kamar su Amrah a gida ba.

Sai wajen goma da rabi ya bar makaranta zuciyarsa kamar farin takarda ranar kwanan farinciki ya yi, gwara ya yi auran nan ko Bilki za ta shiga taitayinta shi yasa aiki na yi masa sauƙi ya je Zaria wajen Baban zaria ya kai masa maganar auren da ya ke son ƙarawa. Akan ya yiwa Baban Mashi magana su nema masa auran.

Cikin mamaki Baban Zaria ya ce" Aure kuma Sahal? Daga samun aikin ka sai k'arin aure ya biyo baya? Anya kuwa?"

Cikin ƙankan da kai Sahal ya ce" Baba Allah ne ya ba mu umarnin mu ƙara in za mu yi adalci sannan da halin ƙarawar. "

"Jin haka ya sanya Baban Zaria fadin "Tabbas haka ne. Na gamsu da mganarka."

Jin haka ya sa ya gyara zama yana sake faÉ—in" Kuma ni da matata muna da fahimtar juna ina da tabbacin babu wata matsala Baba."

"To Alhamdulillah. Haka na da kyau. Za mu je zan yi magana da Baban Mashin in sha Allahu"

Sahal ya ji daÉ—i haka ya baro Zaria cike da farinciki, bayan ya cika Baban Zaria da iyalasa da alheri suna ta godiya.

Tunda ya dawo akai akai yake kira Baban Zaria ya ji yadda ake ciki shi. Baban ya sanar masa sun yi magana da Baban Mashi ya faÉ—awa yarinyar ta shaidawa iyayenta suna nan zuwa ranar lahadi. Murna wajen Sahal ba'a magana daga shi har ita Hawwan suna cikin farinciki, tuni ta sanarwa mahaifiyarta ta faÉ—awa Babansu ta kuma turawa Sahal lambar kanin babanta shi kuma ya turawa su Baban Zaria.

Baban Zaria da Baban Mashi sun isa Kaduna nemawa Sahalu aure kuma an yi musu karban mutumci sosai, bayan dogon jawabi da dalilin zuwansu aka yi fatan alheri. Tare da cewa sun bawa yaro yarinya. So da sun zo da sadaki na sai a daura auren kawai.

Su Baban Zaria suka bada uzzirin Basu zo da shiri ba Aman Su sauarare su nan ba da jimawa nan da sati biyu za su dawo da sadaki da kudin gaisuwa. Ma'auratan kuma su yi gwajin lafiyarsu.

Da wannan daddan labarin suka dawowa da Sahal. Wanda shi tayar masa da hankali labarin ya yi tunda Bai shirya babl. Sai Dai Bai yi turjiya ba tunda yana so Yana Kuma son ya tsura da mutuncinsa a idon yarinyar da iyayenta. Haikan ya tashi ya fara fafutukan kamallah ayyukan da suka rage a sabon gida. Allah ya taimake shi akwai kayan band'aki da suka yi ta siya yanzu kawai ma'aikata ya kira aka fara aikin wasu na fenti wasu na hidimar hattama band'aki da sauransu. Yanzu hankalinsa da burinsa na wajen gama wannan gida da auransa. Bilki ta fahimci baya cikin natsuwarsa amma ba ta kawo komai a ranta ba ta ɗauka maganar da ya yi mata yasa yake ƙoƙarin ganin gidan ya kammallah ashe shi nasa shirin dabam.

Cikin sati biyu aka gama komai hatta fenti an gama. A kuma lokacin su Baban Zaria suka koma suka kai kudin aure tunda sun kira su daga can sun ce su zo sun gama bincike. An saka ranar aure wata daya kamar Yadda Sahal ya bukata a masa alfarma haka tunda bai yi lefe ba.

Ganin Sahal ya kammala da hidimar gini ya kuma bawa Yaya Toure kudi akan ta je Kano ta hado masa lefe. Ta ce kudin ba zai isa ba. Amma zata cika masa daga baya sai su warware.

Ya samu Bilki ya ce an gama gida zasu tare amma yana so ta zaɓi bangaren da ta ke so ko kasa ko tsakiya saboda can sama nasa ne.

"Ban ga ne na zaba ba, dama ba duka bangaren ne namu ni da yara ba?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bilki ta tambaya cikin mamakin sa matuk'a da gaske.

Cikin halin ko in kula ya ce" A a bangare É—aya zan iya ba ki daga ciki."

Mamaki ya sake kamata to me ya sa zai ce haka kafin ta ce komai , ta ji ya cigaba da magana

Cikin dakiya ya ce "Dan mu gama maganar gabad'aya. Ki nutsu ki ji ni da kunnen basira, batun auren da na ce miki zan yi ne ya matso, za'a yi shi a karshen wata mai kamawa idan Allah ya yarda".

Kan Bilki ya sara, zuciyarta ta harba da tsananin gaske. Gidan da ita ta gina da kuÉ—inta shine zai saka wata macen a ciki?"

Wanne irin zalunci ne haka?"

Take ta tuno Abida ta sake tuna Basma da ta ce mata ta yi wautar zuba makudan kudade wajen ginawa miji filayensa. "Tabbas na yi wauta Basma! Komai ya na neman kubuce mini Abida ga shi kin yi mini nisa.!

Bilki ta furzar da wadannan kalaman cikin fitar hayyaci.

Ya make kafaÉ—arsa tare da fad'in dama "Ai nasan wadannan halittun guda biyu basa sona na kuma tabbatar a yanzu Basma ce take d'ora ki a keken bera tunda uwar iya kun yi tawarwatse da su".

Kuka sosai Bilki take yi wanda Duk mai imani sai ya buge shi amma haka ya saka kai ya barta.

Kukanta ya k'aru a dalilin ta ji ciwon yadda ya goranta mata tarwatsewarsu da su Abida ".

Ta dinga yinsa har ta gajiya dan kanta tunda a d'akinsa suka yi da a d'akinta ne tasan da tuni Alti ko Alawiyya sun leko dan ganin lafiyarta.

Da k'yar ta fito zuwa d'akinta ta yi wanka ta yi salla tana adduar neman sassauci daga azabben kishin da yake neman fasa mata zuciyarta.

Washegari ya sake tuntubarta akan ina take so sama ko k'asa don iyayen yarinyar zasu zo ganin d'aki.

Cikin yanayin da yake fahimtar iya gaskiyarta ta ce " Ni ba zan kaura ba ka bata duka bangare biyun. Ni kuma ina nan da yara idan ka samu sararin zuwa ka leko mu".

Ya zuba mata ido amma kuma ya tabbatar da she means her words.

Ya kasa ce mata komai ya share maganar.

Amma gabad'aya jikinsa ya yi sanyi ya tabbatar idan ya amince da hukuncinta sai duniya ta yi masa tofin Allah tsine bayan haka kuma haƙƙinta ba zai bari ya rayu a gidan cikin nutsuwa ba.

Kansa ya kulle ya rasa dabara. Kawai sai ya ya É—auko mata Hajiya har gida ya ce ta yi mata faÉ—a, nauyin Hajiya da yadda ta dinga bata baki da fadin kishiya ai y'aruwace me zai saka ta bar mijinta saboda da wata alhalin shi bai barta ba. Haba Bilki ya da haka kuma? Ke da na ke yabon kirkinki, tunda ya samu ya gama gina gidan nan ki yi hakuri ki karbi bangare É—ayan ki koma, ai yanzu sai mutane su yi ta yamididin ya samu wadata zai yi miki butulci idan na isa da ke ki bi umarnin mijinki, bai kyautu a ce wata ce za ta zo ta fara shiga gidan da aka yi gwagwarmaya da ke ba."

Bilki ta kasa magana tana kallon Hajiya, saboda darajarta yasa ta amince za ta koma gidan babu dogon turanci.

"Ba komai Hajiya in sha Allahu zan koma."

Ta fad'a a takaice.

Hajiya ta yi ta saka mata albarka.

Har haraba ta rakata inda Sahal din ya mayar da ita kamar yadda ya dauko ta.

Tunda kuma ta yi wa Hajiya alkwari ta shiga fakin din kaya Alti da aluawoya na taya ta.

Yara suna ta tsallen murna tun da Dady ya faÉ—a musu zasu koma sabon gida.

Bata siyi komai ba tunda kayanta sabbi ne basu ji jiki ba. Cikin sati É—aya da zuwen Hajiya suka tare a sabon gida, k'asa ta dauka ita da ya'yanta, ta bar musu tsakiya da saman shi da amaryarsa.

Dama kuma zanen gidan kasa da tsakiya duk iri d'aya ne. K'afar benen akwai inda za a shiga ta falo da kuma ta kofar baya.

Dan haka amarya zata dinga amafani da ƙafar benen baya ne ba wacce take cikin falon Bilki ba.

Tunda kuma suka koma sabon gida Bilki ta sake zama shuru shuru, duk da ba ta ji zancen saka ranar auran Baban Amrah ba amma a kalaman Hajiya ta fahimci auran ya zo sai shi da kanshi lokacin bikin saura sati biyu ya ke fada mata, ko a fuska ba ta nuna masa damuwa ba ta yi masa fatan alheri. Shi kansa ya fara damuwa da yadda shirunta ya k'aru har yara sun fahimci rashin son yin maganarta ya ninku sosai sannan kuzarinta ya ragu ainun. Gabadaya ga ni take yi tamkar yarinyar na nunata ko Sahal ya gama fad'a mata yadda suke zaune.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bayan haka abin da Sahal ya yi mata na tarewa da sabuwar amarya cikin wannan gidan ya yi matuk'ar tsorata ta tare da jefa mata firgici da faduwar gaba mai yawa.

An yi biki sosai a can gidan Hajiya duka y'anuwan Sahal sun taru, Bilki ko daga ita sai ya'yanta sai ko Basma. Bata gayyaci kowa ba don kwata kwata bata kwarafniya tafi son yanayin shiru.

Kayan fadar kishiya ma bai yi mata ba haƙuri kawai ya bata tare da gabatar da uzzirin cewa abin ya zo a kurewar lokaci ne. Amma zai mata ita da yara. Bata nuna masa komai ba, don kuwa bata saka rai zata samu wani abu daga bangarensa ba.

Ko ranar É—aurin auran haka ya yi ta rawan kafa da safe kafin su tafi daurin aure. Sannan gayyar abokai ya yi sosai tunda gidan suka biyo suka dauke shi. Daga dauren aure ba su dawo ba sai da tawagar a amarya Tuni Bilki ta sanya Alawiyya da Alti sun yi snacks sosai, sai dai ba'a soya ba, ta adanasu a firij sannan an zuba ruwa da lemu a fridge, ta yi hakan ne idan iyayen amarya sun girmamata sun zo dakinta zata basu idan kuwa basu neme ta ba, sai ta bar abinta a firiza. A gidan Hajiya aka fara sauke amaryar sai daga baya aka kawo ta nan gidan. Kaitsaye falon Bilki dangin amarya suka yada zango.

Sosai Basma da Alti suka karbesu yayin da Bilki take zaune fuskarta a sake. Nan da nan aka kewayesu da ruwa da lemu.

Aka yi addu'a da fatan alheri.

Sannan yan'uwanta suka bawa Bilki amana ta kuma ce ta karba Allah ya basu zaman lafiya.

Sannan suka wuce saman amarya.

Bilki ta saka Alti ta yi musu abinci a daran da safe ma ta ba da umarnin a yi musu abin kari duk da gogon ya kawo musu daga gidan Hajiya Alti take faɗa faɗa mata. Wataƙila yana tunanin Bilkin baza ta yi ba ne.

Washegari da zasu tafi ta saka aka soye musu samosa da springrols aka zuba musu babbar container aka basu. Godiya kan godiya suka yi mata. Ita da kanta Bilkin ta tabbatar mutanan Zaria karimai ne ta gane hakan tun sadda ta yi zaman garin. Yanzu ma sun nuna mata halin girma tunda wasu dangin amarya idan sun kawo ta tun daren suke dasa fitinar da ba wadda yasan inda zata tsaya su tafi su bar y'arsu cikin garari. A zuciyarta ta dinga fatan yarinyar ta yi halin y'anuwanta tare da jin nasihar da suka yi mata. Idan har ta bata girmanta ita kuwa zata yi mata adalci don ba ta yi mata laifi ba, don ta zo gidanta a matsayin second wife. Ba kuma ita ta kawo kanta ba, maigidan ne ya kawota bayan ya durkusa a gaban iyayenta ya nemi alfarmar a ba shi a ita. Shima kuma Allah ne ya halasta masa k'ara aure. Idan kuwa haka ne zata yi iya kokarinta ta danne duk beken Sahal da take ga ni zata yiwa yiwa yarinyar adalci matuk'ar ba ta nuna mata d'ab'iar albasa ba.

Bayan an watse ranar da zai shiga É—akin Amarya ya tarasu a bangaren Bilki ya yi musu nasihan zaman lafiya. Ita dai Bolki ta bashi tabbacin bata da matsala. Amaryan ma ta ce haka.

Ya ce " Maganar girki sai nake ganin a dinga yi tare tunda ke da ita kuna makaranta kullum. So idan Alti ta yi sai a dinga zuba mata Alawiyya na kai mata kafin ta kammala makaranta sai ta fara yin nata.

Me kika ce akan wannan batun Bili?"

Ya fad'a cikin sigar soyayya lallashi.

Take Hawwah ta ji wani iri a zuciyarta, ta sake karaya don kuwa tunda ta sauko ta ganta gaban Malamarta ta ji tana neman rasa confidence din da ta shigo gidan da shi. Duk yadda suke ganin kyaunta ashe daga nesa ba komai suke ga ni ba. Wata irin mace mai kirar kalangu sannan mai dongon hanci da manyan idanuwa ga ta fara tas, sannan doguwar mace sambal. Bayan wadannan kallo d'aya za'a yi mata a gane ilimin rayuwa da addini sun yi mata k'awanya don ba alamun girman kai ko izgili a tare da ita. Sannan kuma kudi sun zauna mata sosai tunda ga yanayin k'amshinta, fatarta da suturarta da kuma yadda ta kawata wajenta da kayan kawa na alfarma.

Duk yadda ta gamsu Sahal na sonta sosai amma yadda ya kira matarsa da Bili sai da ta ji wani iri don kuwa ta zaci ai ta wuce ya dinga yi mata irin wannan soyayyar, ta dauka tunda ta tsufa babu wata soyayya sai zaman hakuri da juna.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sannan sai taga daga ita maik'uruciyar har shi mijin nasu sun zama kamar masu barance a gaban Bilki. Kamewar Bilki da yanayinta na rashin hayaniya ya sake mayar da ita mace mai aji sosai.

Da sanyin murya ta ji Bilkin ta ce "A a bai yi ba, amarya ba zata zauna jiran sai an bata abinci ba. Ta dinga yin abincinta muna yin namu. Duk mai girki a cikinmu ta dinga baka. Bakinta ita kad'ai na za a dora mata hidimar bawa mutanen gida abinci sannan ga hidimar karatu ".

Sahal ya diririce don ya gano Bilki ba zata ba shi tallafin rike masa amarya ba ko kad'an.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Gabaɗaya zuciyarta ta ƙuntata ta rasa me Sahal yake nufi da ita tana ta rufe masa k'ofifin fitina a gida amma ba ya ga ni.

Ciwon kai da jiri sun sako ta a gaba tafi son ta riƙa zama ita kaɗai. Ta yi ta tunani mai zurfi, ba ta iya cin abinci nan da nan ta fara rama tana zaune sai ta ji kawai tana hawaye, miji ba ya ta kanta bai damu da halin da ta ke ciki ba. Daga yaranta sai Alti da Alawiyya sune kawai suka damu da ita, ita kanta tasan ba ta da lafiya. Dole ta shirya ta je asibiti likita ya sake ba ta tabbacin tana bukatar natsuwar jiki da na zuciya domin depression ya kamata ya yi ta mata faɗa akan ta kula da lafiyanta idan ba haka ba za a samu matsala ya bata shawarwari sosai sannan ya rubuta magunguna ta biya phamarcy ta siya sannan ta dawo gida tana zuwa ta ga Basma ta zo tana jiran ta, ko ba ta faɗa mata ba ganin ta kawai da ta yi ya sa ta san ba ta da lafiya.

"Bilki me ke damun ki ne? Kin ga yadda kika lalace?

Bilki ta kasa ba ta amsa sai ido kawai kamar wata doluwa.

"Bilki ki yi mini mgaana ki fidda abin da ke ranki in ba so kike yi ki kashe kan ki ba."

Basma ta faÉ—a cikin tausayin Bilki, ledar magungunan ta É—auka ta dudduba nan ta ga halin da Bilki ta ke ciki.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.'

"Bilki kin kusa mutuwa ban sani ba?

Ta fada cikin tausayawa kamar ta fashe da kuka.

"Ki yi kuka, ki yi kuka ko za ki samu natsuwa Bilki"

Basma ta fad'a cikin d'imuwa.

Tsawon lokaci bata samu ko kalma d'aya Bilkin ta furta mata ba. Amma ita tuni ta gano damuwarta. Bai wuce juya baya da miji ya yi mata ba har hakan ya yi mata sanadin depression.

Ta dauki wayar Bilkin ta fita zuwa falo ta lalubo Yaya Hamida.

Kamar ba za'a dauka ba sai kuma ta dauka.

Ta gaishe ta da girmamawa tare da ce wa "Yaya Hamida zan fad'a miki Bilki bata da lafiya tana bukatarku a kusa gudun sai ta yanki jiki ta fadi da ku ji".

Duk tsiyar Yaya Hamida sai ta rikice da tambayar me ya samu Bilkin?"

Basma ta ce "A zahiri tana zaune lafiya amma a badini tana fama da jinya mai had'arin gaske don magungunan da aka d'ora ta na ciwon damuwa ne.

Dan haka ku yi kokari ku dinga yi mata abubuwan da zasu dinga Debe mata kewa da takaici."

A tsorace Yaya Hamida ta yiwa Basma godiya tare da cewa tana tafe cikin satin nan.

Da haka suka yi sallama sannan da ta koma cikin daki wajen Bilki.

Ta cigaba da bata hakuri, har ta samu cikin kuka sosai Bilki ta fad'a Mata wulakancin da Sahal yake yi mata, sannan duk abin da matarsa ta ce Amrah ta yi sai ya hau ya zauna ya hau sakin kalamai masu ciwo.

Bayan haka abu kadan abu zai had'asu ya yi mata gorin bata da wajen zuwa gidansu ya tarwatse saboda son zuciya.

Hankalin Basma ya tashi ta ce Shi Sahal din ne yake miki gorin ahalinku sun watse kuma iyayenki masu son zuciya ne?"

Da gunjin kuka ta gyada mata kai.

Ta numfasa ta ce kinsan dai mahaifiyata yar Mashi ce Ko?"

Bilki bata ce komai ba illah kuka.

Basma ta ce "Fadar wannan maganar ba abin dad'i ba ce sannan idan ya ji a bakinki har abada ba zai sake miki gorin abin da ya faru a gidanku ba.

Sannan zai iya zama sanadin da zai sake ki. Shin na fad'a miki ko na kame bakina kada ki fad'a masa ya zama sanadin da zaku rabu ki d'ora alhakin mutuwar aurenki a kaina!

Da kuka sosai ta ce "Fad'a mini Maman Abdul na riga na gaji da zama da shi kullum ina addu'ar Allah ya yi mini zabin alheri a rayuwata amma na gaji da Sahal gabad'aya ba shi da kirki bai san adalci da yakamata ba".

Basma ta tashi ta rufe d'akin sannan ta zauna daf da Bilki. Ta sassauta murya ta ce "Kin san Iro Mashi?"

Murya ba amo Bilki ta ce"k'anin babansu Sahal ne, Baban Abuja suke ce masa."

"Madallah! Basma ta fad'a a hanzarce.

"Ko kin taɓa jin labarin ya lalata Yaya Turai? Turmi da tab'arya mahaifinsu Sahal din ya gansu sanadin haka ya fadi shike nan har ya mutu bai sake tafiya ba!

A lokacin Yaya Turai bata zama budurwa sosai ba, kamar dai su Amra haka ya dinga haike mata kamar bunsuru, kuma ya dinga tsorata ta akan idan ta fad'a sai ya yanka ta. Sai da dubu ta cika aka gane. An ce har yanzu yana nan a Abuja yana cigaba da fasadinsa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tashin hankalin da aka yi ba kad'an ba ne kuma wannan bak'incikine ya kashe uwarsu, kakarsu Sahal din kenan.

Kan dole aka hak'ura aka danne maganar a tsakaninsu. Amma wadanda suka sa ni sun riga sun sa ni.

Dan haka kada ki sake damuwa dan ya goranta miki kun yi shari'a da Baba Babba ko kuma Baba Babba ya yi shari'a da ku nasu abin kunyar na tir ne da neman tsarin Allah da shi".

Bilki ta saki ajiyar zuciya ko kadan wannan labarin bata ji dadinsa ba tunda ta had'a zuria da su. Sai dai tabbas idan ya cigaba da taɓa mata darajar gidansu zata fad'a masa. Idan ya so komai ma ya faru .

A gidan Basma ta yini tana ta bata shawara da ban bakin ta yi hakuri ta cire damuwar komai ta kula da lafiyarta. Sai da ta tabbatar da cewa ta samu natsuwa sannan ta ta fi gidanta.

Kwanaki biyu sai ga Yaya Hamida ta iso. Ta ajiye komai ta shiga kwantarwa da Bilki hankali wanda saukowar Yaya Hamida ya sanyaya zuciyarta sosai ta fara warwarewa tana cin abinci.

Sai da ya yi kwanaki hud'u a maimakon biyu da ta zo da niyyar yi sannan ta koma Kano tare da alk'awarin wani watan zata sake dawowa ta ganta.

Tun da likita ya faɗawa Bllkisu cewa idan ta dage nan da lokaci kaɗan za ta warke daga cutar da ta ke damunta. Jin haka ya sanya ta dage ta cirewa kanta dukkan wasu damuwowi da tunanika masu birkita ta, ta dage da adduar samun nutsuwar zuciya. Ta mayar da hankalinta gun shan magungunanta sosai take kula da kanta da lafiyarta. Saboda idan ta biyewa Sahal da amaryarsa ta tabbatar lokaci kaɗan ya rage mata a duniya za ta mutu saboda baƙin cikinsu da takaici, ta kuma ba shi da asarar komai tunda ga shi da ranta ma ya samu madadinta ya'yanta da danginta ne zasu yi asarar rashinta kawai. K'iri k'iri yake danne mata haƙƙin aure amma ko a jikinsa bai damu ba ganin ta zura masa ido sai hakan ya ba shi lasisin yin duk abin da ya ga dama babu fargaba.

Ya daɗe yana yi mata abubuwa a baya sai dai ta zauna ta yi kuka kuma yana zuwa mata da daɗin baki sai ta ji ta yafe masa, amma zuwa yanzu ta daina cewa ta yafe masa domin ta fahimci an kawo gab'ar da komai da saninsa yake yi sannan da son ransa yake aikatawa. Daga lokacin da ya yi auran nan zuwa yanzu ta ga baƙin d'abiu da yawa daga Sahal waɗanda ba ta taɓa saninsa da su ba, daga nan ne ta fahimci cewa ita ce kawai ya daina ra'ayi kamar ma yana zaune da ita na dole ne. Wataƙila kuma tana yi masa zaman ƴaƴansa ne, ko kuma zaman mai yi masa wahala da gidansa, tunda ta fahimci haka ta shafawa kanta lafiya game da lamarinsa da matarsa iyakarta da shi gaisuwa.

Ba ya shigowa bangarenta sai tana da girki, shima barcinsa kawai da huta gajiya yake yi. Amaryarsa kuwa sai su yi sati ba su ga juna ba wani lokacin ma sun fi haÉ—uwa a haraba gida ko ta makaranta su kan gaisa sama sama, duk addu'ar Bilki na kar a bata ajin su yarinyar nan sai da aka jona ta da su a wannan semister É—in.

Ba ƙaramin jarumta Bilki ta yi ba, da karfafa guiwar da Basma ta fara ɗaukansu, duk da tana ganin ƙawayen Hawwa suna nuna ta ana dariya bata taɓa nunawa ta gane abin da suke yi mata ba, abin da ya kai ta kawai take yi da ta gama za ta yi fitowarta, ba ta damu da maganar kowa ba, don ta riga ta gamsu sai ta cire tunanin kowa da k'arantawa kanta damuwa shine zaman lafiyar zuciyarta. Sannan kwakwalwarta ta samu hutun da ake bukata. Dan haka harkar gabanta da ya'yanta da koyarwarta ta saka a gaba. Kullum tana shan maganinta da taimakon yaranta don ko Farha kullum sai ta ce "Mahmah kin sha magani ko na dauko miki ruwa ki sha?"

Bare Amrah da kusan kullum ita take bata. Da ta sake komawa asibiti likita ya yi ta yabon kokarinta ya ce nan da lokaci kadan zai sauke ta akan magani.

Don haka sai ta rumgumi aikinta da yaranta masu sanya ta nishaɗi da farinciki sannan Alti ma tana iya bakin kokarinta. Ga ƙawar amana irin Basma duk bayan kwana biyu sai ta zo ta zauna da ita ya debe mata kewa.

Sosai aka samu cigaba a lafiyar Bilki don tana cin abinci ta warware ta fara mayar da jikinta.

Wani zuwa da Basma ta yi ta dinga yi mata tsiya.

"Hajiya Balki, ko dai Sahal ya lallaɓa ya yi wata ajiyar ne?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bilki ta fara dariya a zuciyanta ta ce yaushe rabon duniya da ayyaraye?

A fili kuma sai ta ce' Ai ni na gama, yanzu lokacin amarya ne ta yi ta zazzaga masa yara.".

Domin ta fahimci ya fi É—okin haihuwar daga bangaren amarya tun da yadda yake b'arin jiki kan cikin nan ko a lokacin da ta yi cikin Amrah ba ta ga ya yi wannan ba'rin jikin ba. A yanayin da ta ke ciki bata ma fatan ta sake haihuwa to ta ina ma ta ga mijin ballanta har ta sake samun ciki? Mutumin da yanzu sun fi wata biyu bai neme ta ba tun samuwar cikin matarsa, ranar kwanan ta ma yanzu ba ta ganewa domin a sati bai wuce sau biyu yake kwana a dakinta ba shima a tafe yake kwana haurawa sama yana duba yar gwal, asuba na yi idan ya fita ba ya sake dawowa. Gabadaya ta rasa ma ina tsarin gidan yake kawia tana cigaba da binsa da ido ne Amma akwai ranar kin dillanci. Yana ta karakaina a kanta, haka Æ´an'uwansa ma kullun cikin zuwa gidan suke da sunan duba amarya. Haka nan itama Hawwan k'annenta biyu sun zo daga Kaduna sun fi sati sannan suka tafi, ita dai sai dai ta ga ana shiga ana fita. Wanda ya shigo wajenta su gaisa wanda bai neme ta ba, ta yi kamar bata san ma ya zo gidan ba cikin irin rayuwar da take ciki ke nan.

Shi kan shi maigidan tamkar wanda aka yi musu farraku abin kullum hauhawa yake yi, ta kuma tabbatar ba wani farraku kawai sabbin bita yake mata cikin littafin kitabur ra'asi. Dan haka bata jin zafi domin Æ´an'uwansa sun nuna rashin kulawa a kanta. Ba ta É—orawa kanta damuwarsu a zuciyarta ba. Ta tabbatar wulak'ancin Baban Amra yafi jan kaso mai yawa na ciwon damuwar da ya kamata fiye da kason damuwar abin da ya faru cikin ahalinta.

Tunda tun kafin ya yi aure yake nausa mata bak'in ciki, yanzu da ya yi aure tozarta ta yake yi ta hanyar fifita yarinyar da bata wuce ta zo a mai yi mata hidimar gida tana biyanta ba.

Ana cikin haka semister ta yi nisa har an yi gwaji, sai ga Sahal ya zo yana yi mata magana, akan darasin da ta ke daukar su Amarya. Wai ta yi musu gwajin(test )kuma ya ga ta bata karamin maki 6 a cikin 20 me take nufi da hakan?"

Ya fada yana wurga mata takardan gwajin a jikinta. Lokacin tana cikin É—akinta tana duba wasu takardu ne na makaranta ya shigo yana yi mata wannan jawabin.

Ko É—agowa ma ba ta yi ba, ta cigaba da duba takardun hannunta. Idan shi ba adali ba ne to kar ya yi tunanin kowa ma irin sa ne, wato tunda tana matarsa ta bata maki 20/20 saboda shi, lalle Sahal ba shi da kunya to ai bai tsinana mata komai na abin arziki ba tun bayan auransa ballatana yarinyar ta ci darajarsa.

"Magana fa na ke yi miki kin yi mini banza?"

Ya fada a fusace Bilki ba ta son hayaniya shi ya sa ta dakata da abin da take yi ta dago tana kallon sa.

"Akan me ka ke magana?

Ta tambaya cikin nuna kamar ba ta gane in da ya dosa, duk bai sa ya fahimci ba ta da lokacinsa ba sai ma ya sunkuya k'asa ya dauko takardar yana nuna mata.

"Kin kyauta ke nan abin da kika yi Bilkisu?"

"Me na yi Baban Amrah?

Itama ta tare shi da sauri.

"Au ba ma kin san laifin da kika yi ba ko?"

Ya fada cikin harzuƙa.

"Ban sani ba, idan na sani ai ba zan tsaya ina tambaya ba."

Ya mika mata takardan yana fadin" Duba ki ga ni."

Ta karba ta duba sannan ta kalle shi tana fadin" Wannan kamar darasina a ina ka samu?"

Ta fada har tana bayyana mamakinta.

Baki ya saki yana kallon Bilki tana nufin ba ta san ko takardar wace ce ba?

"Duba sunan?

"Hawwa Hamza!

Bilki ta karanta a bayyane sannan ta mayar da fuskarta gare shi ta ce

"Wace ce ita? "

Ta tambaya cikin mamakin. Sahal ya yi wani sororo, wuyansa ya lamgwabe kafin ya ce" Kina nufin ba ki ma san ta ba?

"Ban gano wace ce ba, kasan daliban nawa suna da yawa ba zan iya rik'e sunan kowa ba."

Ta fada tana mik'a masa takardar hannunta amma ya kasa karɓa saboda mamakinta.

Ajiye masa ta yi a gefen gado ta d'au takardunta ta cigaba da dubawa.

"Kina nufin ba ki san sunan matata ba Bilki? Amma dai ai kinsan kin fara daukarsu darasi?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Don Allah fa?"

To ban ma taɓa lura ba, kuma ita ta fada maka ina daukarsu? Idan na shiga ajin bana tsayawa tantancesu abin da nake yi basu darasi da tabbatar da sun fahimcin darasin da kyau. Bayan haka bana sanin komai akansu illah zakwakuran cikinsu, Wanda hazakarsu ta wuce gigiggiwarsu. Bana ji itama ta dauke ni malamarta mai daraja don ban tab'a ganinta a aji ko a makaranta ta yi mini gaisuwar da zan shaida ina koyar da ita ba"

Ta fada tana kallon sa.

Kafin ta sake ce wa" Ka fada mata ta mai da hankali gaskiya, ta rage rawar kai a tsakanin kawaye if not , ba zata kai labari ba."

Sahal ya kai k'ololuwar fusata wato da gangan Bilki ta yi wannan muguntar?

"Ke nan da gangan kika kayar da ita a gwajin ko?

"Allah ya tsare ni, abin da ta rubuta shi ta samu."

Bilki ta amsa masa, a É—an zafafe domin ita kam ta gaji da wannan ihun da ya ke yi mata a saman kanta.

"Ko da ba ta ci ba ai darajata sai ki bata maki mai d'an dama Bili"

Ya fada yana wani rage murya har da fadin sunan da rabon da ya ambace ta da shi ta manta.

Ta kalle shi shekeke kafin ta ce" Ai ba na haka, duk inda na ke adalci na ke yi ba zalunci ba, bana k'arawa mutum hak'kin da ba na shi ba."

Sai jikinsa ya yi sanyi domin sai ya ji kamar shagube Bilki ta yi masa.

"To ki d'an k'ara mata ko zuwa goma ne ga ta can tana kuka."

Haushi ya kama Bilki ta mike ko magana ba ta yi masa ba ta shige tiolet ta bar shi nan da ya gaji ne da tsayuwa ya fice sai da ta ji fitarsa sannan ta fito amma ta kwana cikin mamakin Baban Amrah, da ba ya jin kunyar aikata duk abin da ya ga dama. Ban da k'arfin hali har ya zo ya same ta da wannan maganar? A a ba kuka take yi ba, ta yi na jini ma, yarinyar sam bata mayar da hankali wajen karatu kwakwalwarta ba ta ja, sannan kusan kullum sai ta ga tana nunawa mutane ita suna zundenta. Bata taɓa nuna ta gane ba bare ta tanka a bata rashin gaskiya. Shine kuma ta k'i yin karatu, sai kuma ita dan tana tsoron kada ace ta yiwa kishiyarta mugunta sai ta k'ara mata makin din da bata cancance shi ba? Wato ta turo shi ne ya yi mata dole shi kuma ba tunanin komai ya zo zai yi mata tilas. Ta dade tana mamakinsa har Basma sai da ta bawa labari da suka yi waya. Basma ta buga wani zagin Katsinawa sai da Balki ta kashe waya tana dariya. Ashe zance bai k'are ba da aka yi jarabawa ma sai da ya zo ya same ta akan ta bawa yarinya sakamako mai kyau ta ce to babu musu illah iyaka ta kud'iri ajiyar ba zata taimake ta ba, haka nan ba zata danneta ba. Ai kuwa sakamako na fitowa Hawwah ta samu F a darussa biyu ciki har da wanda Bilki take daukarsu wato pharmacology. Sannan sauran ta haye ne irin da k'yar din nan dan haka gabad'aya GDP dinta ya yi k'asa matuƙa da gaske.

Ta dinga kuka sosai tun a hanya yake rararrashinta tare da cewa yasan tana da kokari lififin cikine ya hanata hayewa dan haka ta kwantar da hankalinta yana tare da ita kuma zai yi kokari komai ya daidaita mata.

Cikin rishin kuka ta ce "Ban ci na wacce kake da iko da ita ba sai na wani ne za'a gyara mini? Ni Wallahi ka bude mata k'wanji ta gyara mini sakamakona, na gane bak'inciki take yi da ni tunda ta ga ina da ciki shike nan ta daura aniyar sai ta kai ni k'asa. Duk ajin ni da kawayena kawai ta kayar har wanda muka fi su k'ok'ari duk ta ciccibasu sun haye amma ban da ni da duk wanda nake mu'amala da su."

Suna dawowa gida kaitsaye wajen Bilki ya dira yana neman ba'asin kayar da Hawwa da ta yi.

Bilki da bata son jan maganar ta mik'e ta ce "abin da ta yi ne ta ga ni".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Rikici har wajen Hajiya, itama wai Hajiya kamar ta manta da zaman da suka yi tana goyon bayan Sahal da matarsa.

"Haba Balki abu duk na gida, ai ko don darajar Sahal kya bari ta wuce tunda kina da damar yin haka"

Mamaki ya hana ta magana sai da Hajiya ta ce wai idan ta isa da ita to ta gyarawa abokiyar zamanta jarabawarta.

"Kin ga ciki ne da ita har ya fara girma damuwa kadan zai saka a samu matsala."

Bilki ta gyara zama tana kallon Hajiya ido cikin ido kafin ta ce" Ai ba ni da wannan ikon Hajiya na riga na bawa makaranta duka sakamakon jarabawar komai na hannunsu yanzu, ita ce za ta gyara carryover É—in ta wata shekaran amma ni ba ni da wani taimakon da zan iya yi mata."

Hajiya ba kunya tafara fadin" Haka za ki ce Bilki? Ashe ba kamar uwa kika dauke ni ba?"

"Uwa kuwa mai k'ima na d'auke ki Hajiya. Amma hakan ba zai saka na ci amanar aikina ba. Ko shi Baban Amra nake koyarwa ya kin yi karatu to ba zan ba shi makin da bai cancance shi ba. Don a lahira ni kad'ai zan kwashi zunubin son zuciyata "

Hajiya ta kasa magana Balki ta gama daure ta da maganganu da haka maganata da mutu mussaman da k'anin Sahal din ya ce wa Hajiya ba maganar suna auren miji d'aya wannan daban, bangaren malama da daliba daban idan ta yi abu mai kyau za ta ga ni.

Babu adalci a tilastawa Bilki ta ci amanar aikinta, da haka zance ya k'are ba ta san yadda ya k'are da mai kuka ba. Kan dole Hawwa ta gaji ta hakura tunda ba ta samu mafit ba wato tunda suna auren miji daya bari ta kwanta a gida ta k'i karatu, tana jiran ta wuce a banza, ba mutuncinta take ga ni ba, bare ta taimaka ta cicciba ta, tana ganin yadda take hada kai da kawayenta suna gulmarta suna zundenta.

Sai da ta zo making ta tarar duk yan group din nasu basa wani ja.

Cikin Hawwa ya fito ana gani sosai, tuni ta fara zuwa awo a bakin Alti take ji domin akwai wata rana da Sahal ya sakata ta rakata shi zai kaita sai kuma aka kira shi daga wajen aiki. Ba domin Alti ba, ba ma za ta san wattanin cikin ba ta ga dai ya girma tun da har ya fara turowa a riga sosai.

Ba ruwanta da harkar da ba a saka ta ba, shi yasa ta zauna lafiya in da ta sake godewa Allah warkewarta daga cutar damuwa yanzu ba ta shan magani, sai na hawan jini kawai domin ya kamata, shi ya sa take kiyayewa sannan tana shan mgani.

Ta riga ta kama kanta da sha'anin gidan gabadaya ba ta maida kai akan wasu abubuwan, shi yasa ko wani abu ya faru a gidan sai dai ta ji a bakin yara ko bakin Alawiyya to yau ma tana dawowa daga aiki ta yi yamma a cikin makaranta. Amrah ke faÉ—a mata Abban su ya siyo su dankali da doya bai kawo musu ba duk an haura da kayan zuwa saman Anty. Dama tana son ta samu damar da zata bata labarin abin da ta jiyo kwanakin baya dan haka duk Amra sai ta had'a ta faÉ—awa uwarta abin da ta ji Anty na faÉ—awa Dady, akan batun cefane da mota da kuma super wax.

Wato yanzu shine ya yo mata cefane irin nata da take ga ni tunda garar da aka kawota da ita ta k'are.

Lamarin ya daurewa Bilki kai, har yana da kudin siyan su doya da dankali da kayan miya daga Jos shi ne ita bai taɓa yi siyo mata ba! Tunda ya yi aure ya ce kowa ta yi girkinta ba zata iya tuna abin naira biyar da Baban Amrah ya siya musu na kayan amfanin gida ba. Amma tasan ya kawo mata k'aramin buhun shinkafa da katon din taliya da man gyada 5litr, wanda cikin garar Hawwa ne. Ba zata iya tuna me ya kawo mata ba bayan wannan.

Ba ta yadda da maganar Amrah ba sai da ta tambayi Alti itama ta bata tabbacin ta ga sadda yake hawa da su har da ledar kayan tea ta ga ni.

Shi yake siyawa amaryarsa ita kuma bangarenta idan ba zata siya ba sai dai su hakura da shan tea din, shi yasa ba ta jiransa sannan ba ta tambayarsa idan tana da kudi siyan abin da take so kawai take yi.

Abin ya dame ta amma ta kud'iri niyar sai ta yi masa magana, ranar ko ya shigo d'akinta zai kwana kamar yadda ya saba sai dare ya tsala ya yo shirin barcinsa daga can yake shigo mata.

Har ya kwanta ta ce ya tashi zasu yi magana ya fara faÉ—an sai da ta ga zai kwanta sannan za ta ce za ta yi masa magana.

Ta hakurkurtar da zuciyarta ta ce "maganar ba za ta daÉ—e ba sannan fa ya tashi ya zauna.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Baban Amrah kana yin wasu abubuwa da ban gane musu a cikin gidan nan ba.'

A hassale ya ce" Kamar na me fa? "

"Kamar na yadda kake tafiyar da mu tsakanin ni da yaranka da amaryarka mu ba ka yi mana cefane, tunda ka yi aure sisi na dawainiyar abincin bangarena ba ka bani ba, duk ni ce nake yi, yanzu fa ba da ba ne Allah ya rufa maka asiri dama saboda ba ka da shi ne nake yi, na dauka yanzu za ka yi tunanin karbar ragamar da Ubangiji ya dora maka, amma sai na ga ba haka ba. Ita kana yi mata cefane ni kuma ko oho ni da yaran ka. Ai ya kama ta ka daidaita bisa adalci na yadda ko wanne magidanci yake yi. Kuma ni dai a sanina a farkon aurenmu kai adali ne ba abin da baka yi a gidanka na bajinta ma amma yanzu ka sauya mini gabadaya Baban Amrah!

Ta fada cikin taushin harshe ainun.

Kai tsaye ya ce" Kin taɓa ce mini baku da wani abu ne kika ga ban kawo ba Bilki?

Ya k'ura mata ido yana kallonta sosai.

"Ban gane ban taba fada maka ba. A matsayin ka na megida ai ya dace kasan duka hakkin da yake rataye a wuyanka. Ba bukatar a tunasar da kai."

Ta fada kaitsaye don ta fara harzuk'a.

Ya jinjina kai kafin ya ce" To ai ganin ba kya magana shi ya sanya na dauka kina da komai ne. Hawwa kuma tana fada mini abu kaza ya kusa k'arewa tun ma kafin ya k'are shi yasa kika ga ina siya mata, ke ma idan kin koyi yin hakan zan siya miki ai hakan ba matsala ba ne "

Baki bude Bilki take kallonsa kafin ta samu zarafin magana ya cigaba da fadin" Duk abubuwan da kike yi ke kika saka kan ki. Ni ban tab'a rokon ki alfarmar ki yi ba, saboda haka ba ki da ikon magana. Ko lokacin da ba ni da aiki, ke da kanki kika kika fara abubuwa kan ki tsaye ban roke ki ba, bayan na samu aiki na ga kin cigaba daga inda kika tsaya, kin ga ita ta tasan nine zan bata don bata da sana'ar da zata nuna mini bata buk'atar hidimata sannan ba ma'aikaciyar gwamnati ba ce. Ke kuwa fa?"

Kalamansa sun daki Bilki k'warai da gaske ta kasa magana saboda mamaki.

"So kar ki zargi kowa a kan wannan abun. Ki fara tuhumar kan ki."

Daga haka ya juya ya yi kwanciyarsa ya bar ta, tana binsa da kallon mamaki da tu'ajjibi.

Wato shi Sahal ya mayar da ita wata shashasha, kidahuma kuma sakarya, ba ta sani ba.

Sake kiran sunan shi ta yi yana daga kwancen ya katse ta da fadin" iya gaskiyata na fada miki. Ki bar ni na yi barci don Allah."

Hawaye suka kawo mata amma ba ta barsu sun zuba ba. Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Shi ke nan na gode. Zan gyara a gaba."

"Better."

Ya amsa mata yana daga kwance, ranar kwana ta yi cikin takaici kuma tun daga ranar ta ce an yi an gama daidai da ruwan sha idan babu ba zata sake saka ko sisinta a cikin cefanen gidansa ba.

Ko sati ba a yi ba indomie É—in yara da kwai tare da lemun da suke tafiya makaranta suka rage sauara na kwanaki biyu su k'are. Tunda ya ce ba a sanar da shi, shiyasa baya siya. Sai ta fad'a masa ranar da ya waye a wajenta da safe, yana karyawa.

"Ki ranta cikin kudinki, a siyo komai, zan ba ki anan gaba. Yanzu duka kudaden hannuna na bawa Hawwa zata fara rage siyayyar haihuwa tunda ana saka rai karshen next month ne haihuwar ".

Bilki ta saki baki tana kallonsa saboda yanzu Sahal ya daina bata mamaki al ajabi da tsoro yake bata.

"Ban gane ba?"

"Yadda dai kika ji?"

"Ban gane ka bata ta yi siyayyar kayan haihuwa ba! Haihuwar yau ne ko gobe? Saboda haka so kake yi mu zauna da yunwa saboda hidimar haihuwa?"

Bilki ta tambaye shi cikin karaya da lamari.

Daga faÉ—in haka ya juyo a fusace kamar zai kai mata mari.

"Dakata Bilki ni fa na gaji da hallayarki a cikin gidan nan tunda kika ga na yi auren nan bakincikinki da hassadarki suka taso a kaina. Na fada miki gaskiyata ko so kike yi na zauna har sai an yi haihuwar sannan zan tanadi abin da ya kamata! Idan kina da adalci ai kema haka nake yi miki, amma saboda son zuciya har kina da bakin magana"

Bilki ta saki baki da hanci amma ta kasa magana.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Kin ce abu ya kare na ce ki ranta, ki siya zan baki shima duk bai yi miki ba, kina so ki tsiro da wata magana. Ina ce da ke kike siya? Me ya sa duk ba ki damu ba sai yanzu da aka kawo wata? Ki kiyaye ni kar ki kure ni na gaji da korafinki fa".

Yana gama faÉ—in haka ya wuce fauu ya sauka kasa, ya bar Balki da ciwon zuciya da kyar ta iya rarrafawa ta sauko ta koma dakinta sai da ta yi kuka. Idan ta ce ba ta gaji da Sahalu da gidansa ba ta yi karya.

Ta gaji tana bukatar natsuwar zuciya da na gangar jiki.

Amma matukar tana gidan nan to ba za ta samu haka ba.

Yini ta yi ranta a bace, ba ta da shiga makaranta kwance ta yini tana tunanin rayuwarta da ba komai cikinta sai bacin rai da takaici, ba ta dauka a daran Baban Amrah zai neme ta ba, tunda yadda suka rabu da safe sai ga shi ya zo yana rage mata murya.

Shi kan shi bayan fitarsa da safe yana tafe a mota sai ya ji duk bai kyauta ba, bai kamata ya fadawa Bilki maganganu masu zafi haka ba, shi yasa yana dawowa ya sauka a wajenta yana ta Haba haba da ita, yara ma har kallo ya yi da su sai jan su da hira yake yi.

Sai da daddare sun kwanta ya tausasa harshe yafara lallashintaa.

"Bili ni fa na dauka mun wuce wannan k'adamin a tsakaninmu. Na dauka ni da ke mun zama d'aya . Abin da yake tayar mini da hankali na kasa nutsuwa da ke tunda kika yi mini gori akan kudin da nake cira a asusunki na fara baya dake, ba ki fa da tabbacin budurwa na ke kashewa kudin, a lokacin ma Hajiya ce ba ta da lafiya, amma kika rufe ido kika yi mini gori, shiyasa nake jin zafinki gaskiya tare da tsoron ki. Bana son gori nan duniya Bili ba wata macen da zan aura da zata fiki, ke ce farkona fa, me ya sa zan manta da mafari? Hausawa suka ce da tsohuwar zuma ake magani. Ke din rufin asirince, mai sonace da gaske, ki yi hakuri ki huce kada ki ga dan muna ta samun sabani wai bana sonki ko an sha gabanki ne a zuciyata. Lah har abada ke ta daban ce, ina tuna yadda kika k'i manyan mutane da suke sonki kika zabe ni duk da k'uruciyata da kuma rashin abin yi na. Ki yi hakuri da ni dan Allah!

Tun Bilki na janyewa har ta saki jiki da zuciya ta karbi lallashinsa abin mamaki, tsawon lokaci suka yi suna raya daren a karo na farko bayan tsawon shekaru ta samu gamsuwar da ke bukata a wajensa shi ya sa ta tashi cikin farinciki da sukuni duk da shaidan sai ayyana mata yake yi albarkacin amarya ta samu don kuwa kafin wannan had'uwar bai taba yin jarumta akanta irin haka ba. Ke nan ya yi riveving kansa don ya dinga gamsar da amaryarsa.

Tasan haka ne amma ta kore wannan zaton ta dinga addu'a da fatan karshen matsalarta ne ta zo.

Da safe ya lallabe ta da daÉ—in bakinsa.

"Bili ki siya duk abin da babu, ki rika rubutawa ni nasan abin da nake yi. Ki k'ara hakuri da ni idan Hawwa ta haihu komai zai sauya. Tunda ba batun hidimar haihuwa."

Dama ai ta saba shi yasa bata damu ba ta ce masa to a ranar kuma ta shiga kasuwa ita da Alti ta siyo duk abin da ya kamata ba ta sake bin ta kan Baban Amrah ba tun da ko da yaushe hakuri yake bata akan cewa yana sane da abin da take yi. Sannan yanzu kam ba ya yarda ya wuce sati bai take ta ba tunda ya fahimci idan ya mata wannan harkar yana saurin dankwafe borinta.

Bayan an yi haka ya wuce sai kuma ya tsiro da wani abu. A da iya makaranta yake kai amarya da daukota. Yanzu kuma duk inda zata je sai ya bar komai ya kai ta sannan ya jirata ko ya koma ya daukota.

Yana kafa kafa da ita, kamar yar gwal Balki ta ga shiga hakkin ya yi yawa ita take fama da dawaniyar kai yara makaranta ko da ba da safe zata shiga makaranta ba. Haka nan kullum ita take kwasosu.

Sai ta ce masa ya dinga kai yara makaranta da safe, duk da tana da mota, fitar na safe ne matsalarta.

Amma Baban Amrah ya kafe ya tsare akan cewa ba shi da lokaci sai dai ita ta cigaba da kai su, Bilki kuwa ta ga abin na shi ba adalci. Yana da lokacin kai matarsa duk inda zata bayan makaranta amma ba shi da lokacin kai yaransa makaranta.

Itama ta kafe ta ce ba za ta dinga kai su ba.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "To Alawiyya ta dinga kai su a cikin napep."

Ya fad'a da ya ga sun yi kwanaki biyu basu je ba.

Bilki ta ce sai dai ka ba da kudin drop na wata amma Alawiyya ba za ta dinga wannan wahalar ba tunda da zata d'auke ta ban fad'a kai yara da daukosu na cikin ayyukanta ba"

Kai tsaye ya ce" Ki dauki mai Napep din ba ni da wannan halin."

Bak'inciki ya kama Bilki ta kasa magana kuma abin da ya fada ya tabbata ba ya kai su makaranta. Sai da ta ga fushin ba zai haifar mata da d'a mai ido kan yaranta ba ta sauko ta dawo tana kai su, ko tana cikin makaranta ne idan suka tashi za ta je ta dauka.

Ta so ta hada shi da Hajiya sai kuma ta fasa kamar za ta kauda kai amma ta ji ta kasa rashin adalci kiri kiri fa yake nuna mata, ya koma direban amaryansa amma ya'yansa ba zai musu ba, ita bata damu ya mata ba ma, amma ya yiwa ya'yansa mana.

Wani dare suna kwance ta sassauta murya cikin tausasawa ta fara yi masa magana amma ya taso da fada wai ita ba ya'yanta ba ne? Da sai ta jira ya yi musu abu, da ba ke kike kai sun ba? Me ya sa yanzu za ki fito da tsirfa?

Aikin da na amince ki yi ba alfarma na yi miki ba? Ai ba duk namijine zai yarda iyalinsa kullum tana sintiri a waje ba. Ya ya hakane za ki dinga fitina ta?".

"Saboda na ga alaman kai ba ka da adalci, kai azzalumi ne Sahal "

Ta ba shi amsa kaitsaye.

Ya mike a fusace yana nuna ta da yatsa.

"Ni kike kira Azzalumi Bilki? Dama tuni kike son faÉ—a mini wannan maganar sai yau kika samu dama"

A zafafe ta ce "Na faÉ—a kai azzalumi ne sannan ba ka da adalci. Ka san ba a gidan wahala ko babu ka dauko ni ba. Duk wata gwagwarmaya da babu a gidanka na santa na kuma koyi juriya da hakuri hadi da sadaukarwarka don na rayu da kai. Tare da yi maka kyakkwan zaton kasan alheri, zaka saka mini shi da alheri, ashe ba haka bane, ban karance ka daidai ba".

Ta kammala maganarta idanuwanta na kallon shi ido cikin ido, domin yau ta kai makura wajen shakiyancin da yake yarfa mata.

Ya tunbatsa da fushi yana ayyana lallai zai mata hukuncin da sai ta nemi shi guiwarta biyu a k'asa idanuwanta cike da k'wallar nadama tana neman afuwarsa da son ya cigaba da rik'e ta tunda bata da wajen zuwa . Wataƙila ta manta da hakan amma a yau zai ankarar da ita bubuwa masu yawa.

Ya zuba mata ido ya ce "Tabbas ban dauko ki a gidan wahalar rayuwa ba, sai dai na kwaso ki ne a gidan masu son zuciya da take umarnin Allah. Na d'auko ki ne a ahalin da suka yi shari'a da junansu akan dukiya, na dauko ki a cikin mutanan da abin duniya zai saka su k'i junansu, suka rabu dutse a hannun riga kowa na fatan Allah wadai a tsakaninsu. Ban da rabon haihuwa mai zafi mai ya kai ni wannan kasassabar, don bansan yadda zan ji ba, idan na bude ido na ga Amrah da Faruk na shari'a da gaba da juna akan abin duniya ba."

Kuka mai ciwo ya k'wace mata. Ta dinga kururuwar bak'inciki tare da fatan Allah ya sauko mata da ajalinta take yanke.

Amma duk da haka cikin jarumta ta ce "Tabbas baka yi mini karya ba kalamanka akan turba suke. Amma wataƙila baka da wayo lokacin da zuriar'ku ta haustine da guda daga cikin iyayenku maza ya yi d'ab'iar nan ta k'uda baka haram akan d'iyar wansa uwa daya uba d'aya ".

Ya muzanta ya razana ya ce "A gidan uban wa kika ji wannan batun?"

Hawaye na malala a dukkan idanuwanta ta ce "A kundin tarihin da ba zai gogu ba. Duk inda aka kai da boye shi kuwa. Dan haka mu tarihinmu iyayenmu basu yi abin kunyar da ya yi ajalin guda cikin iyayensu ba. Har abada kuma ba za'a samu irin haka ba tunda gado ne. Dan haka ka shirya zaka ga hakan a ya'yan Hawwah don ya'yantane zasu yi wannan gadon, a gidanka tarihi zai maimaita kansa, kamar yadda ka yi fatan shari'ar da aka yi a gidanmu ta maimaitu akan ya'yana."

Tashin hankalinsa ya bayyana b'aro b'aro a fuskarsa da gangar jikinsa gabad'aya. Ya zuba mata ido yana mata kallon tsana, yana ayyana tamkar ya shak'e ta ko ya yi mata dukan da zai lalata mata kyakkwar surarta, yadda ba mai kwasarta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sai dai ya tabbatar dukanta ba k'aramin bala'i zai rakitowa kansa ba domin duk yadda ya mata gorin ahalinsu sun dare sun tarwatse bata yi arahar da zai saka hannunsa a jikinta da sunan duka ya kwashe kalau a hannun ahalin nata ba. Duk tak'amarsa kuwa.

Tana da yaya kwamishinan y'an sanda (Asad) wanda tun asali yasan bai so aka ba shi aurenta ba. Tana da Usman soja ne wanda shima matsayinsa ya fara nisa a gidan soji. Tana da tantiri irin Ansari kuma mai d'amara ne. Bayan haka ga Farouk da yake da kud'i a hannunsa ya tabbatar zai kashe ko nawane akan Bilki. Haka nan tana da darajarta ta daban kasancewarta tsohuwar ma'aikaciyar kungiyar lafiya ta duniya (W.H.O) Wanda suke had'akar ayyuka da hukumar kare hak'kin d'anadam(Human rights). Bayan haka Munira babbar Lauya ce da take aiki da kotun duniya reshen k'asar da take zaune, sannan jamiar kare hak'kin ya'ya mata ce. Ga uwar iya Abida. Ga Yaya Hamida mijinta babban alkali ne a kotun shari'ar musulunci. Ga Basma yar karare da zata yi zugar da dukkan ahalinsu Bilki zasu yi masa d'aurin talala.

Dan haka a fusace cikin isgili ya ce "Don iyayenki masu son zuciya ki je na sake ki saki biyu, ba don uku tashi guda sakin jahilai ne ba, da na cike miki, shasha mai bak'ar zuciya da bakin k'ishi. Ki je, idan kin samu adalin da ya fini wanda ba azzalumi ba, sannan ba mai gadon abin kunya ba sai ki aura Hakima Bilkisu Isa Funtua!

Yana gama fad'in haka ya fita ya bar mata falon.

Ita kam sai ta ji kanta na juya mata kalaman Sahal na mata kuwwa a kunnenta har ma kwakwalwarwarta bakidaya.

"Ki je dan iyayen ki na sake ki saki biyu"

Tirk'ashi!

Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba.

Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k'addara.

Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad'a bai san abin mayarwa ba.

End of book 2

Muje ga book 3

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BVkUYEzJHcEAhYoST77vEH?mode=ems_wa_t

*Wannan littafin na kudine*

*1k via 2384876855*

*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*

*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*

# 08032773332#

# 09069067488#

*Littafi na d'aya ya zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku suke zuwa a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*DINGISHIN KWADO 3*

*BY*

*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*

*HALIN YAU*

*SABO DA KAZA*

*BAK'AR TA'ADA*

*Barar addu'arku*

*A irin wannan ranar ta 09/09/2000 Allah ya karbi rayuwar mahaifiyata*.

*Ina barar addu'arku da ku taya ni yi mata addu'o'in smaun rahamar Allah*.

*Saboda haka na saki page din a maimakon 10 ha wata da na ambata a farko*.

*Allah ya jiƙanki Mamah yasa aljannar firdaus makoma da dukkan musulmai gabad'aya*.

Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba.

Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k'addara.

Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad'a bai san abin mayarwa ba.

Duk yadda sakin nan ya yi mata wata irin mahangurba sai da ta yi jarumtar had'iyewa a gabansa.

Da murmushi ta dinga fad'in "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Ubangiji na gode da abin da ka yi mini, na gode da abin da kake yi mini. Na kuma gode da abin da zaka yi mini a gaba".

Ta kalle shi sai ta ga tamkar nadama ce ta shige shi ta farat d'aya.

Gabad'aya jikinsa ya sake ya yi tub'us.

Yayin da ita ta kasa fahimtar komai.

Ya koma ya kwanta. Tsawon lokaci tana zaune tana sauraran yadda yake barcinsa sannu a hankali ba tare da tunanin komai ba.

Ganin ta kasa barci bar biyun dare ya sanya ta yi alwallah ta fara nafila. A cikin sujjuda take kuka tana yiwa ya'yanta addu'ar Allah ya tsare mata su ya kuma k'addara musu kyakkwar rayuwa cikin imani da lafiya.

Tana zaune har asuba ba abin da take yi irin tufka da warwara. Ina zata je ne?

Sai yanzu ta fahimci girman k'alubalen da yake gabanta.

Ta dinga kuka tana yiwa iyayenta da Yaya Sulaiman addu'a.

Sai da aka fara k'iran assalatu ya farka.

Ya shiga bayi ya d'oro alwallah. Shi ma nafilar ya yi.

Sai da ya idar ya ce "Bilkisu ina ba ki shawara ki janye kalaman da kika jefe ni da su, sannan ina ba ki umarnin ki ba ni hakuri don bana son na barki ki tafi kina garari tunda dai nasan ba ki da inda za ki je".

Bak'in ciki har mak'oshinta ta ji tamkar ta danna masa ashariyoyi kala kala tsabar bak'incikin da ya taso mata.

Amma ta yi kamar ba da ita yake ba domin tana bude baki la shakka zaginsa zata yi wanda hakan kuma ba d'ab'iar mace kamila mai ilimi ba ne.

Dan haka ta yi masa bakam.

Har aka fara kiraye kirayen sallar asuba bata tanka masa ba.

Ya tafi masallaci yana fad'in "Ki yi shawara da zuciyarki kafin na dawo.

Ta bi shi da kallon mamaki wataƙila bai fahimci girman tozarcin da ya yi mata. Bai fahimci cewar da ya yi wai bata da inda zata je ma cin zarafinta ya yi ba. Ya manta da kalaman da ya yi wajen sakinta.

*Ki je dan iyayenki masu son zuciya na sake ki saki biyu"*

Zuciyarta ta buga da k'arfin gaske. Ta ke ce da kuka a bayyane domin k'arshen kaskanci da cin mutunci Sahal ya yi mata. Bayan haka bai ishe shi ba shine yanzu ya zo yana sake cin mutuncinta. Wato ga ni yake yi gidansa ne kad'ai mafakarta? Ashe shiyasa yake tuka mata tuwon wulakanci kala kala tana ta yin hak'uri da kawar da kai tare da yi masa uzziri kan uzziri. Ashe shi duk kallon bata da yadda zata yi, bata da gata yake yi mata?

Ta girgiza kai tana fad'in "Ko duk zuri'armu sun k'are ba zan sake zama k'arkashin ikon ka ba. Ko da hakan na nufin na dinga kwana a titi ne.

Bare kuma Ubangiji ya riga ya rufa mini asiri.

Kuka ta ke sosai wanda ba na zafin sakin ba ne , kuka take yi na yadda gidansu na Funtua ya zama kongo. Da ace Baba Babba na cikin gidan da ko bangarensu zata je ta bude ta zauna har zuwa ta samu nutsuwa.

Amma a yanzu fa?

Maiduguri zata tafi gidan Ansari ta zauna a hannun yarinyar matarsa ko kuwa Kano zata tafi gidan Yaya Hamida?

Gidan Yaya Hamida ai ba dolenta ba ne tunda itama a k'arkashin wani take.

"Ina zan tafi ni Bilki?"

Ta fad'a cikin rawar murya irin ta kuka.

Ta yi shiru tana tunani. Gidanta ne ya fado mata. Tana da gidaje a Katsina. Bata son ta zauna a gidanta da suka zauna domin ya yi mata girma a matsayinta na marar aure. Sannan zata so ace ba ita kad'ai zata zauna ba. Take ta tuno da d'aya gidanta mai hawa biyu wanda akwai y'an haya a k'asa, saman ne babu kowa watanni uku da suka shud'e aka yiwa wanda yake ciki sauyin wajen aiki zuwa jihar Jigawa. Shine iyalinsa basu tashi ba sai sati biyu da suka shud'e. Wanccan satin ta je ta ga gidan ta saka a gyara a yi sabon fenti don idan za'a sake karɓa a bata kudi da daraja.

Take ta lalubo lambar wanda yake kula da gidajen. Ya dauka yana fad'in "Hajiya da fatan dai lafiya?"

Murya ba amo ta ce "Zan tambaye ka ne an kammala aikin gidan nan kuwa?".

Da girmamawa ya ce "An kammala fenti Hajiya sink din kicin ne ba'a saka ba amma na siyo sabo yanzu haka ma yana gidan."

Ta ce "To ka yi kokari a saka zuwa goman safiyar sannan a share a wanke gidan kafin zuwa azahar din yau. "

"To za'a yi hakan Hajiya da ikon Allah. "

"

Ta ajiye wayar tana jin saukin tashin hankalin da take ciki. Gidan a unguwa mai kyau yake babu hayaninya awon gwamnatine. Matsalar d'aya ce ba ruwan famfo sai dai da rijiya a harabar gidan. Zata samu almajirin da zai dinga d'ebo mata kullum.

Zata tafi da Alti da Alawiyya. Duk da auren Alawiyya wata d'aya ya rage . Nan da sati biyu ma zata tafi garinsu.

Kawai matsalar da tafi damunta makomar Amrah da Faruk ne. Ya ya zusu yi idan suka tashi Babu ita, babu Farha babu Alti ba Alawiyya?"

Ta kifa kanta a akan gado tana gunshekin kukan tausayin ya'yanta.

Bata jin zata fasa barin gidan Sahal. Amma tausayin ya'yanta yana matuk'ar tayar mata da hankali.

A haka ya dawo ya tarar da ita.

Ya zauna a gefen gadon. Ya ce "Ki daina kuka Bilkisu. Ni kaina haka nake jin jikina babu k'wari. Amma maganganunki sun mini ciwo sun tayar mini da hankali. Ki janyesu, ki yi tuba shike nan sai na mayar da ke ki cigaba da zama a d'akinki.".

Ta zuba masa ido hawaye yana ambaliya. Ta ce "A a Sahal ai zama a tsakaninmu ya riga ya k'are, tunda na fahimci baka sona, baka bukatata nake ta faÉ—awa Allah ya kawo mana mafita a tsakaninmu. Ka san ai ban yi shekarun da zan ce bana buk'atar namiji ba. Kai ka samu mafita, ka samu wata ni ce ban samu ba. Da haka kuma ya faru na yi imanin nima tawa mafitar ce ta zo".

Da iyakacin gaskiyarsa ya ce "Wallahi Bilki ina son ki. Har yanzu bana jin Hawwah irin yadda nake jin ki a zuciyata. Amma ban san meyasa bana jin sha'awar ki ba. Na dade ina zargin ko saka hannune don ina jin sha'awar matayen da ba su kai ki komai na cikar halitta ba. Amma watan jiya da na ji karatun Shaikh Ibrahim Khalil da yake bada tabbacin ana cirewa namiji sha'awar matarsa ko da kuwa yana sonta. Ganin ina cikin wannan matsalar ya saka na dinga nazarin to ai ni da ke bamu yi irin wannan shekarun da zamu kai ga wannan bigiren ba. Bayan haka na gasgata ina da rauni a wannan fagen sabanin ke da kike da k'arfi bukatar al'amarin. Sai na ji tamkar na ba ki dama ki je ki yi aurenki, amma sai na ji gara mutuwa ta riske ni kafin na ga kin zama matar wani. Amma jiya sai da kika yi mini cin mutuncin da ya zame mini dole na sallama ki".

Na goge hawayen na ce "Zaman ne ya k'are."

"Yanzu Bilki ba za ki karbi shawarar da na ba ki, akan ki janye kalaman da kika yab'a mini ba? Ba za ki bi umarnina ki ba ni hakuri ba?"

Ya fad'a a zabure.

Cikin nutsuwa ta ce "Ai duk duniyar nan ba mai sakawa na baka hak'uri Sahal. Don ban yi lalacewar da za'a zagi iyayena yayin da za'a sake ni sannan na bada hakuri ba. "

Ya mike yana fad'in"Girman kai ba na ki bane ina jiye miki ragaita duk kasaitaacciyar mace za'a same ta ne a gidan mijinta ko na iyayenta ko na d'anta ko kuma na y'anuwanta shakikai".

Bata kula shi ba don bata da abin fad'a kuma.

Ya sake zama ya sassauta ya ce "kin yi nazarin ya ya rayuwar ya'yanki zata zama idan nabu ke a kusa da su?"

Rauni irin na uwa ya shige ta nan da nan, amma ta shanye ta ce "Idan na mutu ya ya zasu yi ne? Kuma a gidan ubansu zan barsu, don ba zai yiyu da gatansu na tafi da su muna ragaita a titi ba. Ni dai da ba ni da gata zan tafi, ko barance na yi".

Ya yi shiru da alamu ya gane magana ta cab'a masa.

Ta numfasa ta ce"Duk irin musgunawar da ka yi mini na yafe maka darajar ya'yanka. Wannan gidan da aka gina shi da dukiyata Allah ne shaidar na bar maka halak malak, na yafe maka. Amma dan Allah ko ban ci arzikin komai ba a gunka ka dubi Allah ka rike y'ay'anka da amana da tausayawa, na barsu a hannun Allah na barsu a hannunka."

Daga haka kuka na sosai ya k'wace mata.

Ya kamu da ciwon tausayinta ainun, a sanyaye ya ce "Bilki ki zauna na mayar da ke".

Ta kuwa yi wata irin zabura ta mik'e tare da fad'in"Wannan kuwa shine gangan Sahal!

" Ina yi maka rantsuwa da Ubangijin al'arshi zama ni da kai ya k'are ila yaumil k'iyama. Ka mayar da ni, na kuma maidu a fuskar shari'a sai dai tunda shari'ar ta ba ni damar idan ina cutuwa na bijire. To ba zan zauna ba. Aure ya haramta a tsakaninmu tunda ka yi gigin mayar da ni dan kuwa a yanzu ba sai anjima ba sai ka sake ni ".

Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi ya ce "Idan ba za ki zauna saboda ni ba, to ki zauna ki reni ya'yanki".

A zafafe ta ce"Ba zan zauna ba. Na barwa Allah amanarsu, na barsu a hannun ubansu. Zan je na nemi wanda zai mini adalci, wanda ba zai ga tsufana ba, ba wanda zai ga son zuciyar iyayena ba, wanda zai kashe mini k'ishin da nake fama da shi tsawon lokaci."

Kishi mai tsananin gaske ya shak'e shi, har kan harshensa yake jin d'aci.

Ya ce "Yanzu so kike na furta miki na ukun a zo a jarrabe mu Bili?"

Ta ce "Ba wata jarabawar da zamu shiga ai an gama, ina binka a hankali ne saboda alfarmar da Ubangiji ya baka a kaina amma Wallahi komai zai iya faruwa a tsakaninmu idan ka kafe!

Ta fad'a cikin tashin hankali da matsanancin fishi.

Ganin zai fita ya sanya ta yi maza ta wuce shi ta rufe k'ofar d'akin. Ta sunkuya ta ja plate din da ta ci tufa a daren jiya. Y'ar karamar wuka ta dauko mai tsini da kaifi ta ce "Ka sake ni ko ka mini sanadin da zan rasa rayuwata gabad'aya don da na zauna da kai gara na kashe kaina na huta da azabar da kake gana mini da raina!

Ganin gabadaya ta rikice kuma iyakacin gaskiyarta yake ga ni har cikin kwayar idanuwanta ya sanya ya ce "Na sake ki Bilki! Allah ya yi miki musayen alheri".

Ya zauna don sai ya ji jiri na katantanwa da shi.

Dukkansu kuka suke yi irin kukan nan mai taɓa zuciya, kukan kaico, kukan da ake jin an tsinci kai ba a yanayin da ake so ba.

Shi ya yi jarumtar ce wa "To ki yi zamanki a nan Bilki. Na amince ba zan zo wajen ki ba, kinsan nasan dokokin Ubangiji ina kokarin kùma kiyaye su."

Ta girgiza kai ta ce daga yau zuwa gobe zan tafi ba zan zauna ba Sahal. Kuma Wallahi har zuciyata na yafe maka duk irin musgunawar da ka yi mini. Duk hakkina da ka danne mini a zamanmu Ubangiji ne shaidar na yafe maka, bana fatan sakayya ta dawo maka ko ta sauka akan Amrah."

Ya ce "Na gode, na gode Allah ya hana ki kuka Bilki. Amma dan Allah zan roke ki arzikin abu d'aya tak. Ki bar Farha a tare da yaran nan, zan rike ta amana."

Ba ja in ja ta ce "Ka roki abin da ba zan iya yi maka ba. Mutuwa kad'ai zata raba ni da ita, ko uwarta da ubanta a yanzu basu isa su ce na basu ita ba. Bare kuma ace na bada ita a inda ba dolenta ba. Na dai yi maka alk'awarin zata dinga zuwa hutu wajen y'anuwanta ba kuma kowanne hutun ba. Duk inda rayuwa zata wulla ni to zata wulla ni ne tare da ita, itace kad'ai abin da na mallaka da ba wanda zai mini iko ko ya yi mini gayya da ita."

Ta fad'a hawayen tausayin ya'yanta na zuba. Don a yanzu sune damuwarta. Yadda zasu shigo su ga babu ita, babu Farha babu su Alti sai su kad'ai yana matuƙar d'aga mata hankali.

Ya share hawayen idonsa ya ce "Ki yi hakuri, in sha Allah zan iya k'ok'arina akansu sai dai ai ba kamar suna tare da ke ba.

Ya mike tsaye ya ce "Ni fa ji nake yi idan har na bar ki kika tafi ni kuma na zauna da wata matar a wannan gidan na yi zalunci."

Ta zuba masa ido ta ce "katon zalunci ma kuwa Sahal. Ai ko sakina da ka yi cikin izgilin ba ni da inda zan je ma zalunci ka yi. Shiyasa ni kuma na haramtawa kaina zama da kai. Amma kuma Wallahi tunda aure ya k'are a tsakaninmu har abada, to na yafe maka dukkan kuskuren da ka yi mini har zuciyata in sha Allah ba zaka tashi da haƙƙina ba. Ni kuma Allah ya mini sakayyar alheri albarkacin hakuri da afuwar da na yi maka".

Ya rasa me zai ce mata amma har cikin zuciyarsa yasan bai taɓa cin karo da mutum a duniya mai karamci da hakurin Bilki ba. Ya yi asara ba kad'an ba. Sai dai ya yi murna da ya bata dama don ta nemi farincikinta a gaba don idan ba haka ba, hak'kinta kad'ai ya ishe shi zunubin da zai hana shi kwanciya cikin salama.

Ya tausasa harshe ya ce "Allah ya yi miki alheri da kansa Bilina na gode Allah ya had'amu da alheri ya shirya mana zuri'armu da ya bamu".

A hankali ta ce "Ameen.

Daga haka ta tashi ta bude masa kofar ya fice a rikice.

Sai da ya yara suka tafi makaranta ta k'ira Alti d'aki ta fad'a mata halin da take ciki. Suka yi kukansu suka more don Altin ma da take bata hak'uri a yau kukan ta taya Bilki sosai.

Da k'yar suka hak'ura.

Alti da Alawiyya suka fara had'a mata kayan sawarta. Kafin Yara du dawo sun gama had'a wadanda zasu iya.

Sai da daddare ta zauna da ya'yanta cikin hikima ta fad'a musu gobe ko jibi zata koma gidanta amma su zasu zauna a gidansu ne.

Amrah ta ce "Mamah kun rabu ne?"

Ba boye boye ta ce "Aurenmu ne ya k'are amma tunda muna da ku ai bamu rabu ba".

Hawaye ya k'wacewa yarinyar. Yayin da Farha da Farouk suka yi tsamo tsamo.

Ta yi jarumtar rarrashin Amrah da fad'in kina babba kina kuka su kuma su yi ya ya ke nan?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *DINGISHIN KWADO 3*

*BY*

*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*

*HALIN YAU*

*SABO DA KAZA*

*BAK'AR TA'ADA*

*Barar addu'arku*

*A irin wannan ranar ta 09/09/2000 Allah ya karbi rayuwar mahaifiyata*.

*Ina barar addu'arku da ku taya ni yi mata addu'o'in smaun rahamar Allah*.

*Saboda haka na saki page din a maimakon 10 ha wata da na ambata a farko*.

*Allah ya jiƙanki Mamah yasa aljannar firdaus makoma da dukkan musulmai gabad'aya*.

Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba.

Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k'addara.

Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad'a bai san abin mayarwa ba.

Duk yadda sakin nan ya yi mata wata irin mahangurba sai da ta yi jarumtar had'iyewa a gabansa.

Da murmushi ta dinga fad'in "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Ubangiji na gode da abin da ka yi mini, na gode da abin da kake yi mini. Na kuma gode da abin da zaka yi mini a gaba".

Ta kalle shi sai ta ga tamkar nadama ce ta shige shi ta farat d'aya.

Gabad'aya jikinsa ya sake ya yi tub'us.

Yayin da ita ta kasa fahimtar komai.

Ya koma ya kwanta. Tsawon lokaci tana zaune tana sauraran yadda yake barcinsa sannu a hankali ba tare da tunanin komai ba.

Ganin ta kasa barci bar biyun dare ya sanya ta yi alwallah ta fara nafila. A cikin sujjuda take kuka tana yiwa ya'yanta addu'ar Allah ya tsare mata su ya kuma k'addara musu kyakkwar rayuwa cikin imani da lafiya.

Tana zaune har asuba ba abin da take yi irin tufka da warwara. Ina zata je ne?

Sai yanzu ta fahimci girman k'alubalen da yake gabanta.

Ta dinga kuka tana yiwa iyayenta da Yaya Sulaiman addu'a.

Sai da aka fara k'iran assalatu ya farka.

Ya shiga bayi ya d'oro alwallah. Shi ma nafilar ya yi.

Sai da ya idar ya ce "Bilkisu ina ba ki shawara ki janye kalaman da kika jefe ni da su, sannan ina ba ki umarnin ki ba ni hakuri don bana son na barki ki tafi kina garari tunda dai nasan ba ki da inda za ki je".

Bak'in ciki har mak'oshinta ta ji tamkar ta danna masa ashariyoyi kala kala tsabar bak'incikin da ya taso mata.

Amma ta yi kamar ba da ita yake ba domin tana bude baki la shakka zaginsa zata yi wanda hakan kuma ba d'ab'iar mace kamila mai ilimi ba ne.

Dan haka ta yi masa bakam.

Har aka fara kiraye kirayen sallar asuba bata tanka masa ba.

Ya tafi masallaci yana fad'in "Ki yi shawara da zuciyarki kafin na dawo.

Ta bi shi da kallon mamaki wataƙila bai fahimci girman tozarcin da ya yi mata. Bai fahimci cewar da ya yi wai bata da inda zata je ma cin zarafinta ya yi ba. Ya manta da kalaman da ya yi wajen sakinta.

*Ki je dan iyayenki masu son zuciya na sake ki saki biyu"*

Zuciyarta ta buga da k'arfin gaske. Ta ke ce da kuka a bayyane domin k'arshen kaskanci da cin mutunci Sahal ya yi mata. Bayan haka bai ishe shi ba shine yanzu ya zo yana sake cin mutuncinta. Wato ga ni yake yi gidansa ne kad'ai mafakarta? Ashe shiyasa yake tuka mata tuwon wulakanci kala kala tana ta yin hak'uri da kawar da kai tare da yi masa uzziri kan uzziri. Ashe shi duk kallon bata da yadda zata yi, bata da gata yake yi mata?

Ta girgiza kai tana fad'in "Ko duk zuri'armu sun k'are ba zan sake zama k'arkashin ikon ka ba. Ko da hakan na nufin na dinga kwana a titi ne.

Bare kuma Ubangiji ya riga ya rufa mini asiri.

Kuka ta ke sosai wanda ba na zafin sakin ba ne , kuka take yi na yadda gidansu na Funtua ya zama kongo. Da ace Baba Babba na cikin gidan da ko bangarensu zata je ta bude ta zauna har zuwa ta samu nutsuwa.

Amma a yanzu fa?

Maiduguri zata tafi gidan Ansari ta zauna a hannun yarinyar matarsa ko kuwa Kano zata tafi gidan Yaya Hamida?

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Gidan Yaya Hamida ai ba dolenta ba ne tunda itama a k'arkashin wani take.

"Ina zan tafi ni Bilki?"

Ta fad'a cikin rawar murya irin ta kuka.

Ta yi shiru tana tunani. Gidanta ne ya fado mata. Tana da gidaje a Katsina. Bata son ta zauna a gidanta da suka zauna domin ya yi mata girma a matsayinta na marar aure. Sannan zata so ace ba ita kad'ai zata zauna ba. Take ta tuno da d'aya gidanta mai hawa biyu wanda akwai y'an haya a k'asa, saman ne babu kowa watanni uku da suka shud'e aka yiwa wanda yake ciki sauyin wajen aiki zuwa jihar Jigawa. Shine iyalinsa basu tashi ba sai sati biyu da suka shud'e. Wanccan satin ta je ta ga gidan ta saka a gyara a yi sabon fenti don idan za'a sake karɓa a bata kudi da daraja.

Take ta lalubo lambar wanda yake kula da gidajen. Ya dauka yana fad'in "Hajiya da fatan dai lafiya?"

Murya ba amo ta ce "Zan tambaye ka ne an kammala aikin gidan nan kuwa?".

Da girmamawa ya ce "An kammala fenti Hajiya sink din kicin ne ba'a saka ba amma na siyo sabo yanzu haka ma yana gidan."

Ta ce "To ka yi kokari a saka zuwa goman safiyar sannan a share a wanke gidan kafin zuwa azahar din yau. "

"To za'a yi hakan Hajiya da ikon Allah. "

"

Ta ajiye wayar tana jin saukin tashin hankalin da take ciki. Gidan a unguwa mai kyau yake babu hayaninya awon gwamnatine. Matsalar d'aya ce ba ruwan famfo sai dai da rijiya a harabar gidan. Zata samu almajirin da zai dinga d'ebo mata kullum.

Zata tafi da Alti da Alawiyya. Duk da auren Alawiyya wata d'aya ya rage . Nan da sati biyu ma zata tafi garinsu.

Kawai matsalar da tafi damunta makomar Amrah da Faruk ne. Ya ya zusu yi idan suka tashi Babu ita, babu Farha babu Alti ba Alawiyya?"

Ta kifa kanta a akan gado tana gunshekin kukan tausayin ya'yanta.

Bata jin zata fasa barin gidan Sahal. Amma tausayin ya'yanta yana matuk'ar tayar mata da hankali.

A haka ya dawo ya tarar da ita.

Ya zauna a gefen gadon. Ya ce "Ki daina kuka Bilkisu. Ni kaina haka nake jin jikina babu k'wari. Amma maganganunki sun mini ciwo sun tayar mini da hankali. Ki janyesu, ki yi tuba shike nan sai na mayar da ke ki cigaba da zama a d'akinki.".

Ta zuba masa ido hawaye yana ambaliya. Ta ce "A a Sahal ai zama a tsakaninmu ya riga ya k'are, tunda na fahimci baka sona, baka bukatata nake ta faÉ—awa Allah ya kawo mana mafita a tsakaninmu. Ka san ai ban yi shekarun da zan ce bana buk'atar namiji ba. Kai ka samu mafita, ka samu wata ni ce ban samu ba. Da haka kuma ya faru na yi imanin nima tawa mafitar ce ta zo".

Da iyakacin gaskiyarsa ya ce "Wallahi Bilki ina son ki. Har yanzu bana jin Hawwah irin yadda nake jin ki a zuciyata. Amma ban san meyasa bana jin sha'awar ki ba. Na dade ina zargin ko saka hannune don ina jin sha'awar matayen da ba su kai ki komai na cikar halitta ba. Amma watan jiya da na ji karatun Shaikh Ibrahim Khalil da yake bada tabbacin ana cirewa namiji sha'awar matarsa ko da kuwa yana sonta. Ganin ina cikin wannan matsalar ya saka na dinga nazarin to ai ni da ke bamu yi irin wannan shekarun da zamu kai ga wannan bigiren ba. Bayan haka na gasgata ina da rauni a wannan fagen sabanin ke da kike da k'arfi bukatar al'amarin. Sai na ji tamkar na ba ki dama ki je ki yi aurenki, amma sai na ji gara mutuwa ta riske ni kafin na ga kin zama matar wani. Amma jiya sai da kika yi mini cin mutuncin da ya zame mini dole na sallama ki".

Na goge hawayen na ce "Zaman ne ya k'are."

"Yanzu Bilki ba za ki karbi shawarar da na ba ki, akan ki janye kalaman da kika yab'a mini ba? Ba za ki bi umarnina ki ba ni hakuri ba?"

Ya fad'a a zabure.

Cikin nutsuwa ta ce "Ai duk duniyar nan ba mai sakawa na baka hak'uri Sahal. Don ban yi lalacewar da za'a zagi iyayena yayin da za'a sake ni sannan na bada hakuri ba. "

Ya mike yana fad'in"Girman kai ba na ki bane ina jiye miki ragaita duk kasaitaacciyar mace za'a same ta ne a gidan mijinta ko na iyayenta ko na d'anta ko kuma na y'anuwanta shakikai".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bata kula shi ba don bata da abin fad'a kuma.

Ya sake zama ya sassauta ya ce "kin yi nazarin ya ya rayuwar ya'yanki zata zama idan nabu ke a kusa da su?"

Rauni irin na uwa ya shige ta nan da nan, amma ta shanye ta ce "Idan na mutu ya ya zasu yi ne? Kuma a gidan ubansu zan barsu, don ba zai yiyu da gatansu na tafi da su muna ragaita a titi ba. Ni dai da ba ni da gata zan tafi, ko barance na yi".

Ya yi shiru da alamu ya gane magana ta cab'a masa.

Ta numfasa ta ce"Duk irin musgunawar da ka yi mini na yafe maka darajar ya'yanka. Wannan gidan da aka gina shi da dukiyata Allah ne shaidar na bar maka halak malak, na yafe maka. Amma dan Allah ko ban ci arzikin komai ba a gunka ka dubi Allah ka rike y'ay'anka da amana da tausayawa, na barsu a hannun Allah na barsu a hannunka."

Daga haka kuka na sosai ya k'wace mata.

Ya kamu da ciwon tausayinta ainun, a sanyaye ya ce "Bilki ki zauna na mayar da ke".

Ta kuwa yi wata irin zabura ta mik'e tare da fad'in"Wannan kuwa shine gangan Sahal!

" Ina yi maka rantsuwa da Ubangijin al'arshi zama ni da kai ya k'are ila yaumil k'iyama. Ka mayar da ni, na kuma maidu a fuskar shari'a sai dai tunda shari'ar ta ba ni damar idan ina cutuwa na bijire. To ba zan zauna ba. Aure ya haramta a tsakaninmu tunda ka yi gigin mayar da ni dan kuwa a yanzu ba sai anjima ba sai ka sake ni ".

Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi ya ce "Idan ba za ki zauna saboda ni ba, to ki zauna ki reni ya'yanki".

A zafafe ta ce"Ba zan zauna ba. Na barwa Allah amanarsu, na barsu a hannun ubansu. Zan je na nemi wanda zai mini adalci, wanda ba zai ga tsufana ba, ba wanda zai ga son zuciyar iyayena ba, wanda zai kashe mini k'ishin da nake fama da shi tsawon lokaci."

Kishi mai tsananin gaske ya shak'e shi, har kan harshensa yake jin d'aci.

Ya ce "Yanzu so kike na furta miki na ukun a zo a jarrabe mu Bili?"

Ta ce "Ba wata jarabawar da zamu shiga ai an gama, ina binka a hankali ne saboda alfarmar da Ubangiji ya baka a kaina amma Wallahi komai zai iya faruwa a tsakaninmu idan ka kafe!

Ta fad'a cikin tashin hankali da matsanancin fishi.

Ganin zai fita ya sanya ta yi maza ta wuce shi ta rufe k'ofar d'akin. Ta sunkuya ta ja plate din da ta ci tufa a daren jiya. Y'ar karamar wuka ta dauko mai tsini da kaifi ta ce "Ka sake ni ko ka mini sanadin da zan rasa rayuwata gabad'aya don da na zauna da kai gara na kashe kaina na huta da azabar da kake gana mini da raina!

Ganin gabadaya ta rikice kuma iyakacin gaskiyarta yake ga ni har cikin kwayar idanuwanta ya sanya ya ce "Na sake ki Bilki! Allah ya yi miki musayen alheri".

Ya zauna don sai ya ji jiri na katantanwa da shi.

Dukkansu kuka suke yi irin kukan nan mai taɓa zuciya, kukan kaico, kukan da ake jin an tsinci kai ba a yanayin da ake so ba.

Shi ya yi jarumtar ce wa "To ki yi zamanki a nan Bilki. Na amince ba zan zo wajen ki ba, kinsan nasan dokokin Ubangiji ina kokarin kùma kiyaye su."

Ta girgiza kai ta ce daga yau zuwa gobe zan tafi ba zan zauna ba Sahal. Kuma Wallahi har zuciyata na yafe maka duk irin musgunawar da ka yi mini. Duk hakkina da ka danne mini a zamanmu Ubangiji ne shaidar na yafe maka, bana fatan sakayya ta dawo maka ko ta sauka akan Amrah."

Ya ce "Na gode, na gode Allah ya hana ki kuka Bilki. Amma dan Allah zan roke ki arzikin abu d'aya tak. Ki bar Farha a tare da yaran nan, zan rike ta amana."

Ba ja in ja ta ce "Ka roki abin da ba zan iya yi maka ba. Mutuwa kad'ai zata raba ni da ita, ko uwarta da ubanta a yanzu basu isa su ce na basu ita ba. Bare kuma ace na bada ita a inda ba dolenta ba. Na dai yi maka alk'awarin zata dinga zuwa hutu wajen y'anuwanta ba kuma kowanne hutun ba. Duk inda rayuwa zata wulla ni to zata wulla ni ne tare da ita, itace kad'ai abin da na mallaka da ba wanda zai mini iko ko ya yi mini gayya da ita."

Ta fad'a hawayen tausayin ya'yanta na zuba. Don a yanzu sune damuwarta. Yadda zasu shigo su ga babu ita, babu Farha babu su Alti sai su kad'ai yana matuƙar d'aga mata hankali.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya share hawayen idonsa ya ce "Ki yi hakuri, in sha Allah zan iya k'ok'arina akansu sai dai ai ba kamar suna tare da ke ba.

Ya mike tsaye ya ce "Ni fa ji nake yi idan har na bar ki kika tafi ni kuma na zauna da wata matar a wannan gidan na yi zalunci."

Ta zuba masa ido ta ce "katon zalunci ma kuwa Sahal. Ai ko sakina da ka yi cikin izgilin ba ni da inda zan je ma zalunci ka yi. Shiyasa ni kuma na haramtawa kaina zama da kai. Amma kuma Wallahi tunda aure ya k'are a tsakaninmu har abada, to na yafe maka dukkan kuskuren da ka yi mini har zuciyata in sha Allah ba zaka tashi da haƙƙina ba. Ni kuma Allah ya mini sakayyar alheri albarkacin hakuri da afuwar da na yi maka".

Ya rasa me zai ce mata amma har cikin zuciyarsa yasan bai taɓa cin karo da mutum a duniya mai karamci da hakurin Bilki ba. Ya yi asara ba kad'an ba. Sai dai ya yi murna da ya bata dama don ta nemi farincikinta a gaba don idan ba haka ba, hak'kinta kad'ai ya ishe shi zunubin da zai hana shi kwanciya cikin salama.

Ya tausasa harshe ya ce "Allah ya yi miki alheri da kansa Bilina na gode Allah ya had'amu da alheri ya shirya mana zuri'armu da ya bamu".

A hankali ta ce "Ameen.

Daga haka ta tashi ta bude masa kofar ya fice a rikice.

Sai da ya yara suka tafi makaranta ta k'ira Alti d'aki ta fad'a mata halin da take ciki. Suka yi kukansu suka more don Altin ma da take bata hak'uri a yau kukan ta taya Bilki sosai.

Da k'yar suka hak'ura.

Alti da Alawiyya suka fara had'a mata kayan sawarta. Kafin Yara du dawo sun gama had'a wadanda zasu iya.

Sai da daddare ta zauna da ya'yanta cikin hikima ta fad'a musu gobe ko jibi zata koma gidanta amma su zasu zauna a gidansu ne.

Amrah ta ce "Mamah kun rabu ne?"

Ba boye boye ta ce "Aurenmu ne ya k'are amma tunda muna da ku ai bamu rabu ba".

Hawaye ya k'wacewa yarinyar. Yayin da Farha da Farouk suka yi tsamo tsamo.

Ta yi jarumtar rarrashin Amrah da fad'in kina babba kina kuka su kuma su yi ya ya ke nan?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Da k'yar ta shawo kanta ta nutsu ta yi shiru. Ta dinga yi musu nasiha.

Farouk ya ce "Yanzu mu kad'ai zamu zauna a nan side din Mamah?"

A tausashe ta ce "A a tare da Dady sannan Antin ma zata dawo nan din".

Ya yi shiru amma ba haka ya so ba. Can ya ce "Amma ki fad'awa Dady kada ta ce zata dinga takura mana. Sannan Mahma if possible ki bar mana Alti".

Bilki ta shanye tausayinsu ta ce "Ku zauna lafiya da Antinku, kada ku yi mata rashin kunya.

Duk abin da ta ce ku yi, to ku yi mussaman ke Amrah."

Amrah da take kuka sosai ta kasa magana.

Farouk ne ya ce "Mahma to ki bar mana Alti please ".

Sai lokacin Amra ta ce "Maimakon ka bata hak'uri ta zauna da mu sai ka ce ta bar mana Alti?"

Kaitsaye ya ce "Ba zan bata hak'uri ba. Kullum fa sai na ga ta yi kuka duk yadda bata son mu gane.

Kullum Dady ne ya kai anty school da duk inda zata je a mota. Amma when last ya dauki Mamah a motarsa ko kuma mu?Kina ganin Dady yana siyo abu a leda ya kawo side din nan? Amma kullum sai na ga ya kaiwa ta sama abu a leda. Kawai Mahma ki je inda ba za ki dinga kuka ba." Ni fa tuni na gaji kawai dan ba ni da kudin da zan siya mata gida ne. Duk ranar da na je Abuja zan faÉ—awa uncle Farouku senior ya siya mata gidan tunda uncle Sulaiman ba dawowa zai yi ba"

Wannan karon Bilki ta kasa jarumta danne kukanta. Ta fashe da kuka ainun yayin da Amra da Farha suke kukan suma amma da yake namiji tun yana k'arami zuciyarsu mai taurice Farouk bai yi kuka ba. Amma idanuwansa sun yi tsilli tsilli tabbacin yana cikin damuwa sosai.

GabaÉ—ayansu har Alti sai da kukan ya k'wace musu don kuwa duk abin da ya fad'a gaskiya ne. Sannan basu yi zaton Faruk yana ankare da komai ba.

Shi kad'ai ne idonsa babu hawaye.

A hankali ya ce "ku daina kuka ai ba mutuwa za ki yi ba. Shi kuma Dady sai ya cinye gidan ".

Da sauri Bilki ta bige masa baki tare da galla masa harara da manyan idanuwanta da suka yi ja tsabar kuka.

Ya mik'e ya fice yana gunguni. Bilki ta bishi da kallon mamaki da tsoro. Baya rikici da Hawwa shi, asalima da Amrah kawia yake fad'a a gidan. Amma yanzu kam ta ga alama idan ta tafi shine zai fi bawa mutanen gidan matsala ba Amrah ba. Ko da yake Amrah ma ba shiga shirgin Hawwah take yi ba. Kawai ita ce take ce wa Amrah ta raina ta ko ana sakawa ta yi mata rashin kunya. Amma ta lura shi Farouku laifukan ubansu ne danƙare a zuciyarsa.

Ta fara lissafin adadin shekarunsa nan da watanni uku zai cika shekaru goma sha uku. Lallai zata tafi ta bar baya da kura don yanzu shekarun balaga zai fad'a, shekarun da idan ya'ya suka farawa kaiwa sai iyayensu sun kara hak'uri da juriya akan sha'aninsu bare kuma ace suna hannun yarinyar da shekaru kawai ta basu dan shakaru biyar ne tsakaninta da Amra.

Washegari a salube yaran suka tafi makaranta.

Suna tafiya mai kula da gidajensu Bilki wanda tun ma kafin a raba a basu nasu gidajen shi yake kula da su gabad'aya. Don har na baba Babba duk shine wakilinsu.

Ya iso da masu k'atuwar motar d'iban kaya. Dama kuma tun jiya masu kunce gado sun zo sun warwaresu an jingine su, duk kayan kicin dinta masu daraja sun hadesu a kwali wasu ta sake k'arawa Alawiyy akan siyayyar da ta yi mata.

Kayan yara kuwa ba abin da ta dauka illa gadon Farha. Kuma ta bar musu duk abin da tasan zasu bukata na amfani.

Sai lokacin Hawwah ta fara ankara da gidan nasu akwai abin da yake faruwa. Gabadaya Sahal ya susuce ya rasa kuzarinsa ta yi tambayar Har ta ga ji da amsar da ya bata na babu komai.

Bilki bata bar gidan ba sai wata washegarin sassafe a dalilin bata son ta tafi akan idon ya'yanta. Duk da sun fara girma sun wuce a yi musu wanka ko wankin kashi, amma tashin hankalin da suke ciki ba kad'an ba ne. Ita Farha da aka ce da ita za'a tafi bata daina kukan a wajensu zata zauna ba.

Babban zullimin Bilki akan yaranta maganar abincinne da harkar makaranta.

Amma ba yadda zata yi, ta barsu a hannun Allah.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tare da Alti suka hau saman Hawwah. Ta karbesu ba yabo ba fallasa. Cikin mutuntawa ta ce "Hawwah zuwa na yi takanas na yi miki sallama zan tafi don Ubangiji ya k'arar da zamana a gidan nan. Bayan haka kuma na damƙa miki yara a hannunki. Na sani rikon d'an da ba naka ba akwia wahalar gaske. Sai dai idan aka yi dan Allah aka yi hak'uri za'a ci riba a gaba.

Ga yara nan ki yi hak'uri da su, ki sake ninka juriyarki idan sun miki ba daidai ba, ki gyara musu ta yadda zasu fahimce ki. Idan kuma abin yafi k'arfinki ki faÉ—awa Babansu.

Allah ya sauke ki lafiya ya ba ki hak'urin zama"

Daga haka ta mik'e tana fadin"Allah ya sadamu da alheri."

Jikin Hawwah ya yi sanyi sosia ashe abin da ya kwantar da Sahal ke nan a kwanaki biyun nan?

Ta tabe baki. A k'asan zuciyarta tana jin dad'in yadda zata mamaye gidan ita kad'ai. Don kuwa falon Bilki zata mayar da falon yin dabdala ita da jama'arta.

Tana kallo suka fice amma ta rasa kuzarin yi musu rakiya.

Yayin da Sahal yake kwance tunda ya yi sallar asuba ya koma bai tashi ba.

Ba barci yake yi ba, wani irin zazzabi ne yake nukurƙusarsa.

Bilki da kanta ta ja motar tare da Alti suka tafi ta bar Alawiyya sai an tashi zata je ta É—auko Farha sai su same su a gidanta.

Tunda suka isa gidan ta shige d'akin da aka shirya mata gadonta da kayanta.

Kwanciya ta yi, ita ba barci ba, ita ba ido biyu ba. Komai ya k'wace mata, ita da kanta bata san hak'ik'anin matsalarta ba. Amma dai tunanin ya'yanta yafi komai dagula mata lissafi.

Har yamma tana kwance mussaman da fashin salla ya same ta a safiyar nan.

Alti sau uku tana lek'o ta. Amma ganinta a kwance idanuwanta a rufe sai ta fice a zatonta barci ta samu tunda kwanaki biyu basu yi barci ba.

Sai da magariba ta kawo kai sannan Alti ta sake shiga ta ce "Mahmah kwanciyar zata yi miki yawa. Ke ba azumi ba amma tun safe ba ki saka komai a bakin ki ba."

Da k'yar Bilki ta bude idanuwanta da suka yi ja sosai ta ce"Ina Farha?"

Alti ta ce "Tana can tare da su Amrah ta k'i yarda ta biyo Alawiyya".

Murya ba amo ta ce "Dan Allah Alti ki je ki dauko mini ita komin kukanta ".

Cikin rarrashi ta ce"A a mahma rabu da ita. Ai kinsan yadda take ƙulafuncinki da kanta zata neme ki. Amrah zata kula da ita."

Kan dole Bilki ta hak'ura. Sai dai duk kokarinta na ta ci abinci hakan ya ci tura don kuwa tana yin loma d'aya ta ji komai ya cushe mata.

Kwanaki uku Bilki na cikin wannan yanayin ba cin abinci sannan kullum tana d'aki. Wanka kawai take yi. Hankalin Alti ya tashi k'warai da gaske. Ta tura Alawiyya gidan Basma akan ta taho da ita sabon gidan da suka dawo tunda Bilkin ta kashe wayoyinta gabad'aya ta adana su.

Basma bata yi jinkiri ba, don tare suka iso gidan Bilki a motarta.

Tun yammaci take gidan amma har magariba Bilki na kwance uffan bata ce ba.

Kan dole ta hak'ura ta tafi gidanta. Amma washegari kafin ta je wajen aikinta ta biyo ta d'auki Bilki da Alti kaitsaye asibiti ta kaisu ta ga likita ya rubuta Mata maganin da zata dinga barci da cin abinci don ya ce stress ne da damuwa suka yi mata k'awanya.

Akai akai Basma take zuwa sai dai kullum a sanyaye take tafiya a dalilin yanayin Bilki kullum babu cigaba sai sake cabewa.

Gabadaya yanayinta ba na lafiya ba ne amma kuma ba ta ce bata jin dad'i ko ba lafiya ba. Abin da ya damu Alti da Alawiyya yadda take kwana ta yini a kwance kuma ba cin abinci.

Ranar da suka yi kwanaki takwas su Amrah suka zo gidan. Babansu ne ya kawosu, Farha suka rako a dalilin ta fara kukan wajen Mahma zata. Sai ya taho da su gabad'aya tunda weekend ne ya barsu akan zai dawo ya dauke su da daddare.

Ganinsu cikin rashin damuwa sosia bai sanya Bilki ta ware yadda Alti ta yi tsammani ba. Don haka hankalinta ya rub'anya tashi tare da tunanin uwardakinta ta had'u da lalura basu fargaba.

Cikin kwanaki goma sha biyun da suka yi a gidanta sun yi ne cikin mawuyacin hali don al'amarin na Bilki kullum ba sauki. Idan har ta bude baki ta yi magana to kuwa Farha ce a kusa da ita. Ban da haka sai dai ta rufe idanuwanta ko ta yi k'uri tana kallon gefe d'aya. Alti da Alawiyya ba abin da suke yi sai kuka.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sannan tafi son zama ita kad'ai.

Wani zuwa da Basma ta yi juyin duniya ta yi da Bilki ta bude baki ta fadi inda ya jefa wayoyinta amma uffan bata ce musu ba sai ido kawai take binsu da shi.

Ta yi wata irin rama ta farat d'aya.

Ta birikice sosia tamkar ba Bilki sola ma'abociyar kyan fuska da zati ba.

Basma bata da lambar Abida yanzu. Ga shi bata da ta Yaya Hamida.

Ta kalli Alti ta ce "Ban Ga wayarta bare mu shaidawa wani nata halin da take ciki.

Da hanzari Alti ta ce "Ina da lambar Farouk da Saddiqa."

Nan da nan Basma ta ce "Ba ni ta Yaya Farouku ".

Alti ta mik'a mata wayarta ta ce "Duba za ki ga Faroukun Mahma".

Basma ta lalubo layin bugu biyu ya dauka ya ce "An buga an bar ki Altin Bilki".

*

Ya fadi hakan a zatonsa Alti ce.

"Ba Alti ba ce Ya Faruƙu. Basma ce kawar su Abida"

Shima da ya ke ya santa nan da nan ya gane ta suka gaisa.

Cikin hawaye Basma ta ce"Ya Faruk za ku bar Bilki ta mutu ne ba wani a kusa da ita?"

Cikin tashin hankali Ya Faruku ya ce" Subhanallahi wani abu ne yake faruwa da Bilkin?"

Basma ta karɓe da ce wa" Abubuwa da dama sun faru. Aurenta ya mutj sannan kuma tana kwance cikin mawuyacin hali ".

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Tun yaushe?"

Ya tambaye ta a sukwane .

A sanyaye Basma ta ce "kwanaki sha shida ke nan".

"Subhannallah ya furta a takaice".

Ya numfasa ya ce "Yanzu a ina take ?"

Tana gidanta na unguwar Alkali".

Ya ce "Zan zo in sha Allah. Allah ya bata lafiya."

Ta amsa da ameen a sanyaye.

Washegari wajen azahar kamar daga sama sai ga yaya Faruku a gidan Bilki. Ganinsa da Bilki ta yi ya sanya kukan da ya kafe mata tunda ta shigo gidan ya k'wace mata. Ta dinga yinsa tamkar zata hadiye zuciyarta.

Gabadaya ya rikice ya rasa kalmar da zai yi amfani da ita wajen yi mata magana.

Komai ya tsaya masa cak domin ya ganta cikin mawuyacin halin da duk dakiyar zuciyar mutum sai ta motsa.

Da ƙyar ya bude baki ya ce

"Bilkisu ki yi hak'uri, ki daina irin wannan kukan! Duk abin da ya samu bawa mukaddarine daga Allah. Bawa kuma ba ya wuce k'addararsa."

Bilki ta tsananta kukanta ainun wanda ya sake jagula zuciayar Yaya Farouku. Ya tausasa harshe ya ce "Fad'a mini damuwarki na magance miki ita Maigado"

Ta kasa ba shi amsa saboda kukan da take yi. Sai da ta numfasa don kanta.

Cikin kuka ta ce" Ba ni da matsala, ina kukane saboda jiya aka fad'a maka halin da nake ciki, amma yau ka yi asubanci ka bar komai ka taho tunda ga Abuja don ka ga halin da nake ciki. Ko na rasa komai a duniya na tabbatar ba zan rasa ka ba yaya Farouku".

Karon farko da ta bude baki ta yi maganar da bata shafi Farha ba.

Tausayinta ya yi matuk'ar kama shi, don ya fahimci ta yi amannar ta rasa duk wanda yake da muhimmanci a duniyarta. Dawowarta gidanta alamace na ta gamsu ta rasa dukkan muhimman mutane a duniyarta da zata zauna a kafaÉ—arsu. Ya sunkuyar da kansa idonsa ya cika da k'wallar alhini. A ransa yake fad'in zumuncinsu bai yi lalacewar da Bilki zata yi zaman kanta a shekarunta ko da kuwa babu Baba Babba a duniya ba.

Ya tausasa harshe ya kalle ta da kulawa sosai ya ce "da yau zan juya don ban yi zaton aurenki ya mutu ba. Amma tunda hakane zan kwana kafin su Alti su shirya miki kayanki tare da ke zan tafi".

Ba ja in ja ta ce "Na gode sosai na kuma tabbatar zaka yi mini komai a rayuwata, ban tankwabar da kokarinka ba. Amma bana son na kawo maka hargitsi a gidanka. Ka yi hak'uri duk abin da zaka yi mini, ka yi mini ina da ga nan".

Tsawon lokaci suna muhawara amma fir Bilki ta kafe ba zata bar Katsina ta gode da k'ok'arinsa.

Alti ta kyafta masa ido fahimtar hakan ya sanya ya yi shiru, yayin da Bilki ta runtse idanuwanta a zuwan barci take yi.

Daidai lokacin Alawiyya ta kawo masa abinci.

Ya zuba ya ci abinsa suna hira jefi jefi da Alti.

Ganin haka ya sanya Bilki jan bargo ta lullube jikinta har fuskarta.

Da ya kammala ya yi mata magana amma babu amsa kan dole ya hak'ura ya yi musu sallama.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Alti ta bi shi k'ofar gida ta ce "Yaya Farouku kada fa ka yi fishi da Mahma gabad'aya fa ba a hayyacinta take ba. Sannan ba zata yarda ta bar Katsina ba, ba don komai ba sai don ya'yanta."

Ya girgiza kai tare da fad'in "Ko zata mutu kuwa sai ta bar Katsina. Su mata basa tunanin komai da kowa sai ya'yansu? To idan ya'yan suka mutu suka bar ta sai ta fasa rayuwa ke nan? Ko kuwa idan ita ta mutu ya'yan suma mutuwa zasu yi?"

Alti ta yi shiru don bata da ta ce wa akan sha'anin, amma itama kam da za'a samu a raba Bilki da garin da tafi son hakan tunda zullimin da take ciki kada mijinta ya ce ya mayar da ita don bata yiwa Bilki fatan komawa hannun wannan mutumin.

Ya ce "mu je na sake yi mata sallama ko zata amsa"

Suka shiga har d'akin suka tarar har lokacin tana lullube ruf ya kaurara murya ya ce "Maigado!

Ta bude fuskarta sannan ta bude idanuwanta ta zuba su akan fuskarsa.

Ya numfasa ya ce "Zan je na bincika asibitin da ya dace Ki dinga ganin likita. Gobe da safe ki shirya da wuri zan zo na d'auke ki da Alti zuwa asibitin".

Kai ta daga masa tabbacin ta ji.

Ya numfasa ya ce "Za ki je ai ko?"

Nan ma sake gyada masa kai ta yi alamun zata je din".

Daga hakan ya ce "To na tafi sai goben".

Ta d'aga masa hannunta na dama alamun bye bye.

Ya fita a matuk'ar sanyaye don ba zai yaudari kansa ba. Bilki ta samu matsala.

Har mota Alti ta raka shi tana ta yi masa fatan alheri mai yawa.

Tunda ya tafi yake ta nazarin asibitin da zai kai Bilki.

Karshe dai ya ya make shawarar ya kaita babbaan asibitin gwamnati don yafi son kwararren likita ya ganta.

Sai yamma ya samu nutsuwa bayan abokinsa da yake pharmacist ne a cikin asibitin ya ba shi tabbacin Su zo karfe tara na safe zai had'asu da likitan da zai duba ta.

Washegari kuwa k'arfe takwas a gidan Bilki ta yi masa. Ya tarar Alti na fama da ita ta kurbi ko ruwan shayi ne amma ta k'i.

Haka ya É—ebe Su zuwa asibiti.

Basu sha wahala ba suka ga likita. Ya yi dube dubensa tare da tambayoyi wanda sau d'aya Bilkisu ta amsa Duk Alti ke ba shi amsa.

Ya kalli Farouku ya ce "Depression ne ya shige ta!

Don duk alamomin cutar sun bayyana a tare da ita. Zan d'ora ta akan magani sannan a dinga samar Mata da nutsuwa tare da yi mata abubuwan da zai É—ebe mata kewa tare da sanya nishadi."

A sanyaye Yaya Farouku ya ce"Za'a kiyaye Dr. Ya mik'a masa hannu suka yi musabaha, ya yi godiya sannan suka tafi. Mota ya bude musu suka shiga, shi kuma ya wuce ya siyo magungunan sannan ya yiwa abokinsa godiya.

Tunda suka hau titi ya tausasa harshe ya dinga yi mata nasiha da muhimmancin yarda da k'addara.

Ba zato suka ji ta ce '"Na gode sosai Yaya Faruku. Zuwan da ka yi Katsina don ni ya tabbatar mini ina da sauran gatana".

Idanuwansa suka cika da k'walla amma ya sanya jarumta bai bari sun zuba ba.

Da suka isa gidan ya ce "Maigado ki daure ki ci abinci don na tabbatar kin ji dad'in zuwana da gaske."

Ta yi k'asa da kanta.

Ya ce "A zubo miki?"

A hankali ta ce "Eh."

Da azama Alti ta zubo mata kunun gyada da ta yi mata tun dare ya zuba a flask amma bata sha ba.

Ta karba ta kafa kai ta shanye nan da nan ta mik'a mata kofin.

Dad'i ya kamasu sosai. Alti ta ce "To ke fa? Rashin cin abincin ma ai jinya ce babba."

Ya numfasa ya ce "Bilki ina son na tafi da ke Abuja kuma tare da Alti zamu tafi ta cigaba da kulawa da ke ".

Nan da nan idanuwanta suka cika da k'walla ta dinga girgiza kai tabbacin ba zata bi shi ba kenan.

Ganin zata sake rikice wa ya sanya ya ce "To Shi ke nan ki zauna a nan din amma ki dinga shan maganinki akan kari. Idan lokacin komawa asibitin ya yi zan dawo da kaina na mayar da ke".

Murya ba amo ta ce"Ubangiji ya fini yaba maka Yaya Farouku ".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Kafin tafiyarsa sai da ya tura mata kudi masu nauyi ta asusunta, kudin da suka ba ta mamaki ainun. Da za ta yi masa godiya ya bata rai tare da ce wa "Kada ki ce komai fatana ki kwantar da hankalinki, ki dinga cin abinci da magani ".

Ya yi musu sallama ya tafi yana ayyana al'amura masu yawa a kanta.

Zuwan Ya Faruku ya tafi da kaso mai yawa daga cikin damuwarta, mussaman da su Amrah suka zo sau biyu tana ganinsu ba'a yanayin tashin hankali ba. Sannan ga Basma ko da yaushe tana tare da ita, idan ba ta zo ba, za ta kira wayar Alti ta tambayi jikin Bilki.

Sahal tare da iyalinsa. Hawwa a gaban mota zai kaita asibiti awo. Yayin da Amrah da Farouk suke baya sanye cikin uniform dinsu. Dama can Amrah ita ta ke yi musu wanki a injin wanki, sai idan Farouk ya yi mata rashin kunya take ware nasa ta bar masa ya yi da kansa. Amma wankinsu ita da Farha ita take yi, ta kuma zauna ta goge musu tsab. Uwarsu da zata tafi cikin abubuwan da ta bar musu har da injin wankin. Da k'aramin firij, da k'aramin gas da kuma kettle da iron. Hatta tv sai da ta bar musu karama ta cikin d'akinta. Ta ce su dinga kallo.

Fes suke tunda mamarsu ta bar gidan basu yi fada ba. Komai Amra ta ce ya yi baya yin musu yi yake yi, sannan komai tare suke yi. Dan haka itama take yi masa komai. Babansu ya tattaro ya dawo b'angaren Bilkin, ba ya yarda ya hau saman sai idan da rana ne ko yammaci.

Hawwa ta yi fishi da b'acin rai amma bai canja ba. Ya kafe ba zai bar ya'yansa su dinga kwana su kad'ai a k'asa ba.

Kan dole ta ke biyo shi ta kwana tare da shi.

Ban da kwana komai a samanta ya ce ta dinga yi, kasa na yaransa ne.

Makarantar su Farouku ce ta fi kusa dan haka shi aka fara ajiyewa. Ya sauka Amrah ta mik'a masa lunch box d'insa tare da fad'in "Allah ya bada sa'a yayan Mahmah".

Ya karɓa yana murmushi amma bai ce 'kala ba".

Tunda babarsu ta tafi baya yiwa kowa magana sai Amrah. Idan safiya ta yi ya gaida Dady da anty to ba zai sake bude baki ya yi musu magana ba sai ta k'ure ko idan su suka yi masa. Sahal ya fahimci yadda Farouku yake kama da y'an gidansu Bilki haka ya dauko rashin warginsu. A ransa yake ganin Abida ce tafi dacewa ta zama uwarsa ba Bilki ba. Sannu a hankali yake rikidewa yana zama tamkar Sulaiman ne ya haife shi dan haka sosai suke kama da Farha.

Ya zama marar son hayaniya.

Sahal ya ce "Yaya me kika yi muku ne yau?"

A hankali ta ce "Muna da samosa da meat pie a fridge, su na soya mana. Mun karya da golden morn kuma".

Ya ce "Da kyau amma Amrah ba kwa tinawa da Dady. Kinsan yadda nake son snacks din Mahma kuma yanzu da take baku ai sai ki dinga tunawa da Babanku".

Ta dan yi gajeran murmushi tare da fad'in "Idan na dawo zan soya maka to".

"Yauwa uwata Allah ya yi miki albarka ".

Daidai lokacin suka isa makarantar su Amrah.

Ta sauka tana ce musu a dawo lafiya.

Hawwa da take zaune gaban mota ta cika ta yi fam tunda ta shigo motar uffan bai ce mata, ya'yansa kawai yake kulawa.

Tun ba'a je ko ina ba, murnarta ta fara komawa ciki bisa dalilin hankalinsa yanzu ya koma yaran sabanin lokacin da uwarsu take nan hankalinsa kacokan na kanta.

A da ita kad'ai yake É—auka a mota suna tafe yana mata hirarraki masu dadi da saukar da kunya. Haka idan zasu dawo, ya dinga tarayyarta da siya mata abubuwan ciyeciye. Amma yanzu idan ya daukosu ba abin da yake yi sai hira da yara. Sannan ya ce d'akin Bilki ya koma na Amrah. Dakinsu Amrah kuma ya rufe shi. Sannan kicin din Bilki ma yaran ne zasu dinga amafani da shi tunda uwarsu ta bar musu kayayyakin da zasu buk'ata. Dakin Farouku kuwa yana nan a nasa.

Gabadaya ya rikice yana jin hak'kin Bilki kad'ai ya isa ya damalmasa lissafi. Amma sai ta shayar da shi mamaki ta ce ta yafe masa. Shi kuwa tunda ta yi masa hakan zai yi iya k'ok'arinsa ya ga ya'yanta basu wulak'anta ba.

*

Hakan nan baya musgunawa Hawwah don har y'ar aiki ya daukar mata amma ba mai kwana ba, zuwa take yi da safe ta yi shara da moping, sai ta yi girki. Shikenan sai ta yi tafiyarta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sun ajiye Amrah ba jimawa ta ce"Yanzu dai dear baya ta tawa".

Ya ce "Ko d'aya ba wannan batun kawai ina jan yaran a jikina ne dan kada du shiga damuwa da yawa."

Ta langwabe kai ta kalle shi cikin wani irin yanayi ta ce "Ka raina yadda nake kula da su kenan?"

Ya dan yi murmushi kad'an ya ce "Ban raina ba my sweet baby".

Ta ce "Ina son mu dinga zama muna hira da su, amma Farouku sam ya bijire, ya kuma hana yayarsa ma. Da na k'irata ta hawo samana minti k'alilan zai ta k'walla mata k'ira ta zo ta ga wani abu. Shi kuwa idan har ya zo inda nake to gaisuwar safe ce bayan haka duk juyin da zan yi ina k'iransa ba zai nuna ya ji ba bare ya amsa, ya samo wata ear pies kullum yana mak'ale da ita a kunne."

Sahal ya numfasa ya ce"Kin san maza tun muna yara bamu da mu'amala irin taku ta mata. Ni kaina ai kin ga ba wani shige mini yake yi ba. Ki dage ku k'ulla abota da Amrah idan ya ga kina son yayarsa zai sauko. Sannan kada ki yarda ki nuna masa kin gane baya ra'ayinki".

Ta yi shiru tana ayyana ita kam bata ga ribar da ta ci da Bilki ta bar mata gida ba. Mijin hankalinsa yanzu yafi karkata kan ya'yanta. Sannan gidan da take ganin zata mamaye shi ita kad'ai ya ce "Na ya'yansa ne. Bata da alak'a da k'asan idan ba kwanciya barci ba, tunda a d'akinsa na wajen Bilkin suke kwana bisa dalilin ya'yansa yara ne ba za su kwana su kad'ai ba".

Gabadaya yanayinta ya fara sauyawa don da uwarsu ta na nan baya wannan kaffa kaffar da su. A ranta tana ayyana bari ta haihu ba zata yarda da wannan abin da ya b'ullo da shi ba.

Ranar wata asabar tun safe Farha ta dasa kukan ita dai a kaita gida wajen su yaya Farouk.

An yi rarrashin an yi hilar amma ta k'i yin shiru. Bilki ido kawai take binta da shi. Ta rasa me yake mata dad'i.

Alti ta ce "Ga Alawiyya ta tafi bare ta rakata su yini.

Kafin Bilki ta bude baki suka ji ana hawa saman a guje sannan suka ji ana kwnakwasa k'ofa. Da sauri Alti ta bude don tasan babu mai hawa a guje haka sai su Farouku.

Ilai kuwa sune d'in. Farha ta tafi a guje ta rumgume Farouku tamkar jiya basu hadu a makaranta ba. Amran da ta dade bata ganta ba, ba ta yi mararinta kamar yadda ta ke yin ta Farouku ba.

Hankalin Bilki ya dan sake nutsuwa ganin yaranta basa cikin matsala.

Farouk ya rik'e hannunta ya ce "Mahmah kin zama y'ar karama fa! I thought idan ba kya wanccan gidan za ki daina kuka kullum. Ko anan din ma ana saki kuka ne?"

Ta yi jarumta ba ta yi kukan ba. A hankali ta ce "Bana kuka Yaya Farouk. Ya ce "Yauwa ki dinga cin abinci, tunda kika taho nan ba mu yi fad'a da Yaya Amrah ba. Komai ta ce na yi ina yi ko Yaya?"

Ya tambayi yayar tasa.

"Hakane"

Amrah ta tabbatar da jawabansa.

Bilki ta dan murmusa kad'an ta ce "Allah ya yi muku albarka gabadaya ".

Basu tafi ba sai washegari lahadi da daddare lokacin da ya zo daukarsu tuni Farha ta yi barci dan haka lafiya lau suka tafi.

Ganin da Alti ta yi an fara samun cigaba a lafiyar Bilki ya sanya ta roke ta akan ta kunna wayoyinta.

Haka kuwa ta kunna kiran Yaya Hamida ne ya fara shigowa ta dauka suka gaisa cikin k'arfin hali ta fad'a mata halin da take ciki.

Hankalin Yaya Hamida ya tashi ainun amma ta dinga bawa kanwarta hak'uri tare da k'arfafa mata guiwar komai zai wuce tare da yi mata fatan alheri.

Ta kuma bata tabbacin zata zo a karshen sati in sha Allah.

Haka Ansari da su Saddiqa da Anisa duk sun ji halin da take ciki dan haka kullum sau biyu suke yi mata waya suna jin lafiyarta, za kuma su zo dubata a cikin satin da zai kama. Ansari kam takanas ya taho ya gaishe ta. Ganin ta samu sauki ya ce "Ta koma aikinta hakan zai sake rage mata damuwa.

Ta karbi shawararsa amma ta ce "Sai ta koma asibiti, sannan zata cigaba da zuwa makaranta.

Farha sosia ta makale masa ya dinga mamakin hakan a ransa ya ce tasirin jinin mahaifinta take ji a jikina.

Gabadaya ta juye sak Bilki haka da ya ga k'aninta junior sak Bilkin sai dai da za'a ga Sulaiman sai a ce sak shi.

Amma dai ba wanda zai ce Abida ce ta haife su, basa kama da ita.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *

Baba Babba da Yaya Farouk da babban d'ansa Ammar da yake aji biyu a jamiar Abuja da kuma Momi suna falon Baban a zaune.

Ya ce "Anya Farouku lafiyar Bilki k'alau kuwa? Duk juma'ar duniya sai ta gaishe ni amma yau juma'a ta hud'u ke nan ban ji daga gareta ba.

Yau tunda na dawo masallaci nake k'iranta amma layin a kashe yake."

Ba kuzari Yaya Farouk ya ce "Wallahi Baba ban fad'a maka ba ne. Bilki bata da lafiya an k'ira ni sati biyu da suka wuce. Ya yi masa bayanin komai.

Hankalin Baba Babba ya yi tashin gauron zabi ya ce

"Yanzu Farouku kasan da wannan al'amarin ka sakaye mini?"

Cikin girmamawa ya ce "Lokacin kana ta fama da zazzabi Baba ga shi jininka ya d'an hau sai na ji tsoron kada ya yi tashin da zaka jigata, amma na je na kaita asibiti na yi duk abin da ya kamata"

Baba Babba ya ce "Me ka yi Farouk? A ce d'iyar Isa tana zaune a gidanta ba kuma zaman aure ba? Ina da raina, sannan ku ma da ranku? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Tabbas Bilki ta yi gaskiya da ta ce "Su yanzu ya'yan mahaifinsu basu da wanda zai tsaya musu. "

Daga Momi har Yaya Farouk hak'uri suke ba shi akan ya kwantar da hankalinsa.

Murya na rawa ya ce "Hankalina ba zai taba kwanciya ba kuwa matuƙar Maigado tana Katsina tana zaune ita kad'ai ba a gidan aure ba. Ga Abida tana gabana alhalin aurenta ba mutuwa ya yi ba. Lallai na ci amanar zumunci!

Ya fad'a hankalinsa ya kai k'urewar tashi.

Da k'yar aka samu ya daidaita ya daina kuka.

Ya ce " Farouku jibi nake son na ga Bilki a gabana."

Ya ce "Wallahi Baba na yi iyakacin kokarina akan na taho da ita, k'i ta yi, to ganin so nake lafiyarta ta daidaita tunda damuwa ce ta yi mata k'awanya ya sanya na rabu da ita. Kasan mata da y'ay'a.".

Baban ya ce "Har ya'yan ya bar mata ke nan?".

Yaya Farouk ya ce "A a suna wajen Babansu".

Baban ya numfasa tare da fad'in "Ka je ka taho mini da ita umarni na baka. Sannan idan uban ya'yan zai bata su, to ku taho tare da su zan rik'esu gabad'aya."

Kwanaki biyu a tsakani ya tafi Katsina. Ya ji dad'in yadda ya ga ta samu sauk'i.

Dan haka ya zauna ya yi mata bayanin abin da Baba Babba ya ce.

Ta yi shiru tana tunani gabad'aya kanta ya kulle. Yaranta fa da suke zuwa suna ganinta tana jin dad'i suma su na ji?

Aikinta fa, sannan ya zata yi da Alti da bata da kowa sai ita?

Amma bata isa ta ja da umarnin Baba Babba ba don kuwa ta sa ni tun mahaifinsu yana da rai Baban ne mai zartar da komai. Sannan ba zata iya kallon idon Yaya Farouku ta ce ba zata ji maganar mahaifinsu ba.

Kan dole Alti ta shiga had'a mata kaya amma iya na sakawarta don kuwa ta ce zasu dawo. Zuwa zata yi ta bawa Baban hak'uri tare da fahimtar da shi muhimmancin zamanta a Katsina.

Washegari sai da suka je asibiti ta ga likita ya canja mata magani a cewarsa akwai sauyi akan farkon zuwansu. Sai dai ya ga alamun bata samun barci don idanuwanta sun yi tsilli tsilli wanda daga jiya zuwa yau ne ta zama haka, ba dan komai na sai don umarnin da aka bata na lallai ta je Abuja in ji Baba.

Daga asibitin kaitsaye makarantarsu Farha suka je suka dauke ta. Yayin da Farouk junior ya yi tsamo tsamo jin Mamah zata tafi Abuja.

A sanyaye ya ce "Mahmah can za ki zauna ko za ki dawo nan?"

Da rishin kuka ta ce "Idan Baban ya bar ni zan dawo"

Ya rik'e hannunta ya ce ",Idan ya ce "Ba za ki dawo ba, to ki yi zamanki. Ni da Yaya bama fad'a kuma muna cin abinci idan an yi hutu zamu zo".

Daga Alti har Yaya Farouku k'walla ce dam a cikin idanuwansu.

Murya ba amo ta ce ",To yayana, ka fad'awa yaya idan baku jini a waya ba ku k'ira layin Ammi ko na Alti"

Ta shafa kansa ta ce "Allah ya tsare mini ku, ya yi muku albarka".

Sai lokacin hawaye ya k'wacewa yaron. Ya mik'a mata hannun Farha ya ce "Watarana zan zo Farha".

Farha na kuka Bilki ta danna a mota Farouk ya rufe kofar.

Sannan ya doshi wajen mai Sunansa ya duka ya gaishe shi. Gabadaya jikin Yaya Farouku senior ya mutu murus ya kamu da ciwon tausayin Bilki da ya'yanta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya ciro kudi da yawa ya ba shi ya ce ka kaiwa yayarka ku ajiye. Ku dinga siyan abin da kuke so a hankali.

Idan na ji ba kwa yin kuka, to da kaina zan zo na tafi da ku a jirgi idan an yi hutu."

Haka suka ja mota suka bar yaron yana daga musu hannu.

Sai dare suka shiga Abuja.

A gajiye.

Sun samu kyakkwar tarba don Baba Babba da kansa ya rik'e hannun Bilki ya kaita d'akin da yake makwabtaka da na Abida.

Haka momi ta dinga ina ka saka da su.

Y'an aiki suka baibayesu da abinci.

Amma me gabad'aya Bilki ta sake rikicewa ko da gari ya waye ta sake komawa yanayinta na farko. Ba um ba umum sannan ba cin abinci. Ta fi son a fita a barta ita kad'ai. Ga ba cin abinci.

Yaya Asad ya zo gidan da hantsi ya ganta sosia hankalinsa ya tashi da ya ga yadda ta koma.

Ya kalli Abida da take kanta ya ce "Da alamun fa ba'a hayyacinta take ba."

Yaya Farouku ya ce "Tahowar nan da aka yi da ita ne ya sake haustina ta. Kai! ni kaina ban yi barci ba, kwana na yi ina nadamar yaron nan Farouk! Dan har ta fara samun nutsuwa, daga jiya komai ya sake k'wacewa ".

Abida ta numfasa ta ce "Depression ne ya damke ta da kyau idan ba'a bita a hankali ba kuma yana iya zama saikatiric ishus.

Yaya Asad da bai san aurenta ya mutu ba ya ce "To menene damuwar Maigadon da zata hadu da ciwon damuwa irin haka.?

Ya juya ga Yaya Farouku don jin k'arin bayani.

Ya fad'a masa sun rabu da mijinta ta kuma bar masa ya'yansa.

Jikinsa ya yi sanyi don ya san zafin rabuwa da abin da ake so. Ya tuna tashin hankalin da ya shiga a lokacin da ta yi aure. Yanzu kuma shi kad'ai ya san yadda yake ji a dalilin rashin matarsa uwar ya'yansa. Shi kad'ai yasan yadda yake jin tausayin ya'yansa a dalilin suna rayuwa babu uwa. Yasan yadda Bilki take ji a zuciyarta.

Ya kalli Abida ya ce "Wai ya ya ciwon damuwar nan yake ne Dr?"

Abida ta d'ago kanta ta ce "Da yake ba a fannin na k'ware ba, bari na yi maka bayani daidai gwargwadon yadda na fahimta da yadda zaku fahimta."

Ta muskuta ta ce "Sau da yawa, mutane kan shiga cikin halin damuwa da rashin walwala saboda wasu abubuwa na yau da kullum na rayuwa.

Amma idan mutum ya ci gaba da kasancewa a wannan hali na damuwa tsawon makonni ko watanni likitoci kan ce ya gamu da cutar matsananciyar damuwa!

A kan yiwa wannan cuta kallon ƙaramin abu ko kuma wasu ma su ce rashin haƙuri ne, ko rashin tawakkali ke haddasa ta ga wanda ya gamu da ita."

Ta numfasa ta zarce da fadin

"Sai dai masana sun ce abin da mutane ba su gane ba dangane da cutar shi ne damuwa cuta ce kamar kowace irin cuta da kan kama wani ɓangare na jikin mutum!

Haka kuma cuta ce da ke shafar ƙwaƙwalwa, da tunani wanda mai fama da ita ba shi da iko a kai."

Yaya Asad ya ce Sannu Dr Abida. Amma menene alamomin cutar?"

Dr Abida ta ce "Alamomin da ya yawa sannan ya banbanta daga wasu zuwa wasu. Amma manyan alamomin da likitoci suka bayyana sune kamar.

*TSANANIN BAK'INCIKI*

"Babbar alama ga mai fuskantar matsananciyar damuwa ita ce tsananin baƙin ciki na babu gaira babu dalili.

Mai fama da wannan cuta ka iya tsintar kansa a kodayaushe cikin ɓacin rai da rashin walwala.!

Za ka ga kwata-kwata mai wannan cutar ya rasa farin ciki. Abin da zai sa sauran mutane farin ciki, shi zai iya ƙara masa ɓacin rai har ma ta kai mai cutar ga son ƙebewa daga jama'a.

*KEBEWA DA K'IN SHIGA MUTANE*

Dakta Abida ta ce "bayan samun ɓacin rai ga mai cutar, wata alamar da ake ga ni a masu wannan cuta ita ce keɓe kai.

"Idan a baya an saba ana zama da mutum a yi hira, sai a ga yanzu ya fi son zama a É—aki shi kaÉ—ai, sannan zai rage walwala.

Ko fita za a yi gaba É—aya mutanen gidan, mai cutar tsananin damuwa zai ce shi ba za shi ba a tafi a bar shi a gida."

*ÆŠAUKEWAR BARCI KO YAWAITARSA*

Dr Abida ta cigaba da fad'in "yana ɗaya daga cikin alamomin matsananciyar damuwa yawan barci ko ƙarancinsa.

"Yawanci masu fama da cutar damuwa za ka ga ko dai barci ya yi musu ƙaranci ko kuma su yi ta barcin ba ƙakkautawa".[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *RASHIN SON CIN ABINCI KO YAWAN CINSA*

"Yana ɗaya daga cikin alamun matsananciyar damuwa tsananin cin abinci ko rashin cin sa, inda har mutum kan ƙara ƙiba ko rage ƙiba."

Ta nisa ta cigaba da ce wa

"Akwai wadda ta yi tsananin da sai an daɗe ana shan magani kafin a samu sauƙi sannan akwai wadda ɗebe kewa da bayar da shawarwari kawai yake iya magance ta

Sakamakon tsananin ɓacin rai da keɓewa daga jama'a, masu fama da cutar kan yi tunanin rayuwarsu ba ta da amfani, saboda haka sai su nemi mafita - wato kashe kai.

Kisan kai al'amari ne mai sarƙaƙiya wanda yake faɗowa mutum a tunaninsa a matsayinsa ne mafita.

Ko kuma mutum ya yi tunanin ce wa shi ne zai kawo ƙarshen wahalar ko matsin da suke ciki a rayuwa!

Duk da ce wa yana da wuya a fahimci dalilin da zai sa wani ya yi yuƙurin kashe kansa, mutanen da ke wannan yunƙurin kaɗai suka san me yake faruwa a cikin zukatansu."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "61" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c14e6f82315f17460a4c92

"Bilki to be sincire magana nake so mu yi dake, amma heart to heart."

Abida ta faÉ—a tana mai kallon Bilki a tsanake itama ganin haka yasa ta gyara zama tana sauraranta da dukkan nutsuwarta.

"Bilki ki ji tausayina! Ki duba halin da na ke ciki don Allah ba na ba ki tausayi?"

Ta faÉ—a tana mai nuna kanta muryarta har ya fara karyewa tana shirin ta fara kuka.

Abida mai taurin zuciya amma yanzu rayuwa ta sanya duk ta yi laushi.

"Abida ina tausayin ki mana. Amma me ya faru ne?"

Bilki ta faÉ—a itama cikin damuwa ganin sauyawar Abida lokaci É—aya.

"Dube ni fa Balki. Magana ta gaskiya ki ji tausayina ki faÉ—a mini inda Ya Sulaiman yake ida kin sa ni. Ki duba shekaru uku ba kwana uku bane, ba sati uku bane haka nan ba wata uku ba ne, don girman Allah ki faÉ—a mini in dai kin san inda yake Bilki.".

Abida ta faÉ—a cikin karyewar zuciya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "62" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c1534d82315f17460a990d

"Lalle Babban yaya alama da zafin sa ya kutso. Mu yara sai mu mu yi baya "

Bilki ta ji zafin maganarsa sosai ta ɓata rai tana kallon shi kafin ta ce" Ya Faruku abin da za ka yi mini ke nan?"

Kana nufin abin da nake ga ni a idanuwanka wannan karon ma iska zai bi?"

Ya kasa bata amsa sai kawai ya tafi babu sallama.

Zuciyarta ta yi kunci bata yi zaton zata sake son wani namiji kwana kusa ba. Amma tabbas son Yaya Farouk ya kutso da k'arfin gaske daga inda ta sakaye shi a zuciyarta.

*Contact me 08032773332 what'sapp only*

*For all your kayan mata gangariya*

*Bridal package*

*Maijego package*

*Uwargida package*

*Bazawara package*

*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*

*Ciccibin garari*

*Tsumin saiwowi*

*Hakkkn daka emergency*

*Gumbar ridi*

*Gumbar saiwowi*

*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "63" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c157b482315f17460ae55c

"Idan kana son Bilki to ka nemi yardarta idan ta amince, nima na amimce kasan yanzu ba yarinya ba ce tana da wannan damar sannan kar ka manta ko da suke yara ban yi musu auren dole ba bare yanzu tana da y'ancin ta yiwa kanta zaɓin da take so. Idan ta amince da kai to zan fi kowa farinciki zan kuma taya ka da addu'a Allah ya tabbatar. Idan har hakan ya faru komai zai daidaita, waki'ar da ta nisantamu da juna zata gushe a zukatanmu. Ƴan'uwanta za su samu damar zuwa gidanka su yi zumunci kai ma naka za su je, daga nan komai da ya faru na rashin jituwa a baya zai wuce ba na fatan na mutu na barku a cikin wannan halin, Sulaiman ya tafi ba mu san inda yake ba, idan yana raye Allah ya bayyana shi. Idan kuma tana san inda yake ta boye, idan ta zo hannunka kana hillatarta duk za mu ji komai."

Yaya Asad ya ji ƙarfin guiwar tunkarar Bilki a wannan gabar tunda ya samu amincewar Baba Babba da Abida. Dama Abidan yafi ji da Usman amma tunda Abida bata botsare ba yasan Usman ba zai samu tallafi ba. Mamakin yadda Abida ta huce ta yi sanyi akan ahalinsu Bilki yake yi.

Da Bilki ta dawo ba wanda ya yi mata zancen zuwan Asad shi yasa ba ta san ya zo gidan ba. Shi kuma tun tafiyar shi kullum da safe zai tura mata sakon gaisuwar safe da asubar fari. Da daddare ma akwai na mu kwana lafiya. Ga k'iran waya akai akai, yana kashe murya yana yi mata kalamai irin na jirwaye duk da ta fahimci manufarsa amma sai ta nuna masa bata gane komai ba. Kuɗade masu nauyi yake turo mata akai akai, idan ta ce sun yi yawa ko ya daina. Ce mata yake yi idan Sulaiman ne ya tura mata kuɗi ai karba za ta yi ta gode masa, ba ta ce bata so ba jin haka yasa jikinta ya yi sanyi, bata sake ce masa komai ba, idan ya tura mata kuɗi sai dai ta yi godiya amma a cikin zuciyarta ta kudire yayaa Asad ba zai iya siyan soyayyarta da kuɗi ba. Kuma tana jiran ranar da zai gaji da ƙumbiya kumbiyarsa ya fito fili ya faɗa mata, daga ranar za ta fada masa ya daina wahalar da kansa don kuwa bata ra'ayinsa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "64" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c1c4cd006c2321ccbf267b

Ana haka ya je Dubai. Sai ga shi ya siyo mata wani murtukeken bangle da zobensa kallo daya zaka yi ka gane zinare ne sannan ya lashe manyan kudade na gaske. A lokacin Momi ta farga ta gane Asad zaawarcin Bilki yake yi ka'in da na'in.

Bata nuna adawa da lamarin ba, tunda ta san Baba Babba zai yi faricinciki idan al'amarin ya tabbata, tunda auren nasu ne zai ƙara daidaita zumuncin gidan da ya shiga halin ni y'asu.

Sai da ya fara nunawa momi tsarabar Bilki. Ta ga ni da walwala a fuskarta ta ce ",Amma ina na Abida kasana tana ga ni zata hau rikici tunda Bilki kishiyarta ce".

Ya yi murmushi ya ce "Rabu da ita Momi sau nawa ina siyo mata? Ina ce bara ma da na je Saudiyya sai da ta ce na siyo mata sarƙa kuma na siyo mata. Bilkin ma dan ta gane da gaske nake yi ne ba wasa ba."

Ya kammala fad'a yana shafa kansa .

"To ma sha Allah, Allah yasa rabonka ce, zan yi farinciki da hakan."

Ta faÉ—a tana mirmishi, ba shakka idan ya samu Bilki ta san ya gama morewa.

"Amin Momi. Gata nan tana ta yi mini tutsu ki tayani shawo kanta."

Ya fada cikin jin kunya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "65" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c1c583006c2321ccbf30fa

Bilki ta fara kuka mai sauti tana fadin" Ya Farouku me ya sa ba kai ba?

Me ya sa ba ka ce kai ne za ka aure ni ba ? Kana cutar da ni. Tun ina budurwan kasan ina son ka, kai ma na san kana sona amma saboda wani banzan dalili ka haramta mna9 cikar burinmu. Yanzu kuma bayan na dawo ka daÉ—a ja na a jiki ka sanya mini son ka da mararinka, ina ta tunanin wannan karon zan same ka mu yi rayuwa tare. Zuciyata tana girmamaka tana sonka, shi ne za ka zo mini da wannan maganar alhalin ina jin nauyinka. Ni dai gaskiya tunda ba sona kake yi da gaske ba, to kawai mu bar shi a hakan, ka bar batun mutumin can".

Ta gama fada tana kuka wurjajan kamar wata karamar yarinya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Na gode da addu'o'inku Ga mahaifiyata, wanda suka yi mini ta pc da Wanda suka yi a group dan Wanda suka yi ban Sani ba*

Na gode Allah ya karba ya jiƙan dukkan magabatanum*.

*Allah ya bada lada ya bar zumunci*.

*"Amma mene ne makasudin da yake janyo cutar tsananin damuwa?"*

Yaya Faruk ya yi tambayar a nutse.

Dakta Abida ta ce "cutar tsananin damuwa na iya kama kowanne jinsi na mutane, sannan ana ganinta a manya da yara duka.

Sai dai an fi ganin ta a mata da matasa da suke daidai shekarun balaga.

Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce sau da yawa idan wani iftila'i ya samu mutum ne yake shiga halin tsananin damuwa, kamar rasa wani makusanci, karayar arziki, ko kora daga wajen aiki, ko haihuwa mai cike da tangarɗa, da dai sauransu."

Dakta Abida ta cigaba da fad'in "yanayin halittar É—an'adam na taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan matsala.

Wani Allah ya halicce shi da juriya. Ko da abin tashin hankali ya same shi zai daure kuma ba zai zauna masa a rai ba!

Wani kuma ba shi da haka. Allah ya halicce shi yana da rauni kuma ba shi iya jure jarrabawa. To irinsu ne suka fi gamuwa da matsalar tsananin damuwa.

Sai dai wani lokaci ma haka kawai mutum kan shiga damuwa har ta zamar masa wannan cuta."

*"Ana warkewa kuwa dr?"*

Yaya Asad ya sake tambayar Abida.

Ta ce "ana warkewa tsaf daga wannan cuta idan aka samu taimakon da ya dace!

Idan aka lura alamomin wannan cutar sun bayyana ga wani ko wata, abu na farko shi ne a kai shi asibiti kaitsaye. A guji camfi ko jinginawa jinnu don yin wasarere da jinyar na iya sakawa ya koma ciwon hauka!

Yaya Asad ya sake tambayar

"Akwai magunguna da hanyoyin da ake bi a asibiti ga masu fama da cutar damuwa.?"

"Muna ba da magunguna, sannan akwai likitoci na musamman da aikinsu kawai É—ebe wa masu wannan cuta kewa, da ba su shawarwari kan yadda za su tafi da rayuwarsu."

Sannan ta ce "makusantansu su riƙa jan su a jiki, da nuna musu kulawa.

WaÉ—annan ne suke samar da kwanciyar hankali a tare da masu cutar har su samu lafiya."

Yaya Farouku ya ce "Sannu da kokari Abidan Baba. "

Yayin da Yaya Asad ya ce "Gaskiya ina fama da wasu alamomin dan haka nima ya kamata na ga likita. Zan bincika asibitin da suke da kwararrun likitan da ya k'ware a fannin wannan matsalar sai ku dinga zuwa tana ganinsa."

Yaya Farouk ya numfasa ya ce "Tunda debe kewa na kan gaba wajen samarwa da mai lalurar sauki to ya zama wajibi mu taru mu dinga sanyaya mata zuciya. Sannan ke da kike gida ki tabbatar kin gyara mu'amalarki da ita. Duk abin ya faru a baya mu bar shi ya wuce, mu yi ta addu'ar kada a sake jarrabarmu da rikici a tsakaninmu."

A sanyaye Abida ta ce "To".

(Maitama clinic) Anan Bilki ta ke ganin likita bisa rakiyar Abida da Alti.

Ta taimakon Allah da kulawar mutanen da suke zagaye da ita aka samu ta fara komawa hayyacinta.

Mussaman da take ganin yadda Abida ta damu da halin da take ciki. Baba Babba da kansa kullum sai ya zo d'akinta ya duba ya yi mata nasihar ta kwantar da hankalinta ta bi yaranta da addu'a, tare da bata misalai daban daban,. Y'ay'a nawa ne suke rayuwa basu taɓa ganin mahaifiyarsu ba? Ya'ya nawa ne suke rayuwa babu uwa ba uba gabad'aya. Hakan kuma ba zai hana su cimma dukkan nasarar rayuwa ba.

Annabin Rahma (S.W.A) da Allah ya bar shi a maraya ya kuma daukaka shi a cikin kafatalin bayinsa kad'ai ayace da dukkan mai imani zai sake k'arfafa imaninsa.

Don kuwa Allah shine mafi kulawa da rayuwar bayinsa.

Ire iren bayanin da yake mata ke nan a kullum. Da kuma mutanen da suka shahara a yanzu amma kuma sun rayu ne a gidan ubansu babu uwa wala mutuwa ta yi ko kuwa auren ya mutu aka barsu suna yara.

Damuwar da Bilki ta ga ahalinsu sun yi da ita ya yi matuk'ar rage damuwar da ta tsinci kanta a ciki.

Dama matsaloli biyu ne suka ankarata.

Yaranta da kuma yadda Sahal ya ce mata bata da inda zata je. Da ganin tana zaune ita kad'ai din, amma a yanzu ta saduda ta hak'ura da batun yara mussaman da kullum sai sun yi waya ko a layinta ko a na Abida.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tunda Amrah ta shiga s.s1 aka siya mata waya tunda haka tsarin makarantarsu take.

Don akwai darussan da dole sai da bincike a yanar gizo.

Dan haka kullum da daddare suke yin waya don da safe bata tashi da wuri.

Sannu a hankali ta wartsake gabadaya har likitoci suka rage mata magungunan da take sha, suka bada shawarar a yawaita mata abubuwan da zasu sanya ta walwala a guje kuntata mata. Bayan haka a dinga kokarin hana ta zama ita kad'ai na tsawon lokaci.

Abida ta taka muhimiyar rawa wajen dawo da tunanin Bilki daidai.

Don komawa ta yi ma d'akinta kacokan. Hakan kuma na tunowa da Bilki rayuwarsu ta baya mai dad'i kafin komai ya cakalkale musu.

Ana haka Yaya Asad ya biyawa Bilki da Abida umrah.

Ya yi hakan ne don zuciyarta ta sake daidaita.

Ba Bilki kawai ba, hatta Baba Babba ya ji dad'in hakan.

Suka shirya suka tafi aka bar junior a wajen Momi. Don kuwa ana faÉ—awa Bilki zasu tafi Saudi ta ce Da Farha zata tafi. Tunda a satin zata fara zuwa makarantar da za'a saka ta. Idan sun dawo sai ta fara zuwa.

Ba musu aka yi mata yadda take so.

Haka suka tafi su uku. Sati biyu suka yi suka dawo.

Sosai Bilki ta dangana. Ta cire hankalinta akan komawarta Katsina tunda Farha har ta fara zuwa makaranta. Wani lokacin ma Farha ce ke damunta da batun yaushe zasu koma gidansu ne? "

Katsina.

Hawwa ta haihu sati biyu da suka shud'e, daidai lokacin Bilki na umrah. Iya k'arfin iyakarsa ya yi mata hidima. Sai dai ita bata yaba ba don kuwa ta dauke shi maikudine sosai. A yanzu da zaman nasu ya fara nisa ta fahimci ba shi da komai illa albashinsa. A ciki zai yiwa uwarsa da y'ay'ansa da kuma ita da abin da ta haifa.

A lokacin ta fara gane duk arzikin da take ga ni a gidan Bilki ce. Tunda ta bar gidan ta gane ta tafi da abubuwa da yawa tunda ba shi da mai yi masa.

Bayan haka tana zargin Bilki ta yi asirin da zai so y'ay'anta fiye da k'ima, tunda ai farkon zuwanta ba haka yake mu'amala da yaran ba. Asalima shi da kansa ya ce "Amrah ce zata dinga yi mata aikin shara da wankewanke. Amma a yanzu saboda kada a saka ta ya dauki mai aiki. Iya dakin barcinta da band'aki kawai take gyarawa. Sai ko wanki da guga da take yi musu ita da k'aninta. Suma idan kayan masu nauyi ne da kansa yake wanke musu ya dauraye su kuma su shanya. Bata sake hassala ba sai da ya ce mata zai sakawa jaririya sunan Bilki. Ta yi tsalle ta dire akan bata yarda ba, don kuwa ba zata sha azabar nak'uda sannan a sakawa yarinyarta sunan kishiya ba.

Bai zafafa ba amma a gabanta ya k'ira Amrah ya mik'a mata jinjirar ya ce "Ki zaɓarwa kanwarki sunan da kike so a saka mata ".

Hawwa ta ji tamkar ta rufe su da duka daga shi har d'iyar tasa.

Yayin da farinciki ya kama Amrah.

Da murmushi sosai ta ce "Na gode Dady! Na zaba mata sunan Hajiyarka".

Ya taya ta murmushi ya ce "Allah ya raya lubabatu".

Farouk da yake gefe ya ce "Ameen."

Sai lokacin Sahal ya ce "A a yayan Mahmah matso kusa da ni kai kuma ka zabar mata sunan da za'a dinga fad'a mata tunda Yaya ta sanya mata sunan da ba za'a dinga gyatsa shi ba."

Ya girgiza kai ya ce "A a Dady ta zabo inkiyar ma dan kuwa nima idan aka sake haihuwa ni zan zabi sunan da nake so."

"Oh dabararka ke nan?"

"To Allah ya kawo masu albarka".

Daga haka ya karbi yarinyar Amrah tana fadin "Tunda ni Amrah ita kuma Ifrah kawai".

Hawwa a ranta sai ayyana k'arfin halin da aka gwada mata take yi. Yarinya ce zata zaɓarwa y'arta suna tsabagen an shiga an fita an juyar da hankalinsa kansu?

Kan dole ta yi shiru amma matuƙar ta tafi gida yawon arba'in itama sai ta nemo taimakon da zata karkato hankalinsa kanta da d'iyarta.

Duk da idan an tambaye ta menene baya yi mata, idan har gaskiya zata fada babu ce amsar.

Kawai matsalar ta ba kudin facaka a hannunsa yanzu sannan mu'amalarsa da ya'yansa na matuƙar mintsininta har ta dinga jin ina ma uwarsu ta nan?

Haka dai rayuwar take tafiya kowa yana hak'uri da yadda aka zartar masa rayuwa. Alhamdulillah, Allah ka saukaka mana gabadaya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sai da ya yaran suka fita ta dauko robar hadaddiyar gumbarta da ta siyo a Kano unguwar rijiyar lemo.

Tun tana amarya take son gumbar dan ta ga aikinta tunda cikinta ya fara tsufa ta daina ci.

Yanzu da ta dauko ta bata yi komai ba. So take a yi suna ta Ga nawa zata samu ta karbi abinsa zai bata ta sake order gumbar da ciccibin a wajen Hajiya Halima Mai..............

Sannan ta ga robar sanyi flusher da robar kazar sababi na Bojuwa herbs a kicin din Bilki ta tabbatar ingantattun kayane tunda ta gansu wajen Bilki. Tuni ta kwafe lambar a wayarta Sai ta shirya zata yi order din maijego package.

*Abuja*.

Bayan watanni uku.

Zuwa yanzu Bilki ta kammala iddarta. Ta ajiye tunanin komai tana zaune lafiya. Tana shan magani sai dai guda d'aya tak. Gabadaya an sauke ta daga kan sauran.

Daidai wannan lokacin aka yiwa Yaya Asad sauyin aiki an dawo da shi Kwamishinan Y'an sanda na birnin tarayyar Nigeria wato Abuja.

Gabadaya gida ya kaure da murnar cigaban da ya sake samu tare da murnar zai baro fatakot gabadaya.

Amal da Noor sune kananu a gidan Momi suke, makarantarsu aka saka Farha.

Aysha babbar diyarsa barista ce bana ta kammala bar school ta Enugu.

Khadija da take biye da ita tana London tana karantar aikin had'a magunguna Phamarcy.

Hafcy ce a jamiar skyline ta Abuja tana ajin farko tana karantar aikin jarida.

Bilkisu yanzu zata kammala sakandire.

Ranar da ya bar fatakot da wuri ya sauka a Abuja bai je gidansa ba, kaitsaye gidan da muke ya dira. Ya gaida iyayensa.

Suka yi masa murna da fatan alheri.

Baba Babba ya ce "Yanzu a haka za'a yi bikin alherin da ya same ka babu iyali a tare da kai Abubakar?

Yanzu wa zai saka maka tauraron?"

Da murmushi ya ce "Baba hakuri zaka yi ka ara mini Momi ga kuma amaryarka Aysha shike nan ita da Momi sun wadatar."

Baba ya kaurara murya ya ce "Ka mayar da hankali akan batun aure. Iyayen matarka sun zo nan ya fi sau uku akan sun baka kanwarta ka ce sam kallon diya kake yi mata.

Nan makwabtanmu yarinyarsu ta nan ta kammala masters mahaifinta da kansa ya ce mini idan ba ka yi magana da wata ba, ka neme ta zai baka. Na yi maka magana ka ce na dakata kana cikin uzziri, yau kusan wata takwas da maganar amma ka k'i mayar da hankali."

Ya sunkuyar da kansa ya ce "A kara hak'uri Baba zan yi ne in sha Allah, a cigaba dai da yi mini addu'a."

Momi ta ce "Addu'a kam muna yi, daura niyyar auren ne baka yi ba. Kuma duk mukamin nan naka haka ake kallon ka fanko tunda baka da mace. Aure ai shine cikar darajar d'anadam ".

Haka dai suka yi ta yi har suka gaji dan kansu. Ya basu hakuri kamar yadda yake musu kullum.

Bilki ita kad'ai a d'aki don daga Abida har Farha da junior basa nan, yara na makaranta, Abida na asibiti tunda a specialist hospital Abuja take aiki.

Ta yi wanka tana sanye da material din Malaysianfabrics ta yi Fes da ita Sai tashin k'amshi na alfarma take yi.

Alti ta turo kofar d'akin tare da fad'in "Mahmah in ji momi ki zo ku gaisa da yayanku".

Bata tambayi waye a cikin yayin nasu ba.

Don tun jiya ta ji Abida na fad'in Yaya Asad yau zai dawo Abuja gabad'aya.

Ta mike ta bude wadirof ta dauko k'aramin mayafin da ake sakawa da gown, wanda ya dace da material din.

Falon Baban ta dosa kaitsaye don tasan suna can.

Tana shiga idanuwansa suka fad'a cikin nata, tunda yana zaune a kujerar da take fuskantar mai shigowa.

Gabanta ya yi wani irin yankewa ya fadi. Ta rasa yadda zata yi kamar ta juya ta koma d'akinta saboda yanayin da ta tsinci kanta a ciki. Gabadaya ya sake yi mata kwarjini.

Bata san ya aka yi ba kawai sai ta tsugunna har k'asa tana fad'in "Ina kwana Baban Bilkisu?"

Ya kasa amsawa domin bai so ta yi masa irin wannan gaisuwar ta k'ololuwar girmamawa ba. Yafi son irin wacce suke yi masa a dan risinar da kai kadan a gaishe shi, amma yanzu ta wani zube tamkar wadda take gaida Baba Babba ko wani tsohon dattijo.

Murya ba amo ya ce "Maigado ya jikin dai?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ta amsa masa da fad'in "Da sauk'i". Kanta na k'asa.

Baba Babba ya ce "Ah ta warke ita da take batun a samo mata aiki ta gaji da zama haka ".

Yaya Asad ya ce "Ah lallai Maigado ta warware na ji dad'in wannan batun.

ÆŠauko mini duka takardunki, idan na nutsu sai mu ga yadda za'a yi."

Ta mike ta koma d'akinta dan ta taho da takardunta tunda da zata baro gidan Sahal a cikin akwatin ta sanyasu, a cikin akwatin kuma Alti ta hado mata kayan da taho da su nan.

Ya bita da kallon k'urillah, haka yake son mace ta bude ta k'asa. Duk da ya ga yanzu ta tsiyaye ba kamar yadda ya santa ba.

Ta dawo ta sake durk'ushen sannan ta bashi hannu biyu. Ya sake jin babu dadin yadda take yi masa.

Amma ya karɓa ya ajiye a gefensa.

Daga haka ta yi masa sallama sannan ta mik'e ta basu waje.

Da Abida ta dawo ta bata labarin Yaya Asad ya karbi cv dinta za'a samo mata aiki.

Abida ta ji dad'in don hakan alamace Bilki ta yi hak'uri ta bi hukuncin Baba na ba zata koma Katsina ba.

Yaya Farouk da shi ba maaikcin gwamnati ba ne kullum sai ya zo gidan ya taya ta hira. Suka sake shakuwa sosai. Duk sadda zai zo sai ya siyo mata abun da zata ci ko na amfani kuma mai tsada.

Idan ta zauna tana yawan tambayar kanta to shi a ina yake samun kudi ne? Tasan Ladi farm nan ne wajen aikinsa, yanzu kuma da bata hannunsa me yake yi ne?"

Rannan suna falo suna hira shi da ita da Alti don kuwa sosai suke dasawa shi da Alti.

A sanyaye ta ce "Yaya Farouku fad'a wai sana'ar me kake yi ne yanzu?"

Ya yi dariya ya ce "Bilkisu tawa! Ba cima kwance bane ni. Harkar crypto na yi, kinsan farkon harkar an samu kudi da dala, ina cikin wadanda suka yi harkar a farko suka samu alheri. Yanzu kuma Sai nake yin harkar canji.".

Ta murmusa tare da fad'in "Alhamdulillah na ji dad'i sosai, Allah ya taimakemu gabadaya ".

Ya ce "Ameen Maigado ".

Daga haka Alti ta tashi ta shiga kicin don d'ora sanwar dare don tunda ta zo ita take girkin gidan don kuwa Ubangiji ya yi mata baiwar iya girki."

Bilki ta kalle shi ta ce "Yaya Farouku akwia kayayyakina masu muhimmanci a Katsina. Sannan na bar motata, ina son na kwashe kayana a gidan dan a zuba y'an haya tunda dai ka yi zugar da Baba ya hau kai ya zauna ya hana ni komawa".

Ya yi dariya sosai ya ce"Kada ki damu sai Alti ta je su hadu da Anisa tunda yanzu ta koma Katsina da zama su hada miki kayan.

Mota kuma ki bar mata ki ce in jini, ke kuma ki zabi wacce kike so sai na siya miki".

Ya murmusa ta ce ", Allah yaya Farouk ka kama k'asa da yawa amma sai a yi ta dorawa Yaya Asad nauyi da yawa".

Ya kwashe da dariya sosai ya ce"Wa ya ce ya zo a farkon? Maigado yau d'ansanda kike karewa ki bar ni? Ba damuwa!

Ya fada yana jijjiga kai sosai.

Alamun ya yi fishi. Tana dariya sosai ta ce "Afuwan Yaya Farouku ai kasan ni da kai bata b'aci.".

Suka cigaba da hirarsu.

Wata d'aya da karɓar takardunta ya kawo mata upper ta samu aiki da hukumar tantace abinci da magunguna wato (Nafdac). Sosai ta yi murna. Ta fara zuwa wajen aikinta cikin nutsuwa sosai, komai ya daidaita mata dan yanzu ma an daina taya ta kwana daga ita sai Farha suke kwanciyarsu.

Kawai abin da ya takura ta d'aya ne, rashin mota a hannunta. Kullum da Abida suke fita ta ajiye ta.

Idan ma Abida ba morning zata yi ba, haka take tashi ta kaita wanda tasan k'arfin hali take yi domin tun farko Abida bata son a takure ta. Amma yadda Abida ta yi laushi take yi mata kirki abin har mamaki yake bawa Bilki, tausayinta take ji ko kuwa menene? Sannan ta lura Abida ta d'auki son duniya ta dorawa junior. Kowa ya lura da hakan Momi har fad'a take yi mata akan ta rage yadda ta makale shi a ranta.

Bilki dai tasan kowa na son d'anta amma abin Abidan babu sauk'i sai take ganin ko dan bata rayu da Farha bane ya sanya ta É—orawa yaron dukkan soyayya. Don kuwa ko kad'an bata shiga al'amarin yarinyar tsakaninta da Farha kamar yadda take mu'amala da sauran ya'yan y'anuwa. Amma ko kusa ba ta jinginawa kanta ita.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sai ta yi kamar ta fad'awa yaya Farouk batun motar da ya ce zai siya mata, tunda ya saka ta bayar da tata, har Anisa ta k'ira ta yi masa godiya. Sai kuma ta fasa tare da tunanin bai manta ba.

Rannan wajen karfe d'ayan dare ta tashi ta yi fitsari, ta fito a band'aki sai ta ga wayarta na haske. Sai da ta kwanta sannan ya dauki wayar ganin wasu lambobi a jere iri d'aya ta gane layine na mussaman.

Ta ajiye bata dauka ba.

Kafin ta yi tunanin waye mai layin, k'iran ya sake faÉ—owa wayarta.

Ta saka hannu ta amsa tare da kangawa a kunnenta.

Murya ba amo ta yi sallama.

Ya amsa ba alamun barci a muryarsa.

Gabanta ya buga Yaya Asad zai bugo mata waya da tsakar dare?"

Kafin ta samu amsar tambayarta.

Ta ji cikin wata irin ya ce "Maigado na tashe ki ko?"

A sanyaye ta ce"Ba komai".

Ya numfasa ya ce "Ya yanayin aikin ba kya samun matsala ko?"

"Ba wata matsala".

Ta ba shi amsa a takaice.

"Ya ce "Ma sha Allah! Dama zan tambaye ki ne wacce irin mota kiki so , don bana so ki dinga tahowa a taxi ba idan an tashi tunda na ga Abida ke kai ki da safe ko?"

"Eh ita ce, amma mun yi magana da Yaya Farouku zai siya mini. Ka bar ta na gode".

Ya sake tausasa harshe ya ce "Ga shi kuma na yi niyyar yi miki alheri Maigado. Shike nan sai ki had'a biyu, ko ki ce masa ya siya miki wani abin amma mota kam ni zan siya miki".

Abin alheri ya yi mata amma ko kusa bata ji dad'in alherin ba. Don kuwa ta tabbatar akwai abin da zai biyo ba.

A takaice ta ce"To na gode, Sai da safe ".

Ya sake yin k'asa da muryar ya ce "Ko za ki daure na turo miki hotunan motocin ta what'sapp ki zaba so nake a kawo miki da wuri "

Har cikin zuciyarta sai da ji nishin da ya yi kunne a kunnenta.

A kidime ta ce "To" tare da katse kiran zuciyarta na bugawa sosai.

A fili ta furta "Duk masifarka bana sonka, ba namijin da zan sake sa shi a zuciyata idan ba Yaya Farouku ba."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tsabar kidimar da ta shiga ya sanya bata bude what'sapp din ba. Sai da ta ga yana k'iranta ta what'sapp din sannan ta katse ta duba.

A zabure ta tashi ta zauna ganin motocin gararin da ya turo mata da zasu lashe millions of naira wai ta zabi wacce take so.

Ta murtsuke idanuwanta sosai dan ta sake gasgata ita Bilki ake yiwa tayin ta zabi guda cikin wadannan motocin?

Ta tabbatar dai ba gizo ba ne .

Sai ta rubuta masa wadannan duk sun yi mini yawa. WaÉ—anda basu kai wannan ba ta isa.

Ya ce "Amma tunda ba rokona kika yi ba, bai kamata na ce ga yadda nake so, ke kuma ki ce yadda kike so za'a yi ba ko?"

"Hakane"

Ta fad'a a takaice domin ta ji tamkar ya ji haushi ne.

"Kawai ki zabi kalar da kike so".

Ya fad'a cikin sigar umarni.

Maimakon ta yi masa voice irin yadda yake yi sai ta sake rubuta masa "Farar".

"Yauwa Maigadona! Na gode miki sosai Allah ya saka da alheri".

Tana mamakin jin godiyar da yake yi tamkar ba shine ya kamata ta yi masa godiyar ba. Ta jijjiga kai tana fad'in komai ma kake nufi ba yiwuwa zai yi ba dan ba kunyar wadda zaisa na k'wari kaina.

"Wai Maigadona!

Ta furta a bayyane.

Ta juya tana gyarawa Farha kwanciya.

Ta saki tsaki tare da fad'in "Ko ta ina na zama tasa?"

K'ira ya sake fadowa wayarta. Ta rasa yadda zata yi haka ta dauka akan dole.

"Maigado kin yi barcine?"

"A a Farha na gyara ta kwanta kan hannunta ".

"Sannu da kokari to"

Ta share tamkar bata ji ba.

Ya nisa ya ce "Maigado barci kike ji ne?"

Murya ba amo ta ce "um"

"To bari na k'yale ki haka nan, zamu yi magana da safe. Stay blessed".

Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa ta bi wayar da kallo cikin sake mamakin sabbin hallayar da yaya Asad ya tsiro da shi zuwa gare ta, sai take jin wani bambaraƙwai wai namiji da suna Hajara. Ita fa ba yarinya ba ce ta san manufarsa akanta kuma sai dai ya yi haƙuri ba zata taɓa sonsa ba, ba ruwanta da kuɗinsa balle muƙaminsa ya je wani waje ya nemo matar aure dan kuwa ita bai mata ba.

Tunda ga ranar yaya Asad kullum da daddare sai ya kirata yana kashe mata murya, tare da hilatarta. Ita dariya ma yake ba ta É—auka yake yi ba ta gane manufarsa ba nan ko kallon shi kawai take yi tana dai biye mishi sama sama domin ta ga iya gudun ruwansa, har zuwa ranar da zai furta manufarsa ita kuma a lokacin za ta taka masa burki ta faÉ—a masa gaskiyan cewa ba ta son shi daga nan sai ya kama kan shi da ita.

Haka Bilki ta cigaba da gudanar da kyakyawan rayuwarta a gidan Baba Babba ba ta da matsalar komai, gata da wani irin tattali ake nuna mata kamar su lashe ta, ihum kawai za ta ce a taso mata ana tambayanta ko tana son wani abu, ta samu kwanciyar hankali ta fara mai da jikinta kamar ba Maigadon da Sahal ya sukurkutawa rayuwa ba. Ta dawo cikin natsuwarta sai da ta ɗan sauya, wasu sabbin daɓi'u ta fito da su na abu kaɗan ne yanzu yake ɓata mata rai nan da nan za ta ruɗe ta fara faɗa daga nan sai kuka saboda cutar da ta yi na depression shi ya sa yanzu kowa ke lallaɓa ta, har Abida duk tsiyataku ta ta daina yi mata, kaffa kaffa take da ita sosai, zama suke yi su yi hira na tsawon lokaci suna dariya har da shewa, sannan su kan raba dare a ɗakunan juna suna hira.

Ana cikin haka ne irin zuwa ɗakinta da Abida take yi suna hira, ranar ma sun daɗe suna ta hira har wajen sha biyun dare Yaya Asad yana ta k'iranta a waya ta ƙi ɗauka Allah ya taimake ta, ta sanya wayar a silent da Abida ta lura da ta yi mata ɗan biki.

Suna cikin hirar Abida ta zama serious.

Tace "Maigado zamu yi magana muhimiya! Amma amanatul amana".

Bilki ta fara dariya tana tuna yarintarsu da lokacin da Abida ta ke siyar da jarida, idan kuma ba na kuÉ—i ba ne sai ta ce Amana ne.

"To Abida idan kuma subutar baki yasa na faÉ—a ma wani fa. A ranar lahira ta ci ni gudan jini ya faÉ—o?"

Suka kwashe da dariya har suna tafawa suna tuna lokacin yarintarsu da abubuwan da suka faru.

"Kai ba abin da ya fi ƙuruciya daɗi Abida.";

Bilki ta faɗa tana ɗan share ƙwalla daga gefen idanuwanta.

"Kamar jiya ta dawo. Kowa ya fi more lokacinsa a lokacin yarinta."

Bilki ta ce "haka ne kam suna tuno yaya Munnira suna cikin tsananin kewarta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Bilki to be sincire magana nake so mu yi dake, amma heart to heart."

Abida ta faÉ—a tana mai kallon Bilki a tsanake itama ganin haka yasa ta gyara zama tana sauraranta da dukkan nutsuwarta.

"Bilki ki ji tausayina! Ki duba halin da na ke ciki don Allah ba na ba ki tausayi?"

Ta faÉ—a tana mai nuna kanta muryarta har ya fara karyewa tana shirin ta fara kuka.

Abida mai taurin taurin zuciya amma yanzu rayuwa ta sanya duk ta yi laushi.

"Abida ina tausayin ki mana. Amma me ya faru ne?"

Bilki ta faÉ—a itama cikin damuwa ganin sauyawar Abida lokaci É—aya.

"Dube ni fa Balki. Magana ta gaskiya ki ji tausayina ki faÉ—a mini in da Ya Sulaiman yake in kin sani. Ki duba shekaru uku ba kwana uku bane, ba sati uku bane haka nan ba wata uku ba ne, don girman Allah ki faÉ—a mini in dai kin san inda yake Bilki.".

Abida ta faÉ—a cikin karyewar zuciya.

Bilki ta yi tsam tana kallonta cikin wani yanayi na tausayin Abida tare da madaukakin mamakin yadda take cikin alhini da kewar Yaya Sulaiman.

A sanyaye ta ce

"Wallahi Abida na rantse miki da Allah tun ranar da Yaya Sulaiman ya bar gida ban ƙara ji daga gare shi ba. "

Ta faÉ—a tana mai kallon Abida da ta yi tsuru kawai tana kallon Bilki.

"Ki yarda da ni. Wallahi da na sa ni da zan faÉ—a miki."

"Na yarda da ke Bilki. Shike nan mu bar maganar. Ba sai an ji ba"

Kawai sai ta fashe da kuka har da gunji, jikin Bilki ya yi sanyi k'alau itama bata san ta fara hawaye ba sai da ta ji danshi a saman kumatun ta.

Tare suka zauna suka sha kukansu, ita Abida tana kukan gararin rashin mijinta ita kuma Bilki tana yin na rashin Yayanta da tausayin Abida.

Tasan kuma danne abin take yi a ranta dan kada a fahimci fargar jajin da take ciki.

Ranar ma tare suka kwana bayan sun gama kukan su nan Abida ta bingire ta fara barci sai da asuba ta farka.

Haka rayuwa ta cigaba da garawa Bilki ta hak'ura da dukkan zuciyarta mussaman da fahimci ya'yanta basa cikin mawuyacin hali sai kewarta da suke yi. Kullum ne sai sun yi waya sau biyu sau uku.

Domin tana ganin yadda take shiga farinciki in ta ga Ya Faruku ko ta ji ana mganarsa har gobe Maigado ba ta daina son Ya Faruku ba, kamar yadda shima tana da tabbacin bai daina son ta ha amma dai a yanzu ne ta kasa gane yanayin shi tun da yadda yi ma Balki wani kulawa ta musamman.

Washegari ya kama Birthday ɗin Bilki ne sai ga wani kayataccen cake mai delevery ya kawo dauke da sunan Maigado at 36 ɓaro ɓaro a jiki. Mamaki ya kama Bilki domin kuwa ita gabad'aya ta manta da yaune ranar haihuwarta gabad'aya.

Ta dinga tunanin wa ya aiko da wannan tsadadden cake din?. Zuciyarta ta harba don kuwa take ta hasaso mata Yaya Asad. Don shine ya lank'aya mata Maigado har kowa ya kama, sannan shi ko kudi da yake raba musu a envelop lokaci zuwa lokaci Maigado yake rubutuwa a jikin tata. Koma wanenne ta ji dad'i don sai kana da muhimmanci a wajen mutum yake tuna alamuranka mussaman har a rike ranar haihuwarka, ita ta shaafa'a ma 1 ga watan Aprilu ce yau.

Abida na ta fad'in tasan Ya Faruƙu ne ya aiko da sh.

Itama Bilkin fata take yi ace daga Yaya Farouku din ne. Ta dinga jin farinciki na mamamyarta. Tabbas tana son Yaya Farouku zata jure komai indai zata same shi. Duk sababin Jamila wannan karon ba zata bar mata shi ba.

Duk da Balki jin ta kawai take yi amma ita jikinta ya ba ta ba kowa ya aiko da wannan cake É—in ba sai Ya Asad.

Nan da nan Abida ta yi wanka ta shirya cikin tsaleliyar Egyptian abaya ta()

Ta shirya junior. Da yake asabar ne duka muna gidan. Ta leko ta ganni kwance a gado Farha ma a kwance amma ta yi filo da cikinsa. Tana tambayar sauara kwana nawa su yaya Farouk su zo wajensu

Kafin Bilki ta amsa mata. Abida ta bude kofar. Ganinsu a kwance ba alamun komai ya snaya ta bude baki ta ce "Bilki wai ba shirya kuke yi ba dama?"

A sanyaye ta ce "Ni kawai ki dauko mu yanka anan. Me ya mini dad'i ne da zan tafi wani waje da sunan ina birthday!

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ta fad'a da alamun rashin sukuni.

Nan da nan Abida ta bata rai ta ce "Wallahi tunda na shirya sai mun je, ke ba dama a yi miki abin arziki sai kin gwasale mutum?"

A sanyaye Bilki ta mik'e ta ce "To jiramu mu shirya". Don tasan tunda Abida ta rantse to idan har bata kubutar da ita daga yin kaffara ba sai sun yi rikici mai tsananin gaske. Ita kuma a yanzu da suka shirya bata son su sake b'atawa da Abida.

Farha ta fara shiryawa cikin wani leshi Mai kyau Wanda aka yi masa kawataccen dinkin da ya sake fito da ainihin kyaunsa. Kai gaskiya telan d take bawa dinkin Amrah ta k'ware wajen iya d'inkunan yara.()

Ta fesa mata turare, sannan ta ce ta je falo wajen junior ta jirata.

Tunda suka dawo Abuja fir Farha ta ki sakewa da Abida. Duk da ko ina ta yi sai junior ya bita shi kam yana sonta tamkar yadda take son Yaya Farouk.

Ita ma cikin Egyptian abaya din ta Maman asalan da asala ta shirya ()

Ta kalli fatarta a madubi yadda farinta ya sake bayyana ga shi fatarta ta yi taushi ainun. Tunda matar Yaya Asad ta rasa rayuwarta a dalilin canja surar halitta da canja launin fata Bilki ta yi matuk'ar tsorata. Ta tsaya a iya mayukanta na oriflame da Aisha Lame ta zaba mata tun shekaru biyu da suka shud'e. Ta kuma gasgata ingancin products din oriflame. Babban abin da yasa ta likewa Aisha Lame saboda yadda ta nakalci rabe raben fatar dan adam tamkar wata shararriyar likitar fata.

Ta shafa hoda ta gogo man lebe a bakinta. Sai ta feshe jikinta da turarenta mai dad'in gaske.

Ta same su a falo tare da Momi. Suka yi mata sallama sannan suka fice tare da y'ayansu.

A motar Abida suka fice. Bilki a gaba yaran a baya yayin da Abida take tuki.

Kaitsaye millenium Park suka je. Suka dan yi chilling da hotuna. Sannan Bilki ta yanka cake tare da taimakon Farha.

Wani hoton da Abida ta d'auki Bilki ya yi matuk'ar yin kyau

Ta saka shi a status ta yi caption da cewa" Happy Birthday Maigado."

"Haka Mai gadon ta fita?"

Yaya Asad ya yi tagging hoton yana tambayar Abida.

Sai ya ga kamar kyan da ta yi, kamar kowa a wajen ita yake kallo. Kishi ya ji ya turniƙe shi from no where.

Ganinta a status din Abida duk sai ta sukurkuta shi ya ji ba zai iya sake wani dogon jira ba, yana son ya mallaki maigado cikin gaggawa kafin soyayyarta ta yi masa illa.

Abida ko da ta ga maganarsa sai ta tura masa emojin dariya.

"Haka muka fita dai."

Sai ta tura masa wanda suka ɗauka tare da Balki itama abayan ne a jikinta amma na ta ɓaka ce.

"Lalle zan zo na samu Baba Babba. Ya sake muku da yawa."

Haka ya ce mata ta bi shi da dariya.

Abida tana mamakinsa to menene abun da bai kyautu ba a tare da su?

Ranar sai dare suka koma gida washe gari dalleliyar motar ƙirar Toyata da Yaya Asad ya siya mata ta iso gida tunda Abida ta ƙyalla ido ta ga motar nan ta buga tsalle ta ce itama ba ta yarda ba sai an siya mata irinta.

"Tab lalle ne ma Yaya Asad É—in nan, tunda Bilki da dawo gidan nan ya manta da ni. Wallahi nima sai ya siya mini wacce tafi ta Bilki tsada."

Ta fad'a tana kumfar bakin ya yi son kai, tana shinshino wani abune a ransa game da Maigado.

Momi ta gaji da mitar Abida ta saka baki da cewa ita ba tana da mota ba, ya siya mata kwanaki baya.

"Ai itama Bilkin tana da mota. In adalci ne ya siya mana gabaÉ—aya mana."

Abida ta fad'a tamkar ta fashe da kuka.

Baba Babba ya dinga dariya yana fad'in" Abida rigima."

Duk da haka ba ta haƙura ba sai da ta bi Bilki har ɗaki ta tsare ta da tambayoyi.

"Bilki me yasa yaya Asad ya siya miki wannan motar?

"To ni ina zan sani, ki kira shi ki tambaye shi mana"

Bilki ta bata amsa tana cunno mata baki.

Abida ta yi jim kafin ta ce" Baku da gaskiya daga ke har shi. Kuma idan bai siyo mini tawa ba. Billahillazi abin da ya faru a 2022 zai sake maimaituwa a wannan shekarar da muke ciki."

"Ya dade bai faru ba Abida ".

Bilki ta bata amsa cikin murya marar amo.

"Haka kika ce ko Maigado?

Da ni kike zancen, Allah sai na fasa kwan ai tuni na harbo jirginsa."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tun daga ranar Abida ta fara tsokanta da Amaryan yaya Asad, yayin Balki ta yi ta masifa tana kufuluwa, don bata son wannan maganar ta yi tasirin da Yaya Farouku zai sake janyewa daga kud'irinsa akanta.

Dan haka kullum take bawa Abida amsa da fadin

"Allah ya tsare ni ya je can ya nemi amaryansa."

Abida kuwa bata fasa ba, don sosai take dariya idan ta ga yadda take fusata, ji take yi da auren Maigado da Ya Asad zai tabbata da tafi kowa farinciki da murna, amma tana ganin Bilki zata yi gardama, tunda ta lura da Bilki tafi son fararen maza.

Ya Faruku ma da ya zo ya ga mota sai da ya furta.

"Lalle Babban yaya alama da zafin sa ya kutso. Mu yara sai mu mu yi baya "

Balki ta ji zafin maganarsa sosai ta ɓata rai tana kallon shi kafin ta ce" Ya Faruku abin da za ka yi mini ke nan?"

Kana nufin abin da nake ga ni a idanuwanka wannan karon ma iska zai bi?"

Ya kasa bata amsa sai kawai ya tafi babu sallama.

Zuciyarta ta yi kunci bata yi zaton zata sake son wani namiji kwana kusa ba. Amma tabbas son Yaya Farouk ya kutso da k'arfin gaske daga inda ta sakaye shi a zuciyarta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ana cikin haka sai ga Yaya Asad ya zo gidan. Bilki na wajen aiki. Gidan ba kowa sai Baba Babba, Momi ta je asibit ganin likita a dalilin ciwon k'afa ya matsa mata. Dan haka suke ta hirarsu da Baba.Tsawon lokaci yana zaune so yake Baban ya ɗan taɓo masa maaganar aure sai ya kawo masa maganar Bilki amma shiru Baban Allah bai sa ya yi masa maganar ba.

Haka nan ya tashi jiki ba ƙwari . Ya yi masa sallama tare da ce wa gobe zai dawo ya duba momi.

Yana harabar gidan ya ga an bude kofar ya ga motar Abida ta danno. Ya tsaya har ta fito ta nufo shi suka keɓe daga shi sai ita.

Dama tana jiransa ne tana zuwa ta fara masa kukan me yasa ya siyawa Bilki mota ita bai siya mata ba. Kowa sai ya rika nuna ya fi son Bilki akan ta, haka ma Yaya Faruku yake yi mata tun suna yara yanzu ma sun girma ba a daina banbanta su ba.

Ya nisa ya ce "Ho Abida! Yanzu nutsu ki saurare ni da kyau. Zan siya miki mota irin ta Bilki. Wacce kala ki ke so?"

Ta shagwabe fuska ta ce "Golden".

"To zamu yi magana, idan kin ba ni gudunmawa akan lamarin to da wuri motarki zata iso".

Ta murmusa tana jin ba abin da ba zata yi masa ba.

Ya maze sosai sannan ya ce

"Abida yanzu ba za ki taimaka mini a halin da nake ciki ba,? Kin fa son har yau ina son Maigado ba sai na zo na faÉ—a ba ya kamata ki taimaka ki taya nemin soyayyarta ba sai na fad'a miki ba".

Abida ta kunshe dariyanta tana kallon yadda yayan nata ya yi wani laushi

Shegiya Bilki tasan gwara kan maza, mazan ma irin su Ya Asad.

"Abida ki yi wani abu in son na killace Maigado a gidana cikin lokaci ina matukar son haka in kika tabbatar da faruwan haka zan jiyar dake dukkan daÉ—in duniya ba mota ba har ko jirgi idan ina da hali zan siya miki Abidan Baba."

Abida ta ji wata dariya ta sake kawo mata wannan karon ta kasa dannewa sai da ta fito

"Abida na zama abin dariya ne?"

Ya tamba a kufule.

"Abida da gaske nake yi ba. Ina son Maigado.".

Ya faÉ—a yana bayyana mata yanayin da yake ciki tausayin shi ya kamata ta san cewa yana sonta tun suna yara idanuwan Bilki ne suka rufe a wancam lokacin saboda wannan yaron yanzu kuma bata son me yasa ta sake runtse idanuwanta akansa ba.

"Ya Asad kaima da taka matsalar fa gaskiya.'"

"Menene matsalan tawa faÉ—a mini zan gyara in dai Maigado za ta saurare ni."

"Matsalar mu mata bama son idan ana son mu a yi ta kewaye kewaye. Gwara kawai ka fito ka faÉ—a mata gaskiyan abin da yake zuciyarka. Ballatana yanzu Maigado ba yarinya ba ce ta san abin da take so ta san abin da ba ta so, gwara ka tunkare ta da full confidence ka faÉ—a mata abin da yake zuciyarka.

Ya yi shuru yana sauraranta kafin ya jinjina kai ya ce" Haka ne Abida na gode. Cake É—in nan da na aiko Maigado ta so shi kuwa?"

Abida ta yi wata dariya kafin ta ce' Daman kai ka turo shi,? Munafuka shi ya sa ta ƙi yin magana ashe ta san daga kai ne."

Dariya kawai ya yi bai yi magana ba.

"To kai Ya Asad ma kana da makamai a hannunka. Yanzu kawai harsashinka za ka dasa in ya shiga ka fara harbi. Ka samu lokaci ka zo ka ɗauketa ku je wajen da bakowa sai ku kaɗai ku yi magana. Ka jajirce ka nuna mata soyayya ɗan text massages ɗin nan na Friday da na good morning, sannan ka riƙa kiran ta a waya, kana nuna mata ita ce sarauniya duk yadda kake busy ka samu lokacinta sosai. Yadda za ta ji cewar aikinka bai sha gaban ta ba, idan kuma duk ka yi haka ka ga bata fahimta ba sai ka samu babanku ka faɗa masa, shi sai ya yi mata magana."

Ya Asad ya gyaÉ—a kai kafin ya ce" To kina ganin idan Baba ya yi mata magana za ta amince ne?"

Abida ta yi shuru kafin ta ce" Wallahi ban sani ba, ka san yanzu Bilki ta canza tunda ta yi deperession ta zama wata irin fitinanniya abu kaÉ—an ke sakata fushi da kuka, ni saboda yanayinta yasa bana ma shige mata kar na cika matsawa a samu matsala."

Duk ya aminta da mganganun Abida cikin kwarin gwiwa ya ce" Na gode Abida zan yi kuma amfani da shawarwarinki."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ta jinjina masa kai kafin ta ce' Allah ya ba a sa',a Ya Asad Ubangiji ya taka yaƙin nan."

Ta fada tana dariya shima yana taya ta.

Juyawa ya yi ya koma gaban Baba Babba.

Ya fara yi masa jirwayen cewa za a tura su seminar Lagos kuma daga can yana tunanin za a tura shi America domin samun horo kan matsslolin tsaron da muke fama da su a Nigeria.

Baba Babba ya kalle shi yana faÉ—in" Kai Asad a kullum ba ka da wata magana sai ta aiki. Aiki aiki dai ba ka tunanin ma sake ajiye iyali ko ba domin kanka ba domin mutumcinmu iyayenka da yayan ka, kana da yara yanmata da suka isa munzalin aure. Da bakinka ka ce mini iyayen manemin Aysha suna so zo tambaya, a haka zasu zo su same ka, ba ka da mata sai yawon an tura ka can aiki, an tura ka can, kana ganin zaman ka a hakan alheri ne?

Anya ka yiwa kanka adalci Abubakar?"

Ya faɗa yana kallon Asad ɗin da ya sadda kan shi ƙasa.

Sai da Baba ya dire faÉ—an sa, sannan ya É—ago ya gyara zema yana faÉ—in.

"Baba sai ka ta yi mini faÉ—a akan zancen aure. Alhalin bani kaÉ—ai ba ne bani da auran nan, ga yara nan a gaban ka. Gwara Abida da aure a kanta Maigado fa? Ai ba ta da aure amma ba a takura mata ba sai ni?"

Ya faɗa cikin ɗan ɓata rai shi a dole ba shi kaɗai ba ne.

Baba Babba ya karɓe da ce wa" Kai ba ka duba Bilki lallaɓata ake yi? Ta shiga gararin rayuwa kala kala ga rashin miji, ga mutuwar iyaye ga shi an raba ta da garin da yaranta suke yaka ke so ta yi? Ai Bilki abar tausayi ce, idan ba a rarrashe ta an gayyato mata farinciki ba me kake so a yi?"

Ya Asad ya ji daÉ—i an zo gabar da take so.

"To ni Baba ka bani ita na aura. Sai na taya ka rarrasan maka ita."

Ya faÉ—a yana sosa kansa alamun kunya.

Cikin mamaki Baba Babba ya kalle shi kafin ya ce" Asad da gaske kana son Bilkisu?"

Kansa na ƙasa ya ce" Wallahi Baba ina son ta, tsakanina da Allah!

Farinciki ya bayyana a fuskar Baba Babba.

"Idan kana son Balki to ka nemi yardarta idan ta amince, nima na amimce kasan yanzu ba yarinya ba ce tana da wannan damar sannan kar ka manta ko da suke yara ban yi musu auren dole ba bare yanzu tana da y'ancin ta yiwa kanta zaɓin da take so. Idan ta amince da kai to zan fi kowa farinciki zan kuma taya ka da addu'a Allah ya tabbatar. Idan har hakan ya faru komai zai daidaita, wakiar da ta nisantamu da juna zata bushe a zukatanmu. Ƴan'uwanta za su samu damar zuwa gidanka su yi zumunci, kai ma naka za su je gidanta, daga nan komai da ya faru na rashin jituwa a baya zai wuce ba na fatan na mutu na barku a cikin wannan halin. Sulaiman ya tafi ba mu san inda yake ba, idan yana raye Allah ya bayyana shi. Idan kuma ta san inda yake ta boye mana, idan ta zo hannunka kana hillatar ta duk za mu ji komai."

Yaya Asad ya ji ƙarfin guiwar tunkarar Bilki a wannan gabar tunda ya samu amincewar Baba Babba da Abida. Dama Abidan yafi ji da Usman amma tunda Abida bata botsare ba yasan Usman ba zai samu tallafi ba. Mamakin yadda Abida ta huce ta yi sanyi akan ahalinsu Bilki yake yi.

Da Bilki ta dawo ba wanda ya yi mata zancen zuwan Asad shi yasa ba ta san ya zo gidan ba. Shi kuma tun tafiyar shi kullum da safe zai tura mata sakon gaisuwar safe da asubar fari. Da daddare ma akwai na mu kwana lafiya. Ga k'iran waya akai akai, yana kashe murya yana yi mata kalamai irin na jirwaye duk da ta fahimci manufarsa amma sai ta nuna masa bata gane komai ba. Kuɗade masu nauyi yake turo mata akai akai, idan ta ce sun yi yawa ko ya daina. Ce mata yake yi idan Sulaiman ne ya tura mata kuɗi ai karba za ta yi ta gode masa, ba ta ce bata so ba jin haka yasa jikinta ya yi sanyi, bata sake ce masa komai ba, idan ya tura mata kuɗi sai dai ta yi godiya amma a cikin zuciyarta ta kudire yayaa Asad ba zai iya siyan soyayyarta da kuɗi ba. Kuma tana jiran ranar da zai gaji da ƙumbiya kumbiyarsa ya fito fili ya faɗa mata, daga ranar za ta fada masa ya daina wahalar da kansa don kuwa bata ra'ayinsa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: A ranar da take wannan tunanin ya yi mata sakon yana so ya shigo gobe tana gida? Ta amsa masa da cewa tana wajen aiki. Bai ce mata komai ba sai ta ɗauka tunda ta ce tana wajen aiki ya fasa zuwa ne.

Sai me? Washegari zuwan da yamma tana ma shirin tashi daga wajen aiki sai ga wayarsa har sau uku, ba ta É—auka ba sai da ya sake kira ta É—aga nan yake shaida mata yana harabar ma'aikatansu ta NAFDAC.

Mamaki ya kama ta, ta É—auka wasa yake yi sai da ta leka ta taga ta gan shi tsaye shi kaÉ—ai ba masu tsaron shi sannan kamar ba da mota yazo ba. Dariya ta kusa subuce mata ganin gogan ya ci k'ananun kaya har da uban zanzaro.

Dole ta tattara komai nata ta yi sallama da abokan aikinta ta fito haraba tana mai kallon Ya Asad tana danne dariyantan in har saboda ita ya yi wannan gayun, to ta gwasale domin ba ta jin zai sace zuciyarta da haka.

Ita ta É—auke shi a motarta suka bar haraban ma'aikatar. Cikin nutsuwa ta ce "Gida zamu je ko gidanka zan ajiye ka?"

Cike da kulawa ya ce "Yunwa nake ji sosai Maigado. Mu je L&N mu ci abinci ".

Zuciyarta ta harba amma ta had'iye komai. A hankali ta ce "To sai ka dinga nuna mini inda zan bi kasan ba ko ina na sa ni a Abuja ba. Idan kuma zaka karbi tukin to?"

Murya ba amo tsabar yadda ya shagala da kallonta tare da ayyana al'amura masu yawa akanta. Ya ce "Mu je zan yi guiding din ki in sha Allah ".

Bata ce komai ba ta cigaba da tukinta.

Bayan sun je sun natsu ya yi musu oder abinci daga ita har shi suka ci abincin domin itama yunwa take ji, kuma bai dame ta da magana ba sai da suka gama cin abincin suka natsa..

Sannan ya kalle ta yana sake gyara zama.

Bilki itama kallon shi take yi tana raya saka kananun kaya ba zai zama tawaya gare shi ba, tunda kullum cikin zanzaron kakinsu na yan sanda yake.

"Maigado."

K'iran sunanta da ya yi shi ya katse mata tunaninta.

"Na'am Baban Bilkisu."

Ta amsa tana kallonsa.

"Yau ga ni a gabanki ba a matsayin yayanki ba sai a matsayin masoyinki. Mai barar neman yardarki."

Ya yi shiru yana kallonta domin fahimtar yanayinta.

Ta yi k'asa dakanta tana wasa da zoben zinaren da yake hannunta.

Ya numfasa ya ce "Ina sonki kamar me, wani irin so nake yi miki da ba shi da alak'a da sha'awa, k'yale kyalen rayuwa. Tun kina budurwa nake sonki har yau din nan da kika zama uwar ya'ya ban ji son nan ya gushe ko ya ragu ba. Dan Allah Maigado kada ki bari ki sake subuce mini a karo na biyu. Ki ji tausayina ki kalli dinbin soyayyar da nake yi miki. K'addara ce mai karfi ta sake had'a mu. Idan a da kin k'i karɓar soyayyata saboda ina da mata, to Ubangiji ya sake hadamu a yanzu alhalin ba ni da mata. Ki ba ni dama na nuna miki dinbin soyayyar da nake yi miki Balkees".

Ta yi shiru ta kasa ce wa kanzil.

Maigado É—ago ki kalle ni.'

Ya sake faÉ—a cikin wani irin amo. Amo irin na ma'abota soyayya da bege.

A hankali ta É—ago tana kallonsa saboda jikinta ya mutu da kalamansa.

"So nake na killace a d'akina, na yiwa sauran maza kwalelenki. Dama É—aya nake so ki ba ni. Damar da zan mayar da ke sarauniya da ta yiwa mata dubu zarra. Don Allah Balkees kada ki tankwabar da soyayyata, na yi miki alkwarin za ki yi farinciki a tare da ni in sha Allahu."

Ya faÉ—a kamar ya yi mata kuka.

Bilki ta ga idan ta zauna tana jin kalaman bakinsa tausayinsa zai kamata ta iya ba shi dama, shi ya sa kawai ta haÉ—e rai tana kifta idanuwana kafin ta nisa ta ce

"Gaskiya Baban Bilki ka yi hakuri. Ba yanzu na shirya sake aure ba "

Ta fada kai tsaye tana kallonsa Gabansa ya faÉ—i murya na rawa ya ce'" Haba maigado, me yasa za ki ce haka? Ai ba za ki dauwama ba ki yi aure ba, tunda ya zama mahadin rayuwa kuma aurene mutuncin mutum mussaman mace."

"Ni dai gaskiya ka yi hakuri. Kai yayana ne shi ya sa ba zan so na ɓata maka lokaci ba."

Cikin mazarin jiki ya ce" Maigado ba za ki bukaci yin shawara ba?"

"Bana bukatar yin wata shawara na riga na faÉ—a maka matsayata."

Saboda kar ya sake yi mata wata magana ta É—au jakarta ta bar shi a wajen.

Yana kiranta, amma ba ta dawo ba, ta bar sa a wajen ta shige motarta ta kama hanyar gida.

Shi kuma hankalin shi ya tashi nan take ya kira Abida ya fada mata abin da ya faru.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "To ka bar komai a hannuna Ya Asad ba dai ka fada mata ba ai ka gama mai wahalan."

Daga haka suka rabu saboda damuwa da tashin hankali ma. Tawagarsa ya k'ira suka dauke shi tamkar yadda suka kai shi Nafdac office.

Abida kuma ba ta yiwa Bilki maganarsa ba ko da ta dawo, saboda ba ta so ta fahimci kamar za ta yi mata dole ne, amma tana lura da ita domin ta samu wata damar da za ta kawo mata maganar.

Kwana uku tsakani, ranar jumma'a bayan Baba Babba ya dawo daga masallacin Bilki ta zo wajensa suna hira.

A cikin hiran ne ya kalle ta yana fadin"Bilki ina son na yi wata magana da ke."

Bai ba ta damar maganar ba ya cigaba da fadin" Aure nake so na yi miki Bilki. Saboda ina son na ganki kin samu natsuwar irin ta aure, ko Abida da kika ga ban yi mata maganar aure ba ina ji a jikina Sulaiman na nan a raye kuma ina ji a jikina zai dawo in sha Allahu "

Bilki ta yi shiru kawai gabanta na faÉ—uwa.

"Idan har zai yiwu ina son na ba da auranki a karo na biyu Bilkisu."

Baba Babba ya sake fada mata..

So take ta ji wa kuma Baban zai aura mata.

"To Baba."

Ta amsa mishi tana son jin wane ne?

"Idan kin amince Asad zan aurawa ke. Ya zo ya duka mini da rokon na ba shi auranki, nima kuma na so ku da juna amma duk yadda na so abin idan har ba kya so, to ba zan yi miki dole ba saboda sharia ba ta ce na yi miki dole ba"

Bilki ta kalli Baba Babba ta kasa fadin uffan sai kawai ta fashe da kuka har da gunji kamar wata k'aramar yarinya.

*Surayya Dee*

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Cikin ruɗewa Baba ya ce" Subhanallah me ya faru kuma Maigado?"

Amma ta kasa daina kukan, yi take yi har tana gunji yana fidda sauti har sai da Abida ta baro ɗakinta zuwa falo domin ta ji kuken Balki sai ta yi turus ganinta durƙushe gaban Baba tana kuka, duk da ba ta san dalilin kukan ba amma a zuciyarta ta zargi kan maganar Asad ba ne.

"Daina kuka yi shiru Maigado. Ki faÉ—a mini matsalarki, Ai ba dole zan yi miki ba.

Ya faÉ—a cikin sigan lallashi ganin yadda Balki ta ruÉ—e da kuka kamar ranta zai fita.

"Baba."

Bilki ta kira shi da girmamawa

"Na'am Bilkisu."

Ya amsa mata cikin kulawa.

Kai tsaye ta ce" Baba don Allah ka bar wannan batun. Ni gaskiya kallon d'anuwana nake yi masa, bayan haka babu wata alak'a da zan k'ulla da shi".

Ta fad'a cikin kuka na sosai.

"Share hawayenki magana an barta. Amma abin da nake so da ke, dan Allah Maigado ki bawa masu sonki dama. Kada ki ce za ki juyawa aure baya. Aure sutura ne kuma mutunci ne. Allah ya yi miki zabin alheri "

Daga nan ya sallame ta ganin har lokacin ba ta daina kuka ba.

Abida ta ji haushin Bilki ainun ko kunya ba ta ji ba? A gaban Baba Babba za ta ce ba ta son É—ansa? Gaskiya Bilki bahaguwa ce ta k'arshe.

Ba ta nuna mata ba, amma dai ta rage mata walwala alamun ta hasala ita kam Bilki bata san tana yi ba, murna ma take yi tun da Baba ya ce an bar maganar tana son kuma zai dakatar da yaya Asad daga nacin da yake yi mata, shi ya sa ba ta ma kula da yanayin Abida ba, ballatana ta fahimci tana jin haushinta ne.

Ba zata yi auren da bata so ba.

Bilki ta sakankance Baba ya takawa Ya Asad Burki akanta tunda ta ce ba ta so, amma sai me? Sai ta ga ma kamar ya sake kunno kai ne zuwa gare ta da cewa ba gudu ba ja da baya kiran waya saƙonni haka zai baro wajen aikinsa ya zo mata yana takurata mata ita kuma ba za ta iya masa wulakanci ba da za ta iya wallahi da ta yi masa ko ya shafa mata lafiya.

Ranar juma'a ya tafi Auka ta jihar Anambra. Tun yamma yake k'iranta tana ga ni ta yi biris da shi.

Asabar tana idar da salla wayarta ta fara kuwwa. Tasan shine , ta k'yale. Sai dai Kiran ya cigaba da shigowa babu gajiya.

Ta gaji ta amsa amma a zafafe don kuwa ya yi matuk'ar shiga rayuwarta.

"Assalamu alaikum Maigado!

Ya fad'a cikin taushin murya sosai.

Ta amsa murya babu amo.

"Jiya na yi ta kiranki, baki dauka ba, sannan ba ki biyo baya ba".

"Ban samu lokaci ba ne".

Ta fad'a a gajarce tana tuna lokutan baya da take k'iransa da niyyar gaisuwar zumunci baya dauka sannan ba ya biyo sawunta.

Ya tausasa harshe ya ce "Yanzu Maigado ba za ki ji tausayina ki raba ni da zaman kad'aicin da nake ciki ba. Menene aibuna ne da kike ta yi mini yawon k'i tuntuni?"

Ya bata tausayi amma ta maze ta ce "Baka da aibu amma gaskiya Baban Bilkisu bana ra'ayin aure a yanzu, sannan ko zan yi to gaskiya ba da kai ba. Kallon yaya nake yi maka, ka yi hakuri kawai, mu bar shi a haka".

"Gaskiya ba zan iya hak'uri ba Maigado!

Ya fad'a da dukkan gaskiyarsa.

Ta hassala ainun tare da fadin

"Ni fa na ce bana yi, na faÉ—a maka, na faÉ—awa Baba kuma na san ya faÉ—a maka. To gaskiya ka shafa mini lafiya dan kuwa gaskiya ka takure ni ".

"E tabbas ya faÉ—a mini kin ce ba kya so na."

Ya faÉ—a cikin wani irin sauti marar amo.

"To kuma duk ka san da haka binbinin da kake yi mini na mene ne?"

Ta tambaya a fusace saboda ta gaji, yana takura mata da yawa.

Maimakon ta ji ya fusata ya ce ta yi masa rashin kunya. Sai ta ji yana fad'in "Saboda ina son ki. Ina son na killace ki a gidana shi ya sa na kasa haƙura na ƙyale ki."

Mamaki ma ya hana ta magana sai kawai ta yi masa shiru tana jin sa yana ta mata magiya cikin wata yar murya mai kama da nishi wai shi a dole sai ya ja ra'ayinta, shi bai san ma haushi yake ba ta ba.

Da ta rasa yadda zata yi da kasalar da yake haifarwa gangar jikinta sai kashe wayarta ta yi saboda gabad'aya nishinsa ya ruru mata jikinta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Duk wulakancin da take yi masa bai saka ya karaya ba. Ya dinga yi mata manyan kyautuka masu gigita tunani. Ana haka ya je Dubai. Sai ga shi ya siyo mata wani murtukeken bangle da zobensa kallo daya zaka yi ka gane zinare ne sannan ya lashe manyan kudade na gaske. A lokacin Momi ta farga ta gane Asad zawarcin Bilki yake yi ka'in da na'in.

Bata nuna adawa da lamarin ba, tunda ta san Baba Babba zai yi faricinciki idan al'amarin ya tabbata, tunda auren nasu ne zai ƙara daidaita zumuncin gidan da ya shiga halin ni y'asu.

Sai da ya fara nunawa momi tsarabar Bilki. Ta ga ni da walwala a fuskarta ta ce "Amma ina na Abida kasan tana ga ni zata hau rikici tunda Bilki kishiyarta ce".

Ya yi murmushi ya ce "Rabu da ita Momi sau nawa ina siyo mata? Ina ce bara ma da na je Saudiyya sai da ta ce na siyo mata sarƙa kuma na siyo mata. Bilkin ma dan ta gane da gaske nake yi ne ba wasa ba."

Ya kammala fad'a yana shafa kansa .

"To ma sha Allah, Allah yasa rabonka ce, zan yi farinciki da hakan."

Ta faÉ—a tana mirmishi, ba shakka idan ya samu Bilki ta san ya gama morewa.

"Amin Momi. Gata nan tana ta yi mini tutsu ki taya ni shawo kanta."

Ya fada cikin jin kunya.

"Ba ruwanmu a ciki. Ka cigaba da ƙokari in sha Allahu za ta amince."

Ya amsa da Allah yasa tunda kowa na ba shi k'warin gwiwa ai sarewa bana shi ba ne yanzu.

Bai tafi ba, yana zaune yana dakon isowarta.

A falo ta tarar da shi, shi kad'ai, fuska babu sukuni ta zube sosai ta gaishe shi tare da yi masa sannu da dawowa. Daga haka ta doshi k'ofar da zata shige ciki ta nufi d'akinta. Takaici ya mak'ure shi.

Ya bude murya ya ce "Maigado ke nake ta jira, zo ki ba ni mintina goma mu gaisa nasan a gajiye kike."

Kan dole ta dawo ta durkusa har k'asa daga gefe tamkar basarake gaban basarake. Ya yi tsam yana jin wulakanci ne kawia yake Sawa take yi masa irin haka.

"Maigado tunda na yi tafiyar nan nake ta mafarkinki. Yau kuma sai na yi mafarkin kin haifa mini boy".

Ta tsuke fuska sosai ba ta tanka masa ba.

Ya nisa ya ce "Wannan bacin ran fa? Ki daina yi mini haka mana dan Allah!

Ya tura mata k'aramar leda mai kyau wacce take d'auke da tambarin United Arab Emirates.

Ledar kanta abin sha'awa ce bare kuma kayan cikinta.

A sanyaye ya ce bangle da ring ne suka birge ni na siyo miki su a Dubai kin san k'asar suna da gold sosai".

Da k'yar ta bude baki ta ce "Na gode ".

"To ki bude mana"

A hankali ta ce "Ina fama da indigestion afuwan zan shiga ciki".

Ya mike da sauri yana fad'in "Sai na sake zuwa Maigadona".

Washegari kuma ya dawo da Kaya fal leda na Farha da su Amrah.

Da girmamawa ta ce "Hidimar fa ta yi yawa Baban Bilkisu dan Allah ka daina".

"To ni ai ba ke na siyawa ba. Ya'yana ne babu ruwan ki a ciki."

Sai ta kasa yin magana dole dai kanwar na k'i ta yi masa godiya.

Tunda ya dawo ta kuntatawa kanta ta daina walwala. Idan zai kwana yana k'iranta a waya ba zata dauka ba.

Idan ya zo gidan kuwa bata yarda su kebe. Ganinta ma sai idan ta dawo yana gidan to dole ya ganta, nan ma sai ta gabatar da uzzirin band'aki zata shiga. Daga haka kuwa ba zata yarda ta fito ba.

Abida ta Fara kufula da alamarinsu, yana tsananin son Bilki, ita kuma tana tsananin k'insa. To ya hak'ura mana shi da ake ta yi masa tallan y'anmata zabga zabga ma.

Wajen shadayan dare ta k'ira shi a waya. Da kaushin murya ta ce "Dan Allah dan girman Allah Yaya Asad ka hak'ura da Bilki haba na gaji da wulakancin da take yi maka."

Asad ya yi shiru yana jin ta.

Kafin ya sauke numfashi yana fadin" Abida ina son Maigado irin son nan mai wuyar a bar shi".

"To yaya Asad za ka yi ta bin ta ne tana maka wulakanci? Da girmanka da darajarka!

Abida ta fada cikin hassala.

"To ya zan yi! Allah ne ya jarabace ni.".

Idan ba za ki taimaka mini ba kar ki ce na daina bin Maigado Abida."

Ya fada kamar zai yi kuka, sai ya bata tausayi.

"Ya Asad tunda har ka yi mata magana ba ta amince ba, Baba ma ya yi mata magana ba ta ji ba to mafita daya ne yanzu ya rage."

"Mene ne mafitan Abida?'

Ya tambaya a sukwane.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Ya Faruku ne. Shi ne kadai mafitar da ta rage maka. Idan kuma ka gwada a bangarensa ba a dace ba to ka rabu da Bilki ba za ta amince ba Wallahi."

Shiru ya yi kafin ya ce" Kina ganin idan Faruku ya yi mata magana za ta amince?

"Tabbas domin nan duniya Bilki tana ganin girmansa da mutuncinsa, sannan komai ya yi mata umarni tana yi, amma idan dai har shima ka tura shi ba ta amince ba am sorry to say Ya Asad ka haƙura da ita kawai."

TafaÉ—a cikin ba shi tabbacin haka.

Shi kuma ya ce mata ya yi mata alkwarin idan har ya turo Faruku ba ta amince ba to zai hakura da ita.

Da haka suka rabu da Abida. Da maganar ya kwana a cikin ransa gari na wayewa, ya kira Faruk ya ce masa ya zo gida ya same shi yana son ganinsa

Faruku bai kawo komai ba tunda daman yana kiran shi a gida su zauna su tattauna.

Sai dai yau ya ga bambamci domin Asad É—in wani mazurai ya fara yi masa yana tsare gida sannan ya fara masa wasu tambayoyi.

"An ce mini yarinyar nan Maigado na jin maganar ka ko?

Sannan idan ka bata shawara tana karɓa?"

"Haba kwamishina ba girman ka ba ne. Wannan muzaran fa? Faruku ne fa? Ka yi maganarka kawai in sha Allahu ina tare da kai."

Ya Asad na jin haka ya gyara zama yana fadin" Faruku ba za ka taimake ni ba, tunda dai tana ganin mutuncinka, ka taimaka mini na samo kanta, kana ganin ina zaune ba mata kuma burinku na yi aure, itama tunda ba mijin gwara mu haÉ—u mu sanya Babanmu farinciki, tana ta wahalar da ni, na kuma san idan kai ne ka ce kana sonta, ba za ta yi maka haka ba, kuma tunda har ka ambata ka bar mini ita, ka taya ni mana ni na same ta, ko hankalina zai kwanta ina son ta Allah ya sani an jarabce ni akanta. Ina son ta kuma zan cigaba da son ta har abada, wallahi zan rike ta amana da gaskiya, kuma na yi maka alkawarin zan sanya ta farinciki. Don Allah ka taimaka mini Faruku na aminta da kai a cikin y'anuwana na sake jin ce wa kai na musamman ne daga lokacin da ka hakura da ita saboda ni, ka haramtawa kanka ita saboda ni, na kuma shaida ka yi mini kara da kyautatawa mai yawa"

Hankalin Faruku ya tashi idanuwansa suka kawo k'walla.

Ba domin Asad ba, da shima ba gudu ba ja da baya akan Bilki sai dai ya shaida kuma ya san ce wa Aasad ya fi shi sonta, ya fishi buk'atar mace a kusa da shi, ita ma kuma tana bukatar namijin da zai so ta ya kula da ita, ta samu gidan da za ta huta wahalarta ta baya ta shafe daga tunaninta.

Nan take ya ce masa kar ya damu ya ba shi lokaci in ya yi magana da Bilki zai neme shi domin ya ji yadda suka yi.

Asad ya yi ta masa godiya har ya ji kunyan shi ya É—an daÉ—e a gidan suna hira kafin ya yi masa sallama ya tafi yana fita ya kira ta a waya suka yi magana. Ya fad'a mata zai tura mata wani adireshi za ta zo gobe da yamma ta same shi akwai wata maganar da za su yi tunda asabar ce babu aiki.

Bilki na ta murna kamar an biya mata hajji, a tunanin ta yaya Faruku ya gaji da boye boye zai bayyana mata sirrin zuciyarsa kwana ta yi farinciki ita dai fatanta ta rabu da maitar Yaya Asad.

Washegari bayan la'asar Bilki ta sha kwalliya ta yi kyau har sai da Abida ta zolaye ta da cewa ko wani bazawarin ta samo musu? Sai ta ki magana ta fice tana ta dariya farincikinta ya kasa boyuwa.

Wani garden ne inda Ya Faruku ya tura mata nan ta nufa da taimakon map ko da taje ma ya riga ta isowa.

Bayan sun gaisa sun yi hira sannan ya gangaro kan batun da ya zo da shi.

"Bilkisu."

Ya kira sunan ta ta amsa cikin dakewa.

"Naam"

Ta amsa cikin shauƙi.

"Kina da burin sake komawa gidan uban ya'yanki?"

Kai tsaye ta ce masa "a a ba ni da wannan fatan har abada."

Ita fa murna kawai take yi anzo wajen. Yau Ya Faruku zai furta yana son ta. Ita kuma yana cewa yana sonta za ta amsa, ta kuma ce ya faÉ—awa Baba Babba sati daya ma ya isa su yi auransu.

Ya faruku ya yi shuru yana kallonta kafin ya ce" Kin tabbata kin hak'ura da Sahal?"

Ta sake ba shi tabbacin ita fa ta hakura sannan ta kara da cewa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Ni fa Ya Farouku ba ka san ma wata mgana ba. Ko Alti ba ta sani ba. Aurena da Sahal ya haramta. Saki biyu ya yi mini ni kuma na saka shi ya karishe mini dayan saboda wani dalilina da ba sai na fada maka ba."

Jikin Ya Faruku ya sake yin sanyi ya kalle ta yadda take kallon shi tana mirmishi. Jira kawai take yi ya furta ta amince masa.

"Bilkisu!

Ya sake k'iran sunanta a nutse sosai.

"Na'am"

Ta amsa cikin zakuwa.

"Maigado idan na yi iko da ke za ki yarda na isa na yi din ne! Ba za ki ga na so kaina ba?"

"Ba wannan tsakaninmu yaya Faruku ka isa da ni kada ka yi kokwanto"

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Ina so na bada aurenki "

Bilki ta yi kaseke tana kallonsa saboda ba haka ta yi tsammanin ji daga gare shi ba.

"Ga wa?"

Ta tambaya cikin mamaki k'warai da gaske.

"Ga Yayanki Asad"

Hawaye suka kece mata, ta kasa magana saboda ya shammace ta irin sosai din nan ".

"In dai kin aminta da kaunar dake tsakaninmu. To ki sani ba zan cutar dake ba, ba zan yi miki sanadin wahala ko tozarci ba".

A wannan karon kasa amsa masa ta yi.

Ya sake tausasa harshe cikin rarrashi ya ce "Ki duba ni, ki amince ki karbi auran nan da zuciya d'aya ki jira ki ga yadda Ubangiji zai karrama rayuwarki."

Bilki ta fara kuka mai sauti tana fadin" Ya Farouku me ya sa ba kai ba?

Me ya sa ba ka ce kai ne za ka aure ni ba ? Kana cutar da ni. Tun ina budurwan kasan ina son ka, kai ma na san kana sona amma saboda wani banzan dalili ka haramta mans cikar burinmu. Yanzu kuma bayan na dawo ka daÉ—a ja na a jiki ka sanya mini sonka da mararinka, ina ta tunanin ce wa wannan karon zan same ka mu yi rayuwa tare. Zuciyata tana girmamaka tana sonka, shi ne za ka zo mini da wannan maaganar alhalin ina jin nauyinka. Ni dai gaskiya tunda ba sona kake yi da gaske ba, to kawai mu bar shi a hakan, ka bar batun mutumin can".

Ta gama fada tana kuka wurjajan kamar wata karamar yarinya.

Hankalinsa ya tashi ya ji ina ina ma da ace zai iya da shima ya murza hularsa ya fito zawarcinta amma kuma ina ba zai iya ba.

"Bilki ki yi hakuri don Allah ki saurare ni".

Ya fada cikin karfin hali kafin ya cigaba da fadin.

"Ba ki ga gwara na zauna a matsayin danuwanki yafi akan mu yi aure ba?

Ana iya yin aure a rabu duk matsananciyar soyayyar da take tsakani kuwa. Amma duk lalacewar zumunta ba'a rabuwa gabad'aya, ba yadda za'a yi ace mini tsohon yayanki ne, saboda har abada ba za'a rabu ba, duk hargitsin rayuwa kuwa. Ina sonki sosai, ina kaunar ki har cikin zuciyata ina mana fatan Allah yasa mu cikin masu soyayya saboda shi wanda sakamakonsu aljanna ne. Sau tari rayuwa tana zuwa mana ba yadda muka tsammace ta ba. Ba sai mun yi aure ne cikar soyayya ba Bilki! Don kuwa ina tabbatar miki ko kin rasa kowa a duniya ki ji a ranki kina da ni ".

Jikinta ya yi laushi zuciyarta ta narke mussaman yadda ta ga k'walla ta cika idanuwansa ga soyayyarta ta bayyana a cikin idanuwansa da gangar jikinsa gabad'aya.

Hakan da ta ga ni ya sake sanya kukanta ya tsananta ta dinga goge hawaye da majina da tissue.

Yayin da jarumtar Yaya Farouku ta k'wace don kuwa hawayen shi ma yake yi ba tare da ya ankara ba. Ya yi maza ya zaro tissue ya goge idanuwansa.

Tsawon lokaci sun kasa ce wa komai, fama kawai suke yi da tafasar zuciya. Sai shine ya sanya jarumta ya ce " Ya kike ganin za a yi yanzu Bilki?"

Cikin shakewar murya ta ce.

"Ni kam wannan bawan Allah ya matsa mini. Tsakani da Allah ya zalunce ni! Ya je ya nemi wata mana. Dole sai ni, tsofai tsofai da shi zai ce yana sona "

Ta faɗa cikin taɓara da shagwabar da ta sake narkar da zuciyarsa.

Dariya ya yi kafin ya ce" To ban da abin ki Maigado ai ni da Asad É—anjuma ne da É—anjummai ni nake binsa fa, shekaruna da nasa gaf suke ai".

Cikin shagwaɓa ta ce "Ni ina ruwana ko ka girme shi ni dai kai nake so ba shi ba."

Ya kalle ta yana sake yin dariya kafin ya ce" Maigado ba kara, ba ki ji kamar zan ji wani iri ba, a gabana kike kushe Kwamishina?"

Tana hararan shi ta ce" Oh Yaya Faruku nuna mini kake yi wata kusan ta fi wata ko?

Da sauri ya ce" Ba haka nake nufi ba Bilkisu ki yarda da ni".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "To yanzu ya ke nan kin amince na ba shi auranki?"

Tana tura baki tace" ya ci arzikin ka, ba dan ina sonsa ba"

"To na gode da nake da arzikin da zai ci. In dai zaki zauna lafiya ki ba shi farinciki ki mutunta shi, ki girmama shi ai kin gama mai wuyar son da yake yi miki ya isa ya rike auranku."

Haka ya zauna yana ta faman lallashintaa da ban baki har ta saki jiki ta ce ta amince.

Sai gab da mangriba duka suka bar wajen kowa ya shiga motarsa, kafin su rabu sai da ya sake jin ta bakinta ta ce ta aminta.

Tana mota ma kafin ta kai gida sai da ya kirata.

"Bilki kin aminta da kwamishina ba sauya magana?.

Kaitsaye ta ce" Na amince yaya Faruku."

"To zan turo shi "

Ya faÉ—a yana yar dariya.

"To amma ka faÉ—a masa bana son wannan k'ananun kaya da yake sanyawa ya ci zanzaro ala dole shi bai tsufa ba. Ka fada masa ya saka native wears gaskiya."

Ta faÉ—a tana tura baki kamar yana ganin ta.

Dariya mai k'arfi ta k'wace masa sosoa.

"Abida ta koya miki iya shege gaskiya"

Ya fad'a cikin dariya sosai.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "E mana da girmansa amma sai ya wani tsuke sannan ga naci kamar me haba!.

Ya Faruku yana dariya yana sauraranta.

"Bilki bar cika baki kada wani lokaci na ga kina bare bare a kansa fa".

Ta ce "idan zan yi din saboda kai ne amma ba wai don ina sonsa ba.

Shi dai ya yi mata godiya sosai da ta yarda ya isa da ita.

Ya ce "zai zo in sha Allahu"

Da haka suka yi sallama.

Tun yana hanya ya k'ira shi.

Daidai lokacin yana office d'insa shi kad'ai ya kishingida akan kujera sai tunanin me zai biyo baya idan har Faruk bai iya shawo masa kanta ba.

Kwatsam k'iran Faruk din ya fado cikin wayarsa.

Ya dauka da zumudi sosai.

"To Magana ta zaunu sai ka shirya ka je ku tattauna sosai

"Da gaske mun yi magana kuma ta amince."

Asad ya fara murna yana ta godiya.

"Me kake son na yi maka a matsayin godiya Faruku?

"Ba sai ka yi mini komai ba. Ni ai ba abin da ba ka yi mini ba. Amma ta ce na fad'a maka ka daina yin wannan zanzaron idan zaku hadu, domin ba zai boye tsufanka a idanuwanta ba".

Ya kammala fad'a masa cikin matsananciyar dariya.

Shi kansa Mai girma kwamishinan y'an sanda dariyar ce ta k'wace masa tare da tunanin wato ga ni take yi ya tsufa? Ya jijjiga kai tare da alwashin da kanta zata yi alkalancin ya tsufa ko akasin hakan.

Ya matse ya ce "Wato na fara gasgata Abida da take yawan fad'in "Tsiyatakun Bilki sun fi nata tsanananta, kawai ita a nutse take yine sabanin Abida yar hayagaga."

Faruku dai dariya yake yi kawai don sosai batun ya sanya shi darawa.

Daga nan suka yi sallama.

Haka ta koma gida sukuku kamar ba ita ce ta fita da farinciki ba yanzu shike nan Yaya Asad za ta aura ko a mafarki ba ta taɓa hasashensu a matsayin miji da mata ba domin ba ta sonsa, bata son bak'in namiji amma yaya Faruku ya wuce komai a wajenta shi ya sa kawai ta amsa masa.

Yanzu tana amsa wayarsa amma sau biyu. Idan ya k'ira da asuba zata dauka sai kuma da daddare. Amma da rana ko da yamma har ya yi ya gama bata dauka bare ta ji me zai ce.

Duk dare sai ya tambaye ta yaushe zai zo su tattauna? Ta ba shi lokaci.

Kullum fada masa take zata duba ta ga ni.

Ya gaji da yawon da take yi masa da hankali. Hankalinsa a tashe ya k'ira Farouku.

"Farouk anya Maigado kuwa ta amince da gaske? Har yanzu fa ban ga wani sauyi da zai tabbatar mini ta amince ba. Ta bari mu had'u ma yarinyar nan ta k'i fir ".

Da mamaki Farouk ya ce "Ban jin Bilki zata yi magana biyu amma zan tuntube ta."

Ya katse wayar ya k'irata.

"Yanzu Bilkisu dama dad'in baki kika yi mini? Sai wahalar mini da dan'uwa kike yi, kuma ke kika ce na turo shi fa. Ban san ki da magana biyu ba sarauniyar shaiba. Dan Allah yau zai zo, ko gobe?"

"To ya zo gobe da yammaci ".

Ta ba shi amsa murya ba amo bai damu ba ya hau yi mata addu'ar fatan alheri.

Tunda ta bawa Yaya Asad damar zuwa take cikin damuwa amma ranar da zai zo bai hana ta yin kwalliya ba. Abida na ganin komai amma ba ta yi magana ba, tana ganin Bilki ta sha kwalliya a ranta tace munafuka ta ce bata so kuma tana kwalliya, domin duk halin da ake ciki yaya Asad ya k'irata ya fada mata har zuwansa na yau da zai yi.

Shi yasa da zata fi kai Momi asibiti ta tafi da yaran don kuwa Farha ba yadda zata yi ta zauna a d'aki ba sai ta ce sai ta bita.

Amal da Noor kuma idan sun ga babansu suma ba zasu bar shi ba.

Karfe huÉ—u da rabi ya iso gidan ya ci gayu ya sha babban riga kamar yau ne ranar auren.

Da farko bai shigo ba a haraba ya tsaya ya kirata wai yana waje ita kuma ta ce ba za ta fita ba ya shigo falo.

Ya sassauta ya ce "Su Baba na ciki fa!

A gajarce ta ce"Bamu da gaskiya ne? Sannan Baba na ciki Momi kuwa ba fitowa zata yi ba".

Ganin ta dage tana jero masa hujjoji ya fahimci ba zata fito su zauna a harabar gidan ba. Dan haka ya shiga falon da shine farko a gidan.

Kunyar Baba da Momi yake ji amma tunda haka Maigado take so, dole ya bi ra'ayinta tunda shawo hankalinta yake yi.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:43]

Ya jima yana zaune, yana yi yana duba tsadadden agogon da yake daure a hannunsa ƙirar Rolex.

Yana tunanin yadda mata suke son shanya masoyansu da sunan jan aji.

Mintina kusan talatin yana zaune shi kad'ai yana dakonta. Ban da rashin mutuncin soyayya ya za'a yi yarinya kamar Bilki ta dinga yi masa haka. Shi da idan yana cikin kakinsa dubban zarataan maza suke kame masa tare da sara masa. Amma ita ganinsa take yi tamkar takalmin sawarta.

Ya numfasa a fili ya ce "Mata ne jarabawar mazaje a duniya". A hankali ya dinga jiyo k'amshinta na turaren oils na mkbees perfumery da baya jinsa a ko ina sai wajenta na iso shi kafin ya jiyo sautin takunta cikin nutsuwa.

K'amshin ya yi matuk'ar saukar masa da kasala da bege.

A ransa yake fad'in Ko ina take samo wadannan turarukan?

K'amshinta na sake mayar da ita yar gayu ta sosai.

Mkbees perfumery na kawo muku oils perfumes masu matuƙar dad'i da Zama a jiki.

Mkbees sun yi fice wajen sanin sirrin gayu don kuwa kamshine Kan gaba wajen mayar da mace mai aji.

Mkbees Perfumery .Kano 07032456061

A hankali ta iso ta zauna bayan ta yi masa sallama a hankali. Ba ta yi masa magana ba sannan ba ta kalle shi ba ta juyaar da fuska tana tura baki.

Shi kuma ya shagala da kallon ta domin ta yi kyau sosai sai tashin kamshi take yi.

Material din Malaysianfabrics da take gown da su suna matuk'ar yi mata kyau.

Bai san ya shagala da kallonta ba sai da ta É—an kalle shi kafin ta ce" Ni don Allah ka daina yi mini wannan kallon bana so."

Ta faɗa cikin yar shagwaɓa kamar wata yarinya.

Gabad'aya duk ta sukurkuta shi, ya neman rasa yar natsuwan shi.

"Mai gado kin yi kyau ne. Kamar na sace ki zuwa gidana."

Harararsa ta yi ta gefen ido, tare da juyar da manya idanuwanta . Hakan ya kara masa nishaÉ—i. Ya yi dariya ya ce

"Ko yau Baba ya É—aura mana aure kawai Maigado?

Ta kalle shi da mamaki amma bata ce komai ba .

"Allah Maigado ina cikin tsananin buk'atar na yi aure. Kin san ni ba yaro ba ne, na dad'e ba na tare da mace, ke ma kuma a irin takalmina kike ko?"

Ya faÉ—a har yana rage murya.

Kunya ya kamata ta yi maza ta yi k'asa da kanta kafin a hankali ta ce " Ni ba ruwana"

Dariya ya sake yi kafin ya ce" Da ruwan ki kuwa Maigado".

Shiru ta yi masa yana ta sakin layi, wanda mamaki yake ba ta, ko kunya ba ya ji daman haka yake? Yaya Asad ne a gabanta yana kunyata ta amma shi ko a jikinsa, kai maza da abin kunya suke.

Kan dole take zaune yana ta kunyatata.

Ita ke jin kunya amma shi ko a jikin shi.

Suna cikin haka Baba ya fito zai fita tattakin da yake cikin unguwar da yammaci, ya gansu a falo, ya kalle su ya yi dariyarsu ta manya kafin ya ce" A a garin yaya haka Asad ka zo zance gidana amma ba ka nemi izinina ba?"

Ya fada yana mai bayyana murnar ganinsu har a saman fuskarsu.

"Baba Faruku ne ya ba ni izinin zuwa, har aurenma ya ce ya ba ni."

Baba Babba ya yi dariya kafin ya ce" To to haka aka yi? Lallai kuwa tunda Faruku ne ya baka to Bilkisu ta badu babu tantama. Dole kuwa ka ce masa Baba ".

Shi da Yaya Asad suna ta dariya Bilki ta yi gum fuskarta a k'asa nan Baba ya fita haraban gidan ya bar su. Ya Asad na cigaba da zolayarta idan ta turo baki sai ya ji ya fara mazari kamar ya kamata ya matse ya tsotsi bakinta amma ba hali sai dai yana fatan lokaci kaÉ—an ne zai yi hakan ta halastaciyar turba.

Haka dai aka gama zancen tana ɓata fuska da zai tafi ya ce su je mota ya bata sako, dole ta bi shi ya bata leda cike da kayan kwalliya da dogayen riguna, ta karba tana godiya ya shiga mota yana fadin" Maigado ki bar tura baki kwana nawa ne? Ni fa ko yau aka daura na shirya "

Nan ta bar shi yana ta kiran sunanta ta yi bakam ta wuce cikin gidan, don tasan yana yanko mata zancen da sake kunyata ainun.

Da daddare tana kwance Farha na gefenta tana barci. Ya k'irata ta saka hannu ta dauka tare da sallama.

A hankali ta ce "Ka je gida lafiya?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:53]

A sanyaye ta ce"Hakane Baba amma dai ka sanar masa din zan fi samun nutsuwar zuciya."

"To Zan fad'a masa a yau din nan Maigado ".

Ta Numfasa ta sake ce wa "Sannan dan Allah Baba zan je Katsina na bar kayayyakina masu muhimmanci a can, ina son na je na harhadasu tunda muka taho gidan a rufe yake".

"To shike nan zan yi magana da Faruku sai ya kai ku tare da Alti ku yi kwanaki biyu ko uku".

Daga haka sallame ta yana cigaba da yi mata addu'o'i masu dadi da sanya farinciki.

Kwance yake kan tafkeken gadonsa yana waya da babbar diyarsa Aysha da take shirin kammala Bar school ta Enugu.

Cikin nutsuwa ya sanar mata upper week zai tafi America daga can zai biya London ya ga Khadija.

Juma'a mai zuwa kuma zai daura aure.

Zuciyarta ta harba da tsananin gaske.

"Aure Daddy! Da wa kuma?"

Ta tambaye shi a rude don har cikin zuciyarta ta ji wani irin kishi mai tsananin gaske ya shak'e ta gabad'aya.

A hankali ya ce mata da "Anti Maigado ".

Ta yi shiru tabbas watanni biyu da suka shud'e ta tarar da ita a gidan Momi. Ashe aurenta ne ya mutu ba wai jinya kawia take yi kamar yadda Anti Abida ta fad'a mata ba?

A sanyaye ta ce "Amma Dady su Mama ba sun ce sun baka Anti Laura ba?"

Da sauri ya ce "Ai na fad'a musu ba zan iya aurenta ba domin kallonta nake yi tamkar yarinyar da na haifa. So ba zan iya aurenta ba".

Ta kasa magana amma tabbas ba ta ji dad'in hakan ba. To Akan me ma zai sake aure yanzu shekara d'aya kacal da mutuwar mominsu!

Kan dole ta ce "Allah ya sanya alheri. "

Ya amsa da "Ameen"

Ya numfasa ya ce "Ina fatan babu matsala ko damuwa?"

A hankali ta ce "Babu komai Dady".

"Stay blessed sai mun sake magana".

Da ga haka ya katse wayar.

Jikin Aysha ya yi mugun sanyi bata san dalilin da ya sanya ta ji wani abu ya soke ta da ya ce 'Anti Maigado zai aura ba'.

Kamar yadda Baba ya fad'a yaya Farouk ya kaisu Katsina. Farha tana ta murnar zata ga su yaya Farouk. Kaitsaye gidanta suka yada zango. Komai tsab sai dai gidan ya yi kura. Cikin gaggawa Alti ta hau gyaran gidan tamkar ba gajiyar tafiya a tare da ita. Sai da komai ya yi daidai sannan ta D'ora girkin abin da zasu ci. Nan da nan gidan ya kaure da k'amshi. Daidai lokacin Yaya Farouku ya dawo daga masallaci. Ya zauna a falon ya bude murya ya ce "Alti saboda Allah da wanne irin abu kike girki ne? Gabadaya layin ya cika da k'amshin girkin dan Allah fad'a mini abin da kike zubawa Idan kina girki dan na siyawa Jamila, don k'amshi da nake ji a gidana idan ana yin girki bai haka dad'i da k'arfi ba, tunda na doso kusa da gidan fa hancina yake shakar k'amshin dad'i ".

Ta fito da robar curry da spice's din Amreesh spice's Kano ta ce "Ga wasu da Ga cikinsu tafi da su a fara yi maka don nasan Mahma zata siya amarya package".

.......

Ya kwashe da dariya yana fad'in "Ashe haka Alti ta iya turanci ban sani ba?"

Ta koma kicin ta kawo musu abinci falo sannan ta shige d'akinta don ta yi wanka da sallah.

Cikin nutsuwa Bilki ta zuba masa ta saka cokali ta ba shi sannan ta zubawa kanta. Farha tuni ta yi barci don Indomi aka fara dafa mata tana ci kuwa bata jima ba ta yi barci.

Ya kammala cin abincin da ya yi masa kyau a ido, ya cika hancinsa da k'amshi, ya yi masa dad'i a baki. Ya nisa ya ce zan saka kudin spice's din nan a asusunki sai ki yi muku order tare da Jamila."

A nutse ta ce "To". Ko godiya ta kasa yi masa don haka siddan ta ji wani irin abu ya turnike ta mussaman da yake ta ambaton sunan matarsa da son sai dandanon girkinta ya yi irin nata.

Daga haka ya mike ya yi mata sallama zai tafi masaukinsa ya huta shima.

"Idan Alti ta fito ki ce mata na tafi sai gobe zan zo da rana dan haka kada ta yi abin karyawa da ni".

"Allah ya kaimu ka huta gajiya". Bilki ta fad'a a takaice tana jin haushin Jamila da na Yaya Asad na kutsowa tunda ga k'asan zuciyarta. Don tabbas sune mutane biyu da suka yi mata shamaki da samunsa. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:55]

Ya fita bai sake ce wa komai ba don ya lura so take ta hargitse tunda suka iso komai yake neman k'wace mata.

Tana jin sautin takunsa a kafar bene ta ja dogon tsaki tare da fad'in "Yan ta'adda kawai masu son kansu"

Daidai lokacin k'iran gogan nata ya faÉ—o wayarta. Tana kallo har ta katse bata d'aga ba don sosai ta ji haushinsa ya dirar mata. Sai dai cigaba da kiran ya yi, akan dole ta dauka ta yi sallama murya a mak'oshinta.

Yayin da hakan ya jefa Asad cikin wani irin yanayi.

Ya yi k'asa da muryarsa ya ce"Ba ki da lafiya ne?"

ke nan?".

"Lafiyata k'alau".

Ya nisa ya ce Saboda Allah Maigado za ki yi tafiya sai dai na ji a bakin Farouku. Da safe ma mun yi waya na ji alamun a mota kike, na tambaye ki, inda za ki je kika ce wajen aiki, ashe Katsina za ki tafi shine ban isa ki fad'a min ba ko? Amma ni da zan taho Lago din nan sai da na fad'a miki tun ana gobe zan tafi, ina cikin jirgi kafin na tashi ma sai da na sanar da ke ".

Haka kawai ya fad'a ta ji ta harzuk'a tunda dama haushinsa da na Jamila ke ciciiyarta a daidai lokacin.

Dan haka ba tare da ta tauna kalamanta ba ta ce "Amma ai ban rok'e ka, ka fad'a mini ba, sannan akan me duk abin da zan yi sai na fad'a maka?".

Jikinsa ya yi sanyi k'alau tare da tunanin ko ya yi mata wani abu ne?

A sanyaye ya ce "Me yake faruwa ne Maigado?".

"Kamar na me fa?"

A hankali ya ce "Sai da safe".

Ba tare da ta amsa ba ta yi maza ta riga shi katse wayar.

Yana kwance shi kad'ai kan makeken gado na alfarma cikin tsadadden hotel a birinin na Ikko.

Ya yi sororo da waya a hannunsa a fili ya ce "Tooh! Zuciyarsa na bugawa tare da kitsa masa ta je Katsina ta ga mijinta da ya'yanta shine zata birkice ta nemi juyawa maganarsu baya? Ban da haka bai ga dalilin fishi da fisgar da ya ji a tare da ita ba.

A fili ya ce "Allah ka k'addara mini auren yarinyar nan, Allah ka sa rabona ce".

Don gabadaya hankalinsa ya yi mugun tashi. Tunda yasan ba sonsa take yi ba komai na iya faruwa.

Tun Daren suka yi waya da su Amrah ta fad'a musu ta zo garin.

Sassafe Babansu ya dawo daga masallaci Amrah ta tsaya a falo. Ta gaishe ta ce "Dady dan Allah anjima ka kaimu wajen Mahma ta zo kuma ta ce ba zata dade ba, zata juya".

Daidai lokacin Faruk ya shigo falon.

Da sakakkiyar fuska ya ce "To ku shirya tunda hutu kuke yi anjima zan kai ku ranr da zata tafi sai ku dawo".

Dad'i ya kamasu suke ce "Mun gode".

Ya haye sama don yanzu kan dole idan ya dawo masallaci yake hawa saman tunda Hawwah ta kafe kwana Kawai zata yi a k'asa amma ba zata yarda ta dinga biyo shi da abinci ko wani abu daban k'asa ba tunda bata d'aki a gun. Dan haka ya amince dan ra'ayinta tunda ya kafe k'asa na y'ayansa ne ba mai takurasu kuma ba zasu dinga kwana su kad'ai ba. Dan haka itama ya lallaba yake bin ta saman da zarar ya dawo daga masallaci da asuba don su samu daidaita a tsakaninsu.

K'arfe takwas sun gama shirya ko barcin safe basu koma ba. GabaÉ—ayansu zumundin ganin uwarsu ya dabaibaye zuciyarsu. Farouk ya kalli Amrah ya ce ",Yaya ai dai bana yi miki rashin kunya ko?"

Dariya kad'an Amrah ta yi ta ce "Yaushe rabon da ka ce mini Yaya Farouk?"

Ya yi dariya kad'an ya ce ",Saura ki je Ki faÉ—awa uwata zancen da zai dame ta".

Amrah ta kalle shi ta ce "Me zan fad'a kuwa da zai dame ta ?"

Ya make kafada tare da fad'in "Idan kika ce bana magana da anty ta yi mini fad'a Allah muka dawo ke ma daina kula ki zan yi".

Ta jijjiga kai tare da fad'in"Tun yanzu daina kula ni kawai".

Ya yi dariya ya ce "Don dai bana son ki yi kuka ne".

Itama dole ta dara don ya bata dariya sosai.

Ta shiga dakinta ta fito da yar jaka Karama mai kyau d'auke da kayanta set biyu ta ce "Za ka dauko kayan naaka na saka maka ko kuwa?"

Ya make kafaÉ—arsa ya ce "Ki je d'akin nawa ki dauko mini idan ba haka ba, da iya na jikina zan je sai na ga wa za'a yiwa fad'a a tsakaninmu."

Ta kalle shi ta ce "Allah ya shirya ka Farouk ". Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:58]

Sannan ta wuce zuwa d'akin nasa don idan bata d'auko masa ba haka zai tafi, kuma ita Mahma zata yiwa fadan ba ita ce babba ba. Yayin da shi kuma yake tsaye rungume da hannuwansa yana yiwa kansa waka wai shi Yayan Mamah mai kafaciti dole a bi shi".

Amrah ta fito ta ce"Ka daina cika bakin dole na bika. Kawai tausayinka nake ji".

Ya k'yalkyale da dariya yana ce wa "Yayan Mamah ba abin tausayi ba ne Haj Amrah".

Dolenta ta k'yale shi don masu gidan ma hakuri suke yi da shi, don su ba ya kula su, tsakaninsa da su gaisuwar safe, sai ko idan zai faÉ—awa Babansu zai sayi abun makaranta. Amrah dai yake mu'amala da ita kawai.

Basu da wata babbar matsala a gida don su kad'ai suke rayuwa a wajensu, da daddare kuma iyayen su sauko su kwana. Sun sake samun saukin matsala ne da mijin Alawiyya ya dawo da ita cikin Katsina.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Kuma basu da nisa da unguwarsu. Dan haka duk sati suke zuwa gidanta Su yini, mamarsu ta turo musu ita da Amrah su yi samosa da springrols da numa meatpie sai Su tafi da shi su saka a fridge. Duk sadda suke so sai su soya abinsu. Sosai Alawiyya take kulawa da su dan har gidan take zuwa jifa jifa tana yiwa wajensu kyakkwan gyara. Dan haka basu wani tagayyara da yawa ba, mussaman da Hawwah ta kasa samun tasirin da zata

dakile hankalin ubansu a kansu. Tun Bilki bata dad'e da barin gidan ba ta fara cin karo da matsaloli da ashe zaman Bilkin a gidan ne ya hana ta lura da su.

Lafiya take zaune da mijinta amma kuma babu wannan rawar jiki da tarairayar da ya dinga yi mata a watannin farkon na zamansu. A da kafin ta bukaci wani abu sai dai ta ga ya kawo, yanzu kuwa sai ta yi ta fad'a kafin ya samu sukunin siyowa. Sannan su yaya Turai sun koma suna jan kunnen mijinta akan lallai ya saka ido akan ya'yansa kada ya bari su yi kukan rashin wani abu tunda uwarsu da take nan ba abin da bata yi dan ta rufa masa asiri ba. Tuni sun fahimci Bilki ce ta sanya gidan Sahal ya zama gidan masu wadata ta yadda zaka ci abinci laifayye ka k'oshi. Amma tunda ta bar gidan ba dama ka je a baka abinci sai dai ruwan pure water. Idan kuwa yini zaka yi to abincine dai ga shi nan amma ba wani sha'awar da zai baka. Sun sa ni kuma iya k'arfinsa ke nan tunda Hawwah bata da shi dole iya yadda ya bata haka zata yi.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Kun tuna Umm Nihla mai yadinkan Yan gayu da Yabin Bulkacuwa ta yi ta kece raini da su?*

*Tana nan tana kawo muku su zuka zuka, na alfarma, amintattu, akan farashi mai rahusa*

*Malaysianfabricsng*

07020695644.

Haba ba sai sai kuma suka koma suna son ya'yan Bilki ba. Hawwa kullum cikin kuka take tunda yanzu ita aka saka a gaba ana fadin itace farar k'afa ba Bilki ba. Sannan iyashegen da Faruku ya tisa ta a gaba da shi cikin lumana kad'ai na matuƙar damunta. Tsiyataku iriiri yake yi sannan ba dama ya ga Amrah ta hau samanta zai k'ira ta ya dinga yi mata sababin ta tafi neman suna ta bar shi, shi kad'ai. Ba yadda ta iya da shi tunda ubansa ma rarrashinsa yake yi da son ganin dariyarsa.

Da kanta ta fahimci babu riba ko kad'an idan har kishiya ta tafi ta bar maka ya'yanta gara ku zauna kowa ta rik'e ya'yan har Allah yasa su girma. Yanzu ba abin da take so irin ace Bilki ta dawo d'akinta ko dan mijinta ya samu nutsuwa sannan ta tabbatar idan tana nan wulakancin Faruk ba zai yi tasiri ba. Sannan hankalin Sahal ba zai zama kacokan akan su Amrha ba. Yana son d'iyarta tabbas tunda ba abin da ba ya yi mata amma sai take ganin ba kamar manyan ba. Idan zata kwnaa tana Kiran Faruku ba zai amsa ba, ko da kuwa ta bar samanta ta sauko. Idan da safe ya gaishe ta bata amsa ba, Babansa ya yi fadan yaro yana girmamata tana yada girman. Idan ta ce ai baya mata magana sannan ko mai zata ce masa ba zai nuna ya ji ba bare ya tanka. Ya kuwa ce mata ai yaro ne, sannan tunda yana gaishe ta ai ya kyauta kada ta sake ta biye masa watarana ba zai yi ba, bata ga Amrah ma hak'uri take yi da halinsa ba.

Bak'inciki kan bak'in amma ba yadda ta iya haka take hakuri tare da amannar yaran sune jarabawar gidan aurenta.

Da zai kaisu ya yi kwalliya irin wadda Hawwah ta dade bata ga ya yi irinta ba.

Ta kasa hak'uri ta ce "To ko dai kome zaku yi ne Baban Amra?".

Ya yi murmushi ya ce "Idan zaman bai k'are ba sai a yi".

Duk da zuciyarta ta buga amma da murnarta ta ce "Allah ya nufa gara ta dawo d'akinta ko Faruk ya janye kiyayyar da ya d'ora mini haka siddan."

Bai ce komai ba. Don kuwa ya riga yasan Bilki ta yi masa nisa har sai idan aure ta yi ta fito. Da kansa kuwa ya tabbatar matuk'ar ta had'u da namijin da zai biyar da ita ta samu gamsuwa ba zata yi marmarin sake zama da shi ba.

Ya dauki d'auki d'iyarta data ke zaune akan gado ya daga sama tana yi masa dariya sannan ya ajiye ta ya ce "Zan tafi daga can Zan wuce d'aurin aure kinsan yau asabar su kuma zan barsu a can sai ta tafi zasu dawo".

A sanyaye ta ce "A dawo lafiya".

Ta fito ya same su a falon sun Tisa jakar kayansu a gaba. Suna ganinsa suka mike. Ya ce ",Oya ku je ku yiwa Antinku sallama".

Ba musu suka hau k'afar benen yayin da shi kuma ya dauki jakar kayan ya fita zuwa wajen motarsa.

Amrah ce kawia ta hau ta yi sallamar. Amma Faruk nokewa ya yi daga k'afar benen.

Suka sauko a tare Amrah na yi masa fadan ya dinga jin maganar Dady Menene dan ya yi sallama?

Uffan bai ce mata ba. Ya shiga gaban mota Amrah ta shiga baya.

Har k'ofar gidan ya kaisu sannan ya ce su ce yana gaishe ta, haka nan su gaida Alti da Farha.

Ya ja motarsa ya tafi yana jin wani irin nauyi da nadama suna sake mamayarsa tabbas har ya mutu ba zai daina jin ciwon asarar da ya tafka ba.

Da gudu Faruk ya hau saman yayin da Amrah ta hau a hankali tana rike da jakar kayansu.

Alti ya tarar a kicin dan haka ya shiga ya rungume ta yana fad'in "Altina!

Itama ta rungume yaron tana jin dad'in yanayin da ta ganshi tabbacin basa cikin takura.

Daga haka ya sake ta da hanzari ya doshi d'akin da zai ga Mahma.

Mkbees Perfumery*

*Mopping liquid, Air freshener, Body* *mist ,Khumrah,Kulaccam,Hair* *Mist Carpet Spray,Linen Spray *

*Oil perfumes Kano*

*Sirrin gayun mace k'amshin*

07032456061

A bakin gado ya tarar da ita tana gyarawa Farha zaman hularta. Ai tana ganinsa ta ruga suka rungume juna. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:02]

Sakwanni goma suna haka kafin ya sake ta yana fad'in "Farha ya Abuja?"

Ta ce "Lafiya lau ina Yaya?"

Daidai lokacin Amrah ta shigo d'auke da jakar kayansu.

Itama ta rungume ta.

Yayin da suka zauna gefen uwarsu suka sanya ta a tsakiya.

A nutse Amrha ta gaishe ta shi kuwa Faruk jingina ya yi a jikinta. Bilki ta yi matuk'ar sanya jarumta ta karbi gaisuwarsu da sakakkiyar fuska. Amma k'asan zuciyarta tausayinsu fal yake yagalgala ta.

Da sanyin murya Amrha ta ce "Dady na gaishe ki, ke ma Farha ya ce yana gaishe ki ".

Farha da take zaune kusa da Faruku tana tambayarsa k'awayenta na makaranta.

Bilki ta ce "Ina amsawa ina kanwarku? Ya ma sunanta?"

Faruku ya yi fit ya ce"Lubaba".

Bilki ta ce "Sunan Hajiyar ne haka gatsal a bakinka?".

Amrah ta ce"Yana ji fa ina ce mata Ifrah amma dan iskanci indai ya ganta a hannuna ko wajen Dady sai ya wani ce mata Lubaba kullum ya fad'a haka sai Dady ya ce masa baka jin nauyin baro mini Faruk? Amma ba ya dainawa. Gaskiya Mamah ki yiwa yayanki fad'a baya jin magana kullum da abin da zai yi na rashin ji".

Bilki ta rungume shi sosai ta ce "Yayana da dai nasan ba ka neman fitina amma me yasa yanzu ka canja?"

Ya yi murmushi ya ce "Ba na neman fitina har yanzu amma bana son a takura ni ne, Yaya Amrah da Dady sai su dinga takura ni sai na shiga hanyar matar gidan ni kuwa ba zan shiga ba, ta yi harkarta na yi tawa".

Amrah ta ce "To me yasa kake mini sababi idan na je sama ko Idan na dauko Ifrah?"

Ya galla mata harara ya ce "Tunda Mamah bata tare da mu dole ki dinga kula da ni sosai. Akan me za ki tafi ki bar ni? Ki dinga neman shisshigi ai dama zan fad'awa mama ba ki rik'e amanata da kyau ba".

Dariya ta subucewa Bilki don ta lura da gaske yake maganarsa ba wai wasa ba.

Sosai suka hi hirarsu cikin nutsuwa duk da yawan hirar k'orafi Faruk yake ta gabatarwa akan Amrah tana takura shi wanda duk na shagwaba da iyashege ne kawai don uwar tasu da kanta ta gane Amrah ce take hakuri da shi tare da lallaba shi. Da azahar ta yi Alawiyya ta iso. Gidan ya sake kaurewa da murna suna tuna rayuwar da suka shafe tsawon lokaci tare tamkar ba za'a rabu ba, yanzu kuwa had'uwa gabad'aya irin haka zai dinga yi musu wahalar gaske. Wannan kad'ai ya isa a gane ba abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah.

Da taimakon Bilki da Amrah Alti da Alawiyya suka shirya dukkan kayan da Bilki ta ke so wajen d'aya . Duk abin da su Amrah suke so ku suke da bukartarsa ta bar musu. Babban gadonta Amrah ta ce ta bar mata tunda yanzu itace a d'akinta Kuma Dakin babbane gadonta da wadirof sun yi kankanta da yawa.

Faruk ya yi tsalle ya ce ",Ba za'a bata ba, na d'akin baki ya ishe ta tunda suma set ne."

Ta harare shi ta ce "Kai ka d'auki na d'akin bak'in tunda nasan ce wa zaka yi kai ta baka."

Ya girgiza kai ya ce "A a ni nawa sun ishe ni. Alawiyya zata barwa ita kuma ta siyar da nata ta fara business da kudin, ba ki ga yadda take yi mana kirki ba har yanzu? Duk sati sai mun je gidanta mun yi abin da muke so, haka nan ita take zuwa ta yiwa wajenmu general sanitation duk karshen wata. Har firizar can ma ita za'a bawa ".

Amra ta yi maza ta ce "Hakane a bata to".

Bilki ta yi shiru tana nazarin hukuncin da Faruk ya yanke kaitsaye ba tare da neman shawara ba. Amma ta sani gaskiya ya fad'a. A ranta ta ji yafi dacewa da ya amsa sunan Sulaiman don kuwa halayyarsa rabi irin tasa ce.

Dan haka duk ta barwa Alawiyya kayanta har kujerun falon, yayin da Alawiyya ta dinga kuka tana hodiya tare da mamakin yadda ta mallaki kayan alfarma tashi guda. Tuni kuma ta amince zata siyar da nata kayan wasu kuma ta aikawa kanwar Babanta da ta rik'e ta tunda marainiyace ita.

Alti ta dinga taya ta godiya a wajen Bilki.

Da yamma Basma ta je mata suka yi hira ta yi murnar ganin Bilki ta samu nutsuwa zuciya sannan ta ji dad'in auren da zata yi. Ta jaddada mata zata kula da su Amrah iyakacin iyawarta. Itama Bilki ta bata warmers sabbbi sannan ta ce ta duba duk abin take so na amfani ta dauka. Gaf da magariba ta yi sallama suka ta tafi. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:11]

Sai dare mijin Alawiyya ya zo daukarta a mashin d'insa wanda dan kasuwane yana siyar da kayan vegies da yake sarowa daga Raudatul Jannah foods Jos.. A zuwan da Alawiyya take yi siyo kayan snacks da na amafanin gida suka hadu.

Har saman ya hawo ya gaisa da Mahmah tunda dama a gidan ya san Alawiyya sai da suka amince da junansu sannan Bilkin ta tura shi K'afur garinsu Alawiyya ya gana da wakilanta.

Ya dinga yin godiya alherin da aka yi musu tunda Alawiyya waya ta yi masa ta fad'a masa kyautar bajinta da aka yi mata duk kuwa da kayan d'akinta na yanzu Bilkin ce ta yi mata su sabbi Sai dai ai Basu kama k'afar wanda aka bata ba yanzu.

Kafin ta tafi Bilki ta ja ta d'aki ta fad'a mata zata yi aure a cikin sati mai kamawa ta taya ta da addu'a. Farinciki har cikin ran Alawiyya don kuwa bata yiwa uwardakinta sha'awar yin kome. Ta dinga yi mata addu'o'i masu sanyaya zuciyata tare da sake yi mata alkawarin matuk'ar tana cikin garin Katsina to Faruk da Amrah suna da Yaya tamkar uwarsu d'aya ubansu daya zata kula da su irin yadda ta kula da ita. Hankalin Bilki ya sake nutsuwa don kuwa ta gasgata Alawiyya. Ga su Faruk sun sake bada shaidar ba abin da bata yi musu.

Suka yi sallama suka rabu cikin sanyin jiki da fatan alheri.

*Na ce kina yiwa masu aikinki adalci da sassauci kuwa?*

*Ba ki san ta yadda zasu taimake ki a gaba ba. Kowanne dan adam akwai ranarsa, da ace Bilki bata yi mata adalci ba, da bata kular mata da yaranta a lokacin da babu idonta a kusa ba*.

Sai da daddare bayan sun kammala cin abincin dare tuni kuma Farha ta yi barci.

Ita da Alti suka faÉ—awa yaran batun auren da zata yi. Dukkansu yaran jikinsu ya mutu ba karsashi suka ce "Allah ya sanya alheri".

Amma k'asan zuciyarsu sun ji wani iri shike nan ta bar gidansu da dadynsu for ever?

Murya ba amo Amrah ta ce "Mahmah waye shi sannan a ina za ki zauna?"

Ba walwala ta ce "Uncle Asad ne sannan a Abuja zan zauna".

Amrah ta yi shiru ta rasa me take ji a ranta. Amma dai zuciyarta sai ayyana mata take yi mai kudine fiye da dadynsu amma kuwa Babansu ya fi kyau yafi kirki tunda shi ba ya dariya.

Kafin ta ce wani abu Faruk ya ce "Mahmah uncle police wai?"

Kai kawia ta daga masa tabbacin eh.

Ya rik'o hannunta ya ce "Amma takwarana ya fi shi kirki da kyau Mahmah".

Murya ba amo ta ce "Ba kyau na duba ba, sannan haka k'addara ta zaba mini kawai ku dinga yi mini addu'a".

A sanyaye suka ce to don hatta Faruk da yake ganin gara ta tafi inda ba zata dinga kuka ba, batun auren nata ya yi awon gaba da kuzarinsa. Wato kishi bala'i ne, ba ga yara ba, ba ga manya ba.😄Ba ga mazan ba, bare kuma mata masu duniya. Allah kasa mu wanye lafiya.

Washegari suka bar Katsina wanda su Bilkine suka kai yaran gidan Alawiyya akan da yamma su wuce gidansu tunda da sassafe suka tafi a dalilin zasu tsaya a Kano wajen Yaya Hamida.

Suna nisa da Katsina kewar ya'yanta na sake kama ta. Akan dole ta yi hak'uri mussaman da yara basu tayar da hankalinsu sosia ba, amma dukkansu sun yi kuka.

Haka Farha har suka kusa isa Kano kuka take yi akan a barta a wajensu ba zata koma Abuja ba. Sai da barci ya sure ta sannan ta yi shiru.

Taran safiya a gidan Yaya Hamida ta yi musu, suka karya sannan suka shiga daki Bilki ta sanar mata batun aurenta da Yaya Asad.

Take Hamida ta fara kuka tana fad'in tabbas na huce dan ke na ji wa'azi akan illar gaba mussaman ace jini guda ke yin ta. Amma ki sa ni sai da kwakkwarn dalili za ki ga k'afata a gidanki. Me za ki yi da wannan mugun marar mutunci dattijo da shi zai dage sai ya aure ki. Allah ne ya rufa miki asiri bai lalata ki tun kina yarinya ba, masu kakin nan fa kad'an ne na kirki amma wominzers ne na k'arshe. Ai ni tunda bai zo ta'aziyar uwarmu ba, sannan ya daurewa yar iskar Abidan nan gindi akan Yaya Sulaiman Wallahil Azim ba ni ba shi. Dan haka soyayyar da zan nunawa ya'yanki sai na nunawa su Amrah da Farha amma nasa kam kadaran kadaran hakan ma saboda ta jikinki suka fito." Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:13]

Sai dare mijin Alawiyya ya zo daukarta a mashin d'insa wanda dan kasuwane yana siyar da kayan vegies da yake sarowa daga Raudatul Jannah foods Jos.. A zuwan da Alawiyya take yi siyo kayan snacks da na amafanin gida suka hadu.

Har saman ya hawo ya gaisa da Mahmah tunda dama a gidan ya san Alawiyya sai da suka amince da junansu sannan Bilkin ta tura shi K'afur garinsu Alawiyya ya gana da wakilanta.

Ya dinga yin godiya alherin da aka yi musu tunda Alawiyya waya ta yi masa ta fad'a masa kyautar bajinta da aka yi mata duk kuwa da kayan d'akinta na yanzu Bilkin ce ta yi mata su sabbi Sai dai ai Basu kama k'afar wanda aka bata ba yanzu.

Kafin ta tafi Bilki ta ja ta d'aki ta fad'a mata zata yi aure a cikin sati mai kamawa ta taya ta da addu'a. Farinciki har cikin ran Alawiyya don kuwa bata yiwa uwardakinta sha'awar yin kome. Ta dinga yi mata addu'o'i masu sanyaya zuciyata tare da sake yi mata alkawarin matuk'ar tana cikin garin Katsina to Faruk da Amrah suna da Yaya tamkar uwarsu d'aya ubansu daya zata kula da su irin yadda ta kula da ita. Hankalin Bilki ya sake nutsuwa don kuwa ta gasgata Alawiyya. Ga su Faruk sun sake bada shaidar ba abin da bata yi musu.

Suka yi sallama suka rabu cikin sanyin jiki da fatan alheri.

*Na ce kina yiwa masu aikinki adalci da sassauci kuwa?*

*Ba ki san ta yadda zasu taimake ki a gaba ba. Kowanne dan adam akwai ranarsa, da ace Bilki bata yi mata adalci ba, da bata kular mata da yaranta a lokacin da babu idonta a kusa ba*.

Sai da daddare bayan sun kammala cin abincin dare tuni kuma Farha ta yi barci.

Ita da Alti suka faÉ—awa yaran batun auren da zata yi. Dukkansu yaran jikinsu ya mutu ba karsashi suka ce "Allah ya sanya alheri".

Amma k'asan zuciyarsu sun ji wani iri shike nan ta bar gidansu da dadynsu for ever?

Murya ba amo Amrah ta ce "Mahmah waye shi sannan a ina za ki zauna?"

Ba walwala ta ce "Uncle Asad ne sannan a Abuja zan zauna".

Amrah ta yi shiru ta rasa me take ji a ranta. Amma dai zuciyarta sai ayyana mata take yi mai kudine fiye da dadynsu amma kuwa Babansu ya fi kyau yafi kirki tunda shi ba ya dariya.

Kafin ta ce wani abu Faruk ya ce "Mahmah uncle police wai?"

Kai kawia ta daga masa tabbacin eh.

Ya rik'o hannunta ya ce "Amma takwarana ya fi shi kirki da kyau Mahmah".

Murya ba amo ta ce "Ba kyau na duba ba, sannan haka k'addara ta zaba mini kawai ku dinga yi mini addu'a".

A sanyaye suka ce to don hatta Faruk da yake ganin gara ta tafi inda ba zata dinga kuka ba, batun auren nata ya yi awon gaba da kuzarinsa. Wato kishi bala'i ne, ba ga yara ba, ba ga manya ba.😄Ba ga mazan ba, bare kuma mata masu duniya. Allah kasa mu wanye lafiya.

Washegari suka bar Katsina wanda su Bilkine suka kai yaran gidan Alawiyya akan da yamma su wuce gidansu tunda da sassafe suka tafi a dalilin zasu tsaya a Kano wajen Yaya Hamida.

Suna nisa da Katsina kewar ya'yanta na sake kama ta. Akan dole ta yi hak'uri mussaman da yara basu tayar da hankalinsu sosia ba, amma dukkansu sun yi kuka.

Haka Farha har suka kusa isa Kano kuka take yi akan a barta a wajensu ba zata koma Abuja ba. Sai da barci ya sure ta sannan ta yi shiru.

Taran safiya a gidan Yaya Hamida ta yi musu, suka karya sannan suka shiga daki Bilki ta sanar mata batun aurenta da Yaya Asad.

Take Hamida ta fara kuka tana fad'in tabbas na huce dan ke na ji wa'azi akan illar gaba mussaman ace jini guda ke yin ta. Amma ki sa ni sai da kwakkwarn dalili za ki ga k'afata a gidanki. Me za ki yi da wannan mugun marar mutunci dattijo da shi zai dage sai ya aure ki. Allah ne ya rufa miki asiri bai lalata ki tun kina yarinya ba, masu kakin nan fa kad'an ne na kirki amma wominzers ne na k'arshe. Ai ni tunda bai zo ta'aziyar uwarmu ba, sannan ya daurewa yar iskar Abidan nan gindi akan Yaya Sulaiman Wallahil Azim ba ni ba shi. Dan haka soyayyar da zan nunawa ya'yanki sai na nunawa su Amrah da Farha amma nasa kam kadaran kadaran hakan ma saboda ta jikinki suka fito." Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:17]

Hawaye a fuskar Bilki ta ce"Ni ma ba sonsa na ke yi ba, Yaya Faruku ne ya matsa mini amma ko Baba ma ce masa na yi bana sonsa".

Yaya Hamida ta ce "Ni dai tunda kun shirya ke da su ba zan ce komai ba, amma ki sa ni Wallahi mu ba ruwanmu da su mussaman ma Asad mugun mutum mai bak'ar fuska da zuciya.".

Kan dole suka goge idonsu suka yi hirar sannan aka yanka cake din d'iyar Hamida ta biyu wanda ranar take yin birthday da sai yamma za'a yanka amma Saboda ayi hotuna da su Bilki da Farha aka yanka a lokacin.

Duk da Bilki harkar snacks ta k'ware Sai da ta tambayi wacce ta yi cake din tare da su samosa da springrols saboda dad'insu sannan da aka fad'a Mata Farashin sai da ta jinjina tare da karɓar lambar dan ta had'a ta da kawayenta na Kano da suke ta fad'in har yanzu basu samu wacce ta iya snacks irinta ba.

Deenah cakes and more -Kano

09038055790

IG @Deenah cakes and more

Snacks such as :

Birthday cakes

Cupcakes

Samosa

Springrolls

Meatpie

Frozen snacks

Event snacks.

Sai azahar sannan suka kama hanyar Abuja bayan Yaya Faruku ya azalzale su.

Shi Yaya Faruku har yanzu ba wanda yake fishi da shi tunda dama tun filazal na kowa ne.

Sai dare sosai suka isa gida.

Kushen Yaya Hamida akan Asad ya sake tsananta kinsa a zuciyarta sai dai ba zata iya ce wa ta fasa ba tunda ta ce ta amince, amma gabad'aya abin ya sake fita a ranta.

A daren ya k'irata yafi sau biyar bata daga ba ya damu k'warai. Haka da safe. Yayin da ita kuma zuciyarta ce ke ta yi mata rawa tare da wasiwasin ta zazzage shi kawia ta yadda zai hak'ura da kansa. Amma ko kusa ba zata iya yin haka ba tunda ta samu tarbiyar girmama babba tunda ga tushe.

Washegari k'arfe sha d'ayan safiya a gidan ta yi masa. Sanye yake cikin tsadadden farin yadin filtex.

Ya shiga falon ciki ya gaisa da iyayensa suka dan taɓa hira akan tafiyarsa Lagos. Bai wani jima ba ya fito ya dawo falon farko ya zauna. Daidai lokacin Amal da Noor tare da Farha suka fito suka nufe shi suna yi masa oyoyo. Ya d'an biye musu ya basu alawowi da cookies kowa ledarsa daban.

Noor ta ce "Dady yaushe zaka d'auke mu koma gidanmu?"

Ya jata jikinsa ya ce ki k'ara hak'uri, ba na ce miki yanzu Mahmah itace mominku ba?"

Ta daga kai.

"Good idan muka yi tafiya muka dawo zamu zo ni da ita mu d'auke ku har da Farha mu koma gidanmu gabadaya ".

Amal da tafi wayo ta ce"Shi ke nan sun zama y'an gidanmu?"

Ya ce "Haka nake nufi my Amal".

"To amma Dady Ammie da junior fa?".

Ya ce "Su anan zasu zauna kafin dadynsa ya dawo ya dauke su suma.

Murna ta kama Farha jin zasu koma tsalelen gidansu Noor ya zama nasu.

Ya ce "To ku je ku shirya yanzu lesson teacher dinku zai iso.

Ku faÉ—awa Mahma ta zo ta karbi sweet dinta tunda Ammi na hospital."

Suka tafi da sauri dan faÉ—awa Bilki sak'onsa da kuma dauko jakunkunan karatunsu.

Ya jima a zuane yana dakonta. Amma bai kosa ba mussaman da yake ta amsa waya daban daban.

Can ya ji fitowar yaransu suka wuce shi suna fad'in bye dad don suna ganin kafin Su kammala ya tafi.

Sun jima da fita kafin ya jiyo takunta hadi da k'amshin turarenta.

Cikin nutsuwa ta zauna a kujerar da take fuskantar wacce yake zaune.

Kanta na k'asa ta ce "Ina yini?"

Ya amsa da fad'in lafiya but not fine! Kin rikita mini tunanina Maigado! Me na yi miki, me ya faru kika daina daukar wayata sannan komai ya zo bakinki sai ki fad'a mini kai tsaye. What's going on?"

Ya tambaya a rude.

Kanta na k'asa bata yi magana ba.

Ya zuba mata ido ya ga gabad'aya ta yi wani iri babu kuzari a tare da ita.

Ya tabbatar zuwanta Katsina na kan gaba wajen sauyawarta.

Ya tausasa harshe ya ce "Maigado!

Bata motsa ba bare ta amsa.

Ya numfasa ya ce "Ya su Faruk junior?"

Murya ba amo ta ce "Suna lafiya Alhamdulillah!

Ya gyara zama ya ce "Ki ba ni lambar Babansu na roke shi ya ba ni su na sanya su makaranta a nan".

Ta d'ago a hanzarce don maganar ta zo mata a bazata, har cikin zuciyarta kuma ta ji dad'in hakan. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:19]

A sanyaye ta ce "Na gode sosai amma Babansu ba zai bada su ba, suna karatun ma a can".

Ya dan ji dad'in ganin yadda ta dan fara warewa.

Ya ce"To kuwa da zarar sun kammala sakandire dolensa ya bada su don su shiga manyan jami'o'i. Babbar ta kusa kammalawa ne?"

"A a da saura yanzu ma shiga aji biyar(s.s.2)."

"To ai kamar yanzu ne".

Faruk so nake ya yi b'angaren likitanci. Ai yana da kokari ko?"

Ta murmusa tare da fad'in "Wannan Yayan nawa ai sai a hankali ban san zuwa gaba ba. Amrah ce hazik'a irin Abida!

Ya yi maza ya ce"Ma sha Allah! Da ikon Allah kuwa zata yi karatu a d'aya cikin best universities da ake ji da su a duniya".

Da walwala a fuskarta ta ce"Allah ya ida nufi".

Haka ya dinga yi mata hirar yaranta nan da nan ta warware suka yi hira irin wacce basu taba yi ba.

Ganin ya shawo kanta ta ware ya sanya ya yi mata sallama ya tafi bai yi mata maganar soyayya ko aure ba.

Sai da daddare suna waya ta ce "Baban Bilkisu ko za'a bari auren nan sai ka dawo daga tafiyar da zaka yi don gaskiya ni bana son tafiyar".

Zullimi ya yiwa zuciyarsa k'awanya ya ce"Ki yi hakuri kin ji ai ba dadewa zamu yi ba."

Ta yi shiru tabbacin bata yarda ba.

Ya ce "za'a daura auren juma'a mai zuwa ba za'a sauya ba. Zan nemi wajen aiki su tura wani zuwa kwas din, gwara na rasa k'arin girman da na rasa ki Maigado ".

Murya a mak'oshinta ta ce"Ni gaskiya ka tafi, idan ka dawo a daura. Tsakanina da Allah jibi ya yi mini kusa da yawa"

Yana kwance ya zabura ya zauna a tsakiyar gadon.

A kidime ya ce "Saboda me Maigado, me ya faru, me ya canja miki shawara haka? Dan Allah kada ki zama mai yin magana biyu. Allah ne shaidar yadda nake son ki nake tsananin son na aure ki, ba kya jin tausayin zamana haka Maigado? Fad'a mini me na yi miki da ya sanya kika sake shawara?"

Ya yi mata tambayar cikin rarrashi da kwantar da harshe.

Ya bata tausayi ainun. Amma duk da haka ta ce "Gaskiya Baban Bilkisu baka son y'anuwana duk cikinmu da ni kawai kake yin mu'amala mun sake gane hakan ne da Mami ta rasu ba ka zo mana ta'aziya ba sai ta waya, wayar ma a layin Baba ka k'ira aka hadaka da ku, idan ma baka k'asar da gaske me ya hana da ka dawo baka zo mana ba?"

Sannan a matsayinka na babba baka tsawatarwa Abida ta koma d'akinta ta zuaan da mijinta lafiya tunda bai yi mata komai ba, sai ka zuba mata ido saboda kawai baka son Yaya Sulaiman ".

Ya yi shiru ya kasa ce mata komai amma gabad'aya kansa ya kulle. Ya nisa ya kasa furta kalma ko guda don ya tabbatar zuwanta Kano Hamida da sauran suka soki lamarin aurensu tare da gabatar mata da hujjar da ita a da bata gano su ba. Ya yi imanin kitsa mata wadannan kalaman aka yi don da ta k'ulla ce ba zata zo masa ta'aziyar Rukayya ba, tunda kaf ya'yan Baba k'arami ita kad'ai ce ta zo masa ta'aziyar Sai Saddiqa Wanda ya tabbatar ita ta matsa mata suka taho tare, amma ko Ansari waya ya yi masa duk da shi su na d'an gaisawa jifa jifa.

Murya ba amo ya ce "Wallahi Billahi Maigado bana k'asar nan mami ta rasu. Sai da aka yi watanni biyu da rasuwar kafin na dawo. Ba wai dan ina jin haushinta ko dan ina fishi da ku ba ne. Dan Allah ki yarda da ni. Batun Abida kuma kowa da nasa kason na laifi da mu, da ita, da shi Sualiman din da ya gudu. Shi ma da ace Baba k'arami na da rai bai isa ya yiwa Baba Babba fishi irin haka ba. Ni yanzu ba tone tone zamu yi ba. Don kuwa Abidan da kuke ganin mun zuba mata ido ai a cikin nadama take mai tsananin gaske. Kada mu saka matsalolin gidanmu akan lamarinmu Balkees pls. So nake al'amarinmu ya yi tasirin da zai zama tsananin sulhu da afuwa a tsakaninmu. Yanzu ba kya tunanin irin murna da farincikin da Baba Babba yake ciki a kanmu, kin ce masa kin amince sai kuma ki dawo ki ce kin fasa? Yayanki Faruku yana ta rawar jiki da farincikin kin yarda ya isa da ke, sai kuma ki watsa masa k'asa a ido ki kunyata shi? Ki yi hakuri, in sha Allah sai na zame miki alheri, sai gidanmu ya dawo tamkar yadda muka taso muka ga iyayenmu sun kafa Shi, hakan kuma ba zai yiwu ba sai kin ba ni hadin kai, kin yi hak'uri kin jure duk wata gutsuri tsoma. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:22]

Sannan duk inda Sualiman yake da ikon Allah zai dawo cikinmu ya rayu da mu, zan yi kokarina ya dawo gida, don kuwa tabbas ban ji a jikina ya rasu ba."

Jikinta ya yi sanyi ainun. Ta rasa yadda zata yi a kan dole ta ce "To".

Ya dinga yi mata godiya har ta ji wani iri. Don sai ya bata tausayi yadda ya kwantar mata da kai tamkar ba babban dan sanda ba.

Ganin ya shawo kanta ya sanya ya ce "Bari na bar ki, ki yi barci Maigadona, zamu yi magana da asuba in sha Allah stay blessed and I do luv you my dear. Save Restricted Contents Bot, [Sep 13, 2025 at 12:55]

Daga haka ya katse wayar ba tare da ya jira amsawarta ba.

Sai da ya yi matuk'ar tura sako mai nauyi a zuciyarta kalaman nasa sun saka ta cikin nishadi da nutsuwar hakura ta karbe shi a matsayin mijinta. Ta yi shiru tana tunanin yadda zata kasance a matsayin matarsa.

Yayin da shi kuma ya kasa kwanciya. Tabbas da aiki a gabansa tunda a bayyane k'arara iyalin Baba k'arami suke gaba da shi. Sannan dukkan fishinsu akansa suka d'ora. Zai yi komai dan ya auri Bilkisu don hakan ne kad'ai hanyar da zai daidaita Shi da su dari Bisa dari don Idan tana hannunsa dolensu su yi mu'amala da gidansa sabanin Idan watace ko da sun shirya ba lallai su zo gidansa ba, sai da kwakkwaran dalili.

Da k'yar barci ya sure shi. Da asuba yana idar da salla ya k'ira ya dinga tarayyarta da rarrashi da maganganu masu nauyi kafin ya k'yale ta bayan ya tabbatar jikinta ya tsumu da manyan kalamansa.

A daren ranar Baba ya sake zama da Asad tare da Farouku.

Ya kaurara murya ya ce "Na yi magana da Bilkisu ta kuma ba ni tabbacin ta amince da batun aurenku! Amma ka saurare ni da kyau. Duk cikinku kai ne babba, ba sai na maimaita abin da ya faru na rikicin da ya gitta a tsakaninmu ba. Na yi faricinciki da Ubangiji ya k'ulla wannan alherin a tsakaninka da

kuwa a duniya ba abin yake saurin yafe gaba irin auratayya. Yana daga cikin dalilan da Annabin Rahma ya auri mata daban daban daga kabilu mabanbanta, duk kuma kabilar da ya auri y'arsu gab'ar da suke yi da musulunci tana zagwanyewa.

Dan haka ka yi iya k'ok'arinka ka daidaita zumuncinku da ya yi rauni da y'anuwan Bilki. Ka buda musu k'ofar da zasu zo gidanka su sake, haka nan ka yi atiya kokarinka wajen ganin kun sake hadewa kuna zumunci ko da bana raye. Sannan ka cigaba da bincike akan Sulaiman. Kana ganin dai yadda Abida take zaune bata kaunar ayi mata maganar ko zata yi gaiba, a haka ta kwashe shekaru kusan hud'u babu shi, babu alamarsa ga ya'yansa nan basu san shi ba!

Baba ya yi shiru a dalilin kuka na neman kubuce masa.

Sai da Asad ya dinga ba shi hak'uri sannan ya dan nutsu.

Ya numfasa ya ce "Bilkisu ta ce 'Na sanar maka da d'iyarta d'aya zata zo gidanka da kuma Alti.

Mamaki ya kama shi ya murmusa ya ce "Baba ka fad'a mata idan wad'anccan na Katsina ma Babansu zai ba ni to ta zo mini da su zan rikesu gabad'aya".

Sai Monday Kuma in sha Allah.

*Surayya Dee,*

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: [Sep 15, 2025 at 09:44]

Yake furzarwar da k'arfin gaske wanda ya ja hankalin Hawwa da take samanta wanda itama ta ga sanarwa tunda ya koya mata kallon labaran k'asa.

Amma Amrah da Faruk tuni suka yi barci dan haka basu ji hirjinsa ba.

Gulma da son ganin halin da yake ciki ya sanya Hawwah gangarowa a sukwane.

Sai dai yanayin da ta ganshi yana ta sa'a'i tare da suratai ya yi matuk'ar sanyaya mata jiki don kuwa muraran tashin hankali da yake zuciyarsa ne ya bayyana masa a gangar jikinsa.

A sanyaye ta ce "Baban Amrah nutsu ka zauna mana kada ka fadi ka hadu, da jinya fa".

A matuƙar gigice ya ce "Idan har irin wannan suyar mata suke ji idan mijinsu zai ƙara aure to la shakka sun cancanci a yi hak'uri da su a kuma rarrashe su iyakacin rarrashi. Hawwah so nake na mutu ko na huta da azabar ciwon da k'irjina yake yi mini. Da ace nasan haka Bilina ta dinga jin radadin aurenki da na yi a zuciyarta da ban auro ki ba, bare ki zama sanadin rabuwata da masoyiyyita ta gaskiya ".

*Ina tallata muku plastic passion plates masu kyau da aminci*

*Plates da ba ko Ina ake ganinsu ba sai a kicin uwargida Mai kafaciti ko amarya mai authority*

*Da gaske nake yi plates din masu kyau ne da ban sha'awa*

*Ku tuntubi wannan lambar da ganin sampur da Kuma price Dai da ba zai zarta aljihunku na*.

08109544470

A zafafe Hawwah ta ce "Hala dai bayan kishi da yake yagalgalaka har kanka ne ya tab'u? Menene nawa a cikin rabuwarku? Wuka na saka maka ko bakin bindiga akan sai ka sake ta?"

Cikin fitar hayyaci ya ce ", Aurenki ne dai sila. Kullum zuciyarta na zafi da turiri amma ban kula ba, ban rarrashe ta ba, Sai ma danne mata hak'kinta tare da fifita ki a kanta da ya'yanta. Ga shi na rabu da lu'ulu'u na kama azurfa".

Bak'in ciki mai tsananin gaske ya shak'e Hawwah da muryar kuka ta ce "Ni ka misalta da azurfa ka kwatanta wacce take shirin zama matar gabjejen jarumin d'an'sanda irin Asad Funtua da lu'ulu'u? Ta nisa ta had'iye kukan ta ce "Ina tabbatar maka sai Anty Bilki ta ga banbancinka da sabon angonta fiye da banbancin da ka ga ni a tsakanina da ita. Don kuwa shi ba zai yi mata butulci ya yaudari budurwa da dukiyar da take mallakinta ce ba, don kuwa shi gabjejen attajirine ba da kudin mace ya yake tutiya ba.

Bak'in ciki kan bak'in cike ne ya dinga k'wamushe shi. Ga wani irin azabben ciwon da yake barazanar fasa masa k'irjinsa ya yi masa k'awanya. Take jiri ya kwashe shi ya fadi yaraf kan kujera.

Yayin da Hawwa ta ja tsakai mai tsananin gaske ta wuce zuwa samanta tana fad'in "Idan aka wayi gari da kai lafiya to tabbas soyayyarka bata cika ba, don kuwa kamata ya yi ka bak'unci lahira kafin wani ya fara sukuwa a kan matar da kake ƙirarin kana sonta".

A wannan dare Sahal ya gane me kira da nisan dare don kuwa ya Ga tsayinsa matuk'a gaya. Sannan shine dare Mafi tsaurin a dukkan rayuwarsa. Wani irin Kishin Asad da tsanarsa ne suke ta walagigi da shi. Ya dinga addu'ar Allah ya gajartawa Asad kwana Bilki ta yi masa takaba ta dawo masa shi da Ya'yansa.

A masallacin juma'a na k'asa na birnin tarayyar Nigeria aka sake daura auren Bilkisu a karo na biyu da sadaki mai k'ololuwar daraja.

A lokacin da ta ga alert din kudi mai nauyi a asusunta daga kuma Yaya Farouku. Murmushin da babu nishadi ya k'wace mata domin so ta yi ace shine da kansa ya bata sadakin ba waninsa ya biyawa ba.

Bata ce komai ba don sosai alhini ya kutso mata.

Abida ta dinga yi mata d'an bikin ta yi daraja da yawa.

Ba wani shiri Bilki take yi ba Abida ce ta ce sai sun yi walima ta kuma karbi kudade a hannun Ango, na kwalliya da gyaran jiki, masu nauyi.

Ango kuma bakin shi har kunne a wajen yin hoto yana ta kama Balki tana bige masa hannu amma shi bai damu ba, a ransa yake fad'in an daura dai hankalina ya kwanta.

An sha walima a gidan zuwa biyar aka kai Amarya kayattacen gidan Ya Asad bayan Baba Babba ya yi mata nasiha sannan ya damkawa Baba Faruku ita ya ce ya kai ta gidan mijinta, tare da fad'in "ko na mutu ka tsaya mata Farouku!.

Abida da Saddiqa da Momi, da matar Ansari suka bisu a baya.

, [Sep 15, 2025 at 09:52]

Yaya Hamida dai ta ce zata zo bayan biki, don kuwa ta ji haushi da Bilki ta auri Asad mutumin da bai zo musu gaisuwar mami ba.

Ba su wani jima ba suka tafi bayan Abida ta yiwa Bilki raÉ—a.

"Saura ki matsewa yayana cinya".

Bilki ta ture ta tare da fad'in "Abin da yake ranki ke nan ko?"

Abida ta kyalkyale da dariya tare da fad'in "ke kika koya mini irin wadannan zantukan, dan haka gobe da azahar zan zo na ji bayani".

Bilki ta yi mata k'aramin tsaki tare da fad'in ki zo sassafe ma Abida ".

Ta yi dariya ta fice ta samu sauran a falo suka tafi suka bar amarya ita kad'ai.

Tana tunanin yadda zasu kwashe da angon nata da yake ta rawar jiki tamkar ya yi shekaru goma babu mace tare da shi.

Tasan yau dai kam ba zai daga mata k'afa ba

Rawar k'afar da yake yi kadai ya isa ya nuna ya matsu.

Kuma da gaske ne tun mangariba ya shigo gidan, ta dauka lamarin sai dare za a fara amma ina bai jira ba, mangariba kawai ya ja su jam'i ya ciyar da su kaza da madaran da ya shigo da shi, ita ba ta wani ci sosai ba, amma duk da haka bai saurara mata ba.

Sallar nafilar ma sai ta ga a gaggauce ya ja suka yi. Suna idarwa ya juyo ya rungume ta gabad'aya. Jikinta sai b'ari yake yi yayin da zuciyarta take bugawa da k'arfi sosai tamkar yaune karon farko da namiji ya bak'unci gangar jikinta.

Ya dafa goshinta ya yi addu'a, sannan ya mikar da ita tsaye, yana rungumarta sosai. Hannayensa na kai komo a bayanta har zuwa mazaunanta da suke matuƙar tafiya da imaninsa.

Yadda yake rawar jiki ne yasa ta sakar masa jiki, kai yaya Asad namiji ne ba ta taba tunanin za ta iya samun bambamci mai yawa tsakanisa da Sahal ba, mussaman da ta ga ya girmi sahal din sosai, sai ga shi a bugu daya ta fahimci ya yiwa Sahal nisan da har abada ba zai kamo shi ba.

Ga shi itama ta sha gyara da saiwowin asali marasa illa na Surayya Halin yau ta hade tamkar bata haihu ba. Nan fa ya susuce ya yi ta sambatu Allah yasa ma su kad'ai ne a gidan.

Ita ma sai dai ta ki fada amma ta samu gamsuwar zuciya da gangar jikin da ta dade ba ta samu ba, bata san ta ba shi goyon baya sosai ba, sai da suka natsa ta fahimci ta saki jiki da yawa ta dawo tana jin kunya.

Shi dai godiya kawai yake yi mata domin ta ba shi mamaki sosai, yadda ta sakar masa jiki ya yi abin da yake so.

Sai ta ji tausayinsa ganin yadda gabadaya ya rude a kanta.

K'arfe takwas din dare suka samu nutsuwa, sannan suka yi wanka don sallatar Isha. Daga haka suka kwanta yana rungume da ita tamkar zata gudu ta bar shi. Bakinsa daidai saitin kunnenta ya numfasa murya ba amo ya ce "Maigado kin san na sha yin mafarkin wannan al'amarin da ke? Daga baya har tsoron lamarin ya dinga ba ni, na dage da addu'a akan Allah yaye mini tare da yawaita addu'ar tsari daga shaidanun aljanu don har na a fara tunanin ko wata aljana ce zata shige ni take zuwa mini a siffarki! Ashe akwai lokacin da Allah zai tabbatar mini da faruwarsa a zahiri bayan na cire rai da samunki na hak'ura gabad'aya"..

"Uhum".

Kawai ta ce don ita gabad'aya kunyarsa ce ta takure ta. Yaya Asad din nan da take jin tsoronsa kamar me wai shine suke kwance gado d'aya? Shine suka yi tarayya? Ikon Allah yafi ga haka.

Ya dinga yi mata hira yana shafa gashin kanta, yayin da ta yi luf a k'irjinsa har cikin zuciyarta irin haka take fatan ace mijinta na yi mata.

Ya sumbaci kunnenta ya ce. "A yi barci lafiya Maigadona. Yau Allah ya cika mini burina na mayar da ke Maigadona ta gaske."

Ta yi murmushi kad'a ta ce "Dama manufar sunan a zuciyarka kenan?"

Ya yi murmushi mai sauti ya re da ce wa "Har cikin zuciyata".

"Hmm"

Kawai ta ce don abin ya yi mata nauyi.

Sai me wajen karfe d'ayan dare ta ji yana lalubarta hakan ya sanya ta farka, gane da ta yi maimai zai yi, ya sanya ta ce "fitsari zata yi. Ta shiga bayi ta wanke baki ta dawo. Al'amarin da ya shayar da ita ba mai saukin bayyanawa bane kawai dai a ranar ta samu nutsuwar da bata san da ita ba. Hatta abubuwan da ya yi mata bata taba tunanin ana yinsu ba don ita bata same su ba.

Da asuba ma sai da ya sake komawa bayan ya tambaye ta idan ya sake babu takura? Ta fahimci ya yi hakuri tsawon lokaci bai jefa kansa a tsila tsillar mazan yau ba, shi yasa ba ta yi masa gaddama ba, ta ba shi hadin kai, suka biyawa kansu bukata kuma dukkansu suka samu gamsuwa.

Wani irin amarci suke barjewa don babu kakkautawa. Da alamu tafiyarsu ta zo d'aya don duk yadda take fad'in bata sonsa to bata yi masa k'wange kanta, kuma tana matuƙar enjoying al'amarin.

A kwana na uku Abida ta zo gidan maigidan na nan tunda baya fita ko ina, yana hutun angwanci, itama hutun take yi, ba zata koma aiki ba sai sun dawo daga tafiya.

A lokacin da zata fita zuwa wajen Abida.

Tana daf da bude kofar ya isa ya rungume ta tsamtsam yana shinshinar gashinta da ya sha gyara.

K'amshinta yake shaka, yayin da ta yi lamo a jikinsa. A duk sadda ya rungume ta gabad'aya gangar jikinta take karɓarsa, haka nan har kan yatsun kafarta take jin shauki na binta

A kunnenta ya yi mata magana a hankali. "Kinsan dai autar momi yarinyace mai giggiwa da son jin abin da bai shafe ta ba. Kada ki sake ki yi hirata da ita. Bana son raini".

Ta kalle shi ta gefen ido a hankali itama ta ce "Tunda ka ke tubewa a gabana, sannan kake yi mini abin da ban yi zatonsu ba ai ka ajiye batun wani girma a gefe kawai".

Ya cizar mata kunne ta shige jikinsa tana zillon ya sakar mata kunnenta.

Ya saki din amma sai ya ce "Maimaita me kike ce?"

Tana jikinsa cikin shagwaba ta ce "Haka kawai ka samu yarinya kana caje ta, kana neman mayar da ita chopping the rice sannan ka ce wai ba zata bawa kawarta labarin yadda ake gurzarta ba?".

Dariya ta k'wace masa sosai.

Ya nisa cikin kwantar da harshe ya ce "Amma dai kinsan raini za ki janyo mini ko?"

A hankali ta ce "Ba wani raini. Nima ta ba ni labarin yadda Yaya Sulaiman yake take ta amma hakan bai saka na raina shi ba".

Ya ce ",Waton dai sai kin cire mini rigar girma ko?"

Kanta na k'irjinsa ta ce "Ba zan fad'a mata komai ba, amma idan ka yi alk'awarin yau barci zan yi tunda ga farkon dare har k'arshensa."

"Ya sumbaci goshinta tare da ce wa "Ban yi alk'awarin haka ba. Amma na yarda sau d'aya zamu yi sai da asuba kuma".

Ta d'ag fuskarta tana yi masa wani irin kallo mai d'auke da anya kuwa?

Ya yi murmushi ya ce "Maigado da gaske nake yi mana, amma idan kika ga an yi to ke ce kika rikita ni ".

Ta zame ta ce"To bari na tafi kada ta ce na yi mata wulakanci."

Ta isa falon da Abida take zaune tsuru ita kad'ai sai k'arar a.c da babatun tafkekekiyar talabijin.

Abida ta mike tana k'ure ta da kallo.

K'warai ta ga Bilki ta k'ara kyau. Dankararen leshin da yake jikinta ya yi matuk'ar yi mata kyau ga shi an zuba masa dinki na gaske.

Ta isa kusa da ita tana fad'in "Abida na dauka fa sara mini za ki yi da kika zabura kika mik'e din nan?"

Abida ta yi maza ta ce "Saboda kin zama matar d'ansanda ai dole a dinga kame miki Haj Maigado Mrs Asad Musa Funtua."

Bilki ta murmusa don tasan gatse ta yi mata.

"To zo mu shiga ciki ".

Bilki ta fad'a tana nufar k'afar benen da yake falon.

Hawan farko suka shiga falo sannan suka shiga katafaren d'aki.

Basu zauna ba sai da Bilki ta cika gaban Abida da kayan ciyeciye da na shaye shaye.

A hankali Abida ta ce "Kin ga wani ja da fresh da kika yi Sola?"

Bilki ta d'aka mata duka a cinya tana fad'in "Na raba ki da sunan nan kada ki hadu da fishin kwamishina fa".

Abida ta ce"Na hadu da shi din. Yanzu Bilki me kike ci kika yi wannan uban canjawa cikin kwanaki uku kacal, me yake ba ki anan wanda mu bai ajiye mana b?"

Cikin iyashege Bilki ta ce "Vitamin A-z nake sha kinsan shine sinadarin gyaran fatar mace lamba d'aya.

Abin da nake ci da sha anan ya banbanta da na gida mana Abida.".

Abida ta kasa ce wa komai amma kallo kawai take bin ta da shi tare da tausayin kanta. Ita kam da tasan hukuncin da Sulaiman zai yi mata ke nan da bata taho Abuja ba, tunda sai da ya ce mata bai barta ba. Ga shi yanzu ya yi mata nisan da bata san inda zata gan shi, don kuwa ita jikinta bai bata ya mutu ba. Ga wata irin matsananciyar soyayyarsa da take yi mata mahangurba.

Kan dole ta sanya jarumta ta danne kukan da yake neman kubuce mata.

Bilki ta je ta rufe kofar d'akin Har da murza mukulli.

Ta dawo ta ce "Magana zamu yi heart to heart Dr Abida."

Ta zauna daf da Abida har jikinsu na gogayya, ta yi k'asa da murya ta ce "Ba da shakiyanci ba Abida! Fad'a mini a likitance akwai illa ne idan ana yin harkar na ta baki?"

"Abida ta kalle ta da dukkan nutsuwarta amma sai ta shiga rudu tare da kasa gane manufar Bilki kaitsaye.

Murya ba amo ta ce "D'an sake bude maganar ta yadda zan fahimta har na yi miki bayanin da zai gamsar da ke."

Kan Bilki na k'asa ta ce "Ba'a ance miji ya zowa matarsa duk ta inda yake so ban da ta bayanta da kuma idan tana jinin al'ada ba?"

Abida ta ce "Hakane ".

Kan Bilki a k'asa bata yarda ta dago ba ta ce "Shine nake son na ji ya ya matsayin yin harkar ta baki?"

Abida ta dinga kyalkyala dariya mai k'arfi mussaman da ta ga Bilkin da dukkan zuciyarta take neman fatawa akan lamarin, kunya kuma ta hana ta d'ago su kalli juna.

Har Abida ta yi dariyarta mai isar ta bata katse ta ba, kuma bata ce komai ba.

Da kanta ta numfasa ta ce "Maigado fatawar addini zan yi miki matashiya ko kuwa ta likitanci.?"

Murya ba amo ta ce "Duka Abida ni gabad'aya na shiga rudun ne. Kin san kanki yafi nawa ja, tuna mini ma na islamiya din".

Abida ta zama serious tunda ta gasgata da gaske take yi a rude take. Amma k'asan zuciyarta sai mamaki take yi duk shekarun da Bilkisu ta shafe a gidan aurenta bata taɓa sanin oral sex ba sai yanzu?

Ta numfasa ta ce "Bari na fara yi miki bayanin a mahangar musulunci a takaice"

Bilkisu ta gyada kai tabbacin tana sauararen ta.

Abida ta fara da ce wa "Malaman da suke ganin halaccin saka al'aura a baki sun yin haka ne saboda babu wani dalili bayyananne a cikin Hadisi da Alqur'ani da ya haramta irin wannan aiki. Malaman musulunci irin su Yusuf al-Qaradawi suna da wannan ra'ayi!

Haka nan kuma ba a ambaci wannan aiki a matsayin wani bangare na farfaganda ba a Hadisi, duk da cewa Musulunci ya jaddada muhimmancin aika d'an sako kafin fara mu'amala tsakanin ma'aurata kamar su sumbatar juna da tabawa da makamantansu da suka zo a Hadisi k'arara. Mazhabobin tunani (Mazahib) irin su Shafi'i da Hanbali sun dauki hakan a matsayin halattacce, sannan a matsayin wani bangare na yin wasannin da zai ƙara armasa mu'amala. Yayin da wasu mazhabobi ke daukar al'aura a matsayin najasa, suka haramta yi ta baki."

Da k'yar Maigado ta d'ago ta ce"Na fahimta to menene hangen likitoci kuma?"

Abidan ta nisa ta ce "A likitance ana iya yin mu'amalar ta bakine muddin babu wata cuta a al'aurar ma'aurata wadda baki zai iya kamuwa da wani ciwo sanadin hakan, sannan kuma babu rauni ko kuraje a wajen!

Likitoci na ba da shawarar amfani da kwaroron roba ko dam É—in hakori kafin yin kowane nau'i na jima'i na baka.

Amma gaskiya mutane basu karbi amfani da wannan abubuwan ba ko kad'an. ".

Bilki ta ce "To shike nan na gamsu na kuma fahimta".

Abida ta ce "Amma ba'a son idan har za'a yi mace ta bari a dinga tura mata har makwogaronta don kuwa tana iya kamuwa da infection din baki mai tsananin gaske wacce take rikidewa ta koma( Oropharyngeal)

Sai dai maza sun fi mata had'arin kamuwa da cutar Oropharyngeal (tana kasancewa tsakanin wasu kofofi biyu ta makogwaro) .

Idan har miji zai saka bakinsa a wannan wajen a tabbatar an tsabatce wajen sosai mussaman yadda halittar mace take da lungu da loko!

Zaku iya yin abinku amma ki tabbatar kina tsabtace wajen da kyau, ke kuma kada a dinga kai miki har makoshi sannan kada a tsananta yinsa babu kakkautawa. Anfi son yin mu'amalar baki once in a while kin ga ne?"

Bilki ta ce "Na gane sai dai ai shi din ne kuma, ko zai yarda? ".

Abida ta ce "Ban ce kada a yi gabad'aya ba, amma kada ya wuce harshe da lebenki da zagayen bakinki. Kada a dinga yi har can cikin. Sannan ke ma ki tsananta kula da wajenki. Sai kuma a takaita yinsa ya zama a marmarce ta yadda ba zai zama kullum ba."

Gyada kai kawai ta yi tabbacin ta ji.

Ta ce "Farha ta daina kukan nema na?"

Abida ta ce "Jiya ma ta yi, yau dai ban tashi ba suka tafi makaranta. Amal da Noor suna d'an lallashinta.

Abida ta bude maltina ta sha ta kalle ta ta ce

Wato shanye abin da yake zuba miki kike yi shiyasa kika ce mini vitamin A-z?"

Bilki ta mik'e tana fad'in "Kin baci Abida maganganunki sun fi k'arfin kunnuwana."

Maimakon ta yi shiru sai ta ce "Yanzun saboda Allah shi Sahalun ashe kansa a duhu yake ko kuwa tsabar mugunta ya sanya bai taɓa jiyar da ke dad'i mai ratsa kwanya ba?".

Bilki ta zuba mata ido ta rasa abin fad'a.

Abida ya zarce da fadin ko da yake "Gwara hakan kin ga yanzu ai kin banbance mazan ma daban daban ne, na tabbatar kuma cikin k'ankanin lokaci yayana zai sa ki fara jin haushin soyayyar da kika yiwa wanccan yaron.

Ba za'a d'auki lokaci mai yawa ba, za ki fara jin kunyar kiyayya muraran da kika dinga nuna masa tunda yana caje mini ke da kyau da kyau".

Kan dole Bilki sai da dariya sosai ta k'wace mata tana fadin"Ba dai zan ce miki komai ba".

Sai gaf da magariba ya sauko daga samansa wanda shine a k'ololuwar k'arshe.

Har dakin da yake jiyo muryoyinsu ya shiga da sallama.

Abida ta amasa sallama tana kuma gaishe shi.

Ya amsa yana ce wa "Autar momi sai yau kika zo mata?"

Ta ce "Yau din ma ina laifi?"

Ya kalli Bilki ya ce "To na fita masallaci sai na dawo. "A tausashe ta ce "A dawo lafiya".

Daga haka ya fice.

Abida ta dinga fad'in kin ga mutum ya washe ya k'ara k'uruciya wa ma zai ce ba sa'an aurenmu ba ne ? Oh oh Yaya Asad duniya ne, ya ga y'ar yarinya ta ji kayan aiki, shine ya rik'e wuta sai da aka kawo masa ita yake yin yadda ya ga dama da ita. To ki fad'a masa na ce ya batun motar tawa, na ji shiru fa. Tunda ya same ki sai ya cika alk'awarin da ya yi mini."

Bilki ta zabura ta ce"Gaskiya ciccibin nan yana da kyau fa Abida gabad'aya fa na hade na ciko".

Abida ta ce "Gaskiya kayan Bojuwa herbs ba algush, gangariya ne na shaida hakan

Contact 08032773332 for all your kayan mata.

Bata tafi ba sai da ta yi sallar magariba sannan ta tafi a gaggauce.

A harabar gate ta iske shi.

"Yaya ya batun motar tawa ne?"

Ta tambaye shi kaitsaye.

"Tana daf da isowa Abida ai kinsan bana alk'awarin bogi"

Ta ce "Hakane".

Ya kasa sakewa da ita kamar da, domin sai yake ganin sun gama yin gulmarsa da Bilki tunda mata suna son hirar oza room.

Cikin kwanaki biyar da suka yi suna cin amarci Bilki ta san ta auri jarumin maza kuma sadauki ji da ita yake yi kamar tsoka daya a miya ba ya fita ko'ina sai masallaci har wayoyinsa ya kashe abinci kuma safe da rana da yamma Abida ke aiko musu da shi daga gidan Momi.

Bilki ta samu nutsuwar jiki da ta zuciya cikin sati daya a gidan Asad.

Sannan ta gane zaman da ta yi a wanccan auren kusan zaman lalata kuruciya ne kawai.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: [Sep 15, 2025 at 21:55]

A haka suka tafi k'asar America.

Soyayyar da ya nuna mata da gata ya sanya ta fara jinsa a ranta ta dinga tuno lokacin da suka je hutu gidansa daidai haihuwar Bilkisu. Yadda yake shiga kicin ya yiwa kansa abinci a dalilin matarsa na da tsohon ciki. Tabbas yana cikin maza kadan da suke yiwa mata hidima da zuciyarsu da aljihunsu. Don a yanzu ma da ya girma bai fasa komai ba. Tana zaune sai ya hado musu coffee ko ya shiga kicin ya hado musu abin motsa baki dangin fruits ya kawo gabanta.

Yawan motsa jikin da ya rayu akansa ya taimaka masa don kuwa bai tara teba ba, sannan kuma a tsaye yake kan k'afafuwansa ga kuzari da hanzari tunda ya rayu yana motsa jiki.

Idan ya fita Allah Allah take yi ya dawo ya dinga damuk'arta, yana yamutsa ta tana jin dad'i har cikin kanta, abin da bata samu a inda ta zaci zata samu ba, take samunsa a inda ta yi zaton ba zata samu ba.

Amarci gangariya suke zubawa wanda Bilki bata taɓa zaton ana samun irin haka ba. Shi kansa a zuciyarsa yake tambayar kansa wai mata dama ko wacce da irin taste dinta ne ko kuwa dan ita Bilki tafi matarsa k'uruciya ne? Gabadaya ji yake tamkar yanzu ne yake samun gamsuwa da nutsuwar da yake so. Har cikin bargonsa yake jin son Bilki irin yadda bai taba ji akan kowacce mace ba.

Na ce ba? Kina nan kina ta yin tashin hankali akan namijin da idan kin mutu wata zai aura ya sota kamar yadda ya so ki koma fiye da ke har ya manta da soyayyarki? Dan Allah mata mu yi ibada, mu yiwa mazanmu biyyaya iyakar iyawarmu don kuwa aljannar mace zata fi gamsu ne idan mijinta ya amince da ita. Mu rungumi sana'a ko aikinmu da kyau a sassauta soyayyar da zata saka matsanancin kishin da zai hanamu sukuni ya halakamu. A guji canja halitta da nufin burge rijalu! Wallahi ba abin da zai sauya su daga zama polygamist. 😅

Kwanaki ashirin ya kammala aikin da yaje yi k'asar. Suka k'ara kwanaki biyar suna yawon bude ido a cikin birnin California.

Daga nan kuma suka wuce London ta k'asar Birtaniya.

Kwanansu biyu a garin suka kaiwa Khadija ziyara makarantarsu. Itace kuma Bilki ta d'ade bata ganta ba a cikin ya'yansa, tun tana karama sosai. Kallo d'aya tak ta gane yarinyar ta juye Babanta sak ba abin da ya rabata da shi na kammani har hanzarinsa ta kwashe. Aysha da Amal ne suke kama da uwarsu. Sauran yaran kuma gasu nan ruwa biyune. Amma Noor ma kam kamarsu d'aya da Khadijan.

Da walwala ta karbesu da girmamawa. Bilki ta ji dad'in girmamata da ta yi. Ta kudire a ranta zata iya kokarinta ta basu fuskar da zata zame musu uwa, su kuma shigo gidan ubansu ba tare da zullimin babu uwarsu ba.

Ya ce tunda a hutu take ta zo su tafi masaukinsu. Cikin mintina kad'an ta fito janye da k'aramin akwatinta.

Basu koma masaukinsu na sai da Khaditta jagorance su zuwa gidan abincin da suke da halastaccen abinci (Halal food).

Daga nan suka koma hotel din ya kamawa Khadija d'akinta wanda tazarar gaske da nasu d'akin.

Sosai suka huta suka sha hotuna wanda Khadija take yi musu wani sun sani wani ma kawia daukarsu take yi basu ankara ba.

Zamansu na London ta fahimci Baban Bilkisu mai tsananin son ya'ya ne. Don kuwa asuba yake k'iran Khadiha ya ji ko ta tashi sallah. Idan zasu koma barci bayan sun idar sai ya sake k'iranta yana fad'in "Idan kin ji yunwa ki yi order duk abin da kike son ci kada ki ce sai kin jiramu". Idan sun tashi, sun yi wanka sun shirya sai sauka k'asa ta fito su hadu sannan a wuce wajen karya su karya tare.

Sannan kuma ta fahimci shi mutum ne mai yin abu babu nuku nuku ko cutar da kai don idan Khadija zata yi musu hoto ita ce take nuna masa yadda zai tsaya ko zai rik'e Bilki. Ya yi kuma yadda ta ce din babu jin nauyi ko kunya. Haka itama yake rungume ta Bilki ta yi musu.

Ana jibi zasu bar London Khadijah ta ce "Dady zamu je gidan Anty Ayusha fa na fad'a maka tana mini kirki, Ina zuwa na yi weekend a gidanta, k'asan idan y'an arewa muka hadu a turai duk zama muke yi dangin juna. Ita da mijinta suna mana kokari suna guiding dinmu sosai."

Ya ce"To zuwa anjima idan mun je yiwa sisters dinki tsaraba sai mu je gidan".

Sosai Khadijah da Bilki suka saba suka samu kyakkwar fahimta duk da Khadija tana yawan tuna mominsu tare da jin da yanzu itace a gefen Dady ba Anty Maigado ba. Sannan yadda yake zumudi akan amaryarsa ta gane ko momi na da rai zai iya nad'e k'afar wando ya yi zawarcinta har ya aure ta duk rikicin da za'a yi kuwa. Amma ta danne don kuwa gara ace auren ya yi da ace Babansu na harkar banza da zubar da mutuncinsa da nasu.

K'arfe biyar saura na agogon GMT Ummi ta karbi ziyarar manyan baki cikin sa'a suka tarar da Baban Husna a gida dan haka da karramawa ya karbi kwamishina a falonsu. Cikin mintina kad'an aka cika gabansu da cimaka iri iri. Sosai ya yi musu godiyar yadda suke kula da su Khadija suka basu kofar zuwa wajensu. Ya yiwa yaransu kyautar bajinta sannan suka tafi. Bilki tana yaba kirkin Ayusha da mijinta tare da yiwa Husna, Hanan da Aryan addu'ar su zama masu albarka.

Fatan alheri ga kanwata marubuciya Ummi Ayusha Muhammad da iyalinta da suke zaune a birnin London.

Washegari suka mayar da Khadijah makaranta suka yi bankwana suka rabu cikin sanyin jiki don sun ji dad'in zamansu taree que ne illa tuna mominsu shike nan su da ita sai a darussalam. Ta dinga yi mata addu'o'in neman gafara har ta samu nutsuwar zuciyarta.

Ta dauki wayarta ta shiga what'sapp ta shiga ta tura hotunansu cikin group dinsu da Aysha ta bude musu su kad'ai. Su hud'u ne a ciki Aysha Khadija Hafcy sai Bilkisu tunda itama da wayarta Amal da Noor ne babu su.

Cikin mintina kad'an Aysha ta yi tagging hoton Bilki da Babansu ta ce amma kuwa Khadija kin ci amanar momi da kika turo mana wannnan abin, na rantse tunda na zo duniya ban tab'a ganin abu mai muni a zuciyata irin wannan pic's din ba. Yanzu Dady abin da ya zama ke nan, ji yadda ya wani mak'ale ta? Ke kuma da yake sarai sunanki shine har da turo mana?"

Hafcy ma ta ce "Yaya Khadijah kam ai gabadaya al'amarinta babu kishin kai ".

Bilkisu dai stickers din dariya take ta turawa babu adadi don gabad'aya Dady ne ya bata dariya yadda yake sanye da k'ananun kaya ya dawo kamar saurayi yana ta soyewa abinsa.

Aysha kuwa ta kufula ta zazzage ta tare da fad'in zata cire ta daga group din tunda take dariya bayan abin kuka ne ya same su.

Khadija ta ce "Ya Aysha ki yi hakuri Anty Maigado bata da damuwa. Da ya auro wacce bamu santa ba ta zo ta cutar da shi muma ta cutar da mu fa? Ai gara ita duk tsiya dai y'aruwarmu ce".

Nan da nan Aysha ta danna voice na tsawon lokaci tana fad'in "Ta ina ta zama danginmu? Sun kai Baba Babba fa kotu? Sannan an ce za'a ba shi anty Laura don ta cigaba da kula da su Noor tunda sun saba da ita amma fir ya k'i ta. Sai kawai ya kwaso mana wannnan mai tafiya mazaunai na sittin, saba'in, sannan yanzu na gano tuntuni ya so aurenta tunda har mai suna ya yi mata." Ta fara kuka murya na rawa ta ce"Na tausayawa poor momi! Allah sarki ta sha wahalar haihuwa an tashi an sakawa d'iyarta sunan budurwa wohoho me za'a ce da maza ne?"

Ta kammala cikin tsananin kuka.

Khadija tana kwance tana sauararen Aysha jikinta ya mutu tabbas itama ta ji babu dad'i amma kuma ya zasu yi ne tunda ba zata dawo ba, sannan basu isa hana shi yin aure ba. Kanta ya kulle mussaman ita bata ga aibun Anty Maigado ba. Sannan zuwansu duk abin da zai yi mata baya shawara da matarsa kawai bata yake yi, kuma bata ga ko a fuska Anty Maigado tana jin babu dad'i ba. To shi ke nan duk kokarinsa na ya faranta musu, sai kuma su k'i kwnatar masa da hankali ta hanyar zama lafiya da matarsa. Ta kuma fahimci Aysha tana son jagorantarsu su musgunawa matar Babansu ta yadda zamanta da shi zai gagare ta.

A sanyaye ta yi nata voice din da fad'in Momi is gone ba zata dawo ba forever. Mu yi hak'uri mu zauna da matar da Dady ya aura da girmamawa dan yasan mun gode da hidimar da yake yi da mu babu gajiyawa. Idan ya gane muna da damuwa da matarsa zai kasa samun nutsuwar da ta dace da shi. Don haka mu yiwa Momi addu'ar samun rahamar Ubangiji shine abin da tafi bukata. "

Nan da nan Aysha ta ce "Hidimar da yake da mu ashe ba Allah ne ya kallafa masa ba? Tunda ke ba kya kishin uwarki sai ki k'arata ke kad'ai sannan kada ki kuma turo mana wannnan bak'incikin!

Hafcy ta yi tagging da fad'in "Wlh kuwa Yaya Aysha duk yadda nake son matar nan yanzu haushinta nake ji, tunda ta yi kuskuren auren Dady ai ba sauran girmanta a idona tamkar mai jiran momi ta mutu ta aure shi".

Bilkisu dai bata ce komai ba sai dai ta shiga tunanin maganganun yayarsu na cewa saka mata sunan anty Maigado ma

cin amanar mominsu aka yi.

Daga haka Khadija ta sauka daga what'sapp din tare da tunanin Aysha zata d'agawa masu gidan hankali dama ita bata da dad'in mu'amala.

Yayin da Aysha ta dinga jan kunnensu Hafcy saura su ce zasu shige mata.

Tirk'ashi.

Ranar juma'a da daddarre suka sauka a birinin Abuja suka tarar da tawagar y'an sanda na dakonsu.

Har gida aka kawo su.

Ita dai Bilkisu tana kallon yadda ake ta k'ame musu tare da sarawar girma.

Wannan nau'in gaisuwar na matuƙar yi mata dad'i a zuciyarta.

A daddafe suka yi wanka da ruwan zafi sannan suka yi salla suka kwanta barci ya yi awon gaba da su don sun gaji lik'is.

Da yake asabar ce da suka yi sallar asuba sake rungume ta ya yi suka koma barcinsu. Sai wajen 12 suka farka. Suka yi wanka sannan suka nufi kicin don karyawa don kuwa a cikin katafaren kicin din dainin eriya yake.

Tuni an tanadar musu abinci kalakala na alfarma. Da kansa ya zuba mata sannan ya zubawa kansa. Ita dai cikin tsantseni take cin abincin duk kuwa da ba shi da makusa kawai ita yadda duka ba musulmai ba ne suke yi musu abinci ne ya dame ta.

A tausashe ta ce "Baban Bilkisu mu je gida anjima mu gaida su Baba daga nan mu dauko yara da Alti".

Ya girgiza kai tare da fad'in "A a Sai na gama hutuna zasu dawo".

Ta zuba masa ido ta ce "Baban Bilkisu ka ce mini fa za'a sake baka hutun tafiyar da ka yi na sati biyu. Kuma yanzu sai mu yi ta zama haka?".

Ya zuba mata ido cikin wani irin salo ya ce "Ba za su dawo su dinga katse mana amarci ba. Dan haka gobe zamu je mu gaishe su amma ba da yara zamu dawo ba".

Ta yi k'asa da kanta don har zuwa lokacin nauyinsa da kunyarsa basu gama barinta ba. Ya cigaba da kallon yadda ta sake yin fari, fatarta ta yi wani irin smooth na ban mamaki. Zuciyarsa ta harba da sauri don kuwa ta sauya sosai wanda bai lura da hakan ba sai a lokacin.

Zuciyarsa ta amince masa cikine da ita don gabad'aya ta danyace ta sake zame masa yarinya sosai.

Ya tafi lissafin aurensu idan har daidaine suna cikin sati na bakwai don anyi bikin da sati biyu suka tafi America. Sun shafe satika biyar kafin su dawo, ke nan suna daf da shiga watanni biyu. Zuciyarsa ta cika da farinciki a duniya yana son yara yana son ya'ya da yawa. Tun kafin ya tabbatar da zatonsa ya ji son abin da yake cikinta yana ratsa shi ta ko ina.

Ya tausasa harshe ya ce "Me yasa kike son su dawo tun yanzu?".

Cike da tab'ara ta ce "Gaskiya ban son abincin wannan matar na fi son na Alti".

Ya yi shiru tare da tunanin yadda shi da iyalinsa suke son girkin charity mussaman ya rabota da hotel d'in da take aiki ta dawo zama a gidansa gabad'aya. Tana da d'akinta a sashin y'an aiki. Ya numfasa ya ce"To kafin su dawo ki dinga yi mana dan gaskiya ba zan yarda hankalinki ya kasu biyu ba a wannan kwanakin. Kawai ki bari na kammala cikace su".

Ta rausayar da kai ba tare da ce masa komai ba domin duk zalamarta akan al'amarin yayan nata ya k'ure ta. Matuk'ar ya mu'amalance ta sai ya gurje ta da kyau.

Ta fara jinsa cikin zuciyarta, duk wani kallon da ta dinga yi masa a baya na baibai ya fara gushewa daga idanuwanta. Ta gasgata Abida da take yawan fad'a mata bak'in namiji ba shine muninsa ba, sannan yayansu ba mummuna bane kawai dan ta rufe zuciyarta akansa ne. Yanzu kam ta amince ba mummuna bane sannan tabbas jarimi ne ko cikin jarumai.

Washegari sai yamma lis ya dauke ta zuwa gidansu, da ledar tsarabar mutanen gidan. Da kansa yake tuki, yayin da take gefensa a zaune. GabaÉ—ayansu sun yi kyau na ban mamaki. Sassanyen k'amshi na tashi a jikin kowannensu.

Da farinciki sosia Baba Babba ya gaisa da su yana jin auren Asad da Bilki ne tsanin yin sulhu a zuri'arsu don kuwa ya lura ya'yan Baba k'arami gabad'aya basa iya yin mu'amala mai yawa da shi da ya'yansa dama Bilkin ce tafi sassauci. Yanzu kuwa saboda ita zasu yi mu'amala da gidan Asad daga haka kuma har komai ya warware albarkacin addu'ar da yake yi a kullum na kada zumuncinsu ya waste gabad'aya.

Ya dinga sanya musu albarka tare da nasiha mai ratsa jiki. Yayin da tausayinsa ya kama Bilki ya tsufa sosai gabad'aya rauni ya baibaiye wanda ba na rashin gata ba ne illa na rashin cikakkiyar lafiya da kuma rauni irin na gajiya da duniyar da tashin hankalin da yake cikinta.

Suka ajiye masa tasa tsarabar wnada jallabiyoyine fararen sai turaren alfarma.

Haka momi ta dinga yi musu addu'a cikin bayyananen farinciki.

Ta yunk'ura a hankali ta yi ciki wajen yaran tare da adduar Allah yasa Abida na gida.

Dakin Abidan ta fara shiga ta tarar da ita kishigide a gadonta junior na kwance jikinta yayin da Farha ke can gefe a zaune tana cin cookie's. Amal da Noor kuma na kan kafet suna game a tablet.

Farha na ganinta ta zabura ta mik'e ta nufe ta a guje. Yayin da Bilki ta yi yunkurin d'agata amma ga mamakinta sai ta kasa. Mamaki ya rufe ta don ba wani girma Farha ta k'ara ba haka nan ba nauyinta ne ya k'aru ba. Kan dole ta hak'ura ta rungume ta tare da jan hannunta suka zauna bakin gado. Ta kalli yarinyar ta ga idanuwanta sun cika da k'walla ta ce "Menene?"

Muryarta na rawa ta ce "Mahma na dauka nima guduwa mini kika yi kamar yadda muka gudo muka bar su Yaya a Katsina".

Jikin Bilki ya yi sanyi. A tausashe ta ce "Amma ai na sha fad'a miki ce wa "Duk inda zan je da ke zan tafi mutuwa ce kawai zata rabamu".

Ta goge hawayen idonta tare da rik'o hannun Bilki ta ce "Dan Allah Mahma to zan biki yanzu ni dai na gaji".

Ta fashe da kuka sosai.

Bilki ta jata jikinta ta ce"Zan zo na d'auke ku tare da su Noor next week inji dadynsu ke ma yanzu shine dadynki".

Ta yi shiru can ta ce "To dadynmu na Katsina fa?"

A hankali ta ce mata "Dadynki ne mana. Amma tunda zamu koma gidansu Noor to ba uncle za ki ce dinga ce masa ba sai Dady".

A hankali ta ce "To! Amma dai Mamah yau zan biki gaskiya. Junior ya yi ta tsokanata amminsa ta hana ni dukansa, su Noor ma su dake ni Ammi sai ta ce ",Ni na tsokanesu na rufe bakina na dame ta da kukan shagwaba. Alti ce kawai take kula ni".

Na jijjiga kai na ce ki yi hak'uri idan kuka dawo gida ba zan bari su dinga dukanki ba, amma ke ma ban da rashin kunya tunda basu Yaya Amrah bane da basa iya dukan ki".

Abida ta jijjiga kai ta ce "Duk yadda ake kaffa kaffa da ita ki ji sharrin da take hadawa?".

Bilki ta yi murmushi kad'an ta ce "Ke dai Abida ki yi shiru amma Farha bata karya kawai kina bawa d'anki kariya idan ya tsokane ta.

Abida ta jijjiga kai tabbacin mamakin yarinyar ya yi matuk'ar kamata.

Daidai lokacin su Amal suka iso kusa da ita suna fad'in "Mahma sannu da zuwa, ina yini tare da Dady kuka zo?"

Ta mik'a musu hannunta suka rik'e ta amsa da fad'in "kuna lafiya? Dady na falo".

Suka fice da azama ta bude hadaddiyar jakar hannunta da ta siya wajen umm asalan Egyptian items.....

Ta fito da tissue ta gogewa Farha hawayen idonta cikin rarrashi ta ce "Oya je ki gaida Dady ki yi masa welcome kada ya hana ki tsarabar da muka siyo miki ".

Ta sauka da sauri ta fice.

Sai lokacin ta mayar da hankalinta ga Abida da ta lura ta kafe ta da kallon k'urillah.

Murya ba amo ta ce "A a Abida wanne irin kallo ne haka ne?"

Da dariya ta ce "Ga ni na yi tamkar cikine da ke Maigado".

Zuciyarta ta tsinke don kuwa ita da kanta tana k'alubalantar sauyawarta tashi guda. Sannan kasala ta dabaibaye ta. Kasa d'aga Farha d'azu ya sake jefa mata shakku a zuciyarta. Duk da bata da tabbas din cikin ne.

Ta nisa ta ce "Daga dan zamanmu ne har za ki fara yi mini batun cikin Abida? Inace ban gama rufa watanni biyu da auren ba?".

Abida ta watsa mata wani irin kallo ta ce "ko jiya kuka tare sai ciki ba zai shiga ba? Wannan gagarumar sauyawar da kika yi fa, ko duk vitamin A-z din da yake zuba miki a baki ne?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 15, 2025 at 22:07]

Wata irin kunya mai yawa ta dirar mata.

Ta yi maza ta yi k'asa da kanta tare da fad'in "Allah ya shirye ki kawai".

Abida ta kyalkyale da dariya tana fad'in ".Yaya Asad ya hada wata da aiki nan da watanni zamu ga sakamakon da zata ba shi.

Kafin Bilki ta ce komai, Alti ta turo kofar da hanzari bakinta d'auke da sallama.

Bilki na ganinta ta yi karfin halin mikewa da sauri suka rungume juna.

Abida ta kallesu tana jin babu yadda za'a yi ta yarda ta had'a jikinta da na y'ar aikinta duk da dai Bilkisu ta yi matuk'ar yiwa Alti wanka babu wani abin aibu ko na k'yama a tare da Altin.

Sakwanni biyar suka saki junansu dukkansu fuskokinsu d'auke da bayyananen farinciki.

Alti ta zauna a gefen kafet yayin da Bilki ta zauna a inda take zaune.

Suka gaisa cike da karrama juna. Jimawa kad'an Alti ta fice.

Jummai wacce yar kabilar Nufe ce ta shigo d'auke da tiren ruwa da lemo ta dire a gaban Bilki sannan ta durkusa cikin gurbatacciyar hausarta ta ce "Anty barka da yanzu, sannu da zuwa".

Bilki ta amsa da fad'in "Ba hausa mun same ku lafiya?"

Ta murmusa ta ce "Lafiya kalau Alhamdulillahi Anty.

Sannan ta fita. Jummai zata yi shekaru ashirin da biyar ta taba aure har da yaranta biyu suna can garinsu a Bidda a wajen Babansu, tunda suka rabu. Tun kafin a yi mata aure take hannun marigayiya Rukayya sosai ta iya gyara babu gajiya, haka nan ta iya girkin gargajiya daban daban dan idan tana yin sakwara sai ka zaci ba da hannu ake yi ba. Sannan ta iya rainon yara da juriyar fitinarsu. Amal da Noor sun yi matuk'ar shak'uwa da ita. Shiyasa har yanzu take nan tana kula da su.

A zuciyatar Bilki ta kudire Alti da jummai kawai sun ishe ta amma charity sai ta bar gidan ba zata zauna ahalil kitabu na yi mata girkin abinda zata ci ba.

A matuƙar sanyaye Abida ta ce "Yanzu Maigado ba za ki tausaya mini ki fad'a mini gaskiya akan Yaya Sulaiman ba. Ke ko tausayina ba kya ji. Dubu yadda vitamins din da ake zuba miki na watanni biyu kacal ya mayar da ke amma ni kullum k'ara baki nake yi ina yamushewa, sai na bude baki na fad'a miki ina da buk'atar a zuba mini ne?"

Dariya ta subucewa Bilki ta sosai. Ta numfasa ta ce "Allah Abida kalamanki na kashe ni da kunya. Amma fa watannin baya na yi miki rantsuwar ban san inda yake ba. Wallahi tunda ya tafi ban sake ji daga gare shi ba."

Hawayen nadama suka k'wacewa Abida babu zato. Cikin rishin kuka ta ce "Na gaji Bilki, Wallahi na gaji, ni kam na shiga ukuna".

Tausayinta ya kama Bilki sosai ta matsa kusa da ita ta rik'e ta. Murya a dakushe ta ce "Sannu Abida ki k'ara hak'uri mu cigaba da addu'a da ikon Ubangiji idan yana raye zai bayyana.".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.